Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace " lafiya lau kawai yarinyar tayi min kama da wata ƙawata da ta rasu ne wlh shine fa da na ganta se na tuna da ƙawata ,mutuwar ne ta dawo min sabuwa "ayya Allah ya gafarta mata "suka haɗa baki " Ameen ,zan shiga ciki ina bukatar hutawa zamuyi magana anjima .........



*Kwana biyu nafara* *ƙyiuwar typing kuyi* *haƙuri pls*


*Comments and share*


Real Bazamfaria ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:1️⃣8️⃣


Yau kam jiki babu kuzari Meerah ta shiga ,gida ,ƙarin sayin jikin ta ma da ta samu Yaya Labaran ya dawo ,a tsakar gida ta samesu dan haka ta ɗan zauna suka gaisa ,kafin ta shiga daga ciki
Bayan ta wuce ne Yaya Labaran ya kalli Aunty yace " wai Nafisa lafiya Ameerah take kuwa se nake ganin kamar tana cikin damuwa tunda ga yanayin gaisuwar da tayimin zan iya fahimtar hakan ,wai daga ina ma take tun ɗaxu nike tambayar ki se kwana-kwana kikeyimin.

Ayya,Yaya na faɗa maka ta je gidan ƙawarta ne kuma ma bata daɗe da fita ba kaikuma ka shigo ,maganar damuwa kuma ,xe iya zama ko yau da gobe ne kasan sha'anin rayuwa ,amma dai lafiya lau muka tashi a gidan nan zan tambaye ta ko akwai abinda yake damunta ne zuwa anjima .

Tashi yayi yana saka takalmin sa " to shikenan ni dai zan fita se zuwa dare ko zan dawo dan zan zazzaga ne kinsan na daɗe wanan karon banzo ba tun a mota,su Kabiru suke kirana "adawo lafiya, ka gaishe su

Yana fita Aunty ta tashi da sauri kitchen ta shiga ta ɗaukowa Ameerah abincin ta ,a zaune ta sameta tayi tagumi da duka hannunta biyu ,tayi nisa sosai a duniyar tunani,Aunty ta ta bata ,sauke ajiyar zuciya tayi tace " Aunty kece ,zauna mana "ta faɗa tana matsa mata gefen katifar ta ,zama Aunty tayi ,tana kallon ta batace da ita komai ba har tsawon lokaci seda ta gama nazarin ta " Hajia saudah tazo ne? Da sauri ta kalli Aunty cikin mamaki tace " ya akayi kika san haka? Murmushi tayi tace " iya wannan firgicin da kike ciki ya isa sanar dani cewar fuskar Hajiya Sauda ne ya samar dashi a xuciyar ki ,sedai tambaya na anan taya hakan ya faru ,bayan nasan Ameerah bata da tsoro musamman ga abinda ta saka a gaba? .

"Hmmm Aunty bazaki gane bane nifa ba ita bace ta saka ni jin tsoro ,kawai dai yadda suke neman maida zancen wani iri Hajiya Sauda ta ganni shine ta firgita ,a tunanin ta ko Yaya Maryam ce ,to shine fa sukace wai sedai idan ni mayya ce taya ma za'a ce daga ganina ta rasa hankalin ta daƙyar Allah ya temakeni ,ɗan ɗan gidan ya shigo ,yace na tafi ,dan na rasa yadda zan wanke kaina ,saboda wlh nima firgicin da ta shiga ya bani mamaki ,dan ba wannan nike so ba nida nikeso na shiga jikinta ,to idan tayi sanyi ² dani ai komai xe lalace min.
" Hajia saudah bazata taɓa ganin ki ta kasa tankawa ba ,dakuwa bata ɗauke ido ga yara mata bare ke ,kawai dai yanxu tayi shock ne da ganin ki amma ina tabbatar miki cewar ,kafin gobe tunanin ta ze dawo ke kuma se kisan yadda zakiyi da ita "yawwa Aunty sega yaya ya dawo duk na tsorata yanzu ya za'ayi na rika fita daga gidan nan "Ameerah nima tunanin da nike kenan sema Kinga yadda ya tsareni da tambayar ina kike ,kuma na fahimci kamar be gamsu da cewar da nayi gidan ƙawarki kika je ba,wai yasan baki damu da zuwa gidan kowa ba " akwai matsala kenan Aunty " karki damu Insha'Allah zamusan yadda zamu tsara sa ,kici gaba da tafiya ba tare da yagane ba ko ? da sauri Meerah tace " me kike tunanin samu sanar masa ya yarda kinfa san halin yaya ,akwai saukin kai kam amma ,a irin wannan baya sanya ,ni wlh nafara jin na sare akan lamarin nan Aunty " badai nice nace kibarni dashi ba to ai nasan me zan faɗa masa kedai kiyi ƙoƙarin cire damuwar nan a fuskan ki saboda kar ya sake zargin wani abun.

"to shikenan Aunty Insha'Allah bama ze gane komai ba

Rufaidah#

da dare Hajia saudah na shirin tafiya ɗakin Abba ,kasan cewar yanada ɗaki a kowane party ,kuma taji shigowar sa tun ɗazu dan haka take shirin tafiya ,seda takammala komai kafin Rufee tace "am Mama wurin Abba zakije? Kallon ta Hajia saudah tayi tace "ko akwai damuwa da hakan ne" a'a Mama kawai dai naso mu ɗanyi magana ne "ta faɗa tana sosa kai ,dawo wa Hajia saudah tayi ta zauna ta ce " ina jinki "Mama dama da baki nan ne Abba yakemin magana akan aure ..."se kuma tayi shiru " go on ina jinki ,kinada wanda kike so kenan?Ehhh Mama sedai yadda naga Abba ya nuna tare yakeso ya aurar dani da Rumaisa ne abun beyimun ba , kinyi alƙawarin idan na tashi aure za'ayi bikin da ba'a taɓa yinsa ba a garin nan ,to me yasa zece wai ayi tare da su salon munafurci ne kawai Mama wlh sekinga irin abubuwan da sukayimin da ba ki nan ,Abba ma se faɗa yakemin ,wai inada baƙin hali " ajiye zancan su a gefe maganar haɗa bikin ne dai ko ni bazan lamunta ba to hala itama ta samu me so ne? Taɓe baki Rumaisa tayi tace "ni ina zan sani kinsan ba shiga sabgar su nikeyi ba " washe baki Hajia saudah tayi tace " to ke wa kika samo mana ,danfa har munso mu haɗaku aure keda yaron Hajia Sa'a"ashe Allah ya tsare dai ban amsa ta kai tsaye ba nace se na tuntuɓe ki ,ashe ma ke kinada wanda kike so ,to waye kuma ɗan waye?".
"Haba Mama waye kuwa idan ba Ya Mu'aiseen ba ,ina kinsan da wannan zancen da daɗewa "ashe baki da hankali Rufaidah ban sani ba me zakiyi da wannan shegen yaron ,da baya son uwarki baya ƙaunar ta ,ban taɓa samun matsala da Alh ba se a dalilin sa to idan ma mafalki kikeyi ki falka dan bazan taɓa goyon bayan wannan sakarcin ba ,na faɗa miki,tun wuri kisake tunani kisamu wanda ya dace dake ,ko kuma ki amince da Anwar ɗan wurin Hajia Sa'a
dan ko babu abinda ake nema ga namiji wanda baya dashi ,kyakkawa ne ajin farko na tabbata idan kika ganshi zasan yafi wancen sakaran komai ,sune suke da kuɗi ,mulki ke komai na da kika sani na rayuwa Allah ya basu ,rashin amsa mata da banyi ba bawai yana nufin dan bazan basu bane , a'a nayi hakan ne saboda na nema miki daraja ,kina lokacin da zaki fitar da wani mijin daban amma wlh idan kikayi wasa zansa Alh ya aura miki Anwar koda bakya son sa"tana gama faɗa ta bar dakin dan bata son Rufee ta karya mata zuciya wannan ihun na na ƙarfin haline ,Allah kaɗai yasan irin son da takeyiwa wa Rufaidah amma batajin hakan zesa ta yarda ta auri wani sakarai wai Mu'aisam

Mutuwar zaune Rufaidah tayi dan bata taɓa tunanin zuwan ranar da zatace tana son abu Mama tace a'a ba ,a iya saninta duk abinda takeso shi Mama keyi koda kuwa hakan be gamshe ta ba "kai wasa Mama take wata ƙila dai saboda bata cikin kwanciyar hankali ne shiyasa tayi mata hakan dan ta kula tun abinda ya faru ɗazu har yanzu bata dawo dai² ba ,kema Rufee meyasa zakiyi mata wannan maganar bayan kinsan bata cikin natsuwa"duk zuciyar ce ke faɗa mata wanann ,kuma ta yarda da hakan ,dan haka bata wani damu ba ,takoma ɗakinta tayi kwanciyar ta ,se kuma abinda ya faru tsakanin Hajia saudah da Meerah ya dawo mata ,abun ya matuƙar bata mamaki ganin irin firgicin da dukansu suka shiga anya basun san juna bane ? "Kai ina ma Mama zata san wannan matsiyatan tun da ta san babu wani alaka ma da ze iya shiga tsakanin su ,to ko de mayyar ce? Idan kuma hakane da gaskiyar Ya Mu'aisam da itace zata fara cinyewa ,amma dai bara tagani wlh idan har gobe Mama bata dawo hayyacin ta ba to se tasaka an kama Meerah kai ba itaba ma har shegun iyayen ta "da wannan saƙe-saƙen har bacci ya ɗauke ta .

Meerah#

da wuri tagama shirinta ,bayan tagama aikin gida kamar yadda ta saba ko wace safiya bata fita se ta ragewa Aunty aiki ,dawo wa tayi ta zauna tana jiran fitowar Aunty saboda tanaso taji ya sukayi da Yaya, ya amince ko kuwa ,ganin lokaci yana ƙure mata ,se duba agogon wayarta takeyi ,daga ƙarshe dai ta yanke shawarar zuwa ɗakin su ta duba su ,a bakin kofa sukaci karo da Aunty , murmushi sukayiwa juna suna shigowa ɗakin "nasan ko wani bacci bakiyi ba ko kina tunanin ko Yaya ya amince ko a'a"wlh kuwa Aunty ,inajin tsoron yaki amince wa ,kinsan wanann mijin naki se ke "dariya tayi tace aikuwa dai dan gashi na tsara sa ya amince harda baki kuɗin abun hawa "kai Aunty da gaske nikam ne kika faɗa masa haka? Banyi tunanin ze amince cikin sauƙi ba " Meerah kenan duk yadda kike tunanin Namiji ,to ba komai bane a gaban matar sa sedai idan ita ɗin batasan kimarta ba ,bayan ya dawo ne dai yaganni kamar ina cikin damuwa ,shinefa yaketa tambayar menene ,nace masa babu komai ,dana ga ya damu kansa shine nace " wlh Yaya wani ,karambani nayi ,se yanzu ne nake nadamar yinsa batare da na ji ta bakin ka ba ,inajin tsoro bansan tata zaka ɗauki al'amarin ba ,wato gani nayi Ameerah ko yaushe tana zaune a gida ita ba karatu ba kuma ba sana'a ba ,se zaman banza shi ne ,ranar da naje gidan ƙawata na sameta tana koyar da yara dinki ,se nayi sha'awar itama Meerah ta koya ,nasan gaba zeyi mata anfani a rayuwar ta ,to shine fa take zuwa kullum da safe zuwa karfe 2 ta dawo jiya ma da kadawo baka sameta ba tana can ne ,naji tsoron na sanar dakai ne ,saboda bansan ya zaka ɗauki zancen ba ,amma dai dan Allah kayi haƙuri ,karkace zata dakata da zuwa"

Shiru yayi ,yana saurare ,kafin ya ja dogon nunfashi yace " Haba Nafisa wanann ai abun karuwa ne menene na ɓiyemin kuma ,bawai zan hana ta bane ,amma baki ganin illa a cikin sammakon da takeyi tana fita sanin kanki ne se tayi tafiya kafin ko zata samu abun hawa ,banason wani abu ya sameta kamar yadda ya samu Maryam " Insha'Allah Yaya babu abinda ze faru se Alkhairi kaaide kayi mana fatan nasara " to shikennan Allah ya temaka yabada abinda ake nema" kinji fa yadda muka yi dashi ,har tabada kuɗin abun hawa".
Rungume ta Meerah tayi cike da farin ciki tace " Aunty Nagode miki sosai wlh naji daɗi , Insha'Allah babu abinda ze faru yanzu Bara naje nayi masa godiya ko ,dama tun ɗazu na shirya ke nake jira"
a dawo lafiya Aunty tayi mata ta fita.

Amamakin Meerah tana fita daga gidan ta samu motar Manager a kofar gida ,tabbas ta gane motar amma se tayi kamar bata gansa ba taci gaba da tafiyar ta , seda takai bakin titi tana shirin tsaida mashin se taga yayi parking a gabanta ,ɗauke kai tayi taci gaba da tafiya ,da sauri ya fito daga motar yasha gabanta " haba Ameerah wai ya kikeso nayi da kaina ne sam kin ƙi bani damar da zan samu kusanci dake ,ki yi haquri idan na takura miki amma wlh lefin xuciyata ne ina sonki ,dan Allah kixo kishiga na ajiye ki inda zakije se mu karasa maganar a mota" ganin idan bata shiga ba zeci gaba da binta se kawai ta bi bayanshi da kansa ya buɗe mata motar ta shiga sannan shima ya zagaya ya shiga ,seda suka ɗauki hanya yace " ina muka nufa? dama bakasan inda zanje ba amma shine ka dage seka ɗaukoni " Murmushi yayi yace " to ayi hakuri ni ai banki mu zagaye garin nan a haka ba saboda haka idan ma baxaki faɗa ba zanci gaba da zagaye dake " aikin naka fa? Uhmmm zan kira nace yau Madam ta hanani fitowa" bata lakacin da murmushi ya suɓuce mata ba ,harseda haƙoranta suka bayyana " haba koke fa ,kina da kyau idan kika haɗe fuska to ya kike tunani a lokacin da kikayi dariya? Cike da son kauda zancen tace " unguwar da ka ganni ranar can zaka kaini" kallon ta yayi cike da son karin bayani ,se dai ta kauda fuskarta gefe saboda Allah yagani bata son yawan shige matan nan da yake yi ,dan ita fa babu tsarin auren me mata a rayuwarta ,sedai abinda Allah ya rubuta a gareta.
Har bakin get ɗin gidan yakaita,duk da ya dage akan se ya shiga da ita ,daƙyar ta samu yayi parking a wajen ,a xuciyar ta take ayyana dan besan matsayinta a gidan bane ,kafin tagama tunani taji ya sakomata tamabaya " me kike zuwa yi a gidan nan ? Da sauri ta kalleshi ,seda ta buɗe murfin motar kafin tace " Aikatau" daga haka ta rufo masa kofar ko waigowa batayi ba tayi knocking me gadi na buɗe mata ta shige da sauri kamar zata kife , A harabar gidan ta samu Mu'aisam yana karanta jarida ,sauri ta kara dan bata so ya ganta ,seda takusa shigewa taji saukar muryasa akanta " ke zo nan..........



Comments and share pls


Real Bazamfaria ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:1️⃣9️⃣


jiyowa tayi cike da addu'ar Allah yasa ba da ita yake ba ,kusan hakanne dan hankalin sa na kan jaridar da yake karatu ,bama zaka taɓa tunanin shine yayi magana ba "wata ƙil nice banji da kyau ba ,dagani ma beyi magana ba" abinda zuciyarsa ta gaya mata kenan aiko se taci gaba da tafiyarta ,har ta shige party ɗin da take aiki, hakan da tayi ba ƙaramin ɓacin rai ya saka shi ba ,idan akwai abun da ya tsana befi yayi wa mutum magana yajishi kuma ya share shi ba ,wanda ya kula ɗabi'ar yarinyar kenan duk lokacin da zakayi mata magana ko tambayarta kayi se tayi kamar ma bata ji ka ba "amma zan koya mata hankaki ai " daga haka yaci da abinda yake yi

da sallama ta shiga falon ,sedai kamar kullum bata isko kowa a ciki ba ,dan haka kawai ta fara aikin ta ,tana cikin aikin ne Hajia saudah ta fito daga ɗakin Abba turus tayi tana kallon ta ,maganar da Abba yayi ne yasaka ta saurin amsahi cikin rawar murya " Saudah kema Kinga abinda nagani ko? cikin rawar Murya tace " me kenan? Nuna mata Meerah yayi yace nasan kema Kinga kamar "a'a ni banga komai ba ,kamar wa kuma kagani gareta " wlh Hajia ina ganin ta na tuna da Birrester,badan nasan da ya mutu be bar kowa ba kuma ba dangine da shi ba to da se nace tabbas wannan ɗin jinin su ce "kai Alh idon ka ne kawai yagane maka haka ,to taya ma wannan zata zama jinin su bayan Rufaidah ta faɗa min a titi take yawon bara shiyasa ma ta temake ta ,kaima kasan wannan batayi kama da masu arxiƙi ba " hakane kuma ,amma dai ni kam gaskiya naga kamar su ,ke bani ba ma nasan ko Hajia Ammi ta ga wannan zatace suna kama"
Cikin fushi tace " to ko suna kama dai bance wata can ta rika shiga lamarin gidana ba ai koda basuyi kama ba zata iya cewa sunyi tunda har kai kace ,kasan ta da muna furci ,nikuma bazan faɗi karya kawai saboda na faranta ran wani ba ,kuma wlh wannan ƴar aikin dai tawa ce babu wanda ya isa yayi min shishigi a kanta"

Shiru yayi yana sauraren ta ,mace kamar me aljanu to menene abun faɗa anan ,tun da ba wani yace xe ɗauke yarinyar yakai wani gu ba ,sanin idan yayi Magana zasu iya seda hali a gaban Meerah se kawai yace " to nide asamu a shiryamin abun kari da wuri na faɗa miki zuwa 10 fita zanyi bara naje mugaisa da su Ammi ko ? Taɓe baki tayi tace" banda damuwa da wanan kuma salon nayi magana kace na cika kishi kaidai wlh Alh kaji tsoron Allah ,mutum ya girma amma besan ya girma ba ko yaushe se rawar ƙafa akan mace mtsswww" ta barshi tsaye a wurin ,ita dai Meerah al'ajabi ne ya kamata ,a zuciyar ta take ayyana wane irin mutum ne Abba ,shikennan shi beda kataɓus a lamarin iyalin sa ,a fuska dai kaga cikakken mutum amma a zuci ba haka bane" ganin Hajia Sauda ta shige cikine ya saka Meerah saurin duƙawa tana gaishe shi " yauma dai babu lefi ya amsa mata fuska a sake "duk da yanayin da yaɗan sauya ,da alama abun da Saudah tayi ne ya taba zuciyarsa sedai yakasa nuna hakan a gabanta.

Koda Hajia saudah ta shiga ɗaki se ta kasa zama ,xuciyar ta se saƙe² take ,wani tunani ne yazo mata ,se ta saki murmushi tana dauko wayarta ,lambar Hajia Laura ta kira ,bayan sun gaisa tace " Hajia Albushirin ki ,Kinkuwa san naci karo da wani zinari mai matuƙar kyau a gidan sedai da alama xeyi wuyar ɗauka ,dan na fahimci da zafin wuta a jikin sa ,ina tunanin ban taɓa samun zinari irin na wannan lokacin ba gaskiya "daga can Hajia Laura tace " ke uwar daba ,fayyacemun ingane me ze hanaki ɗauka idan ke kinajin tsoro ne ,ba gani ba kinsani bana tsoron komai yanzu ya za'ayi naga kalar design ɗin nasa kafin nasan hanyar da zamubi dan damƙeshi batare da wani matsala ba? " Uhmmm to bara ayi yadda aka saba bani some minutes ,zan turo Miki" kashe wayar tayi ta shiga wanka a gurguje ta fito ta shirya cikin wani doguwar rigar lace ,kayan ya amshi jikin ta dan gaskiya babu lefi itama Saudah tana ji da kyau wanda kusan ma shine abinda ya fara jefa ta wannan rayuwar

Bayan Meerah tagama gyara ɗakin Rufaidah se tace da ita ta shiga dakin da yake opposite na Mama ne kitabbata kinyi komai yadda ya kamata,kuma ki kiyaye hannun ki da ɗaukar abun da xe iya zamo miki masifa"Murmushi Meerah tayi tace" karki damu shi kansa hannun ai dole ze kiyaye ,dan yasan ba'an halicce shi saboda ɗaukar abinda bana sa bane ,shiyasa yafi sabawa da neman lada ,bara nayi sauri kar na ɓata lokaci" haka ta fita tabar Rufaidah ciwon zuciya ,dan ita fa bata gane magana Meerah ta faɗa mata ba kawai dai taji haushine ganin taki nuna ta damu da maganar da tafaɗa mata

A ƙofar ɗakib ta ja ta tsaya ,se kuma xuciyar ta keyi mata tunanin " yanzu idan kika shiga ta murƙushe ki cikin ɗakin nan fa? anya ba gangancin zanyi wa kaina ba? kai ina ma ai bazata fara aikata hakan ba tunda tasan zan iyayun ihu na tona mata asiri " da wannan karfin gwaiwar ta samu ta sai-saita natsuwrta tayi knocking , sedai shiru babu amsa ,ganin tayi har sau uku ba'ayi magana ba se tayi tunanin ko bata ciki ne saboda haka kawai ta murɗa ta shiga saboda ,ganin dakin yayi kura sosai ga kuma toilet a sake da alama anyi anfani da shi anmanta ba'a rufe bane ,sam bata kula da Hajia saudah da ke can wani ɗan lungu da ke tsakanin gado da madubi ba ta duka ne da alam tana neman wani abune ,shiyasa Meerah bata kula da ita ba ,ganin ɗakin yana bukatar gyara na musamman se kawai ta cire hijabin ta ta aje gefe ƙyam saudah ta kafe idon ta akan Meerah ,dan kuwa irin tight shirt dinann ne a jikin ta ya ɗame ta sosai hakan yasa duk wani hallita da baiwar da Allah yayi mata ya bayyana ,ga gashin ta da ta tufke a gefen kafaɗa ,yawun wahala saudah ta sauke " ashe duk yadda take tunani ma yarinyar ta wuce can tabbas wannan zata kawo kudin da bata taɓa samu da wata mace ba ,dole ne ta ajiye kishi gefe ta mora kuma tabawa se Sanator su mora dan tana da tabbacin ze iya bayarda ko nawa ne akan wannan .
Meerah da bata san wainar da ake tuya ba ,ta saki jiki aikin gabanta kawai take gashi har wani girgiza jiki take wanda ita a wurinta sauri takeyi while Haija saudah kuwa mutuwar zaune hakan ya sakata.

Tsaf tagama gyara toilet din kafin ta zo tafara gyara gado yaye bedsheet ɗin da ke shinfiɗe tayi ,ta je tasaka a ta buɗe weldrop tana neman wani ,cikin Sa'a kuwa ta samu zuwa tayi zata shinfiɗa ,mamaki ne ya cika Hajia saudah ƙarfin halin yarinyar ko waye yabata damar canja wa ,duk masu aikin su babu wanda yataɓa haka sedai idan itace taga yayi mata datti idan sun shigo se ta ciro masu tace su shinfiɗa wannan ,amma ita ta saki jiki kamar tana gyaran gadon gidansu ,seda Meerah ta shinfiɗa ta zo wurin soke gefe da gefen gadon ne idon ta ya sarƙe cikin na Hajia Sauda ,ihu ta saki dan har ga Allah taji tsoro ,cikin sarƙewar murya Hajia Sauda tace " ke..la.fi.ya? Ita fa a tunanin ta ko tsawa tayiwa Meerah ,sedai batasani ba duk wanda yaji maganar ta ze iya fahimtar cikin halin da take ,da sauri Meerah ta rarumi hijabin ta ta saka ,ta dawo " dan Allah Hajia kiyi hakuri wlh bansan kina ciki bane nayi knocking naji shiru "Hajia saudah bata son Meerah ta fahimci wani abu se ta fitar da wayarta. Kamar tana dannan wa tace " ya Sunan ki? Suna na Aminatu waye Mahaifin ki? raurau tayi da ido kamar xatayi kuka tace " Labaran dan Allah Hajia karki koreni ni wlh zanyi duk abinda kikeso ,indai zan samu kudi iyayena talakawa ne ,nikuma banaso na tashi cikin rayuwar talauci ,shiyasa ma nake wanann aikin da zan samu wanda yafishi ma zanyi.......


*Yanzu za'a fara wasar*

Amma *babu tabbacin kusamu karashe dan wlh na raina wa comments ɗInku ,kuma indai mutum ya sanni to ya san halina dan na dakata da labarin nan ba sabon abu bane a gareni har sadda kuka shirya gyarawa se muci gaba*

Akwai ƙura fa ,dan kunji Rufee tayi scarce a wannan page ɗin to tana can tana nemawa kanta mafita ne dan dole zata aure Mu'aisam😂



Masu yimin comments ina godiya kuma wlh inajin daɗi , luv you so much billahi❤️❤️

Comments and share


Real Bazamfaria ce❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:2️⃣0️⃣


*This* *page goes to my VIP my Mom @Maryam Sa'ad and Anmata Khairatu* *nasan cewar* *zeyi muku daɗi* *dan anzo wurin da kukeso* *ina godiya da* *soyayyar ku gareni Allah yabar ƙauna*❤️


Murmushi Hajia saudah tayi mata ,tana faɗin " jeki karasa aikin ki" kamar gaske Meerah ta tashi cikin mutuwar jiki tana ci gaba da gyaran gadon ,tashi Hajia Saudah tayi tabar mata ɗakin ,tana fita Ameerah ta sauke ajiyar zuciya ,tare da zama daɓas kan kadon ,duk da tana cikin murnar ganin

Please Login or Register in order to submit comment