Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya manta ma da badashi suke maganar ba se samun kansa yayi da tambayar " meyasa Mama zata tafi da ita ,ina ga kawai ku sallame ta ,dan ba ma lallai bane iyayen ta su amince a bar garin nan da ita ba " to kai Yaya miye naka ,kasan dai talakawan nan yadda suke bare ma su da suke neman kai da ita suna ganin kudi da gudu zasu amince ,ni bama zanso hakan ta faru ba kasan fa duk yaran da Mama take ɗauka tana sakasu school ne cikin lokaci zaka sun waye ,nikuma bazan so hakan ya faru akan wannan ba "Mu'aisam bece komai ba yaci gaba da kallon sa ,saboda zuciyarsa da ta tafi dogon nazari na dalilin da zesa Meerah tabar kedi
Cikeda Mamaki Rumaisa tace " aikam dai Ameerah tana da kirki sis Rufee bansani ba dai ko kece baki fahimci hakan ba ,ni damuwa ta ma kar ace ko batada lafiya ne ,gashi ban tambayeta gidan su ba bare naje na duba ta ,dan ko Ammi ta damu da rashin zuwan nata"
Allah wadaran naka ya lalace ,kice kune kuke sakar mata fuska shiyasa har take tunanin kawomin raini ,yanzu idan ba neman suna ba ne xe kaikimu wurinsu ,koda nasan ma ba samunta xakuyi ba dan na fi tunanin a bakin hanya seke kwana itada iyayen ta so don't bother ur self" jeki ki shirya yanzu idan nadawo sallah zamu fita da Rufaidah se mutafi dukan mu harda Auta ma kishirya ta " ba tare da dukan su sun san me yake nufi da hakan ba ,suka amsa da to " duk da kasan zuciyar Rufee ba haka taso ba ,taso ne Sufita su kaɗai saboda su fara samun kusanci da juna ,akwai kuma maganar da take so suyi ,wanda tasan matuƙar suka fita waƴan nan jarababbun to ba sake wa zasuyi ba ,bata so ta koma sashen su dan kar Mama ta gane cewar zasu fita da Mu'aisam dan haka tayi zaman ta anan , toilet din da kecikin falon Rumaisa ta shiga ta ɗauro alwala ,da tafito ta kalli Rufee da take canja channel tace " sis Rufee ko zakiyi alwala ne akwai ruwa a cikin toilet "batare da ta kalli Rumaisa dake maganar ba tace " am off salat" taɓe baki Rumaisa tayi tana shigewa bedroom.

cikin doguwar Riga ta shirya tayi kyau sosai fitowar ta yasaka Rufee kallon ta batadai ce komai ba itama Rumaisa batayi mata magana ba ,ta shiga ɗakin Ammi lokacin ta sameta tana sallah saboda haka direct kan gado ta nufa dan tashin Nawwara dake bacci ,bubbuga bayan ta tafara, kasancewar batada nauyin bacci se gashi ta budé ido ,tana ganin Rumaisa tafara narke fuska kamar zatayi kuka tace " Yaya baccin be isheni ba " ok bara mutafi mu barki to dama Yaya yace natashe ki zamu fita shopping" ai tana jin zancen yawo se ta tashi da sauri ,tana faɗin " to mutafi" hararan ta Rumaisa tayi tace " kinyi sallah ne da zaki ce mutafi kuma kinsan baxaki bimu a haka ba ko? Nawwara batayi magana ba ta shiga toilet da sauri alwala tayo ta fito fici-fici tayi sallar saboda batason su tafi su barta ,koda ta gama Rumaisa ta fito mata da kayan da zata saka dan haka ta sanya mata ,suka tsaya jiran Ammi tagama addu'a suyi mata sallama ,bayan ta idar Rumaisa tafaɗa mata zasu fita ,adawo lafiya tayi musu ,cikin wasa tace " wato kun faki idon Mimi da Nurain shine zaku fita ko aiko idan yadawo gidan nan ya samu kun fita da Auta kunsan za'ayi darga da shi " Ammi karki damu xan siyo masa Icecreem ,ko Yaya? ta kalli Rumaisa ,dariya tayi mata a haka suka fita

Fitowar su yayi daidai da fitowar Mu'aisam daga cikin ɗaki da alama ya daɗe da dawo daga masallaci dan kuwa har ya sauya kayan jikinsa yayi kyau sosai wanda har Rufee ta kasa ɓoyewa seda ta maganta " gaskiya Yaya kayi kyau ko har ka fara hasken amarci ne? Haɗe fuska yayi bece komai ba ,ita kuma Rumaisa se tace" yaya smile mana ,Allah baka ganka ba kamar zakaje wurin babyn ka anya kodai ,zance zamu raka ka? murmushin gefen baki ya sakar mata tare da faɗin " wlh za'a fasa fitar nan ,naga kuna neman maidani wani abokin wasan ku"
Rufaida da takaicin maganar Rumaisa ya cikata se taja tsaki tace " wahalar tambaya name kikeyi bayan kinsan tare dani ze fita wannan duk wani yayiwa" fahimtar inda zancen ta ya dosa se Rumaisa tace " haba ke kam ai uwar gida ce sis Rufee ,kika sani ko har ya fara kyarkyarar amarya waƙil ma ku biyu za'a kai masa kinsan masu iya magana sun ce me mata ɗaya abokin gauro ,so yayana ze fita daga cikin su "cikin tsawa Rufee tace " aniyar ki tabiki Rumaisa sedai idan kece kike son sa wannan zamu iya zaman kishi dake amma babu wata mace da ta iso ya so ta ni nasan wanann ,hassada ne da baƙin ciki koda yake na daɗe da gane cewar kema kina son sa " riƙe baki Rumaisa tayi tace" ikon Allah kin taɓa ganin yaya ya auri ƙanwarsa ko kin manta alaƙana dashi ne ni matsayin ɗan uwan da aure ya haramta a tsananin mu nake masa ,da ace ina son sa kamar yadda kika faɗa kema kinsan da baxaki sameshi ba"Rufee xatayi magana ta tare nunfashin ta da faɗin " ki ajiye kalamanki zuwa gaba wata ƙil zeyi miki amfani a lokacin da kika gane cewar akwai wacce yakeso ba keba "da sauri ta wuce ta bar Rufee na sababi ,koda suka iso motar har ya gyara parking Rufee har ta buɗe gaban mota zata shiga se ta ga Nawwara zaune ,cikin haɗe fuska tace " ke fito ki koma baya " ɗago kai Mu'aisam yayi ya kalleta sedai bece komai ba ,har ta fita ta shiga baya ita kuma ta zauna gaban.

tana shiga ya tada motar suka fita

Babban shopping mall ya kaisu yace kowa ya zaɓi abinda yake so ,sosai suka zaɓi manyan tarare irin desingners dinnann masu matuƙar tsada ,daganan suka tagi gefen kayan yara teddies masu kyau Auta ta zaɓa ,daganan ne suka tafi gefen su chocolate,wannan kam Rufee da Nawwara ne kawai su diba dan ita Rumaisa bata shan kayan zaƙi ,Atm yabada a cire kuɗi ,har anyi debited se Nawwa ta hango wani babban boll cikin net ɗinsa irin elastic dinnann da ake hurawa da sauri ta je ta ɗauko tace " yaya musiyawa Nurain wannan " kai kawai ya ɗaga mata yasake bada Atm ɗin suka cire kudin suka tafi ,har zasu fita daga wurin idon sa ya hango mishi bangaren da ake seda irin jalabiyoyin nan ,dan haka kawai yabasu key yace su jirashi a mota yana zuwa , haka ya tafi ya zaɓo jalabiya har kala 3 masu shegen kyau da tsada , sannan ya dawo suka bar wurin.


ganin kamar ba hanyar gida ya ɗauka ba yasaka Rufee kallon sa " Yaya ina kuma zamuje nifa nagaji gida nikeso na koma "to ko mu ajiyeki se ki shiga Napep dan zankai su wani wurin ne " haba yaya yanzu saboda Allah kamar ni dinnann se na tsaya a titi neman Napep? " ke ba mutum bace ko kinfi sauran muta ne ne " to Yaya abun ai a bayyane ne kaiman kasan ta zara me yawa da Allah yayi tsakanin talaka da me kuɗi ,saboda haka ni gaskiya bazan shiga Napep ba " to ko se kijira har mugama abinda mukeyi se ki koma a mota ,daidai lungun su Meerah ya shiga da motar sa , parking yayi daga nesa kaɗan da gidan dan ganin wata motar da ke a jiye kusa da gidan ,wannan karon kam hatta Rumaisa se da tayi magana dan mamakin inda ya kawo su tace " Yaya ina ne nan ɗin ? wlh kamar ba'a kd ba " hararan ta yayi ta madubin motar yace " idan kin fita kya tantance ,fitowa yayi ya ce dukan su su fito ,babu musu suka fito ,kiran Auta yayi yaimata raɗa a kunne ,a mamakin su se sukaga ta daga tsalle tana faɗin " da gaske yaya ? Kai ya ɗaga mata alamar tabbatar wa tare da mata nuni da ƙofar gidan su Meerah.

kallon su Rumaisa tayi tace" yaya yace nan ne gidan Aunty Ameerah mushiga mugani ,kallon mamaki sukayi masa sedai be basu damar magana ba ,sema cewa da yayi "Rumaisa kishiga kudubata sauri nakeyi " bin banyan Meerah tayi ,ita dai Rufee kamar wacce aka kafe a wurin tama kas motsi ,lokacin da suka kai kofar gidan yayi dai² da fitowar Meerah tare da Muhsin ,alamar rakiya tayo masa ,sam bata kula dasu ba se da Nawwara ta rungume ta tana murnar ganin ,da mamaki ta cire hannayen ta da ta zagaye cikin ta dasu itama cikin jin daɗin ganin su tace " Auta waya nuna muku gidan mu? munxo ne muduba ki kwana biyu shiru ko bakida lafiya ne ,ashe ke kina nan soyayya ta ɓoyeki "ta faɗa cikin sigar zolaya "rufe ido Meerah tayi tana daria tace " Aunty ai wannan yaya ne ko? Tayi maganar tana kallon Muhsin ,se a lokacin Rumaisa ta gaidashi ,amsawa yayi yana shiga Mota tare da faɗin " bara na wuce tunda kinyi baƙi xamuyi waya dai Allah yaƙara lafiya"bata amsa shiba sedai ta ɗaga masa kai kawai tare dayimasa waving ,seda ya tada motar tukuna ta ja hannun Rumaisa tace" mushiga ciki Aunty " bin bayanta Rumaisa tayi.......


Comments and share pls

Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:2️⃣6️⃣


suka shiga gidan lokacin Aunty tashig ɗaki dan haka direct ɗakin ta ta shigar dasu ,a bakin katifar ta Rumaisa ta zauna ,dan itakam Nawwara tana maƙale da ita ,fita tayi tasanar wa Aunty zuwan su " to ki ɗauki ruwa a firjin ki kai musu mana " a plate ta ɗora ruwan ta kaiwa Rumaisa ,dukda bata jin ƙishi amma haka ta fasa ruwan ta ɗan sha saboda kartaji wani iri ,ajiye ruwan tayi tana kallon Ameerah da ke yiwa Auta magana " ashe bakiji daɗi ba ,kwana biyu bamu ganki ba ,shine muka tambayi uwar ɗakin ki gidanku ashe ma batasani ba se yaya ne ya kawo mu " yaya? Meerah ta tambaya cikeda mamaki "murmushi Rumaisa tayi tace " nima bansan ya akayi shi yasan gidan ba nayi tunanin ko yana zuwa zance ne" ta faɗa da sigar zolaya
Zare ido Meerah tayi tace" wane zance kuma ,rufamin asiri dan Allah ,idan ma zeje zance kinsan badai a irin unguwar nan ba ,nima tun ranar da nadawo nake fama da ciwon kai ,da safe har na shirya na taho se ga zazzaɓi ya rufeni seda nasha allura ,amma Alhmdulilah naji sauƙi dama gobe nike shirin dawowa " ayya sannu har kin faɗa kuwa ,amma Ameerah wannan da nagani shi zaki aura? Noce kai tayi bata ce komai ba ,dan haka Rumaisa taci gaba da faɗin " gaskiya kam nayi miki murna da ganin sa yana sonki sosai , sedai zan so ace karatu kikayi ba aure ba cox u'r teenager fa har yanzu under age kike ,dudu du baxaki fi 15-16 ba idan kikayi karatu zeyi miki amfani a rayuwa " hmmm Aunty Rumaisa kenan , bakisan wace ce Ameerah shiyasa kike wannan tunanin yarinyar da saboda rashi take zuwa aiki a gidanku ina kike tunanin zan samu damar karatu ,wannan tunanin se ku da kuke da gata kukeyin sa mukam ai bama wani kallon karatu" dukda haka dai Meerah gidanku bakuda irin raunin nan da xakice haka dube ku ba ,kamar baku cikin wani hali ,ni wlh se nake ganin ma sam babu wani wahala a tattare dake ,Ameerah kina kallon kanki kuwa ,duk inda wata mace me gata ke kaiwa kin kai koma nace kin zarta ,ni idan har zaki yarda zan temake ki kiyi karatu ,kinga yanzu Sis Rufee aure zatayi ,Kuma da tayi aure shikennan sedai mamanta ta tafi dake garin da take zama kici gaba da aiki a can ,me ze hana ,ki ajiye aikin tun yanzu Kinga ni kuma zanyiwa Yaya magana nasan ze temaka mana kici gaba da zuwa school "

Shiru Meerah tayi dan bata san me zata ce ba kuma ,saboda Rumaisa bata san cewar bawai iya aiki yakawo ta gidan ba ,amma a fili se tace " Masha'Allah ashe aure zatayi to Allah ya sanya Alkhairi "to baki tambayi wa zata aura ba " Aunty to miye nawa na tambayar wanda zata aura ,tunda dai aikine kawai nakeyi mata maganar arziki ma baya haɗamu " taɓe baki Rumaisa tayi tace " wai yayan mu zata aura " yayanku? yayanku fa kika ce dama mutum yana auren yayan sa ne? Se lokacin Rumaisa ta tuna Meerah bata san komai game da gidan su ba se kawai tace " kinsan yaya Mu'aisam cousin brothern mu ne ba Abba bane ya haifesa "ohhhh na fahimta to Allah yabasu zaman lafiya aikam sun dace ita jin kai shi izza" dariya Rumaisa tayi tace" yayan namu ne me izza"
"ohhhh yi haƙuri Aunty mantawa nayi" dariya Rumaisa tayi tace" idan kika faɗa a gaban sis Rufee,aikam zakisha tijara ,kinsan dai halinta ,kinga tare da yaya fa muke yana mota bara mu tafi karya mun shanyan shi ,amma bamu gaisa da Mama ba ko bata nan? Ohhhh yi haƙuri na manta ne wlh ,bara na kira ta ,har ta miƙe zata kira Aunty se gata ta shigo da fari'arta suka gaisa, sannan suka tashi dan tafiya Meerah ta bisu domin ta rakasu
Har bakin mota ta kaisu da alama lokacin Rufee suna faɗa ne da Mu'aisam ,akan kawota da yayi ya jiye a Wannan unguwar ,ganin Rumaisa da Meerah ne yasakata yin shiru ,a mamakin Mu'aisam ko kallon inda suke Meerah batayi ba bare ma yasamu gaisuwa ,shima se yayi kamar be ganta ba yacewa Rumaisa " shigo mutafi dan naga alamar wacce kikazo ganin ma lafiyar ta ƙalau ,sakarci ne yahanata zuwa aikin ta "kai Yaya Allah tayi rashin lafiya ne "seda ya kalli Meerah ta ƙasan ido kafin yace " amma zata iya fitowa wurin samarin ta aikine bazata iya zuwa ba ko?".

"tsaki Rufee ta ja tace" kaima yaya dai akwai ka da shiga abinda be ganoka ba ,to miye amfanin ta idan bata kula mazan ba ba karatu takeyi ba ba kuma kuɗin karatun ne dasu ba ,sedai nayi mamakin ganin wanda yazo wurin ta ,yayan ƙawata ne kuma babban mutum ne ,matar shi ta haɗa komai ga wayewa dan bama a ƙasar nan tayi karatu ba ,bansan me yake yi a Wannan unguwar ba koda ance dama haka yaran talakawan nan suke ,idan sukaga suna ɗan da hasken fata se su fara bibiyar mazan da suka fi ƙarfin su ,kasan dai babu abin da wannan zeyi da ita seko idan lalata sukeyi dan ta samu kuɗi kasan mutumin banza sam ba ya raina mace duk cunkushewar ta ,Allah dai ya kyauta " tun da tafara maganar cikin su kowa yayi shiru dan sam basuji daɗin cin fuskar da tayi ba , musamman Mu'aisam da yake ganin kamar shine sanadi tunda shine ya ɗauko zancen ,a mamakin su se sukaga Meerah tayi murmushi cikin sanyin muryarta tace " wai dama Hajia tare kuka zo ni ai sam banma ganki ba seda kikayi magana ,na tayaki murna ashe aure zakiyi Allah ya sanya Alkhairi" tafaɗa tana miƙa mata hannu ,wani irin kallo Rufee tayi mata ,ganin haka se ta janye hannun ta tace" au yi haƙuri fa na manta ni talaka ce amma duda haka yakamata mufara gaisawa tunda nan da wani ɗan lokaci na zama matar me kuɗin nima ko da inata wasa da dama na dan bansan matsayin wanda zan aura ba se ga zuwan ki ya wayar min da kai ashe babban mutum ne ,kinsan dama mu yaran talakawa irin su muke nema ko zamu ɗanɗana irin rayuwar da kukeyi ,gaskiya na gode Allah da yayi ni farar mace ,dan na fahimci yanzu kamar mune zaɓin mazan yanzu, gashi zan auri me kuɗi saboda hasken fatar kai Alhmdulilah dama iyayena sun daɗe suna faɗa min cewar ni matar manya ce dan ni ɗin kyakkawa ce ban yarda da hakan ba se da kema kika faɗa da bakin ki ,dan na kula kamar tsoron kyan nan nawa kikeyi saboda duk lokacin da zakiyi magana se kin ambacesa , shikenan Nagode da ziyara nakuma ji daɗin zuwa dubani da kikayi ,kigaishe da Hajia dan Allah kinsan yanzu ita zan cigaba da yiwa aiki

Cikin zafin rai Rufee ta fincikota " ke dan ubanki har kin isa ki gayamin magana ,ina kyau yake anan ,me kike taƙama dashi? Maimakon Meerah tasakeyin magana se ta harɗe hannu tana kallon ta , Mu'aisam kuwa shiga yayi mota yayi mazan sa kamar ma besan abinda sukeyi ba , Rumaisa ce tayi saurin shiga tsakanin su tana jan Rufee " haba sis Rufee wannan ai girmanki kike zubarwa ,taya za'ayi ki tsaya sa insa da ƴar aikin ki ,kuma ina lefin wanda abun alkhairi ya sameka yataya ka murna?wanann ai kin zubar da girmanki ne a gaban ƴar aikin taki"a fusace Rufee ta fixge hannu ta tare da jan dogon tsaki ta shige mota ,haƙuri Rumaisa ta bawa Meerah tare da miƙa mata ledar da Mu'aisam ya bata ,ƙin amsa tayi dukda batasan wanda yabata ledar ba a tunanin ta ma ko Ruimasar ce ta kawo mata wani abun ,da taga ma ta matsa mata se ta amsa se kawai tayi tafiyar ta da sauri tana ɗaga musu hannu ,shiga Mota itama Rumaisa tayi tace" yaya tafaƙi amsa" batare da ya kalleta ba yace fita kisamu yaro ya kaimata ,tunda idan tabarshi me za'ayi dashi ko kina so ne? Ƙunshe dariyar ta tayi tace" a'a yaya ko ina so ai bazemin ba tunda nafita tsayi kuma nasan length nata ka ɗauko " jin maganar da suke yasaka Rufee fincikar ledar tana buɗe wa ,ganin tsala-tsalan rigunan da ke ciki yasakata kafeshi da ido tana masa kallon tuhuma ,yi yayi kamar be ganta ba ,ya kunnan mota ze tayar ,fixge key din motar tayi cikin fushi tace " Mu'aisam me kake nufi da siyowa wannan matsiyaciyar tsadaddun kaya ,nifa ban gane ba wani muna funcin kuke ƙullawa ,taya ma kasan gidansu ,dama nasan ƴan uba miyagun bayi ne ,to wlh koma me kuke ƙullawa baku isa ba ,dan nafi ƙarfin wulaƙancin ku kuma kubari mukoma gidan zan sanar da Abba shine yahaɗa auren nan idan baze yiyu ba tun wuri a warware.

"haba sis Rufee me kike faɗa haka ,ina kome yaya yiyuwa Ameera to saboda ke ne tunda zaman ki takeyi besides ma yaga tana buƙatar kayan ne kina ganin yadda take zuwa aiki a duƙunƙune "ɗaga mata hannu tayi tace "dakata bana son muna funcin kinayi kamar bakisan komai ba ,dama shiyasa kikace zakizo gidan wlh da nasan nan ze kawoni da gara na hau Napep na tafi gida dan yagama tozarta ni ,ita kuma zata zo ta sameni ne idan ma wani asiri ne tazo dashi to wlh a banza ,dan batada muhalli a gidan mu " ke Rufaidah bana son rashin hankali ,haba ke baki gajiya ne kinbi kin dameni da surutun ki marasa amfani ,me kike tunani , me zuciyar ki ke baki ko bansan ciwon kaina bane wlh kar ki kaini bango ,yanzu na ɓaɓɓalaki anan sakaryar yarinya ,duk haukar da kikayiwa ƴar mutane kinji na ce wani abu sauƙin ta ma itama ta iya tsiwar irin naki ,kinja yarinya ƙarama ta faɗa miki magana kuma hakan be isheki ba ,kinzo nan kinayi mana hauka ,duk ranar da kika ƙureni wlh zan baki mamaki"

Aiko Rufee se ta fashe da kuka ,abunka da ƴar uwa se tausayin ta ya kama Rumaisa kuma se taga rashin kyautawar Mu'aisam ,sedai shiru tayi batace komai ba ,haka suka ci gaba da tafiya sheshekar kukan ta kawai ke tashi a motar ,har suka kai gida.........


Manage

Comments and share pls


Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:2️⃣7️⃣

*_Wannan page ɗin* *wa_* *dukkan* *_Mabaraciya fans ne Nagode sosai da soyyayar ku Haƙika comments naku nasakani nishaɗi* *one* *luv guys* ❤️_


tunda suka dawo Mu'aisam yake tunanin hanyar da xebi dan dakatar da Meerah daga bin Hajia saudah,sedai yasan beda wani mahita matuƙar iyayenta suka amince da ta tafi ,amma ai akwai mafita guda wacce yake tunanin itace zata iya hana Meerah fita daga Kaduna ,Aure ne kawai xe hanata barin garin dan yasan cewar duk mijin da zata aura baze barta sake fita ba "to waya faɗa maka ma tanada saurayi? Zuciyarsa ta tambayeshi ,tunawa da Muhsin da suka gani ɗazu yazo wurinta ,yasakashi jan dogon tsaki "daga ganin wannan irin ƴan Yahoo ne ba auren yarinyar xeyi ba ,sekuma ya tuna da kalaman Rufee da tace sedai idan lalata xeyi da ita "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un"ya furta dan jin irin faɗuwar gaban da ya riskeshi.

Rumaisa kam lokacin da tafaɗawa Ammi abinda ya faru lokacin da suka fita ,dariya kawai tayi tace " bansan me yasa Hajia Sauda ta tusa wa yaranta rashin ƙaunar talaka ba ,bayan ita dinma ,bawani arziƙine dasu ba hasalima koda Alh ya aurota , basuda komai business ɗin da take yi ne take riƙe iyayenta dashi dan kuwa duk sun tsufa ,da ta samu Alh ne abubuwan suka fara walwale mata ,kuma a haka take ƙyamar talauci ,kai Allah dai ya kyauta " nifa Ammi ko kamar akwai abinda nake hange a game da yaya ,se nake ganin kamar son yarinyar nan yake ,idan ko hakane ai Meerah ta zama abun tausayi ,ina ita ina kishi da sis Rufee?".

Murmushi Ammi tayi irin nasu na manya tace " Rumaisa kenan to inbanda ke da abunki ,ina ruwanta da Rufaida ina mijine dai kuma duk matsayin su guda a wurin shi ,kuma da ya samu ma mace me biyayya gaskiya ,dan nide tunda na fara ganin yarinyar naji ina son ta a zuciyata ,musamman ma da takeyimin kama da matar Birrester ,itama nasan Allah xe bata mijin da ze kula da ita ba dole se Mu'aisam ba

"hmmm amma Ammi nifa nayi mamakin ganin Mama tayi sanyi a maganar auren nan ban taɓa tunanin zata amince cikin sauƙi haka ba ,anya ba wani abun take shirya wa ba? Ke Rumaisa banas ofon shiga abinda be ganoki ba ,kiyi mata kyakkawan zato mana ,ai mutum baze riƙa girma yana cin kasa ba ,kuma dama ƙiyayyar saboda ni ne ,nikuma sam bata gabana ina nan dai inayi masa addu'ar zaɓi mafi alkhairi a rayuwar sa ,dan nikam bazanyi shishigi a lamarin Ubangiji ba" har Rumaisa zata sake magana Ammi ta katse ta da faɗin " dare yayi kije ki kwanta ,ina morning lectures kike da shi? tashi tayi tace to Ammi seda safe da wuri kam zan fita ga Amrah ma tace zata zo goben "to shikenan Allah yabamu alkhairi.

Rumaisa#
Wannan daren kam kwanan baƙin ciki tayi musamman da ya kasance bata da wanda zatayi sharing problems nata dashi ,dama ace abun da Mama ke so ne ,tasan da ita ce zatayi mata yaƙi akan wannan wulaƙancin ,to ita ɗin ma ba so takeyi ba ,dan haka ta yanke shawarar kiran Aunty Khadija gobe dan tasan ita bazata ƙi ta auri Mu'aisam ba ,da wannan tunanin ta samu kwana (bacci) ɓarawo ya ɗauke ta.

Meerah#

tun da ta koma gida yanayin ta ya sauya ,komai cikin sanyin jiki takeyin sa wanda har se da Aunty ta kula da hakan ta tambayeta " waike me ke damunki ko jikin ne "yaƙe tayiwa Aunty tare da faɗin

Please Login or Register in order to submit comment