Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana ne se murmushi ,last time ma fa har kika bar gidan nan banji maganar ki ba ,ke wannan ai bazaku shirya da yaya Mu'aisam ba dan ya tsani yayi magana kayi masa shiru ko kayi nodding ,ke kuma na fahimci kamar halin ki kenan ,ranar da kuka fara zuwa Allah na zata ko ke budurwar sa ce kundace sosai" rufamin asiri dan Allah wace Ni" ta faɗa tana zare ido ,aiko Amrah se ta fashe da dariya tace " aikinga yanzu kinyi magana ko? To ma miye na zare ido kika san ikon Allah " Kinga bar zancen nan ,ina cewa kikayi zakiyi girki muje kawai mu fara dan maybe ba daɗewa xamuyi ba naji kamar Ammi tace zamuje wani gida..........



*Typing yafara bani* *wahala saboda issues na* *school*


_Ku daure kuyi comments_ yadda _ya kamata maybe hakan yasa nariƙa squeezing time inayi muku_

Kunsan dai akwai rikici idan Hajia Sauda ta gane cewar Ammi ta fitar mata da yar'aiki


Comments and share pls


Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:3️⃣1️⃣


*Bansan ta* *ina zan fara ba but what I know is I offended ,kuyi haƙuri , insha'Allah na dawo kenan se mun kammala ,kuma ku daure kuyi comments domin na ƙara samun ƙwarin gwiwa, Nagode sosai da nuna soyayyar ku akan wannan littafin feedorh na matuƙar kaunarku* ❤️


Tsaf su Hajia Sauda suka shirya ,kafin ta aika Larai ta kira mata Meerah ,cike da girmamawa tace " Hajia kamar ta tafi gida dan gaskiya tun ɗazu banganta ba "Gida? kai a'a tasan zamu fita bazata tafi gida ba jeki kidubota dai "
Babu musu Larai ta sake fita duk inda ta san Meerah na zama idan ta gama aiki seda ta duba amma bata ganta ba ,dan haka ta dawo ta shedawa Hajia Sauda ,kallon² aka fara tsakanin ta da Hajia Laura kafin suyi magana Larai tace " am Hajia bansani ba ko ta shiga bangaren su Nawwara"wani irin kallo tayi mata tare da faɗin " dama tana shiga can ne? Batare da Larai tasan matsalar da fadan xe kawo ba tace " ehhh sosai ma Hajia ai idan ta gama aikinta ta kan shiga can kafin lokacin ta shinta yayi "

Cikin tsawa tace " amma kinsan da wannan me yasa baki faɗa min ba bayan kinsan dokana duk wacce ke aiki sashen nan bana bari tayi hulɗa da su ,maza jeki can sashen ki dubomin ita" har ta kama hanya se kuma ta dakatar da ita " bara intafi da kaina dan inji dalilin Zainabu na ƙulla alaƙa da me aikina".

da sauri ta fita Hajia Laura na ta ke mata baya ,shigansu sashen yayi dai² da fitowar Mu'aisam ,shikuma yana sauri xeje masallaci ,daga sama har ƙasa yake binsu da kallo ganin suna shirin raɓashi su shiga ciki yace " akwai matsala ne"?.

"Matsalar ita ta kawo mu amma wannan zuwan na uwar ɗakin ka ne ba kai ba dan haka zaka iya bamu hanya mu wuce" Murmushi yayi yace " to aiko bakubi adreshin da ya dace ba dan banada uwar ɗaki Anan se dai uwar goyo ,idan sako kukeda shi wurinta zaku iya faɗawa ɗanta ,dan ita bata saba hayaniya ba kuma ba za'a saka ta yinta ba yanzu" Hajiya kar dai wannan mara mutuncin shine ake ƙoƙarin haɗashi da Rufaida?". Cike da ta kaicin rashin mutuncin Mu'aisam tace " kindai gani ai wlh Alh yagama cuta ta , amma nasan makirci ne kuma wlh zanyi maganin abun kar kayi tunanin cewar zaka auri Rufaida ita din tafi ƙarfin ka matsiya ci irin ka ɗan talakawa " gyara tsayuwar sa yayi yana binta da wani malalacin Murmushi ,cike da rainin wayo yace " kice sakon ma nawa ne ba na uwata ba dama abun da kukazo sanar mata kenan to bara kiji nima karkiyi tunanin liƙamin ƴarki da akayi zesa na ɗaga miki ƙafa ,kuma idan ma makirci ne to ƴarki tayi dan ita ce ta samu Dady tana kuka tare da rokonsa ya aura mata ni kisani arzikin Ammina yasa na yarda zan amshe ta ,ba wai dan so ko sha'awa ba ,sedan nasan inada damar da zan iya auren wacce tarbiyyar ta zata dace da tawa ko nan gaba ne ,zaku iya tafiya,dan naga alamun inda aka saba zuwa zaaje".

"galala sukayi da baki suna kallon shi ,duk da Sauda ta san rashin mutuncin sa amma bata taɓa tunanin ze iya yi mata haka ba ,za ta sake magana Laura ta ja hannunta suka fita ,girgiza kai Mu'aisam yayi a fili ya furta " kin kusa zuwa hannu"

Bata saki hannunta ba har se da suka shiga dakinta ,wani irin kallo takebin Sauda dashi kafin tace " kin bani mamaki Hajia ina ta ƙamar da isar ,to wlh matukar kika bari wannan yaron ya auri ƴarki to fa ko mai yafaru da ita ke kika so babu kunya babu tsoro yake fadar baya sonta ,shi ba ɗan gidan nan ba amma naga alamar shike mulkin gidan dan haka shawara ya rage naki ki dauki matakin da ya kamata ko kuwa kiyi kuka a gaba" ajiyar zuciya Sauda tayi tana me mayar da hankalin ta ga Laura " yanzu me kike gani zanyi Laura na faɗa miki idan na matsa akan maganar auren nan to Alh ze iya sakina dan naga take-taken sa "ke kuma tsoro kike kar ya sake ki ko ? Muda bamuda mazan me hakan ya rage mu se ma ƴanci da muka ƙara samu ,amma shikenan na fahimceki ina da shawara ɗaya da ze rusa auren nan ba tare da kowa ya zargeki ba idan kin amince" cike da zaƙuwa Sauda tace ina jinki "a kunne tayi mata raɗa ,zare ido tayi tana girgiza kai da alama shawarar batayi mata ba ,ganin haka se Laura ta haɗe fuska tace " to idan kina da wani mafita bayan wannan se a gwada ,ko kina ji kina gani ƴarki zata auri wanda sam be san darajar ki ba har yana tsayawa a gabanki kina faɗa yana faɗa"

" Hajia Laura ina tsoron abunda xeje ya dawo ne se nake ganin wannan shawarar taki kamar yana nufin nayi blackmail na ƴata ne ,amma tunda kina ganin shine mafita na amince indai hakan zesa a fasa wanann auren "yaawwa ƴargari yanzu kikayi magana nayi miki alƙawarin babu abinda ze faru".


Haka Su Meerah suka wuni ba su suka dawo ba se goshin magrib ,dan haka Ammi tace su fara ajiye ta a gida ta shiga tayima Mamanta bayani saboda kartayi wani tunani ,hakan yayiwa Meerah daɗi kuwa dama tunanin abunda zata faɗa wa Aunty takeyi ,

Itace a gaba su Ammi na binta a baya ganin lungu da take bi dasu tunani me yawa ne a zuciyar Ammi ahaka suka shiga cikin gidan da sallama suka shiga dukan su babu kowa a tsakar gidan se wasu uban kaya da aka jibje gefe ɗaya ,kallon mamaki Meerah takeyiwa kayan " ko masu gidan ba sa nan ne? Maganar Ammi ta dawo da ita daga tunanin ta "a'a ina tunanin dai ta shiga sallah ne ku shigo Ammi kafin ta ƙara sa ,babu musu suka bita har cikin ɗakin ta ,kakkaɓe musu yololuwar katifarta tayi suka zauna " to Ameerah ko zaki bamu ruwa ne muyi alwala ,shima Alh yace masallacin da muka gani bakin layi ze tafi yayi Sallah "

To Ammi bara na zuba muku ruwa"Seda ta fara shiga toilet ta wanke duk da bayada datti dan Aunty sam bata yarda da ƙazanta ba ,ruwan ta zuba musu tazo ta sanar dasu ,batare da nuna ƙyanƙyami ba kuwa Ammi ta shiga bayin kafin su gama alwala har Meerah ta shimfida musu tabarma yadda ze wadacesu tunda pray mat ɗayane a ɗakinta seda suka kabbarta kafin itama taje ta ɗoro nata alwalan ,sadai bata shiga ɗakin ba daga nan waje tayi amfani da praymat tayi sallahr ta ,har ta idar Ammi na kan tabarma da alama azkar takeyi dan bata ko motsa ba ,shiga Meerah tayi ɗakin Aunty dan duba ko ta gama sallahr a bakin ƙofa suka ci karo .

"Haba ashe kece inatajin motsi da magana sama² gashi na rigada na fara sallah ,se tunani nakeyi su waye suka shigo ya akayi kikayi marece har haka ,kinsa yayanki ya dawo se jaraba yake min wai zaki dena zuwa koyon ɗinkin nifa tsoro na ɗaya randa xe gane cewar ba ɗinkin kike zuwa koya ba "

Maimakon Meerah ta bata amsa se tayi Murmushi tace " muna da baƙi ne Aunty kizo ku gaisa "cike da mamakin suwaye baƙin nasu tabi bayan Meerah

Da sallama suka shiga ɗakin lokacin Ammi tana tsaye tana naɗe tabarma ,da faria ta juyo tana amsa musu ,gaisawa sukayi da aunty cikin mutunci anan Ammi ke bata haƙuri kan cewar itace ta fita da Meerah shiyasa bata dawo da wuri ba " ayya babu komai Hajia dama dai kam hankalina ne ya tashi kinsan yanzu duniyar tamu ne babu gaskiya ga kuma yayanta ya dawo se masifa yakeyi " yayanta? Ammi ta tambaya da mamaki ,kenan ba tare da iyayenta take ba ? Shiru Aunty tayi saboda bata san me tambayar matar ke nufi ba shin bata san Meerah batada iyaye bane ko ba itace Hajia Sauda din ba ? Ganin haka se Ammi ta tashi tana fadin to mu zamu tafi ina sallah ma naji me gidan ya kira waya nasan xece mu fito ne munbarshi a motor " Allah sarki Hajia tare kuke kenan ,bazaku tsaya kuci tuwo ba " Daria Ammi tayi tace "maci watarana inda rabo yanzu dai muna sauri ne " to mun gode Hajia Allah ya saka da Alkhairi ,har sun fito se Aunty tace Hajia jirani dan Allah " babu musu kuwa su Ammi suka tsaya kayan da suka gani a tsakar gida ne ta buɗe ta ɗauko musu ledan alewa da cingum ,Nawwara ta mikawa tana faɗin " kusa albarka kuma ,kayan sa ranar Meerah ne auren ta nanda 2weeks insha'Allah " aure ? Ammi ta furta da ɗan ƙarfi dama aure zakuyi mata? Amma meyasa zakuyi mata aure tun yanzu ku kuwa ,kuma ita din bata faɗa mana ba "Hajia auren nan yanzu haka itama batasan da zancen ba se zuwa anjima yayanta xe sanar da ita ,wlh ni kaina banso hakan ta kasance ba dan nice nasan wacece Meerah nasan se anyi gwagwarmaya ko zata amince " jiki a sanyaye Ammi tace " to Allah ya sanya Alkhairi , insha'Allah kuwa zanzo"

Lokacin da Ammi ke fadin zatazo yayi daidai da zuwan Meerah wurin dan dama ita bata fito ba ta tsaya neman wayarta dan ta haska ta takasu kasancewar duhun Isha yakawo kai ga babu nepa duhu sosai ne a lungu su ,dan haka bata kawo komai a ranta ba ta tafi rakasu ita kuma Aunty ta koma ciki.

Jiki a sanyaye Ammi ta shiga Mota wanda har Dady seda ya fahimci sauyin yanayi da ta samu , sedai be tambaye ta ba har suka koma gida .

Meerah ma tana dawowa gida tambayar da tafara yiwa Aunty kenan "kayan miye na gani a gidan nan ?". Shiru Aunty tayi tana kallon ta da bata san ta inda zata fara yi mata bayanin ba ,ganin ta matsa ne yasakatafaɗin" Ameerah yayanki yayi kokari sosai wurin kula da ke ya kyautata miki fiye da tunani bawai ina yi miki gori bane ,inaso kisani cewa baze taɓa yin abunda yasan cewar ze cutar da ke ba muna sonki Meerah kuma burinmu ya za'a yi rayuwarki ta inganta ya za'ayi kiji daɗi irin na kowace ƴa mace ,muna da tabbacin zakiji daɗin hukuncin da muka zartar kanki ,duk da bamu tuntuɓe ki ba munyi miki shishigi cikin rayuwar ki Meerah ki daure a karo na farko nake roƙonki kar ki watsa mana ƙasa a ido mu ɗin nan masu sonki ne kuma komai kikaga ya faru da bawa to yana cikin littafin Qaddarar sa ne kin daɗe kina roƙon Allah yayi miki zaɓi a rayuwar ki to ki ɗauka wannan shine zaɓin da yayi miki ,kimanta da komai duk wani buri naki ki yi haƙuri wata ƙila ma inda zakije Allah ya baki damar ɗaukar fansa cikin sauki ze iya kasancewar kuma base ke kin ɗauki fansa ba Allah zeyi maganin ta da kanshi ,Ameerah wanann kayan da kika gani kayan auren ki ne aka kawo maganar da nake miki har sadaki yayanki ya amsa ya kuma tsayar da ranar auren nan da sati biyu ,tare da amincewa ta duk da zuciya ta cike take da zullumin yadda zaki ɗauki al'amarin ,amma karki cuci kanki idan har kinsan bazaki iya mana biyayya ba to ƙofa abuɗe take se mu maida musu da kayan su".


Jikin Meerah babu inda baya rawa ,tunda Aunty ta fara maganar jikinta yayi sanyi auren da ta ambata kuma se ya haifar mata da karkarwa

"Kinyi shiru Ameerah ,baki so ko? Kiyi hakuri Bara ya dawo zan sanar dashi ya maida musu kayansu dama seda na faɗa masa mutuƙar baki amince ba to baza'ayi miki tilas ba " still dai Meerah bata ce komai ba ,haka Aunty ta ƙarashi surutun ta tagaji ta shige ɗaki tabar Meerah nan zaune

Ameerah kuwa banda zagaye babu abinda Kanta keyi tunani takeyi shin mafalki ne ko da gaske wai aure ta nan da 2 weeks to waye mijin? Shine tambayar da zuciyarta keyi sedai bakinta yaki bata haɗin kan da zata tambaya lokacin da Aunty ke sanar da ita ,haka ta ci gaba da zama wurin har aka fara kiran sallar isha' har aka gama bata motsa ba se kusan 9pm ta samu daƙyar ta ja ƙafarta tayi alwala tayi sallar isha'i da batayi ba ,tana sallamewa ko addu'a batayi ta zame a wurin ta kwanta ,tama rasa wane irin tunani zatayi ,a wannan yanayin Aunty tazo kiranta wai yayanta yana neman ta ,ko ba'a faɗa mata ba tasan dai zancen ɗaya ne ,dan haka bata ce komai ba tabi bayanta .

Cikin dasashiyar murya ta gaishe shi kamar tayi kuka ,wanda har se da yanayin Muryar ta yasa ya ɗago ya kalleta " bakida lafiya ne? " . Ya tambaye ta ,kai kawai ta girgiza masa alamar a'a dan haka ya soma kora mata bayani duk da dai maganar da tayi zato ita dince " Ameerah na bada auren kine a bisa wani dalili nawa ,kuma ina tunanin hakan xe temaki rayuwar ki ,kuma Auntyn ki ta shedamin cewar kina son sa ,kuma zakiyi daraja a gare su ,ina gaya miki girma da darajar iyayensa ne yayimin kwarjini na kasa Musa musu ,xe fita wajene wani aiki ya samu a can kuma matar shi tace ita bazata bishi ba saboda ita ma tana aikine a nan sukuma iyayensa sukace basu amince ya fita babu mata ba ,dan haka yazo neman auren ki ,da farko ban amince ba seda iyayen sa sukaxo da magiya,nace se nayi shawara da Auntyn ki ,itace tace na amince a ganinta wani dama ne zaki samu da zaki inganta rayuwar ki kema kuma zakiyi karatun da kike so a can ,amma karki cuci kanki idan baki amince ba" Yaya wai waye ? Kafin yabata amsa Aunty tace " Manager ne Muhsin Abban su Hanifa " shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhari a garemu "jin furucinta ya matuƙar faranta ransu dan haka sukayi ta saka mata albarka tare da fatan wannan auren yazama silar farincin ta na har abada

Ammi.........




Comments and share pls


#Real@Bazamfaria❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:3️⃣2️⃣


Ammi
Har suka koma gida babu walwala a tare da ita ,har se da Rumaisa ta fahimci hakan " Ammi ko wani abu ya faru ne a fitar da kukayi? Kallon Rumaisa tayi tace " me kika gani? Kawai dai naga kamar kin shiga damuwa ne " babu komai ,Rumaisa ai har gidansu Ameerah muka tafi kinga alewa ma anbamu wai na auren ta nan da sati biyu masu zuwa " washe baki Rumaisa tayi tana duba alawan " kai Masha'Allah,amma wlh nayi mata murna zata huta da bautar wasu tayi auren ta duda kam tana da ƙarancin shekaru Allah ya sanya Alkhairi kusan tare da na su Yaya ma kenan aikam zamuje mata biki"

Ammi dai bata ce komai ba se bin ta da ido ganin yadda take ta washe baki.

Haka Meerah ta kwanta a wannan daren badan ta na tunanin bacci xe iya ɗaukan ta ba se juyi kawai takeyi tarasa dalilin Muhsin na yi mata wannan aika-aikar dan ita bata wani yarda cewa uzurin tafiya ne yasaka shi yin haka ba Idan ma haka ne kamata yayi ya tuntuɓeta kafin yazo wurin iyayenta ,taso ta kira shi amma setaga rashin dacewar hakan tunda har shi be ne Meta ba to ita ma bazata neme shi ba kuwa ko hakan yana nufin har zuwa ranar da za'a kaita gidan shi.


Biki se ƙara kankama yake shirye shirye akeyi a ɓangaren Ammi dan suna saka ran fara saukan baƙi a gobe da bikin yayi saura sati ɗaya ,dan haka duk wasu ɗakuna da ke rufe a sashen ta ta saka an buɗe an gyara su fess , ɓangaren Hajia Sauda kam sha'anin gaban ta kawai takeyi dan tabarwa Hajia Laura wuƙa da naman yi duk abinda take ganin mafita ne gareta.

tunda Muhsin ya kawo kayan auren besake zuwa gidan su Meerah ba kuma be nemeta a waya ba dan yana tsoron rikicin da zata iya yi masa ,ita kuma hakan da yayi se ya ƙara ƙona ranta ,tafara tunanin kawai auren rashin mafita ne zeyi mata tunda matarsa ita tanada abunyi tace bazata bishi ba ,shine yayi anfani da talaucin su yazo wurinta ,tana wannan tunanin hawaye yafara bin fuskanta ,tausayin kanta takeyi ,wannan wane irin aure ne to zatayi ace baze ma kira yaji me take bukata ba ,juyi kawai take kan katifar batasan shigowar Aunty ba sedai taji ta rungumota daga kwancen da take tana share mata hawayen fuskanta ,ai kamar jira take se ta sake fashewa da kuka me ƙarfi ,Aunty batace da ita komai ba se tapping bayanta da takeyi alamar rarrashi seda ta fara ajiyar zuciya alamar tayi kukan me isarta kenan ,kafin Aunty tafara yi mata magana " menene damuwar ki Meerah,idan auren nan ne bakiso wlh se a fasa ni bazan lamunci ganinki cikin wannan yanayin na damuwa ba kece da kanki fa kika ce kin amince ko Muhsin ɗin yayi miki wani abu ne?".

"Aunty yau kusan sati ɗaya kenan fa da ya kawo kudin auren sa gidan nan ,amma ko a waya be nemeni ba bare yazo gidan nan me hakan ke nufi? "Baya nufin komai Ameerah Yakamata kiyi masa uzuri ,jiyama ya kirani yake sanar dani be samu zama bane yana cuku-cukun tafiyar ne ,amma idan ya samu lokaci yau ze shigo ,shiyasa ma nazo na tambayeki ko akwai abunda zakiyi na tarbonsa se gashi na sameki kina kuka " haba Aunty beda number na ne ko me ni ban isa ya kira ya sanar min bane komai ,nifa dama nasan dalilin da yasa ya biyo ta wurinku kenan to ni yayi zaman sa bana buƙatar zuwan sa ya jira se ankaini gidan sa yanzu ma barin gidan nan zanyi "

Da ido Aunty ke binta ,dan ganin sabon halin da take ƙoƙarin takitawa kanta ,har tagama surutan ta ,tashi Aunty tayi tace " nide na faɗa miki ze zo kuma zaki fita.

Misalin ƙarfe 5 na yamma kuwa ya iso gidan ,be kirata ba se ya kira Aunty ya sanar da ita zuwan shi ,haka ta tasa Meerah ta sauya kayan jikin ta ta fito ,kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin damuwa idonta sunyi ja sosai ga kumburin da sukayi daga sama alamun ta daɗe tana kuka ,a zaune ta sameshi cikin zauren gidan ,an shimfida masa dadduma ,tasan aikin Aunty ne dan haka ta samu wuri daga dan nesa kaɗan ta zauna ,bata ce masa komai ba se ma binsa da ido da takeyi " Subhanallah Ameerah badai zancen auren mu ne ya sanya ki shiga cikin wannan yanayin ba ,Kinganki kuwa? daga jin yadda Muhsin keyi mata tambayar kasan hankalinsa ya tashi ganinta cikin wannan yanayin ,share hawayen da suka zubo mata tayi cikin dasashiyar murya tace

"Abban Hanifa me ya kawo ka wurina da har kake tunanin zaka aureni ta hanyar da ka biyo ?" Soyayya" shine amsar da yabata a takaice ,wani irin Murmushi tayi me hade da hawaye wanda ke bayyanar da irin kuncin da zuciyarta ke ciki ,tace " Soyayyah tanada matuqar tasiri,tasirinta yana dawwamane a ckin zuciya yanada tsantsar karfi yana kuma sanya zuciya ta jigata qarfin tasirinsa yawuce misali d hasashe.idan soyayyah tasamu tanada matuqar tasiri haka kuma tana mallakar wani qarqarfan qarfi ne Wanda zaizamo tubalin dake manne d ruhin dan Adam, ina faɗa maka ma'anar soyayya ne ,to a tunanin ka taya za'a mallaki wannan karfe? dole hanya ɗaya ce idan kana so ana sonka , meyasa kai baka yi wannan tunanin ba kafin ka samu magabatana? ko da yake bazakayi ba saboda ku masu kudi a koda yaushe nasara kuka sani ba faɗuwa ba ,amma karkayi tunanin zan aure ka saboda soyayya ne ko ɗaya auren biyayya zanyi maka domin bazan iya cewa a'a ga magabata na ba ,saboda haka kayi tunanin yadda zaman biyayya yake saɓanin na soyayya ,idan zuciyar ka ta amince a haka zata zauna da ni shikenan ,tawa ƙaddarar kenan "tana gama faɗa ta sake fashewa da kuka .

Duk da bata fito kai tsaye tace bata son shi ba amma kalaman ta sun isar da sakon ta zuwa gareshi ,tabbas da ze iya haƙura da ita to da ya barta sedai Allah ya sani so ne yake mata na gaskiya kuma yana da tabbacin itama watarana dole zata so shi ,dan haka duk wannan kalaman nata baze dameshi ba , handkerchief ya Ciro daga aljihunsa ,batayi tsammani ba se ganin sa tayi tsugune a gabanta yana share mata hawayen fuskan ta ,wani irin baƙin ciki taji ya sake lulluɓeta,lallai se yanzu take nadamar sake masa da tayi tun farko ga abinda yayi mata yanzu

" zan shiga daga ciki dan naga kamar baka da abun faɗa '' Murmushin gefen baki yayi yace " dole zan rasa abun faɗa tunda kin ƙaramin ƙarfin gwiwa tare da tabbacin cewar zanji dadin rayuwa da ke a matsayin mata ta ,na gode ma Allah da har kika fahimci menene soyayya da abubuwan da ke samar da ita ,hakan yabani tabbacin cewar zaki soni watarana ko da a yanzu ma bazan iya cewa baki so na ba ,kiyi haƙuri Ameerah kisani Allah ne yayi keɗin rabo na ce kuma duk kiyayyar da zaki nuna baze saka a fasa abinda Allah ya rubuta ba mace bata auren mijin da ba rabon ta ba ina sonki ,kuma ina fatan kema ki so ni. Nazo ne domin naji abubuwan da kike da buƙata ,kiyi hakuri da jina shiru da kikayi".

"baka tambayi ra'ayina ba kafin kazo gidanmu ,bana tunanin yanzu dan kazo tambayar ra'ayina zaka burgeni ,bana buƙatar komai se alfarmar da zan roƙa kar ka sake zuwa gidan nan kabari har se ankawo ni gidan ka " ko zan iya sanin dalilin fadar hakan? babu wani dalili ra'ayina ne kawai ,ina kwanaki ne ya rage kamar yadda ka buƙata ,to se ka jira se an kawo Ni amma dai ko kazo bazan fito ba "hmmmm to shikenan kifaɗawa Aunty za'a kawo kayan lefe zuwa gobe ko jibi idan Allah ya kaimu " yanzu da ka kira kafaɗa mata zaka zo wani har ta tursasani fitowa wani ka aika? se ka sanar mata da kanka danni banda wannan lokacin "au yanzu saboda Allah Meerah har se da aka tursasaki kafin kika zo gareni? Bata tankashi ba tayi shigewar ta ciki ,Murmushi yayi dan shi a tunanin sa tana son sa kawai ƙuruciya ne ya hanata ta gane hakan ,ko kuma wata ƙila akwai irin yarannan da suke

Please Login or Register in order to submit comment