Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sane da sa idon da mutanen gari sukayi mana ko? to ki kwantar da hankalinki ,ki ta tsesa sosai kuma ai zaku iya riƙa anfani da ita ku duka biyun Kinga kenan riba kan riba" Hakane fa Kinga farko duk banyi wannan tunanin ba ,amma Hajia Sauda yaushe ne tafiyar ina fatan dai bazaki ɗauki lokaci a can ba?".

"Ehhh to kema kinsan badan Alh yace ze dawo daga Cyprus ba to babu abinda zesa na koma gida yanzu ,to bazan iya barma munafukar matarsa shi ba ,shegiya wai ita me kirki duk abinda zanyi mata bazata taɓa tankani ba ,shiyasa nagaji na ƙyaleta ,raina yana baci idan naga tana mammanewa Alh" tafaɗa cikeda takaici ,tsaki Hajia Laura tayi tace "wlh Hajia ni kina bani mamaki ,miye abun kishi ga namiji ,bayan macece keyi miki abinda ko rabinsa baze iya yimiki ba ,ni da zaki bi nawa ma da kinbar mata shi can su karata ,amma ina mamakin me wanan Alh yake da kike masa wannan son har kike ɓoyemana saninsa ,ko kina tunanin zamu iya kwace Miki shine,kinsani dai ni Namiji baya gabana ,idan ko kikaga nabashi kaina to inada bukatar wani abunne" Murmushi Hajia saudah tayi tace " komai zan faɗa baza ku gane ba mijina ba kamar sauran mazan bane shidin na dabanne ,ni ce nasan kan abuna ,saboda haka kudena ma tunanin wai zan barshi ,a'a ko ba komai auren ma wani kariya ne a tunanin ku idan da banda aure waye ze yarda da zaman nan da Nike ai dole za'a zargeni ,amma da yake Alh wayayyen mutun ne rayuwar sa irin na turawa baya tauyewa mutum hakkinsa tunda na faɗa masa dalilin zamana anan shikennan ya yarda so kudena wanna maganar ,jibi zan tafi amma bazanfi sati ɗaya ba dan a wannan karon inaso na shiga kauye saboda na samo mana yaran da suka dace"

da harara suka bita a kaikaice ,saboda sunajin haushin yadda take nuna mijinta yafi kowa, bayan wasu daga cikinsu a ta dalilinta suka rasa nasu auren........




Follow me on wattpad@damselfeedo



Real Bazamfaria❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:1️⃣4️⃣


Ameerah#

A ƙofar gidansu ta tarad da wata haɗaɗdiyar motor tayi parking,da kallo takebin motar Kasan cewar baƙin galass ne bata iya ganin wanda yake ciki ,sedai a zuciyarta tana mamakin wanda yayi kasadar shigowa da mota lungun su dan ta tabbata se yasha wuya kafin yafita ,idan ma beyi Sa'a ba yaran unguwar zasu zane masa mota ,janye idon ta daga motar tayi tanufi shiga cikin gidan su " Ameerah" ta tsinkayi ankirata da wani calm voice ,faɗuwa taji gabanta yayi batasan dalili ba , addu'a tayi tana jiyowa dan ganin wanda ya kirata ,jiyowanta yayi dai² da isowarshi inda take ,dan zare ido tayi ganin kamar ta ganeshi ,shine mutumin nan da yataɓa neman ta shiga motan shi

" Kinyi mamakin ganina ko? ai nafi 2 hours a wurin nan ina jiran dawowar ki saboda na fahimci kamar bakison magana a titi ,any way sunana Muhsin ni managern banki ne ,inada mata da yara biyu kuma gaskiya a da banda ra'ayin karin aure saboda gwargwado matata tana kula dani amma tunda na ganki naji na kamu da sonki ,shiyasa ranar da kika ƙi yarda nakawo kiga se nabiyo bayanki har seda naga unguwar da kike ,fatan zan samu karɓuwa a gareki"ya ƙara sa yana kafeta da ido.

Kamar yadda yake kallon ta ita ma kallon sa takeyi ,dan sosai yabata mamaki,koda bata taɓa soyayya ba amma bata tunanin haka tsarin yake ,daga ganinta bema nemi izinin ta saurare shi ba kawai ya saki baki se zuba yake ,koda ace tanada ra'ayin soyaya ma yanayin tsarin sa beyi mata ba " ke nike saurare ranki ya daɗe " murmushi tayi wanda ya kasance kamar halayyarta ne yawan yinsa ,cikin sanyin murya ita ma tace " kayi haƙuri baza'a barni nayi soyayya a yanzu ba" tana faɗa masa bata jira jin me zece ba kawai tayi shigewarta gida kasancewar dama a bakin zauren gidan suke.

Murmushi Muhsin yayi dan ze iya cewa ya hango alamun nasara dan ya fahimci yarinyar xatayi sauƙin kai,bin gidansu yayi da ido a ranshi yace "tabbas masu kyau na irin wuraren nan wanda talauci ya boye a gansu bare har a ga kyansu yanzu wannan da ace gidan masu kuɗi take aikam da se irin yaran masu kuɗi nan zata aura" matarshi ya koma se gashi yafito da wata leda a hannunsa irin na shopping dinnan ,duk da dai kayan ciki kamar bamasu yawa bane saboda ledan ba wata babba bace ,waige² yafarayi dan neman yaron da ze aika,cikin Sa'a ko ya ga wani yaro ya fito daga wani gida kiran yaron yayi ya basa ledar yace " shiga ka kaiwa Ameerah kaji"

Koda Ameerah ta shiga gidan ta same Aunty zaune kan tabarma daga dan jikin kitchen ɗin su inda inuwa tafara kaiwa ,a gajiya ta zube itama tana faɗin "wash "sannu kin gaji ko" wlh kuwa Aunty nagaji ga yau garin ana rana ,yunwa ma nikeji me kika dafa mana? "Bansani ba haka kawai kina wahalar da kanki, ni tsoron da nikeji ma kar se yayanki ya dawo ya ce baxaki ci gaba ba" toro baki tayi tace nide Aunty kibani abinci naci kinji " tashi tayi ta dauko mata abincin harda pure water me sanyi ta kawo mata "tnx Aunty na uwar gidan yaya ,idan dai kikaci gaba damin irin wannan ai zan hana yayana ya karo aure " au Meerah kice da har yana tunanin ƙarin aure anya yarinyar nan ba wani shirin kikeyi dashi ba? hhhhh Aunty kenan kema kinsan ai daga ke ba ƙari"dariya itama Aunty tayi tace " Meerah aishi ƙarin aure ƙaddara ne bare ma ni dinnan idan na hana yayanki yaƙara aure ai banyi masa adalci ba ,tunda dai kingani ni ba haihuwa nikeyi ba ko a haka yayimin halacci duk da nasan yana buƙatar yara amma yana ƙoƙarin ɓoyemin" ajiye cibin da ke hannun ta tayi ,tace " haba Aunty kinsanfa likitoci sun tabbatar da lafiyan ku lau ku duka kawai dai lokacine beyi wa ,wani rabon a nesa yake , Insha'Allah very soon zaki haifa mana babies karki just we shall keep on praying" ganin kamar Meerah ta damu ne se Aunty tayi Murmushi tace " karki damu Meerah kinji ,ɗazu ma anzo neman ki ,wai wani ko wa nade manta sunan da yaron ya faɗa nace bakinan ,hala ko na samu surikine" tafaɗa cikin zolaya ,rufe ido Meerah tayi ,kafin tayi magana ma se ga yaron da Muhsin ya aiko ya shigo Meerah ya mikawa ledar yace "Aunty wai gashi inji wani me mota " kasan cewar duk yaran unguwar da haka suke kiranta dan duk ranar Thursday nd Friday tana tarasu tayi musu lesson ,shiyasa dukansu suke sonta saboda tana da son yara

Da ido suke binsa daga ita har aunty.

Ganin ita batada niyyar karɓa ,se Aunty ta karɓa tace " kace ta gode"

Ajiye ledar Aunty tayi batare da ta buɗe ba ,tace " wai Meerah ba yunwa kikace kinaji ba se wasa kikeyi da abincin idan baxaki ci ba ai da rufewa kikayi" batace komai ba ta ci gaba da tsakurar abincin dan neman yunwar da takeji tayi ta rasa tunani take waye Muhsin kuma menene dalilinsa nayi mata haka ,ok ko yayi ne saboda ya dauka ita maƙwaɗaiciya ce ,abun hannun sa zesa ta so shi " kayi a banza dan bazan taɓa son ka ba " kideyi a hankali bakinsa gaba ba wataƙil zaki iya son sa" seda taji maganar aunty ne sannan ta gane cewar a fili ta faɗi maganar ,rufe abincin dake gaban ta tayi tace " Aunty wlh fa ni ban san shi ba bansa wanda ya nuna masa gidan nan ba ,kuma saboda beda kunya wai har yake faɗa min yana sona ,ni me zanyi da wanda yakeda mata? Dariya Aunty tayi tace ,kice saboda matar sa kike kishi to ke miye naki tunda yasan yanada matar kuma yace yana sonki,idan dai har da gaske yake yi nikam zanyi murna gaskiya saboda irin mijin da nike roƙa mikine yazo Meerah inaso kisamu rayuwa me ingancin idan kika aure talaka hakan baze samu ba inason kisamu mijin da ze dawo da jin daɗin da kika rasa " haba Aunty kidena ma wannan maganar aishi jin daɗi base ga me kuɗi kawai ake samu ba kedai kiyi fatan samun miji nagari shine jin daɗin mace nawa ke auren masu kuɗin amma basuda kwanciyar hankali,yanzu keɗinnan yaya da Rufin asirin da Allah yayi masa ya riƙeki harma ni ɗinnan kuma saboda son da yake Miki ne kullum cikin soyayya da kulawa kuke ,na tabbata kinfi wasu matan masu kuɗin kwanciyar hankali,saboda haka ni duk wanda zan aura gaskiya se wanda ya iya soyayya sosai dan nikam nafison soyayya da kulawa Fiye da komai" ikon Allah Meerah yau ni kike faɗawa kinfison soyyaya idan kikayi aure? Daria sosai Meerah tayi tace " kai Aunty ai gara na faɗa Miki tunda kece uwar amarya,ƙawarta kuma yayarta so duk kika ga na kawo mijin auren gidan nan ,wanda be iya soyayya ba karma ki amince na aure sa dan ba zama zanyi ba" dariya kawai Aunty tayi tace to buɗe mana ledar muga me mota me ya kawowa ƙanwata" perfumes ne masu kanshi da tsada har kala 3 se wani dan card da alama complementary card dinsa ne " Masha'Allah kam Meerah da gani wannan yasan takan soyayya baki gani ba kyautar turare a zuwan farko nide shawara gaskiya karki wulaƙanta sa bamusan me Allah xeyi nan gaba ba ,Kinga wuce da turaren ɗakin ki kinsamu na shafawa " a'a Aunty kiɗauka dai keda kikeda miji zefi miki anfani" hararanta Aunty tayi tace" banson shirme maza kwashe abunki " Allah aunty ki ɗauka duka na baki ai inada sauran turaren da yaya yakawo mana da yazo " duk da haka dai Meerah kiyi anfani da wannan ɗin " to gaskiya aunty kiɗauki biyu Ni se nayi anfani da ɗaya" haka dai suketa musu daƙyar Aunty ta yarda ta ɗauki ɗaya daga cikin turarukan.

Da daddare bayan sun gama sallahr isha'i suna zaune itada aunty take faɗa mata cewar dazu da sukayi waya da yaya yace xe dawo karshen makon nan ,cike da jin daɗi Meerah tace "Allah ya dawo dashi lafiya kwana biyun nan ban samu zama ba mundaɗe bamuyi waya dashi ba ,koda ma aini fushi nikeyi dashi tunda ko tambayata bayayi" Dariya Aunty tayi tace ai kunfi kusa idan yadawo sekuyi Shari'a keda shi.

daga tsakar gida suke jin sallama wai ana kiran Aunty Meerah a waye ,kallon juna sukayi itada Aunty kafin tayi ƙarfin halin fitowa ganin yaron tace "Jabir kaine waya aiko ka kirana cikin daren nan? " Wanine dan gaju Aunty bakiji kanshin tutarensa ba kuma ma da ƙatuwar mota yaxo" tunda taji haka ta gane Muhsin ne " jeka kace tayi bacci kaji" har ya juya ze tafi Aunty da fitowar ta daga daki kenan tace Jabir jeka kace tana zuwa ,kallon Aunty tayi tana narke fuska kamar xatayi kuka tace amma Aunty me ze kawo shi cikin daren nan bayan ɗazu yazo ni wlh banson maita daga ganin sa xeyi naci sosai "kitsaya shegen musunki dai karki yi sauri kita fi ,kasan wayar dake hannun Aunty ta karɓa dan tayi anfani da toch light ɗin kasancewar akwai hijabi a jikinta ,ta tafi.

A bakin zauren gidan tayi tsaye tana kallonsa daga inda yayi parking marfin motarsa a buɗe ƙafarsa daya a waje saboda akwai hasken farinta wata shiyasa zaka iya ganin komai

Muhsin ma tunda tafito yake kallonta a tunaninsa zata karaso wurin da yake ne ,amma Sega ta tsaya hakan ya tabbatar masa da sedai shi ya sameta kenan , murmushi yayi dan garga Allah jan ajinta ya burgesa ,da sallama ya karaso ,itama bata ɓata lokaci ba ta amsa masa dan sanin muhimmanci sallama da tayi ,daganan kuma sukayi shiru ,shidai ƙare mata kallo yake a yayin da ita bata masan yanayi ba dan ta duƙar da kanta kasa tana wasa da wayar hannun ta ,katse shirun yayi da faɗin " ina wuni" harga Allah ita ta manta da bata gaida shi ba ,rufe fuska tayi ta ce " yi hakuri dan Allah na sha'afa ne ,ina wuni ya gida da yara? Cikin jin daɗi ya ce duk suna lafiya yara sunce na gaida musu da Auntyn su kafin su zo da kansu su gaisheta"

Kallon mamaki tayi masa se kuma tayi murmushi tace "har sun samu labarina tun banyi accepting ba kenan" dariya yayi " ai nasan zuciyata bazata taɓa son abinda baze so ta ba tunda na ganki ta faɗa min cewar ga abokiyar rayuwa ta sake zaɓa min a karo na biyu

idan babu damuwa ko zamu ƙara sa daga cikin mota saboda gaskiya akwai abinda nikeso na faɗa miki ,kuma kema zanzo nasan ke wacece a takaice " a'a karka damu ni yanzu ma zan shiga da ga ciki ne and gaskiya bana tunanin zan shiga motar ka da sunan hira ,kaganni ko kaga kuma gidanmu ,so idan kana ganin bazaka iya tsayuwa anan ba sedai ka hakura ,banada wurin ajiye ka dayafi wannan ,hira a mota yana zubar da mutunci and be kamata ma a matsayin mu na musulmai muriƙa kebe wa a mota mubiyu da suna hira dan munsan illar hakan ,dazu naga sako amma gsky banji daɗin hakan ba nide karka sake kawomin wani abu pls" to shikenan naji Insha'Allah zan kiyaye ,but tunda kince baxaki riƙa shiga moto ba se Nike ganin kamar tsayuwar anan ma ze iya zubar da mutuncin why not kibani tym da zan riƙa zuwa Kinga se muriƙa shiga daga zaure ko kamar hakan zefi " ehhh to amma kabani kwana biyu zanyi tunani akan hakan kuma dan Allah karka sake zuwa a week dinnan dan bazaka samu ganina ba akwai yan ayukka da Nike yi " yadda kike so haka za'ayi duk da nasan zuciyata xatayi ƙunci na rashin ganin ki har kwana biyu zuwa uku,sedai zaki bani contact naki Kinga se na rika kiranki hakan ze rage min kewarki " shiru tayi kamar karta bashi ,sedai ganin ko bata bashi ba tunda har yasan hanyar neman gidansu ,to contacts nata baze masa wuya ba ,saboda haka bata Musa ba ta bashi ,godiya sosai yayi mata har zata shiga gida yace " am bakiji ba" dawo wa tayi tace " mefa? Yace yaranki sun bada sakon gaisuwa nakawo Miki but baki basu nasu sakon ba " murmushi ta saki batare da ta shirya ba" kace ina amsawa sosai ,nima kuma ina gaishe su yaushe zasu zo su gaisheni? to zan faɗa musu se su saka ranar zuwa gaisheki da kansu.........



*Am sorry* *nayi anfani da wasu kalmomi uku and ba lallai bane wasu daga cikin ku su gane saboda banbancin Hausa* a *inda *nace (Cibi) ina nufin (cokali.spoon) se kuma zaure ina nufin (soro) se hira ( zance ,ko taɗi)*

08039228702

*Wattpad@damselfeedo*

*Comments and share pls*

Real Bazamfaria ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:1️⃣5️⃣


Rufaidah da bata san da zancen dawowar Abban su ba kasan cewar bata shiga sha'anin mutanen gidan bare ta san hidimar da akeyi ba ,shiyasa tayi shirinta cikin atamfa riga da sket ,key din motar ta ta ɗauka ta fito ,daga falo take kwalawa Larai kira ,da sauri tazo ,abinda zata dafa mata da dare ta faɗa tana wani yamutsa face ,cikin girmamawa Larai tace " am Hajia fita zakiyi? Da ido Rufee tabita dan jin tambayar rainin wayo ,ya tana ganinta da gyale a hannu kuma take tambayar ta fita xatayi ,ganin haka yasa Larai fadin " yi hakuri dama gani nayi yau Alh ya dawo ,kuma nasan idan ya dawo dukanku babu wanda yake fita shiyasa Allah ya huci zuciyar ki " Larai kika ce Abba ya dawo fa? yaushe kuma ai ko shekaran jiya munyi waya dashi meyasa be faɗamin ba " ai dama nayi mamaki da naga yadawo baki fito nace kodai baki sani bane " lallai ba sunga Mama batanan ba shiyasa suka kwamushe sa a part nasu ,su muna fukai ,a jiye gyalen hannun ta tayi tafita cikin fushi.

Motocin da tagani a fake harabar gidan ne yaƙara tabbatar mata da maganar Larai ,idan ranta yayi dubu to ya ɓaci ,saboda haka kai tsaye ta shiga party ɗinsu Mu'aiseen tana shiga duka hankalin su yadawo kanta , kasancewar lokacin duk suna hira ne a tsakaninsu da ido take bin kowanne daga cikinsu sedai bataga Abban ba ,ganin ko sallama batayi ba yasaka dukansu babu wanda ya tanka ta sema ci gaba da hirar su sukeyi ,haɗe fuska tayi ,cikeda rashin mutun ci take " se a wani tsare mutum da ido kamar ba'a san shi ba " ta karasa faɗa tana jan tsaki " ke Rufaidah iskancin ki ya tsaya can sashen ku ,wlh baxaki zo nan kinemi rainamana hankali ba " Rumaisa ta faɗa cikin fushi itama ,da ido Ammin su tayi mata alama da tayi shiru ,duƙar da kanta tayi kasa saboda a duniya idan akwai abinda ta tsana be wuce rashin kirkin da Rufee keyiwa Ammin su ba kuma idan zasuyi nagana se ta hanasu "ke Rumaisa yaushe nafara wasa dake da har zaki gayan magana ,ke kinsani ganina a part dinnann dalili ne badan Ubana da aka hanashi zuwa dubani ba saboda munafurci ,ai da babu abinda ze kawo ni anan ...bata samu karasa maganar ta ba saboda tsawar da aka daka mata ,ba ita ba hatta su Rumaisa seda sukaji tsoro ,cikin kakkausar murya Mu'aiseen da fitowar sa daga ɗakinsa kenan kunnunwan sa yajiyo masa rashin kunyar da takeyi yace " zan babballaki Rufaidah meyasa ke sam bakida kunya ne waye zeyi miki muna furci anan ,ke san bakisan ki girma ma kowa ba ko maza barnan"ya nuna mata hanya ,marairaicewa tayi saboda harga Allah batasan cewar yana gidan ba dan bata kula da motar sa ba ,dan duk iskancin da takeyi batayi a gabansa ,duk da yana da saukin kai amma matuƙar aka taba Ammi tofa baya sararawa kowa ,kuma ko bacin haka ,ita duk duniya babu wanda take so kuma take fatar ta aura kamar Mu'aiseen, dan kuwa ya haɗa duk wani abun da mace zata so a wurin namiji.tsawar da yasake daka mata ne yasaka ta saurin kankameshi tare da fashewa da kuka ,duka suka bita da kallon mamaki ,ganin yadda ta rikeshi kamar wacce zata shige ciki ,ko kunyar Ammi bataji ba

Sannu da fitowar da taji yaran sunayiwa Abbane ya saka ta ɗagowa ta kalleshi ganinsa tayi cikin farar jalabiya,sajen fuskarsa ya sake kwantawa ,sakin sa tayi da gudu ta tafi wurin Abba tana kara fashewa da kuka ,jan hannunta Abba yayi ya zaunar kan kujera kafin shima ya zauna cikeda kulawa yace " me akayi wa ƴar shagwaɓa ta take kuka haka? Haba Abba yanzu shikennan saboda anga Mama batanan shine har zaka dawo gidan nan bansani ba kuma baka nemeni ba ,shi ne nashigo na gaishe ka Rumaisa tayimin Rashin kunya nayi magana shine yaya Mu'aiseen yake min tsawa " tasake fashewa da kuka

Kallon Rumaisa Abba yayi yace " Rumaisa meyasa kikayiwa yayarki rashin kunya? Rasa abun cewa Rumaisa tayi se kawai tace " Abba tayi hakuri to ni ba rashin kunya nayi mata ba "dawo da idon sa yayi kan Mu'aiseen da yahaɗe fuska yace " Mu'aiseen kariƙa bincike kafin ka zarta hukun ci" haba Abba kasan me yarinyar nan tayi kuwa"Mu'aiseen"Ammi ta kira sunan sa ,batare da ya kalleta ba yace" ayi haƙuri Abba Insha'Allah zan kiyaye "yafadi hakanne dan yasan dalilin kiran da Ammi tayi masa kenan ,besake magana ba se kawai ya fita ya bar gidan dan ransa yagama baci

Lallahin Rufaidah Abba ya shiga yi daƙyar ta yi shiru se kuma suka shiga fira ita da shi ,kamar babu kowa a falon ganin haka Ammi ta tashi tashiga daga ciki itama Rumaisa kama hannun su Nurain tayi suka shige ɗaki ,dan ranta yagama baci da abinda Rufee tayi .

Rufaidah wai nikam ya zancen school kina zuwa kuwa? " Kai Abba na kammala fa 2 months kenan yanzu service kawai ya rage mana" kai Masha'Allah kice se aure kenan tunda angama karatu" dariya kawai tayi " so nikeyi na hadaku keda yar'uwarki na aurar duka na huta se naji da yan biyu na su Nurain" haɗe fuska tayi tace "nide gaskiya Abba baza'a haɗa bikina da kowa ba ,to yaushe ma ita ta girma duka duka fa yanzu take UG 3" dariya Abba yayi yace" lalai Rufaidah ko kunyata bakiji ba kike zancen baxaki jira Rumaisa ba , shikennan waye surikin nawa "lah Abba bawani bane fa a gidan nan yake" to ikon Allah waye nikam a gidan nan nide sani na ba bu wani namiji a gidan nan sedai masu yi mana hidma kuma nasan baacikin su bane "haba Abba dan Allah kadena ma zancen wa'yannan ai basa cikin lissafi" to shikennan dai yanzu faɗamin waye" uhmm ba yanzu ba "to shikennan babu damuwa nasan dai idan andafa a boye ai baza'aci boye ba idan tayi tsami ma ji" dariya Rufaidah tayi ,haka suka ci gaba da hira ,gwanin ban sha'awa kai bazakace ma da baban ta bane.

ta ɗauki tsawon lokaci anan part din kafin ta tashi tace " Abba bara na tafi ,Allah huta gajia "au wai har angama min hirar kenan " yamutsa face tayi " kawadai dai nasan kana bukatar hutu ne amma ai zaka shigo wurinmu ko? ta tsare shi da ido "zan shigo mana ,yanzu ma da zaki tsaya muyi dinner anan tare da yan' uwanki ,Rufaidah inaso naga kun haɗa kanku dukan ku abu ɗaya ne sam banajin daɗin rashin jituwar da bakuyi musamman keda Rumaisa ,dan Allah kicire duk wani damuwa a ranki dukan ku yayana ne kuma ina sonku, Kinga lokacin yayarku Amina ai bahaka takeyi ba tana son yan uwanta sosai "haba Abba to yanxu me nayi kana gani fa daga shigowa na suka nemi su walakanta ni ,taya zan riƙa zuwa inda ake munafurta na ,and dukansu nice yayyarsu so idan ma wani zebi wani sune yakamata ,any wai dai Abba zan wuce ina jiran zuwan ka" girgiza kai kawai yayi dan ya san halin Hajia saudah ne Rufaidah ta kwashe wanda Amina ita sam bata biyewa bakin halinsu zuwa goma idan xatayi gidan to se ta je ta gaishe da Ammi ,kuma tana jansu Rumaisa a jikinta.




*Manage pls wlh yau na* *fita ne *banaso* *nayi* *disappointed naku shiyasa nayi muku wannan**



Real Bazamfaria ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:1️⃣6️⃣


kamar kullum , Ameerah tayi shirinta da wuri dan zata iya cewa tunda tafara wannan aikin to bata taɓa saɓa lokacin da Rufee ta bata ba ,cikin doguwar rigar atamfa da ɗan farin hijabin ta yiwa Aunty sallama ta tafi

Saukanta daga kan mashin yayi dadai da zuwan Mu'aiseen,da alama ya dawo daga motsa jiki ne , da sauri ta biya me mashin kuɗin sa tashige ciki dan tana kula da irin kallon da yake yi mata.

A kitchen tasamu Larai gaisawa sukayi kafin ta shiga ciki dan fara aikin ta ,kamar kullum ƙasa take fara gyarawa kafin Rufee ta tashi bacci se ta gyara saman,cikin natsuwa take aikin ta ,bayan ta gama morpin se ta dawo guguan plasman da ke manne a falon , motsin da taji ne kamar anshigo yasakata waigawa dan a tunanin ta ko Larai ce sedai arba da tayi da wani Farin dattijo yana sanye da farar jalabiya se counter da ke makale a babban ya tsan sa ,sunkuyawa tayi tana gaishe shi ,cikin fari'a ya amsa mata tare da tambayar ta Rufaidah "bata riga ta tashi ba " shine amsar da ta bashi ,ganin bece

Please Login or Register in order to submit comment