Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai ki yi suna ko burge mutane,ba yan kin san haramun ne a addini kuma bayan haka malamin ahalari yace.Wal mar'atu kulliha aurati ma adal wajha wal kaffaini.Wato ita mace dukkannin ta al'aura ce sai dai fuska da tafukan hannaye. Gaskiya ya..."


" Wash Allah na! Wallahi Maman Najwa kin cika cika mutum wannan dalilin ya sa ban cika zuwa gidan ki ba.Ke kullum sai kin yi ma mutum wa'azi,ke da uztazi kika aura sai kin addabi mutum da wa'azi ina ga ko sallah mutum ya yi zaki ce ba dai-dai bane." Ta ɗan numfasa ko za ta ce wani abu sai ta ɗora da cewa jin ta yi shiru ajiyar zuciya ta sauke.

"In kin kira ni ne ki yi min wa'azi ba ni da buƙata matar liman sai kije masallaci ko in da ake buƙata.Ni ya maganar mu na fara yin sana'ar zuwa waje kin yi mishi bayani."Ta canza maganar don ta gundire ta ita ba ta da wani aki sai na yin wa'azi ita kam ba za ta iya ba,ita dai da ta ga za ta iya kashe rayuwar ta da kuruciyar ta sai ta yi Allah ya ba ta sa'a.


Dariya ta yi jin ta canza maganar tace." Na gaya miki tun ranar ni ba zai barni na fita zuwa wata ƙasa saro kaya ba,gara mu dinga basu kuɗin ko mu yi oder kin san yanzu komai a sauƙaƙe yake."

"Taɓ kin yi makaranta amma kamar baki waye ba ok da ma kina jira ya amince miki ne? Dama ba sana'ar kike so ki fara ba,ai koni da kika ji nace zan yi ba zan gaya mishi ba,sai ya ji na fara ke ranar da na ɗan sako mishi maganar Yayyina suna zuwa waje yin business,bai kalle ni ba yace ai da yake mazan na su mahaukata ne basu san mahimancin iyali ba.Shiru na yi bance komai ba ai sai dai ya ga na ɗaware inna dawo koma me zai faru ya faru Am ready for the conseqeuncy."


A ranta ta na girmama irin halin Zainab wacce sab ba ta tsoron miji ga shi Allah ya yi mijinta da son girma,sai dai bai samu macen da za ta ba shi wannan girma ba aiko za'a sha daru don shi ma ba daga baya ba.

" To shike nan Allah ya sa ki gane ni dai ba zan baki kuɗina ba kar mijin ki ya ji na baki,ni ina daraja aurena ke na lalata miki na ki gara na ba shi ya yi min oder hankalina kwance,sannan ki je ki rarrashe shi ki ji abin da ya haɗa su ko ma bai gaya miki ba don Allah ki ba shi kula kina sakaci da mijinki fa kar wata ta yi miki kwace."



Ta faɗa da tsigar tsokana duk da ta san Zainab yanzu za ta harzuƙo mata da shegen baƙin kishinta amma ta kasa kula da shi.


" Kinga ni ko zamu fara Allah babu wata matsiyaciyar mace da za ta shigo min gida,na kuma riga na gaya miki in ta yi wannan kuskuren to ta tabbata ni ce ajalin ta.Kuma hankalina kwance yake ya yi min alƙawari,wace mace za ta aure shi baya haihuwa ko ni haƙuri nake."



Faɗin likita ba Allah bane Zainab in Allah ya so sai ya haihu domin ubangiji yudabbirul amri ne ya na jujjuya lamaruran sa,don haka ban ji daɗin abin da kika faɗi haka kuma kinga ya na iyakan ƙoƙarin sa.


Zainab sai ta ji wani iri a ranta ta na fatan hakan don yanzu yadda A.m yake son ya haihu har yake zubar da hawaye ta na son ko ɗaya ne ta haifa mishi ita fa ba ta son tara yara.
" Ina fatan haka Allah ya amshi addu'armu sannan da kike cewa na je na rarrashe shi Allah ya sauwaƙe haka kawai kema kin faɗa min don ki tsokane ni ne ko?A kan maganar fita waje ai dama ban miki dole ba.Ni na gaji da wayar nan don takaici kike ƙara min zan shigo gidan ki kawai mu tautauna ki gashe min da yara."


Ta maza ta datse wayar ta na baƙin cikin halin da ƙawarta ta ɗaukar ma kanta saboda ta yi aure sai ta hana ci gaba a rayuwar ta?Tsaki ta yi ta ɗauki wayarta ta ta shige ɗaki zuwa can ta fito ta ci ado kamar wacce za ta gasar kyau,ta ɗauki key ɗin motarta da wayarta ta fice ta na ba za ƙamshi mai sanyaya zuciyar duk wanda ya yi katarin shaƙar shi.

A.m riƙe da waya a hannunsa a cikin haɗaɗɗen ofishin sa sai ya duba numbar A.k da nufin ya kira sai kuma ya yi cilli da wayar a kan duguwar kujerar da ke cikin ofishin.


Ya yi haka yafi sau a ƙirga gabaki ɗaya abubuwa sun rikice mishi a kampanin wanda har Daddy ya fara ƙorafi,ya sani A k wani jigo ne a cikin kampanin amma ransa ya ɓace ya je ya gaya mishi maganganu mara sa daɗi ga shi tun ba'a je ko ina ba ya fara dana sani.


" An ya Juwairaah auren ki alkhairi ne?"Ya faɗa da tsigar tambayar kansa saboda ganin da ya yi kan maganar auren ta kawai ya bata da aminin na sa wanda suka zama kamar ƴan'uwa.


Miƙewa ya yi ya tsaya a windon dake ofishinsa ya na kallon waje ganin Daddy ne da ƙaninsa yake tuƙa shi,ya yi maza ya fice daga ofishin tare da shigewa cikin wani ofis wanda ya san ba za su neme shi acan ba ya kulle kansa.


" Wayyo Allah na! Ya zan yi na san Daddy ya biyo ni ne ganin na ƙi ɗaukar wayarsa ga shi kwana biyu A.k bai zo ba abubuwa duk sun caɓe.


Sai ya yi shahadar kiran wayarsa duk da ya san ba dole ba ne ya ɗauka saboda ya yi fushi tunna mai tsanani da shi.


ilai kuwa wayar ba ta shiga wanda ya tabbatar mishi da ya yi blocking ɗin layin ne,ɗaga wayar ya yi zai yi jifa da ita sai ya fasa ganin kira ya shigo a ransa ya na addu'ar Allah ya saka shi ne,duk da ya san abu ne mai wuya ya kira shi

Ganin kiran Daddy sai hankalinsa ya tashi ya kai hannu zai kashe bai san sadda hannunsa saboda ruɗewa ya danna masa amsa kira ba har kuma ya saka a amsa kuwa.

"Son lafiyar ka kuwa wai me ke faruwa ne?Rejecting ɗin wayana kake yi are you alright kuwa? Ina A.k wayarsa ba ta shiga lafiya yake mai ya faru tsakanin ku mutane suna ta kirana suna complaining tun shekaranjiya na ɗauka ko bai jin daɗi.Gashi gobe ne tafiyar ku chaina.


Daddy ya fara magana ya na jero mishi tambayoyi cikin tsananin damuwa wanda ya ƙara ta da hankalinsa to mai zai cewa Daddy shi kam ya yi nadama sosai ya san ya na da saurin fushi amma nan da nan yake sauka.


"A.k ya yi fushi sosai dama haka yake da ɗaukar abu gaskiya na shiga ruɗani kawai na haƙura da auren bani da rabon haihuwa ne don ba zan iya karya alƙawarin da na yi ma Zainab ba,ba zan iya rabuwa da ita ba don ina son ta na tabbata duk ranar da na kawo wata mace Zainab za ta yi kisa in kuma ba ta yi ba za ta kashe kanta ko ta rabu da ni,ni kuma ina sonki bazan iya rabuwa dake ba."


Sai kawai ya rintse idanunsa ya na jin wani gululun baƙin ciki ya tokare shi a maƙogaron sa ya duka ƙasa don jin shi yake zai faɗi."Hello ka na ji na a kwai abin da kake ɓoyewa son ban yarda yadda yake girmamani,zai daina zuwa aiki ba maza ka shirya muje gidan sa duk in da kake ka dawo ina jiranka ga shi nazo ofis ɗin ka baka nan."


Muryar Daddy ya katse mishi tunanin sa ya firgita lokacin da ya faɗi haka dama ya san babu wanda zai yi gigin gaya masa sun samu saɓani ne in ba so suke su rasa aikin suba.


" Um um Daddy ba ni kusa na fita a mashin zan karɓo tsako bari na dawo sai muje."

" Ok duk ma in da kake yanzu ka yi maza ka dawo."

Daddy ya ba shi umurni tare da katse wayar sa ya bi wayar da kallo ya san dai a kwai abin da ya haɗa su,amma haka kawai A.k ba zai ƙi zuwa gurin aiki ba sanin sa mai ƙwazo da kiyaye halalin sa.

Kamar an ce ɗaga labule sai ya hangi A.m ya zura da gudu ya na sanɗa ya fice daga kampanin kamar wani ɓarawo,kamar yadda mutane suka tsaya suna mamakin haka tare da tunanin lafiyarsa kuwa Daddy sai abin ya ba shi dariya ya kira Mudassir ya nuna mishi shi,dai-dai lokacin da ya fice da gudu har ya na buge kai da get.


Dariya suka ƙara kwashewa da shi." Wai me ke damun son ne ya canza kwana biyu."Daddy yace ya na kallon Mudassir shiru ya yi kawai don ba za'a ji mutuwar Sarki bakin shi ba.

Yafi kusan rabin awa in yakai hannu zai ƙwaƙwasa gidan sai ya janye ya kai ma iska naushi ya na jin tsananin nadamar abin da ya yi masa.

" A'a yallaɓai kai ne a tsaye."



Megadin gidan da ya fito da ninyar ya siyo abu a shago ya gansa tsaye.Jikinsa ya hau rawa don shi bai ji ya ƙwanƙwasa kofar ba ya san zai sha faɗa." Don Allah ka yi haƙuri wallahi ban ji ja ba kuma ba bacci nake ba."


Ganin ya gigice sai ya buɗe baki a wahalce yace." Karka damu yanzu na zo."A taƙaice ya haɗa kalmomin don baya son magana.

" To shigo zan ɗan siyo a bu a shago ne."
Yace ya na waigen in da yabar motarsa amma ganin bai gan ta ba ya wuce abin sa.


A hankali yake taku zuwa cikin gidan ya na isa kofar shiga falo ya ga an buɗe ƙoda tun kafin ya ƙwanƙwasa,matar A.k ne ta na dariya." Hangoka na yi na Zey."Tace masa da masa.

" Uhumh kawai yace ya ƙara sa ciki ya zauna."Ina mijin ki na yi mishi laifi don Allah ki ba shi haƙuri tun kafin ya fito duk da na san ba dole ba ne ya fito."Yace mata cikin damuwa.

" Oh wannan tsakanin ku ne ya dai kama ta ku din ga haƙuri kun girma fa shi ma tun da lamarin ya faru yake ta huci na ba shi haƙuri amma yaƙi."


Tace sannan ta miƙe ta nufi ɗakinsa ba ta jima ba ta dawo fuskarta babu walwala na ƙin zuwa da ya yi duk irin haɗa shi da Allah da ta yi kan ya gane kuran sa.Bayan fitar ta ne A.k ya rintse idanun sa ya na jin ɗacin abin da ya faru tsakaninsu shi da Allah yake son shi ba wai don kuɗin sa ba,amma haka A.m ya rufe idanunsa ya na gaya masa baƙaƙen maganganu kuma sab ba zai goya mishi baya akan abin da yake so ba.


A.m ya canza fuska tun da ta gaya mishi bai ce da ita komai ba idanunsa a rintse ya miƙe tamkar wanda ƙwai ya fashe mawa a ciki ya fice ba tare da yace komai ba,abin da ya sa ya zo tsoro yake kar A.k ya gaya ma Daddy abin da ke faruwa kawai ya haƙura,amma tun da yaƙi fitowa bari ya ɗauko Daddy koma me zai faru ya faru.

Da ya koma hankalin Daddy ya tashi ganin yadda ya ɗan faɗa tsakanin kwana biyu,dafa kafaɗarsa ya yi." Ka na cikin damuwa lafiya wai me faruwa ne?Ina A.k ɗin?"


Ya jera masa tarin tambayoyi a tare ya shaƙi numfashi ya fesar sai kawai ya kwanta akan kafaɗar Daddy cikin muryar kuka ya na hawaye yace." Daddy A.k ya yi fushi da ni mun ɗan sami saɓani ne saboda wata ƴar matsala kuma na je gidan sa na ba shi haƙuri,ni na janye wannan maganar amma yaƙi saurarata har ya ije aiki.Daddy shi ne ya ɓata min rai na kasa riƙe kaina na faɗa mishi baƙaƙen maganganu, amma na yi nadama sai dai ya datse layina layika na ba ya son magana da ni."


Sai ya sa kuka kawai hankalin Daddy ya ƙara tashi yau shagwabar ta tashi kenan.

Miƙewa ya yi." Oya tashi muje gidan na sa amma ba ka kyauta ba duk da tsaƙanin harshe da haƙori ana saɓawa,nan gaba ka kiyayye ba'a ɓata ma wanda yake kusanci da kai sosai in ma hakan ta faru ƙoƙari ake a riƙe fushi don dole zaku ne mi juna."

Daddy yace ya na shafa bayan sa." Gaskiya ne Daddy na ba shi haƙuri fa kuma na yi nadama.


A lokacin da suka isa gidan da matar shi ta shiga da nufin ta gaya masa,har ya ji muryar Daddy a falo da sauri ya zo ya durkusa ya na faɗin." Da kan ka Daddy ai da ka sanar min ni zan zo."

" Ta ina zan sanar maka bayan ka kashe wayarka.Son ya yi laifi a yafe mishi don kawai kun samu saɓani za ka dai na zuwa aiki, in ka ƙara hakan zan hukuntaka ta hanyar turaka ƙasar waje ka yi wata biyu ba tare da ka dawo gurin iyalin ka ba,saboda ka ɓata min rai kuma na yi fushi da kai."

Jin abin da ya faɗa da sauri maman Najwa ta miƙe tare da ficewa ko gaisuwar da ta tsaya ta yi ma Daddy ba ta yi ba,don ya ba ta kunya duk da ta san in ya yi hakan ya cutar da rayuwar masoya.

" Ka yi haƙuri Daddy na yi nadama hakan ba zai ƙara faruwa ba! Da ma A.m ɗin ne ya...."


" Daddy ya yi haƙuri kawai ya koma aikin sa ni nama haƙura akan maganar da muka yi na fasa na janye."



Yace da sauri ya na kallon A.k don ya tsorata ya ɗauka gaya ma Daddy zai yi.Daddy ya kalle su duka kamar a kwai abin da suke ɓoye mishi wanda shi ne ya kawo musabbabin faɗan.

" To wai me ya kawo rikicin?"


Ai kafin ya rufe bakinsa A.m yace."Daddy ba komai ai mun shirya ya wuce."


A.k dai bai ce komai ba Daddy ya kama hannunsa ya haɗa." Kar na ƙara jin kun yi faɗa ku yi min alƙawari."


"Hakan ba zai ƙara faruwa ba Daddy komai ya wuce."Kamar sun haɗa baki don a tare suka faɗa. " Ok ka shirya ka taho aiki dama ina son na ƙara maka girma."


A ranar dai ba wata magana na amininai da ya shiga tsakanin su,amma tare suka fita zuwa aikin sai dai A.k ko zuwa su tafi cin abinci kamar yadda suka saba bai yi ba,don har yanzu ya na jin haushin abin da ya yi mishi hakan ya sa yake yin azumi don ya rage mishi fushinsa tunna ko Allah muna mishi laifi kuma ya yafe,amma shi mutum ne wanda ya san mahimmancin kansa.

Ƙin zuwa su je suci abinci hakan ya tabbatar ma A.m bai huce ba sai da ya daidaici ya gama tarin aiyukansa da ya jibga ma kansa,ya shiga ya na zaune a kan kujerar ofishin ya rintse idanun shi wataƙila bacci yake.


Shigar shi ya farkar da shi ya tashi ya zauna." Don Allah ka yi haƙuri haba na san ina da fushi,amma ba ni da riƙo na lura kafi son Juwairiya da ni na haƙura da haihuwar don ni ba zan aure ta ba don na rayu da ita har abada,amma tunna ba ka so mu manta da zancen.


Ga mamakinsa sai A.k ya bugi bayan sa ya na dariya yace." Haba na manta da wannan kuma akan maganar Juwariya na yadda ka aure ta Allah zan ba ka gudummuwa in har Daddy zai amince ya nema maka auren ta a sirri."


Ya ɗan kalle shi ko ya yi tunanin wasa yake masa amma bai ga alamun haka ba sai ya rungume shi ya na faɗin." Na ji daɗin amincewar ka yamzu mu tafi gurin ƙanin mahaifin ta."














Tofa masu karatu kun dai jin yadda ta kaya game da waɗannan aminan juna,Baba Sani zai yadda ya basu auren ta.Ku ci gaba da bibiyata na gode da yaba lintafina da kuke.

ƊUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ƊIN KU YA NA SAKA NI NISHAƊI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM








Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha huɗu.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.




*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 14*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


Sakamakon aiki da ya yi musu yawa sai hakan ya hana su zuwa kamar yadda suka shirya a ranar,saboda ba su tashi daga gurin aiki ba sai bayan sun yi sallar magariba daga nan kowa ya nufi gidan sa.


A.m ya ji daɗi sosai ranar kasa bacci ya yi gani yake kamar ya auri Juwairah ya gama musamman da aminin sa ya amince,duk da a cikin zuciyar sa har yanzu ya na tunanin mai ya saka A.k ya sauko har ya amince duk da dokin naƙi da ya hau daga farko.


A haka dai ya yi ta saƙe-saƙen shi amma ya rasa gano komai daga ƙarshe ya janyo bargon da Zainab ta rufe jikinta da shi ta na bacci,ya rufa da shi tare da juyawa dai-dai fuskarta ya rungumeta ya na shaƙar daddaɗar ƙamshi daga gareta,yayin da hankalin sa yake kwance kamar ya yi baƙo ya mutu a ransa duk ya ƙosa gari ya waye su ji yadda za su kaya da ƙanin mahaifin Juwairah.


A.k kuwa ko da ya koma gida hankalinsa a tashe gani yake kamar ya aikata zunubi me girma akan amince masa da ya yi,amma da ya auna a mizanin hankali sai ya ga da ta auri wannan tsohon rayuwar ta ta shiga garari gara A.m da ko ba komai za su samu ci gaba a rayuwa,duk kuma abin da zai faru wannan kuma ya bar ma Allah lamuran sa shi yake da iko akan komai,kawai abin da zai yi shi ne ya gaya ma Juwairiya kar ta yadda zuciyarta ta fara son A.m.


Ya daɗe sosai ya na shawara kafin ya furta ya amince da auren musamman da ya ji mahaifiyarta ba da lafiya,a taƙaice dai tsotsan tsamiya suke yi a rayuwar su tare da alhini.


Washegari da safe A.m ya yi mishi dirar mikiya ko karyawa a gidan sa ya yi,wanda Maman Najwa ta yi mamakin sammakon sa amma sai ta yi tunanin ko ya na son A.k ya manta komai.


Bayan sun gama karyawa suka nufi gidan su Juwairiya.


Baba Sani ya na ƙoƙarin fita gurin aiki da ƴar ƙaƙuran motarsa da yake riƙe da makullin ta a hannun sa ya na karkaɗawa.

Ganin su a kofar gidan sai ya yi turus ya na tunanin mai ya kawo waɗannan larabawan kofar gidan ko sun yi makuwa ne,saboda ya na da ɗagawa sai ya ɗauke kansa zai shige cikin motar sa ba tare da ya kalli in da suke ba,duk da tunani ya cika ran shi ganin sun tunkaro sa.


"Assalamu alaika Malam barka gurin ka muka zo,don Allah ko zaka ba mu lokacin ka duk da ba ka san da zuwanmu ba,amma in ka bamu ƴan mintuna zamu tafi musammam in ka yi ma abin da ke tafe damu kyakykyawar fahimta."



Yace da shi da murya mai sanyi duk ƙoƙarin sa ya tabbatar masa da baƙin sa ne saboda fuskar sa ta nuna kokwanton ko sun yi makuwa ne,duk da ya san ya na da ƴan mata amma ko kaɗan bai yi tunanin za su zo neman ɗaya da ga cikin su.


Ya kalli A.m da ya ɗaure fuskar sa kuma bai ce komai ba ya lura wamda ya yi mishi magana ya fi shi sakin fuska,sai ya mai da hankalinsa ga A.m yace a cike da shakku don shi har yanzu bai yadda gurin sa suka zo ba.


" An ya gurina kuka zo ko kuma kun yi makuwa ne wataƙila tambaya ce da ku."


" Ka na shakkun mun zo gurin ka ne mu ba mutane ba ne? Ko aljanu ka gani." A.m ya ce mishi ba tare da ya kalle shi ba hankalin sa na gurin wayar sa dake hannun sa ya na daddannawa.


Baba Sani nan take ya ji ran shi ya ɓace ya kalle sa a ran sa ya na faɗin." Ba ka sanni ba kenan amma bari na ji da wanne kuka zo."


" Gashi kuma sauri nake zan tafi aiki sai fai ku dawo wani lokacin." Ya ce fuskar sa a ɗaure ganin A.m ya zo da rainin wayo.Am ya buɗe baki zai yi magana sai A.k ya watsa mishi kallo kuma aka ci sa'a ya yi shiru ya ci gaba da kallon wayar sa.

" Don Allah ka yi haƙuri ka bamu ƴan mintina kamar yadda na buƙata da farko ka saurari abin da yake tafe da mu."


A.k ya ce cikin marairaicewar fuska ya kuma haɗa hannun sa biyu ya na roƙon sa.A.m kuwa kofar gidan ya din ga bi da kallo ya na jin wani tsigar jikin shi na tashi,wai shi zai haɗa jini da ƴar wannan wulaƙantaccen gidan mai kama da bola,duk da Baba Sani ya na ƙoƙarin gyarawa amma abincin wani gubar wani.



" Ok to muje in har zaku taƙaita maganar da ta kawo ku a cikin lokacin da kuka iba."

" In sha Allahu."

A.k ya bashi amsa a lokacin da suka shiga cikin gidan zuwa ɗakin Baba Sani A.m ya na ta wulƙita ido ko zai ga Juwairah don shi yanzu ma ya manta da kamannin ta.

"Maza ku gaya min mai yake tafe daku da farko ina fatan ba laifi na yi ba kuka zo kama ni."Ya faɗa kamar kuma ya ji tsoro a fuskar sa.

Hakan ya sa A.k ya murmusa shi ko A.m ko kallon sa bai yi ba.A.k ya gyara zama ya kalli Baba Sani ya ma rasa yadda zai fara ya na son ya ce A.m ya faɗi buƙatar da ta kawo su,amma ya san dunƙula maganar zai yi ta yadda ma ba zai fahimce shi ba ya lalata abin,bayan dai in ina da ya yi,ya kuma shiga ƙumbiya-ƙumbiya daga ƙarshe ya faɗi abin da ya kawo su don barin kashi a ciki baya maganin yunwa.


Alokacin da Baba Sani ya ji maganar da A.k ya faɗa sai ya ji kamar bai fahimci maganar ba kuma har ga Allah a cikin zuciyar sa ya gasgata hakan da bai ji ba.


" Ikon Allah bayin Allah don Allah ka ƙara maganar wallahi ban ji me ka ce ba yadda ka san ciwon kurumta ya kamani,a lokacin da ka yi maganar sake faɗi kamar yadda ka faɗa kuma da Hausa don Allah ba turanci ba.


A.k ya so ya yi dariya jin ya ce ya yi magana da Hausa ƙila in ya ƙara maganar da larabci zai ce ya yi mishi,A.m ya mai da wayar sa a aljihun rigar sa shi bai ga dalilin da A.k zai tsaya ya na ɗan waken zagaye ba,ya san a ran shi irin abin da suka zo mishi da shi bai isa ya hana auren Juwairah ba



" Auren Juwairiya kuka zo nema!" Ya maimaita hakan ya fi sau ba adadi daga bisani ya miƙe zubbur ya na faɗin." Haba dama na yi tunanin a lokacin da na ganku irin yaran

Please Login or Register in order to submit comment