Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na son ya canza musamman akan yarinyar da take ba shi girma

"Abnaj fito na gyara muku tibin ku barta ta yi aikin ta,kun dame ta da surutu."Yace da yaransa da suke kicin ɗin suna ta zuba da Anty Juwairiya kaza,ita kuma ta na ta yi musu dariya ba yan ta basu kwan da ta soya musu.

Yaran suka bi shi suna murnar zai gyara musu tibi,bayan tafiyar sa ziciyar Juwairiya ya buga dam!Da ta kalli ƙwayar idanunsa cikin rashin sani ganin yadda ya kafa mata idanu lokaci guda,abin da ta hango ya matuƙar tsorata ta wanda bai yi kama da so ba sai tsantsar sha'a warta da ta hango.In ko haka ne abincin ta ya ƙare a gidan.

Bayan fitar sa ta ɗaga labule ta na kallon farfajiyar harabar gidan,sai kawai ta ji hawaye ya na sauka a kan ƙuncinta bai yi kama da mutumim banza ba saboda ya na da dattako.To me ƙwayar idanunsa suke nuna mata?Ita kuma irin na ta jarrabawar kenan?




Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na takwai.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA TAKWAS*


Tun daga wannan ranar Juwairiya ta ga canji a tattare da shi,ya sakin mata sosai kuma ya na matuƙar kyautata mata,ko hira yake da matar shi sai kiji ya tsoma ta ciki yace"Wai haka aka yi Juwairiya ita za ta faɗi gaskiya."

Ranar da ya fara mata hakan ta yi matuƙar razana ta kalli Anty Naja ta ga ko me za tace amma sai taga sai dariya take ta na jin daɗi har ta na ƙara tambayar Juwairiya,wani tsabar takaici kaɗa kanta kawai ta yi ta shige kicin ɗin wanda dama shi ya ƙwala mata kira don kawai ya tambaye ta.

Bayan sati ɗaya sai gashi ya dawo gidan da wuri da yake a ranar matar sa na gurin akin ta na night duty acan za ta kwana.Bayan ya yi sallar magariba ya kulle ko ina na gidan ya shigo,tun da taga ya dawo da motar sa ya wuce masallacin kofar gidan sa gabanta ya faɗi hankalinta ya tashi,domin ita canjin da ta gani a gurin sa ya na tsorata.

Bai fito ba ya na karatun kur'ani har kiran sallar isha ya tafi masallaci,sannan bayan ya yi sallah ya dawo ya zauna a falo shi da yaransa suna kallo shi kuma ya na aiki a laptop ɗin sa.
"Abnaj je ka kira min Antyn ka Juwairiya kace ta zo ta bani abinci."Yace mishi ba tare da ya kalle shi ba,burin sa ya ganta ya san ta ɓoye kanta a ɗaki don kar ya ganta.

Yaron ya ruga da gudu zuwa can ya dawo yace."Ga ta nan zuwa."Ya ci gaba da kallon sa bata jima ba ta fito da dogon hijabin ta har ƙasa.Ita sai yanzu dake matuƙar dana sanin gadin mijin wata da yaran ta da take,don a a kwai haramcin haka a cikin addini mace baliga da namiji ba muharramai ba dama na ukun su sheɗan ne.

Nesa da shi ta tsaya kamar za ta yi mishi magana sai kuma ta juya ta shige kicin ta ɗauko abincin shi ta ije mishi za ta juya."Ba kiji ba Juwairiya."Yace da ita ganin za ta shige ɗakin da take kwana har ta na haɗawa da gudu-dugu.

Tsayawa ta yi bata re da ta juyo ba ta na watsa da yatsun hannunta gani take kamar zai haiƙe mata kamar yadda ƙanin mahaifinta ya yi mata,amma sai ta ga ya ƙaraso ya tsaya ɗan nesa da ita ya miƙa mata sabuwar waya mai kyau a kwali ya ɗan daure fuska."Ga shi na ji Antynki tace Abnaj ya saka miki waya a ruwa ta lalace shine na hutar da kuɗin ta,amma fa ki kiyaye ki dai na basu don nan gaba in kika bari suka lalata sai na haɗa da bulala kafin na canza miki wata."Yace ya na kashe mata ido.
Zare ido ta yi ganin wayar da ya siya mata irin wanda take gani a hannun su masu kyau da tsada,ina ita ina wannan wayar ta na ƴar gidan Malam Shehu kuma me za ta ce ma Anty Naja."

Kamar ya san me take tunani sai ya kaɗa kansa yace."Karki damu na san me kike tunani zan yi mata bayani.Kuma ba ni da nufin na cutar dake alkhairi ne zuciyata,don Allah ki karɓa kin san babu kyau mai da hannun kyauta baya."Yace da ita ya na wani marairaice fuska sai kace maraya.

"Gaskiya ka bar shi bana so ina gani a matsayina na ƴar aiki bai kama ta na riƙe irin wayar nan ba,don daga ganin ta na san za ta yi tsada kuma in Anty Naja ta gani me zan ce mata?"Sai ta tsinci kanta da furta hakan yayin da takai aya ta tsare shi da ido ta na tambayarsa.

Shi ma ya ɗan razana jin tambayar da ta yi mishi kansa ya ɗan sosa ya kafe ta da idanunsa yace."Haba Juwairiya kina abu kamar ba mace ba,kice mata saurayin ki ya baki mana."

"Ka yi haƙuri don Allah ba na son kyakykyawar alaƙar mu da matarka ya ɓace,kai sheda ne mace ce na ƙwarai kuma ta yi min halacci."Tace dashi da murya raunanniya yayin da hawaye suka fara turereniya a fuskarta.
Ganin haka sai jikinsa ya yi sanyi ya ɗan yi shiru ya na nazarin maganar ta zuwa can ya ja numfashi yace."Laifi ne don nace ina sonki ni fa bani da nufin na cutar dake,kawai ina son ki zamo uwar ƴaƴana ne."Tsananin tsoron da ta nuna ta na me gwalo ido sai abin ya ba shi dariya.

Tafe take cikin sauri bayan ta tashi daga aikin zuciyarta tunanin sabon halin da mijin madan ɗin ta ya fito dashi,yake damun ta har ta fara tunanin ko ta aje aikin ƙila in Anty Naja ta gane ba lalle-lalle ne ta fahimce ta ba.Kallon tsadaddiyar wayar dake riƙe a hannunta da ya bata take kallo wanda ya rantse ya maya in har ba ta ɗauka ba to zai ba wa Antynna ta da take tsoron sani ta bata da kanta.

Abin mamaki dai-dai za ta shiga gida ta ji an dameta da hon,kamar ba za ta juya ba sai kuma ta juya in da ta ga mijin Anty Naja a cikin mota ya na ɗaga mata hannu,wato biyo ta ya yi ba tare da sanin ta ba ya ga gidan su.Tsabar takaici ba ta kula shi ba ta shige cikin gida.

Koda ta gaya ma Mama abin da ke faruwa hankalin Mama ya tashi ƙwarai ta yi shuru kawai ta na jinjina abin a ranta,ta ɗauki tsawon lokaci ba tare da tace komai ba zuwa can ta nisa tace."Ina ga ko haƙura da aikin nan tunna mun sami jari Juwairiya,ni nafi son kiyi aure shine mutuncin ki.Kin san maza basu da ta ido zai iya furtawa hakan ya jawo miki matsala gara mu yi rabuwar mutunci,in ban da shi ma ina ke ina kishi da Anty Naja mace me mutunci."
"Nima haka na gani Mama hankalina ya tashi ƙwarai."Tace da ita ta na juya wayar da ya ba ta."Kinga gobe ki mayar mishi da wayar shi,kice ni na ce ki mayar masa na tabbata ya tsorata ki ne amma ba zai yi gigin bata wayar ta baki ba,in dai ba ya na so ya kira ma kansa ruwa bane."
"To Mama in sha Allahu zan mayar masa,ni ma bana son na riƙe irin wayar nan don Allah kaɗai ya san abin da Baba Sani zai faɗawa jama'a."
"Haka ne Allah ya fishi."Ta bata amsa tare da miƙewa don ɗauro alwalar kiran sallar magariba da ke ta kwaɗawa masallacin kusa dasu.
Washegari da ta je gidan bayan fitar matarsa ya dawo kamar yadda ƴan kwanakin yake mata,ta na ganin shi ta ƙara tamke fuska kamar ba ta ganshi ba ta ji gaba da aikin ta.
Ta yi tunanin zai yi mata magana amma sai ta ji shiru na tsawon lokaci,da sauri ta waigo sai ta ga ita yake kallo kamar bai taɓa ganin ta ba.Miƙa masa wayar ta yi tace."Mahaifiyata tace na dawo dashi,kuma don Allah ka yi min rai ka fita sabgata domin ba za ta amince aci amanar Anty Naja ba."
"Ni kuma sai na shiga wani hali ko?Wannan dalilin ya sa kika ƙi ɗaukar wayata jiya da daddare sai ma kika kashe wayar.Dama masoyi ya na zama maƙiyi Juwairiya?"Ya ƙarashe maganar da sigan tambaya,a yadda ya furta maganar sai ta ji ranta babu daɗi,ganin namiji mai natsuwa ya na mata magiya akan ta so shi.

Wani irin abu ta ji a ranta in da ace matarsa ba ta shiga tsakani ba,babu yadda za'ai taƙi auren shi sai dai ba za ta zama butulu ba.Ganin taƙi kallon sa bare ya saka ran za ta yi magana,sai ma hawaye da ta soma ganin haka ya ɗauki wayar da ta ije mishi ya fice ya san ta na sonshi,amma tsoro ne ya cika mata zuciya in ko haka ne zai je har gida ya nemi aurenta.

Kwana biyu haka suke wasar ƴar ɓuya ganin haka sai ya dena shiga sabgar ta ko dawowa gida ya dai na,ya na shirye-shiryen zuwa gidan su ya nemi auren ta.
Ranar wata yammacin talata ta tashi daga aiki kasancewar an yi rana sosa,da yake lokaci ne na damina garin ya fara haɗa hadari.Juwairiya sauri take ta isa gida saboda ta kauce ma baƙin hadarin da yake tasowa ya na canza garin da yake duhu sosai.
Hon ta ji an danna mata ta waiga sai ta ga Daddyn Abnaj ne ya na mata murmushi yace."Maza shigo na kaiki gida kar ruwa ya zane min masoyiyata."Ta yi kamar ba za ta shiga ba amma ganin har an fara iskar hadari ya sa ta buɗe gidan baya ta shige,tare da haɗe girar sama da ƙasa don karya tambayeta dalili

Hakan sai ya ba shi dariya sosai bai ce komai ba suka fara tafiya, sai ya sai ta madubin motarsa dai-dai in da take zaune."Wato na zama direban ki ko."Ya jefa mata tambaya dai-dai lokacin da ya fara tafiya.
"Ina wuni."Tace ba tare da ta amsa mishi tambayar ba.
"Ba zan amsa ba ina fushi."Yace ya na kallonta ta gilashin motar.
Ba tace mishi komai ganin hakan ya sa ya fara magana da murya mai taushi."Matsalar ƴan mata kenan da kun ga namiji ya na ƙaunarku,shikenan kun samu zaren ja amma babu komai nima lokacina ya na nan zuwa,don na fara hango sona a cikin ƙwayar idanunki."
Ta ɗan saki ranta saboda ta fara sabawa da shi ya wan janta da ɗawainiya da yake musu ta ja numfashi ta sauke ta fara magana da cewa."Ku kuma maza ba amana ka san kusancin dake tsaƙanina da matar ka,amma ka bijiro da wannan lamari haba kai ma ka auna ka gani bai dace ba."

"Kija min aya da ya hana hakan ko hadisi."Ya faɗa a raunane kuma a taƙaice.Babu amma Bahaushe ya na girmama al'adarsa hakan ya saɓa ma al'adar Bahaushe."Sitiyarin motar ya buga da ƙarfi yace "Kin ji ko in da karatun naki ya tafi ina miki zan can addini kina yi min wata magana can,kawai na gane bakya sona ki ce na haƙura kina da wani hakan zai sa na bawa zuciyata haƙuri duk da na san za ta shiga wani hali."

Yanayin da ya yi maganar sai ya bata tausayi amma ta san abin da yake so ba mai yiwuwa ba ne.Murfin motar ta ɓalle za ta fita ganin sun ƙaraso gida ya yi parking,sunan ta ya ƙira da wata irin murya.Ta waigo ba tare da tace ƙala ba,sai ƙasa da kanta da ta yi wato alamun ta na sauraren sa.
"Ki yi tunani zuwa ƙarshen sati nan nake so na turo magabata na,ina ganin za ki dakata da akin nan kafin kizo a matsayin ƙanwa kin ga sai ki ɗora daga in da kika tsaya ki na samun lada rututu!

Ɓalle motar ta yi ta fice dai-dai lokacin da ya miƙa mata ƴan rafar ɗari biyar kusan kimanin dubu ishirin ba tare da ta karɓa ba ta fice,musamman da ta ga Baba Sani tsaye a ƙofar gida shi da wani mutum ya zura mata ido.

Ganin jikinta ya soma rawa ya kalli in da take kallo,sai hakan ya yi mishi daɗi domin faɗuwa tazo dai-dai da zama,ya buɗe murfin motar ya fito ya nufi su Baba Sani dake kallon Juwairiya kamar ya shaƙe ta.

Da sauri ta matsa za ta bi ta bayansa ta shige cikin gidan da ya bake ƙofar,amma sai ya daka mata tsawa tare da jan hijabinta."Ina zaki ƴar iska maza dawo,iskancin naki ya kai har a kawo ki gida a mota.Kawai sai ya saka salati da ƙarfin sa ya ci gaba da cewa."Inna lillahi gara da ka mutu Yaya Ahmed in da ka na raye Juwairiya ita za ta ƙashe ka.Karuwa kika zama fa ke ko kunya duniya ba za ki jiba tunna baki ji na Allah ba."
"Ashsha!Subuhanallahi haba Malam ya za ka dinga jifan ta da waɗannan muggan kalamai?Iya sani na Juwairiya yarinyar kirki ne ta ɗaɗe ta na tare damu ta na mana aiki.Yanzu haka mun daidaita ne nake son ka bani auren ta,ma'ana na yaba da hankalinta ina sonta."

Wayyo Allah faɗin haka da ya yi wato ya na son Juwairiya ji Baba Sani ya yi kamar ya watsa mishi fetur ya kyasta ashana domin baƙin cikin sa biyu ne a kan maganar.Na farko ta ya ya za 'ai mutum me hannu da shuni yace ya na sonta,sannan kuma baƙin kishinta ya taso ya lulluɓe mishi zuciyarsa kawai sai ya ƙara kuka ya na faɗin ma abokin da suke hira cewar."Kaji ko wai na ba shi aurenta bayan ya gama iskanci da ita ni nasan ya na naɗe tabarmar kunya ne.Amma ta ya ya zai auri mazinaciya!Ba Juwairiya dake tsaye ta na kuka ba har ta Daddyn Abnaj sai da yaji wani irin abu ya soke shi ya rintse idanunsa ya na jin kamar ya shaƙo wuyar Baba Sani,take ya fahimci wani abu wato na zaman ƙunci da suke yi iya zaman su da ita bata taɓa basu labari ba,duk da ya san cewa ba lai-lai bane ta gaya musu kasancewar ta na da zurfin ciki.

Ya kalli Juwairiya da ta ƙara sautin kukan ta ganin mutane sun fara taruwa Baba Sani yaci gaba da magana da ƙarfi ya na nanatawa,sai ta ruga da gudu dai-dai lokacin da Baba Sani ya kai mata bugu a bayanta.

Ba ta san ya suka ƙare ba ya dai shigo gida ya na ta faɗa tare da ja mata jifa'i kala-kala, Juwairiya ta so ta tanka saboda abin da ya yi mata a gaban mutumim da yake girmama lamarin ta,amma Mama ta hana duk san da ya gaya mata baƙa ta buɗe baki za ta yi magana Mama za ta hana ta,har ya gaji da rashin mutuncinsa ya fice.

A ranar Juwairiya ta ci kuka sosai ta ji ta ƙara mugun tsanar shi a ranta.
Washegari ganin taƙi shiryawa taje aiki Mama ta shigo ɗakin ta tsaya ta na kallonta tace."Juwairiya ba zaki je aiki bane naga rana ta yi."
"Na haƙura da aikin Mama gara na zauna a gida dama kin san mun yanke shawarar na daina zuwa,sai ga abin da Baba Sani ya yi min a gaban shi Allah kunya nake ji matuƙa.Karuwa ya kira ni."Sai kawai ta saka kuka ta na jin zafin kalmar da ya danganta ta da ita."
Mama a ranta har tafi Juwairiya damuwa amma sai ta ɗan gyara murya tace."Ki yi haƙuri komai lokaci ne watarana sai ya yi dana sani,amma da kin daure kije kila ma ya shafa miki lafiya don na tabbata ba zai ƙara miki maganar soyayya ba,ganin yadda ya tozar taki."
"To Mama shikenan a haka rayuwata za ta ƙare duk wanda ya fito neman aurena sai Baba Sani ya ɓata lamarin gaskiya na gaji."Tace cikin hawaye yayin da ta tuna katoɓarar da ta yi na faɗin hakan,kamar ta nuna ta na son auren kenan sai ta zari hijabinta da sauri ta fice zuwa aiki.

Ko da ta isa bata sami Anty Naja ba duk da ta san dama abu ne me wuya ta same ta,abin mamaki ta yi sallama ta shiga fuskarta babu walwala,sai ta same shi zaune akan one siter ya zuba tagumi ya na kallon hanya,ganin ta ya saka shi sakin ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske.
"Shigo mana Juwairiya hankalina ya tashi matuƙa na yi zaton wannan mara kirkin Baban nan naki ya hanaki zuwa "Yace da ita ganin ta dogare a bakin ƙofa,ta ɗan tsaya ta na kallon shi sai kuma ta ƙara haɗe fuska haushin sa take ji don shi ya yi shishshigi a lamarinta,har ya saka Bab Sani ya yi mata wannan tozarcin.

"Gaskiya ban ji daɗin abin da ya faru ba!Haba sai kace ba ƙanin mahaifinki ba.Lamarinsa ya tsoratani baƙin cikina yadda yaƙi yadda da maganata akan ina sonki da aure.Kawai ki gaya min dangin ku naje can na nemi aurenki."

Yace da ita ya na kare mata kallo don ya fahimci a wani hali take,takaici ya kamata jin abin da ya faɗa sai ta miƙe hanyar kicin ba tare da tace mishi komai ba.

Gabanta ya sha tare da riƙe mata hijabi yace."Na fa fara ƙosawa da halin ko in kula da kike min haba waike dutse ne a ƙirjin ki ba zuciya ba!Ki ji tausayina ko don halin da kike ciki ki zaɓe ni a matsayin mijin ki hatta mahaifiyarki ba za ta zauna a wannan gida ba.

Takai hannu da nufin ta ƙwace hijabinta sai ya riƙe hannun cikin kalar tausayi ya na jin kamar ya yi mata kuka,ganin sam ba ta da rangwame akan soyayya.Baki ta buɗe da nufin ta yi magana sai suka ji sallamar Anty Naja ta shigo da sauri da alamun gajiya tare da ita.

Da sauri ya saki hannunta ya matsa gefe ya na zare ido,ita ma cikin tashin hankali ta tsaya ta kasa haɗa ido da ita ta na jiran tashi n hankalin da za ta fuskanta.
Amma sai dukansu ta basu mamaki ta faɗa kan kujera ta na lumshe ido "Wash Allah! Na gaji matuƙa Juwairiya bani ruwa don Allah."Tace cikin sakin fuska ba tare da ta fahimci komai ba."
Da sauri Juwairiya ta shige kicin ta na mamakin sokanci irin nata haba ta ya ya za'ai tace bata fahimci komai ba.Bayan ta kawo mata ruwan ta haɗo har da abin motsa baki,ta shige kicin ta ci gaba da aiyukan ta can sai ga shi ya shigo yace."Ina jiranki in kin gama zaki tafi ina hanyar da nake tsayawa sai mu ƙarashe tautaunawar.

Ganin ba zai saduda ba Mama tace ta haƙura da aikin in ta bata kuɗin aikin ta na wata haka kuwa aka yi,bayan ta yi mata albashi ta ƙara mata harda zannuwa masu kyau biyu nata sai ɗaya Mama ta ɗinka,kasancewar suna da biki a family ɗin su kuma tare da Juwairiya za su tafi garin Kano.

Hankalin Anty Naja ya tashi matuƙa ganin ba ta zo aiki ba,ta shiga ruɗani ta din ga tunanin ko ta yi mata wani abu amma bata gano ba.Shi ma hankalinsa ya tashi sosai duk da yaso sai sun gama daidaitawa a tsakanin su sai tabar aikin,amma ta yi sauri gashi ya na son yaje gidan ya na tsoron tijararren ƙanin mahaifinta

Sai ya azalzala ma Anty Naja ta shirya ya kaita har ya na mata barazana da ya na nan akan bakan sa in dai ba Juwairiya ba sai dai ta bar aikin,ai kuwa ba shiri ta shirya suka taho ya ijeta a kofar gidan ta shiga ciki ya zauna da yaransa ya na jiran ta fito,burin sa ya ga Juwairiya.

Juwairiya na tsakar ta na girki Mama ta na zaune ta na jan carbi ta yi sallama ta shigo,da sauri Juwairiya ta saka hannu ta rufe fuskarta ta na dariya.
Anty Naja ta harareta ta na kallon Mama tace."Da ma Mama haka Juwairiya take bata da kirki? Kawai ta guje mu ba tare da mun yi mata wani abu ba,hankalina ya tashi ƙwarai Mama gaskiya ba ta kyauta ba."

Ta ƙarashe maganar ta na kallon Juwairiya sannan ta ɗora da cewa "Ko mun yi miki wani abu ne?Ai gaya mana ya kamata ki yi ba ki ɗauke kafafunki ba.Ni da yara da Daddyn su Abnaj duk hankalin mu ya tashi."

Mama ita ba tace komai ba tace komai ba sai dariyar yaƙe take mata,bayan sun shiga ɗaki suka yi gaisuwa a tsakanin su sanann shiru ya biyo baya.Sannan Anty Naja ta katse shirun tace."Me ya faru Mama kwana biyu bata zo aiki ba na yi tunanin ko wani ba lafiya,amma da nazo naga kowa lafiya.Ko na yi laifi ne Mama."

Matuƙar kunya sai ya lulluɓe Mam ta ji kamar ta nitse ta rasa yadda za ta fara mata bayani,har Juwairiya ta yi sallama ta shigo,ganin Mama ta kasa mata bayani ta kalli Juwairiya tace."To ko auren ne ya zo,in kuma wannan ne Mama ai ni ce me haɗo kayan ɗaki ko?"Ta ƙarashe maganar ta na me tsigar tambaya.
I ta dai Juwairiya ba tace komai ba ta na ta wasa da yatsunta,Mama ta daure tace."Ba shi bane ban san dai yadda zaki ɗauki zancen bane shi yasa na kasa sanar miki,amma ranar wanka ba'a ɓoyan ciji."

Gaban Anty Naja ya faɗi daram!Sai ta ji zuciyar ta ta raya mata lai-lai a kwai abin da suke ɓoye mata,duk da bata san ko menene ba amma taji ta firgita Allah ya sa ba wani lamari me girma ya faru ba.
Ganin ta yi shiru ba tace komai ba jikinta ya yi sanyi Mama dai ta daure tace."Dama mijinki ya bijiro da wata magana ya na son auren Juwairiya har ya shigo da maganar gida,mu kuma muka ga rashin dacewar haka saboda irin halaccin da kika yi mana shi yasa nace ta dakata da aikin kawai ki nemi wani."Tace ta na karantar fuskarta.







Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na Tara.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakaƙuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA TARA*

Abin mamaki da yake macece wayayyiya sai bata nuna komai ba duk da irin tarin luguden da zuciyar ta take mata,ta na jin kamar ta fita ta shaƙo shi munafiki kawai haba ya kamata a ce ta ɗago tuntuni saboda yadda yake yabon ta da kalamai magana ɗaya biyu ya sako sunanta,amma da yake ba ta da wayo sai ba ta ɗago ba ta danganta kular da yake bata a dalilin ta

Please Login or Register in order to submit comment