Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da murmushin da ya yi mata lokacin da ya tabbayi sunan ta idanuwanta suke hasko mata,ta rintse idanunta da ƙarfi ta na son su daƙile mata ganin ta ga mutumim da take jin kamar ya saka ta a aljihun sa su yi ta yawo.

Bayan ta dawo gida ta na zaune jingine da bangon ɗakin su idanunta a sama ta na aikin tunanin da ta ɗaura ɗamara da shi tun lokacin da idanunta suka yi tozali da shi.

Mama dake tsaye ta na karantar yanayin ta tun da ta kawo mata kuɗi tace wani mutum ya siye,ta zauna a gurin ta na kallon sama sai hakan ya tabbatar mata da a kwai lauje cikin naɗi.

" Juwairiya lafiyar ki kuwa."Mama ta kalleta lokacin da ta dafa kafaɗarta,amma ba ta ji ta ba har sai da ta maimaita sau biyar ba ta ji ba sai ta juyo da fuskarta.

Ga mamakin ta sai ta ga ta juyo tare da saka hannunta ta rungumeta ta fashe da kuka,hankalin Mama ya ƙara tashi dama tun safe take jin wani irin zafi-zafi a ƙirjin tare da sauke wani irin ajiyar zuciya mai kama da zai tafi da rayuwarta.
Yaƙe me kama da murmushi ta yi tace." Akan maganar auren ki ko Juwairiya ya za mu yi da ƙaddarar ubangiji,komai kika ga ya faru Allah ne ya ƙaddara."

Ta sauke irin wannan ajiyar zuciyar da ke barazanar ɗauke numfashin ta sai kuma hawaye suka fara turereniya a kan ƙuncinta.
Ta buɗe baki da nufin ta yi magana amma ta kasa sai ta rufe bakin tare da sakin kuka wanda ya fi na Juwairiya sauti.

Hankalin Juawairiya ya tashi matuƙa!Tun da lamarin ke faruwa Mama ita take kwantar mata da hankali amma yau haƙurin ta ya gaza.

" Don Allah ki de na kuka wallahi na haƙura ba zan ƙara nuna damuwata ba,in dai akan auren nan ne kin san yanayin ciwon ki.

Ta faɗa ta na share hawayen ta don ta na tsoron kar ciwon Mama ya tashi,ga shi aure za ta yi babu wanda zai kula da ita sai Ibrahim wanda ba cikakkiyar lafiya gare shi ba,don har ɗingishi yake yi kafar sa ɗaya ba lafiya.

Mama ta miƙe ba tare da tace komai ba ta fice daga ɗakin ta na jin matuƙar tausayin ta kasancewar ba ta sami bango abin jingina ba.Tanimu ba mutumim aure ba ne ita kuma mace ta na zama zinariya ce in har ta samu miji na gari,ta fauwala ma Allah lamuran sa saboda Allah na iya can za lamuran sa iya addu'ar da take yi wa Juwairiya rayuwar ta ba za ta taɓe ba.

Buta ta ɗauka ta shiga bayi ta tsarkake kanta ta fara kai kukan ta ga Allah Sarki gwani gagara misali!

Ganin haka Juwairiya ta miƙe tare da sakin kuka ta toshe bakin ta bayi ta shige ta saki bakinta ta na kuka mai tsuma zuciyar me sauraro." Me ya sa ka shigo rayuwata a lokacin da nake jin duniya ba ta da muradina a cikin ta gyambo biyu kake so na yi ta jinya a cikin rayuwata! Na rashin ka da auren mutumim da na tsana a rayuwata!"Kuka sosai ta yi sannan ta fito ta yi alwala tabi sahun Mama.

Wunin ranar ta yi shi ne a suku-suku tamkar wacce ba ta da lakka a jikinta,ta kasa cire shi a ranta.Da daddare ta na kwance sai mutsu-mutsu take ta na jin Mama na ajiyar zuciya ƙut!Ƙut! Wanda hankalinta ya tashi kwarai ba ta rintsa ba sai kusan asuba ta ji ɓarawo bacci ya kwashe ta.

Da asuba bayan ta yi sallah ta na karatun alkur'ani ta yi mamakin da Mama ba ta tashi ta yi sallah ba,sai ta miƙe dai-dai lokacin da Ibrahim ya shigo ya dawo daga masallacin dake kusa da su.

" Mama ki tashi ki yi sallah." Amma shiru ba ta amsa mata ba da sauri ta ƙara jijjigata sai dai ta ga Mama idanunta sun ƙanƙance jikinta ya saki da ƙyar take janyo numfashin dake barazanar kuɓucewa gangar jikin ta.

" A'a Mama don Allah karki mutu ki bar mu kin ji Mama!"Kuka take sosai ta na girgiza Mama da ta ƙasa buɗe idanun ta saboda nauyin da sukai mata,a jikin ta ta na jin wani irin zafi me kama da rushi ya na zagaye ilahirin jikinta don har huci yake ya na fitar da tiriri me zafin gaske!

Jin ihun Juwairiya ya sa matar Baba Sani ta shigo wanda hankalinta ya tashi matuƙa ta na tausayin su sosai,sai dai ta san halin tijararren mijinta zai iya shuka mata rashin mutunci koma ya sake ta bare yanzu da yake mata rashin mutunci zai ƙara aure.

Kuɗi ta miƙa ma Juwairiya ta saka yaron ta ya nemo me keke napep aka saka Mama a ciki zuwa asibiti.



*********
Bayan A.m ya fita gidan iyayen shi ya nufa don ya ɗan kwana biyu be leƙa su ba,ya na shiga ya ga ana ta murnar matar ƙaninsa ta haifi ƴan biyu gidan ya cika sai murna ake,saboda daga asibiti nan aka wuto da ita.

Jikinsa ya yi sanyi ya irga yaransa yanzu huɗu kenan sai kawai ya ji zuciyar sa na bugawa,bai ƙara shiga cikin tashin hankali ba sai da aka ɗora masa yaran masu kama da larabawa a kan cinyarsa.

Gidan gabaki ɗaya sun ruɗe suna ta ɗaukar yaran waya kamar zasu ƙarar da jikin su saboda ɗaukar hoton,har sai da ya tsawatar da su bari sannan suka dena suna ta kallon yaran.

Hawaye yaji suna bin ƙuncinsa ya kasa ɗaukar yaran ya na kallon su gunun sha'awa kamar ya kwace yace ƙwansa ne shine ya haife su.

Ganin ya na hawaye sai dukannin su jikin su ya yi sanyi suka koma suna rarrashin sa,amma ya kasa tsaida hawayen da ke kwaranya kamar an buɗe famfo.
" Zainab an ya kin yi wa rayuta adalci kuwa?"
Ya tamabayi kansa dai-dai lokacin da mahaifiyar sa ta dafa kafaɗun sa ta na rarrashin sa.Bayan ya sawa yaran albarka ya fice daga gidan kai tsaye kampanin su ya wuce tare da jiran A k su haɗu da shi farfajiyar kamfanin.

A.k ya sanar mishi ya na kampanin in ya iso ya kira shi kawai,amma sai A.m ya nuna ya fito kawai ya jira shi saboda yanayin da yake ba zai iya ƙara kiran waya ba.

Ya na isowa ya same shi tsaye da waya a hannun sa da alama waya yake sai kuma ganin shi ya sa ya kashe wayar,tare da maida ta cikin gabar rigar sa ya ƙarasa gurin da A.m ya yi parking ɗin motar sa.

Ina ga muje farfajiyar da Daddy yake hutawa abin zai fi ko a bisa mu yi magana don nima ina da maganar da nake son mu tautauna akai."A.k yace da shi bayan ya nufi hanyar gurin ba tare da ya ji amsar da ya ba shi ba.

Ganin haka sai shi ma ya bi bayan sa ba tare da yace komai ba.Bayan sun zauna shirun na su na ƴan mintoci ya biyo baya wanda sai da nabi dindigi na gano dalilin shirun na su a duk lokacin da suka haɗu kafin su fara maganar da ta kawo su,wanda suna yi ne don su sami natsuwa tare da nazarin maganar da zasu tautauna a tsakanin su.

A.k ya buɗe baki da nufin zai fara magana amma sai A.m ya hana shi ta hanyar taran numfashin sa tare da gyara zama yace."Abokina ka fara bani dama na yi magana domin na samo mafita a kan damuwata,na yi tunani sosai kan maganar da muka yi da kai na Juwairaah.Tabbas yarinyar ta kwanta min a rai kuma na yaba da hankalin ta amma saboda alƙawarin da na yi wa Zainab,kuma ita kaɗai nake son takasance matata zan auri Juwairaah mu yi auren
kwangila da ita shekara ɗaya,kamar yadda ka bani labarin ƙanin mahaifinta ni kuma zan siya shi da ruwan kuɗi ya fasa auren da zai yi mata da wannan tsohon."

Ya numfasa ya na kallon sa ko zai fahimci yadda ya karɓi zancen,amma sa ya ga ya na mishi kallo kamar irin amma ka zare ko!

Bai damu ba ya ƙaɗa kansa yaci gaba da cewa."Tunna ka gaya min ta yawon aikatau sai mu ɗauketa akan za ta koya wa matata girki da kula na tsawon shekara guda,kaga a wannan lakacin in ta samu ciki zan ɗauke ta daga gidan na kai ta wani guri,na san yadda zan tsara Zainab ta amince ta karɓi ɗan burina na ga ɗana kafin na mutu.

"Amma baka da hankali ko na ɗauka alkhairi ya sa ka kira ni nan,ashe ka je ka bugu ne ka zo ka ɓata min lokaci."A.k yace tare da miƙewa yayin kamar zai fice daga gurin bayan ya miƙe sai ya dawo ya ƙara zama ya na kallon sa yace." Aikin banza kawai na ɗauka auren ta za ka yi na ɓata lokaci na gurin sanin tarihin rayuwarta! Abin takaici sai ga shi kazo ka na min maganar banza. Shin baka da zuciya ne a ƙirjinka har ka kasa tausayawa rayuwarta na halin ƙuncin rayuwar da take ciki? Ko ƙyamar talaka da kake yi ne ya sa kake son ka cutar da zuciyar ta.

Ya ƙara miƙewa don ji yake kamar ze rufe shi da duka ya na jin zai iya gaya mishi duk maganar da ta zo bakinsa,saboda tun jiya da ya ji halin da take ciki Allah ya saka mata tsananin tausayinta a ranta.

A.m hannun sa ya kama shi ma sai hawaye ya na faɗin." A tsakanina da ita waye yafi kusanci da kai ina cikin wani hali bani da nufin na cutar da Juwairaah wallahi tsananin son ganin ɗana ya sa nake jin zan iya komai.In har ka amince ka bani goyan baya mukai auren sirri da ita na yi maka alƙawari rayuwar Juwairaah sai ya canza daga talauci zuwa mafi ƙololuwar jin daɗi na rayuwa.Kuma ko banza aurena zai zamo katanga a tsakanin da tsohon mutumim nan,ƙanin mahaifinta da yake takurawa rayuwarta duk haɗuwana da ita zai saka ya dena saka mata ƙahon zuƙa."


" Rufe min baki nace! Shashasha!Kawai ka san yadda zuciyar mace take da rauni kan soyayya.Kai fa namiji ne da ko wace mace za ta yi mafarkin samu,ka na tunanin in ka auri Juwairiya za ta iya haƙuri da rashin ka ne,a kan maganar soyayya kuɗi ba ya tasiri mace za ta iya baka rayuwarta kuma ta sadaukar da rayuwarta duka gabaki ɗaya in har ta na sonka,ba za ta taɓa damuwa da halin rashi ko baƙin cikin da za ka saka taɓa."


Ya saukar da zazzafan huci ya ja numfashi sannan ya kalle shi da idanunsa da suka kaɗa suka yi jajur." Ina tunanin yaudarar Zainab kake da kake faɗin ka na sonta don da ka san yadda soyayya take tasiri da baka buƙaci auren Juwairiya na wucin gadi ba, don na tabbata kafin ku rabu sai Juwairiya ta faɗa kogin son ka koda yankan namar jikinta kake yi ɗanye,bare kuma za ka raba ta da abu mafi girma a rayuwarta kawai za ka rabu da gangar jikinta ne amma zuciyar da da ruhinta duk za ka raba ta da shi.Ba ka san yadda uwa take zama akan yaron ta ba,saboda ba ka haihu ba shi ya sa baka san soyayyar da Allah ya saka tsakanin ɗa da mahaifi b..."

"Ya ishe ka! Rufe min baki nace banza mara mutunci! Har ni za ka yi ma gorin haihuwa na rantse tunna ka yi min gori sai na aureta kuma na raba ta da yaran na kai ma matata,na yi alƙawarin sai kaga ƙwaina a duniya."

Ya matso tare da taɓa ƙirjin shi da ɗan yatsa yace." Saboda nace zan aure ta ka wani tada jijiyar wuya'duk na gane kauce-kaucen ka don ta na talaka ba ka son na aureta.To siyan ta zan yi da kuɗina kai ma ka san in ka yi tunanin zan aure ta na yi rayuwar har abada ka yaudari kan ka, me zan yi da ƴar talaka wanda basu da komai sai tsiya,kuma ka sani ko ban aure ta ba ina da kuɗin da inna ce zan auri ƴan mata waɗanda suka fi ta kyawu da ɗaukaka zan iya auren goma in ana yi."


"To kaje ka auri ƴan matan duniya duka in kana son ɗan ƙaruna amma ba zan haɗa hannu da kai na saka rayuwar ta a cikin matsala."

Ya faɗa tare da ƙoƙarin barin gurin rigar sa ya jawo ya juyo da shi gaban sa ." Ko ka sa min hannu ko ka ƙi sai na aure ta ita kaɗai ce na ji zan iya rayuwar aure da ita ba yan masoyiyata Zainab,don haka in dai kuɗi na aiki ka ba ni sati biyu za ka gan ta a gidana kuma a matsayin me aikin matata za ta shigo gidan."

Ran sa ya ƙara ɓaci da ya tuna ya sha zuwa gidan ya ga Zainab ta daki me aiki,hakan ya na nufin in ranta ya ɓace za ta dake ta kenan aiko in dai haka ne a kwai zalinci.

" Ai kin banza kawai sai dai in zaka ɗauki numfashina ma'ana ba ni a raye,amma ni da kai na zan tona asirin ka kuma na ga uban da zai karɓar maka auren tunna ba ƴar tsana ba ce,sai da waliyin ka za'a baka.Yace a fusace.

" Ok haka kace ko zan nuna maka true color ɗina dama duk abin da aka haɗa da jaki sai ya ci kara,ka haɗa hulɗa da talaka matsiyaci da be da komai sai tsiya na yi dana sanin tarayyata da kai don bi amfana min komai ba,duk halaccin dana yi maka ni da dangina muka ƴanta rayuwarka shi ne zaka saka min da haka!"


To fa ran A.k ya ɓace matuƙa kawai sai hawaye ya kalli A.m da yake ta ga ya mishi maganganu mara sa daɗi da baƙan ta rai,don shi in dai ran shi ya ɓace bai iya magana ba."

" A she haka kake dama na daɗe ina tunanin wannan ranar za ta zo,saboda a gaba na kasha wulaƙanta talawa irin na na gode in sha Allahu daga yau ba ni bakai,ba zan ƙara hulɗa da kai ba kuma na bar muku aikin ku ka sana ni ba jahili ba ne ko yau na yanke alaƙa da ku sai kun yi jimamin rashina."Yace ya na me tabbatar da hakan a ran sa.


Kai ɗin me kai ɗin banza me kake da shi kaje a kwai waɗanda suka fika ilmi da zasu buƙaci gurbin ka.".
Lamarin fa ya yi tsamari gabaki ɗayan su kowa ya hau dokin zuciya duk da zo mu saɓa zo mu zauna,amma ba su taɓa samun saɓani irin na yau ba.

Ko da A.k ya nufi hanyar fita A.m jawo kwalar rigar sa ya yi tare da dawo da shi ya hau shi,da dambe don gani yake ya ma rai na mishi wayo ya na karkashin sa,sai ya manta abokantakar su ya dawo kan matsayi.

Aiko A.k a zuciye ya kai mishi mari ya kauce shi ma ya kai mishi suka rikice da dambe kici-kici.Me ba ma fulawa ruwa ya zo ya gan su da gudu ya ruga ya yi kiran mutane,su raba don ba zai yi gigin shiga tsakiyar su ba su bar shi da jinya yadda suke ji da karfi.

Da ƙyar mutane suka raba su sai huci suke tamkar wasu zakuna.Faruwar lamarin sai ya yi matuƙar bawa mutane mamaki,tuna yadda suka shaƙu kamar wasu ƴan'uwa suna ta jimamin lamarin me ya haɗu ko ma dai mene ne lamarin me girma ne,amma da suka tuna tsakanin harshe da haƙori ana saɓawa sai suka ba su haƙuri tare da ɗauko musu ruwan sanyi,domin ya sanyaya zuƙatan su saboda sheɗan da ya yi nasara haddasa fitina a tsakani aminnan ko nace ƴan'uwa.


A.k da ran sa ya ɓace ko jiran wanda ya nufi zuwa cikin kampanin ya ɗauko musu ruwa bai yi ba ya fice ya na jin a ran sa ya tafi na har abada.

Ko da a ka ɓalle murfin gorar ruwa aka zuba mishi ruwan wurgi ya yi da kofin tangaras ɗin ya nufi motar sa,ya shige tare da figar ta kamar zai tashi sama.


Ko da ya iso kofar gidan ya shiga sakin hon ba ƙauƙautawa.Allah Sarki Audi direba dake cikin bayi da cikin sa ya murɗa ya shiga kenan ya ji hon wanda ya tabbata matar gidan ne me shegen yawon tsiya,amma da ya tuna ya ga ta fito ɗazu sai ya yi maza ya fito ba tare da ya gama abin da yake ba sai dai hon ɗin da ake saki na rashin hankali.

Ya na wangale get ɗin sai yaga megidan sa ne yake ta zuba wannan hon,hankalin sa ya tashi kwarai don a tunanin sa ba lafiya ba.

Ya na shiga ko parking bai yi ba ya fito ya ƙarasa gurin Audi direba dake mishi sannu ya na son ya kulle get ɗin ya ruga bayi,don har lokacin cikin sa bai dai na murɗawa ba.

Mari ya zabga mishi." Kai wane irin banza ne matsiyaci kawai gidan ubanka ne da zan ɗauki lokaci ina hon baka amsa min ba? Ko kuɗin da nake biyan ka da shi haƙo su nake!"


"Allah ya baka haƙuri ina bayi ne cikina ya lalace."


Bai saurare shi ba ya shige cikin gidan falo ya shiga gibbiyar ta na kwance a doguwar kujera me cin mutum uku da remote a hannunta ta na kallo.


Ba tare da kallon in da take ba ya shige cikin ɗakinsa ruwa me sanyi ya dinga kwankwaɗa har sai da ya cika cikin sa,amma bai ji zuciyar sa ta dai na tafarfasa ba don ji yake kamar za ta fito.


Ya yi cilli da robar ruwan dai-dai lokacin da ta shigo ta na mishi kallon ko ya taɓu ne? Tsaki ta yi kawai ta fice ta san in ta tambaye shi zai iya gaya mata baƙa ita kuma sai ta rama,don haka ba ta tanka mishi ba ta ɗauki wayar ta dake kan gado ta fice a ran ta ta na faɗin." To wa kuma ya taɓo wannan kububuwan?Ba zan yi mishi magana ba ya ƙare a kaina bari na bari ya huce."Ta koma ta yi kwanciyar ta ta na kallo.


Tofa masu karatu kun dai jin yadda ta kaya game da waɗannan aminan juna.Ku ci gaba da bibiyata na gode da yaba lintafina da kuke.

ƊUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ƊIN KU YA NA SAKA NI NISHAƊI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM








Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha uku.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 13*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


A.k ya na tuki ya na jin zuciyar sa na wani irin tafasa sai dukan sitiyarin yake ya na tsaki ji yake kamar ya je ya shaƙe shi,ya na ji a ran sa ba zai ƙara hulɗa da shi ba don ya tabbata ba shi da mutunci kuma yau zai mayar mishi da motar da ya siya musu a tare da suka je Dubai.


Da sauri ya taka burki ganin ya na son ya buge wani yaro dake sai da rake a tire,ya yi ƙoƙarin janyo natsuwa don ya samu ya isa gida lafiya saboda da ƙyar yake gani.

Matarsa na zaune ita da yaranta suna assigment sai ganin sa ta yi ya shigo kamar an jeho shi,bai amsa sannu da zuwa da suke mishi ba ya shige ɗakinsa wanda ya ɗaga hankalin ta ta miƙe ba shiri ta bi bayan sa.


Ganin yadda ya haɗe kai da gwiwa ta ɗauka rasuwa a kai don haka jikinta a mace ta ƙarasa gun sa tare da dafa shi.

" Lafiya Baban Najwa in ce ba wani abu mummuna ya faru ba?"


Ta faɗa cikin tsoro ganin yadda idanun sa suka canza sannan ta ƙara cewa." Ka yi haƙuri dama haka duniya take ni dai fatana ba mutuwa akai ba,ko wani mummunan lamari ya faru! Don Allah ka yi magana."
Bai amsa mata ko ɗaya ba ya ɗauki ruwa ya na sha.Ganin haka sai ta janyo jikinta bayan ta ƙara A.c ɗakin ta janyo mishi kofa a ran ta ta na addu'ar Allah ya sa lafiya.


Kimanin rabin awa ya ɗauka a cikin ɗakin sannan ya yi wanka ya fito da duguwar farar jallabiya a jikin sa,gefen ta ya samu guri ya zauna ya na kallon ta da ɗan murmushi a fuskarsa.

Sai hakan ya sanyaya zuciyarta da take ta bugawa ta na tunanin ko wani abu me girma ne ya faru.

Ido ya zura mata bai ce mata komai ba hannunsa ta kama tare da ɗora kanta a kafaɗan sa." Zuciyata ta ku san bugawa da na ga ka shigo a cikin wannan halin."

Shafa gashin kan ta ya yi yace a hankali da muryar da har yanzu a kwai ɗan ɓacin rai a cikin ta." Mun yi faɗa ne da A.m kuma me zafi don har na bar mishi aikin sa,zan kuma mayar mishi da duk wani abu da ya mallaka min."

Ya faɗa ya na furzar da wani irin huci mai zafin gaske.

Kallon sa take da irin ba za ku taɓa canzawa ba duk cewar ta san suna faɗa amma wannan karan da alamar faɗan ya yi tsamari ganin yadda ransa ya ɓace.

" Me kuma ya ƙara haɗa ku?"

Miƙewa ya yi ya ɗauki wayar sa zai koma ɗaki jin tambayar da ta yi mishi wanda ya ɗaukar ma kan sa wargaza shirin,amma kuma bai gaya mata ba sai yace." Wanann kuma sirri ne a tsakaninmu."

Ya ƙarashe shigewa bayan ya riƙe hannun Farha dake ta nacin ya ɗauke ta tun da ya fito daga ɗaki,ya bar ta a tsaye ta na jinjina wane irin rikicine ya faru a tsakanin su har ya yanke barin aikin.

" Ko ma mene ne su suka sani haba! Suna girma suna cin ƙasa." Tace cike da takaicin halin su sai kuma ta yanke shawarar ta kira Zainab ta tambaye ta sai da wayar ta yi ringin sau ku,sannan ta ɗauka tare da sakin wawan ajiyar zuciya.

" Hello sahiba ki yi haƙuri ina falo na bar wayar a cikin na manta da ita,sai da Atine me aiki ta kawo min.Ina yarana?"

Ajiyar zuciya ta yi tace " Ba komai wallahi suna lafiya dama na kira ki na tambaye ki ko A.m ya na nan,na ga aminin na sa ya shigo kamar sun sami saɓani hankalina a tashe yake."


Tsaki ta yi ta taɓe baki." Humh ke kika kula shi ni nawa da ya shigo ko kallon sa ban yi ba,na kyale shi don ba na son ya haɗa min zafi saboda ni ma a cike na ke da wata da ta yi min rashin mutunci a tiktok."Ta ba ta amsa ta yamutsa fuska.


"Zainab!Wai ke ba zaki dai na yin rawa a tiktok ba! A da baki aure amma yanzu ke matar aure ce hakan bai dace dake ba,kin ci sa'a shi A.m sam ba ya yin tiktok amma in Allah ya so ya kama ki sai kiga wani ya tura mishi kuma ba zai ji daɗi ba."

" Umh ke ni kyale ni lokacina ne kin san iya yawan adadin mutanen da suke bibiyata,so kike na yi asaran mutanen da suke zuzuta kyawuna?Ai in kika ga na dai na ƙila na mutu ne."


" To Allah ya shirye ki da masu hali irin naki a matsayin ki na matar aure ji je kina bayyana surar ki ɗora waƙa ki nabi don

Please Login or Register in order to submit comment