Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyu ba lafiya take da shi ba,ya sa za ta gaya ma Mariya ta nema mata aiki ta din ga yi don da yunwa ya kashe ta gara dukan Baba Sani ya kasheta ita kaɗai.Ta san ya na hana su abinci ne don kawai ya cutar da rayuwar su ko ya samu biyan buƙatar sa,amma ba wai don ba shi da kuɗi ba tunna aikin gwannati yake yi.

Ranar da Baba ya yi arba'in sun sha kuka bayan sun yi mishi saukar alkur'ani suka haƙura da kukan suna mishi addu'ar Allah ya jiƙan shi.

Cikin sa'a bayan kwana biyu da gaya ma Mariya ta nema mata aikatau,ta zo da murnar ta an samu saboda ta na samun aikatau da dama kusan ita dillaliyar masu aiki ne.

Tafiyar da Baba Sani ya yi sai hakan ya ba Juwairiya damar ta fara aikin ta cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya sani ba.Duk da ita Mama taso ta bari ya dawo su tambaye shi amatsayin sa na mahaifi,amma taƙi ta kafe daga karke wasu irin maganganu ta jefa ma Mama wanda yasa ta ji babu daɗi,a yadda take gaya mishi magana duk da ta san dama ba sa shiri,amma ko ba komai yanzu shi yake da matsayin mahaifinta kuma ko aure za ta yi shi yake da alhakin komai.

Faɗa sosai ta yi mata don ganin ta a maganganunta har da rashin kunya,wanda hakan bai dace ba musamman shi da yake da matsayi mai girma a ranta.Juwairiya ta ji maganganunta amma yadda ta faɗe su haka ta watsar da su a gurin a ranta take faɗin."Ta ya ya za'ai na mutunta mutumim da yake da burin ɓata min rayuwa,ko da mahaifina ne ya bijiro da wannan iyakan abin da zai yi mishi kenan Mama,domin babu biyayya ga abokin sabon halitta!Kema da zaki ji abin da yake so a gareni sai kin yi mishi fiye da nawa."

Matar da Juwairya za ta yi ma aiki likita ce a shika ta na da yara uku,a kwai wata mace tsohuwa wacce take mata girki ita kuma Juwairiya aikin ta kula da yaranta mata biyu da namiji ɗaya,in da za ta din ga mata aiki ta na tafiya har islamiya ta saka su tare da yaranta.Ranar da kuma take da aikin kwana za ta kwana da yaranta da safe ta shirya su ta tafi makaranta,wanda ta ba ta zaɓi in ta gama shirya su za ta tafi gida duk da ita matar makaranta ta ba Juwairiya zaɓi ta koma ta zana jarrabawar fita sakandiri.

Juwairiya ta ji matuƙar daɗi na samun aikin duk da ta na jin tsoron abin da Baba Sani zai yi mata in ya fahimci ta na aikin.Taƙi amince mata kan shawarar da ta ba ta da ta koma makaranta,duk da ita ma ta na da buƙatar haka amma ta san Baba Sani ba zai bar ta ba.

Sai dai cewar da matar ta yi za ta dinga kwana da yaranta in ta na aiki ya so ya ɗan tsorata ta,amma da ta gaya mata a kwai Baba tsohuwa sai hankalinta ya kwanta don ta yi tunanin tare za su din ga kwana.

Juwairiya ta ƙara son ta yi aikin jin an ambaci kuɗi mai tsoka,sannan da suka tashi za su tafi sai ta ba ta kayan abinci da kuɗi naira dubu ta sallami Mariya da tsoka,saboda ta yaba da hankalinta musammam da ta ganta ba ta da ƙazanta.

Mama da ta ji aikin har da kwana sai ta fara yiwa Juwairiya faɗa kuma tace sam ba za ta yi aikin ba,ta na ta faɗa in da take shiga ba nan take fita ba.Ganin hakan sai ta saka kuka ta miƙe domin ta yi sallar magariba."Ba gara na zauna a gidan Anty Naja ba tunna na ji Mariya tace mijinta ustazi ne me gamu,akan ƙanin mahaifina dake son ya ɓata min rayuwa.

Juwairiya ta yi tunanin za ta shawo hankalin Mama,amma sai ta ga ta kafe a dokin naƙi in da ta ƙara mata da cewar sam ata fau ba za ta yi aikin ba.

A ranar da suka shirya da Anty Naja za ta fara aikin,Mama ta kafe ko da Mariya tazo suka lallashi Mama shi ma bai yi wani tasiri ba ganin haka sai ta haƙura,akan ta nema mata wani kawai wanda ba za'a din ga kwana ba.

Da maraice ta na zaune akan kujera ta na wanke-wanke sai suka ji sallamar Mariya da wata a bayan ta,da sauri ta ɗaga kanta duk da cewar ba ta yi ma Anty Naja kallon kirki a ranar ba,amma ta sheda ta.

A kunyace ta amsa mata sallama tare da yi mata jagora zuwa ɗaki,ta ibo mata ruwa a kofi ta ije mata sannan ta fice daga ɗakin ta na jan numfashi ta riƙe turaren Anty Naja da ya baɗe ɗakin na su,wanda Juwairiya ta so ya dauwama a ɗakin saboda daddaɗar ƙamshin sa.

"Ba ki sanni ba ko Mama?"Anty Naja tace bayan ta ɗauki ruwan da Juwairiya ta kawo mata cikin sakin fuska,kuma ta sha ruwan sosai ba tare da nuna ƙyanƙyani ko tafi ƙarfin shan ruwan randa,wanda hakan sai ya yi matuƙar burge Mama wani ƙarin burgewa ta baje akan tabarma har ta na cire hijabin ta da ɗankwalinta.

Hakan ya yi matuƙar ƙara burge Mama sai ta ƙara jin ta saki jiki da ita tace."Bam ma sanki ba yarinya,amma da na ganki da Mariya ƴar maƙocin mu na gane kece wacce aka yi maganar aiki da Juwairiya..."

"Ni ce Mama tabbas ni ce ina ta jiran ta ba ta zo ba,sai da ga ba ya Mariya ta zo tace min kin hana ta "Tace tare da ƙatse Mama ba tare da ta kai aya ba.
"Haka ne gaskiya aikin nan ki nemi wata kawai."Mama tace ta ɗan canza fuska kaɗan,ganin haka sai jikin Anty Naja ya yi sanyi amma saboda ya ba hankalin da ta yi na Juwairiya ta kasa haƙuri tace."Don Allah Mama karki hana ta wallahi ba ni da matsala da ga ni har mijina,kuma in kina tunanin kwanan da za ta yi ne mijina ba zama yake ba wani lokacin ni kai na sai na yi bacci yake dawowa."

Ta matsa kusa da Mama tare da riƙe hannunta ta yi rau-rau tace."Don Allah Mama kar kice a'a ban ɗauki Juwairiya a matsayin me aiki ba ƙanwa ce a gareni,kuma duk ranar da kika ga wani abu ya faru mara daɗi a tsakanin mu ki hana ta zuwa."

Ta yi shiru ko Mama za ta ce wani abu amma sai ta ga ta kauda kanta ta na tunanin wanda ba za ta iya cewa ta yanke ta barta ko a'a."Kin ji Mama ki amince don Allah!Na yi masu aiki da dama amma basa iya riƙe min amana,bayan haka sace-sace suke min."

Duk maganganun da take yi ba ta ce mata komai ba,aranta ta na tunanin karta amince a za a sami matsala da Baba Sani duk da shi ma ya na da laifi,in da ace ya na taimaka musu da ba za ta yi aiki ba.
'Ki na ji Mama da ban so na gaya miki wani sirrina ba,amma nuna amincewar ki ya zama dole na sanar miki domin ki taimakeni ki ceci aurena.Mai aikina mijina ya kama ta da yarana tana basu kirjinta suna tsotsa ita kuma ta na saka musu hannu a gabansu.Hankalinsa ya tashi ƙwarai ba yan ya miƙa ta ga hukuma ya kawo su asibitin da nake aiki,hankalina ya tashi ƙwarai na yi kuka kuma mun yi rikici da shi daga ba ya yace dole na bar aiki ko mu rabu.Ina son aikina saboda da shi nake taimaka iyayena,sannan ina son aurena na yi-na yi a dai na saka ni aikin kwana amma ba zai yiwu ba.

Mijina ya bani zaɓin na bar aiki na kula mishi da yaransa ko ya rabu da ni,domin yaƙi barin na ƙara ɗaukar me aiki.Mun yi rikici da shi sosai daga baya ya haƙura na samu mai aiki amma daga wannan ya kama ta da wani matsala zai rabu da ni."Tace cikin hawaye ta ja numfashi sannan ta ɗora da cewa.

"Mariya ita ta ja ra'ayina akan Juwairiya saboda ta gaya min ta na da hankali,da ƙyar na amince da na ganta na yadda da maganar Mariya ki taimake ni Mama in har kika amince zan zama tamkar ƴarki,zan taimaka ma rayuwar ku."

Jikin Mama ya yi sanyi sosai har ba ta san sanda ta amince ba jin aure na shirin mutuwa,duk da watarana ita ma aure za ta yi."Na amince Allah ya kyuata amma ƴar nan ya kamata ku din ga kiyaye wa,ni ma matsalar ba daga gareni ba ne a kwai ƙanin mahaifinta ba lai-lai ba ne ya amince amma ta fara mu gani."

Sosai ta ji daɗi ta buɗe jakarta ta ciro dubu ishirin da biyar tace."Ga kuɗin ta na wata biyu dubu ishirin sai ki fara koda sana'a ne,sannan dubu biyar na baki kyauta kuma gobe in Allah ya sa tazo za ta taho da tsaƙo."

Mama ta ji daɗin kuɗin da ta bata ta na ta murna da saka mata albarka har ta yi mata sallama,ta kama hannun Juwairiya tace."Sis sai kin zo gobe ko?Don Allah ki zo da wuri ƙanninki suna ta maganarki."Tace tare da shafa kanta.
"Gaskiya ta na da kirki sosai."Mama tace ta na juya kuɗin da ta bata,sai kuma ta aje kuɗin ta kalleta tace "Kin san me ba zan taɓa kuɗin nan ba sai mun ji me Baban ku Sani zai ce."Da sauri ta miƙe kawai ta na faɗin."Ki ba ni naje na yo miki sare-sare ki fara sana'a ni fa ko me zai yi sana yi aikin nan,tunna shi ba taimakon mu yake yi ba don haka ba shi hurumin da zai hana mu."

Ta yi maza ta fice daga ɗakin kafin Mama tace komai sam ba ta jin tsoron abin da zai ce in dai ba kasheta zai yi ba ta rantse sai ta yi aikin.

Kamar yadda ta gaya mata mijinta ba mazauni bane haka kuwa ta gani,don tun da ta fara aiki ba ta gan shi ba sai tanƙamemen hoton su da yake manne a falon wanda tun da taje ranar da Mariya ta kaita ta gan shi a hoto,wannan dalilin ya sa hankalin ta ya kwanta ko da ta ga Baba me aiki aikin ta take yi ta tafi ba ta kwana.

Ta na aikin ta cikin kwanciyar hankali ga abinci da take ci kullum taci mai kyau ta sha mai kyau,don Anty Naja ba ta da rowa ko nama taci sai ta rage mata saboda yadda Juwairiya take kula da yaranta ga ta da tsafta ko ina na gidanta tsaf ya na tashin ƙamshi.

Kusan sati biyu ta na aiki cikin jin daɗi kuma har zuwa wannan lokacin Baba Sani be dawo ba,kullum in dai za ta dawo Anty Naja na sawa a yi girki da su ta saka mata a kula kuma da yawa,don haka ba sa matsalar abinci ga ɗanye da take badawa a kai ma Mama in dai za ta yi aikin kwana.

Ranar Juma'a da safe bayan ta gama aikin ta ta shirya musu abincin karyawa ta ibi nasu kamar yadda ta yi mata umurni,kasancewar ta gama aikin kwana za ta yi hutu har ta bawa Juwairiya hutun kwana biyu.

A hanya Juwariya ta na tafe ta na ta yi mata addu'a don tsakanin su Allah ne kawai zai biya ta,saboda irin kyautata mata da take yi fara aikin ta ta bata kaya masu kyau sosai da abin alheri ko hijabi kala biyar ta bata,sannan ko baƙi ta yi bata ce mata me aiki sai dai tace ƴar'uwanta ta na da matuƙar kirki sam bata nuna wani abu ko rashin mutunci.

A dai-dai ƙofar gidan su ta tsaya cikin firgici ganin Baba Sani ya ɗare kan motar sa ya na riƙe da ƙatuwar bulala,sai juya ta yake ya na zare ido ransa a ɓace da ga ganin yadda ya ɗaure fuska alamun ba mutunci.



Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na bakwai.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE)

Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*



*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA BAKWAI*



Tsananin mamaki ya kama shi ganin yadda Juwairiya ta gan shi amma sai ta yi tsaye ta na kallon shi, ba tare da nuna wani tashin hankali a fuskar ta ba ko tsoro.

Ya ɗan ƙare mata kallo cikin mugun nufin sa amma sai ya ga duk da ramar da ta yi,ta ƙara mishi kyau ɗan tafiyar da ya yi.

Juwairiya da tsaya ko zai ce wani abu amma ganin ya yi shiru,ya sa ta nufi hanyar shiga ƙofar gida za ta shige.Da dauri ya sha gaban ta a ransa ya na mamakin dai na tsoron shi da ta yi,tun ranar da ya nemi haɗa jiki da ita.
"Da ga gidan uban wa kike?"
Ya tambayeta da fuskar shanu y na zare mata idanunsa da suka kaɗa suka yi ja,saboda tsabar fitina da ya saka ma kansa.Ta ɗan ja ta tsaya tare da matsawa nesa da shi ganin yadda ya matso daf da ita.

"Ba na hanaki yawon maula ba,shi ne don kin ga ba na nan kika mai da shi sana'ar ki?"Ya tambayeta tamkar zai kai mata bugu.

"Ni ba maula naje yi ba,aikatau na samu nake yi domin na ciyar da kammu."Ta faɗa mishi ba tare da jin tsoro ko shakku a ranta ba.

Wani irin azababben mari ya wanka mata wanda ya sa ta yi taga-taga za ta faɗi,amma ta dake duk da azabar da ta ji kamar za tai fitsari a tsaye sai ba ta nuna mishi ba,don a shirye take ta shirya tsaf!Ko kasheta zai yi.

Matuƙar mamaki ya kama shi wai yaushe ya yi sake har ta raina shi haka,amma sai ya ƙara ɗaure fuska yace."Na ga kwana biyu kin raina ni Juwairiya saboda na nuna miki manufa ta a kanki,to wallahi har yanzu ina kan baka na saina cika muradina gara ma ki amince ki sami maslaha a rayuwarki."
A wannan lokacin ta ji wasu tagwayen hawaye sun cika mata fuska,zuciyarta ta amince da lai-lai shi ba mutum bane don ta yi tunanin rasuwar mahaifinta zai saka ya haƙura da ƙudirin sa.

"Ka sani ko mutuwa zan yi ba zan lamunce ka biya buƙatar ka a kaina ba!Ina matuƙar kaico a rayuwata da ka fito a matsayin ƙanin mahaifina.Ko mutuwa zan yi sai dai na mutu."Tace mishi ta na ƙoƙarin shigewa gida.

Sororo ya yi lai-lai ya yi sake tunna har taga wallar shi ta na faɗa mishi mugayen kalamai,masu tsauri a cikin idanunsa ba tare da shakku ko shakkar sa ba.

"Tun da kika ce haka mu zuba ni dake,bari na tuna miki akan ki zan iya komai tun da kika girma na ɗora kwaɗayina akanki Ki kuka da kanki zan iya komai don na cimma manufata."

Ta buɗe baki za ta yi magana wani irin takaici ya toƙare mata maƙogaro,sai hawaye da suka fara turereniya a fuskarta da ta tuna ƙanin mahaifinta yake mata wannnan halin,sai ta ruga a guje ta shige cikin gida ta na kuka.

Mama dake ƙoƙarin hura wuta a murhun gawayi idanunta duk sun yi ja, suna zubar hawaye saboda wutar taƙi kamawa sai saka leda take yi.Sai ganin ta ta yi ta shigo da kuka ta shige cikin ɗaki ta buɗe baki da nufin ta yi magana,duk da cewa ta san dalilin kukan saboda ta ji dirin motar sa sanda ya dawo sai kuma ga shi ya shigo.

"Saboda ba na nan shi yasa kika saka ta ta na yawon maula ta samo muku abinci ko?Na rasa wani hali kike so ki koya mata shi yasa na tsaneki saboda mugun halinki."
Ta yi shiru ba tace komai ba dama ɗabi'ar ta kenan duk sanda zai yi mata rashin mutunci ba za ta tanka ba,haka ma yanzu mutuwar Yayan sa bai saka ta canza ba.
Har ya gama bambamin sa ya fice bata ce ƙala ba,amma ta na jin gara su haƙura kawai da tashin hankalin da zai jawo musu.Bayan ta gama kukan ta ta share kamar kullum don Mama ba za ta taɓa lallashinta ba.

"Juwairiya ina ganin a haƙura da aikin nan kawai."Tace cikin ƙunar zuciya ta na kallon ta."Gaskiya Mama sai dai kiyi haƙuri,amma ba zan haƙura tunna shi ba taimaka ma na yake ba."

"Amma kina ganin tijarar da yake mana ko?Kin san halin shi ba shi da kirki,ni fa bana son tashin hankali ya dinga jibgar ki a banza."
Juwairiya shiru kawai ta yi a ranta ta saka komai zai faru sai dai ya faru,amma aikin Anty Naja yanzu ta fara.Hankalin Mama ya tashi da safen ranar da ta gama hutun ta bayan Juwairiya ta yi sallah ta tafi aikin ta,ba ta kula da kiran da Mama take ƙwala mata ba.

Da yamma da ta dawo Baba Sani ya shigo da bulalarsa ya yi mata duka,har bata iya tashi amma ba hana washegari ta koma aikin ta ba.Ganin irin dukan da yake mata Mama ta hana ta aikin,sai dai wannan karan ta bijire ma umurnin ta don ta rantse ko kashe ta zai yi ba za ta bar aikin ba.

Tsakanin ta da mijin Anty Naja ba ruwanta da shi tun da ta fara aikin so uku ta gan shi,duk sanda ya shigo ya ga yaran a kusa da ita sai ya fara musu faɗa ya kora su cikin ɗaki ya na harararta ya na mazurai,a yadda yake mata ta lura ya matuƙar tsorata da halin masu aiki.

Ganin haka ta ƙara kame kanta ta na mamakin yaran duk da suna zuwa islamiya amma ba su wani iya karatu ba,don ko babban dake da shekaru tara ko alhamdu bai iya cikakka bare ya damu da sallah ba,sai kallon catoon da suke yi kullum ba ƙauƙautawa,ganin haka ta dage da koya musu da saka su su yi salla,abin da ya ƙara saka Anty Naja son ta a cikin zuciyar ta.

Ganin ƴan canjin da yaransa suke samu abin ya burge shi har yake amsa gaisuwar ta a sake,wani lokacin har kyauta yake mata na kuɗi yace ta kaiwa mahaifiyarta don Anty Naja ta gaya mishi mahaifinta ya mutu.

Kusan kullum Juwairiya ta dawo sai taci na jaki a gurin Baba Sani jikin ta duk shatin duka ne,amma hakan bai saka ta karaya ba ta ci gaba da aiki don yanzu suna ci ga Mama dake sana'ar ta rayuwar su ta na tafiya cikin rufin asirin Allah sai dai takurawar da Baba Sani yake mata,wanda hakan ya na damin Mama ga shi taƙi ta dai na aikin.
A haka rayuwa take gara musu yau fari gobe tsumma,yayin da kullum burin Baba Sani ya cika burinsa amma Allah bai ba shi damar ida mugun nufin sa a kanta ba.Ganin haka sai ya ɓullo mata da nuna mata kuɗi ya na jan ra'ayin ta akan ta amince mishi ko sau ɗaya ne,amma taƙi duk ta gan shi sai ta nemi tsari da sharrin sa don ganin sa take kamar wani sheɗani.

Ta ɗauki tsawon shekaru biyu ta na aiki a gidan Anty Naja,a lokacin ta girma ta ƙara wayewa ga hankali da natsuwa kullum cikin hijabi take bata cirewa sai in mutanen gidan ba sa nan,ko ita Anty Naja ba za ta ce ga yanayin jikin ta ba,don tun kafin takai haka da Baba Sani ya saka mata ido ta yi tunanin ko jikinta yake ruɗarsa,bare yaanzu da ta zama ƴan mata ta cika ta batse ga Anty Naja da take ba ta kaya masu kyau kuma ta ba cin me kyau,har mai na shafawa da na wanke kai take siyar mata.
Maza da dama sun sha bayyana soyaryarsu gurin ta wasu kuma suje gurin Baba Sani,amma sai ya taƙarƙare yace Juwairiya ƴar mace ce sannan ba ta da kamun kai har kwana take a waje.Ya faɗi mugun abu da ba ta mata suna ya gaya musu,wasu suna jin haka za su tafi wasu in suka nace ya yi musu korar kare don ya rantse,in har ba ta amince mishi ba to ita da aure sai dai ta ga ana yi ko kuma in ya mutu.

Juwariya yarinya mai kimanin shekaru sha tara.Ta na da haske amma ba can ba,fuskarta mai kyau irin zagayayen fuska gareta,da dogon hancin ta haƙoran ta masu kyau ga ƴar wushiryar ta a tsakiya,wanda in ta yi dariya yake ƙara ma kyau matuƙa!Da dimful ɗinta.Bata da jiki amma a kwai shafe sannan doguwa ce ba can ba,amma ta na da tsawo wanda yake ƙara mata kyau.

Ƙirar jikinta me kyau ne ko ita ta na alfahari da hakan wato irin jikin nan ne mai ɗaukar hankali waɗanda ko wane namiji yake burin samu mace mai irin sa.Wannan dalilin ya sa kullum take cikin hijabi do ko ƙawayenta suka shigo suka gan ta ba hijabi,sai su yi ta zuzuta ta su na yaba kyawun jikinta.

A wata ranar litinin da safe bayan mutanen gidan sun gama karyawa suka wuce gun aiki,kasancewar da garin a kwai zafi sannan Anty Naja ta tura mata da tsako a cikin wayarta me botira da ta siyar mata,don ta din ga kiran ta ko kuma in ta tafi aiki da wuri ta gaya mata abin da za ayi,don yanzu girkin su ya dawo hannunta saboda Baban Abnaj yafi son girkinta.
Waina da miyan karas za'a yi da farfesun rago,ganin ta na da aiki ya sa ta zage damtse ta na yi tun ta na cikin hijabi har ta cire ta na ta aikin ta,ta kunna wayarta ta na sauraron karatun kur'ani cikin suratul ma'ida.Ta shafa'a ta na ta aikin ta sai ƙanwar Abnaj mai suna Ibtihal ta danna remote ta ɓata saitin tibin,Abnaj ɗan shagwaba ya saka kuka ya zo ya na sanar da Juwairiya akan ta zo ta gyara musu.

Hannunsa ta kama suka nufi falon da nufin ta gyara mishi,ta na tsaye a gaban tibi ta na ta ƙoƙarin yadda za ta gyara amma ta kasa gashi ita ba ta san yadda ake yi ba,sannan gashi har sun fara kuka akan a gyara musu.
A hankali ya buɗe ƙofar ya shigo da sallama a bakinsa,Juwairiya da hankalin ta ke kan tibi ba ta san ya shigo ba,ko in ce dukan su sai bayan ya ɗauki tsawon lokaci ya na kallonta cikin mamaki a ransa ya na mamakin dama a kwai wannan halittar a gidan sa?Don shi zai rantse bai taɓa mata kallo ko na sakan bane ya san dai ta na da kyau a fuska.

"Oyoyo Daddy!"Abin da yaran suka ce kenan wanda ya ɗauki hankalinta ta miƙe a razane ta yi diri-diri,tamkar za ta shige cikin ƙasa yayin da wani irin kunya ya lulluɓeta.
Ganin yadda ta diririce sai ya shige ɗakin sa akan ya ɗauko abin da ya saka shi ya dawo saboda mantuwa da ya yi,wato wasu fayal da ya ije da nufin ya tafi dasu sai gashi ya manta da su kuma ana buƙatar su.Ashe da rabon ya yi gam da katar!Don shi ya ga matar aure dama tuni ya yaba da hankalinta.

Ko da ya shiga cikin ɗakin wani irin kasala ya ji y rufe shi ya faɗa kan gadon shi ya na jin wani irin shauki na ta ya na zagaye ilahirin jikin shi.Ko da ya shiga ɗakin faɗa kan gadon sa ya daɗe ya na jin wani girmar lamari har na tsawon lokaci,sannan daga bisani ya miƙe ya ɗauki fayal ɗin ya fito.

Kawai sai ya tsinci kansa da bin hanyar kicin ɗin ya ɗan tsaya nesa da kicin ɗin zuciyar sa na bugu da ƙarfi,take yake jin lamura suna sauya mishi har ya fara dana sanin dawowar sa gida gashi komai

Please Login or Register in order to submit comment