Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni zaka buga aiko ruwan sama se inna so bare wani gardi can.Duk mutanen gidan ku kuwa sai an koya musu hankali ai ban yi kalar matar duka ba.Ko ka manta matsayin uba na."Ta numfasa sanann ta ɗora ta na kallon shi da tsananin ɓacin rai ya sa shi tsaye ya na kallonta.

" Kuma da kake faɗin karna zage ka inna zage ka me za ka yi?"Tace mishi cikin zallar rashin kunya ta na karkaɗa ƙugunta.A.m ya yi ƙuta yace.
" To ki kwatanta ki gani fitsararriya kawai."
Baki ta turo mishi tare da murguɗawa." Ni ba fitsararriya ba ce banza mara m....".

Wani irin mari ya gaura mata wanda yasa ta ɗauke lokaci guda ta yi taga-taga za ta faɗi amma ta dake tare da kwarma wani uban ihu,abin ka da farar fata lokaci guda fuskarta ta sunduma domin marin ya gigitata sosai.
Amma saboda taurin zuciyarta ta cakume shi ta na ihu ta na zagin sa shi kansa ya yi mamakin kafiyarta,ture ta ya yi ya shige ɗakinsa tare da bugo ƙofar kai tsaye bayi ya wuce ya sakar ma kan shi ruwa,domin ta haɗa mishi zafi kwanyar shi har wani tafasa take yi.





Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na goma.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*



*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA GOMA*

Bayan ya fito da ga wankan ya na jin yadda sautin kukanta yake tashi ya na mishi kuwwa a kunninsa,sai ya ji be kyauta ba da ya mari rabin ransa take ya zira doguwar riga ya fita don ya rarrasheta.

Ɗakin ta ya shiga ya ganta ta na ta kuka ta na haɗa kayanta tare da ƙoƙarin kira a wayarta,sai dai da alamu ba ta samu wanda take kira ba.Wayar ya fisge tare da rungumeta cikin tsigar rarrashi.
Dukan sa ta fara a ƙirjinsa ta na ƙoƙarin raba jikinta da na sa,da kyar ya samu ta sausauta kukan ta ɗan yi shiru ta na sheshsheƙar kuka cike da shagwaɓa.

Da ƙyar ta ya samu ta yi shiru amma ta rantse mishi duk ranar da ya ƙara kai hannunsa jikinta sai ta haɗa shi da Daddy ɗin ta,shi dai aikin lallashi yake ya na gaya mata maganganu masu daɗi har da kama kunninsa ya na faɗin ya tuba.

Bayan sun shirya suka kwanta cikin ƙaunar junan su kamar babu abin da ya shiga tsakanin su.Yanayin garin sai ya basu damar yin bacci cikin shauki suna maƙale da junan su.
Washegari suka tashi kamar babu wani abin da ya shiga tsakanin su na saɓani.Bayan ya yi wanka ya fice gidan amininsa ita ma ta gallah wanka ta fice aiki.
Parking ɗin motarsa ya fito ya caɓe Anwar ɗan gidan A.k da ake goyo don yanzu ya iya tafiya.
Juya shi ya yi ya na dariya tare da ɗauko tsarabar sa ya ba shi wanda duk ze zo sai ya kawo musu,sannan suka shiga cikin gidan sai ga ƴayarsa ita ma ta rugo da gudu ya ɗauketa haka dai ya shiririce ya na musu wasa har ya ɗauki tsawon lokaci.
" Yau kai ne a gari in ji maƙi baƙo ka ga angon Zainab to sannu da zuwa."Matar A.k tace ta na dariya bayan ta kawo mishi ruwa.
Shafa kansa ya yi ya na dariya yace."Gaskiya kince wani abu irin wannan kirari haka,kin san ƙawar taki bata da dama ba ta bari na naje ko ina gaskiya kin cancanci tukwici."
Dariya ta yi tace."Gaskiya makka da madina nake so a kai ni."Tace da shi."Duk kin je sai sai in kina buƙatar zuwa sai na saka sunan ki a cikin jerin masu zuwa."Dariya suka yi duka.
Sannan ta wuce ta na gyara dinning domin cin abincin rana.Bayan A.k ya fito daga ɗakin baccin sa ya ba shi hannu suka tafa tare da tsokanar junan su A.k yace."Ina madam Zey."Ya shafa gemun sa ya ɗan canza murya yace ƴar rigima za ka ce min na san yanzu ta wuce gurin aiki."
Dariya ya yi shima ya na kallon shi."Ai hali ne ya zo ɗaya an haɗu ne da an dace."Su kai dariya tare da ƙara tafawa."Madam ta gama shirya abinci ka zo muci."A.k yace da shi yamutsa fuskarsa ya yi ya na kallon shi, nan take sai hankalin A.k ya tashi musamman da ya ga ya maida kan shi a jikin kujera ya na kallon shi.Nan take ya fahimci amininna sa ya na cikin damuwa.

" Ya dai aboki a kwai matsala ko yanayin ka ya nuna a kwai abin da ke damun ka."
Ya kauda kansa gefe ya na faɗin."Kai ma ka san matsalar a kan Zainab ce ta na ba ni ciwon kai lamarin ta a kwai gyara.Na rasa yadda zan ɓullo mata ga kafiya da taurin kai."
A.k ya watsa hannun shi in akan wannan ne be wani dame shi ba yadda ka san auren dole a ka yi musu kullum cikin faɗa."In dai akan wannan ne ba ni da matsala daku kai ba haƙuri ita kuma kafiya ni lamarin ki ya na bani mamaki.Kun fi kusa kun san yadda zaku sasanta kan ku."
Ya faɗa ba tare da wata damuwa ba don ba yau ya saba kawo mishi ƙarar ta ba,kuma ko yaje ba saurarsa take ba gashi shi baya iya haƙuri da fushin ta haka kawai su yi ta sa maka ɓacin rai.
"Ko zamu keɓe ina da wata magana da zan ɗan tautauna a tsakanin mu kuma sirri ce."A.m yace da muryar raɗa ya na kallon gefen matarsa don ya yadda da aminin na sa ba zai gaya mata ba.
"Ki kawo mana abincin falona."Yace sannan suka shge cikin ƙaton falonsa da ya sha gyara ya na ta ƙamshi.Bayan sun ci abinci sun natsa har sai da suka yi salar azahar sannan suka natsa tare da taɓa hirar kasuwancin su.
A.m ya gyara zama ya na kallonsa cikin fuskar tausayi ya fara magana duk da wani gefe na zuciyarsa ta na masa gargaɗin karya faɗa masa amma ya fara magana da cewa.
" A kwai wani sirri da na ɓoye a raina na san zaka fahimce ni kuma ka ba ni shawara me kyai kamar yadda ka saba,ina ganin kamar na yi wa iyayena rashin adalci da na ɓoye musu cewar ni ne ba na haihuwa bayan ba haka lamarin yake ba.
"Na yi wa Zainab alƙawarin ba zan yi mata kishiya ba kuma ba zan taɓa gaya ma iyayena cewar ba ta haihuwa ba,amma na yi tunanin za ta canza halayenta mu yi zaman lafiya amma kullum ƙara bijiro da abin da zai saka mu samu saɓani,jiya duk ruwan da ake ta na waje wai sun je fati kamar ba matar aure ba,gabaki ɗaya ba ta damuwa da halin da zan shiga in ta ɓata min."

Ya yi shiru ko zai ce wani abu amma be tsinka shi ba sai kallon shi da yake yi ganin haka sai ya ɗora da cewa." Jiya ta kai fagen da na mareta wanda daga baya na yi dana sani.Ka ba ni shawara kar Zainab ta haukani."

A yanayin yadda ya yi maganar sai ya ba shi tausayi,sai dai ya na mamakin wai Zainab ɗin ce bata haihuwa kuma ya yi mata alƙawarin va ze gaya ma iyayen shi ba,sannan ba ya yi mata alƙawarin ba ze ƙara aure ba to wane irin shawara yake son ya ba shi don ya san be wuce yace ya ƙara aure ya samu matar da za ta ba shi yaro ba.
"Gaskiya ka yi wauta kana tunanin in kai ne ba ka haihuwa za ta yadda ta zauna da kai?Kuma ka cuci iyayenka kullum muka haɗu da Daddy sai ya yi min ƙorafin rashin haihuwar ka ya na tausaya maka,ga kuma masoyinka da yake ɓatar da kuɗin shi gurin yi maka sadaka da neman maka magani."

Ya numfasa ya na kallon shi a tsanake yaci gaba da cewa."Wace shawara kake son na ba ka bayan ka yi mata alƙawarin ba zaka ƙara aure ba kasan dai zuriya ta hanyar aure ake samun su,don haka Baban soyayya kaje kuci gaba da soyewa kawai shine shawarar da zan baka."

Abin da A.k yace mishi kenan ya miƙe don ransa ya gama ɓaci.A.m shima miƙewa ya yi don ba shi da abin da ze ce kan shi ya ɗau zafi,shi dai ya san koma mene ne ba zai karya alƙawarin da ya yi mata ba.

Bayan sun fito ya kalli matar A.k da take tattara gurin da yara suka ci abinci ya na dariya."To ni madan zan wuce."Dariya ita ma ta yi "Wato an gama gulmar mu ko ba komai nima ina nan zuwa gidana musha namu."
A.m ya ƙara dariya yana cewa."Baku da dama ne shi yasa musamman mutuniyar ki.A.k ya ja hannun shi ya na faɗin.Muje ka ji in ka biye mata sai ta ɓata maka lokaci da surutun ta suka fice.
******
Juwairiya ta ƙara samun aiki a gidan wata mata mai suna Hajiya Binta,matar ta na da kirki matuƙar gaske yaranta bakwai.Kusan dukkan aikin gidan Juwairiya take yi,saboda yawan yaranta take wahala a gidan sai dai amma babu laifi suna ƙaruwa da ita.Matsalar ta ɗaya mafaɗaciya ce sam ba ta da haƙuri kamar zawo take,duk yadda take taka tsan-tsan amma sai ta rori abin da za ta yi mata faɗa.

Saboda ba ta saba da irin aikin ba sai yake ba ta wahala ƙwarai,in ta dawo aiki ba ta iya taɓuka wani aikin watarana ma sai tasha maganin ciwon jiki.

Ganin irin wahalar da take sha Mama ta ba ta shawarar ta haƙura da aikin,amma ta nace sai ta yi musamman da ta ga kuɗin aikin na ta da tsoka.

Yaran matar kwata-kwata basu da mutunci ga rashin kunya abu kaɗan za su hauta da zagi suna ci mata mutunci,mahaifiyarsu kuma ba ta son ganin laifin ɗanta hakan ya sa ba ta kula su.
Abin da ya ƙara tsorata ta ganin sun girme mata ƙaramar cikin su ita ce take tunanin za su zo tsara da juna.

Hatta wankin su ita take yi musu don tsabar rashin mutunci harda pant da breziya suke ba ta wanki,amma ta yi haƙuri ta jure burinta ta samu abin da za su dinga ci.

Sai dai rashin mutuncin da suke mata da ta fahimci ba me ƙarewa bane ta yi tsalle ta fara nuna musu sam ba za ta ɗauka ba.
Hakan ya saka suka ƙara saka mata ƙahon zuƙa,domin zuciyar su tsabar hassada ce suna ƙyashin kyan da Allah ya yi mata musamman da suka ga sun ɓata jikinsu da mayukan bilicin.

Abin da Hajiya Binta ta tsira ya sa Juwairiya ta ji aikin ya fita a ranta,saboda kullum ta zo sai ta tuhumeta da cewar ta yi mata sata.Hakan ya tinzira ta ta saka a ranta duk ranar da ta ƙara za ta bar mata aikin ta.

Haka kuwa aka yi taƙi zuwa aikin bayan kwana biyu da barin aikin sai ga motar ƴan sanda da Hajiya Binta akan Juwairiya ta sace mata sarƙar gwal ɗin ta.
Juwairiya ta shiga cikin tsananin tashin hankali ganin yadda ɗan sandan yake ƙoƙarin tasa ta zuwa ofis ɗinsu,hankalinta ya tashi matuƙa ya dinga kuka tana rantsuwar ba ta ɗauka ba.Tsananin tashin hankalin da Mama ta shiga ba'a magana duk da ta san halinta,amma sai ta shiga ruɗu ta din ga tamabayarta da in ta san inda yake ta fito mata da shi,hakan ya saka Juwairiya cikin tashin hankali ta dinga wani irin kuka gani take kamar Mama ba ta yadda da ita ba.

Baba Sani ya sami abin da yake so don haka ya ƙara zuga Hajiya Binta kan ta tafi da ita ofishin ɗan sanda,burinsa ya cika dama tintuni yake addu'ar Allah ya sa haka ya faru.

Mama na gani aka tafi da Juwairiya ta na wani irin kuka gani take kamar dukan ta zasu ta yi har sai ta amsa laifin da ba ta aikata ba.Ganin an tafi da ita Mama ta nufi hanyar shiga cikin gida ranta na wani irin suya,hango halin da Juwairiya take ciki da yadda take kuka ta na kiran sunan ta,sai kawai gani akai ta yanke jiki ta faɗi ƙasa.

Hankalin Mariya ya tashi matuƙa wacce take zaune a ƙasa ta na kuka sosai,gani take kamar ita ta saka ta a cikin wannan hali saboda hanyar aikin da ta yi mata.

Ita da mahaifiyar ta suka kama Mama suka shigar da ita gida,sai dai daga baya kan dole suka kwasheta zuwa asibiti ganin numfashinta na ɗaukewa gashi ta na aman jini!

Baba Sani ya yi matuƙar jin daɗin faruwar lamarin duk da ba shi da shiri akan hakan sai dai ya na ganin yanzu ne burinsa zai cika akanta,don ya tabbata basu da wanda zai yi belin ta hakan zai ba shi damar ɗora mata sharaɗin zai yi belinta amma sai ta amince za ta yadda da buƙatarsa,don haka ma yaƙi zuwa ogishin da nufin sai sun yi mata dukan kawo wuƙa ta galabaita saboda ya san ta a kwai kafiya.

Juwairiya na zaune a cikin cell ɗin ta ƙudundune kanta a cikin jikinta tun da suka kawota take kuka,tunanin halin da Mama take ciki yake damunta wani irin sauro da yake damunta da ihu da cizo,yasa take ta zubar jawaye ga yunwa dake ƙwaƙularta."Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir."Abin da bakinta yake faɗi kenan cikin tsananin tashin hankali.

Tun da Hajiya Binta ta kawota ba ta ƙara zuwa ba sai washegari da safe lokacin ta matuƙar galabaita,bayan sun tuhumeta amma taƙi amsa laifinta dukan tsiya suka yi mata sannan aka maida ta.

Da rana sai ga Baba Sani ya shigo ofishin ya na zare ido,gurinta yazo ya na kallonta." Kin ga abin da kika jawo ma kanki kosaboda shegen taurin ranki.'Yace ya na kallonta duk da ita ba shi take kallo ba saboda taƙi ta kalleshi wani irin tsanar sa take ji matuƙa.

" Har yanzu kina da dama zan iya fitar dake amma sai kin amince za ki yadda da buƙatata."Yace da ita ya na kashe murya.
Wani irin kallo ta watsa mishi " Allah ya yi min tsari da mugun nufin ka,da na amince gara na tabbata a gurin nan ko ya zamo shine ajalina."
"Ok haka kika ce ko?To ai shikenan kuɗina ya huta tunna kin zaɓi rayuwar zuwa gidan mutane kina sata."Yace tare da watsa mata harara ya fice daga ofishin,kuka ta saka tare da cigaba da addu'ar ta ta na roƙon Allah ya kawo mata mafita.

Kwanan ta uku a gurin ranar da Hajiya binta ta shigo ta buƙaci a saki Juwairiya taga sarƙarta,duk da cewa ƙazafi aka yi mata amma ko haƙuri basu bata ba.Ita dai da gudu ta dawo gida tasan yaran Hajiya Binta suka ƙulla mata wannan ƙullalliyar amma Allah ya fisu kuma addu'a takobin mumini.

Ƙarin tashin hankali da ta zo Mama ba ta a gida Ibrahim ne yake sanar da ita ciwon Mama,wani kukan ta saka ta fita zuwa gidan su Mariya domin Mariya bata gaya mata Mama ba lafiya ba.

Yadda ta ga Mama hankalinta ya tashi ƙwarai rungume Mama ta yi ta na kuka sosai.Mama ce ta buɗe ido jin muryar Juwairiya hankalinta ya ɗan kwanta ganin ta fito,don ba ta san halin da take ciki ba shi ya sa jikinta yake rikicewa.

Likita ne ya shigo ya miƙa ma Mariya takadda yace."Gashi ki siyo wannan maganin ya kamata ku din ga kwantar mata da hankali, domin ta na da hawan jini ga ciwon zuciya, matuƙar ana ɓata mata rai to watarana zuciyar za ta buga!"
Wani ƙarin tashin hankali Juwairiya ta shiga jin Mama na da waɗannan ciwuka rungumeta ta yi tana kuka."Mama kema mutuwa za kiyi?Don Allah karki mutu ki barni!Rayuwata za ta shiga cikin garari.Allah na gode maka ka bani ikon cin jarrabawa,amma karka ɗauke min mahaifiyata ka barni da azzalimi."

Mariya ta kama ta ta rungume ta na buga bayanta hawaye ya na kwaranya a fuskarta tsananin tausayi ya cika mata zuciya ganin halin da take ciki."Kin ga ni Mama za ta barni ko!Wai me ya sa rayuwata tazo a baƙin jadawali ne?Nake kurɓar ruwan bakin ciki mafi zafi da ƙuna a zuciya."Tace cikin kuka." A'a Juwairiya karki faɗi haka!Kada ki kasa cinye jarrabawarki kin san Allah ya na jarraba mutum dai-dai imaninsa.Kar zuciya ta sa ki yi saɓo.Ina ji a jikina zaki ji daɗi a rayuwarki.Allah zai ba Mama lafiya."Ta gaya mata ta na shafa bayanta.

Daƙyar Juwairiya ta daina kuka sai ajiyar zuciya hannun Mama ta kama ta riƙe ta na kallonta.Duk wani hidima na asibitin su Mariya da mahaifinta suka yi har kuka ta yi ta na gode musu domin Allah ne zai biya su.

Bayan Mama ta samu sauƙi aka sallame su akan Mama za ta din ga zuwa ganin likita ta na karɓar magani,hankalin Juwairiya ya tashi ta na tunanin ina za ta din ga samun kuɗin da Mama za ta din ga zuwa ganin likita.

Kan dole ta ƙara saka Mariya ta nema mata wani aikin don sana'ar da suke yi sun cinye tsugune kawai suke,da fari Mama taƙi yadda ta ƙara yin wani aikin amma daga ƙarshe dole ta haƙura ganin yunwa na so ta yi musu tabo.

Kwasam ta haɗu da wani matashin saurayi mai suna Mas'ud Allah ya jarabci Juwairiya da son shi yaro ɗan gata da sanyin rai ga kyautatawa.Shigowarsa rayuwarsu ya sa sun samu canji sosai,duk da ya ga ita yar talaka ce amma be saka yaƙi sonta ba don da Allah yake sonta.Mas'ud ya na temaka musu sosai ya na aiki a Jami'ar Ahamdu Bello a library kuma ɗan samaru ne iyayen sa sun rasu sun bar mishi dukiya sosai,sannan ɗan kasuwa ne.

Juwairiya ba ta taɓa jin ta na son mutum ba sai akan sa, gabaki ɗaya ta ji ta na son ta aure shi sai dai tasan hakan ba me yiyuwa bane,don babu yadda za'ai Baba Sani ya barta ta aure shi sai dai akan yadda take jin sonsa, za ta iya fito na fito a tsakanin su ko gidan me unguwa za ta iya kai shi.

Haba tunna ya ga ya na zuwa gurinta ya saka tashin hankali yayin da shi ma Mas'ud ya kafe,ganin shi ma ɗan zamani ne sai yace bai tashi uren Juwairiya ba don bashi da kuɗi,nan take yace mishi kar ya damu ya amince zai yi mata komai.

Ranar da Mas'ud ya kira Juwairiya ya gaya mata Baba Sani ya amince da auren su har ya ba shi izini ya turo magabatansa,kawai jin sa Juwairiya ta yi amma ba ta yadda da abin da yace mata ba.Ganin haka sai ya ƙyaleta kawai in ta ga zahiri ta yadda.
Da misalin huɗu da kwata ɗan Baba Sani ya yi sallama ya shigo ya yi kiran Juwairiya taje shashin Baba Sani ya na kiranta a ɗakin matarsa.

Gabanta ya faɗi amma sai ta saka hijabinta ta nufi ɗakin ganin a kwai baƙi ya sa ta ji a ranta a kwai abin da ke faruwa sai ta tsaya daga kofa ta na sallama."Yauwa Juwairiya shigo."

Baba Sani ya faɗa da murya sanyaya a hankali ta yaye labulen ta shigo tare da tsaya daga nesa ta na kallon mutane jikinta ya bata dangin Mas'ud ne.

Miƙo mata alkur'ani ya yi tare da canza fuska kalar tausayi yace." Dangin yaron nan Mas'ud suka zo neman auren ki,amma ni bazan cuce su ba sun yi min tambayar kina da tarbiya nace gara suji a bakin ki, don nasan ke ƴar mace ce sannan kin yi yawon aiki gidajen masu kuɗi,duk mazan gidan sun sanki a matsayin ƴa mace ga abin kunya na satar da kika yi,har aka kulle amma ga kur'ani ki rantse musu hakan be faru ba "

Taɓ ji ta yi ƙasa ta gaza ɗaukarta ta ji wani irin hajijiya ya kamata." Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un."











Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na goma sha ɗaya.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G0J8rS0cxTtCCC38iwA3B9*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA GOMA SHA ƊAYA*


Ganin taƙi karɓar kur'anin hawaye ya na zuba ƙuncinta ya yi murmushin mugunta,ya juyo ya na kallonsu sannan ya ƙara saka kuka har da hawaye share-share yace." Kun ga abin da na gaya muku ya zama gaskiya? A matsayina na ƙanin mahaifinta babu yadda ban yi da ita ba akan ta zama macen ƙwarai, amma taƙi jin maganata!"

Juwairiya da take cikin wani yanayi na tashin hankali mara misaltuwa,ta rintse idanunta ta na jin wani irin ƙaton abu ya taso daga ƙirjinta ya tokare mata kirji ya kuma ƙi wucewa.

Tana son ta ji saukar hawaye akan ƙuncinta ko ya rage mata raɗaɗin da zuciyarta take ciki.Kunnuwanta ba za ta iya jure jin kalamai da yake yi ba,ya na aibanta ta ita da mahaifiyarta.

Ta muzanta iya muzanta da ƙyar ta yi nasarar jan jikinta ta fita zuwa shashin su,ta bar shi da bayin Allah da suka yi zuru suna kallon shi,yanayin su bai nuna sun yadda da maganar da yake musu ko akasin haka.

Da gudu ta faɗa ɗakin tare da ƙanƙamre Mama ta na wani irin kuka." Mama duniya ta min zafi! Ina jin wani irin baƙin ciki a cikin zuciyata,wallahi nafi buƙatar mutuwa fiye da rayuwata! Wai me na yi wa Baba Sani ya tsane ni haka!Gara ya kashe ni da ɗacin da yake saka ma rayuwata."

Mama ta rungumeta ta na shafa bayan ta don gani take kamar hauka ta yi." Lafiyar ki ɗaya kuwa?Ki yi shiru ki yi min bayanin yadda zan fahimta."

Kusan minti goma ta na kuka ganin ta kasa magana sai ajiyar zuciya take,a ranta ta na jin baƙin cikin rabuwa da masoyinta,don ta san yadda ya aibata ta babu yadda za'ai su yadda ɗan su ya aureta.

Da ƙyar Mama ta samu ta daina kukan sannan ta yi mata bayani.Ran Mama ya ɓace sosai ba ta san sanda ta ji jawaye ya na zuba a ƙuncin ta ba." Na gaji da halin da yake min! Zuciyata ta fara gajiya amma ba komai Allah ya fi shi da ikon Allah sai ya yi nadama,akan halin da yake miki."

Sosai Juwairiya take kuka koda Mas'ud iyayensa suka koma gida suka sanar mishi a abin da ya faru,hankalinsa ya tashi matuƙa duk ƙoƙarinsa na ya fahimtar da su,amma sun ƙi ƙarshe wan mahaifinsa ya gyara zama yace." Ko da a ce yarinyar ba halinta bane,to ƙanin mahaifinta ba ya son ya baka ita ka kyale musu yarinya ga ƴan'uwan ka nan sai ka zaɓa a cikin su."

Ransa ya ɓace matuƙa da ma ya ba shi izinin ya turo dangin sa saboda ya faɗa musu haka.
Motarsa ya ɗauka sallama ya yi bai ko tsaya Mama ta amsa ba ya faɗa gidan,a yadda ta gan shi ta san ba

Please Login or Register in order to submit comment