Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

manya ne da suke shaye-shaye su yi ɓatan kai su dami mutane,kun ga tunanina ya zama gaskiya ga ku kamar mutanen kirki ta waje amma ta ciki ba hali."


Ya numfasa sannan ya ci gaba da cewa ba tare da ya ba su ikon koda jan numfashi ba." Wallahi na ɗauka wani abin ya kawo ku ko ba sa rana akan Juwairiya a bazan taɓa yadda ta auri wani daga cikin ku ba,bare na ba da Juwairiya yanzu haka bikinta saura sati ɗaya don haka ku wuce ki bani guri ƴan ƙwaya kawai."


A.m ya harzuƙo ya na faɗin." Wa kake ce ma ƴan ƙwaya kai ne mugun ɗan ƙwaya da ka kasa gane mutanen kirki da na banza,ba giya muke sha ko kuma kamfanin ƙwayar muke haɗiya."



"A.m ya kamata ka saukar da fushin ka kasan me muka zo nema."


A.k ya ce mishi tare da kama shi ya zaunar ya na dafa kirjin sa.
" A'a ka barshi ya yi min rashin kunya ya biyo ni har gida zai gaya min magana,a ɗakina fa kake.To bari kaji ko mutuwa za kai sai dai ka mutu, kai ko maka mutu ne aka fito da kai a ƙabari,a ka ce na baka auren Juwairiya numfashin ka zai dawo wallahi sai dai a turbuɗaka a cikin ƙasa ta rufe maka ido."
" Wai tsaya kun ma san me kuka zo min da shi?Juwairiya da na tsana a rayuwata shi ne zaka kazo ka na da kuɗi ka aura taɓ wallahi ina."


Da aka kai wannan gabar sai A.m bai ce komai ba ya rintse idanun shi kawai don aikin A.k ne.Amma sai ya ji A k ya yi shiru ya na kallon Baba Sani da yake faɗin ƙiri-ƙiri ba ya son ƴar wansa ta ƙaru,kai wannan wane irin mutum ne an ya a kwai zumunci a duniya saboda son duniya ko ya ce son kai,mutane sun manta zumunci bayan Allah ya gaya mana zamu tsallaka siraɗi mara zumunci ba zai sha ba.


A.m ya buɗe baki zai yi magana ganin A.k yaƙi magana dai-dai lokacin da Baba Sani ya sausauta murya ko me tuna ya sa ya yi sanyi ya ce." To kai in ban da ku me za ku yi da mace irin Juwairiya yarinyar da ta gama zagaye duniya ta na yawon aikatau kuma duk mazan gidan sun san ta,sam ba ta da hali mahaifiyarta ta koya mata bin maza har sata take yi ka tambaya har kulle ta a ka yi a prison."

Ya ƙara sausauta murya ya matsa kusa da A.k don ya fi A.m sauƙi ya fara magana kamar zai yi mishi raɗa amma A.m ya na jin me yake faɗi." Ina da yara sun yi karatu na boko in kuma so Juwairiya ba ta san komai ba har talla yi take yi,ai da ka aure ta gara na yi maka fatan ka mutu ba aure.

" Juwairah nake so kuma zan aureta ko da ace duk mazan duniya sun san ta a matsayin ƴa mace."A.m ya ce ransa a ɓace.


" To ba zan ba da ba kuma kamar maganar ta ita matar wani ne na rantse,a yau zan ɗaura mata aure ba sai an jima ba don ina zargin ku za ku iya sace ta.To ni sai in ce kamar an yi maka baki kamar ka mai zai saka ka auri Juwairiya uban ta har ya mutu faskare yake yi, a gurin faskaren ya sara ma kansa ya mutu shi ne za ka ce ka na sonta.


" Nima ba son ta nake ba ban taɓa jin ina son wata ƴa mace bayan matata ba,kai ma in ka furta ina sonta ka yaudari kan ka don duk faɗin unguwarku ban ga macen da zan ji ina son ta ba."


Kawai sai ya yi galala ya na kallon shi a ransa tunani yake to uban me zai yi da ita,koma dai mene ne ba za ba shi ba in ma ya na son ya yaudare shi ne ya ba shi aurenta,yadda ya rantse Juwariya ba ta ba jin daɗi a duniya tun da ta kange kwaɗinsa a kan ta gara ya ba ma wannan tsohon ya wulaƙanta rayuwar ta.

" Ku faɗi ko me za ku ce ni ba yaro ba ne kuma ba zan baku auren ta ba yanzu ma zan ɗaura mata aure don haka ku cire wanann tunanin."

A.k ya karkace ya zaro makullin mota ya ije masa a gaban sa sannan ya janyo cek da ga aljihun sa ya ije na kimanin miliyan biyar.


Wayyo Allah zo ka ga ido sai ya zare ido can kuma ya fara mitsinan kansa ya gane ko mafarki yake." Ka bar cutar da kanka ta hanyar mintsnin kanka ba mafarki ba ne a zahirin gaskiya lamarin ke faruwa,in har ka bamu haɗin kai har gida zan canza maka rayuwar ka ta dawo sabuwa in har zaka ba ni auren ta."

A.m ya ce da shi ya na kallon sa yadda ya ruɗe kamar zai zare." Ikon Allah don Allah in mafarki nake ku dake ni sai na farka wai ni ne zaku ba wannan kuɗin don ku auri Juwairiya an ya ku ba ƴan cin kai ba ne?"

Ya faɗa ya na ƙarewa A.m kallo tunanin sa shi ne babba a wurin cin kai saboda ya fi A.k jiki da faɗi."Ko ma duniya muke ci ba ruwan ka in mun cinye ta tunna ba ƙaunarta kake ba."

A.k ya ba shi amsa amma kuma sai A.m ya kalle shi ya ce.

"Ka daina danganta mu da wannan mu mutane ƙwarai ne kawai fatanmu ka amince da buƙatarmu."

Ga mamakin su sai suka ga ya tattara kuɗin ya saka a aljihun wandon sa har da makullin motar ya fara zare ido. " Duk da cewar na tsane ki saboda wani ƙudiri na wa ba na fatar in da za ya huta ta ji daɗin aure,amma ba zan bari wannan damar ta wuce ni ba Juwairiya sai dai wallahi ina tsananin baƙin cikin faruwar lamarin da na ɗaya daga cikin ƴata kuka nema Allah bari na kira ta sai dai Juwairiya ta nuna mata kyawun halitta amma ta na da hali."


Miƙewa ya yi sai A.k ya kamo hannunsa ya zaunar da shi." Ka barshi ba buƙata ita dai Juwairiyar ya gani yake son ya aura na wucin gadi,shekara ɗaya tak za ta yi zai rabu da ita don a cikin sirri za' a ɗaura auren."


Ya ɗan kalle su a fakaice ya tabbatar da gaske suke yi ko fim suke son shirya wa suka yaudare shi haka." Tabbas haka maganar abokina yake ni zan aureta na shekara ɗaya matata ce ba ta haihuwa,shi ne nake son ka aura min ita bayan ta haihu zan ɗauke ɗana na sake ta ita ma zan biya ta kamar yadda da na yi maka."

Wani irin daɗi ya cika mishi rai ya kama hannun A k ya riƙe ya na faɗin." Kasan Allah ko auren kwana ɗaya kake son yi da ita zan baka, kai duk abin da za ka yi da rayuwar ta ba nida matsala in har za ka bani kuɗi sai dai da sharaɗin komai ya din ga biyo wa ta hannuna."

" Wannan kuma ba zai yiwu ba za mu baka duk jin daɗi na rayuwa,amma Juwairiya na cikin wani hali a yanzu ina da labarin mahaifiyarta da ba lafiya kuma za 'ayi mata aikin zuciya kaƙi ka taimaka,ga ƙaninta da yake da matsala tun mahaifinta na raye yake da burin a yi mishi aiki don haka zamu fitar da shi da mahaifiyarta,ita ma mu saya mata gida,sannan ba su da cin yau bare na gobe ka ga ya dole mu inganta rayuwarta wanda da shi zamu ci ƙarfin ta har ta amince da auren."



Baba Sani take ya haɗe rai jin baza a ba shi na Juwairiya ba da ya rantse ba zai ba ta da yawa ba,amma sai ya ɗan saki fuska ya na ce wa." Ni ma ki yi min uzuri ba ni da shi ne da na taimaka mata,wannan aikin wahala kawai nake yi ai nima abin a taimaka min ne."

A.k tsaya wa ya yi ya na mamakin sa ya sani ce wa a kwai mutane masu son kuɗi amma wannan ya wuce tunanin sa an ya na da imani kuwa.



Yauwa a matsayin ƴar aikin gidana za ta zo wanda za ka gaya ma mahaifiyarta za ta aiki na tsawon shekara ɗaya ta koya wa matata girki,wanann dalilin ya sa na ingamta rayuwar ta haka."Ba ka da matsala in ma a matsayi ƴar gadi za ta zo ai wallahi sai an yi auren,na san yadda zan yi da su duka hatta mahaifiyar ta tunna ka ba ni kuɗi ba ka da matsala.


Yace ya na tare da zaro makullin motar ya kalla sai kuma ya maza ya mayar lokacin da A.m ya miƙe a tunanin sa ƙwacewa zai yi don ya ga ba shi da kirkin ɗaya.


" Oh Juwairiya ban sani ba a she ke jarina ne mahaifin ki ya mutu ya bar min dukiya nima na yi kuɗi!Ai wallahi ƴan mata biyu zan gallo a rana ɗaya wayyo Allah!Ashe dama zan yi kuɗi Wallahi mutane za su ga rashin mutunci ehe."


" Yauwa ina motata kuma a ina gidan yake sannan kamar yadda ba ka son matar ka ta sani haka iyayenka kenan ni ne waliyin ku duka ba matsala in ma ka na son a ɗaura yanzu ba matsala."

Tsabar takaici ya sa A k yaƙi ce wa komai don ya fahimci jahili ne ku kuma son kuɗin ne ya rufe mishi ido yake faɗin ya zama waliyin su duka,sai shi ma ya miƙe ba tare da ya ce mishi komai ba A.m ne ya miƙa mishi takadda ya ce ga shi duk abin da kake son ka sani ya na ciki.


Zai fita A.k ya kalle shi ya ce " Ai ya kama ta a kira Juwairiya mu gaya mata ko in ce ka yi mata bayani ka san waƙa a bakin me ita tafi daɗi."

A.k ya ce mishi cikin gatsali shi har ya fara jin kunyar ta tun kafin ta fito haka kawai daga haɗuwa sau ɗaya sai su zo mata da wanann tatsuniyar.

" Baku da matsalar ga ya mata ita ɗin banza ai gaba ta kai ta."Ya ɗan matso ya na cewa." Dama wannan ɗan iskar tsohon ba ya bani wasu kuɗin kirki yau zan mayar mishi da kayan tsiyar shi,ana harkar kuɗi me za' ayi da tsiya ai ni mutuwar mahaifin ki gaba ta kai ni gobarar Titi a Jos."


" Ga ra dai ka kira ta shi ya sanar mata."A.k ya ce shi dai A.m bai ce komai ba sai dai ya ji wani iri lokacin da Baba Sani ya fita daga ɗakin ya na faɗin bari na dubo ta shegen yawo ne da ita ai kai da zama za ka yi da ita sai ince baka dace mata ba."

Juwairiya ta na duƙune a murhun gawayi ta hira wutan yafi sau ba adadi amma da ta hura sai ya mutu muɗis,kusan kuka take son ta yi don har ta fara hawaye ganin wutar ta taƙi kamawa ta miƙe tsaye tare da zura mata ido,ji take kamar ta ɗora hannu aka ta yi ta ihu.

Ta takaici ta kalli ledar taliyar da take son ta dafa ma Mama ba ta jima da dawowa daga asibiti ba take son ta ɗora musu abinci da ruwan zafi ta kai musu.


Kawai sai ta ki muryar Baba Sani ya na magana tare da ƙoƙarin shigowa duk da ba ta ji me yake faɗi ba,amma ta tsorata matuƙa gani take kamar zai ce ta dafa taliyar ya ɗaura aurenta.


" Juwairiya ina kike ashe dama ke jarina ne?Oh ikon Allah dare ɗaya Allah kan yi bature."Oya maza biyo ni kika abin mamaki aike kin samo mana can jin rayuwa Juwairiya yarinya ɗiyar albarka."


Cikin rashin hayyaci ta tsaya ta na kallon shi sam taka sa fahimtar wai yau Baba Sani yake ce mata ƴar albarka,sai ta fara shakkun ko ya zare ne jikinta ya fara rawa ta matsa nesa da shi,ta na karanto duk addu'ar da ta fito bakinta.


" Ke ban san hauka maza wuce kina da baƙi a falona kuma wallahi in kai min hauka,zan iya ajalin ki kin san bani da wasa akan kuɗi gara ma ki kiyaye!Maza wuce."


Da sauri ta ruga zuwa shashinsa jikinta na kyarma haka kawai jikinta ya ba ta Alhaji Taminu ne ya zo,sai ta rintse idanunta ba ta son ganin shi a haka ta faɗa ɗakin tare da sallama wanda na yi tsammanin a zuciya ta yi,don ko ita kanta ba na tunanin ta ji.


Tsayawa ta yi a ɗakin ta kasa buɗe idanunta sam ba ta son ganin fuskar sa mai kama da biri.

Wani ƙamshi wanda ta shaƙe shi a rayuwarta wanda ba za ta taɓa manta mamallakin ƙamshin, ba har iya tsawon rayuwarta,tun daga ranar da ta shaƙe shi take jin ƙamshin a jikinta har zuwa yau da ta haƙiƙance ma kanta lai-lai wannan mamallakin ƙamshin,mai sanyaya zuciya da kawo nishaɗi ga duk wanda ya shaƙesa ya na kusa da ita,musamman da ta ji sautin da zuciyarta take ta na bugawa da ƙarfi kamar za ta fito fat!Fat!!Har sai da ta dafe gurin.


A hankali ta sauke idanunta da suka kaɗa sukai jajur saboda wahalar hura wuta da tasha,duk da taji an kira sunan ta wanda ta gane ba muryar sa ba ne saboda ko tari ya yi za ta gane muryarsa,amma sai ta tsinci kanta da ɗora idanunta a kansa yayin da idanunnata sukai rau-rau sun canza kala suna ba da wani tarwatsi a cikin su.

A.m da ya ji shigowar ta duk da ba ta yi sallama ba amma ya ji an buɗe kofa an shigo,sanann kiran sunan ta da A.k ya yi sai ya kasa ɗaga idanunsa ya kalleta,duk da ya na son ya kalli wacce yake so ta zamo ɗa ga abu ɗaya tal mafi soyuwa a gareshi don ko sun rabu aba' a sake ma tuwo suna.



"Ya ilahi! Allah na roƙe ka ka farkar da ni daga mafarkinsa da nake,kuma wanann ya zama na ƙarshe tunna na kusa zama matar wani."Ta faɗa aranta ta na ƙoƙarin mai da hawayen da suke son bayyana ɓoyayyaen lamarin da ke cikin zuciyarta.


" Juwairiya ki zauna mana."

A.k ya ce ganin hankalinta ya tafi wani gurin ga mamakinsa sai ya ga ta nemi ƙasa ta zauna tare da saukar da kanta ƙasa.

Gaishe su take son yi amma ji take kamar babu harshenta a cikin bakinta ta ƙara buɗe bakinta amma ta kasa.

Ganin sun yi shiru duka sai ta ƙara ƙasa da kanta ta na kallon kafen ɗin dake ɗakin tamkar ta na son ta gano ko an maguɗi gurin yin sa.

A.k ya miƙe ya kalli A.m da yake ta danna wayarsa amma a zahirin gaskiya bai san me yake dannawa ba, tunanin sa ta ina zai fara kuma ta fahimce shi,shirun da ya yi ya na son ko A.k zai yi mata bayani amma sai ya ga ya miƙe.


" Bari in jira ka a mota in kun gama tautaunawar ina mota."


Ya fice ya na girmama lamarin da suka zo da shi. " Juwairaah! Babu gaisuwa wataƙila kin manta ni ko."Ya faɗa don rashin sanin ta in da zai fara.

Ta ɗago idanunta ta zuba mishi amma ba ta ce mishi komai ba,sai dai a ranta ta ce." Ta ya ya za'ai na manta da kai bayan ka tafi da zuciya da ruhu gangar jikina kawai ka barmin,amma to mai ya kawo shi gidammu wanda har Baba Sani ya yadda na zo gurin sa.Aurena yake son yi?".

Ta tambayi kanta sai ta yi saurin kawar da wannan bahagon tunanin ta ce " Kai ina wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa."


"Wai ni kurma kika zama bayan rabuwarmu?Ko kina mamakin ganina ne"

Ya ɗan tambaye da hasala a ranshi ganin yadda take basar da shi kuma ya tsani hakan.

" A'a ai ba'a mamaki da ikon Allah."

Iya abin da ta ce kenan ta ƙara naɗe bakinta ta yi shiru tanani fal a zuciyarta.


Ganin ta tafi wani tunanin daban sai ya ce " Haka ne ba'a mamaki da ikon Allah don haka kar ki yi mamakin na zo nai man aurenki amma fa na kwangila auren shekara ɗaya nake son mu yi dake kuma cikin sirri."


Juwairiya ta ɗago kanta da sauri ta kalle shi a wannan karan ba tare da ta ji nauyin sa ba." Aurena zai yi amma na kwangila mai hakan yake nufi?Sannan kuma cikin sirri to suwa ye ba' a son su san auren?"


Tambayar da ta yi ma kanta kenan a cikin zuciyarta wanda ba ta san maganar ciki ta fito fili ba.Ya gyara gilashin idanun sa ya miƙe tare da juwa mata baya.

" Yes abin da kika ji hakan nake nufi kin san ke ba sa'ar aurena ba ne,na tabbata kina tunanin me ya sa zan aure ki?Kamana ɗan gayu kuma ɗan masu da shi yayin da ke kina talaka kucaka dake.Ki kalle ni mai aji kama na ban yi kama da wanda zai aure ki ba."

Ya numfasa ya juyo ya na kallonta ganin yadda ta saki baki hanci ido ma'ana ta yi galala ta na jin tatsuniyar da yazo mata da shi.

" Matata Zainab wacce nake so fiye da komai rayuwata mace mai aji yarinya ƴar babban gida,Allah bai nufe ta da haihuwa ba ni kuma bazan iya haɗa ta da wata ƴa ɓace ba don na yi mata alƙawarin bazan yi mata kishiya ba,ga shi ina son na ga ƙwaina a duniya shi ya sa nake son na aure ki a sirri ki haifa min ɗa ɗaya na ba ta amma a gidana zaki zauna amatsayin ƴar aikin ta."

Wani irin hajijiya ta ji ya ibeta sai ga shi a gabansa ta zare ido jin a bin da ya faɗa,take ta ji wani hajijiya zai yarda ita ƙasa ta rintse idanunta,hawaye suka fara turereniya a kan fuskarta da ta shiga da tashin hankali.

" Allah na roƙe ka ka farkar da ni daga wannan mummunar mafarkin na farka ba tare da na gan shi kamar yadda yake tsaye a gabana! Ya Allah ka ɗauke ganina da shi na har abada da kunnuwana su ƙara ji min abin da yake faɗi ba,Ai gara na auri Alhaji Tanimu da na amince na auri mutumin da nake jin,bayan shi babu wani ɗa namiji a duniya shi ne yake son na yi rayuwa a gidan shi a matsayin ƴar aikin matarsa.


Wayyo Alla!gara na ga ranar mutuwata don zan fi samun maslaha a cikin ƙabarina da na amince da buƙatarsa.




Tofa ga dai Baba Sani ya amince shin Juwairiya za ta amince ya auren zai kaya?Ku dai ci gaba da bibiyar lintafin SAKACINA KO HALIN MAZA.





ƊUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ƊIN KU YA NA SAKA NI NISHAƊI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM








Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha huɗu.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.



*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 15*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

A karo na biyu ta ƙara gwalalo idanunta." Ina hakan ba zai taɓa yuwu ba!Gara na rayu a cikin talauci na kuma mutu a cikin sa.Anya ya san me yake faɗi kuwa.
Sai kawai ta nufi hanyar fita ba tare da tace mishi komai ba.
Juwairaah!"

Ya kira sunan ta da sauri tare ƙofar ya kama hannunta wani irin hajijiya ya kama ta wani abu mai kama da shokin,ya na zagaye jikinta yayin da yake fitowa daga gurin da ya riƙe ta ya na ƙara wutar sonsa a cikin zuciyar ta.

" Don Allah ka cika ni ba zan iya abin da kake faɗi ba,hakan ya tabbatar min da ka tsane ni ba ka son ganin farin cikina dama na san ni ba'a sa'ar auren ka ba ne, to amma kaje ka auri mata masu aji irin matarka ta yadda za ka samu ƴara daga gidan kuɗi,ba irina wanda mahaifina ya mutu bai bar min komai ba.


Ta faɗa tare da fisge hannunta da sauri ya sha gabanta ya toƙare kofar da take son ta fice, jikinsa ya yi sanyi ganin kamar ba za ta yarda ba,amma kuma ya zama dole ya san yadda zai yi ya shawo kanta,saboda amincewar ta ne kawai zai sa ka ta jure duk wani abu da za ta gani a gidan.


" Nima na so haka na sami mace mai aji kama ta, amma kin san babu wata mace mai aji wanda zan nema ta yadda da hakan.Kasancewa ta ɗa namiji da kowa ce mace za ta yi burin samu shi ya sa naƙi nai mar me aji iri na, don na san ba za a kwashe dai-dai da ita ba,kuma kema fa so nake na ceci rayuwarki daga ƙangin talaucin da kike ciki.

Ya ƙarashe maganar da murya na salon yaudarar shi ya na son ta amince.
Hawaye suka ƙara turereniya a fuskarta ta kalleshi da nufin ta saka wani mugun tsanar shi a cikin ranta,amma sai ta ji wani madarar son sa ya na ƙara shiga cikin bargon jikinta a duk sanda ta yi kuskuren haɗa ido da shi.

" Sai ni talaka ko?Ni da Allah bai saka min zuciya na so ba.Ko naƙasun talauci ya na yin tasiri a zuciya duk lokacin da ta ke son wani?Shi ya sa za ka zo ka cuci rayuwata ta ɗa na kake son na haifa na ba wata mace na har abada?Don Allah ka fita daga cikin rayuwata na roƙe ka na san ba za ka samu matsala da ƙanin mahaifina ba,amma ni ba zan amince da mugun nufin ka a kaina ba.A yau na yi burin dama ban taɓa sanin ka a cikin rayuwata ba."

" Ke ya ishe ki ƴar talaka kawai zaki zo ki na jera min wasu maganganu kamar wani ɗan ki!Dama ban yi miki dole ba."

Ya faɗa tare da kaucewa ya ba ta hanya ganin hakan ya sa ta zura da gudu za ta fita,dai-dai lokacin da Baba Sani ya yi gyaran murya."Ya kamata ka wuce abokin ka ya na jira,kawai ka nemo waliyin ka a duk sanda kake son a ɗaura auren kar ka damu da ita ko amincewar ta"
Da ido ya kalleta ya na gasgata abin da yake faɗi." Kin ji da kunninki abin da kwaɗayayyen ƙanin mahaifin ki yake cewa?Don haka ina tambayar ki ne don kar ayi ba tare da yaddar ki ba kizo ki ɓata komai."

Ya zaro waya mai kyau da tsada ya ije mata." Ga shi zan wuce na gaji da wannan kukan nan naki da kika tasa ni da shi.Fisabilillahi sai kace na zo gidan ta'aziya,duk abin da kika yanke zan kira sai ko gaya min." Ya miƙa mata kuɗi masu yawa." Ga shi ki je ki yi ma marasa lafiya siyayya.Ina ƙara gaya miki ɗa ɗaya kawai nake son ki siyar min bayan nan zaki iya auren namiji wanda ya fini,domin zan ƴanta rayuwarki zan gina ma mahaifiyarki gida na ba su duk wani jin daɗi na rayuwa.

Shekara ɗaya ne fa kawai za ki yi kina ma masoyiyata aiki in ma kin sami ciki, da wuri zan ɗauke ki daga gidan kin ga kin huta kenan,sannan ki iya takun ki ba da

Please Login or Register in order to submit comment