Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na kular mishi da yara,sam ba ta yi tunanin zai ce ya na sonta ba ganin basu da komai ƴar Malam Shehu.
Wayancewa ta yi ta na dariyar yaƙe tace."Haba Mama ni na yi tunanin wani lamari ne me girma yasa kika hana ta,amma akan wannan ɗan ƙaramin abin zaki hana ta,in dai a kan wannan ne karku damu ai gara ya auro wacce na sani da ya ɗauko min wata.Kuma karku manta shi fa mijin mata huɗu ne,don Allah karku ce zaku hana mishi aurenta."


Yanayin yadda take maganar ya nuna da ƙarfin hali kawai take yi,amma ta na ƙoƙarin ƙaƙalo dariya.
"Haba ƴar nan ai ana barin halas don kunya kawai ya nemi wata,amma Juwairiya ba tsarar auren sa bane."
Anty Naja ta dage ta riƙe kishinta ta na ba ma Mama baki akan ta haƙura ta yadda ayi auren,sannan ta ɗora da ko ba zasu bashi ba don Allah Juwairiya ta dawo aiki.

Daga ƙarshe ta yi ma Mama sallama ta fita har ta na tonon Juwairiya ta fito tare suke da angon ta yazo biko,ita dai ba tace komai ba a ranta take mamakin wani irin hali take dashi.Bayan ta jaddadawa Juwairiya tazo aiki ta yi musu sallama ta fita.

Bayan ta fita ta buɗe murfin mota ta shige tare da haɗe girar sama da ƙasa a ranta ta na mamakin raina mata wayo da ya yi wato ya turo ta ta yi mishi bikon budurwar shi,bayan ta sheda Juwairiya yarinyar kirki ne sai tace amanarta suke ci.
A yadda ya ga yadda ta fito sai hankalinsa ya tashi don bai yi tunanin za su gaya mata abin da ke tsakanin sa da ita ba,sai ya yi dana sani da tuntuni ya tare ta da maganar.
Bayan sun fara tafiya ya kalleta yadda ta ƙara cin magani fuskarta ba rahama yace cikin ƙarfin hali ya yi mata tambayar."Ya take ko ba ta jin daɗi ne?"

Haba kamar jira take ya yi tambayar lokacin da take kallon waje ta fara bala'i in da take shiga ba nan take fita ba tace."Munafiki da zamu taho ai da ka gaya min biko zan je na yi maka.Da ma amanata kuke ci kai da ita da ta amince ƙila sai dai in ji ta tare a gidana ko."

Nan ta ɓalle ta na gaya mishi kalamai zafafa mara sa daɗin ji,in da take shiga ba ta nan take fita ba a hanya ta zage shi tatas! Ta yi mishi wankin babban bargo.Shi dai shiru ya yi mata don ya san ya ibo ruwan dafa kansa kuskuren shi ɗaya da bai sanar mata ba,kuma bai ɗauka su Juwairiya za su yi suɓul da baka su gaya mata ba.
A haka suka kwana sam ba ta barshi ya rintsa ba,shi kan shi bai san ta iya rikici ba,sai ayau ya san ta na da zafi mata da kishi humh ba'a magana.
Washegari Juwairiya ta na zaune ba ta da ninyar zuwa aiki amma Mama ta matsa mata akan taje.Sai dai yadda ta ga gidan ta san ba su kwana lafiya ba.

Tun daga falon take kallon yadda ya hargitse ko ina an birkita shi sai gabanta ya fara faɗi ta san cewa a kwai wani girman lamari da ya faru.
"Munafuka kema me ya kawo ki gida!Maza fita matsiyaciya me kwacen miji kawai,in banda ke jahila kina ƴar talaka za kiyi tunannin mijina zai aureki."Anty Naja take magana cikin zafi sannan ta ɗora da cewa."Fita kar na ƙara ganin ki a gidana,sai abi wani sarkin amma mijina yafi ƙarfin ki.

Ko da ta dawo ta sanar ma Mama tace."To shikenan Allah ya sa haka yafi alkhairi.Hankalin Baba Sani ya kwanta ganin Juwairiya ta bar aiki kullum ta na gida,hakan sai ya yi masa daɗi musamman da yake tunanin yanzu komai zai kwaɓe musu.
Juwairiya ta yi tunanin Baban Abnaj zai biyo bayan ta,amma shiru kake ji Malam yaci shurwa wato matarsa taci ƙarfinsa.Ganin haka sai suka kama sana'a sosai da kuɗin da Baban Abnaj yake basu,yanzu har abincin siyarwa suke yi Ibrahim ya na kai wa ƙofar gida.Kuma suna samu ba laifi don da shi suke cin abinci.


*********

Kimanin shekaru huɗu da auren su suna zama cikin so da ƙaunar juna,sai ƴan saɓanin da ba'a rasa ba a tsakanin ma'aurata.Kullum A.m ya yi kasaƙe ya ji Zainab tace mishi ta na da ciki amma hankalinta ba shi a gurin tunna ba ta taɓa yi mishi maganar baby ba.


Lamarin sai ya fara damunsa musamaman da ƙannin shi da sa'annin shi suna da yara,amma shi matarsa ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba.

Sai kuma Allah ya ɗauki son ƴara ya ɗora mishi in ya gan su kamar ze zare.Ya na matuƙar son yara kullum ya na hanyar gidan ƴan'uwan shi ya na manne da yaransa.Daddy ɗin shi ya fara ƙorafi ya na tsoron kar A.m ya ɗauko rashin haihuwa sai ya fara mishi ƙorafi sosai kullum ya na kiran waya akan suje likita ya duba su.

Ganin yadda ya ɗauki son yara ya ɗora ma kansa sai Zainab ta yi gum da bakinta ba ta taɓa suɓutar baki ta nuna mishi ita ce ba ta son ta haihu take shan ƙwayoyi ba.
Sun ɗan fara samun saɓani yadda yake kwaso yaran ƴan'uwan shi ya kawo gidan ya siyo musu kayan wasa.Ranta ɓaci yake sosai ta na ganin hakan kamar takuratawa rayuwarta ne,duk yaran da ze kwaso ba ta musu komai sai masu aiki.Gaskiya Allah ya jarabce shi da son yara sosai.

Wataranar Alhamis Zainab ta tashi da ciwon ciki kamar za ta mutu,hankalin A.m ya tashi matuƙa ganin a sume ya ɗauke ta ya saka a mota suka nufi asibiti.
Bayan an karɓe ta aka yi mata ƴan gwaje-gwaje tare da turata ɗakin hoto,duk abin da ake ta na kwance kamar gawa ba ta san in da kanta yake ba.Likita ya gano mahaifarta ce ta samu matsala sakamakon tarin ƙwayoyi da ta din ga ɗinkira ma kanta masu ƙarfi na hana haihuwa.Wanda sakamakon haka mahaifar na gabda ruɓewa in da likitan ya ba A.m shawarar ayi mata aiki a cire mahaifar.
Tsananin tashin hankali A.m ya shige shi ya din ga kallon likitan kamar ƙarya ya yi mishi."Me yasa Zainab za ta aikata hakan?Hakan na nufin ba ta son shi ne har take shan maganin hana ɗaukar ciki don kar ta haihu?"
Irin tarin tambayoyin da yake yi ma kansa kenan amma ba shi da amsarta,daga bisani ƙeƙeshe zuciyarsa ya yi kan ƙaryata likitan ya san Zainab ba za ta aikata hakan ba,musamman yadda ta ga Daddyn shi ya mutu akan ya ga ya haihu,sannan yadda yake nuna mata ya na son ta haifa mishi baby ta na nuna masa Allaha ne be kawo ba.To hakan na nufin yaudararsa take.

Sai ya yi zuru ya na kallonta da take saukar da numfashi cikin rashin haiyaci ta na bacci,sakamakon allurar baccin da likita ya yi mata.Sai ya shafi fuskarta ya na me tausaya mata halin da ta shiga.

"Gaskiya ban yadda da maganar likita ba ina ta ya ya zan rayu ba tare da na ga ɗan cikina ba,duk da na san Allah ya ba jarabtar bayinsa amma gara wata jarrabawar ba wannan ba.Ya na ganin halin da Daddy ɗin shi yake shiga saboda rashin ɗa duk dukiyar da ya tara ya tafi a banza.In in haka ne ya zan yi da shares ɗin da na saka ma yarana tun kafin su zo duniya a ƙasashen waje.

Nan take zuciyarsa taƙi amincewa da abin da likitan ya faɗa duk da ya san asibitin su ƙwararru ne.
Kusan awa ɗaya ta na baccin wahala sannan ta buɗe idanunta.Da sauri ya riƙe mata hannu ya na shafar kanta."Kin tashi babyna sannu. Yace ya na ƙoƙarin temaka mata tashi ta zauna.

Bayan ya haɗa mata tea ya ba ta tasha ta lumshe idanunta ta na ji har yanzu wani abu ya na karta mata a cikinta,ita kaɗai ta san irin tarin azaba da raɗaɗin da take kwankwaɗa.

"Ya jikin sannu kin ji abin da likita yace game da ciwon ki?"Ya tambayeta da murya mai sanyi ya na gyara mata ɗaurin ɗankwalin ta da yake son ya warware.Ba tare da tunanin komai ba tace."A'a hubbina."A taƙaice ta ba shi amsar don ba ta son dogon surutu.

Ya ɗan ja numfashi ya fesar ya jinjina girman lamarin baya so ya gaya mata,bai san yadda za ta karɓi lamarin ba cewar ba ta haihuwa mahaifarta ya fara ruɓewa wanda dole sai an yi mata aiki.To amma ya na son ya gane shin da gaske ita tasha maganin hana ɗaukar ciki har ta illanta musu kanta,ba yan haka da ya bari sai ta warke.

"Likita yace ba zaki taɓa haihuwa ba yanzu ma mahaifarki za'a yi miki aiki a cire."Yace da ita ya na son yaga yadda za ta ƙarɓi lamarin.
"Inna lillahi.Tace tare da bayyano wani tashin hankali a fuskarta nan take fuskarta ta sauya sai hawaye,ta yi ƙasa da kanta ta na son ta yi magana amma ta kasa sai hawaye dake ta gasar sauka a fuskarta.A zuciyar ta kuwa illa tarin nadama da faɗin"Na cuci kaina!"
"Ina son na sani da gaske ke kika illan ta mahaifar ki Zeey sabosa bakya son ki haihu da ni,ko dama ba kya sona ne ko a kwai wani ƙudiri a ranki."Yace bayan ya yi ƙasa da kan shi dai-dai da kunninta saboda baya son aji me yake faɗi.

Ta dago ta kalle shi fuskarta cike da hawaye ganin yadda fuskarsa ya bayyana da tashin hankali,don in ba ta yi ƙarya ba har hawaye ta gani a fuskarta.
"Na shiga uku yanzu in yace ya na son ya haihu ga shi ni bana haihuwa ya zan yi?Kuma wallahi ba zan taɓa iya lamun ce na gan shi da wata mace ba.Gara ma ace na ga ranar mutuwata!Tace a zuciyarta ta na kukan nadama.

"Ka yi haƙuri hubbi ka yafe min na san na yi wa rayuwata illa ba zan taɓa haihuwa ba!Girman lamarin ya yi wa zuciyata girma.Duk akan sonka ne ina son karka juya min baya inna fara haihuwa na saki sanann jikina ya canza,kuma na sha jin kana faɗin baka son jikina ya canza kafi son na kasance yadda nake.Kuma a wannan lokacin ban shirya haihuwa ba gani nake yara kamar takurane a gareni duba ga irin yanayin aikina."Sai ta fashe da kuka ta na ƙarawa taci gaba da cewa."Wallahi ba zan iya buɗe idanuna na ga wata mace a matsayin muharramar ka!In kuwa ranar ta kasance to kasa a ranka zan kashe kai na na kasheta sannan na kasheka.In taƙaice maka mutuwar kasko za muyi,don ina sonka ba zan juri wata a kusa dakai ba."
Tsananin tashin hankali ya shige shi tare da nadamar furta mata waɗannan kalamai da yake na baya son yanayin ta ya canza,duk da be yi tunanin za su yi tasiri a gareta ba har ta aikata wannan abu su yi dana sani.

Ya zura hannun sa a aljihun wandon sa ya na kallon yadda fuskarta ya canza zuwa tsabar tashin hankali,ita kanta ya san ta yi nadama amma kuma mara amfani.
Ganin be ce mata komai ba ya na tunanin wanda shi kansa be san tunanin da yake ba,sai ta ci gaba da cewa."ko ma me ya faru duk akan sonka ne A.m ina kishin ka zan iya komai a kanka,son da nake maka ya sa na lalata mahaifata."
Ta kalle shi idanunta ya na zubar hawaye ta kama hannunsa ta haɗa da nasa tare da kai bakinta dai-dai saitin kunninsa."Don Allah ka yi min wani alƙawari,ka amince za ka yi min sannan gaya maka."
Ya damƙe hannunta ƙaƙam ya na hawaye matuƙar tausayinta ya kama shi ganin duk akan son shi ta shiga cikin wannan halin domin ta burge shi.
"Na yi miki alƙawari amma wa ya gaya miki in mace ta haihu mijinta ya na tsanar ta ni fa ina yaba miki kyawun halittar ki amma ba wai ba na son ki haihu ba.Yanzu ya zan yi da iyayena da suka ɗora idanunsu akaina suna son suga jikar su?"
a tambayeta ya na ganin tsananin wautar ta da ta aikata hakan,ita ma da ma wannan kan gabar take so yazo sai ta ƙara damƙe hannunsa tace." Ka yi min alƙawari ba zaka taɓa juya min baya ba kuma wannan ya zama sirri tsakanin mu cewar nice ba na haihuwa,sannan ka gaya ma dangin ka cewar matsalar da ga gareka take.Bayan haka ba za ka taɓa yi min kishiya ba,in kuma ka yi to lai-lai nice ajalinmu baki ɗaya."
Ta faɗa da farko da son ya ɗauki alƙawarin muryarta a shaƙe ta na murza hannunsa,amma daga ƙarshen maganarta sai ta ƙarashe da murya kamar wacce take ba shi umurni ko tsoratarwa.

Rungumeta ya yi ya na jin matuƙar tausayin ta duk da girman lamarin amma sai be ga wata illa a ciki ba,musamman da ya ga duk akan sa lamarin ya faru don haka zai amince ya gaya wa iyayensa da hakan, dama shi a duniya be ga wata mace wacce za ta haɗa kanta da Zey ɗin sa ba ita kaɗai ya ji ta burge shi kuma zai ci gaba da son ta ba tare da ya haɗa ta da wata ƴa mace ba don babu ita a duniya.

"In dai akan wannan ne karki damu na miki alƙawari,zan shirya mana viza zuwa ƙasar indiya a duba min ke don ban yadda cewar ba zaki taɓa haihuwa ba.Ƙara ruƙunƙume shi ta yi ta na faɗin."I love you nureel ƙalbi.!"

Loakacin da suka ji Zainab ba lafiya hankalin su ya tashi take a ka cika asibitin domin sun ɗauka ko ciki ta samu.Mahaifinta da ba shi ƙasar ya na jin ta na asibiti ya biyo jirgi ya dawo,ya na ta addu'ar Allah ya sa ta samu juna biyu,saboda ya na tsoron kar ita ma ba ta haihuwa kamar Mominta,duk da ya so ya ƙara aure ta yi ruwa ta yi tsaƙi ta hana.

Wani irin gata suke nuna mata sosai musamman gidan su A.m duk tunanin su ya sami ɗa ne,saboda tunanin su ya sa suke yi mata abinci irin na masu ciki suna kawo mata.
Hakan sai ya sa jikin A.m ya yi sanyi ya na tausayin su don haka ya shirya musu biza suka wuce Indiya domin a duba lafiyarta.
Kwanan su biyu suka huta sannan suka fara ganin likita,sai dai gwajin farko da suka yi mata aikin gaggawa suka sa aka shigar da ita tiyata,saboda mahaifar ta fara ruɓewa ta na narkewa a jikinta wanda hakan zai iya kawo mata matsala.A.m ya shiga tsananin tashin hankali duk yadda yake cikin tashin hankali sai ya kwantar da na sa ya na lallashinta ganin ta na son ta yi ƙaramin hauka.

Be baro ƙasar ba sai da ya tabbatar ta warke garau babu wanda ze ce an yi mata aiki.Sannan suka wuce zuwa yawon shaƙatawa don ya kwantar mata da hankali.
Zainab ta yi kuka har ta ba uku lada daga ƙarshe suka tattaro suka dawo cike da alhini.
A lokacin da A.m ya sanar ma family ɗin sa sun shiga cikin tsananin tashin hankali barim ma Daddy da har sai da ya yi kuka,ya rungume A.m ya na shafa bayan sa da tsabar tausayi da ya cika mishi zuciya." Yanzu son kai ma ba zaka ga ƙwanka a duniya ba.Allah Sarki ni da kai ne kawai ba mu da rabon haihuwa."Sai ya ci gaba da sharara hawaye.

Mahaifin shi ya jinjina lamarin tsananin tausayin ɗan na sa ya kama shi."Ni yanzu nafi tunanin matarsa an ya anyi mata adalci ina ga ka bata zaɓi kawai,domin na tabbata da ita ne ke da matsalar aure zaka ƙara in kuma ta amince za ta zauna dakai kaga ba'a shiga haƙƙin ta ba."Yace ya ba kallon ɗan nasa cikin tausaya wa.

A.m ya ji matuƙar tausayin iyayen nasa ganin yadda suka tashi hankalin su,suna jimami da alhini anya ya kyuata musu kuwa.Sun ba shi tausayi matuƙa wanda ya sanyaya jikinsa amma ko ma menene ya riga ya yi mata alƙawari.
"Haka ne Baba nima na bata zaɓi,amma tace ba za ta iya rayuwa ba ni ba."Ya ba shi amsa kansa duƙe." To shikenan Allah ya kyauta ai faɗan likita ba na Allah ba ne,sai kaga Allah ya canza lamuransa "Sun yi matuƙar jimami suka fauwala ma Allah lamuran sa ƴan'uwan shi suna ta yi mishi tayin ya karɓi yara daga cikin ƴaƴan su,duk da ya na son hakan sai dai ya san Zey ɗin shi ba za ta yarda ba.

Zaman nasu sai yaƙi jituwa tun daga lokacin sai suke samun saɓani da ya fara mata faɗa, sai ta saka kuka tana faɗa masa don ya ga ba ta haihuwa ne.
Tun ya na haƙuri har ya fara kai su gaban iyaye mahaifin shi kullum haƙuri yake ba shi ya na nuna mishi halin mata,dama tunna baya haihuwa ya shirya karɓan fiye da haka a gurinta.

Rashin zaman ta a gidan shi yake ƙara damun sa kullum ya dawo aiki ba ze sameta a gida ba sai tarin ƙazaman ƴan aiki masu kama da mayu a gurin kallo.Shi ya manta rabon da yaci abinci me daɗi in dai ba gida yaje ba ko,gidan amininshi A.k.Kullum ba ta da gurin zuwa sai ƙawa ta gayyace ta bikin ƙawarta ana birthday ɗin ƴar ƙawarta aikin ta ne kullum yadda ka san ana tsikarin ta in ta zauna a gida mace kamar me aljanun fita yawo.

Ya dawo da misalin karfe huɗu da rabi rabi na yamma yanayin garin hadari yake haɗawa ya canza iskar garin ta na bada wani iska mai sanyi-sanyi babu abin da yake so ya sha ruwan tea me ƙamshi ya shige cikin bargo ya yi bacci shi da ƴar matar shi.

Sai dai abin takaici ya na shigo da motarsa ya ga ba nata motar tsaki yaja ya yi parking ɗin motar a kasale ya fito be kula sannu da ma'aikan gidan suke mishi ba ya shige ɗaki.

Sharab!Ya zauna a falon sa ya na jin wani irin ƙunci ya saka yatsu biyu ya tallabe gemunsa ya lumshe ido da takaici,burinsa ya buɗe idanunsa ya sauke su akan kyakykyawar matar shi amma sai ya yi tozali da mero me aiki da tiren abinci ta kawo mishi tsaye ta na kallonsa.
"Ke!Uban wa kike kallo."Ya daka mata tsawar da yasa ta watsar da tiren abincin za ta ruga,sai kuma ta dawo da sauri ta tsaya ta na ƙoƙarin gyara gurin ganin iri n aika-aikar da ta yi.
" Anty ce tace na kawo maka abinci in ka dawo."Tace da shi bakinta na rawa ta na ci gaba da kallonsa.Ji ya yi tamkar ya shaƙeta ya miƙe kamar ze kai mata duka da gudu ta ruga..
"Zainab kina bani tarin matsala na gaji da kwashe-kwashe da kike min gaskiya."Ya faɗa idanunsa suka ƙara rinewa saboda tarin damuwar da yake ciki.

Bata dawo gidan ba sai zuwa ƙarfe tara na dare ta shigo da gudu saboda ruwan da ake yi tamkar da bakin ƙwarya,a lokacin A.m na zaune akan kujera two seater ya matsu ta shigo yau sai ta gane kuranta.
Ba ta kula da shi da yake zaune da waya a hannunsa ya na dubawa ba,ta tsaya a falon ta na ƙoƙarin cire kayanta da ruwa ya soma jiƙata saboda tafiyar da ta yi zuwa cikin gidan.
Gyaran murya ya yi wanda yasa ta fahimci ya na falon gaban ta ya ɗan faɗi,amma ta dake bata ce komai ba sai ƙoƙarin ta na cire doguwar rigar da ya matseta kamar za ta yi amai,ta na ƙwala ma Mero kira.

Wani ƙarin haushi ya turniƙe shi ita sam ba ta kishin jikinta ganin shigar da ta yi,sannan ta na cire kayanta amma take kiran me aiki tazo kai Zainab lamarinta a kwai gyara.
Bayan ta cire rigar ta umurci Mero ta ɗauko mata wani wani kayan ta saka,sannan ta nufi gurin sa da yake zaune saboda tsaban takaici be kalleta ba bare ya tanka mata,sai kallon agogon hannunsa yake.
Ba tare da nuna damuwa ba taja tiren abincin da ya saka Mero ta kwashe wan can ta kawo mishi,saboda tsabar yunwa da yake ji amma ya kasa cin abincin sam babu tes jira yake a gama ruwan ya ya yi take away.

Fara ci ta yi ta kalle shi tace."Habibi ba ka ci abinci ba lafiya."Banza ya yi da ita yaci gaba da kallon wayarsa ya na danne-danne a cikinta.

Kai hannu ta yi ta taɓa wuyan shi ko ta ji da zafi a tunaninta ba shi da lafiya,amma sai ta ji jikinsa normal.Taɓe bakinta ta yi ta ci gaba da cin abincin a ranta ta na faɗin."Miskilancinne ya motsa bari na kama kaina."

Kusan minti talatin ya na kwance be tanka mata ba har ta gaji da zama yaƙi kunna kallo ta san ta na kunnawa, ze taso mata tunna dama a yadda ta gan shi jira yake ta taɓo mishi,sai ta miƙe sif za ta shige ɗakinta ta hau charting.
Idanunsa a lumshe ba tare da ya buɗe ba yace."Da ga ina kike?"Yace a cikin wata irin murya me kama da da baya son maganar.
Dawowa ta yi ta zauna ta duburbuce ta fara in ina.Ya ƙara jeho mata wasu tambayoyin da cewa."Sai yanzu kika dawo ba na hana ki dawo min gida da daddare ba?Me yasa baki wuce gidan kuba.Kuma da izinin uban wa kika fita?"

Gabaki ɗaya ta tsorata ta kuma ruɗe ganin yadda yake jeho mata tambayoyin da ta kasa amsa koda ɗaya ne.
Miƙewa ya yi ya matso kusa da ita ya na kallon kayan da tasa ya ɗauka ya na kallonta a wulaƙance."Ba na hanaki saka irin kayan nan ba wai ke me yasa bakya kishin kanki yanzu fa a gaban ƴar aiki kika canza kaya,sam bakya kishin sirrina Zainab hauka kike son na yi a kanki na fara gajiya da halinki."

Duk cikin maganganunsa ba wanda ta ji haushi sai tambayar ta daga ina take da ɗan yi jim ta kuma dake ta ba shi amsa da cewa."Ina tunanin mun gama magana akan fita ba sai na tambaye ka ba saboda gaskiya ban ga a na wannan takurar a gidan mu ba.Kuma fa gidan ƙawar Anty Usaina muka je yau ake birthday ɗin ɗanta."Ta ƙarashe maganar ta na son ta ja hankalin shi ya sausauta fushin da ya ɗauka.
Ya ƙara jan tsaki me ƙarfi dama ya san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi.
Tsawa ya daka mata yace "Malama karki raina min wayo na gaji da waɗannan banzan bidi'oin da kika saka a ranki.Kin raina ni matuƙa Zainab baki ɗauke ni da daraja ba a matsayina na mijinki,watakila haka kika ga ana yi a aure a matsayinki na matar aure ba zaki shigo gidana ba sai tara da mintina."
Kaɗa kansa ya yi ya miƙe yaci gaba da cewa."Kin san nace miki in har kika fita ba da izinina ba,ban yafe miki ba kuma mala'ikun rahama suna tsine miki harki dawo sai ki kiyaye."
Hararan shi ta yi tace cikin gunaguni."Taɓ ni ai na gaya maka ba zan amince a takurawa rayuwata ba.Haka kawai to meye amfanin ilmina na lura so kake ka mai dani irin gidahuman matan nan marasa ilmi,waɗanda suke bari namiji na raina su wai duk in da zani saina tambayeka Allah ya kyauta."
Da takaicin yadda ta raina shi bata shakkar shi yace."Ba ma fita ba na hanaki driving sai dai duk in da zaki a yi driving ɗin ki."Ya na faɗin haka ya fara taka matakalan bene ze haye.
A sukwane ta jawo rigar shi ta baya cikin fushi tace."Wallahi ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa Ka mata ni zan yadda wani shashashan direba ya tuƙa ni,karka manta kusan motocina daga gidanmu na zo da shi bare ka yi min iko,in ma akan wace ka siya min ne ba zan ƙara hawa ba amma ba wanda ya isa ya kafa min dokoki."

Nu na ta da yatsa ya yi ya na cewa."Ba na hana ki kuma na yi miki warning akan riƙe min riga da kike yi ba,to wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara wannan gangancin.Kuma kika kuskura kika zage ni sai kin raina kanki,don jikin ki ze gaya miki."

Dariya ta yi me sauti ta ba shi amsa da faɗin."A lai-lai da ka tabbata ɗan ƙwaya kamar

Please Login or Register in order to submit comment