Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tari a cikin iyayenta,su kansu tsoron sa suke yi duk da mahaifinta shine babba.
Miƙewa ta yi ta ɗauro alwala ta yi magariba sai ta yi zamanta ta na jan carbi yayin da hawaye ke zuba fuskarta,wani gefe na zuciyarta ta na hasaso mata lamura sosai game da Baba Sani.
Baba Sani ya yi tsaye a gurin bayan tafiyar ta ya na tunani sannan ya ƙarasa dakalin ƙofar gidan ya zauna ya na gadin masu zuwa gurinta,ko da ka kira sallar isha'i ya yi sannan ya dawo ƙofar gidan ya ci gaba da gadin gurin.
Sai misalin tara na dare mahaifin Juwairiya ya yi sallama ya shigo da ƙullin leda mai ɗauke da garin rogo gwangwani biyu da siga.Mama ce ta amsa sallamar ta ƙarbi ledan tare da shinfiɗa mashi tabarma,lokacin har baccin wahala ya fara ɗaukar ta don yunwa take ji matuƙa kuma kamar zazzaɓi yake son kama ta.
Jin sallamar ya sa ta buɗe idanu ganin leda a hannun Mama ya sa ta miƙe tare da ƙarban ledar bayan ta yi mishi sannu da zuwa ta fice dan ta jiƙa garin.Ya kalli Ibrahim dake kwance ya na bacci ya shafa fuskarsa ya na faɗin." Ya jikinsa?Ina can amma hankalina ya na nan kin san jiya ƙafarsa ta bani tsoro."Yace ya na lasar bushashshen bakinsa dan rabon sa da abinci tun jiya da yamma da suka girka taliya leda ɗaya gashi ya wuni ya na faskare.
"Da sauki amma ya kama ta a maida shi asibiti gaskiya,yau ya bani tsoro ina ki kamar zan rasa Ibrahim saboda halin talaucin da muke ciki."Tace sai kuma ta rushe da kuka ta na fyace majina.
A sanyaye Juwairiya ta ije garin da ta jiƙa ganin Mama ta na kuka ta koma gefe ta zauna ta na jin zafin Baba Sani dan ita gani take shi ya takurawa rayuwarsu da ya hana ta naimi aiki,in da ace ta na aiki rayuwar su ba ta yi muni haka ba,ga Mariya da take aikin suna jin daɗi kuma matar ta na taimaka musu.
"Ki bar kuka dan Allah da kin san halin da na wuni da kin tausaya min!Na dage tuƙuru ina faskare sai da na gama Malam Aminu yace bashi da kuɗi sai gobe,daƙyar na samu ya bani naira ɗari biyu wai shima kwana biyu ba cinikin iccen.
Shuru sukai cikin jimamin rayuwar su kowa ya na takaicin yadda suke tsotsan tsamiya,ganin Baba ya dawo Juwairiya ta miƙe tare da yi musu sai da safe ta tafi ɗakin da take kwana.
Washegari da safe misalin bakwai da rabi ta shafa addu'a,sannna ta miƙe ta nufi waje dan wanki zatai da aka kawo musu da safe kuma ana so anjima,murna sosai ta yi dan aka wo kuɗin wankin za su sami su yi girki.
Da sauri ta ƙarasa ta na faɗin."La Mama har kin fara."Bata ce mata komai ba sai botiki da ta miƙa mata ta ibo ruwa a randa.
Basu gama wankin ba har misalin tara da rabi bayan sun gama Juwairiya ta fita tayo musu cefanen taliya suka dafa da mai da yaji.Bayan ya dawo daga sallar asuba ya kwanta don ji yake ko ina na jikin sa ya na ciwo,bai tashi ba sai da aka gama girki shi ma sai da Juwairiya ta tashe shi,dan tasan yunwa ce ke damunsa.
Bayan yaci abincin ya miƙe tare da fita ya na son ya ga kanin nasa,akan maganar komawa da Ibrahim asibitin da kamar yadda likitocin suka faɗa.
Ya na ƙoƙarin shiga shashinsa suka yi kicibis saura kaɗan su yi karo,Baba Sani ya matsa ya na kallon ɗan'uwan nasa ya ce."Lafiya yaya baka da lafiya ne?Ji yadda ka koma kamar wanda ake iban shi ana miya."Yace da maganar shi ta izgilanci ya na karkaɗe jakar zuwa aikin shi,dariya kawai ya yi mai kama da yaƙe yace."A irin wannan rayuwar ka na sane da halin da nake ciki ni da iyalina,yanzu ko taimakon da kake yi min ka daina."Ya ƙarashe magana da takaicin yadda ɗan'uwan nasa ya daina taimaka mishi tun tsawon shekaru da irin butulcin da ya yi mishi.
Hannun shi ya watsa ya kalleshi ya na kallon agogo."Sauri nake yi yaya kaga na yi latti kuma kasan yanayin aiki na,yi sauri ka faɗi abinda ke tafe da kai.Kuma da kake maganar ba na taimaka maka nauyi ne ya yi min yawa kowa ya ji da kansa."
"Haka ne Allah ya shige mana gaba,amma ya kama ta ka duba rayuwar Juwairiya kaga ni bani da shi da zan saka ta a makaranta,kuma kace ba aure zakai mata ba baka da ƙuɗin auren da ita."
"Haka na ce don ni yanzu ba ta aure nake ba,sabon gidana nake son na kammala.Ya bashi amsa a taƙaice sannan ya ɗora da ce wa."Kuma da kake maganar na saka ta a makaranta baka ga yadda take mara kamun kai ba can zata dinga watsewa da mutane,ka na sane da irin ƙorafin da nake maka a kanta ni nasan halinta da nake zaman gida."
Shuru ya yi ya na takaicin abinda ya faɗa ransa ya yi zafi,shi dai yasan kawai ya tsaneta ne amma yasan wacece 'yarsa wani irin hali take dashi.
"Yaya na fa gaya maka aiki zan tafi amma ka tasa ni gaba kana ta wasiƙar jaki,ina sauri ne in kima baka da abin faɗe na tafi imna dawo saimu tattauna."Ya ce dashi ya na ƙoƙarin fita da sauri ya tare shi sannan ya ce."A kan maganar komawa da Ibrahim asibiti ne,kuma gashi bani da kuɗi dan Allah ka taimaka...."
"Haba yaya kasan fa bani da ƙuɗi nima hidima tayi min yawa kowa yaji da kansa,amma ga dubu ɗaya kuje Allah ya ba da lafiya."Ya miƙa mishi 'yan ɗari biyar guda biyu ya fice ya barshi a tsaye kamar sanda ya na tunanin butulci irin na ƙanin nasa.
A sanyaye ya shigo cikin sasan sa ya zauna akan turmi kamar babu laka a jikinsa,bai ce komai ba har zuwa wani lokaci sannan ya ja numfashi ya na kallon Mama dake ninke kayan da suka wanke har sun fara bushewa.
"Lailai ɗan adam butulu ne."Yace cikin raunanniyar murya sannna ya ɗora da cewa."Wai yau ni Sani yake wulaƙanta wa kan kuɗi ya manta yadda na wahala dashi dan ya sami ingantacciyar rayuwa.Mama ba tace mishi komai ba sai gyaran murya da ta yi,dan babu wani abu sabo a cikin halinsa duka sananne ne a gurinta.
Juwairiya na kwance bayan ta tashi ta yi sallar nafila ta yi addu'a ta koma ta kwanta,idanunta babu alamun bacci sai juyi take yi ganin haka sai kawai ta janyo carbi ta na ja,idanunta a rintse zuciyar ta na fatan samun maslaha a rayuwar su tunannin ta inda za'a sami kuɗi a mai shi asibiti,don likitocin suna tunanni aiki za'ai mishi a ƙafar.
Kawai sai ta ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakinta tsoro ya kama ta,tunawa da ta yi ta manta bata saka sakata ba da ta fita zuwa alwala.Tsananin tsoro ya kama ta ta rintse idanunta ta na tunani ta ya ya kai wani ya shigo cikon gidan su,dan Baba Sani ya gyara gidan kuma akwai ƙofa na masu kuɗi mai ƙarfi gidan.
Ba ta gama wannan tunanin ba ta ji mutum ya shigo ya nufi makwancinta,ta buɗe baki da nufin ta yi ƙara sai kawai taji an toshe mata baki da wata irin murya da nufin a ɓatar da tunanin mutum ga sanin mamallakin muryar aka ce."In kika yi ihu saina kashe ki?Ya faɗa tare da soka zungureriyar wuƙa dai dai cikinta,amma ta yadda bazai cutar da ita ba.
Wani irin tsoro da tashin hankali ya ziyar ce ta taji tamƙar numfashinta zai yi balaguro zuwa wata duniyar wacce take da banbanci da wacce take rayuwa a cikinta."Da gaske abin da sautin amon kunnnuwana suke gaya min muryar Baba Sani take amo a cikin dodon kunnuwana?To mai ya shigo dashi cikin ɗakina a wannan sulusin daren?"Irin tarin tambayoyin da suke ta bijiro mata a cikin zuciyar ta wacce ba ta samu ko da amsar ɗaya ba.
_Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na uku dan har yanzu shinfiɗa ne har ba'a fara ba.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku man da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA UKU*



Hannun Baba Sani ya sauka a ƙirjin Juwairiya tare da wasu tagwayen hawaye masu tsananin zafi da ƙuna a fuska.Ta jin wani irin tsananin tashin hankali a zuciyarta yayin da take ji a cikin zuciyar ta tamkar za ta haɗiye zuciya ta mutu."Da ma burin sa kenan a kai na ya hana rayuwata samun sukuni,kullum ya na bibiyata tare da daƙile farin cikina?Me na yi masa wanda ba zai iya ɗauke mugayen idanunsa a kaina ba,a matsayina na ƴar wansa wanda suka fito ciki ɗaya?Wayyo Allah ina ma ace ranar mutuwa ta ce aka nuna min ba wannan ranar mai baƙin gani da muni a cikin zuciya ta ba.Ihu ya kama ta na yi ya kashe ni kamar yadda yace ko na yi shiru ya ɓata min rayuwa?"Ta tambayi kan ta cikin tsananin ruɗani dai-dai lokacin da ta ji saukar hannun sa a hurumin da ba na shi ba.Sai ta rufe idanunta ta na kiran sunan Allah tare da karanto duk addu'ar ta da fito daga cikin bakin ta.
Da sauri Baba Sani ya janye hannun sa daga ƙirjin ta tare da fasa abin da ya yi ninya,jin motsi daga waje."Sannu Malam ka yi a hankali jikin ka babu ƙarfi."Suka ji muryar mahaifiyar Juwairiya ta na magana cikin tausayi.
Hankalin Baba Sani ya tashi sosai ya daɗe ya na dakon wannan ranar tun lokacin da Juwairiya ta fara girma ya saka kwaɗayin sa a kanta,gashi ya sami dama amma kuma kamar hakonsa bai cimma ruwa ba.
Dai-dai saitin kunninta ya saita tare da raɗa ma ta."In kika yi magana sai na kashe ki."Hakan ya sa Juwairiya kame bakin ta ta yi shuru sai hawaye dake zuba a fuskarta.
Ya tsorata iya tsorata ganin sun shige cikin bayin ya buɗe kofar ya fice cikin sanɗa,Juwairiya ta fashe da kuka tare da fita daga cikin ɗakin a ranta ta ƙudirta ba za ta ƙara kwana a cikin sa ba.Fitowar ta ya dai-dai da lokacin da suka fito daga cikin bayin.Faɗawa kan jikin Mama ta yi ta fashe da kuka ta na wani irin kuka mai ƙarfi da ta da hankali ba ta damu da daren da ya tsula ba.Cikin tashin hankali da tsoro Mama ta rungume ta ta na faɗin."Lafiyar ki ɗaya Juwairiya dare ne fa?Ko kin yi gamo ne."Irin tarin tambayoyin da take mata amma ba ta kula ta ba sai kuka da take yi mai ɗaukar hankali,ganin kukan na ta ba na ƙarewa bane Mama ta ja hannunta suka shiga cikin ɗaki lokacin Baba har ya shige ya kwanta,saboda gudawa da yake fama da shi ya kasa tsaya wa ya tambayi abin da ke faruwa.
"Mai ya same ki lafiya?"Mama tace don zuwa yanzu kukan ya fara ba ta tsoro ta na ganin kamar Juwairiya gamo ta yi,yayin da ta wani gefen ta fara ba ta haushi bacci ne sosai a idanunta.
Juwairiya ta kasa magana sai kuka haka Mama ta yi ta gaji ta koma ta kwanta yayin da ta barta zaune tamkar ta haɗiye zuciya ta mutu.
Washegari da safe Mama duk lallashin da ta yi mata akan ta gaya mata abin da ya faru,amma taƙi ƙarshe sai dai ta yi mata ƙaryar mafarki mara kyau ta yi.Mama ba don ta yadda ba ta ƙyaleta amma zuciyar ta ta na gaya mata a kwai ɓoyayyen lamari,kasancewar Juwairiya ba ta taɓa kasa kwana ita kaɗai ba.Hankalinta ya tashi musamman da Juwairiya tace mata ba za ta ƙara kwana a ɗakin ita kaɗai ba,sai dai a haɗa ta da Ibrahim wanda Mamma bata iya kwana sai da shi saboda ciwon sa,gashi ta na da mugun bacci.Duk da jikin Baba da ya kwana babu daɗi amma haka nan ya shirya ya fita bayan ya sha magani.
Wunin ranar Mama ta kasa gane kan Juwairiya duk irin tarin tambayoyin da take mata,don ko ruwan koko da ta dama taƙi sha daga ƙarshe wani ƙarya sake yi mata tace ba ta da lafiya.
******
Gidan cike yake da mutane kai da gani kasan ana farin ciki a dalilin bikin ƴaƴan gata, ga kayan abinci da na tsotse-tsotse da a ke ta fita da shi.Bikin na yaran manya ne waɗanda duniya take hannun su kuma ta yi na'am da zuwan su duniyar,suke rayuwa a yadda suka tsara kuma suke ƙurɓar ruwan daɗi a cikin ta.
Naira ta na tsala kuka tare da nai man taimakon agaji da son ɓoyeta domin ta adana kanta ga masu buƙatar ta.Ruwan kuɗi kawai yake tashi da jerin gwanon motoci wanda ba zasu irgu ba.Wannan biki ne wanda ya amsa sunan sa kuma ya buƙaci a buga a jarida,wato bikin Muhammad Dawood Turaki da amaryar sa Zainab Abubakar mai shadda.Waye bai san waɗaɗnan hamshaƙan masu kuɗi da samu rayuwa mafi ƙololuwar daɗi a gare su ba.
Muhammad Dawood ɗa ne ga wani hamshaƙin mai kuɗi daga cikin turaki Family,wanda duniya ta san shi har da ƙasashen waje don ma yafi gudanar da harkokin sa a can.Tsarin rayuwar su irin na turawa da zallar boko.Gida ne na ƴanci da rayuwa babu taƙurawa da samun kwanciyar hankali.Suna da matuƙar kyau da asali mahaifin sa haifaffen garin Zariya ne.Ya gina katafaren gidan sa mai kyau a unguwar Zangon shanu,gida mai kyau na bene da tsari.Matan sa biyu Hajiya Khadija wato mahaifiyar A.m sai amarya Hajiya Binta Yaran sa bakwai Muhammad shi ne na farko wanda aka fi sani da A.m,sai kanin sa na miji sauran mata ne guda biyu sai kuma bangaren amarya ta na da uku.Suna zaman su lafiya kuma kan su a haɗe yake.
A.m mutum ne mara daɗin sha'ani ga rashin haƙuri ga saurin ƙulewa,ba ka taɓa gane in da ya sa gaba shi kullum mutum a gurin sa bai iya ba kuma ba a yi mishi gwanin ta ba.Kannin sa suna shan faɗa shi ya sa basa ƙaunar ya zauna a gida in kayi magana,yace ka faye surutu in kayi shuru yace ya na magana an raina shi.Shi komai a gurin sa laifi ne sannan ba shi da fara'a ko wasa ba ya yi dasu.Faɗin halin A.m abu ne mai wuya domin ya na da murɗaɗɗen hali baka gane in da yasa gaba,wannan dalilin ne ya sa ba shi da wasu abokan sai A k wanda ya jure halin sa duk da wani lokacin shi ma hutsu ne,amma ya san yadda yake tafiyar da shi.Muhammad ɗan gata ne a gurin mahaifin sa ga shi fari kyakykyawa dogo mai aji da tsafta.Wan mahaifin sa Alhaji Sama'ila ya na matuƙar ji da shi domin a hannun sa,ya tashi ya ma fi Daddy sa kuɗi sai dai shi Allah bai ba shi haihuwa ba.
Ya na matuƙar son yaga ya haihu saboda ya samu magaji har ƙasar waje ya kai matan sa uku a ka yi musu dashen kwai,amma Allah bai nufa cikin zai tashi ba,ƙarshe daga baya kan dole ya fauwala ma Allah lamuran sa ya na addu'ar Allah ya sa ya na da rabon haihuwa a duniya.
Tun kafin a haifi A.m mahaifin sa ya yi ma Yayan sa alƙawarin ba shi duk abin da ya haifa,saboda haka ana yaye shi aka miƙa ma matarsa Karime.A.m ya taso cikin gata da shagwaba bai san damuwa ko a kasin haka ba.Duk karatun sa a ƙasar waje ya yi in da ya karanci (Economis)bayan ya kammala ya dawo gida Nigeria amma ba ya wata yake fita waje.
Family ɗin Turaki mutane ne da ba ruwan su da harkan talaka ba sa hurɗa dasu,kuma ba sa shiga sha'anin su.A.m da ya tashi ɗauko tsanar talaka sai yafi kowa a cikin Family ɗin na su,don shi tunanin sa laifin sa ne da yaƙi tashi ya nema ya tsaya lalaci.Saboda mugun tunanin sa akan talaka ya sa ya tsani ma'aikatan gidan su kullum cikin hantara da mari yake musu laifi kaɗan zai kai duka,musamman masu aikin cikin gida.
Zainab Abubakar ƴar gidan wani ɗan majalisa ne da yake tashe a yanzu kuma hamshaƙin ɗan kasuwa.Yarinya mai tashen kyau da ƙuruciya ta na ji da kanta tare da alfahari da kyan da Allah ya yi mata,ga ɗagawa da son nuna ita ma wata ce mai ilmi da kuma nera.Sannan ra'ayin ta yazo ɗaya da A.m na ƙin talaka ba ta da kirki sosai,amma in baka shiga sabgar ta ba ba zaka gane hakan ba.Zainab likita ta karanta a ƙasar indiya.Mahaifinta ya na ji da ita don ita kaɗai ya haifa,sukai hatsarin mota ya samu naƙasa ba zai ƙara haihuwa ba.
Saboda haka yake ji da ita ba ya son ya ga ɓacin ranta komai take so shi take yi,gara mahaifinta ya na ɗan jan ido akan lamuran ta musamman shigar ta da ya tsana,amma mahaifiyar ta Hajiya Mariya ba ta barin ya tsawa ta mata a cewar ta in basu ba ta gata ba wa zasu ba.
Zainab mace ƴar ƙwalisa da gayu ga ƙamshi a kwai son turare masu tsada da kamshi,ga son kwalliya ta na ɓata lokacin ta akan kwalliya ita rayuwar ta tafi ba ta hamimmanci akan kwalliya da charting,sai ta wuni ta na kalle-kalle a waya ko ɗaukar hoto.Kullum rana na duniya Zainab ta yi wanka sai ta ɗauki hoto ta yi posting ɗin shi ko da wankan kwanciya ta yi.Bayan kwalliya da take so a rayuwar ta sai waya ko da yaushe wayar ta ya na hannun ta.
Wani lokacin mahaifin ta ya na tonon ta ya na kiran ta suna mai aljanar hoto ta na son ɗaukar hoto ta tura a Social Media a yi mata comment da liking a na zuzuta kyawun ta,ko ta ɗora a tiktok. Zainab mace ce mai son jiki da hutu duk da ba ta da ƙiba sai dai jiki na mata,amma a kwai son jiki ko waya a kace ta ɗauko sai tace wash!Ta miƙo ta na ya mutsa fuska ko alamar gajiya.
A taƙaice ba ta cas ko as ɗakin ta kullum mai aiki za ta shi ga ta share,sannan mai wanki ta kwashi kayan ta hatta innerwears ɗinta,mai aiki take wanke wa ko al'ada ta yi sai dai mai aiki ta kwashe abin a bayi ta zubar sannna ta wanke.Ta na matuƙar alfahari da gatan da iyayen ta suka bata tare da yi musu addu'a.Mace sangartacciya mai son jiki da hutu da zallar wayewa mai ƴanci wacce rayuwarta a cikin fararen fata ta yi.
Zainab ta na da kyua na nuna wa tare da mannata a hoton irin matan nanne waɗanda ka na ganin su kaga hutu,ko kai mace in ka hansu sai ka yaba.Doguwa fara ga gashi da kyan diri sannan ta na ƙara zuzuta kyanta da mayuka na gyara gashi da fata da kuma sabulai masu tsada.Ita dai ta yadda ta bautawa jikinta ko da za ta karar da wunin ranar ne,shi yasa in ka kalleta dole ka ƙara.
Ta na da girman kai a gurin samari ga ta da farin jini,amma duk saurayin da yazo za tace bai yi mata ba.Mahaifinta ya na matuƙar son yaga ya yi mata aure don ta haifa mishi jikoki,shi yasa kullum yake lallashin ta akan ta fidda miji daga cikin yaran masu da shi da alhazawan da suke neman ta,amma taƙi ita ganin ta aure taƙurawa rayuwar tane.Tafi son rayuwar hutu da jin daɗi sannan ba ta son taƙura da shishshigi ga lamarin ta.
Abin da ƙara tsoratar da ita ganin ƙawarta Nihal da ta yi aure shekara ɗaya da ya wuce.Ta na da kyau da gayu,amma tun da ta yi aure ta haihu ta zama ƙatuwa ga tumbi da ta yi,sannan ƙirjinta ya zube,kullum cikin aikin yara ko a gurin aiki ta rage ƙokari,ga takurawa ɗan tiktok ɗin da take yi mijinta ya hana.
Wannan dalilin yasa ta ƙara tsanar aure ta na gani kamar koma baya ne a rayuwar ta,ganin mahaifinta na da kuɗi kuma ita ma ta tara kuɗin da za ta ɗauki nauyin kanta.Ta saka ma ranta ba za ta yi aure ba,in ma dole sai ta yi aure to ba za ta yadda ta haihu ba kawai za ta yi rayuwar hutu ne don gani take kamar tara yara wahala ce gata likita kuma bata son jikin ta ya canza.
Duk mazan da suke zuwa gun ta kullum cikin kushe su take yi ta na yi musu wulakanci,kuma in auren za ta yi tana son namji mai kyau wanda ya fita gayu da tsafta.Ba ta taɓa jin soyayyar wani a cikin zuciyar ta ba,shi ya sa take wulaƙanta duk wanda ya zo gurin ta.
Kwasam!Ta haɗu A.m a ranar wata daren alhamis da misalin ƙarfe shidda saura kwata agogon birnin a ƙasar London,ta raka yar gidan ƙanwar mahaifiyar ta siyo kaya.Suna zaune a cikin jirgin za su dawo A.m ya shigo hannunsa riƙe da waya da cingam a bakinsa ya na taunawa a yangace.A.m na son cin cingam kamar mace hakan ya samo asali ga matar Alhaji Sama'ila da ta rike shi ta na son cin cingam.Hausawa sun ce zama da maɗaukin ƙanwa shi ke kawo farin kai.Aiko haka ta kasance A.m ya koya cin cingam a gurin ta duk lokacin da ya ci abinci ko ransa yake a ɓace,sai ya huce a kan cingam ɗin.
Ran shi a ɓace yake akan taron da suka yi da safe a companin su,sam yadda yaso taron ba haka ya kasance ba,wannna dalilin ya saka shi baro London bai kammalla abin da ya kawo shi ba.
Ya shigo cikin jirgin fuskar sa kamar an yi mishi mutuwa,bai kalli kowa ba sai kujerar sa da ya nufa ya na murza tafin hannun sa tare da tauna cingam ɗin da ƙarfi saboda fushin sa ya ragu.
Wani irin kallo ya watsa mata ganin ta zauna masa a kujerar sa,da fari ya ɗauka makauniya ce saboda kowa da numbar kujerar sa amma ganin ta na riƙe da waya sai ya daka mata tsawa da ƙarfi yace."Za ki iya tashi a ƙujerata ki nemi taƙi tunna baki je makaranta balle kin san yadda ake irga numbobi."
A hatsale ta miƙe tare da faɗin."What."Ita sai yanzu ta kula ba'a gurin ta ta zauna ba,saboda hankalin ta na kan wayar ta sanda ta shigo.Ranta ya ɓace jin kalaman sa sai kawai ta ɗaga hannunta da nufin ta wanka ma mutumim da ya kira ta jahila mari,sai ya banbance waye ke da jahilcin atsakanin shi da tunna idanunsa sun kasa gane mishi wayayya mace mai a aji da class,wacce take tashe a tiktok.

Zainab ta sauke hannunta a hankali jikinta ya yi sanyi matuƙa ganin matashin saurayin da ya kafa mata manyan idanunsa ya na kallonta,cikin zafin rai a yadda idanun sa suka nuna jira yake ta mare shi ƙila ball zai yi da ita yadda ya haɗe fuska.
Ta shiga in ina ta na ƙoƙarin matsawa daga gurin ya tureta ya na faɗin."Matsalar ƴan matan bahaushe kenan daga sunga sun fita waje su dinga nuna isa.Da kin mare ni wallahi sai na yanke duk yatsun ki na kai ma karan gidan mu nan gaba sai na ga da wane hannun zaki yi mari."Ya ja tsaki tare da zama ya maƙala earpis a kunninsa tare da harɗe hannun sa duka a ƙirji,zuwa can ya cire earpis ɗin ya lumshe idanunsa.


Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na huɗu dan har yanzu shinfiɗa ne har ba'a fara ba.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba

Please Login or Register in order to submit comment