Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA HUƊU*

Jiki a sanyaye ta koma kujera ta zauna ta na jin wani shauki ya na ratsa bargon jikinta,hannu ta sa ta share zufan goshin ta tare da jingina kan ta da bayan kujera ta na kallon sa cikin wani irin yanayi.Ganin halin da ta shiga Imsal ya matso dai-dai kunninta tace."Gaskiya gayen ya na da kyau sosai."
Zainab ta ƙara lumshe idanunta ta na kallon shi ba tare da tace mata komai ba,amma ta na jin wani girmar lamari a tare da shi,zuciyar ta ta na bugawa da sauri-sauri haka bugun ƙirjinta.
A lokacin da jirgin ya fara tafiya Zainab ji take kamar ta je gurin sa ta yi mishi magana,ji take komai na ta ya sukurkuce,amma ganin yadda ya ɗaure fuska idanunsa na rufe ya sa taji karayar zuciya.
Wayarta ta ciro ba tare da ya sani ba ta dinga ɗaukar sa hoto,ta na turawa ma ƙawayen ta da ta yi saurayi.Ko da suka iso Nigeria bai kalli in da take ba,ya na janye da troley ɗin sa hankalin sa na kan A.k da yazo ɗaukar sa.
Da sauri ta ƙarasa gurin sa tare da shan gabansa saura kaɗan ta faɗi,amma ba ta kula ba ta tsaya ta na mishi murmushi mai ɗaukar hankali.
A.m ya juya bayan sa ya na kallo a tunanin sa wani take ma murmushi a bayan sa,don shi sam ba yarinyar ba ta yi mishi ba,saboda tsiwarta sannan shi a wannan lokacin babu so a tsarinsa,bai shirya aure ba duk da burin iyayen sa kenan.
Kallo ya bita da shi tun daga saman ta har ƙasa ta na da kyau shi ma ya san haka,amma hakan bai wani dame shi ba kasancewar ya sha haɗuwa da mata kala-kala.
Wani ƙarin murmushi ta ƙara saka mishi tare da bin sa da sauri ganin ya fara tafiya."Don Allah ka tsaya ina son magana da kai,in ba damuwa ina son mu ƙulla abota."Ta faɗa tare da miƙa masa hannunta .
Wani ban zan kallo ya yi mata mai kama da ya ga kashi yaci gaba da tafiyar sa ba tare da yace mata uffan ba.Jikinta ya yi sanyi ta na tsaye ta na kallon shi har ya shige cikin motarsa,wanda A.k ya tuƙo don ya ɗauke sa.Da idanunta da suka canza kamar za ta zubda ƙwalla ta kalli bayan motar.
TURAKI FAMILY
Abin da taga an rubuta keman a bayan motar wani irin farin ciki ta ji ganin A.m ko ɗan waye,sai murna ya kama ta sosai tasha jin mahaifin ta na waya da wani daga cikin family ɗin.Ba ta son wulakanci sannan ta sha wulaƙanta maneman ta,amma wannan karan ta na ji ranta sa samu kalan mijin da take so.
Ko da ta isa gida tunanin wannan kyakykyawan saurayin ya tsaya mata a zuci,da ta rufe idanunta kyakykyawar fuskarsa take hangowa.Tun kafin Abban ta ya dawo ta kira tare da bashi labarin saurayin da ta haɗu da shi,kuma ya tafi da imanin ta.
Dariya ya yi sosai kin yadda ta ruɗe akan shi ta na mishi shagwaba da ƙyar ya samu ya lallasheta,ta kashe wayar ta bayan ya yi mata alƙawarin gane ko waye daga cikin family Turaki saboda ya san Alhaji Sama'ila abokin cinikayyar sa ne.
Ko da ya dawo gida haka ta sa shi a gaba ta na ta yi mi shi magiya,har ya gaji da ƙorafin ta ya kira Alhaji Sama'ila.
Bayan ya gaya mi shi dalilin kiran sa dariya sosai tare da farin ciki ya yi,a ransa ya na roƙon Allah ya sa A.m ya so Zainab ko ba komai ya yi dacen mace,sannan zumuncin kasueancin su zai ƙara ƙarfi.
Duk yadda Abba ya yi da ita kan ta haƙura da numbar A.m da ta kafe sai an turo mata,amma taki daga ƙarshe kan dole ya ƙara kiran Alhaji Sama'ila ya turo mi mi shi da numbar.
Da gudu ta ruga cikin ɗakin ta da wayar ta a hannunta bayan ta kwashe numbar a wayarta.Kan gadon ta ta faɗa ta na ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske ,tare da ƙanƙame filo a ƙirjinta.
Ran ta ya fara ɓaci ganin ta yi kira ya kai sau biyar ba'a ɗaga wayar ba,da ga ƙarshe sai ta ji an kashe wayar jifa ta yi da wayar ta ta zauna akan gadon ranta a jagule.
Ko da Alhaji Sama'ila ya tare shi da zancen yarinyar da suka haɗu a jirgi,nuna ya yi bai gane ba in ma ya haɗu da ita ya manta.Ganin kauce-kaucen da yake mi shi sai ya yi masa umurni da yaje ya ganta ya na son ya nemi aurem ta.
Babu yadda A.m zai yi ba tare da ya so ba ya amince duk da a wannan lokacin ya fara tunanin lokaci ya yi, da zai yi aure ya huta da damun da iyayen sa suke mi shi a kan ya yi aure sannan ya na buƙaƙar ya ga yaransa ga ƙaninsa ya na da biyu.
Da wannan tunanin A.m ya amince ya je gidan su Zainab tamkar za ta yi hauka haka take ji a ranta,da ta gan shi ruɗewa don Allah ya saka mata son shi a birnin zuciyar ta.
Tun ya na share ta har ya bada kai bori ya hau.Zainab ba ta a cikin matan da namiji zai wulaƙanta ita kanta ta na alfahari da hakan.Haka suke shan soyayyar su kullum suna maƙale da waya ana ga ya ma juna kalamai so.
A hankali A.m ya fara jin tsanar wasu daga cikin halayan Zainab,musamman yanayin shigar ta da tsabon son jikinta,sannan shi namiji ne mai son mace wacce ta iya girki amma tunkafin su yi aure ta gaya mi shi ita ko ƙafar kicin ba ta shiga.
Dariya ya yi kawai don ya yi tunanin tsokanar shi take yi ganin ta wayayya mai aji,ya san babu yadda za'a ta bari ƴar aiki na yi mi shi girki,ko a gidan su Amminsa take mi shi abinci.
Haka dai aka dinga cin soyayya har Allah ya kai si ga aure.Bayan an gama shagali amarya ta tare a ɗakin mijinta.Shi kaɗai ya shigo bai nemi rakiyar kowa ba,ko A.k daga kofar gida ya tafi ya na ta mishi dariya.
Da gudu ta taso ta rungumshi ya janye ta jikinsa,kasancewa wannan ne karon farko da mace ta rungume shi,idanunsa ya kafa mata duk rashin kunyar ta sai ta ji ta kasa haɗa ido da shi ta sunkuyar da kanta.
Bayan sun yi sallah sun ci kayan daɗi da ya siyo musu,suka tsunduma kogin soyayya.Wani irin tarairayan juna suke yi ma junansu A.m bai san ya kamu da soyayar Zainab ba sai da ya aure ta yake jinta a zuciyar sa.Koda yaushe suna maƙale da juna in ba shi a gida suna kan waya.Ya na matuƙar ji da ita ba ya son ɓacin ranta.
Abu ɗaya da ya fara kawo musu cikas yadda Zainab take son jiki komai suka yi amfani da shi,a nan za ta barshi sai in shi ya ɗauke da fari abin bai dame shi ba,amma daga bisani sai ya ji ya na taɓa zuciyar sa.
Kusan shi yake ɗan wasu aikace-aikace na gidan.Sati biyu da auren su mahaifiyarta ta kawo mata masu aiki mata guda biyu.Da fari A.m yaƙi amincewa amma daga kan dole ya haƙura,saboda yadda shaƙar numfashin gidan yake son ya fi ƙarfin sa.Hankalinta kwance ta ci tasha ta tafi gurin aiki.Hakan bai wani dame shi ba saboda ya na matuƙar sonta.
Kamar yadda Zainab ta tsara ba tare da ya tsani ba take shan maganin ha na ɗaukar ciki a ɓoye,ba ta damu da mai zai faru ba duk da ta san illar sa musamman da take likita,amma yadda A.m yake yaba halintar ta ya sa take shan maganin don ba ta son canjin jikinta.Kuma mafiyawancin family ɗin su suna da ƙiba.
Tsaye yake a gaban madubi ransa a jagule ya na kallon kansa a madubi,zuciyar sa babu daɗi.Matuƙar yunwa yake damun shi amma ba ya son cin abincin masu aiki,saboda daɗin shi bai kai na amminsa ba ya na jin kunyar zuwa ƙarɓo musu abinci,wanda ita Ammin da kanta tace ya kama ta su fara girki saboda ta gama kawo musu na amarci,in bai manta ba rabonsa da abinci tun daren jiya da ya ci a gidan A.k.
Ya ɗauki kum cikin ɓacin rai ya na tunanin bayan ya na matuƙar kiahin Zainab,sannan ita ba ta da kiahin kanta don ko masu aikinta mata yadda take fito musu kamar tsirara ya na bashi haushi amma ita ko a jikinta.Da namiji zai ɗauko kuku ya dinga mishi girki.
A hankali ya ji an turo ƙofa an shigo wani ɗan murmushi dole ya yi mata ya na jiran ta ƙaraso,amma sai ya ji an yi shuru kamar ba'a shigo ba idanunsa ya ɗaga da nufin ya kalleta yau yangar ce ta motsa.
Sai ya ga mai aikin su wacce bai ma san sunan ta ba tsaye ta na kallon ƙirjinsa ta na lashe baki,idanunsa ya kai kan jikinsa tare da jin kunya don daga shi sai ɗan tawul iya gwiwarsa."Ke!Uban me kike kallo ƙazama kawai?"Yace da ita ran shi a ɓace ganin yadda take kallonsa kamar wata mayya.
Da sauri ta matsa cikin tsoro muryar ta na rawa tace."Madam ce ta bani umurnin na shigo na share ɗakin."Ta ba shi amsa tana jin wani lamari dangane da shi.
"Tunna kin ga da mutum ba sai ki fita ba,banza mayya kawai."Yace da ita bayan ya ƙara daka mata wani tsawan,da sauri ta fice har ta na buge kanta da ƙofa.
Ya zama dole na ɗauki mataki ba zan lamun ce da waɗannan ƙazaman arna suna shigo mim ɗaki ba,gajerun wandunan sa ya kwashe ya saka a sif ɗin sa ya na takaici don ya san masu aiki suka wanke.


Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na huɗu dan har yanzu shinfiɗa ne har ba'a fara ba.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*






*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*


*SHAFI NA BIYAR*

Juwairiya zaune a gefen Mama ta na yi mata kitso,Ibrahim ya na zaune a gefenta ya na wasa.Baba ya buɗe labulen ɗaki ya fito dai-dai lokacin da Baba Sani ya kwaɗa sallama daga nesa da su.Ganin sa Juwairiya ta zabura kamar za ta gudu,tun lokacin abin ya faru ta ƙara matuƙar tsoron shi ganin shi take kamar kumurci.

Baba Sani ya kalle ta da wani irin kallo wanda shi kaɗai ya san ma'anar sa,sannan ya miƙa ma Baba takadda yace."Gashi na gaji da biyan kuɗin wuta ni kaɗai,yau za su zo ka biya ko kuma a yanke na ka."Ya faɗa ya na kallon bangaren Juwairiya da ta rintse idanunta tun bayan da lamarin ya faru ta yi katanga da shi,ko ina ba ta zuwa islamiya ma ta haƙura gara ta din ga zama a gida da ta gan shi.

Baba ya yi kasaƙe ya na kallon sa na tsawon lokaci sannan yace."Ka sa su yanke nawa in dai baza ka iya biya ba,bani da shi kuma na ga ko waya babu wanda yake da shi a cikin mu hasken kawai muke amfani da shi."

" Oho ko ma me zaka ce kace na gaji da wahala."Ya sa kai ya fice ya na bambami.
" Ikon Allah na rasa me ke damun shi ya canza gabaki ɗaya.Allah ya ganar da shi."Yace sannan ya ɗauki gatarin sa ya fita.Juwairiya ta yi shiru ta na tunani a ranta zuwa can ta miƙe tare da shiga bayi ta saka kuka.

Mama ba tace komai ba illa baƙin cikin halin da yake nuna musu,wanda ta san tsananin ƙiyaryarta ya sa yake nuna musu hakan.Idanunta suka kawo ruwa amma sai ta yi ƙoƙarin sharewa,ba tare da Ibrahim ya gani ba.

Juwairiya ba ta fito ba sai da ta sha kukanta ta ƙoshi sannan ta wanke fuskarta ta fito,a ranta ita kaɗai ta san halin da zuciyarta take ciki.Duk da Mama ta gane kuka ta yi ba tace mata komai ba,domin ita ma da za ta samu dama kuka za ta yi ko zuciyarta ta rage raɗaɗin damuwar da take ciki.

Yanayin rayuwar da Juwairiya take ciki babu daɗi ji take kamar ta na rayuwa a gidan kurkuku!Kusan kullum sai ta yi kuka ta na matuƙar bakin cikin halin da iyayenta suke ciki,burinta bai wuce ace ta samu aiki ta na taimaka ma iyayenta ba.

Tsakanin ta da Baba Sani tun faruwar lamarin take jin wani tsanar sa mai tsanani ya na ƙara shiga cikin ranta,ko muryar shi ta ji sai ta yi ta'awizi a cikin ranta tsananin mamakin mugun halin sa take.

Duk yadda ta so ta taimaka wa iyayenta abin ya ci tura har takai su kwana basu ci ba,tashin hankalinta yadda Ibrahim yake yi,amma ƙiri-ƙiri Baba Sani ya hana matar sa basu abinci.

Ganin halin da suke ciki wani lokacin ta yi kuka kamar numfashin ta zai rabu da gangar jikinta.
Mahaifin Juwairiya na tsaye ya rataye gatarin sa a kafaɗa hankalinsa baya jikinsa,tunani yake sosai a cikin ransa ga wata irin yunwa dake ƙwaƙularsar.Tunani fal a cikin ransa ya na tunanin kuɗin aikin da za'a yi ma Ibrahim aiki a ƙafar sa.

Ya daɗe a tsaye ya na tunanin mafita daga bisani yaci gaba da saran iccen da yake yi cikin rashin kuzari,tare da rashin madafa sai tsaƙa da warwara yake a cikin zuciyar sa.

Ya ɗaga gatarin sa a sama ya na can ya na tunani bai ankara ba sai ji ya yi gatarin ya dawo tsakiyar kansa! "Innalillahi wa inna ilaihir ra ju'un."Iya abin da yace kenan ya zube a ƙasa a sume jini na ta zuba kamar famfo!

Hankalin Malam Audi dake gefen icce ya na bayar da iccen ya fahimci abin da ke faruwa, da sauri ya iso garesa ya na salati cikin tsananin razana tamkar zai fasa ihu ganin halin da yake cikin.
Mutanen dake gurin suka yo kansa suna salati ganin abin da ke faruwa,kama shi suka yi aka saka shi a cikin mota suka nufi a sibiti da shi.

Lokacin da labari ya riske Juwairiya hannunta saka a ka sai kuma ta yi ƙoƙarin daƙile zuciyar ta da take ninyar kwarma ihu,ta fara salati ta na faɗin."Inna lillahi wa inna ailaihir raji'un."Sai hawaye bayan ta yi nasarar faɗin haka ta yi koyi da faɗe na ubangiji da ya umurci bayin sa da su faɗi haka duk lokacin da wata musiba ta same su.

"Wayyo Allah rayuwa ta me ya sa daga wannan sai wannan?"Ta tambayi kanta cikin tsananin ruɗani.Gabaki ɗayan su sun ruɗe ganin halin da yake ciki kai ya kumbura kamannin sa ya canza,sannan an ɗaure kansa da bandeji duk ya ɓace da jini.

A lokacin da suka je ko magana baya yi idanunsa a rufe ba ya iya ko buɗe idanunsa,daga ganinsa ya na cikin wani hali babu alamun numfashi tare da shi sai bugun numfashin sa da yake sauka a hankali a cikin tsananin wahala.

Rintse idanunta ta yi a jikinta take jin kwatankwacin zafin ciwon dake jikin Baba,ta kasa kuka sai hawaye da yake gasar sauka a ƙuncinta ba tare da sanin ta ba.

Suna zaune har tsawon wani lokaci amma bai farka da ga baccin da yake ba,saboda allurar baccin da aka yi masa.Har misalin tara na dare sai a lokacin Baba Sani ya shigo ya na ta zare ido,a cewar sa yanzu ya dawo gida ya ji labari.

"Ni na rasa wannan lamari na ka Yaya kamar wani mai bakin uwa,kullum rayuwarka ƙara taɓarɓarewa take.Haba wannan wane irin musifa ne! Tun ba yau ba nake maka maganar kabar yin faskare amma kaƙi ga shi nan abin da ka jawa kanka."

Ire-iren kalaman da yake faɗi kenan ba tare da nuna tausayi a fuskarsa ba,sai dai nuna rashin damuwa da faɗin maganganu mara tsari.Juwairiya da ta kifa kanta da akan gadon asibitin ta na wani irin kuka.

Hankalin su ya yi matuƙar tashi ganin halin da yake ciki,Juwairiya kamar ta mutu haka take ji,ƙiri-ƙiri in aka buƙaci kuɗi Baba Sani yake ƙin bayar ba kullum da uzurin sa da yake faɗi.

Da ga baya Baba Sani yake zuwa ya na kwana da Baba.Baba Sani tsaye akan Yayan na sa da misalin ƙarfe ɗaya na dare,kallon sa yake da mugun nufi a ransa.Filo ya janyo tare da danne masa kai.

Allah Sarki bawon Allah da yake kwance a cikin mawuyacin hali ya fara mutsu- mutsu da ƙafafun sa,bai jima ba ya yi dip alamun babu numfashi a jikinsa.

" Gara ka mutu kowa ya huta kullum cikin wahala nake da kai da iyalan ka,sannan ɗan buƙata ta da nake son na biya na rasa.Kaje kawai Allah ya haɗa mu a kiyama!Abin da yace kenan ya kwanta da ninyar da safe ya fasa ihun ya mutu.

Washegari da safe Juwairiya tun da asuba take azalzala wa Mama da su je asibiti,irin mugayen mafarkin da take yi akan mahaifinta ya sa hankalinta ya tashi sosai.Mama ce ta ɗan ƙarfafata har suka dama koko suka sha,duk da dai Juwairiya ƙurɓar kokon take wanda ko siga babu hankalinta na gurin mahaifinta.

Ko wanka ba ta yi ba ta ɗauki ruwan kokon ta na addu'ar Allah ya sa ya iya sha,Mama dai ba tace mata komai ba duk da ranta babu daɗi.Ko da suka isa asibitin gaban Juwairiya ya yanke ya faɗi ras!Sai ta kira sunan Allah ta riƙe kofin kokon ta na wani irin tafiya zuwa ɗakin da yake tamkar wacce ƙwai ya fashe mata a ciki.

Gabaki ɗayan su suka yi mutuwar tsaye ganin Baba Sani tsaye, a ɗakin ya ɗora hannu a kansa ya na ƙwala ihu, da kuruwa tamkar yadda jahilan farko suke yi yayin da wata musiba ta afkawa ɗayan su.

Sautin kukan sa yake tafiya tare da bugun zuciyarta,ta rintse idanunta ta na addu'ar kar Allah ya sa mafarkinta ya zama gaskiya!In kuma da gaske ne ya za suyi da rayuwar su a duniya bayan ba mahaifin su?

Sai kawai ta fara ja da baya ta na girgiza kanta tare da nuna mahaifinta, ta na faɗin dai-dai lokacin da Mama ta saka kuka domin ta tabbata ya riga mu gidan gaskiya."A'a bai rasu ba wallahi mafarki ne!Don Allah kar kuce min mafarkina ya zama gaskiya.Mahaifina ya na raye bai mutu ba."

Sai ta ruga za ta fita waje tashin hankalin ta ta ya ya mahaifinta zai mutu ya bar ta da azzalimi!Mutuwar sa na nufin ya yi nasara akan ta zai cika mummunan nufin sa kenan?

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na shidda dan har yanzu shinfiɗa ne har ba'a fara ba.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*




*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA SHIDDA*


Duk yadda Juwairiya ta so ta kwantar da hankalinta akan mutuwar mahaifinta, abin ya ci tura!Da ta tuna mugun nufin Baba Sani sai ta ƙara rikicewa,irin yadda ta nuna na rashin tawakkali ya so ya fara tunzura Mama tun ta na ba ta haƙuri, ta taushe tashin hankalinta domin Juwairiya ta natsu amma ta kasa,sai uhu take ta na furta sunan Baba.

Ganin irin abin da take yi sai Mama ranta ya ɓace matuƙa,ta saki hannun Juwairiya dake son a kyaleta ta fita da gudu kamar wata kamun aljanu tace."Ku kyaleta ta yi duk abin da ta ga dama,ban san baki da tawakkali ba sai yanzu Juwairiya!Na ɗauka saboda ƙarfin imanin ki ni zaki din ga ba ma haƙuri,tare da jawo min aya akan na ɗauki haƙuri domin duk mai rai mamaci ne."

Juwairiya ta duƙa tare da ƙara sakin wani kuka dai-dai lokacin da Baba Sani ya ƙaraso gun ta ya na mata wani kallo,mai kama da tausayi ko akasin haka tare da sausauta murya yace."Ku kyaleta rashin mahaifi abu ne mai ciwo na tausaya miki matuƙa,domin hakan da kika yi sai kika tuna min lokacin da mahaifin mu ya mutu ina kuka mahaifinki Yaya Ahmed shi ya dinga lallashina!"

Sai ya saka kuka ya na faɗin."Allah Sarki!Allah ya jiƙan ka Yaya."Ya nufo Juwairiya dake kuka tamkar ranta zai fita,da nufin zai riƙe ta ya lallasheta.

Da sauri ta matsa ta na wani irin kuka kamar za ta shiɗe,ja da baya take kamar ta ga dodo.Ganin haka sai ya kyaleta a ran sa kuwa murmushin mugunta yake mata.Bayan an gama cuku-cuku aka ba su gawar Baba da har ta fara sandarewa.

Hankalin Juwairiya bai ƙara tashi ba sai da suka dawo gida ta ga inda yake kwanciya,wani ƙarin abin tausayi tun da Ibrahim ya ji mutuwar mahaifinsa ya ɗauke numfashi ko motsi ba ya yi.Lamarin sai ya jagule ma Mama ta rasa in da za ta sa kanta ta ji sanyi,ga wani irin kuka da Juwairiya take yi taƙi ta yi shiru.

Bayan an yi wa Baba sallah aka kai shi gidan gaskiya gidan da ko wane bawa yake da gadon sa domin ba'a wahala gurin mallakar sa.Cikin dare Juwairiya ta na kwance ta kasa bacci!A ranta ji take kamar mahaifinta kashe shi aka yi musamman yadda ta ga Baba Sani bai nuna tashin hankali game da mutuwar sa ba.

Ta na lura da shi har shinkafa ya siyo a dafa ma ƴan zaman makoki,wanda ko mutuwa za su yi ba zai taimaka musu da shi ba.

Kwana ishirin da rasuwar Baba amma har yau sun kasa manta shi a kullum ta ranar duniya sai sun yi kukan rashin sa,musamman Juwairiya da yake sokanar ta duk san da zai fita ya na cewa Allah ya nuna mi shi ranar auren ta,a she ba shi da rabon gani.

A lokacin da Baba ya yi arba'in Juwairiya ta saka ma ran ta za ta yi fito na fito da Baba Sani duk abin da ya shirya a shirye take ita ma.Tun lokacin da Baba ya rasu bai ƙara shiga sabgar ta ba,duk da cewar ba ganin ta yake ba don ba ta fita ko ina.

Ganin ba su da cin yau bare na gobe sannan Mama ita ma kwana

Please Login or Register in order to submit comment