Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi cikin hayyacin sa.

Da sauri Juwairiya ta ruga da gudu don ta saka hijabi ganin ya shigo." Mama ya Baba Sani zai yi haka? Juwairiya ya aiba ta a gaban iyayena. Wai me kuka yi mi shi ya tsane ku?"Ya faɗa yayin da idanunsa suka kawo ruwa.

Cikin jimamin lamarin Mama ta share hawaye ta kalli Mas'ud da ya haɗa kansa da gwiya hawaye na zuba a fuskarsa,sai ya ba ta matuƙar tausayi ta san yadda yake son Juawairiya duk da iyayensa suna da shi amma a haka yake son ta.

Ka yi haƙuri ka san matar mutum kabarin sa Allah be nufi Juwairiya matar ka bace,ka bi zaɓin iyayen ka ni na san duk korar mata masoya da yake in har lokacin ta ya yi bai isa ya hana ba."

" Gaskiya Mama ba zan iya jure rashin Juwairiya ba zan je na sami Baba Sani duk abin da za'a yi sai dai ayi haka kawai ya din ga cusgunawa rayuwarku.Ya katse ta da faɗin hakan ransa a ɓace tare da miƙewa.

" Zo Mas'ud don Allah karka je a yadda ranka yake a ɓace za'ayi ɓatatta,ka san halin shi ba shi da haƙuri ni ce na haifi Juwairiya ina me baka haƙuri ka haƙura da ita,shi kaɗai ne wanda take gani a matsayin na ta in har aka ɓata mishi wa za ta riƙe?Ka yi haƙuri Allah be nufa za ka aure ta ba."

Kawai sai gani ta yi ya saka kuka ya na kallon Juwairiya da ita ma take kuka na tausayin halin da suke ciki." Juwairiya zuciyata za ta shiga cikin wani hali na rashin ki.Ki yi min addu'a Allah ya ba ni mace me irin halin ki,ni na san ke wace ce ko idanunki mutum ya kalla ya san kina da tarbiya da natsuwa.Ina sonki zan haƙura da auren ki saboda umurnin Mama."

Fita ya yi har da gudun sa ya na sharen hawaye Juwairiya ta miƙe da gudu ta shige ɗaki tare da saka kuka.Sam ita ba ta ga dalilin da Mama za ta hana shi ba,ba ta san me Baba Sani yake nufi da ita ba shi ya sa take girmama shi,abin da ya sa taƙi ga ya mata ta san duk ranar fa ta gaya mata ƙudirin sa akan ta, ƙila zuciyarta za ta buga domin abin ya yi muni.

Tun daga wannan ranar ba ta ƙara gani Mas'ud ba ko wayar da ya siya mata Mama ƙwacewa ta yi ta ije,don a yadda ta ga take-taken ta za ta iya kiran shi kuma shi ma haka.Tun ta na saka ran ze dawo har ta cire sai dai ta wahala kafin ta cire son shi a ran ta,sannan da ga baya taci gaba da al'amuranta.

Mariya ta sami miji za ta yi aure anan kusa da layin su za ta yi auren don haka su Juwairiya su ne ƴan mata.Su Juwairiya an sha gayu da lalli an yi kyau sosa,ana ta hidimar biki don ba zama an saci ɗan ɓarawo.
Zaune suke ana hirar ƴan mata Juwairiya ta kalli Mariya yadda ta sha kyau yace."Su amarsu kin ganki kuwa,dama komai munin amarya ranar bikinta sai ta haska."

Fari ta yi musu ta na dariya tace." Ku zauna kuna rungume filo ni dai Allah ya hutashshe ni na shige daga ciki,ku tsaya kuna ruwan ida kwayi kwantai."
Wani irin dundu Juwairiya ta duma mata ta nafaɗin." Ji min ƴar baƙin fata wato fatan da kike mana kenan tunna kin shige daga ciki ko? To in sha Allah muna bayan ki."Sauran ƴan matan suka taso mata ita dai Mariya dariya take musu,sannan tace." Ai ke Juwairiya Baba Sani ya hana ki aure da tuni kin haihu ma.Amma ba komai Allah ya na tare dake lokacin ki ne kawai ba yi ba."
Shiru ta yi sai hawaye yayin da mutanen ɗakin suke ta ba ta baki.
A haka suka sha bikin Mariya aka kaita ɗakin ganin Juwairiya za ta tafi ta kama ta tare da saka kuka.Sai kuma ta ba Juwairiya tausayi ta rungumeta ta na share mata hawaye.

Mariya ta share hawaye tace." Maganar da mukai dake akan aikin nan kije Allah za kiji daɗi kin ga ni na yi aiki da su."Juwairiya tace." Ke ni raba ni da aikin nan don na yisu amma ban ji da daɗi ba."
" Allah ki gwada wannan kin ga yanayin halin da kuke ciki,ga shan maganin Mama dole kina buƙatar kuɗi."
" To zan shawarci Mama duk abin da tace sai na je."Da wannan Juwairiya ta tafi gida cike da kewar ƙawarta wacce ta temaka mata.

Koda ta yi ma Mama magana shiru ta yi zuwa can tace." An ya zan barki kiyi aikin nan nifa tsoro nake yi kina ganin rashin mutuncin da Hajiya Binta ta yi miki,amma tuna kin ce Mariya tace ta na da mutunci sai ki je Allah ya tsare ki."

Numfashi ta saki tace." To bari na gwada mu gani."

Juwairiya ta fara aikin cikin jin daɗi ga karatu da take samu ake yi wa yaran lesson da islamiya matar ma ba ruwanta.

Watan ta biyu a gidan ranar ta kammal aikin ta za ta tafi matar tace." Don Allah Juwairiya ki tsaya zamu je gidan biki ni da yarana,zuwa yamma zamu dawo sai ki tafi in kuma na yi dare zan kaiki a mota."

Duk a ranta ba ta so ba amma sai ta amsa da." To." Ta koma ta zauna yayin da ita kuma ta shirya da yaranta suka fita.

Tun da suka tafi har aka kira sallah ba ta dawo ba,ranta ya fara ɓaci don ba ta son ta yi dare kar Baba Sani ya dawo ya kuma ƙara mata wani sharrin.

Jin ƙarar mota sai ta yi maza ta leƙa ta windo ta na tunanin ita ce,sai dai cikin takaici ta koma ta zauna ganin mijinta ne ya dawo.
Ya shigo da sallama ya amsa ya na kallonta." Juwairiya har yanzu ba ki tafi ba?"Ya tambayeta ya na kallonta." Eh tunna ka dawo bari na tafi "
" No ki kira ta nima ƙara fita zan yi."
Don takaici ko amsa mishi ba ta yi ba to me ya dawo da shi koma wa ta yi ta zauna.

Ya shiga cikin ɗakin sa mintina biyar ya fito sai kawai Juwairiya taga ya yi kanta gadan-gadan! Da sauri ta miƙe tare da saka salati dai-dai lokacin da ya fisgota ya haɗa ta da jikin sa da ƙarfi.

Kasancewar shi namiji me jiki da ƙarfi ya yi nasarar kayar da ita ƙasa tare da yi mata rumfa,yayin da dabbe ya kaure ko kaɗan ba ta yi tsammanin ya na da wannan halin ba.Kuka ta saka ta na rokon shi,amma bai kula ta ba yaci gaba da ƙoƙarin ida nufin shi.

" Inna lillahi Faruk!Me zan gani dama amanata kuke ci?"Ta furta cikin ƙaraji! yayin da ta yo kan juwairiya ta hau ta da bugu.

Juwairiya ta yi kuka ta yi ihu ji take kamar numfashinta zai fita domin kanta ta hau ga ta da ƙiba,da ƙyar ya samu ya ɓamɓare Juwairiya ta samu ta gudu.

Da ƙyar ta samu ta isa gida ta na kuka a ranar ta rantse ba za ta ƙara yin aiki ba,ko da mutuwa za su yi yadda ta shigo Mama ta tsorata.

Bayan ta yi mata bayani tana kuka Mama sai da ta zubar mata da hawaye ganin halin da take ciki.A ƙalla sai da ta yi sati ta na jinyar jikinta don har sai da ta kwanta ciwo.

Haka rayuwa take tafiya musu yau baƙi gobe tsummma ga ciwon Mama ya yi tsanani.Wani abin ƙarin tashin hankali Ibrahim da dama can ba lafiyayye bane,saboda sikila ne shi jikin sa da ya yi sauki amma a cikin kwana biyun nan jikin ya tashi.

Ciwon shi sai yake son ya danne na Mama amma duk wanda ya ganta ya san ta na cikin tsananin ciwo.Ga kuma Baba Sani da ya sanar da Juwairiya ya yi mata miji wato Alhaji Tanimu.

A ranar da Baba Sani ya gaya mata sumewa ƙau ta yi don ya tabbata Baba Sani ba ya ƙaunarta,don ita da ya aura mata shi gara ta zauna ba aure ko ace mutuwa ta yi.

Waye a faɗin garin be san Alhaji Tanimu ba wanda ya mai da mace tamkar rigar sawan shi.Mutum ne mara addini ga shi kamar wani hor.Kusan duk shekara yake sakin mace ya ƙara aure bayan ya tabbatar sun sami ciki,don baya son haihuwa a tunanin ta shi kan shi be san iya yawan yaran shi ba,duk da wasu ya na ba ma iyayensu mata kyauta wasu kuma ya kai su almajiranci.

Sannan an sha kama shi ƴara ƙanana ya na musu ya lalata musu rayuwa irin mutumin da Baba Sani yake son ya zama mijinta kenan.Ai Juwairiya ƙaramin hauka ta yi don gara yace ta shiga duniya.

Shiko Alhaji Tanimu se ɗinkirama Baba Sani kuɗi yake yi hankalinsa kwance ganin zai mallaki wannnan zuƙeƙiyar,shi ya sa be damu ba ko sanda ya zo zance taƙi fitowa tallar ta fa aka kawo mishi har gida.

Rayuwa a wannan karan tafi yi wa su Juwairiya illah ga aba abinci sannan dukkanin su ba lafiya,ga Baba Sani da yake ta shirye-shiryen bikin ta don har an kawo kayan sa rana watan gobe biki.

Mama ta shiga tashin hankalin ciwonta ya ninku ga yunwa har takai sai su wuni ba su saka komai a bakin su ba.
Juwairiya ta tsara ma kanta ta gudu amma in ta ga halin da su Mama suke ciki sai ta ji kamar ta kashe kanta ta huta,ita kanta ba lafiya take da shi ba don ta na ganin har tafi su Mama jigatuwa saboda zuciyarta da take ji kamar za ta fashe.

Ganin yunwa zai kashe su sannan duk kuɗin da Baba Sani yake karɓa bai ta ba ba su koda na sabulu ba,ta je gurin Mariya ta ara mata naira dubu biyu ta fara jarin gyada.Da wannan suke samun abinci.

*******
Zaune yake cikin damuwa sai kuma ya miƙe don a yau jin sa yake duk shawarar da amininsa ya ba shi zai iya ɗauka saboda halin da yake ciki.Makullin motar shi ya ɗauka ya nufi gidan A.k.
Sai dai cikin rashin sa'a ba ya nan don haka bayan sun gaisa ya fice daga gidan ya samu wani guri mara hayaniya ya tsaya,tare da ciro waya ya kira A.k.

Ba'a fi minti goma ba sai ga A.k akan mashin ya sauka ya buɗe gaban motar ya shiga ya na share zufa."Am sorry aboki motar da ka siya min na kai ta service ba'a gama ba kan dole na baro motar na hawo mashin.Are you under the weather?"Ya tambayi aminnin nasa ganin yanayin sa.

Yace ya na kallonsa bai tanka ba illa ajiyar zuciya da ya yi ya kauda kansa gefe guda,ganin yadda aminin na sa yake ya san yauma ba lafiya to ko dame yazo oho don ya san dai zancen.
Suka ɗan yi shiru ba tare sun ce uffan ba na tsawon lokaci sannan A.k ya katse shirun da cewa." Lafiya na gan ka wani iri in ce ba mutuniyar bace ta haɗa maka zafi."

"Akan maganar da na nemi shawarar ka yau ma na ƙara bijiro maka da ita.I really need your advise pleese help me out."A.k ya kalle shi yadda idanunsa suka kaɗa suk yi ja ga mamakin sa sai ya ga hawaye ya na sauka da ga ƙuncinsa.
Ya kama hannunsa ya haɗa da nasa ya riƙe sosai ya na kallonsa ya ci ga ba da cewa."I know my wife she is a woman of raging jealousy.Bazan iya haɗa ta da wata mace ba kuma ba yan haka na yi mata alƙawari,amma ina jin zafin rashin yaro da ba ni da shi wanda hakan in ban ɗauki mataki ba zai iya taɓa lafiya ta,domin a yanzu ya kai matsayin da ba na iya bacci.

Tun da ya fara magana A.m ya yi shiru ya na kallon sa a ransa tunani yake to ko amininasa ya ci kai ne ko kuma rashin haihuwar ya taɓa tunanin sa, kamar yadda yace shi dai ya san ta aure ake samun haihuwa ya ba, shi shawara yaƙi bi saboda wani alƙawari na shi na banza to amma bari ya ji me yake tafe da shi.

Ganin ya yi shiru ya dafa kafaɗarsa ya na cewa."Try to be patient ka san zuriya kake buƙata kuma dole a aure za ka same shi,ba zaka so ka sami ɗanka ta zina ba wanda na san ba halinka bane,amma ni banga dalilin da zai sa kaƙi ƙara aure ba bai ita ta ɓata mahaifinta da kanta ba?"Ya ɗan faɗa da zafi kuma da tsigar tambaya.
" Haka ne." Ya ba shi amsa sannan ya ci gaba da cewa." Duk akai na ne ta samu wannan matsalar gaskiya i can't make up my mind ko zan iya cin amanarta."

Ƙarin takaici maganganunsa suka ƙara ba shi gani yake ba shi da tsayuwa a gidan sa,amma shi bai ga yadda matar shi zai ta da hankalin shi ba,don kawai zai ƙara aure kuma duk laifin tane.
Ya kaɗa kafaɗunsa yace."It is up to you ni dai na gama baka shawara."Yace amma sai kuma ya ga hankalin aminin nasa ba shi a gurinsa wataƙila ma be san me yace ba.

A hankali ya bi gurin da yake kallo shima Juwairiya ce da tiren gyaɗa a kanta da ga ganinta ka san ta na cikin wani hali, kusan ma ta na tafe ta na share hawaye saboda har Alhaji Tanimu ya kawo kayan auren ta na jin gara ta haƙura ta aure shi,wataƙila shi Allah ya tsara ya zamo mijinta ta san bawa ba ya wuce abin da Allah ya tsara mata,sai dai yanayin halin da Mama da Ibrahim suke ciki ya sa ta zagaya wa da gyaɗar da yau ba ciniki ta haɗa da kuɗin da Mariya ta ba ta ta kai su asibiti.

A.m da ya zuba mata ido ya na kallonta bai taɓa ganin mace me sanyi da wani irin shauki a tare da ita ba sau,haka kawai ya ji ta kwanta mishi a rai ba wai son ya na son ta ba irin zai iya magana da ita har ya ba ta lokaci su yi wasa da dariya,kuma ya nemi shawarar ta kuma zai iya yin komai don ta yi farin ciki,zai iya cewa yau ne rana ta farko da ya ga wata mace bayan Zainab har ya na jin zai iya mata magana.

Wato in ya fahimci zuciyar shi ƙawa yake son ya mai da ita ko ƙanwa." To amma duk tsanar talaka da na yi sai ace na yi ƙawa da ƴar talaka kuma ƙasƙantacciya ƴar talla kai an ya da wuya.".
Yace a zuciyar a cikin zuciyarsa ya na me ƙoƙarin kauda idanun sa daga gareta don jin hakan bai dace ba ace duk matsayin shi.Sai-dai idanunsa sun kasa ɗauke kan su daga kallonta ya na ƙara zaƙulo kyawunta.

Ta na tafe cike da damuwa har tazo ta gaban su za ta wuce." Me gyaɗa." Kalmar da bakinsa ya furta ba tare da ya ba shi umurni ko tunanin hakan ba.

Juwairiya ta ji wani irin sansanyar murya mai kama da sarewa ta kira ta ta na son ta juya amma sai ta daƙile kanta da juyawar,don ƙila in ta ga mamallakin wannan muryar ba ta san halin da za ta shiga ba sai kawai ta ci gaba da tafiya yayin da aranta take addu'ar Allah ya sa karya ƙara kiranta, don ta san in ya ƙara kiran ta ba za ta iya tursasa zuciyar ta da ƙin juyawa ba.
A.m ransa ya matuƙar ɓaci ƙazama da ita ta na talaka zai kira ta taƙi waigowa ya so yaje ya yi watsi da kayan tallar,ya ga uban wa take taƙama da shi taƙi amsa kiransa amma da ya yi tunanin ko kurma ce sai ƙara kiran ta a karo na biyu.
Cak! ta tsaya amma ba ta wai go ba ta na addu'a a cikin ranta yayin da idanuwanta suka zaƙu da suga wannan mamallakin muryar.A hankali ta tako ta iso gun motar su ta tsaya ta kasa magana kuma ta kasa ɗaga ido ta kalle shi.
Kusan minti goma ta na tsaye ba tare da ya kalleta ba me ya gani oho ganin ita ma ba ta da ninyar ta yi mishi magana kuma ba ta tafi ba A.k dai ya na zaune ya na kallon ikon Allah.

A.m ya buɗe motar da nufin ya yi mata wulaƙanci dai-dai lokacin da idanuwan su suka tsarƙe da na juna.
Kyansa yanayin jikinsa idanuwansa da yadda yake kallonta suka ruɗa ta ta yi kamar za ta faɗi, amma sai ta dafa jikin motar sa ta na kallon shi cikin wani irin shauki,lokaci guda ta ji abu me kama da guduma ya sauka akanta! Yayin da wani irin shokin na soyaryarsa suka dinga ɗana mata son shi a cikin ranta,har ta ji za ta iya mutuwa in ba ta same shi ba.

Idanun su da suka tsarƙe da juna sai ya tsinci kansa da kasa mata rashin mutuncin da ya yi ninya a yatsine yace."Nawa-nawa gyaɗar."
Ta zuba mishi idanunta sai kuma ta janye ta lumshe su tare da kauda ganin ta gare shi ahankali da sanyaryar murya tace.Hamsin gwagwani ɗaya."
Ya ɗan ƙura mata ido haka kawai kyawunta da muryarta yake ruɗan shi a kanta."Duka buhun nake so nawa."Yace tare da barin kallonta lokacin da ta ɗora idanunta akan sa.
Zare ido ta yi " kwai yawa fa kusan na dubu uku da ɗari biyar ne.Tace mishi hakan sai ya burge shi ya tsinci kansa da yin murmushi.
"Ok bari in ci Allah ya sa da daɗi."Da sauri ta saka hannunta da baya rabo da lalli ta miƙa mishi ta na faɗin." A kwai daɗi kaci kaji."
Yabi hannunta da kallo ya karɓi gyaɗar ya ɓare tare da taunawa,lumshe idanunsa ya yi yace da ita."Gaskiya a kwai daɗi zuba min a leda sauran kiyi sadaka da shi."
Da sauri ta zuba mishi sannan ta kalli gefen A k da ya yi mutuwar zaune saboda tun tarihin rayuwarsa da A.m yau ce rana ta farko da ya siyi abu a gurin masu talla,sai ya yi lakato ya na kallon A.m da ke cin gyaɗa har ya na faɗin ta ƙara mishi ya yi daɗi.
" Yayana kai fa ba ya cine."Ta kalle shi sai kuma ta mai da maganar da tsigar tambaya ta na kallon A.m,kaɗa kafaɗunsa ya yi ya na kallon shi ya ma manta da shi yace."Ba ya ci."
Juwairiya tace " Ka tambaye shi ne?"Sai kuma ta kalli A.k tace."Wai haka Yayana?"
"Yes Am ok."Yace da ita ya na kallonta.
Zuba gyaɗar ta yi ta miƙa mishi ta na faɗin."Kaci a kwai daɗi."Ya ƙarɓa tare da faɗin."Thanks sis."
A.m ya zaro kuɗi da yawa ya miƙa mata. Gashi sis ki cire kuɗin ki sauran ki ƙara jari."Zare kuɗin ta ta yi tace."Siyan da ka yi na gode."
Hakan sa ya yi matuƙar birge shi ya na ta kallonta har ta yi nisa ya leƙo ta cikin murfin motar yace." Manene sunan ki."
Ya ɗan ɗaga muryarsa yadda za ta ji don ta yi nisa,waigowa ta yi ta kalle shi tare da sakar masa murmushi ta tabbata wannan kyakykywa gayen ya yi mata sata mafi girman abu a rayuwarta,wanda ta san ba zai dawo mata da shi ba kawai za ta ci gaba da renon giɓin rashin abin da ya ɗauke mata har iya tsawon rayuwarta!
" Sunana Juwairiya Ahmad."Tace tare da ƙoƙarin ɓullewa a ranta ba ta son ta ƙara haɗuwa da shi don ta san babban goro sai magogin ƙarfe.
A hankali ya kwantar da kan shi akan jikin kujerar da ya saukar da kansa ya na murmushi ya furta.Juwairaaah! Da wata irin murya ya ja sunan ya yi mishi wasali sosai." Ta na da kyau haka kawai sai na ji ta burge ni."

Ba tare da wani shakku ba A m yace."Bayan kyau a kwai hankali da natsuwa .Rayuwarta a kwai tarin tausayi ka aureta kawai ta haifa maka yara.

Da sauri A.m ya buɗe idonsa ya ɗora akansa wani irin ɓacin rai da takaici ta ya ya zai haɗa shi da ita ƴar talaka me talla ita yake nufin ta haifa mi shi yara!Ina imposible wasa yake yi.

Ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya figi motar tamkar zai zubar da su,A.k dai bai ce komai ba koma kashe su zai yi, ya yi amma iyakan shawarar da zai iya ba shi kenan kuma in dai bai ɗauka ba to ba zai ƙara kula shi akan damuwar sa.

Ƙofar gidansa ya ije shi ba tare da yace komai ba bayan ya fito daga motar ya leƙa ta tagar motar yace.Allah ya bamu alkhairi ka yi tunani shawarar da aka yanke ina sauraranka."
Ba tare da ya tanka mishi ba ya ja motar a guje dariya ya saki tare da girgiza kan shi ya shige gidan sa.
A.m da ya koma gida sai yaji wani tashin hankali game da maganar da ya yi mishi,amma ya kasa amincewa wanka ya yi ya kwanta don baya so ya yi tunani akan maganar,sai dai bayan baccin ya kwashe shi sai ya yi mafarkin ga Juwairiya ta na kuka ta miƙo mishi yara guda biyu shi kuma ya na cikin ƙaton rami ya fito da ninyar ya ƙarɓa sai ta ɓace ta na wani irin ihu,ihun da ya fargar da shi ya miƙe a zabur! Ya na salati don har yanzu bai daina jin sautin kukan a cikin kunninsa ba.

" Ita za ta haifa min yara amafarkin da na gani kenan amma a kwai matsala.Tabbas matsala babba don ko ni auren ta zan yi cikin sirri ba tare da sanin kowa ba wato auren wucin gadi,na ƴanta mata rayuwa na ba ta jin daɗi amma mu yi aure na tsawon shekara ɗaya tazo a matsayin me aikin gidana bayan ta samu ciki, na ɗauke ta na kai ta wani gurin in ta haihu na biyata na karbi yarona na kawoma matata masoyiya Zainab."

Tofa masu karatu kun ji A.m abin da yake so.
*Hakan zai yiwu?
*Ta ya ya A.k zai karɓi lamarin shin zai bashi goyan baya kuwa?
*Wani irin aure yake son yi?
*Shin ya zai yi da Baba Sani da ba shi da buri sai dai rayuwar Juwairiya ta wulaƙanta,zai amince mutum me daraja da matsayi ya aureta?
*In ma ya amince taya za'ai Juwairiya ta yi rayuwa a gidansa a ɓoye a matsayin matarsa amma kuma azahiri ƴar aiki?
*Ta ya ya za ayi auren sirri ba tare da sanin Mama ba?
Ku dai biyo ni a shafi na gaba"SAKACINA KO HALIN MAZA"
NAGA RUWAN COMMENT IN ANA SO NA CI GABA.😘😘😘😘😉😉TAKU JAMILA LAWAL ZANGO💔💔💔💔❤❤




Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G0J8rS0cxTtCCC38iwA3B9
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA GOMA SHA BIYU*



Juwairiya ta na ɓacewa ganin sa ta tsaya ta tsuguna tare da sakin wani gigitaccen kuka sosai wanda ba ta san dalilin yin hakan ba,sai bayan tasha kuka sosai zuciyarta ta fara jera mata tarin tambayoyi."

Me ya sa nake kuka ga mutumim da na san ba zan taɓa samun shi a cikin rayuwata,na sa ni cewar dariya ba so ba ne.! Maganar da ya yi min ba ya nufin zai iya sona a cikin ransa,sannan na tabbata ya yi aure har ma da iyali saboda kamalar shi ta nuna na cikakken mutum me iyali."

Ta tallabe fuskarta da hannunta wani sashi na gefen zuciyarta,ya na ƙara jaddada mata da cewar ko da ya nuna ya na sonta Baba Sani ba zai taɓa ba shi auren ta ba,mutane wanda ba su kai shi matsayi ba sun nemi auren ta amma ya hana bare shi da ga ganinsa kasan ya jiƙu da nera,da duk wani ababen more rayuwa.

Sai ta share hawayenta tare da ɗaukar tiren jiri na jiri ya na iban ta ta na ji kamar ta haɗiye zuciya ta mutu in ta tuna wannan tsohon ze mallaki jikinta.

Gizo-gizon hoton sa

Please Login or Register in order to submit comment