Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sani ta zan yi komai ba."

Ya numfasa ya na kallon ta yadda ta yi zuru ta na kallon shi,yayin da zuciyarta ta ci gaba da bugu cikin tashin hankali.
"kamar yadda na gaya miki haka za ki yi don haka ko kallona kar ki yi in dai ta na kusa da ni.Kasancewarta ba mai zaman gida ba ne kinga haka zai bamu damar aurenmu ya tafi cikin sirri."

Ya ce da ita sannan ya fice ya barta a tsaye tamkar gunki sai da ta ɗauki tsawon lokaci sannan ta yi zaman ƴan bori a ƙasa tare da fashewa da kuka.
" Don Allah karfa ku yi min ƙarya ku dawo fa in ba haka ba wallahi sai na nemo ku duk in da kuke don ba zan ga samu na ga rashi ba.

Motar su na ɓacewa ya ruga da gudu ya shige ɗakinsa alokacin Juwairiya har ta miƙe ta share hawayenta za ta fice." Ƴar albarka Juwairiya zo mai ya baki."

Sai kuma ya hangi damin kuɗin da ko ta kan shi ba ta bi ba, ai da sauri ya dafe ya na washe baki sannan ya miƙa mata dubu biyar ya ce." Gashi maza ki tafi Juwairiya ya gaya miki komai ko?Ai Allah ya tarfa ma garin ki nono kin huta da auren wannan mutumin,dama ɗan iskan tun da ya ga na ba shi auren ki ya dai na bani komai,duk da na yi baƙin ciki amma ko ba komai ai na samu ta sanadin ki rayuwata za ta shiga cikin jerin masu da shi."

Juwairiya ba ta ce komai ba har ta kai ƙofa za ta fita, sai kuma ta dawo ta ce." Ni fa ba zan aure shi ba haba Baba ka ji tausayina mana!Wallahi in..."

"Rufe min baki banza shashasha!Don ma kin samu zai aure ki wallahi da bai zuba uban kuɗin nan ba, to ko megadin gidansa yake son ki yi masa ba zan bari ba,ai ke gaba ta kai ki ko banza a shekara ɗaya zaki rayu cikin daula,ko banza za'a sha zaƙi da maiƙo a rabu da tuwo wanda shima ba kullum ake samu ba."

Da sauri ta fice jin maganar da yake mata wanda duk cin fuska ce.

Juwairiya ta shiga cikin tsananin hankali tun lokacin da ta fito da ga ɗakin Baba Sani ta kife kanta ta na wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare.

Yayin da tausayin kanta ya rufe ta ganin mutumin da take matuƙar so ya zo neman ta akan auren kwangila."Yanzu inna auresa shekara ɗaya za mu yi? Shima tsakanin mu tamkar mage da ɓera tunna matarsa ta yi katanga a tsakanin."

Abin da take ta faɗi a ranta kenan sai kuma ta share hawayen da damuwa cike a zuciyarta,don ta rasa yadda za ta kwatanta wannan auren da yake son su yi,amma a ranta ta ƙudira koma me zai faru sai dai ya faru don ba za ta aure shi ba,ai gara ya barta a cikin tsananin talauci saboda in talaucin bai kashe ta ba,tsananin son da take mishi da kishin matarsa zai kai ta lahira!

Ko da ta isa asibiti ba yan ta gama girki abin mamaki sai ta ga Baba Sani zaune a can,ya dage sai zuba ruwan surutu yake yi tamkar wani aku.

Sai Juwairiya ta kasa shiga ta tsaya ta na kallon shi da mamaki ganin yadda yake ta magana har da dariya ga uban leda da ya siyo musu abu.

Mama shiru ta yi ta na kallon shi da mamaki."Oh ikon Allah duniya juyi-juyi!" Abin da ta ce kenan cikin tsananin mamakin sa.

"Ƙaraso mana Juwairiya kin ga har na riga ki ai daga gurin aiki sai na taho,ban san kina gida ba."

A sanyaye ta shigo tare da ije abincin dai-dai lokacin da Baba Sani ya tashi tare da yi musu sallama ya tafi.

Da sauri Juwairiya ta bi bayan sa ya na ƙoƙarin shiga motar sa ta riƙe murfin motar idanunta na zubar hawaye " Ba zan aure shi ba gara ya barni a halin da muke ciki,amma ba zan yi aure ba wanda mahaifiyata ma ba'a son ta sani!Tun wuri ka mai da masa da kuɗin sa ni zuciyata ba irin naka ba ne!Na san mutuncina ai talauci ba hauka ba ne "

Kau ya gaura mata mari " Baki da hankali kina wasa da ni ke baki san halina,ni murucin kan dutse ne! In har kika ce ba za ki yi wannan auren ba,kin ji na rantse miki Juwairiya zan iya kashe ki har da mahaifiyar ki.Don haka in baki bi umurnina ba ki kuka da kanki."

Ya ja motar sa ya barta a nan tsaye cikin tashin hankali sai kawai ta rushe da kuka,sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi shuru ta wanke fuskarta ta shiga cikin ɗakin da Mama suke.

" Ikon Allah abin duniya ba ya ƙarewa kin ga abin mamaki ko.Ai addu'a takobin mumuni ne."
Juwairiya ta ce."Umh Mama."Sannan ta ɗauki filet ta zuba mata abinci.
"Juwairiya bayan fitar ki likita ya zo ya ce in dawo ki je ki same shi,sannan ya ba da takadda kamar na magani ne."

Ta ce cikin damuwa da murya ƙasa-ƙasa kai da ga ji ka san ta na cikin jinya mai tsanani.
" To Mama bari na je na same shi."
Ta miƙa mata abincin sannan ta fita zuwa ofishin likitan.
"Ok zauna"

Ya ce da ita bayan ta ƙwanƙwasa ta shigo a hankali ta zauna cikin tsoro-tsoro don ba ta san dalilin da likitan ya kira ta ba.

Ga sakamakon gwajin da muka yi ma mahaifiyar ki nan gaskiya ta na cikin matsala ya kama ta a canza mata asibiti,saboda zuciyar ta ta kumbura dole a yi mata aiki.
Da sauri Juwairiya ta miƙe tare da zare idanun ta jin abin da likitan ya faɗa." Na shga uku Allah ka kawo min ɗauki!Mama za'a yi wa aiki!"

Sai hawaye shar-shar a fuskarta ta koma ta zauna kamar yadda likitan ya umurce ta ganin ta tada hankalinta.

" Ki yi haƙuri! Jarrabawa ce amma kar ki yadda ta ji lalurar da take da shi wannan dalilin ya sa na so namiji ya zo na gaya mishi,amma sai ta nuna ke ɗin dai zan gaya ma wa."

Da sauri ta miƙe tare da ficewa daga ofishin har ta kai ƙofar ɗakin da Mama ke kwance, sai kuma ta ja da baya ta tsaya kamar wata zararra!Tuna likita ya ce kar ta gaya ma Mama komawa ta yi wani guri ta na son ta yi kukan amma ba hawaye sai tuƙuƙi da zuciyarta take yi mata.

Ta ɗauki tsawon lokaci sannan ta koma cikin ɗakin.Da daddare Juwairiya ta kasa bacci sai juye-juye take,abin duniya ya haɗu ya yi mata yawa ji take kamar ta ɓace a cikin duniyar.

Kwana biyu kuma sai Ibrahim ya fara ciwon ƙafa wanda in ya na yi yake fita cikin hayyacin sa,don har tsuma yake na tsawon lokaci bai farfaɗo ba.Abin duniya ya yi mata yawa ga tunanin A.m da yake son ta baƙunci kabarin ta kafin mutuwarta,duk ta yi fari ta rame kamar wacce ba ta da jini a jikinta sai ƙashi da ya zama ado a jikin ta.

Zaune take a gefen Mama ta zura mata ido ta na tausayin halin da suke ciki,don ko wannen su da jinyar da yake yi.Hannu ta sa ta yarfe zufan dake goshin ta,wanda yake tsatstsafo mata duk sanda ta tuna da A.m.
" Inna lillahi."
Ta ce tare da miƙewa ta tsaya bakin windo sai hawaye." Wai dama haka ciwon so yake?Allah na roƙe ka ka cire min soyayyar son maso wani a cikin rayuwata,yayin da nake tsananin son sa shi haɗuwar mu ya zama dama a gare shi ya faranta ma masoyiyar sa rai.

Likitan ne ya yi sallama ya shigo wanda ya saka Juwairiya ta juyo da hawayen dake zuba a fuskarta,ya tausaya mata sosai amma sai ya miƙa mata takadda ya ce." Ga shi Juwairiya an baku sallama duk da jikin mahaifiyar ki bai warke ba,amma baku da kuɗi kuma mai asibitin ya na buƙatar kuɗi."

Juwairiya da ta ji ta daskare amma sai ta kai hannu ta ƙarɓa jikinta a sanyaye ba tare da tace mishi komai ba,ita zuwa yanzu hawaye sun ƙare da ga fuskarta sai wani azaban raɗaɗin baƙin ciki da take kurɓar ruwan sa mara daɗi a cikin zuciyarta wanda yafi na guba illah.

Sai ta fara haɗa kaya dai-dai lokacin da likitan ya fice daga cikin ɗakin.

Kwana biyu da dawowar su jikin Mama ya rikice Juwairiya a daren ranar ta ɗauka ba za ta kwana ba,da safe ta sami Baba Sani ta na kuka ya taimaka ma Mama da ranta yake tsakanin mutuwa da rayuwa.

"Kin ji na rantse miki Juwairiya ko mutuwa za ta yi sai dai ta yi matuƙar ba za ki amince da auren A.m ba.Ya faɗa ya na zare ido sannan ya ɗora da ce wa."Ai dama ba son ta kike ba in banda ƙashin tsiya ne dake Juwairiya irin A.m ko auren kwana ɗaya yace ki yi,ai na ɗauka jikinki na rawa za ki amince."

Haka ta dawo jiki a sanyaye ta zauna ta tare da zuba ma Mama ido ta na hawaye.Sai ta ji ɗakin ya ɗauka da wani irin abu kamar na vibration,da sauri ta miƙe don ita tsoro ta ji sai da ga baya ta koma ta zauna tuna wa da ta yi A.m ya ba ta waya,wace tun ranar ta ije ta amma abin mamaki cajin bai ƙare ba.

Sau uku ana kira amma ba ta tashi ba ta na kallon Mama dake bancin wahala,sakamakon rashin baccin da ba ta samu ba daren jiya,yayin da kiran ya ci gaba da shigo wa sai hakan ya ƙular da Juwairiya ta miƙe da sauri ganin Mama ta fara mutsu-mutsu za ta farka.

Waje ta yi da wayar ta kai hannu da nufin ta kashe don ta tabbata shi yake kiranta sai kuma ta fasa tuna da halin Mama take ciki,ta saki nauyayyar ajiyar zuciya.

Wata gefe na zuciyar ta ta bijiro mata da ta amince da auren A.m don ta ceci rayuwar mahaifiyarta duk da ta san ba ta yi ba Mama adalci ba,amma halin da suke ciki zai saka ta amince ba tare da ta yi tunanin komai ba.

Sannan ko ba komai ai auren sa ya yi mata katanga da auren tsoho a lokacin da suka rabu,ta na matsayin bazawara ba wanda ya isa ya yi mata karan tsaye a rayuwarta.

Sai dai da ta tuna tsananin son shi da take da kuma ɗanta da za ta ba ma matarsa,wacce take jin yanzu bayan mutuwarta babu abin da ta tsana fiye da ita.

Ta na wannan tunanin ne ta ji muryarsa ta daki dodon kunninta ya na faɗin." Hello Juwairaah ki na ji na?"

Bata san ta danna wayar ba ashe ta amsa kiran da sauri ta kanga wayar a kunninta ba tare da ta yi shirin hakan ba,jin daddaɗar muryarsa da ya saka ta manta komai ta ji kamar ta zuƙo shi ta wayar saboda wani irin ƙaiƙayi na son ganin sa da idanuwanta suke mata.
" Ina jinka."
Ta ce jin ya maimaita maganar har sau uku.Ba tare da ya yi wata doguwar magana ba ya ce." Ya maganar mu kin yanke shawara? Saboda zan yi tafi zuwa India kin ga sai na gama komai kafin na tafi."

A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta sauke cikin baƙin cikin daina magana da ya yi,saboda jin muryarsa take kamar ana busa mata sarewa.

Sai kuma ta fara sheshsheƙar kuka ta buɗe baki za ta yi magana sai kuma ta fasa tare da kecewa da kuka.
" Oh my God! Ni fa ba na son mace mai saurin kuka haka kawai ki dinga kuka,in dai kuka za ki dinga min zamu tsamu matsala dake."
Ya numfasa ko za ta ce wani abu sai ya ji ta yi shiru sai ɗan sautin kukan dake tashi a ajiyar zuciyar da take yi.
" Na amince!"

Ta furta tare da ƙara sakin sabon kukan duk da gargaɗin da ya yi mata ya shiga jikinta don umurnin sa kamar yankan wuƙa ne,sai da ta kasa hana kuka a ranta ta na tunanin yadda za su yi a tsakanin su ba a lokacin da aka ɗaura auren.

Ta ƙara buɗe bakinta da ƙyar ta ce " Don Allah ka kawo ma mahaifiyata ɗauki ta na cikin wani hali diɓ!."Ta kashe wayar tare da tsugunawa a gurin ta na jin wani hali wanda duk ƙwaƙwana na kasa gane halin da take ciki domin ita kaɗai ta san halin raɗaɗin da take ciki.

A.m ya ji wani sanyi a zuciyarsa waya ya ɗauka ya kira A.k nan take ya fara shirye-shiryen yi ma Mama biza.

A lokacin da aka fita da Mama ba ta san halin da take ciki ba Juwairiya har ta cire ran zai kawo ma Mama agaji,saboda da ta ga kwana uku da maganar su bai kira ta ba wanda hankalinta ya tashi sosai.

A ranar na uku Baba Sani ya sanar ma Juwairiya su fara shiri har sujjada shukuriya sai da ta yi gani take kamar Mama mutuwa za ta yi.


Ba ƙaramin mamaki ta ji ba lokacin da Baba Sani yake gaya mata har da Ibrahim za'ayi tafiyar,zuciyarta ta haƙiƙance mata Allah ya kawo mata A.m a cikin rayuwarta don ya fitar da su halin da take ciki,sai dai in ta tuna son shi da ya mamaye mata zuciya ta na jin tausayin ranar da za su rabu wataƙila shine sanadin ta.


Su Juwairiya na ƙasar waje A.m da A.k suka shirya zuwa gidan Daddy domin su shawo kansa ya amince ya ƙarɓar mishi auren Juwairiya.

Gabansa ne yake faɗi ras! Har suka isa gidan maigadi ya wangale musu get,A.k da shi yake tuƙi ya shigar da motan.
Daddy ya na falonsa ya na ganin A.m ya tashi ya rungume shi tare da jawo A.m suka zauna a kujera me cin mutum biyu." Na yi kewar ka son ya kuka dawo? Wannan mutumim ya kirani don Allah son ka rage zuciya ka san harkan kasuwanci sai an yi haƙuri."

Sumar kan shi ya shafa tare da sakin murmushi duk da mutumim ya ɓata mishi rai matuƙa,amma yanzu ba shi ya kawo su ba.

Bayan sun ci abinci wanda A.m bai so ya ci ba amma Daddy ya matsa mishi,duk yadda yake da hope a kan sa sai gashi ya kasa sanar mishi ya na ta tunanin yadda zai fara magana.
A.k kuma ya yi banza da shi ya na ta kwasar girki shi ko tun da ya kai loma biyu wanda ya ci ne saboda takurawar da da Daddy ya yi mishi.

" Am Daddy don Alah a kwai abin da yake tafe damu,amma muna roƙon ka ka fahimci abin da ya kawo mu don Allah Daddy."
Ya yi ƙundumbalar faɗi da fuskar tausayi ya na hararar A k da ya manta da shi ya na ta aikawa cikin sa bayani,kamar da ma abin da ya kawo su kenan.
" Ina jin ka son dama har a kwai abin da za ka kasa sanar da ni?"
" Aure nake ne ma amma a kwai ƴar matsala."Ya ce ya na kallon Daddy ya ga yadda zai karɓi zancen.
Daddy kuwa tsananin tausayin shi ya kama shi da ya tuna shi ma haka ya din ga aure-aure don ya samu ɗa,amma kuma shi ne ba ya haihuwa ba matarsa ba me ya sa yake son ya ƙara aure.
" Son mata biyu anya za ka iya zama da su kai da baka da haƙuri,ɗayar ma ya ka cika bare ka tara fiye da ita.Amma tunna zaka iya faɗa min ƴar wacece kuma su waye ahalin ta?"

Wannan karan A.k ne ya ce." Ba ƴar kowa ba ce asalima mahaifinta ya mutu ƙanin mahaifin su yake riƙe da su."
" Son ƴar talaka matsiyata kake son aure ka manta Zainab ko ƴar wace ce ita?"
Ya miƙe tsaye tare da furta hakan ya na mamakin A.m da ya canza duk yadda yake nuna tsanar talaka sai ga shi ya jajibo auren ta.
Ya shafa kansa ya na faɗin." Karka damu Daddy auren nawa na wucin gadi ne,sannan saboda ita Zainab ɗin zan ƙara aure."Take ya kwashe komai ya gaya masa.

Sosai yake kallon sa ya na mamakin wai Zainab ce ba ta haihuwa amma ya ce shi ne baya haihuwa.Lai-lai ya tabbata ya na shaye- shaye.
" Ka yaudare mu Abdurrahman an ya ka yi m kanka adalci ka n ganin in kai ne ba ka haihuwa za ta yadda ta zauna dakai?Ka san ciwon rashin ɗa har yau kuka nake kan ban taɓa haihuwa ba duk da mahaifin ka ya ba ni kyautar ka.Wallahi da sake dole kowa ya sani sannan ka canza mata ba ƴar talaka ba don ba ma haɗa dangi da matsiyata!"
Ya ce tare da miƙewa zai fice ga mamakin sa sai ya ga A.m ya yi sauri ya kama ƙafafunsa ya riƙe ya saka kuka kamar wani ƙaramin yaro ya na roƙon sa,wanda magana uku ya yi masa har ya saka ya zauna jikin sa sharɓar da zufa ya na kallon su.
" Daddy ka tuna Zainab ƴar amininka ne kuma a saboda ni ta kamu da wannan ciwon,Zainab ta rantse in har na haɗa ta da wata mace za ta rabu dani,rayuwata ba za ta yiwu ba in babu Zainab ina sonta raina fansa ne akan duk abin da take so."

Waɗan nan kalamai ya gaya masa ya na kuka wanda hakan ya sa ya zauna don ya saurare su." Na ji to yanzu ya kuke son ayi ni fa ba mahaukaci ba ne kuma ni soyayya ba ta mai da ni zautacce ba,kar na zo na biye maka mu aika ta hakan lamari ya caɓe mu rasa yadda za mu yi."
Ya tambaye shi ganin A.k ya miƙe ya ba su guri saboda yadda Daddy yake kallon sa kamar ya na buƙatar hakan.

" Saboda haka ya sa na zaɓi ƴar talaka wanda ba su da komai ka ga ta gurin ta hankalinmu ba zai tashi ba,kuma ni na tallafi rayuwar ta.Matsiyata ne basu da komai sai talauci da garari a rayuwa sannan ƙanin mahaifinta wani irin mugun me son kuɗi ne ya kuma tsane ta don haka kar ka damu."Ya ce ya na kallon shi don duk wani kalamai da zai gaya mishi ya ƙare shi dai burin shi ya amince.

" Kai ku tashi ku tafi kai son ka je ka yi tunani na baka nan da sati biyu,in baka sanar da mahaifin ku gaskiyar lamari ba to ni zan fasa ƙwai maza tashi ka wuce!
Hankalin A.m ya tashi matuƙa ko kaɗan bai yi tunanin zai yi kafiya akan lamarin ba,saboda yadda ya ga baya son ya ga ɓacin ransa,ƙara riƙe ƙafar sa ya yi ya na kuka da roƙon sa,amma haka Daddy ya janye ƙafarsa ya shige ɗakin sa duk da kukan shalelensa na yi masa ƙuna sai dai lamarin da ya kawo mai girma ne.

A mota suna tafe babu mai yi wa juna magana A.m tunanin kuɗin da ya kashe take yi,sai ya ji ya ƙara samun ƙarfi wanda washegari Daddy na fitowa daga masallci ya gan su a tsugune.

A ƙalla sun ɗauki tsawon wata suna jerangiya amma Daddy ya hau dokin naƙi,cikin ikon Allah A.m har ya haƙura sai ga kiran shi ya sanar masa su shirya yau zai je a ɗaura aure.


Haka kuwa aka yi bayan an idar da sallah aka ɗaura auren Juwairiya Ahmad da Abdurrahman Dawood akan sadaki naira dubu ɗari biyar wanda Baba Sani ya dage hakan zai ba da,ba tare da damuwa ba ya amsa wanda Daddy ne ya biya kuɗin.

Tofa masu karatu ga shi Allah ya kawo mu an ɗaura aure kuci gaba da bibiyar lintafin domin mu ji yadda za ta kaya.

SHIN JUWAIRIYA ZA TA IYA DANNE SON DA TAKE MASA TA ZAUNA DA SHI KAMAR YADDA YA BUƘATA?NI DAI NASAN SON GASKIYA BA YA ƁUYA WAƊANDA SUKE CIKIN SO SUNE KAWAI ZASU AMSA AMIN TAMBAYAR NAN.

TAKU JAMILA LAWAL ZANGO










ƊUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ƊIN KU YA NA SAKA NI NISHAƊI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM








Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha shidda.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da

Please Login or Register in order to submit comment