Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shiga makaranta.
Kullum Burina ALLAH ya warware wannan *Sabon Al'amaree* kema ki zauna lfy agidan mijinki, in kobazaki koma can gidanba kiyi wani Auren amma kullum abubuwa sai k'ara nisa sukeyi Abu kamar wasa.
Iman ta CE, "gwaggo wlhy nidai dankunk'ine amma dakawai kun yarda nayi aurena, nasan shima idan yaga nayi Auren zai daina fad'in *Bai sakeni ba* d'in.
Mama ta sauke ajiyar zuciya iman har yanzu ke yarinyace shiyyasa, bazaki gane had'arin hakanba, dolene mucigaba da Addu'a har komai ya bayyana, idan muka baki dama kikayi aure bazamu sami nutsuwaba, zamu rink'a kokwanto kokinyi *aure akan aurene*, tunda mijinki ya CE, " *bai sakeki ba*, kullum yana kan bakansa na fad'in hakan.
Tokinga kuwa akwai Matsala kenan.
Nasiha sosai gwaggo tashiga yimata, ta CE, "tadage da yawan addu'oi, suma suna nan suna mata akullum, komai zai zama labari insha ALLAHU.
Saida gwaggo taga tad'an kwantar da hankalinta sanan takama hannunta suka tafi dansuyi breakfast.

A6angaren Dr Isma'il kuwa kuka yashigayi rirus tamkar mace ko k'aramin yaro, tuni k'irjinsa yayimasa nauyi, tun yana iya kukan har komai yatsaya, numfashinsa yafara fita dak'yar, yasa hannunsa yadafe k'irjinsa.
Musayeef kam yana FIta da gudunsa yanufi 6angarensu deexerh, ak'ofar fallo yaci karo da daddyn deexerh, da Sauri yad'aukeshi yad'agashi sama yana fad'in my son yaushe kazo?.
Mom d'in deexerh dake bayansa tana musu dariya ta ce, " tun jiya aii yana nan, sunzo shida Isma'il da daddare Baka dawoba.
Okey tafad'a yana sumbatar kumatun Musayeef, yarona INA momy?.
Da hannu Musayeef yanuna mom d'in su deexerh.
Dariya yayi a'a ba wannan nake nufiba mom d'inka..... Mom d'in su deexerh tak'atsemasa zancen dafad'in a'a aii Aunty maa zaka CE masa, in ba hakaba bazai ganeba.
Dariya Yaya yayi, ya CE, "nikam sunann yana bani dariya wai aunty maa, nifa nama k'asa fassara ma'anarsa.
Dariya itama tasakeyi ta CE, " yaro kenan shi INA ruwansa bayaji deeni yana cemata aunty ba, shikuma bazaice auntynba kad'ai bakuma zaice mamaba shine yahad'a gabad'aya yana fad'a aunty maa ko Musayeef?.
Musayeef yay 'yar dariya Dukda ba gane maganganun su yakeba gaba d'aya.
Shima dady dariya yayi ya CE, "to INA zaka make gudu?.
Da Sauri ya CE, " daddyne ya CE, "nazo mom tasamin kaya, okey yaron mom to jeka, yafad'a yana mik'a matashi, amsarshi tayi tana dariya suka nufi d'akinta.


Kowa ya hallara a 6angaren mama za'ayi break amma babu Dr Isma'il, Yaya ya CE, " Marwan tashi kakira mana Uncle d'inku, ko ya mantane ana jiransa.
Marwan yamik'e yana fad'in to daddy.
Da sallama yashiga ganin babu kowa a falon yasashi shigewa cikin bedroom d'in.
Da Sauri yak'arasa bakin gadon danji Dr Isma'il yana sauke wani irin numfashi.
Dagudu yakwaso yayi 6angaren mama yana kwala kiranta daddy! Daddy!! Kazo uncle zai mutu....
Aii tukafin ya isoma kowa yamik'e, ahanya suka had'u suka koma 6angaren Dr Isma'il, Yaya baijira komaiba ya cicci6eshi shida mom d'in su deexerh sukayo waje, amota suka sakashi sai asibiti........

*(Kai masu karatu INA tausayin Dr Isma'il wlhy,😭yana shan wahala)*







*luv u oll my fan's*
*((S))......2017*
[8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*




*NA Bilyn Abdul*




_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com




*miya kamata nayi?*
_Duk wanda yace shine tofa bashi bane, idan ALLAH yay maka wata d'aukaka kada kazama mai wulak'anta mutane, kada kazama mai Girman kai, kada kazama mai izgilanci, kada kazama mai fankama da fad'i._
_dum abinda kasamu anan zaka barsa, duk girman d'aukakarka daga randa tauraranka yadishe kazama labari, 'yan kanzaginkama gudunka zasuyi, dama wasu ba k'aunarka sukeba, saboda d'aukakarka suka ra6eka_
_d'aukaka bakomai bace 'yan uwana, ita tamkar rana take, sanda ta haskaka kowa zai ganka, data dishe ka kasance cikin duhu sai kowa ya fara neman wata._
_Kigane nagane Mugane, mugyara kodan tsira awajen ubangijin talikai._
*ALLAH yasa mu gane*




*(page 22)*
k'arfe 5:00pm Xoxo tashigo asibitin, wayar deexerh takira tafito ta tareta.
Cike da farinciki suka rungume juna, hannunta taja suka nufi d'akin da aka kwantar da Dr isma'il, danya farka, su yayama sunje gida, daga deexerh sai marwan aka bari a asibitin kafin Yaya yadawo sukuma su tafi.
Lokacin dasuka shigo Dr Isma'il yana zaune akan sallaya ya idar da sallah yana addu'a.
Guri suka samu suka zauna, marwan suka gaisa da Xoxo, suna 'yar hirarsu k'asa2 da deexerh, Dr Isma'il ya idar.
Tasowa yayi Yakoma kan gadonsa yana murmushi, k'awarmu kece?.
"Murmushi Xoxo tayi itama, wlhy kuwa nice daddyn Musayeef, Ashe kuma abinda yafaru kenan?.
Wlhy kuwa k'awarmu.
To yajikinka?.
Jiki alhmdllh.
Yagajiyar ranar?.
Tayi 'yar dariya aikai za'a tambaya gajiya daddyn Musayeef kaida ka tuk'omu.
Baice komaiba sai murmushi dayayi.
Wayarsace tafara wringing, da Sauri marwan yad'auka yabashi, akunne yakara yana murmushi, Nabeel ykk?.
Lfy lau abokina, gani a k'ofar asibiti.
" kai haba da gsk?."
"Wlhy kuwa Kasan bazan iya hak'uriba sainazo na ganka."
Tom ga marwan nan zai shigo dakai.
Marwan jeka shigo da Dr Nabeel.
Okey uncle, marwan yafad'a yana mik'ewa.

Bayan kamar minti hud'u suka shigo da sallama, su deexerh suka amsa, Dr Nabeel yak'araso gaban gadon, ayya abokina karame sosai wlhy, ya jikinka?.
Dr Isma'il yay murmushi, Alhmdllh Nabeel.
Su deexerh suka gaidashi, shi saima yanzu ya lura dasu, bakinshi nad'an rawa yanuna Xoxo, nikam a INA nasanki🤔.
Xoxo tayi murmushi, amakarantar su jman, lokacin dakaje d'aukar daddyn Musayeef.
Yes hakanefa.
Murmushi Dr Isma'il yayi, danganin yanda abokisa ya waske, tunfa ranar yake damunsa akan yana son Xoxo, ya musalta masa kamanninta, shiyyasa randa ya d'akkosu kallo d'aya yaymata yaganeta, amma yanzu jiba yanda yanuna yama manta Inda yasanta.
Daga nan fira suka farayi sosai, Xoxo data d'ago saisu had'a ido da Dr Nabeel, ita kunyarma kallon dayake mata takeyi, duk ya wani tsareta da mayun idanunsa.

Xoxo takalli agogon hannunta, kai deexerh bari nawuce dare yafara yi, daddyn Musayeef ALLAH yak'ara lafya.
Amin hafsat ngd sosai, Dan ALLAH kigaidamin 'yan gidan.
Zasuji insha ALLAHU ngd Nima.
Dr Nabeel ya mik'e, abokina bari nayi rakkiya ko, yafad'a yana kanne ido😉.
Dariya Dr Isma'il yay yana jinjina kai.
Suna fita wayar deexerh tahau wringing, kallon Number tatsayayi Dan bata ganeba.
Har wayar ta yanke aka k'ara kira sanan ta d'aga da sallama.
Assalamu alaiki gimbiya, muryarsa ta daki dodon kunnenta, ajiyar zuciya tasauke, tareda fad'in wa'alaikassalam.
Humm kin manta dani ko?.
Aiini bamma ganekaba deexerh tafad'a tana d'an murmushi.
Oh God sorry, Sunana Umar farukh, Wanda muka had'u a asibiti.
Okey nagane.
Yauwa to ykk?.
Ina lfy.
Masha ALLAH.
Dan ALLAH idan bazaki damuba inason kawomiki ziyara gidanku gobe idan ALLAH ya kaimu.
Kai Haba malam daga had'uwa sau d'aya saikuma zuwa gida.......katseta tayi da fad'in pls gimbiyata, ke mai ajice bakidace da afad'amiki ana sonkiba awaya, dole sai anbaki girmanki zuwa gida.
Murmushi deexerh tayi, shikenan gwanin dad'in Baki, zan turomaka address d'in.
Babu dad'in baki komai nafad'a akanki gsky ne, ngd sosai saina jiki.

A6an garden su Xoxo ma kusan hakan take, kiran deexerh da akayi awaya yayma Dr Nabeel dad'i, Dan gani yake yasamu damane.
Yakalleta cike daso da k'auna, 'yammata nifa kinmun sata wlhy.
Ido Xoxo tazaro😳sata kuma malam?.
Yes yafad'a yana wani lumshe idanu, Xoxo ta had'e fuska kai malam banason sherifa, wanan idan wanima yaji aisai yazata gskyne?
To aii gaskyar CE kedama kin zata wasa nakeyi.
Mtsowwww malam bani hanya na wuce kaji, humm aii bakida damar tafiya saikin bani madadin abinda kika satar min, kokuma namiki ihu.
Harararsa tayi, tokayi ihun mana, ya ce, "kin yarda kenan?.
Banza tayi masa Dan yafara bata haushi, wayarta tad'akko tafara danna Kiran iman, fisge wayar yayi ya yanke kiran, 'yammata saifa kin saurareni.
To tunda ana dole basai muganiba.
Dariya yayi sosai, zan kar6i number ki wajen khadija zan gaya miki satar dakikamin, sanan kijira zuwan rundunar sojoji gidanku kar6ar madadin satar dakikamin..
Daidainan deexerh ta k'araso, yamik'a mata wayarta tareda fad'in sai kinjini, kud'i yad'akko yabama deexerh, khadija ga wanan kibama bak'uwarmu tahau mota.
Deexerh ta rissina ta kar6a tana fad'in to uncle angode.
Xoxo kan gaba tayi bata tanka musuba.
Hannu yasaka a aljihu yana binsu da kallo har suka 6ace sanan Yakoma cikin asibitin yana murmushi masifar Xoxo.
Dr Isma'il ya kallesa kai abokina duk kawani rud'e wlhy.
Dariya Dr Nabeel yayi, badoleba abokina soyayya aii ba k'arya bace.
Hakane Dr Isma'il yafad'a yana murmushi.

Deexerh ta ce, " aunty hafsat Kodai Kodai keda uncle Nabeel ne?.
Kodai2 me Xoxo tafad'a tana zaro ido😳.
Dariya deexerh tayi, naga kamar sonki yakeyine?.
Tab rufani ki sayani, ko d'aya tafad'a tana tare adaidaita sahu, saida tashiga sanan Deexerh tasaka mata kud'in da Dr Nabeel yabata a jaka, toga k'yautarki.
Tab nifa bazan kar6aba ki maida masa kayansa.
Habadai ai ba'a maida hannun k'yauta baya, ngd sosai kigaidamin mutan gidan.
To zasuji mai adaidaita yaja suka wuce deexerh na d'aga mata hannu.

Iman kuwa tunda suka bar asibitin tazama wata shiru2, koda suka koma gidama d'aki tashige tayi shiru, sallah kaiwai ketashinta, wajen k'arfe 6 taji wayarta tad'anyi wringing, d'auka tayi taduba, saitaga Xoxo, tayi murmushi 'yammata ni kikema flashing?.
Komawa tayi takwanta, ganin xoxo bata sake kiraba yasa ta tashi, d'ari biyu ta d'auka tafice.
Deeni na zaune afalo yana cin abinci tabasa, deeni idan ka gama Dan ALLAH d'an siyo min kati.
To aunty, Dan ALLAH Nima d'an bani d'ari, inada d'ari nacika nasiyo katin, data nakeson saya.
Hararasa iman tayi, kai Dama kud'inka aii a sayen data zasu k'are, ALLAH ya shiryeka.
Amin aunty, nidai idan zaki bani aii babu matsala.
Fita tayi bata tanka masaba, babu dad'ewa tadawo da d'ari biyu ahannu tabashi.
Kai my aunty ngd, shiyyasa wlhy nake k'ara sonki.
Iman tayi murmushi kawai takoma d'aki ta kwanta.
Babu dad'ewa yakawo mata katin tasaka.
Saida tafara gwada Number Reefat, har yanzudai bata Shiga, afili ta ce, "ALLAH yasadai lafiya.
Xoxo takira bugu d'aya ta amsa, suka gaisa cike da kewar juna, Xoxo ta ce, " ai d'azu naso na kiraki nace miki INA wajen mijinki, saikuma aka samu matsala.
Aii flashing d'inki Dana ganine ma yasa nakira da fushi nakeyi dake.
Ohh my sis.... Kiyi hak'uri, wlhy zanzo gobe idan ALLAH ya kaimu insha ALLAHU, wani abunema yahana in zuwa jiya da yau.
To shikenan na hak'ura, kinsan bana iya fushi dake, ALLAH ya kawoki lfy.
Amindai,
Wai Yaya kema har yau bakya samun Reefat?.
"Wlhy bana samu, ni harma nafara tunanin ko lafiya?, wlhy Nina haka, to ALLAH yajishemu alkairi.
" Ameen dai".
Sukai sallama kowa ya kashe wayar.

_Bayan kwana hud'u_
Jikin Dr Isma'il yayi sauk'i sosai harma an sallamesa yau.
Iman dai bata sake zuwa dubashiba, bakuma takira wayarsaba, gwaggo da Abbah sunje har sau uku, hakama su aunty salma sun sake zuwa, Xoxo ma tak'ara zuwa.
To Dr Isama'il ALLAH yak'ara sauk'i.

*_WATA SABUWA_*
Gidan su Dr isma'il yau cike yake da mutane, dangin mahaifinsu ne sukazo dubashi, ciki kuma harda baban su aunty sadiya, bayan anci ansha aka zauna ana hira.
Acikin hirarne kawu Falalu yake fad'in sufa dawata magana sukazo, mama ta ce, "to falalu muna saurarenka.
Kawu falalu yagyara zama yana kallon mama, ya ce, " maganace akan Sama'il, lokaci yayi daya kamata yayi aure, wanan zaman dayakeyi bazai haifar da d'a mai idoba, tunda kowa yasandai ba'a komawa saki uku, to Dan haka yama fidda rai akan matarsa, saidai idan darabon zama nan gaba zasu zauna.
Hakane mama tafad'a fuskarta babu walwala, Dan tasan Dama ba alkairine yakawosuba.
Kawu falalu yacigaba, to yanzu dai mun yanke shawara Nida Lurwanu da Maharazu, da Karima akan zamu k'ara k'ulla zuminci, mudai nida maharazu da Karima bamuda yara mata, sai Lurwanu, Dan haka muka Yanke shawarar aurama Sama'ila Zakiyya,(Raihan).
Gaban Dr Isma'il ne yafad'i da Sauri yad'ago yana kallon kawu falalu.
Kawu falalu yacigaba da fad'in, to yanzudai maganar damuke muku, ni na biya sadaki an d'aura auren tun a can, shinema dalilin dayasa kukaga mun taho da Raihan, gata nan munkawota suzauna lafiya, ga 'yar uwarta nan intayi ba daidaiba zata ringa tsawatar matane, kumadai saiku kula, intayi ba daidaiba a gyara mata Dan kunsan yarinyace karama sai hak'uri.
Tunda yafara maganar falon yakarayin tsit, bakajin motsin kowa, sai aunty da Raihan Dasuke murmushi.
Yaya ya bud'e baki zaiyi magana mama ta girgiza masa kai alamar yayi shiru.
Shirun kuwa yayi amma idanunsa sun cika da kwallah, tu da mahaifinsu suka bar duniya, dangin mahaifinsu suka watsar dasu, basa kulawa dasu ko kad'an, basa zuwa Inda suke, har saida sukaga sun girma sun zama wani Abu, shine akazo aka k'ak'aba masa auren sadiya, zuwan sadiya baifi da wata ukuba uwar 'ya'yansa tabar gidan mamansu deexerh.
To gashi kuma yanzu an mannama Isma'il Raihan, bayan abaya mahaifiyarta ta CE, "bata yarda Isma'il ya auri Raihanba baza'a tara mata 'ya 'ya agida d'ayaba........
Maganar mama ta takatse masa tunani.
Shikenan falalu, mun amshi k'yautarku ALLAH yasanya alkairi, saidaifa kunyi kuskure Dan yakamata kafin kuyi Auren kukiramu asanar damu Dan aji tabakin Isma'il d'in, amma yanzu ya wuce saidai Atari gaba kawai.
Baban su raihan ya katse mata zancen da fad'in, Maryama kinsandai munada iko da Sama'ila muma ko?, Dan duk duniya bashida iyayen dasuka wuce mu, ko Neman auren zashi wani waje dolene mune wakilansa, to tunda abin yazama na gida kuwa aikinga koya sani ko bai saniba, koya yarda kobai yardaba dolene yakar6i 'yar uwarsa yarik'e da hannu biyu, kuma naga dama suduka suna son juna daga sama'ilan har Raihan d'in, kawai abaya ALLAH ya rubuta bazata zama matarsa bane.
Kaga Lurwanu nifa babu abinda nace maka, Dan haka maganarnan bata 6acin rai bace, aurene kun d'aura kuma nace mun kar6a, to saime?, duk wata maganarma kun Isa bata tasoba, Inda bama ku isanba aii wlhy babu mai aurama yarona aure batareda yardarsaba.
Sunsan halin mama sarai Dan haka suka Shiga bata hak'uri da magana mai dad'i, anandai ka masu Dr Isma'il nasiha shida raihan.

Deexerh taji zafin wanan had'in ammafa tawani 6angaren taji dad'i, Dan idan bata mantaba aranda suka Gana da bilyn Abdul tace musu inama Raihan ta Auri Uncle, da komai saiyafi saurin fitowa fili.
Wanan yasa bataji haushiba sosai.

Saidai ana gamawa da uncle d'inta aka dawo kanta.
Kawu Maharazu ya ce, "kema hadiza mun Baki nan da wata Biyar Kodai ki fito da mijin aure kokuma muhad'aki aure da Kamilu na wajena.
Ido deexerh ta zaro ta ce, " kawu Kamilufa kace?.
Eh shifa nace, Dan haka saikiyi gaggawa..... Dr Isma'il ne ya katse masa zancen da fad'in a'a kawu nanfa ba huruminku baneba, domin khadija jikace agareku, mune iyayen khadija mu Muke da damar aurar da ita lokacin da mukaso, ayanzu kuma karatu takeyi, sainan da wata Tara zata kammala, saikuma ta kammala sanan zamuyi mata maganar aure, mudai damuke 'ya'yan d'an uwanku, Duk abinda kukaga dama kuyi damu, saboda darajar kun kasance jinin mahaifinmu na kusa.....
Sama'ila mukake gayama haka Dan ubanka, to ai ko Mahammadu dayanada rai bazai fad'amin hakaba akan zuri'arsa......
Mama ta katseshi, Maharazu gskya fa Isma'il yafad'a bakuda hurumin za6ama hadiza miji, sudai dasuke 'ya'yanku zaku iya amma banda su hadiza jikoki.
Ehh lallai maryama aii dama duk wata wuta kece kike kunnata tsakaninmu da yarannan, kece kikasaka basa ganin darajarmu, wanan mugun halin naki yasa Karima ta CE, "bazata biyomuba.
'Mama tayi wata 'yar dariya, Maharazu kenan, aiini duk abinda zakuce dangane da yarannan banida Matsala daku'.
Kundai San inada iko dasu, todan haka maganarma ina 6ataku agunsu aii daga baya kenan, Dan tuni sukasan matsayin su agunku.
Haka aikata cacar Baki, daga bayadai Yaya yashiga tsakani aka sulhunta.
Washe gari su kawu lurwanu suka koma.............



_to masu karatu koya Iman zataji wanan labari?,._
_Yaya zaman Raihan da Dr Isma'il zai kasance?._
_shin auren Raihan zai kawo mafita dangane da matsalarsu Dr Isma'il da Iman, kamar yanda Bilyn Abdul tafad'ama su deexerh?._
*humm kubiyoni danjin yanda zata kasance*




*luv u oll my fan's*
*(((S)).....2017*
[8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!._*





*NA Bilyn Abdul*




_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com




*miya kamata nayi?*
_babu nakasashshe sai kasashshe, babu maraya sai rago._
_Karka zauna kadogara dawani, kadage kidake munemi nakammmu, addini yana ingantuwa idan masuyinsa suna cikin natsuwar wadata, ba tarin dukiya bane wadata, wadar zuci itace wada, komin k'ank'antar abinka ka rungumeshi kasaka masa albarka, kahangi na k'asa dakai, kada ka hangin nasama dakai, kagodema ALLAH dakad'an d'in daya Baka, duk Wanda yakasa Gode kad'an koya samu mai yawa bazai godeba._
_Duk Wanda yagaza godema ALLAH to kuwa zai godema azabarsa._
*ALLAH yasa Mugabe*




*(Page 21)*
Ya Majeed nagaba, hannunsa rik'e da affan, aunty salma tana bayansa, iman CE ak'arshe, tafiya take tamkar wadda kwai ya fashewa aciki.
Saida suka shigo cikin asibitin sosai sanan ya Majeed yad'auki wayarsa yayikira, assalamu alaikum.
Eh gamu mun iso, okey.
Juyowa yayi yace kumuje nama gane d'akin.
Ak'ofar wani d'akin suka tsaya ya Majeed ya kwankwasa, sanan yatura da sallama suka Shiga, d'akin cike yake da mutane, aunty salma da iman suka shigo, sannu dazuwa aketa musu, itadai iman kanta yana k'asa bata kalli kowaba.
Jitai an rik'e hannunta da Sauri tad'ago danson ganin waye, deexerh tayi dariya my aunty nabaki tsoro ko sorry.
Ido iman tazaro sai yanzu ta fahimci Wanda sukazo gani..... Deexerh ta k'atsemata tunani da fad'in kai auntyna naji dad'in zuwanki wlhy, murmushin yak'e tayi suka k'arasa, su aunty sunata gaisawa da mutane datanbayar mai jiki.
Iman ma ta daure ta ce, "INA yininku, yamai jiki?.
Gabad'aya aka amsa, Dr Isma'il dake a jingine da fillo, 'yan biyu sun sakashi tsakkiya, yasaki wata wawuyar ajiyar zuciya saboda ganin Iman.
Gaba d'aya d'akin aka maida kallo gareshi, ganin wadda yake kallo yasa suka dawo da kallonsu kanta, babu Wanda yagane Iman da farko, saboda ta lull6e fuskarta da gyale.
Mama ta ce, " hadiza wacece wanan?.
Dariya deexerh tayi, lallai mama kindai k'ara tsufa wlhy, to aunty Iman CE, ta janye galen iman.
Mama ta mik'e da sauri ta Isa Inda suke, hannun iman takama tana mai jin dad'in ganinta, iman 6oye mana kanki kikeyi?.
Cike da kunya iman ta rusina tana gaida mama, mama ta rungumeta haba iman duk kin manta damu, Yaya da mom deexerh sai murmushin sukeyi, amma aunty tuni nasaka mata alamar tambaya, Dan afirgicema take kallon iman d'in.
Mama takama hannun iman taje ta zaunar, harga ALLAH tana tsananin k'aunar iman domin yarinyar kirkice, k'addarace kawai tarabasu Dan basuda yanda zasuyi.
Iman ta rissina tana gaidasu Yaya, cike da fara'a suka amsa, Yaya ya ce, "iman kin manta damu ko?.
A'a Yaya wlhy karatune.
Da k'yau, yanzu kina level nawa?.
"Ina level 3, iman ta amsa kanta ak'asa.
Lallai Iman kun zama manyan 'yan boko, murmushin tayi batareda tace komaiba.
Ya Majeed ya ce, "zadai su zama nagaba kad'an, aii sun d'akko hanya Majeed Yaya yafad'a yana dariya.
Iman tad'an kalli Dr Isma'il ta ce, " INA yini, ya jiki?.
Dr Isma'il dake zaune ya dasa mata idanu ko k'yaftawa bayayi, ya sauke ajiyar zuciya ahankali ya ce, "da sauk'i ykk?.
Shiru tayi bata amsaba, deexerh dake gefe sai zabga murmushin take, jitake inama har yanzu Iman tana tareda Uncle d'inta.
" gsky lokaci yayi dazata taka rawar gani wajen binciko gskyar Al'amaree, amma zata nemi Xoxo akan shawarar dasukayi ranar na nema *bilyn Abdul*, ance tashahara wajen irin wanan aikin, akwaita da naci wajen nemo rahoto, insha ALLAHU zasu nemeta kuma ko nawa takeso zasu biyata taimusu aiki, itadai Uncle d'inta yasamu farinciki.
Marwan da Musayeef suka shigo d'akin da sallama, Dama basanan an aikesune.
Yana hango mamansa yasaki hannun marwan ya cilla da gudu ya rungume iman, aunty maa yaushe kikazo?.
Kansa ta shafa tana murmushi, yanzu nazo Musayeef.
Aunty maa kinzo ganin dadyna bashida lafiya?, kai tad'aga masa kawai, Yakuma fad'in danfa bakizo kin koya masa game bane ranar, yake rashin lafiya ko daddy?.
Kai Dr Isma'il ya d'aga masa alamar eh.
Yadawo da kallonsa kan iman, ni babu ruwana dake, yafad'a yana ja da baya tareda turo Baki.
Mutuwar zaune iman tayi, a zuciyarta ta ce, "kajimin yaro zai d'aureni azaune.
Yaya ya ce, " a'a my son aii ba'a 6atawa da uwa, zonaji miya faru?.
Wajen daddynsu deexerh yanufa, Iman Addu'a take ALLAH yasa kada yafad'a tasan shegen surutun Musayeef. Wayonsa ya girmi shekarunsa.
Yaya ya CE, "miya faru kaida aunty maa d'in kake fushi da ita.
Dady ba ita bace, nasa daddyna yakiramin ita na ce, " tazo takoyama daddyna game, ta ce, "zatazo amma tak'i zuwa.
To kayi hak'uri ai yanzu gata Tazo zata koya masa Kaje Ku shirya. Musayeef ya kalli iman, aunty maa wai zaki koyama dadyna game d'in?.
Ganin yanda Dr Isma'il ya tsareta da idanu yasa ta gyad'a kai alamar eh, tsallen murna yafarayi.
Yanufi dadynsa, hannun yasa ya d'auki d'aya daga cikin wayoyinsa dake gefensa yakaima Iman, to gashi zoki koya masa, idan mun koma gida sai muringa yi nida shi.
Iman ta ce, ''kaga yanzu bashida Lafiya kabari saiya warke sainazo har gida na koya masa.
Ehumm ehumm!, Musayeef yafad'a yana nok'e kafad'a da kya6e fuska😞.
Iman tayi banza dashi Dan taga rigimarsa bamai k'arewa bace, yakware Baki zaiyi kuka.
Da sauri mom d'in su deexerh ta ce, " kaga ishirunka yarona zata koya masa, jeka bata wayar.
Jin anfad'i haka yasashi saurin kallon Iman, ta had'e fuska tana harararsa, yaja da baya yana hawaye.
Dr Isma'il dake kallonsu saidai babu magana, sabida baya iyawa sosai, ahankali ya ce, "pls My live ki kar6a..
Dukda ahankali yayi maganar duk sunji abinda yace, aunty tana siririn tsaki Wanda basu jitaba.
Hannun iman tamik'ama Musayeef ya d'ora mata wayar daddynsa ahannunta,

Please Login or Register in order to submit comment