Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'yar adam azija, suma suka kwanta badan sunajin barciba, saidan taya k'awar tasu jimami da tunanin jiyanta da yau, dan gobenta gaibuce.

Dr Isma'il
Doctor ya tsura ma abokin nasa idanu, cikin karsashi da dadishewar murya ya ce, "Nabeel wai saiyaushe ne iman zata amince BAN SAKETA BA?.
shin haka zata cigaba da kasancewa da nauyin aurena akanta??, haka zata cigaba da barina kullum cikin AZUMI da bagenta?, tanisanta kanta dani, ta nisanta MUSAYEEF dani, alhalin yanzune nafi buk'atarsu akusadani.......
Wasu 'yan kwalla suka mak'ale masa akan gashin idonsa na k'asa.....yacigaba da faďin, Nabeel inaga lokaci kaďan yaragemin a DUNIYA, domin SON iman yakusa hana numfashina aiki cikin kwarewa.
Lokaci yayi dazanbarma IMAN duniya gaba ďaya k'ila bayan raina ta sanar daku BAN SAKETA BA..........
hanunsa Nabeel ya damk'e cikin sigar lalashi ya ce, "haba abokina kadaina faďar waďannan kalaman, kaifa MUSULMINE kuma mai ilimin addini dana zamani.
Nasan kasan k'addara da wanzuwarta da shuďewarta, to inaso kaďauki wannan lamarin amatsayin JARABAWAR RAYUWARKU, na tabbata akwai wani k'ulli dabamu saniba.
Nayi imanai IMAN bazatace kasaketaba alhalin BAKA SAKETA BA, bazata nuna takardar nanba abisa k'arya koson rabuwa dakai.
Saidai abinda yake bani mamaki da ďaure kai waye yayi irin rubutunka? wajen rubuta sakin iman, indai har yanda kake bani labari hakane tafaru to tabbas akwai ruďi da wanzuwar SABON AL'AMAREE a lamarinku.
Saidai babu abinda yagagari ubangijin al'arshi, dan haka mucigaba da tsananta addu'a insha ALLAHU komai yana daf dazu k'arshe, kuma ko waye asirinsa yana gab da tonuwa wlhy.
Dan haka inaso ka kwantar da hankalinka kodan gudun tashin ciwonka da wanzuwarsa, Nida kai duk munga JIYAN MU, MUNGA YAU, amma bamusan GOBENMU BA domin kasancewarta GAIBUNMU.
Musayeef kuwa kana zuwa ganinsa kana waya dashi aduk lokacin dakaso dan haka ka kwantar da hankalinka insha ALLAHU SAUDAT tana gab da dawowa FADARKA amatsayin SARAUNIYAR KA..
Dr Isma'il yasaki wani sassanyar murmushi tareda sauke ajiyar zuciya ahankali, to ALLAH ya tabbatar Nabeel, amma lamarin yana k'ara bani tsoro, atunanina nisanta kaina da iman zaisa randa tagani ta ďokantu.
Amma kash ganina saiya sakata acikin ruďani da shiga uku, Nabeel inason Saudat wlhy sosai, zan iya cewa babu wani mahaluki daya ta6a son wata kamar ni.
Asanadin iman nakamu da ciwon ZUCIYA da hawan jini, amma kash takasa fahimtata, takasa yimin uzuri, kodayake batada laifi itama tana cikin ruďanine kawai.
Hakane abokina, iman tana cikin ruďani wlhy.
Saidai kawai mucigaba da barma ''UBANGIJI "komai dominshi yanasane da shiga da fitar kowa, kuma shine masanin gaibu.
Hakane, ALLAH yasa mu dace to.
Haka Nabeel yayta kwantarma Isma'il da hankali harya samu 'yar nutsuwa, yakira yayansa suka gaisa harda Deexerh da marwan, dakuma mama da maman su deexerh, da aunty.

WASHE GARI.
duka 6angarorin biyu sun tashi sukuku, gakuma kowa yatashi da uziri, iman tatashi da uzirin text.
Isma'il yatashi da uzirin aiki, an turasu kwantar dawata tarzoma a RIVERS STATE, dan kawai bashida ikon k'in zuwane amma daba inda zaije, sauk'insama harda Nabeel a tawagar tasu dan haka damuwar tasa tayi sauk'i.

Babu laifi iman ma taďan saki jikinta dan yau harta iya rubuta wani abu a text ďin.
Su Reefat sunji daďin sakin jikinta sosai, harma a fuskarsu sun nuna.
Iman tana k'aunar k'awayen nata, dan duk wanda yadace da k'awaye irin xoxo da Reefat yagama dacewa, bakuma zai ta6a yima k'awa kallon baibaiba.
Dahaka suka rarrafa zuwa ďaki agjiye.
Amma wanan bai hanasu sonjin labariba kasancewar yau iman adaidai take sa6anin jiya da shekaran jiya data shiga cikin ruďin zuciya dana jiki.
To itamadai yau harga ALLAH tayi niyyar cigaba dabasu kabarin dan haka suna gama komai suka zauna.

LABAREE.
.......Nakai tsawon minti talatin dashiga ďakin banji motsin kowaba, sai zuwa wani ďan lokaci naji ana buga k'ofar ahnkali, tuni jikina yahau 6ari da 6aran6arama, cikin rawar murya na ce, "waye......?
Doctor ya ce, "kibuďe kinyi ba k'i.
Da farko ban yardaba, dan azatona wayau zayimin, amma saina rink'ajin maganar mutane sama2, jiki babu k'wari na sakko daga gadon nabuďe k'ofa.
Babu doctor awajen dan haka na k'arfafa jikina dankarsu zargi wani abu.
Nazo na gaidasu, suka amsa cikin fara'a da bina da kallo.
Matane dayawa yara da dattija da 'yammata, da alamadai danginsu doctorne.
Babu daďewa doctor yafito daga ďakinsa, ya zauna kan hannun kujera kusada wata tsohuwa amma ba tukuf ba.
Ya ce, "Saudat 'yan sakoto ne dangin mahaifinmu yanzu zasu tafi shine sukazo miki sallama.
Kaina a k'asa na ce, "sanunuku, suka ce yauwa amaryarmu.
Daganan ban sake furta komaiba kasancewar inajin kunyarsu dashi kansa doctor ďin.
Sunďan ta6a hira da doctor sanan suka mik'e, tareda yimin sallama da fatan dawowarsu suna wata shekarar.
Nidai bance komaiba sai doctor daya ce, "ALLAH ya tabbatar.
Bayan tafiyar 'yan sokoto saiga deexerh da Marwan waďanda dama can nasansu ahoto, saidai yauce rana ta farko damuka haďu.
Na tarbesu da murna dan deexerh sa'a tace, shikuma marwan nagirmesa, suma sai fariciki suke daganina, saidai bansan daliliba.
Na kawo musu cincin muka zauna muna hira.
Ahaka doctor yashigo yasamemu, cikin farinciki suka tarbosa suna faďin oyoyo uncle.
Shima yataresu da murna, yarana ina kuka shigane haka??, muna nan uncle, kawaidai gajiyar bikice.
Yay dariya kokuma ganin bak'iba.
Suma dariyar sukayi suna faďin dama wanan ďin.
Nakula doctor yana matuk'ar son deexerh da marwan, sunkuma shak'u sosai dan kusan a 6angarena suka wuni ranar sai nan nan yake dasu kamar wasu yaran goye.
Washe gari 'yan jalingo suka tafi suma bayan sun shigo har 6angarena suma, tundaga randa aka kawoni bansake zuwa 6angaren mamaba bamma gantaba.
Wanan yasa nayima doctor tsogumi, ya ce, "nayi hakuri saboda akwai bak'i a 6angarentane amma insha ALLAHU yau zanje.
''Na ce, "to shikenan..........✍🏻









💕💚💕









Page ......9⃣.

.............Yau 6angaren mama mukaje cin abinci sa6anin da damukeci a 6angaren yayansa.
Muka shiga da sallama.
Tana zaune akujera mai zaman mutum biyu, k'yak'yk'yawace itama fara tas, tana matuk'ar kama dasu doctor, idan bama kasaniba saikace itace ta haifesu.
cikin fara'a taďago tana amsa mana sallamar, ta ďora dafaďin lale da ďiyata, zonan kinji.
Cikin jin kunya nak'arasa wajenta, kusada k'afafunta nazauna, na ce, "ina yini?.
Ta amsa da lafiya lauw ďiyata ya bak'unta?".
Nayi murmushi batareda na amsaba, suma sauran suka gaisheta.
Bayan an gama gaishe gaishe muka ci abincin rana anan, sanan muka dawo falon aka sake zama.
Doctor ya ce, "Saudat".
Na ce, "Na'am".
Ya gyara murya to kinga family ďina kamar yanda na sanar dake abaya, kuma kema yanzu kinzama 'yar cikin wannan family ďin.
Da farkodai ga mahaifiyarmu wadda muke kiranta mama, ya nunan yayansa wanan kuma shine yayana Mansur, muna kiransa yaya, wanan itace matarsa ina kiranta aunty, yanuna matarnan dabatiminba.
Yacigaba waďanan kuma sune yaranmu Hadeeza da Marwan.
Dan haka ina rok'onki ki girmama family ďina kamar yanda kike girmama naki, gaba ďaya family ďina suna sonki suna farincikin kasancewarki acikinmu.
Kaina yana k'asa na ce, "insha ALLAHU zaka sameni yanda kake buk'ata, kuma nima inason family ďina nabiyu, nayi alk'awarin zan zauna da kowa lafiya, kuma ina matuk'ar farincikin kasancewa daku nima.
Ya ce, "to Alhmdllh".
Nakula dukansu maganata ta burgesu, musamman dasukemin kallon k'aramar yarinya mara wayau, amma sai sukaji zance raďam kamar wata babar mace.
Mama ta ce, "mungode ďiyata ALLAH yay miki albarka kinji, yakuma bamu zaman lafiya da zuri'a ďayyiba.
" Duk suka amsa da amin".
Amma bandani.
Yaya ya ce, "to aini duk abinda zance kunriga kun faďa, saidai na ce, "ALLAH yabamu zaman lafiya.
Nanma akace amin".
Aunty kam batace komaiba, da doctor ya ce, "auntynafa mizakice??.
Ta ce, "a'a ni banida abin faďa, wanda kuka faďa yawadatar.
Nakula kamar maganar bataima kowa daďiba, musamman yaya, deexerh ma baki naga ta ta6e tareda gallama aunty harara.
Daganan hira aka cigaba dayi, wadda sukaďai suke abinsu bandani, itama auntyn saita gadama take saka baki.
Munďan daďe muna hira daga baya suka tafi sallar la'asar, nima muka tafi 6angarena nida deexerh.
Inason deexerh kasancewarta k'yak'yk'ya nutsatstsiya, gata alamunta suna nuna mai hak'urice da kawauci.
Muna idar da sallah muka dawo falo domin yin kallo, muna nan zaune doctor yadawo, yashigo da sallama muka amsa.
Kusadani ya zauna yana faďin kundaiyi sallar ko?.
Atare muka amsa da eh munyi.
Ya ce, "masha ALLHU".
Namik'e nakawo masa ruwansha, cikin murmushi yakar6a yana faďin ALLAH yay miki albarka.
Na ce, "amin ngd".
Deexerh ta shagwa6e fuska, uncle anbamu aikifa tun wancan satin, kuma gobe idan ALLAH yakaimu za'a amsa, nikam nakasa yin nawa.
Dictor ya ce, "haba my daughter keďin aiba abinda zai gagareki saboda nasan kwakwalwarki akwai jaa.
ALLAH uncle bawasa nakeba.
Okey, tojeki ďakko nagani.
Da gudu tafice daga falon, yayinda shikuma yadawo kujerar dana koma, yazauna kusadani tareda rungumoni zuwa jikinsa.
Ina masifar son turaren doctor dan haka nak'ara kwantar da kaina ajikinsa ina shak'a.
Shikuma yasake nutsani sosai a jikinsa, ahankali yafurta my iman ina k'yaunarki dayawa wlhy.
Nima na ce, "ina k'yaunarka doctor.
Da sauri yaďago fuskata yana kallo, yak'ara k'ank'ance idanunsa yana k'aremin kallo kasa2, da gsky Imaniiii!!!??.
Yanda yaja sunan nawa saida tsigar jikina tatashi.
Na ďaga kai ahankali".
Yasaki k'ayataccen murmushi, ashe yau zaki amince mukwana gado ďaya kenan?, saboda na nuna miki tsantsar k'aunarki dake kwance acikin jinina da zuciyata.
Kaďan naďago ina kallonsa, na maida kaina da sauri dan ganin ya kafamamin idanunsa......ahankali ya matso da fuskarsa kusada tawa danufin bani sumba sai deexerh tashigo ďakin.
Yay saurin janye fuskarsa yana 'yan kame2 narashin gsky, yabani dariya amma saina gimtse nima nayi saurin tashi daga kujerar na canja wata.
Deexerh tak'araso kusada shi ta zauna ta bashi littafin nata.
Kar6a yayi yana satar kallona, nikam kaina yana k'asa.
Bayan yagama dubawa ya ce, "my dee....bari nagaya miki kiringa rubutawa, babu musu deexerh tayarda dan kwakwalwar tata tanaja yanda yakamata.
Ina zaune ina kallonsu yana faďa mata tana rubutawa har suka gama, yakar6a yagyara mata inda batayi daidaiba.
Ya ce, "wai ina Marwan?."
Deexerh ta ce, "yana ďakin mama uncle barci yakeyi.
Barci da yammarnan haka?.
Ta ďaga kai alamar eh.
Baice komaiba yamik'e yashige ďakinsa, mukuma muka cigaba da kallo.

Haka rayuwar take tafiya, ina gidansu doctor amatsayin amarya amma ta nesa, dan babu wata alak'a dake tsakanina dashi.
Har yanzu bana shiga kicin aunty take mana girkin gidan itada 'yan aiki.
Komai na rayuwar gidan yana tafiya yanda yakamata, saidai matsala ďaya nake fuskanta itace auntynsa, nakula ko kaďan bata sona agidan, tana nunamin abubuwa dayawa kawaidai ina sharewane.
Kuma banta6a faďama kowaba, dan ba itabace agabana.
Ana cikin haka kiran gaggawa yasamu doctor awajen aikinsa, dan haka yashirya yatafi badan yasoba.
Ranar dazai tafi harda kuka nayi kashir6an mama na lallashina.
Bayanda zanyi dole na hak'ura, deexerh tacigaba da tayani kwana, kodayaushe muna tare, dan haka shak'uwa ta musamman tashiga tsakanina da ita.
Kullum kuma sai munyi hira da dictor ta waya indai yasamu lokaci kunsan soja sai ahankali.
Wani abin mamaki shine tunda nazo gidan banyi al'adaba, dan haka babu zancen ciwon mara.
Hakan yayimin daďi, duk wata kuma sai doctor yatanbayeni, cikin jin kunya nake cemasa banyiba.
Ana haka doctor yadawo a safiyar wata juma'a.
Babu wanda yafaďama zaizo saidai muka gansa kawai, munyi farinciki sosai da ganinsa dan watansa na uku kenan da tafiya.
A6angaren mama ya ara sauka.
Sai bina da kallo yake cikin mamaki dan ganin nayi k'iba kai harma da k'ara tsawo.
Nikam duk kunya ta dabaibayeni dan ganin irin mayen kallon da yake bina dashi ko kunyar mama bayaji bare aunty..
Bayan angama gaishe2, yaci abinci yak'oshi, sannan yamik'e yana faďin mama bari naje nayi wanka na huta kafin lokacin masallaci.
Mama ta ce, "to auta afito lafiya.
Aunty ta ce, "nibazakamin sallamaba kenan, ko kallonta baiyiba yafice daga falon mama yana faďin ke asuwa kuma?.
Dukda ta dake nasan maganarsa ta 6ata mata rai.
Mama ta kalleni iman tashi kije wajen mijinki mana.
Akunyace namik'e nafice, dan dama kunyartace ta hanani bin bayansa.

Kutashi muyi sallah ko sisters.
Xoxo da Reefat suka mik'e kowa baiso aka katse labarinba.
Amma damun idar da sallah zakicigaba ko??, xoxo tafaďa tana bin iman da kallo.
Insha ALLAHU my hafsy zan cigaba damun idar..................✍🏻









Am busy 😂👌🏻










Luv u oll my fan's
((S))......2017
Battery low 🔋😁👌🏻

.a
[8/6, 6:00 PM] mrs bilkisu: *_________________________________*
*BAN SAKETA BA*
*__________________________________*
*NA*
*BILKEESA IBRAHEEM*
*{bilyn Abdul}*
*___________________________________*
https://mrsbilkisa.blogspot.com






_Sadaukarwa_~*ya Abdul {city phone's}*




*MIYA KAMATA NAYI??.*
_amatsayina na *MUSLIMI* baidace daniba nashagala da duniya da abinda kecikinta, a *DUNIYA* ake neman lahira, to tayaya zan nemi tawa_ *LAHIRAR?*.
_mun shagala aduniya, kalon *FILM* karatun *NOVELS* awaya zuwa *biki*.......da sauransu sunsa mata dayawa mantawa da zan *MUTU* na riski *"UBANGIJINA"* ya salam, 'yar uwa ringa tunawa da mutuwa mai zuwa babu ďan aike, ringa tunawa da *sallah* ringa nafila, zikiri akowace rana, karkibari nishaďin duniya yasaki dana sani awata rana mai cike da *hargitsi,* tsarama kanki lokaci yanda ke da mijinki da 'ya'yanku zaku amfana, a duniyarku da lahirarku, duk wanda yay asarar *aljanna* amatsyinsa na *musulmi* to dolene atayashi kuka da jaje_.
_muhaďu agaba domin jin yanda yakamata ki tsara_ *Duniyarki 'yar uwata*_domin keda *zuri'arki*ku amfana_ *a lahirarku*
*ALLAH yasa mugane*.




~page.......~1⃣0⃣.

*............*da sallam nashiga falon babu kowa alamun *doctor* yana cikin _bedroom_ kenan.
Dukda inajin kunya wannan bai hanani nufar ďakinba, nashiga da _sallama_.
Yana tsaye atsakiyar ďakin yana k'ok'arin cire kayansa, yajuyo ahankali yana kallona, nikam nayi k'asa da kai saboda kunyarsa danakeji.
Yasaki _murmushi_ mai k'yatarwa, ahankali ya ce, " *my iman* k'araso mana.
Nak'ara k'asa da kai saboda kunya, na ce, "bari naje falo idan kagama saina dawo, wlhy bammasan kana shirin wanka bane.
Takowa yayi cikin takun k'asaita har inda nake tsaye.
Nikam jinake tamkar na zura da gudu, amma babu dama.......kusantowarsa gareni tasa na ďago da sauri muka haďa ido.
Nai saurin maida kaina k'asa.
Baice min komaiba sai kama hannuna dayayi muka k'arasa cikin ďakin sosai.
Ya zaunar dani abakin gado sanan yacigaba da cire kayansa.
Araina na ce, "waishi doctor baisan inajin kunyarsa bane?.
Ina nan zaune harya gama cire kayansa, ya k'araso yazauna kusa dani dagashi sai gajeren wando.
Yaďan rungumoni jikinsa yana magana ahankali tamkar mai raďa ko baisan tada yaro mai barci.
_farin cikina abar alfaharina, har yanzu kunyar tawa bata k'arebane?_.
Maimakon nabashi amsar tambayarsa sainace kadawo lafiya?.
Yakama hannuna danake wasa dashi yaďan matsa, naďago da sauri ina kallonsa dan naji zafi.
*Ya ďaga min gira*
Miyasa baki bani amsar tambayataba??, saikika sakko taki tambayar??.
Nayi murmushi wanda yakeso yaga nakasance akoda yaushe inayi, amma ina niďin _muskilancina_ bazai barniba.
To kayi hak'uri nafaďa atak'aice.
To nahak'ura *saudat* nasameku lafiya?.
Lafiya k'alau.
Ya aiki?.
Aiki *Alhmdllh* saidai kewarki da begenki sunta addabata musamman alokacin barci.
Ban bashi amsabama yanzu.
Ganin haka yasa yasake matseni sosai ajikinsa, saikuma nafara masa rawar jiki, nakan bashi mamaki idan yaga nashiga wani hali alokacin daya haďani da jikinsa, amma saiya basar.
Yamik'e tareda mik'ar dani tsaye, zomuje ki haďamin ruwan wanka.

Bayan gama haďa masa ruwan wanka na ce, "nagama.
Kafin ya ce, "wani abu nafice.
Rakani yayi da wani shu'umin kallo, ala66ansa yafurta iman kinkusa zuwa hannu aii, kunyar nan tana cutata dayawa.
Bayin yashiga yayi wanka yafito, dashirin kwanciya yafito amma sai yaga lokaci yatafi kasancewar yau _juma'a_ shirin masallaci yayi cikin jar shadda sai maik'o takeyi.
Ya murza bak'ar hula da bak'in agogo, turarensa na kullum ya fesa, tunkafin yafito k'amshinsa yayo gaba.
Na tsurama k'ofar ďakinsa idanu, yayinda yafito aisai naga tamkar ba *Dr Isma'il* ďinaba, yayi kyau harya gaji.
Sosai na dasa masa idanuna ko k'yaftawa banayi.
Jinai anhuremin ido".
Na sauke nannauyar ajiyar zuciya, tareda cusa kaina cikin cinyoyi saboda kunyar yakamani ina kallonsa.
Kusadani yazauna yana dariya da faďin ďago abinki ki kalli _mijinki_ matana, niďin nakine ke kaďai.
Ina nakasa ďagowa saboda ba k'aramar kunya najiba wlhy.
Da kansa yaďagoni yakuma rik'e fuskar tawa tamau atafin hanunsa yanda bazan iya kwacewaba.
Rintse idona nayi dan bazan juri haďa ido dashiba, shikam yadasamin mayun idanunsa tamkar yau yafara ganina.
Yakai tsawon minti biyar yana kallona.
Ban fargaba naji bakinsa cikin nawa, cikin kwarewa yake sumbatata, ban hanashiba domin nima inajin daďin hakan dayakemin, *kunsandai SO yanda yake, yakansa ka aikata abinda bakayi niyyaba*
_dan so yahaďu da so, sai ahaďu asoye tare_
Munkai tsawon minti ashirin ahaka, doctor yana abuďaya, saida yayi mai isarsa sanan yazare bakinsa ahankali yana maida numfashi, fuskarsa cike da *annuri na musamman*.
Yaji daďin yanda yau natayashi abinda yakeso.
Saidai ni kaina nayik'asa ina fidda nawa numfashin ahankali.
Wata sassanyar dariya yasaki akunnena, cikin sigar *Salon so* ya ce, "lallai my iman kin fara haddace karatun aure.........
Bai k'arasaba marwan yashigo shima cikin shirin masallaci, doctor ya hararesa koma kayi sallama.
Marwan ya narke murya *ALLAH* Uncle nayi bakujibane kawai.
Banason k'arya".
*ALLAH* kuwa marwan yaske faďa kamar zaiyi kuka.
Na ce, "yayi sallamafa.
Ya maido da kallonsa gareni, kinji kenan?.
Kai naďaga batareda nayi maganaba.
Yay k'asa da murya, kece kika rikitani har nakasaji nakasa gani, *INASONKI DAYAWA SAUDAT*.
ajiyar zuciya nasauke ahankali, yayinda shikuma yamik'e yana kama hannun Marwan.
My boy ya akayi?".
Marwan ya ce, "daddy ne yadawo shine na ce, "bari na sanar dakai.
Okey my son muje.
Saida suka kai k'ofa sanan yajuyo ya ce, "idan kinjishiru munwuce masallaci.
Kaina ak'asa na ce, " *ALLAH* yatsare, yadawo daku lafiya.
Amin mungide yafaďa yana fita.

Dr da Marwan suka nufi 6angaren yaya, da sallama suka shiga.
Yayansa yana zaune shima cikin shirin masallaci da alama su yake jirama.
Yamik'e da sauri tareda warema doctor hannu, alamar yazo.
Aiko da sauri yak'arasa yashige, suka rungume juna da faďin kewar dasukayi na nisantar ruhinsu.
Yaya ya ďago kan doctor suka haďa ido suna sakarma juna murmushi, autan mama *soja* kuma *likita*, katafi kabarmu da kewarka ko??.
Kuyi hak'uri yaya wlhy nima nayi kewarku, duk son danake nazama *soja* yanzu sainaji yafita kaina.
Yayansa ya nunasa yana dariya anya kuwa zan yarda dakai Isma'il??.
Dr yayi dariya, wlhy gsky nake faďama yaya.
Rungumesa yayansa yaskeyi saboda jin daďin maganarsa.
Aunty ta balla musu harara batareda sun ganiba, azuciyarta ta ce, "naga *rai da mutum,* k'arewar 'yan uwantaka.
Amma afili saita ce, "zakuyi missing ďin sallaffa Abban deexerh, dan ďaya harta kusa.
Da sauri suka saki juna suna kallon agogo.
Tak'araso tana salo ta fesama yaya turare tareda ďora masa hularsa akai.
Ya ce, "ngd gimbiyata.
Murmushi tayi masa, sanan tajuyo ga doctor zata fesa masa turaren, amma saiya kauce da sauri, yana faďin a'a wanda matata tasamin ya wadatar.
Dariya yaya yamusu ya ce, " *ALLAH* yashiryaka Isma'il, kazama mara kunya dai.
Fita doctor yayi yana dariya.
Gaff sukai karo da mutum abakin k'ofa.
Yaďago da niyyar masifa amma saiyayi shiru dan ganin wadda sukai karon.
Suduka sun k'urama juna ido cikin wani yanayi wanda bakowane zai iya fassarawaba,
Bawata bace illah *Raihan* k'anwar aunty Sadiya, matar yayansa.
Shine yafara janye nasa idon akasalance, itako Kallonsa take tamkar zata cinyeshi ďanye.
Yadaure ya ce, "Raihan kece a kanon mu yau??.
Tasaki dariya cikin salo ta ce, "eh wlhy *yaa Isma'il*.
Ya ce, "sannunki dazuwa to, yafaďa yana k'ok'arin kar6ar k'aton akwatin hannunta, wanda yanuna da shirin dogon zama tazo garin na kano.
Taďan janye tana faďin haba yaa Isma'il aiiba girmanka bane.....
Kafin yabata amsa yayansa yafito yana faďin kaidawa auta.......?
Maganarsa ta kakare dan ganin Raihan tsaye da kaya nik'i2, wata 'yar fara'a yasaki maikama da yak'e, a'a Raihan kece tafe??.
Ta ce, "eh yaya, ina

Please Login or Register in order to submit comment