Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai kufce mata alokacin datake buk'atar zama taredashi.
Yaya ya katse mata tunani da fad'in saikumuje k'yamis kukuma Dan tabbas akwai wani babban Abu da kuka aikata ga Isma'il, kowa yasan hak'uri irinna Isma'il, amma har kuka kaisa mak'ura...... Aunty ta bud'e baki zata fara rantse2 yadaka mata tsawa, bana buk'atar jin komai daga bakinki harsai Isma'il ya farka.
Shiru tayi Dan tasan halinsa zaiyiya k'ara mammaujeta ne.
Marwan kam sai hararsu yakeyi, dama haushi suke bashi.

A6angaren iman kuwa komai Normal, bayan taraka Xoxo tadawo tahad'a wankin gwaggo da musayeef tanayi musayeef yana tayata konace yana wasan ruwa.
Tana gamawa tayima musayeef wanka suka shige d'aki, wasa suketayi tana biye MASA sunata dariya cike da farinciki, yau tunda tatashi takejin wani irin nishad'i na musamman Wanda ita kanta batasan na miyeba, jitake tamkar an sauke mata wasu kaya masu nauyi aka.
Suna cikin wasansu duksun hargitsa gadon gwaggo talek'o, oh ni ALLAH ya shiryeku, kaidai ka maida uwar taka kamar wata kakarkama.
Nidai kutaso kuyi mama girki da wanan shashancin.
Iman tayi dariya to gwaggo.
Fitowa tayi tana dariya Musayeef nabinta waisaita MASA goyo, tsugunnawa tayi ya d'ane bayanta suna dariya, ahaka suka Shiga kicin , gwaggo tabisu da kallo tana murmushi, ta d'aga hannu sama tana fad'in Ya ALLAH ka kawo farinciki da alkairi a rayuwar wanan yarinya da d'anta, ALLAH ka bayyana gsky itama takoma gidan mijinta kokuma tayi wani aunren...
*_(Araina nace gwaggo addu'arki aii tadad'e da kar6uwa😁).............._*





*luv u oll my fan's*
*(((S))).........2017*
[8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*





*_NA Bilyn Abdul_*





_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com



*Gargad'i!!!.*
_hummm namiki magana karki k'ara sakani group dabai daceba kink'iji ko?, wlhy idan kika k'ara kaini Group na iskanci kowanda aka danganta dawani Abu sainaci.......humm bana zagi, amma tabbas zakisha mamaki, banason ciki da iskanci kinjiko, banmiki kama da 'yar iskaba, Dan haka kishiga hankalinki_
_sauwajen uku ina tsintar kaina agidan banza, kuma idan naduba sainaga kece kika kaini, nafarko namiki nasiha k'ink'iji, nafita anabiyu bantankakiba, yanzu kinkaini na uku, to wlhy ana hud'u ubanki zanci, bazan fad'i sunankiba amma kinsan kanki, kuma kika k'ara zan yayatakine wlhy._
_Kikama kanki kafin watan cin ubanki yatsaya, shaid'aniya kawai maikafa gidan banza mtsooooww._
*idan kunne yaji👉🏻😡*





*(page 30)*
Gaba d'aya ahalin gidan suna falon mama, kowa yayi jigum jugum Dr Isma'il kawai ake saurare, ya share kwallan dasuka cika MASA ido tareda cije le6e.
Yaya ya ce, "isma'il kayi hak'uri kasanar mana abinda ke faruwa, gaba d'aya kunsakamu aduhu wlhy.
Dr Isma'il yawatsamasu Raihan harara tareda girgiza kai, idonsa yak'ara cikowa da kwalla yanuna aunty Yaya dama matarka itace silar shigata Matsala arayuwa, itace ta rabani da farincikina matata.
Haba sadiya minayi miki?, mina tare miki agidanan?, mi saudat tayimiki ne haka da zafi?.
Tunda yafara maganar suke binsa da kallon ikon ALLAH, su kalleshi su kalli su Raihan, mama ta ce, " Isma'il bamufa ganeba har yanzu.
Raihan ta fashe da kuka wlhy mama nidai ba laifina bane aunty CE tace muyi haka, amma ALLAH bani baceba, Dan ALLAH ya Isma'il karka sakeni INA Sonka wlhy, rashin mafitane yasa na yarda da shawarar aunty alokacin...... Wata razananniyar tsawa Dr Isma'il yadakama Raihan, walhy kokimin shiru kona shak'eki kimutu!!!!!.
Yaya Yakama hannunsa yamaidashi zaune, ya ce, "Raihan fad'a mama mike faruwane?.

*_Tuna baya_*
Kamar yanda kuka sani munso juna da yaa Isma'il sosai bayan bikin aunty da Yaya, harma anyi maganar aurenmu amma Mamana ta ce, " bata yardaba baza'a had'a mata yara agida d'ayaba, dagani harashi. Mumshiga damuwa har aka hanani zuwa gidanan gaba d'aya.
Bayan kamar shekara uku da faruwar haka sainaji auren yaa Isma'il dawata baniba, hankalina yatashi matuk'a amma babu yanda zanyi na hak'ura, kowa yazo bikin daga sokoto amma bandani saboda kishi, bayan komawarsu sukaita bani labari akan Yaa Isma'il yarinya ya aura amma sun dace, wannan yasa hankalina yatashi nakira aunty ta ce, "nashirya nazo kano.
Bansamu matsalaba su mama suka barni nazo domin itama tafara son Ya Isma'il sanan, amma bansan dalilintaba.
Hankalina yatashi sosai daganin matar ya Isma'il, gakuma soyayya dayake nuna mata wadda ni ko rabinta bai nuna minba sanda muna tare, wannan yasa muka fara k'ulle k'ullen rabashi da IMAN nida aunty, mun aikata abubuwa dayawa ga iman amma bata ta6a fad'awa kowaba, inaga sai deexerh, ganin munyi2 babu nasara yasa aunty takirani awani daren juma'a.
*(" Raihan kinason Isma'il da gsk?. Eh wlhy aunty inasonsa. Kinason samunsa?. Dasauri na ce, "eh mana. Dariya aunty tayi irinta muguntarnan, tamik'omin takarda, kar6i ki karanta wannan".)*
Takardar nakar6a na karanta wadda aka rubuta takardar sakin iman, nasan rubutun ya Isma'il sosai Dan haka nad'ago da sauri INA kallon aunty, aunty kina nufin Yaya dakanasa yarubuta sakinnan?.
Kallona tayi tana murmushi, miyasa kikamin wannan tambayar?.
" aunty naga irin rubutunsa.
Dariya, tobashine yarubutaba nice nan.
Kece kuma? To tayaya?.
Hummm auta haryau ke yarinyace, bazaki ganeba, nad'au tsawon lokaci ina kwaikwayon rubutunsa hardai ALLAH yabani nasara na iya, dama saboda irin ranarnan nakoya.
Jinjina kai nayi INA mamakin kalamanta, to aunty tayaya kike gani Yaya zaiba iman takardar sakinnan?.
Aunty tayi murmushi wannan ai mai sauk'ine kedai kisaka idanu kisha kallo.
Bayan kwana uku dayin maganarnan da yamma sai aunty takirani tabani takardar wai naje k'ark'ashin filon iman nasaka, cike da tsoro nake kallonta tadakamin tsawa, ke sakara idan bazakiyiba abarsa kefa nake taimako zaki zauna kina kallona.
Jiki tana rawa na kar6a na nufi 6angaren iman, babu kowa afalon sai TV daketa 6a6atu, asand'a nashiga d'akin iman nanma babu kowa saidai naji motsin ruwa abayi alamar tana wanka, da Sauri nad'aga filon farko nasaka takardar nafita da Sauri, gafff mukai karo da Ya Isma'il ak'ofar Fita daga falo, yanda jikina ke 6ari saiya tsaya yana kallona.
Kekuma lfy?, yafad'a idonsa akaina.
Da Sauri na daidaita nutsuwata na ce, "wlhy 6era Nagano Kasan kuma INA tsoronsa.
d'an murmushi yayi yana girgiza kai, kekam keda 6era kun k'ulla, amma ta inama 6era yashigo gidanan?.
Na ce, " halan ta k'ofar baya ko.
Hakane kuma, bari zan fad'ama saudat taringa rufe wajen idan yamma tayi.
Okey bari nawuce dama nazo Neman Deexerh ne Ashe bata nan.
Tom saida safe tafad'a tana shigewa.
Dagudu na Isa 6angaren aunty na rungumeta INA dariya na ajiye wlhy ammafa ankusa kamani, anan nabata labari tayi dariya kedai akwai shegen tsorone kawai.
Shikenan matsalarmu ta k'are muka tafa.
Washe gari bayan tafiyar yaya iman tasamu takardar....... Raihan tak'are maganar da shashshekar kuka, wannan shine abinda ya faru.

Gaba d'aya falon aka d'auki salati da tafa hannaye.
Aunty da Raihan sai kuka sukeyi.

Yaya yanisa yamaida hankalina akan Dr Isma'il, ya ce, "to kaikuma alokacin miya hanaka kiran wayarmu?, miya hanaka dawowa bayan sati biyu kamar yanda kace.
Dr Isma'il yacije le6e, bayan barina gida anturamu Maiduguri, bayan zuwanmu da kwana hud'u aka harbeni a kafad'a yajanye rigarsa, hudin shigar bullet suka gani akafad'arsa, mama ta fashe da kuka, yacigaba da fad'in bayan harbi nasamu raunika sosai wannan yasa nahana akiraku Dan banason hankalinku yatashi, saida nayi jiyya ta wata biyu dawasu kwanaki, inasamun lfy nataho kano dannaga halin dakuke ciki shine natara wai matata bata gida.
Mom da mama da marwan duk kuka suke suma na tausayin Dr Isma'il, falon yayi shiru babu abinda kakeji sai shashshakar kukansu.
Mama ta ce, " kunga kutashi mutafi gidansu iman yanzunan.
Haka kuwa akayi gabad'a suka d'unguma said gidansu iman.


*Gidansu Iman*
Iman da musayeef suna tsakar gida zaune tana ninke kayansa data wanke, shikuma yana d'ebowa daga kan igiya, gwaggo tana kicin tana girkin dare.
Da Sauri iman tajuyo danjin sallama, da Sauri tamik'e Dan ganin kaf 'yan gidansu Dr Isma'il, dagudu Musayeef yaje ya rungumesu yana murnar ganinsu.
Gwaggo tafito daga kicin danjin ihun murnar musayeef, Ita kanta tatsorata daganinsu amma dukda haka saita ce, "sannunku dazuwa.
Yauwa suka amsa mata, ta ce, "kushigo.
Iman dai tana tsaye tamkar gunki, Dr Isma'il yak'araso gareta tareda kama hannunta, da Sauri ta fisge hannun takoma ta zauna, sukuma suka wuce cikin falon Inda gwaggo take musu maraba.
Bayan sun zauna suka gaisa da gwaggo, Yaya ya ce, gwaggo Abbah fa?.
Yana wajen aiki mansur ALLAH yasadai lfy?.
Alhmdllh gwaggo saidai munason ganinsa munzone dawata magana.
Babu damuwa bari akirashi gwaggo tafad'a tana d'aukar waya.
Bugu d'aya abbah ya d'auka tamasa bayani komai, ya ce, "gashinan zuwa gidan.
Gwaggo takoma kicin ta had'o musu kayan sha tadawo, har yanzu iman tana tsakar gida zaune ta rabga uban tagumi da hannu biyu.
Ita atunaninta kosunzo su k'ar6i musayeef ne, tab lallaikam Ashe yau da bala'i wlhy, Dan mairabani da yaronnan saiya shirya, wlhy koza'a kasheni bazan yarda su d'aukeshiba.
Tana cikin zancen zuci abbah yashigo, a'a iman lfy?.
Ta share hawayenta abbah Dan ALLAH karku yarda sunzo kwace musayeef ne nikuma wlhy bazan basuba.
Abbah baice komaiba Yakama hannunta suka Shiga falon ,Dan shima komai za'ayi bazai basu musayeef ba.
Bayan anyi gaisuwar mutumci da tambayar rayuwa Abbah ya CE, ALLAH dai yasa lafiya.
Lfy lay Alhaji alkairine yakawomu.
Yaya yacema Raihan ta maimaita abinda tafad'a agida.
Tiryan2 ta zayyane komai, Dr Isma'il ma ya d'ora da nashi, salati su abbah sukaitayi, itako iman kuka Rurus takeyi tamkar ranta zai Fita, wlhy ko amafarkinta bata ta6a kawo hakan arantaba yanzu dama mijinta *bai saketa ba* aka rabasu kai ALLAH yarabamu Da saharrin mak'iyidai.
Bayan maida zance abbah ya ce, " INA Neman wata alfarma agunku mansur da Isma'il harda ke mama.
Suka amsa dato suna saurarensa.
Abbah ya ce, "Dan ALLAH karku saki matanku kubarsu kawai, Haka ALLAH ya hukunta.
Arazane Dr Isma'il yake kallon Abbah, abbah ya ce, " alfarma nanema inafata zakuyi mini.
Mama ta ce, "shikenan Alhaji insha ALLAHU bazasu sakesuba.
Dr Isma'il yay wani murmushi mugunta, azuciyarsa ya ce, " wlhy sai sungwammace inama mun sakesu, Dan zasusha mamaki humyimm k'yarrrk.
Anan kuma Dr Isma'il ya ce, "yanason sutafi da iman yau.
Itako tafashe da kuka ta ce, bafa yauba.
Mama ta ce, " a k'yaleta to har sanda tasa shiya, aii bama zaiyuwuba Isma'il, kata6a ganin an raba mutum da gidansu tashi d'aya, kabarta har sai sanda ta shirya,....... A'a abbah ya katseta, insha ALLAHU nanda sati d'aya ko kwana goma zata dawo d'akinta shima nace hakane saboda shirye2.
Dr Isma'il ya ce, "abbah kardai asayama iman wasu kayan d'aki tunda ba'a kwaso wad'ancanba, insha ALLAHU awanan karon nizanyi komai, iman kawai da musayeef nake buk'ata.
Shike nan Isma'il ALLAH yayi muku albarka.
Iman tashi tayi tashige d'akinta tana hawaye, Dr Isma'il yabita da kallo.
Gado tafad'a tana kuka, wai Ashe Doctor yak'ara aure bata saniba, dama Ashe Raihan budurwarsa CE ya6oye mata, kuka take sosai, wlhy badan kar iyayenta sauce ta rainasuba da babu Inda zata, dabazata koma gidansaba saidai ya saketa kuwa, haka taita kuka zuciyarta na k'una saboda kishi, sai yanzu tagano canjin dayay mata.

Dr Isma'il kam badan yasoba yabi su Yaya suka tafi, yaso ace ayau aka bashi iman suka tafi tare, amma yazaiyi dolene yabi Maganar many a...............







*luv u oll my fan's*
*(((S)))..............2017*
[8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*






*_NA Bilyn Abdul_*




_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com



*miya kamata nayi?*
_humm hattara 'yammata rayuwar kece raini had'ari CE, duk Wanda yace shi wani ne, kosai yazama wani, tofa yana tareda wahala arayuwarsa._
_wanan rayuwar tana bala'in wahalar da 'yammata da matan aure, abinda wance tayi nima sainayi kota halin k'ak'a, hakan ba daidaibane, wanan rayuwar tana jefa mata dayawa fad'awa zina mad'igo kowani mummunan yanayi, burin sainafi wance kosaina tarar da wance yajefa matan aure dayawa bin maza._
_haba 'yar uwata miya rud'eki saboda San duniya kiringa zina da aurenki?, shin kinmanta da d'unbin zunubin dake bibiyarki ga cin amanar Addininki, cin amanar aurenki, ga cin amanar 'ya'yanki, ga cin amanar iyayenki, ga cin amanar 'yan uwanki._
_tsaya matsayinki domin haka ALLAH yayimu wani yafi wani, indai zaka ringa kallon na sama dakai to kanatare da wahala da asarar rayuwa kuwa._
*ALLAH yasa mugane*





*(page 31)*
Haka iman tawuni ad'aki tana kuka, da musayeef yaje wajantama koroshi tayi, yafito yana kuka, gwaggo ta ce, "lfy na gwaggo?.
Aunty maa ce takoroni wai na 6ace mata dagani anan.
Jawoshi gwaggo tayi jikinta tana share masa hawaye, kaga ishirunka yau aunty maa batada lfy ne, kabarta ta huta, kaji na gwaggo.
Kai yad'aga alamar to, yauwa na gwaggo, Abbah yafito daga d'aki yana shirin fita, a'a Na gwaggo lfy dai ko?.
Shida mamansane, kasan iman da zuciyar tsiya.
Murmushi Abbah yayi, yakama hannun musayeef kaga muje karakani anguwa.
Tsalle musayeef yafarayi na murna, suka fice shida abbah, gwaggo kuma tanufi d'akin iman.
Kwance take akan gado idonta arufe amma hawaye sunata zirara, filon duk yajik'e alamar tadad'e tana kukan.
Gwaggo ta girgiza kai tareda k'arasawa Inda iman take, bakin gadon ta zauna tad'ago da kan iman tamaida kan cinyarta.
Batayi maganaba amma tana shafa kan iman tareda d'an bubbuga bayanta alamar lallashi, sunkai tsawon minti15 ahaka, har iman tayi shiru saidai ajiyar zuciya datake saukewa ahankali.
Gwaggo ta ce, " haba iman miye kuma abin kuka muda yau abin farinciki ya riska, kinsan kuwa yanda muke farinciki nida abbahn Ku?, kobakison komawa ne?.
Da sauri iman ta gyad'a kai.
Humm to saboda mi?.
Gwaggo yafariga ya k'ara aure, gwaggo tayi murmushi, yo iman Dan isma'il yak'ara aure shine bazaki komaba?, kowa bada halinsa zai zaunaba agidan, karki mantafa yanada hurumin auren mata hud'u fa.
Nifa gwaggo bawai ina nufin haka bane, wlhy ina tsoron abinda zaije yadawo, tunkafin tazo gidan suka iya fiddani balle yanzu tana cikin gidan amatsayin matarsa.
Gwaggo ta ce, "hakane iman, nidai abinda nakeso dake kizama mai yawan addu'a da Neman kariyar ubangiji, kid'auka abinda yafaru a baya yana cikin k'addararki, jiyanki tawuce yanzu gobenki zaki tsunkanya, fatana kiyi nasara a gobenki da jibinki, amma ta yaya?.
Ta sanadin hak'uri da yawan juriya akan lamarin rayuwa, indan kika rik'e k'yautatawa da biyayya tsafta tattalin mijinki da 'yan uwansa ina mai tabbatar miki kece mai nasara insha ALLAHU.
Isma'il yana sonki karki manta asanadin rashinki yakamu da ciwo mai ban tsoro, Dan ALLAH ina rok'onki karki maida hannun agogo baya, nasanar da 'yar uwarki tanata murna itada mijinta, muma gamu muna cikin farinciki, haka family d'in Isma'il suna cikin farinciki, mizaisa kebazaki kasance a farincikiba?.
" kebak'ya buk'atar farin cikinmune?, kobaki so musayeef yarayu agidansu cikin 'yan uwansa, wanan yawon da'ake dashi bashida wani fa'ida".
Ina buk'ata gwaggo, iman tafad'a tana share hawayen idonta.
Yawwa 'yar albarka toki kwantarmin da hankalinki kinji, kizama mai tawakkali arayuwa, kefa yanzu uwace, idan kina saurin karaya arayuwa yaza'ayi ki k'arfafama musayeef gwuywa shikuma?.
Kinutsu kicigaba da walwalarki, kinga nanda kwana goma abbahn Ku yace zaki koma, to yakamata mufara shirye2 Dan yanzu bake kad'ai baceba.
Itadai iman batace komaiba sai kai data d'agama gwaggo alamar to.
Haka gwaggo tayi ta mata kalamai masu dad'i harta saki jikinta.


Su Dr Isma'il kuwa suna zuwa gida yanufi 6angarensa, Raihan madai ganin kowa yanufi NASA 6angaren yasa itama jiki a asanyaye tabi bayan Dr Isma'il.
Afalo ta iskeshi zaune saman doguwar kujera, yajingina bayansa da kujera Kansa Asama idanunsa alumshe sai faman murmushi yakeyi.
Tayi tsaye tana kallonsa, jitake wani bali'in sosa yana k'ara ratsa sassan jikinta, tamkar taje ta rungumeshi haka takeji, amma babu dama.
Gwuywa a sa6ule taje gabansa ta durk'usa, muryarta narawa ta ce, "yaa Isma'il!.
Yanajinta yay shiru, amma ya daina murmushin dayakeyi.
Takuma fa d'in my One!.
Ak'ufule yad'ago ya ce, " a'a uban my one, yanunata da d'anyatsa "k kishiga hankalinki wlhy, idan kika k'ara kirana da wanan sunan sai jikinki yayi tsami, kuma tun wuri ki 6acemin dagani kafin na 6a66allaki na 6allah banza.
Da Sauri ta mik'e tabar falon tashige d'aki tana hawaye.
Yarakata da wata uwar harara, yana tsaki ai bama kiyi kukaba yariya sainan gaba, saikince inama sakinki nayi yafimiki alkairi, yamaida kansa ya kwanta, kiran Dr Nabeel ne yashigo wayarsa, yad'aga suka gaisa.
Isma'il ya jikin?.
Da sauk'i d'an uwa, wai kasan miya faru kuwa?.
A'a saika fad'a cewar Dr Nabeel.
Labarin duk abinda yafaru yabashi, Al'ajabi da mamaki suka cika zuciyar Nabeel, ya ce, " lallai nayarda kaidin mata yafi na shaid'an, irin wananan k'ulli haka, amma miyasa Abban Iman yahanaka sakin banza?, aii daga ita har yayarta sun cancanci saki wlhy.
Humm karka damu Nabeel wlhy saisun gwammace mun sakesu da zamansu atare damu, nikad'ai nasan abinda nake shirya musu zasuci ubansune aii, kaidai zakasha labari.
Nanda kwana goma iman zata dawo, ka saurari zuwana gobe idan ALLAH ya kaimu.
To shikenan ALLAH yakaimu goben saikaxo, Nima zan lek'a gidansu Hafsat ne, wlhy harnayi kewarta.
Humm mutumina kaimafa kashiga dayawa.
Dariya Dr Nabeel yayi, bama kasan nashigaba sai hafsat tazo gidana.
To ALLAH yakaimu lokacin, aii gara mu aurar dakai muhuta da tuzurancinka.
Hhhhhh zan rama sai iman tadawo.
Zadai karame na hafsat.
Wayar suka yanke kowa yana dariya.


*bayan kwana uku*
Dr Nabeel yabama Xoxo labari, Dan haka tazo har gida tak'arajin bayani, tayi farinciki, takumayi bak'incikin Auren Raihan da Dr Isma'il yayi, amma zata bar gidanne da k'afarta wlhy.
Xoxo tabama Umma labari, lamarin ya girgiza Umma sosai, kuma tad'au aniyar gyara iman Dan jinta take kamar Xoxo, har gida taje tarok'i gwaggo da abbah suka bata iman ta taho da ita.
d'aki guda aka ware mata, gyara na rikita guys ake mata, bata fita ko k'ofar d'aki, duk abinda take buk'ata Xoxo take mata.
Humm masu karatu kunga kuwa yanda iman takoma, abin sai Wanda yagani, dolenefa mace ta rikice balle namiji, (nace humm su Dr Isma'il za'a🙊 baridai nayi shiru).

To a6angaren Dr Isma'il mafa gyara sosai akema 6angarensa, Dan yayansa ya ce, "shine ya cancanta yayi komai, ALLAH sarki Yaya da ana samun yayye irinku da k'anne bazasuyi kukaba, gaba d'aya gidan ansake MASA fenti tamkar za akawo sabuwar amarya, Raihan da Aunty sunata kallon ikon ALLAH, _(lallai zakaran da ALLAH yanufa da cara, ko ana mazuru ana shaho saiyayi)._
Suna cikin tashin hankali kam, Dan yanzu babu mai kulasu agidan, sunzama tamkar mujiyoyi, yaya ma dayake mutumne mai zuciya, haryau baicema Aunty komaiba, ammafa yadaina Shiga d'akinta, baya amsa gaisuwarta, ko kallo bata isheshiba dama yagaji da mugun halinta, idan yashiga 6angarensa yaganta afalo zaune d'auke kai yake kamar bai gantaba, idan tashiga d'akinsa ya korota.
(Tashiga tashin hankali, gara ace yazaunar da ita yay mata masifa akan shareta d'in dayakeyi yanzu).
Suna zaune itada Raihan sun zabga tagumi.
Raihan tashare hawayen dasuka cika mata idanu, aunty yanzu yakike ganin zamuyi, nifa wlhy har yanzu inason ya Isma'il, gashi yanzu yace ko shigowa yayi yaganni afalo wlhy saina gane kurena, kina ganin yanzu andaina cin abinci damu, babu mai mana magana agidanan, aunty kinsakamu amatsala munshiga uku mukam, munzama mujiyoyi.
Aunty ta ce, "humm Raihan kenan, nifa d'azu marwan marina yayi wlhy,.
Marifa kikace?, marwan d'in?.
Wlhy kuwa Raihan, kuma babu damar ramawa bare nad'au wani mataki, nifa sonake kawai Mansur yasakeni.
Kai aunty kidaina manager fatan saki wlhy, k'ila nangaba su hak'uri, kinsandai zaman sokoto d'innan bawani dad'i bane, ko abincin arzik'i babu.
Nima abinda nake hangowa kenan Raihan shiyyasa d'azu na k'yale marwan.
Mucigaba da hak'uri akan duk abinda ZAMU gani watarana sai labari aii.
Shikenan ALLAH yabamu ikin jurewa.
*(ni bilyn Abdul na ce, " humm, jurewar nan dakamar wuya, musamman idan Deexerh tadawo, ah ah ah,)*

Marwan ya Sanar da deexerh komai Dan haka tak'agara su gama Exam ta taho gida, ita kad'ai tasan muguntar data shirayama k'ananan 'yan iskannan, gashi takira wayarsa Iman akashe, Dan haka ta hak'uri tabar komai saitazo gidan.
Iman kam tanajin gyara wajen ummansu Xoxo, aunty Salma tana aikawa da nata agefe, itamadai gwaggo tana bada gudummawa sirrinsu na manya, Xoxo da iman ma suna 'yar tasu fasahar dasuka sani,
_(nace humm zafa Ku haukata Dr Isma'il)._
Shi hankalinsama atashe yake, Dan saikiran wayarta yake akashe, arikice yazo gidansu gwaggo ta ce, "aii batanan, d'aukar Musayeef yayi suka yafi gidan aunty Salma, nanma akace MASA batanan,.
Aunty pls.... Karku haukatar dani Dan ALLAH tana ina?.
A'a k'anina bazaka haukaceba, iman sunyi tafiya da hafsat, amma insha ALLAHU zasu dawo nanda kwana hud'u.
Aunty nanda kwana hud'ufa kikace, randa iman zata koma gidana.
Hakane insha ALLAHU.
Kai Dr Isma'il yadafe, yana fad'in wayyoni ALLAH na.
Aunty tayi dariya, to kwana hud'u aii kamar yaune insha ALLAHU, daga nan ba kayarka za'a maida makaba.
Dariya ya Majeed yayi, kai abokina kadafa kayimana kuka wlhy, irin wanan damuwa haka, idan sak'one kawo nabata.
Dr Isma'il ya hararesa, aii nama lura hardakai aka kulla 6oyeta.
Hhhhhh yanzu kuma kaina zaka dawo, to bazadai mu bayarba sainan da kwana hud'u.
Tashi Dr Isma'il yayi yasa6i musayeef dayayi barci akafad'a, aii shikenan zan rama Nima, nabarku lfy.
Dariya sosai aunty Salma da ya majeed suke masa, shima Fita yayi yana dariyar.

*RANA BATA K'ARYA*
yaune wa'adi yacika, tunda sassafe akadawo da iman gidansu, gwaggo sai latsa jikin iman takeyi cike da mamaki, iman kin canja mi umman hafsat d'in tarink'a bakine haka?, kai ALLAH yasakama wanan baiwa da Alkairi, ALLAH yasa munada Rabon ganin bikin hafsat haka.
( Na ce, "amin gwaggo).

Dukda Dr ya ce, " kar a kaita da komai, saida aka k'ara siya mata kayan kicin Nagani na fad'a, ga d'inkuna sababbi cike da akwati da aunty Salma da ya majeed sukai mata, ummansu Xoxo ta had'a mata turarirrika masu sirrin k'amshi, najiki na d'aki nagashi na kaya, kai lamarinfa sai godiya.

*_8:00pm_*................







*luv u oll my fan's*
*(((S)))...........2017*
[8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*






*_NA Bilyn Abdul_*





_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com




*miya kamata nayi?.*
_kizama mai kamunkai, wlhy 'yammata iskanci baida wata riba, babu abinda yakai budurci daraja ajikin 'ya mace, shin miye ribarki

Please Login or Register in order to submit comment