Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har tsawon sati uku, dan haka ba'ayi taron sunaba, andai raďama yaro suna *Musayyeef*, to iman ALLAH yaraya mana musayeef, amin.
Bayan sati uku aka sallamemu, amma wannan karon gidanmu aka dawo dani, dan ina buk'atar kulawar gwaggona, haka nacigaba da rainon musayeef wanda kulum kallonsa yanasani tunawa da ubansa, dan kamarsu tayi yawa matuk'a, kullum mama tana k'ok'arin kwantar da hankalina, ahankali yauda gobe harna dake, komai yafara zama tarihi na maida hankalina akan rainon musayeef.
Musayeef yanada wata ďaya da kwanaki aduniya aka dawo da doctor gida, danya samu sauk'i sosai, shima yawan addu'ar da aka dage ana masa yasa yadake yanzu, kwanansa uku da dawowa yayansa yarakosa yaga musayeef, jiyayi kamar yamaida musayeef acikinsa, yana matuk'ar k'aunar ďansa gudan jininsa, dak'yar yayansa ya lalla6ashi suka tafi.
Yayi yayi yaganni amma nak'i amincewa, dole yahak'ura suka tafi wani abu na sukar zuciyarsa.
Daya koma gida saida aka haďa da lalashi, dan yanzu ba'aso yana tada hankalinsa.

Haka naci gaba da rainon musayeef nida gwaggo harya shiga shekara ďaya, asanane kuma ya majeed yabada shawarar nazana s,s,c,e ďina nakoma karatu, abbah ya yarda da shawararsa, dan haka nayi Exam, cikin amincin ubangiji nasamu result mai k'yau, dan haka ba'asamu matsalaba wajen nema mini makaranta.
ALLAH yacidani samun nan (A B U zariya), samun makarantar yasa na yaye musayeef na maida hankalina akan karatuna.
Shima doctor yakoma aikinsa yabarma ubangiji komai, amma lokaci2 yana zuwa duba musayeef, hakama yaya da mama da aunty.
To yanzudai ansaka musayeef makaranta kuma yayansa ne da wanan aikin, idan anyi hutu yana zuwa gidansu hakama weekend ana kaisa yayi kwana biyu.
Tunda nabaro gidan bansake haďuwa da doctor ba, bamma k'ara zuwa gidanba, idan yazo ganin musayeef kuwa bana yadda muhaďu, zadai akai masa ďansa, kuma susha hirarsu da gwaggo, ammani yagagara ganina, garama lokacin da maman su deexerh zata koma gidan naso zuwa amma ALLAH bai k'addaraba.
Xoxo ta ce, "oh maman su deexerh takoma??.
Eh yaya ya maidata yanzu hakama tana gab da haihuwa deexerh tace min.
ALLAH sarki kai natayata murna wlhy, musamman ma su deexerh dan babu abinda yafi karayu da 'ya'yanka daďi.
Wlhy hakane xoxo Reefat tafaďa.
Iman ta ce, "to wanan shine sirrin dana daďe ina 6oye muku.
"To miyasa kike yawan waige2? cewar Reefat.

Iman tayi murmushi, wato tunda nazo makarantarnan lokuta da dama nakanji turaren doctor ya yawaita awaje, wanan shine ke sakani yawan kuka da waige2, kuma kunga ranar nagansa, wanan yatabbar mini dashi ďinne saidai yana 6oyema ganina.
Tabbas labarin iman ya girgiza k'awayenta Reefat da miss xoxo, kuma sunyi alk'awarin taimaka mata har agano gsky, dan suma basu yarda cewa doctor ya saketaba, sunaji ajikinsu *bai saketaba*, amma basu sanar da ita zasuyi komaiba.
Saidai sun tanmbayeta yanzu ina deexerh?.
Deexerh tana nan, tana karatu a jami'ar abuja yanzun.
"Kuna waya?".
Eh muna waya sosai da ita, kuma aii kunsan haka, saidai sanan bakusan wacece itabane.
Hakane suka faďa, xoxo ta ce, "yakamata mukaima deexerh ziyara.
Iman tazaro ido ziyara kuma?, tanafa makaranta nece, eh aii makarantar zamuje, amma sai weekend, tunda bawani nisa bane tsakanin zariya da abuja.
Shiru iman tayi dan batasan amsar daya kamata tabasuba, Reefat ta ce, "iman kinyi shiru.
Ajiyar zuciya iman tayi, bashiru nayiba Reefat kawai ganin abun nake abaibai.
Babu wani baibai, deexerh sa'ar muce, kuma tana k'aunarki aii yakamata zumincinku yacigaba karya yanke.
Xoxo ai zumincinmu bai yankeba tunda muna gaisawa, kuma idan ina kano tana zuwa aii mugaisa, tana zuwa ta ďauki musayeef.
Eh dukda haka, yakamata mukai mata ziyara.
To shikenan saimu duba ranar daya dace saimuje kenan.
Okey ALLAH yakaimu.

Ammafa iman kinsamu akwali, wlhy da duk zatonmu gwaggo ta haifi musayeef.
Dariya iman tayi ta ce, "tokuyi hak'uri.
Suma suka dara tareda faďin yayuce, munyimi uzuri.................







_*((S)).........2017*_
_*luv u oll my fan's*_
_*battery low*_
[8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!_*




*_NA Bilyn Abdul_*



_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*




_*sak'on barka da sallah*_
_dolene nafara isar da sak'on barka da sallah ga masoyana aduk ida suke, kafin na tsunduma alabari_
_Nasan bazan iya jere sunanku dukaba, saboda yawa, wasuma bansansuba, amma dukda haka zan kawo sunayen kad'an daga cikinku insha ALLAHU._

*gaisuwa gareku*
*_Aysha Manshat, Reefat yahya, hafsat (miss xoxo), Ayusher muh'd, Abba Gana, Sajna, Maman Shaheed, Maryam 'yar mama, cwtjiddah, feedo, saffiya galadanci, billy galadanci, Lemcy, Maman useey, my Ikilee, deexerh, hudallah, zarah ms, Feedausi, Maman 'yan biyu, Zainab Zanfara, Teema, Maryam Nijar, salma Nijar, sa'adatu sa'ad, hafsy, Aysha umar Abubakar, shamsiyya muh'd, umayma, fa'iza, Xee Salees, Fatee, Xee babe, ummy, Maman aneesat, Maman yasmeen ,muneerat,nanerh, khadeejarh, beauty angel, bby hanan, Aysha umar, d'an mom, ikram saje, kairat safyan, sadiya baby, mimin mom, Luby, Afra'ce, maigadon zinaree, sumayya waziri, Aysha mai'tama, Maman Affan, momyn sultan, momyn Aysha, ummulkairi, Mrs muh'd, Mrs Amman, Asma'u taura, ikileema Zaria, Maman Mubarak, Ruky, Ash-Nur, Mrs uwaisu, matar Safwan, ummy ta kano, Rashida madaki, Mrs isma'il._*
_bari nadasa aya an an badan kun k'areba, kubini bashi a page nagaba, Dan bazan gaji da kwarara sunankuba awajen gaisuwar sak'on sallah, INA muku fatan Alkairi, da addu'ar ALLAH yakar6i ibadinmu baki d'aya, ya yafe mana zubanmu, ameeen_

*hak'uree*
```Kafin nacigaba zanba masoyana hak'uri, saboda jinkirin sosai Dana d'auka banyi typing ba, hakan yafaru me sakamakon bikin k'anwata, bayan kuma nadawo aka fara azumi, kuyi hak'uri dani, insha ALLAHU yanzu komai zai tafi yanda kukeso, ngd da k'aunarku gareni, Nina INA k'aunarku aduk inda kuke```.
*luv u oll❤❤😁😁👌🏼*.



*(Page 16)*

Yau cikin damuwa sosai su iman suka tashi sakamakon yajin aiki dasuka wayi gari makarantarsu ta tafi, bak'aramin haushi abin yabasuba, Dan suna ganin aski yazo gaban goshi, nanda 'yan watanni zasubar makarantar Baki d'aya, amma saigashi matsala ta gitta musu.
Agefe kuma sunajin kewar rabuwa da juna saboda tsananin tsak'uwar dasukayi, kowa ka kalla fuskarsa babu walwala har suka gama shiri tsaf,.
Xoxo datun d'azu hawaye suka cikamata ido saboda harta fara kewar aminannata, ta share hawayen cikin dabara batareda su iman sun luraba.
Wayar Reefat tafara wringing kobata dubaba tasan mai kiran, Dan wringing d'insa na musamman ne, ganin wayar naneman tsinkewa yasa iman tayi saurin d'auka tasa akunen Reefat.
Jiki a sanyaye tayi masa sallama, ya amsa, bayan sun gaisa ya CE, "yafa iso, tafito sutafi Dan garinsu da nisa.
Hawayene suka shiga gangaro mata akumatu, iman da Xoxo suka kalli juna, sanan sukace lfya Reefat?.
Kusan atare sukayi furicin.
Wani kukane yatawo mata, tafara shashsheka, cikin kukan ta ce, " ya Usman ne wai har yazo d'aukata.
Kamar jira suke suma suka fashe da kuka, (nace tofa akwai matsala).
Yanda suka had'e kai suna kuka dolene subaka tausayi, sukuma burgeka, sunkai minti sha biyar suna kukan, Dan saida ya Usman yak'ara kira sanan suka mik'e, 'yan kayanta suka ida had'a mata, sanan suka ja hannunta har wajen ya usman.
Tundaga nesa ya hangosu, ya lumshe idanu ahankali yana sauke numfashi, jiyayi zuciyarsa tayi sanyi da ganin masoyiyarsa uwar 'ya'yansa nanda wani d'an lokaci, yana matuk'ar k'aunar Shareefat gsky, har suka iso kusadashi bai saniba, saida suka kuma had'a baki wajen yin sallamar sanan yay firgigit alamar dawowa daga tunani.
Kusan atare suka gaisheshi harda Reefat, fuskarsa cike da murmushi ya amsa, idonsa akan Reefat, ya ce, "k'awayenmu ya karatu, Alhmdllh suka fad'a atare, sund'an ta6a hira da wasa da dariya, sanan ya ce, " Reefat tashiga sutafi lokaci yana k'ara ja.
Rungume su Reefat tayi tasake fashewa da kuka, suma kukan suke, ya Usman ko yatsaya yana kallon ikon ALLAH, tosu wad'anan Randa suka gama makarantar sai Yaya kenan?.
Ganin babu mai amsa masa tambayarsa yasa yafara lallashinsu da basu hak'uri, tareda dad'ad'an kalamai.
Haka suka hak'ura Reefat tashiga mota suka tafi, su Xoxo suna d'aga musu hannu, har saida motar ta6acewa ganinsu suka hak'ura.
Jiki a sanyaye suka koma hostel suka ida had'a kayansu Dan suma su kama hanyar kano, dukda dai babu wani nisa sosai.
Bayan kamar minti talatin suma suka fito bakin titi, fira sukeyi kad'an2 kuma duk ta Reefat, iman tad'aga kai tana kallon yanda sararin samaniya ta had'e rai tamau.
Ahankali ta sauke numfashi, my sisi garinanfa akwai hadari wlhy, itama Xoxo saman takalla, tamaido dakanta kan iman, tokodai mutafi tashane?.
Tasha kuma?, aii mun maida hannun agogo baa kenan, wlhy saimunfi saurin samun mota anan gurin.
Shikenan Xoxo tafad'a tana zama.
Hadari kuwa sai k'ara d'aurewa yakeyi, garin Yakuma jajaur alamar akwai iska a hadarin.
Lokaci lokaci sukan kalli agogon hannunsu, tun d'azur sai tare mota suke amma yawanci duk acike, gashi basu kad'ai bane awajen, akwai tsurarin d'alibai irinsu suna jiran mota, ahankali iska tafara kad'awa, mutane sai kaikawo suke kowa k'ok'arinsa yasamu mafaka.
Hankali tashe Xoxo takalli imam, wayyo sweet sis kinga abinda kika jamana ko?.
Itama iman hankalinta atashe yake, Dan ba k'aramar iskace tarufe titinba, wasu motocinma sai gangarawa suke k'asan titi suna tsayawa, kobasa ganin gabansune oho.
Garifa yafara turnik'ewa fiye da tunaninsu, ahaka sukayi nasarar tare wata bos, amma kuma gurin mutum d'ayane, sukuma su biyune, afusace direban yaja mortar suna mita shida kwandastansa, tuni iman tafara hawaye, Dan batason ruwa yajik'ata hakan yana kawo mata Marsala sosai.
Da k'arfi ruwan yafara sauka gakuma iskar na dad'a tasowa, wata jar motace tadawo dabaya Dan harta gotasu, daidai saitinsu tatsaya, deexerh tabud'e tafito, lah ashekuwa da gsk auntyn CE.
Ajiyar zuciya iman tasaki itada Xoxo tareda fad'in deexerh kece?, nice aunty kushiga mutafi, cikin hanzari tabud'e but suka zuba kayan itada iman, xoxo kam harta shige baya.
Suna gamawa wata iska ta taso wadda da'alama zata iya d'aukar mutum sukutum zuwa sararin samaniya, dasauri deexerh ta tura imam gaban motar, itakuma tashige baya.
Iman bama tasan Inda tashigaba saboda k'ura yashigar mata ido, tunda ta zauna kanta yana cikin hijjabi tana k'ok'arin goge k'asar idonta.
Dr Isma'il yajuyo yana kallon Xoxo, k'awarmu miya zaunar daku cikin wanan iskan haka?.
Tunda Xoxo tashigo motar tagane Dr Isma'il dukda sau d'aya tata6a ganinsa, tayi murmushi wlhy, iman CE, tunda muka fito nace mata muje tasha tadage wai ana samun mota anan wajen.
Tunda yafara magana gaban lman yafara fad'uwa danjin muryar Abun k'aunarta Wanda kuma take gani ayanzu babu Wanda ta tsana kamarsa.
Deexerh ta ce, "lallai aunty akwai kasada, wlhy harmun wuce uncle ya CE, " wancan kamar aunty imam, na ce, "kai uncle anya kuwa?.
Ya ce, " Baradai mutsaya muduba, shinefa muka dawo baya Ashe kuwa kune.
"Wlhy mune!". kuwa,ammafa mugode sosai daddyn musayeef, d'an murmuahi Dr Isma'il yayi, ya ce, "yakaratu ?.
Alhmdllh Xoxo tafad'a, hankalinta yana kan iman dataga tak'i d'agowa tun d'azu.
Iman wai lfy kuwa?.
Lfy lau tafad'a batareda ta d'agoba.
Xoxo tasauke ajiyar zuciya, Kodai k'asa yashigar miki Idone?.
Kai ta girgiza mata, alamar A'a.
Dr Isma'il ya ce, " humm k'asane a idonki mana ai INA kallon sanda yashiga, kid'ago na cire miki.
Banza tayi dashi kamar bama tasan dazaman saba.
Deexerh ta CE, "aunty kibayar aduba miki karya Zame miki Matsala, ido baya son bak'o wlhy.
Nifa babu komai a idanuna iman tafad'a ido arufe da hijjabi.
Dr Isma'il yad'an girgiza kai, tareda tada motar ya haura saman titi, aransa yana fad'in idan kinga kin kasa gani ai k'ya bada aduba miki.
Shiru yabiyo baya nad'an mintuna, daga nan Xoxo da deexerh suka cigaba da hirarsu ahankali, dansu Dr Isma'il basajinsu, hira suke akan abinda yafaru akansu iman d'in shiyayasa sukeyi ahankali.
Agaba kuwa d'if kakeji babu mai magana, Dr isma'il yanata tuk'i ahankali, Dan baya gudu saboda ruwa akeyi sosai, iman kuwa har yanzu bata d'agoba dukda tacire k'asan daya shigar mata idanun.
Saidai turaren Dr Isma'il dukya addabeta, nema yake yarikita mata lissafi gaba d'aya, shikansa yana tuk'i hankalinsa yana kanta, lokaci2 yakan kalli Inda take zaune atakure, yakand'an murmusa idan wani Abu yafad'o masa na rayuwarsu da iman abaya.
Bayan sunyi 'yar tafiya iman tagaji da rude fuska tabud'e, amma ta kauda kai gefe tana kallon k'ananan k'auyuka, da saukar ruwan sama.
Murmushi Dr isma'il yayi, Dan wata dabarace tafad'o masa, ganin yanda iman ta shagala da kallon waje, ga ruwa ana ketawa sosai, sai kawai yasauke Gila's d'in gefenta, wani iskane da feshin ruwa suka buso mata afuska, da Sauri tajuyo tana fuskantar Dr isma'il dake murmushi, takalleshi sosai shima daidailokacin daya juyo suka had'a ido, wani lallausan murmushi yasakar mata tareda kanne ido d'aya😉, harara tasakar masa, harda d'an murgud'a baki😏.
"Nice one".
Yafad'a ahankali cikin wata irin kasallaiyar murya.
Muryar iman na rawa ta ce, " pls karufe INA jik'ewafa, kuma ruwanan zai iya cutar dani.
Bai kalletaba bai kuma rufe Gila's d'inba, amma fuskarsa har yanzu d'auke take da murmushi, cigaba yayi da tuk'insa cikin kwarewa, Xoxo da deexerh kuwa suna baya suna k'unshe dariya, Dan duk abinda yake faruwa akan idonsune.
Iman kuwa tamkar tafasa ihu takeji, wanan aii zalincine tafad'a azuciyarta, saida yaga tajik'e gurin data bada k'arfima yajik'e sanan yay sama da Gila's d'in, ahankali ta sauke ajiyar zuciya Dan wani irin sanyi tafaraji yana shigarta, tad'ago ido tasaci kallon Dr Isma'il, sanye yake da k'ananun kaya, blue d'in wando da jar Riga anmata digo2n fari, k'ugunsa d'aure da farar rigar sanyi ta sak'a, tad'an ta6e Baki azuciyarta tace saikace wani mace, kakama k'ugu ka d'aure da riga.
Ganin irin kallon datake masane yasashi 'yar dariya, yaymata kallon fisha ya maida kallonsa saman titi, ahankali ya ce, "kallonfa?, ko namiki k'yaune?.
Da sauri iman ta kauda kai tana fad'in mizan kalla anan.
Ya ce, " handsome mana.
Yanda yayi maganar saida tsigar jikin iman yatashi, Duk abinda yake faru su Xoxo basu saniba hankalinsu yana kan waya, deexerh tana nuna mata hotunan bikinsu iman d'in.
Ya ce, "INA my son?.
Baki iman ta ta6e tareda fad'in na siyar dashi.
Wata 'yar dariya yayi, harda dukan tityari, ya ce, " dakin burgeni kuwa my sweedy!.
d'an tsaki taja danjin ya ce, "mata sweedy, wayarta tajawo tafad'a kiran Reefat amma arufe.
Tajuyo tana kallon su deexerh, sisi tafad'a tana kallon Xoxo!. "ma'am".
Kinga No d'in Reefat yak'i tafiya, wlhy Nima tun d'azu nake gwadawa, amma inaga bata kunna wayarta bane.
Kumafa hakane iman tafad'a tana gyara zama.
Awani d'an k'auye Dr Isma'il yatsaya, Dan gsky ruwan yawuce tunanin jama'a, zugashi akeyi sosai, yanzuma harda k'an k'ara akeyi, gani yayai baya ganin gabansa sosai Dan haka yabi sahun direbobi masu tsayuwa, shima ya tsaya.
Ju yowa yayi sosai yana fuskantar iman, itakuma ta had'e rai tamau..............





_kuyi hak'uri da wanan❤👌🏼_

*luv u oll my fan's*
*(((S)))........2017*
[8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!_*






*_NA Bilyn Abdul_*



_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*



*Gaisuwar Sallah*
*_Fateema sulaiman Nijar, zeenaseer, fatee Axlad, ummiee jafar, Ruk'ayya Kt, zaliha, hauwa kaka, humyluv, ummiee Khalil, hauwa lele, xeynab, sumie Carly, teemacool, Nafisa Raji, Maryam, ayusha umar, Maimunat (kakus), lawusa, ayeesh, muhmeelat, Mina, Raheenat Basheer, Asy Khalil, zee Elkaseem, Zainab muh'd bello, Maryam zuntu, zeenur, Asmy b, mammu magaje, Maman ihsan, shamsiyya abas, hamie danjani, Maman shureim, barakarh, haleema muh'd Ali, Maryam Ab, meenat, Aysha, khareema, ummu musakeen, Aliya jos, khairiyya, suhaila Tafida, umman marwan, Mrs Izz, zeenat A kabeer, Bily sokoto, Ameera Musawa, Ameera sokoto, 'yar India, mufeeda show, Ifteehal, Ameena kd, Asiya masak'a, Tani tani, badee, Bara'atu ce, Bahijja, Maman shamwul._*
_Bari nadasa aya anan, muhad'u a page nagaba, INA fata duk kunyi sallah lfy??._




*(page 17)*
'Dan murmushi yayi Dan ganin yanda tawani d'aure fuska. Yajuya yakali su deexerh, yaga hankalinsu baya kansu, ta waya sukeyi.
"Juyowa yayi kan iman, data maida kallonta ga Gila's, *_"Imman!"._* yafad'a dawata irin murya mai cike da kasala.
Banza tayi masa kamar batajiba, ya ce, " wlhy koki juyo kona k'ara bud'e Gila's d'inan, nanama shiru tayi masa bata tankaba.
Ganin bazata juyoba yasashi sauke Gila's d'in, wani sanyi yafeso harda k'ank'ara, babu shiri tajuyo tana sauke ajiyar zuciya, Gila's d'in yarufe yana 'yar dariya, haushine yaturnik'e zuciyar iman, sai Kawai tafashe da kuka.
Jingina bayansa yayi da murfin k'ofa yadasa mata mayun idanunsa, ko k'yafatawa bayayi, sai yanzu yay mata kallon tsaf, ganin yayi tak'ara k'yau harda 'yar k'iba, dakaga Iman zakasan tana cikin kwanciyar hankali, atake zuciyarsa takawo masa wani tunani.
"Koadai Iman k'arya take ita tarubuta takardar sakin nan Dan bata sonsa??, wani irin d'aci ya turnik'e zuciyarsa"..
K'irjinsane yafara masa nauyi, indai hakane Iman taci Amanarsa, tajefashi cikin mawuyacin hali, ga ciwo ga matsananciyar sha'awarta dake addabarsa, saboda gudun fad'awa halaka yasashi kullum yake kasancewa cikin azumi, gashi yanzu dukda yana azumin dauriya kawai yakeyi, yarintse idanunsa, Azuciyarsa ya ce, " *BAN SAKETA BA!* miyasa zatace nasaketa?, shin dama bata k'aunatane?, wani dogon tsaki yaja, Wanda baisan yafitiba, gaba d'aya suka d'ago suna kallonsa.
Tada motar yayi yafisgeta da k'arfin tsiya.
Gaba d'ayansu hankalinsu atashe yake, ganin yanda yafisgi motar yasa deexerh datasan halin dayake ciki, kuma taga Iman na kuka sai hankalinta ya tashi.
"Ta ce, ''Uncle lfy kuwa?".
Baice mata k'alaba Dan yafara fita hayyacinsa, shikansa baisan ayanda yake tuk'inbama.
Ganin sunfara yawo a titi yasa hankalin Iman komawa Kansa.
" innalillhi wa'inna ilaihirraji'un", Doctor! Pls karka kashemu, kayi hak'uri Dan ALLAH.
INA baimasan tanayiba, da sauri deexerh ta taso tayi nasarar tsaida motar, danta iya, gefen titi suka gangara, saura kad'an subigi wata bishiyar Tsamiya, Xoxo da deexerh suka k'ank'ame juna suna Addu'a, Iman ma Dr isma'il ta k'ank'ame tana kuka, dukda baya cikin Nutsuwarsa saboda nauyin da k'irjinsa yayi masa, wannan bai hanashi rungume Iman ba sosai.
Ya kwantar dakansa jikin kujera yaruntse idanu, ga Iman rungume ak'irjinsa, sai wani irin Numfashi yake saukewa awahale.
Jin motar ta tsaya dakuma saukar Numfashin Dr Isma'il yasa deexerh d'agowa da Sauri, gabantane yafad'i, afili ta ce, "nashiga uku, kardai ciwon Uncle ne yakeson tashi?.
Sai asanan Xoxo da Iman suka d'ago, Iman tafara mutsu2n kwace kanta, amma takasa danba k'aramin ruk'o yaymataba.
Da sauri deexerh ta kwantar da kujerar, Yakuma k'ank'ame Iman kamar za'a kwace masa ita.
Motar tayi shiru bakajin motsin kowa sai saukar numfashin Dr Isma'il, da hannu yayma deexerh Nuni data bashi magani, cikin hanzari tabud'e motar tafita, gaban motar takoma, tabud'e wani waje, magungunansa tagani awajan, wani d'an farin roba tad'akko, Wanda tagani yana amfani dashi idan ciwon ya motsa kafin aje asibiti.
Abaki tasaka masa yazuk'a sau uku, yajanye bakinsa, Yakuma rungume Iman yanda bazata samu hanyar barin jikinsaba, cikin 'yan sakwanni barci yay gaba dashi.
Xoxo da deexerh bud'e mortar sukayi suka fita sabida an daina ruwan, said'an yayyafi.
Ga Iman so kawai take takwace jikinta, amma dukda barci ya d'aukeshi ta kasa.
Saida suka fita Xoxo talek'o.
"Iman pls kiyi hak'uri kinutsu waje d'aya, dadyn Musayeef yana buk'atar taimakonki, kitausaya masa halin dayake ciki, mu zamu zauna a waje harya farka idanma kunyarmu kikeji.
Shiru tayi dantasan maganar Xoxo gsky CE, to Amma aii babu dacewa, tunda ayanzu Shiva mijinta bane, gani take zunubi kawai zata kwasa abanza a wofi.
Wasu zafafan hawaye suka zubo akumatunta, addu'a tashiga karantowa ahankali harta samu nutsuwa.
K'ara gyara kwanciya tayi sosai, tak'ara kwantar da kanta visa faffad'an k'irjinsa, tunanin rayuwarsu tabaya tashiga yi da Doctor, taringa tuno so da k'auna gamida tattali daya ringa nuna mata, amma gashi yanzu k'addara ta rabasu, sunyi nisa da juna, ahaka taringa tunani da shak'ar kamshin daddad'an turarensa har barci yay ayon gaba da itama.
(Nace da k'yau iman, anji k'irjin boss😜).

Xoxo takalli deexerh, kinga gawata rumfa can kozamu koma Canne?. eh wlhy kuwa muje can, Dan naga ruwan yanad'an jik'amu ahankali.
Kafin su wuce deexerh talek'a Dan taga halin da Uncle d'inta yake ciki, murmushi tayi tareda share hawayen tausayi, Dan ganin yanda itama iman barci ya d'auketa.
Xoxo ta k'araso tana fad'in lfy kuwa?.
Murmushi deexerh tayi tana nuna mata su iman, itama d'an murmushi tayi, sun bata tausayi matuk'a, suna kewar junansu sosai, amma zalunci yasa an rabasu, (tana k'ara tsinewa azalumin dayayi wanan zalincin, Dan tasan ALLAH bazai barshiba).
Hannunta deexerh taja suka tafi runfar, wadda da'alama an tanajeta saboda irin hakan.
Wuri suka samu suka zauba sunata hira, da tattauna yanda zasu taimakawa su iman.

*Reefat*
A6angaren Reefat kuwa, tunda suka tafi ta kifa kanta saman cinya tanata kuka, ya Usman bai hanataba Dan yasan zafin rabuwa da masoyi, tuk'insa kawai yakeyi, gashi yaga alamar hadari agarin.
Saida sukayi tafiya mai nisa sanan yaga kukan na Reefat bamai k'arewa bane, Dan haka yay gyaran murya, tareda fad'in Shareefat!.
Ahankali ta ansa, batareda ta d'agoba, ya ce, "d'ago mana kiji wani Abu.
Bata musa masaba, tad'ago kanta, idanunta sunyi jajur, ya ce, " kalleni mana.
Ahankali tad'ago tana kallonsa, yasakar mata lallausan murmushi, da Sauri tayi k'asa da kanta itama tana murmushin.
Kokefa yafad'a yana dariya, kukan ya Isa haka, muyi hira.
Nanma murmushi tayi, ahankali yarink'a janta da hira harta saki jikinta aka koma soyayy😜lol.

Saida su Dr Isma'il suka d'auki tsawon minti Arba'in suna barci, Dr Isma'il yafara farkawa, yabud'e idanunsa ahankali ya sauke akan fuskar iman datake barci cikin kwanciyar hankali.
Wani lallausan murmushi yasaki tareda jin wata zazzafar k'aunarta tana k'ara shigarsa, yashafa kumatunta ahankali. Da sauri tavud'e ido takalli inda fuskarsa take.
"Ido suka had'a tai saurin kauda kai tana k'ok'arin tashi daga jikinsa, bai saketaba saidai k'ok'arin tashi dayakeyi da ita ajikinsa, zaunar da'ita yayi sosai acinyarsa.
Muryarta na rawa ta ce, " dan ALLAH ka cikani kaga babu dacewa acikin hakan.
Baicemata komaiba sai k'ok'arin gyara kujerar dayakeyi da hannu d'aya, hannu d'aya kuma yana rik'e da ita.
Jingina yayi da kujerar sanan yakuma had'eta da jikinsa, yajuyo da fuskarta suna fuskantar juna, ido ta runtse dan bazata iya kallonsaba, bata ankaraba taji bakinsa cikin nata, tuni jikinta yafara

Please Login or Register in order to submit comment