Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Murmushi yayi, saboda yaga amfara zuwa wajen, ya gyara kwanciya yana faďin amma aini mijinkine ko?.
Na ce, "eh."
Ya ce, "masha ALLAHU."
To zoki shafa min addu'ar.
Dukda ina jin kunyarsa hakan bai hanani amsawaba, saboda yauda kullum, sabo da soyayyarsa sun k'ara tasiri acikin zuciyata fiye da tunanin mai karatu.
Koda nazo daf dashi sainace to kashe fitilar.
'Yar dariya yayi, saboda mi?, sai ankashe fitila?.
Na ce, "inajin kunya.
To sarkin kunya nakshe azo amin, yafaďa yana kashe fitilar gefen gadon.
Na matso kusada shi sosai, dukda yakashe fitilar sai nake gani tamkar yana kallona, dan haka na rintse idanuna sannan nakai hannuna ajikinsa ina shafa masa addu'ar.
Wadda shikuma yakejinta tamkar tafiyar tsutsa nake masa, ban ankaraba sainajini kwance a faffaďan k'irjinsa..........dan ALLAH basaina faďaba abarshi haka, iman tafaďa tana kallon fuskar Reefat da miss xoxo.
Tab!!, suka faďa atare, wlhy babu ďaga k'afa sai an faďa mana komai.
Iman tashiga lalla6arsu amma sukace basu yardaba saita faďa, basa son kwange.
Babu yanda zatayi dole taci gaba, tunda alk'awari ta ďauka musu.
........'yar rungumenin daya sabayi yasa banji komai arainaba, bankuma kawo komaiba, saima k'ara nutsa kaina danake cikin k'irjinsa ina shak'ar daddaďan k'amshinsa, turarurrukan doctor sun kama jikinsa sosai wanan yasa duk motsin dayayi sai k'amshinsa ya baza waje.
Nashagala da shak'ar k'amshin sai naji hannunsa wata tashar daban, naďago da zummar kwace kaina amma ina saiya k'ara matseni gam, cikin muryar mai fara shirin kuka na ce, "doctor pls kasakeni, muryarsa naji cikin kunnina yana faďin nutsu my saudat, zan ďansha k'amshinkine.
Yanda yake maganar hannunsa kuma nacigaba da shafa inda tunanina baita6a kaiwa doctor zai ta6aminba, sai jikina yakama rawa, na fara kuka, bakina ya laluba ya haďe danasa.
Tuni labari ya sauya salon tafiya, doctor yanata k'ok'arin kaiwa inda yake kwaďayin zuwa, nikam tuni kuka yaci k'arfina, amma doctor yakasa control ďin kansa domin lallashina.
Hummm! aranardai doctor bai barniba saida ya maidani cikakkiyar mace, saidai nasha matuk'ar wahala, nayi kuka harna rasa hawaye, har sumar wucin gadi nayi.
Shima kansa yasha bak'ar wahala, saidai yauďin yanajinta rana tadaban agareshi, har yarasa irin addu'ar dazaiyimin awanan lokacin, yana gefe yana maida numfashi, yayinda nikam naketa kuka mara sauti, saidai hawaye daketa zurara a kumatuna.
Bayan kamar minti 15 yaja jiki kusadani, sosai ya ringumeni, nikan atunani zai k'arane dan haka na ruďe dabashi hak'u cikin magiya da dashashshiyar muryata.
Yanda narikice masa saina bashi tausayi, ya janye jikinsa yana faďin sorry iman babu abinda zan sake miki, nima ina tausayinki.
Mik'ewa yayi ya kunna fitilar ďakin, wata leda yabuďe yafiddo da magunguna kala2, wannan ya tabbatarmin da dama yashirya zuwan wanan rana kenan.
Dakansa yayimin wanka ya sakani aruwan ďumi, har sanan ban daina kukakaba, shima yanata aikin lallashina, bayan an kammala wankan yasani nayi wankan tsarki sanan ya naďoni kamar wata jinjira yadire saman kujera, kasancewar gadon duk ya6aci da jini, saida ya cire zanin gadon ya juya katifar, yasake shimfiďa wani sananan ya maidani saman gado.
Madara yabani nasha kađan, dan bana sha'awar komai asanan, bai takuraniba ya bani magani nasha, yamatseni yamin allura.
Yasha raki kafin barci ya saceni.
Ya tsuramin ido tareda sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, fuskarsa cike da murmushi mai k'ayatarwa, acan k'asan zuciyarsa kuwa sai kwararamin addu'oi yake na musamman.
Wanda ballagazar mace bata samun irinta.😜
Jiyake kamar shi kaďai ALLAH yayma wanan gatan na samun nutsatstsiyar mace, nagartacciya, kamila, ahankali yake shafa kaina yanata murmushi abinsa, aii dolene yayta godiyar ubangiji shikam daganan har wayewar gari, bargo yaja ya k'ara lullu6eni sosai saboda sanyin fanka, nikam bammasan yanayiba, inata barcina.
yamik'e shima zuwa bayi domin gyara jikinsa.
Yana fitowa yafara jera nafilfili da mik'a godiyarsa ga sarkin sarakuna, shugaban talikai, har k'arfe uku sanan yahawo gadon tareda rungumeni tamkar za'a kwace masani, cikin nishaďi barci yay awon gaba dashi.

Da asuba yarigani tashi, dan haka bai tadaniba yay alwala suka tafi masallaci shida yayansa da marwan.
Shidai yayansa sai kallonsa yake cikin mamaki, dan ganin yanda gabaďa ayyukansa ke nuna kasancewarsa cikin farinciki, saboda marwan kawai yakasa tambayarsa harsuka idar da sallah suka fito.
Koda suka shigo gida sai marwan yawuce 6angaren mama, to anan yayansa yasamu damar tambayarsa ko lafiya?.
Yayi murmushi yana sosa tsakkiyar kansa, babu komai yayana mikaganine?.
Yaya yaďan tsura masa ido yana murnushi, ban yardaba auta akwai labari atareda kai gsky, gabaďaya ayyukanka suna nuna alamomin farinciki atareda kai.
Nanma murmushi yayi yana ďan duk'ar da kai, yayansa yay dariya shikenan tunda ba'aso nasani, k'iladai k'anwatace tajagoranci farincikin, ALLAH yak'ara baku zaman lafiya.
"Amin doctor yafaďa yana 'yar dariya cike da kunya.
Kafaďarsa yayansa yaďan buga yana dariya shima, daganan kowa yanufi 6angarensa.
Har zuwa sanan ban tashiba inata barcina, doctor yazauna gefen gadon saitin fuskata yana murmushi, ahankali ya janye bargon danake k'udundune aciki, ya rankwafo ya sumbaci kumatuna, saikuma yakoma shafa kaina ahankali.
Na buďe idanuna dasuka ďan kumbura saboda kuka saikuma na maida na lumshe, cikin muryarsa mai daďi ya ce, my saudat adaure atashi ko?, yafaďa yanaďanjan hancina.
Nakuma buďe jajayen idona na waresu akansa, kallo ďaya namasa na rufe fuskata da hannayena, yayi murmushi mai sauti tareda yaye bargon gaba ďaya, har yanzu idanuna arufe suke, dan haka yaďaukeni gaba ďaya zuwa bayi.
Da sauri nabuďe idanuna danjin ansakani aruwan ďumi, narik'eshi da sauri da zummar tashi, amma saiya yimini k'yak'yk'yawan rik'o.
Ashagwa6e nafara faďin ruwan da zafi doctor!.
Cikin sigar lallashi yake ya ce, "sorry my iman, kinga idan baki shiga ruwan zafinnanba sosai gurin zai ringa miki ciwo, kidaure kinji jarumata, hakadai yaytamin kalamai masu daďi har ruwan ya huce.
Yamin wanka, na ďauro alwala muka fito.
Yaďakkomin zanin sallata da hijjab, yashinfiďamin sallaya nayi sallah, ina idarwa na kwanta akan sallayar na hau barci, shikuma yana bayi yana ďauraye zanin gadommu daya jik'a jiya da daddare.
Cak ya ďaukeni yamaida saman gado, yarungumeni muka koma barci.

_*9:30 am*_
Sai k'arfe tara muka farka, konace bugun k'ofa ya tadamu, doctor yatashi da k'yar yaje yabuďe k'ofar, aunty sadiya ce, bata jira wani abuba tadanno kai cikin falon, yabita da kallo tareda faďin lafiya kuwa?, wani kallo tasakar masa mai tattare da abubuwa masu tarin yawa, ya ďan kauda kai daga kallonta.
Ta ce, "kalli agogo isma'il k'arfe tara da rabi baku tashiba kaida matarka, kunbarmu munata jiranku ayi break.
ďan k'aramin tsaki yaja tareda nufo ďakina, saida yaje bakin k'ofa sanan ya ce, "kije muna zuwa, baijira amsartaba yashigo ďakina ya murza key.
Jitayi kamar yadaka mata kulki akai, tacije le6e tana ballama ďakin harara sanan tafice tana k'unk'uni.
Shikam yak'araso gaban gadon yatadani, dak'yar na iya tashi ina kare fuska nashige bayi, yakula kamar tafiyata taďan canja, dan haka yabiyoni yana faďin nak'ara shiga ruwan zafi, to na amsa masa akunyace.
Shima ďakinsa yanufa domin yin wanka.
Cikin 'yan mintuna muka shirya muduka, ina k'ok'arin fitowa yana k'ok'arin shigowa mukayi karo.
Ya rungumoni da sauri yana faďin sorry dan naďan bige kaina ajikinsa, na lumshe idanuna saboda k'amshin turarensa dana shak'a.
Ya ce, "harkin shirya?, kai kawai naďaga masa ina ďan murmushi, na ce, "ina kwana?, lfy lau tawan, yajikinki??, ahankali nafurta lafiyata k'alau nikam, ya ce, "ko?.
Naďaga kai batarda nayi maganaba, shima 'yar dariya yayi yakama hannuna muka fice zuwa 6angaren mama.
Da sallama muka shiga, kowa ya hallara mukaďai ake jira, muka gaida mama da yaya, na gaida aunty, su deexerh ma muka gaisa bayan sun gaida uncle ďinsu, na kalli kujerar danake zama yau Raihan ta zauna.
Deexerh tasan wani k'ulline kawai, dan haka tamik'e akan tata takoma kusada aunty inda yakamata Raihan ta zauna, dama kujerarta kusada doctor take, nida ita muke sakashi tsakkiya, koda tatashi sai muka zauna, doctor yazauna inada deexerh ta tashi, nikuma nazauna kujerar dayake zama.
Muka fara break, babu abinda kakeji saik'arar cokali da filet, mamadai sai kallona take, dan takula banida walwala ga idanuna sunďan kumbura da kuma ja.
Nidai akunyace nakecin abincin dan gani nake kamar kowa yasan halin danake ciki, munhaďa ido da aunty yafi ak'irga tana hararata, nikam ko kallo bata isheniba wlhy, dan inada uzuri mai yawa agabana.
Bayan mun kammala mama takasa hakuri ta ce, "iman kobakida lafiyane??.
Cikin rawar baki nabuďe baki zanyi magana, idanuna kuma akan doctor, shima kallona yake, ganin kamar zan 6aro masa aiki, yay saurin cewa mama kantane yake ciwo tunjiya da daddare.
Mama ta ce, "ayya sannu kinji ďiyata, auta tasha magani dai ko??, da sauri ya ce, "eh mama tasha, yanzuma idan munje zata k'ara sha.
Yayansa dai dariya kawai yayi, dan tuni ya harbo jirgin k'anin nasa, amma dukda haka saida yaymin sanu, da kuma nuna tausayinsa akaina, hakama aunty ta gane komai dan haka adak'ile tamin sannu, Raihan ma dai dan dole ta ce, "sannu.
Marwan kuwa da deexerh sun nuna tausayinsu sosai, marwan harda faďin aunty bari naje nasamo miki kayan jinya, gasassar kaza kikeso ko mi??, gaba ďaya akasa dariya afalon amma banda aunty, doctor ya ce, "lalai my son yau momy tazama abokiyar wasa kenan?.
Nandai mukaita dariyarmu, daga baya doctor yajani muka koma 6angarenmu, yakuma bani magani nasha.
Tsawon kwana uku doctor yana jinyata da riritani, aranar kuma yake shirin tafiya washe gari, jinake kamar karya tafi, gashi inatajin faďuwar gaba, harma na sanar dashi, ya ce, "nayita addu'a insha ALLAHU babu komai sai alkairi.
Shawararsa nabi nayita addu'a azuciyata, da daddare koda muka kwanta yaso raya sunna, amma saiyaji jikina da zazza6i dan haka ya k'yaleni yabani magani nasha muka kwanta.

_"sosai iman take kuka, wanda yabama su xoxo mamaki, hardai suka kasa hak'uri suka shiga tambayarta dalili, bata basu amsaba saida tayi kuka sosai, konace saida taga k'awayen nata suma sun fara, (kai jama'a wanan k'awance yana burgeni, dan cike yake daso da k'yaunar juna), ta tasagaita da kuka tareda share hawayenta"._
Ta ce, "abinda yasani kuka, shine tunowa da ranar cin amana, ranar data zamemini barazana arayuwata, har yanzu nakasa mantawa da ita.
Bayan doctor yatadani yatafi masallaci hakanan na tashi jiki babu kwari, nayi sallah, kasancewar nasan tafiyar wuri yakeyi yasa ban koma barciba, sainaje na haďa masa shayi, nasoya kwai kawai dan banaso yatafi baici komaiba.
Yana dawowa yatadda ina kicin sai kawai yaje ďakinsa yay wanka, yafito yashirya cikin kakin sojoji, kayan suna masa matuk'ar k'yau, yabaza turarensa na kullum, sanda yafito harna jera masa komai afalon.
Cikin tsokana ya zauna yana faďin tawan kinaji dani wlhy, yanzunan har an haďamin breakfast, dariya kawai nayi na ce, "aika isane, ya ce, "ko?".
Na jinjina kai ina murmushi, to nagode yafaďa shima yana shan shayi, saida yagama tsaf, sanan yashiga yimin nasiha mai ratsa jiki, daga nan yaje 6angaren mama da yayansa, bai daďe sosaiba tunda tun dare sukayi sallama, saiya dawo, duk abinda nake buk'ata tun adaren jiya yabani shi, dan haka koda yadawo saiya rungumeni yana faďin dama mama da yaya zasu yarda dasai muyi tafiyarmu musha amarci acan iman.
Amma nasan bazasu yardaba, insha ALLHU nanda sati biyu zan dawo kinji.
Nashare kwallar data cikamin ido na ce, "to ALLAH ya tsare minkai, yabada sa'a, yaka'ara ďaukakaka mijini.
Amin yafaďa yana k'ara matseni ajikinsa, daga nana yahaďe bakina danasa, ayaudai nabada gudummawa, dan sosai nataimaka masa yasamu farinciki wajen sumbata, wadda inada tabbacin yasamu ďin kuma.
Saida yayansa yakirashi awaya sanan yazare bakinsa daga nawa akasalace, baiyi maganaba ya ďauki jakarsa yasa akafaďa yana ďagamin hannu, nikam nai k'asa dakai saboda hawayen dasuka cikamin ido.
Banyimasa rakiyaba gudun karnaje gaban mutane ina kuka, saikawai nakoma đakina nakwanta ina kukana.

_*11:56 am*_
Har k'arfe shaďaya dawani abu ban tashiba, nayi kuka harna gaji, nikaina bansan dalilin kukan nawaba, saboda bayau doctor yata6a tafiya yabarniba, amma nafijin zafin tayau da kewarsa, zuwa shabiyu saura na hak'ura natashi domin gyara ďaki, ina cikin kakka6e gado naga takarda tafaďo.
Harna ajeta saman durowar gado dazaton doctor ne ya manta da ita, saikuma zuciyata takasa nutsuwa na ďauka nabuďe.
_"Inna lillahi wa'inna ilaihirra raji'un"_, kawai nake ammbata, jikina sai rawa yake.
Adaidai wanan lokacin deexerh tashigo ďakin...............



_*kuyi hak'uri dajina shiru, wlhy abubuwane suka min yawa, amma insha ALLAHU bayan biki zaku cigaba da samun book ďin yanda yakamata masoyana, ina alfahari daku sosai*._
*luv u oll*







_*((S))..........2017*_
_*luv u oll my fan's*_
_*Battery low*_
[8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *________________________________*
*BAN SAKETA BA!*
*________________________________*
*NA*
*BILKEESA IBRAHEEM*
_*{bilyn Abdul}*_
*________________________________*
https://mrsbilkisa.blogspot.com





_sadaukarwa_ *ya Abdul {city phone's}*




*MIYAKAMATA NAYI?.*
_'yar uwa! ďan uwa!, yakamata dani dake da kai mutaru mu mutunta juna, k'yautata mu'amularku da jama'a 'yan uwanku, walau musulmai ko ba musulmaiba_
_karku zama masu girman kai, saboda wata ďaukaka ta duniya, babu wanda yafi wani gurin ALLAH sai wanda ya k'yautata ibadarsa, to ashe nidake da kai duk bamuda tabbas, domin duk k'ok'arin ibadarka wani yafika, ballema yanzu damuka lalace, muka shagala aduniya da kayan cikinta._
_saika samu mutum yahaďa shekara ďaya bai karanta *alkur'ani* ba, baya sallah akan lokaci, baya neman ilimi akan addininsa, baya tunawa da *ubangijinsa* sai masifa ta rikesa sanan ya ce, "ALLAH ne ya ďora masa, humm kaji ďan adam sarkin butulci da izgilanci, duk sanda alkairi yasamesa saiya ďauka wayonsa da iyawarsace tabasa, wanan kuskurene da jahilci._
_mudaure murunga neman _ilimi akan addini, bawai aboko_ kawaiba, _saikaga mutim yanata_ _fafa shi yanada digiri ko_ _difloma_ _ko yana karatu a jami'a kaza, amma_ _wlhy idan zaka tsaresa bazai iya_ _kawo maka alwala cikakkiyaba,_ _bare azo ga sallar kanta, amma_ _turanci da iya salo abakinsa ko_ _mista k'yarank'yan yashafa_ _masa lafiya, larabcikan sai ace_ _aiba yarena bane._
_to hajiyata alhajina shi turanci yarenkine?, hasalima turancin namak'iyankine, afannin addini al'ada jinsi, dan bature bazai ta6a k'aunar musulmiba kuma bak'in mutum, larabci kam abin al'faharinkine tunda koba komai *Annabinmu* yafito daga wanan tsatsonne._
_Inaga lokaci yayi dazaki gane ka gane na gane cewa da mutunci ake gano mutunci, da ilimi ake gano gyara, to *miya kamata nayi?* na nemi ilimi na addini bawai boko kawaiba._
*ALLAH yasa muga ne.*




*~page.......15~*

..................da sauri deexerh ta rik'eni nafaďo hannunta dan tuni numfashina ya tsaya, k'arar da deexerh ta kwallace ta jawo hankalin jama'ar gidan harda yaya dadyn su deexerh.
Da gudu suka iso 6angarenmu suna tambayar lafiya??, ganina akwance yabasu tabbacin nice babu lafiya ba deexerh ba, aunty ce tafara cewa akira doctor, amma yaya yahana, wani abokinsa aka kira, kafin ya iso yaya yazare takardar daya gani ahannuna, tuni zufa ta wanke masa dukkan sassan jikinsa, sai k'ara maimaita karanta takardar yake kamar wanda akabama hadda.
Ya maimaitata yafi ak'irga, tuni kuwa ya haddace komai dake cikin takardar, mama tana lura da halin dayake ciki, zuwan doctor ne yahanata tambayarsa.
Dr Auwal yadubani tareda mak'alamin k'arin ruwa, ya ce, "insha ALLAHU zuwa anjima zan tashi normal, yanzuma wani abune ya firgitani na suma, amma na farfaďo.
Godiya sukai masa sanan yatafi.
Dama tuni yaya yabar wajen, yana 6angaren mama, acan mama tasamesa zaune akujera kamar gunki, idonsa cike da kwallah, zuwan mama yasa yatashi sosai, yasa gefen rigarsa ya share kwallar data gangaro masa kaďan agefen ido.
Jiki asanyaye mama ta zauna dan tabbas tasan ba lafiyaba, yaya yanada k'ok'arin 6oye damuwa komai tsananinta, amma yanzu hakan ya gagara, cikin sark'ewar murya mama ta ce, "Mansur miya faru ne?.
Yaya yaja ajiyar zuciya, muryarsa naďan rawa ya ce, "mama Isma'il ya saki iman!!.
Cikin wani irin yanayi mama take kallonsa, ta ce, "ban ganeba Mansur mikakeson faďamini?.
Takardar hannunsa yamik'a mata, ta kar6a takaranta.....
*ni Isma'il Muh'd basheer!. Nasaki matata saudat sulaiman saki uku!!. Idan tasamu miji tayi aure.*
Tuni gumi ya wanke jikin mama, bata buk'atar k'arin bayani danhaka tayi tagumi kamar yanda yaya yayi.
Yayane yay k'arfin halin faďin mama amma yaronnan ya cucemu, yanzu dan ALLAH dawane ido zamu kalli iyayen yarinyarnan?, ni abindama yake bani mamaki shine miya haďasu dahar zai mata saki har uku?, miya hau kan yaronnan haka?, kuma wlhy mama rubutunsane barema ya musa mana.
Mama taja ajiyar zuciya toni Mansur ai komaima ya kwace mini, bansan yanda zan kira wanan abinba kuma.
Haka mama da yaya sukaita tattaunawa, kuma wani abun mamaki sunkira wayar doctor arufe, mama ta ce, "tunda yasan miya aikata ai dole yakashe waya, kabarsa kawai.
Nikam ina ďaki ina barci, aunty da deexerh da Raihan suna 6angarena, saidai basusan abinda yake faruwaba, dan deexerh ma bata karanta takardarba tunda tana zuwa ina suma.
Haka akaita tafiya har zuwa yamma dana farka, mama dakanta ta taimaka mini nayi wanka, aka bani abinci naci kaďan har zuwa sanan kuka nake rurus.

*bayan kwana uku*
Yau tsawon kwana uku kenan angaza samun number doctor kwata2, nikuma namatsa zanje gida, dan yakama iyayena su san halin da'ake ciki, mama da yaya basaso natafi, hakama deexerh da marwan, amma yaza'ayi da k'addarar ALLAH, ganin namatsa yasa mama da yaya suka kaini har gida.
Bak'aramin ruďani gwaggo tashigaba itada Abbah dajin abinda yafaru, dan su yaya basu 6oye musu komaiba, suka ďora dabasu hak'uri.
Abbah ya ce, "babu komai haka ALLAH ya k'addara aii, bayan ďan tattaunawa dabawa juna baki su yaya suka tafi aka barni agida.
Tunda nadawo gida banida wata walwala, kulum cikin kuka nake, ga rashin lafiya data tasoni gaba, dandanan nayi bak'i na rame kamar baniba, lokacin da labari yakai kunanen aunty salma da ya majeed ransu ya 6aci matuk'a, ya majeed ya ce, "bazai k'yaleba saiya ďauki mataki akan doctor, da k'yar abbah da gwaggo suka shawo kansa ya hak'ura.
Ganin yanda na k'untata kaina agidan yasa ya majeed rok'on abbah yabari nakoma wajensu k'ila zanfi samun sakewa, abbah baiyi musuba dan dama farin cikina yakeso, aranar muka tattara muka koma.
Acanma haka nayita rashin lafiya wadda tasa dole suka kaini asibiti, tofa wata sabuwa, bayan gwaje2 da likita yayi ya tabbatar mana inada ciki na sati uku, tun agurin nasa kuka sai anzubar dashi, amma ya majeed ya hana.
Ranar nayi kuka harna godema ubangijina, duk wanda yaganni saiya tausaya mini.
Muna dawowa gida ya majeed yasanarma su abba halin da'ake ciki, aranar kuma aka sanarma gidansu doctor, mama da yaya sunyi matuk'ar murna da wanan abin farinciki, dan cikin zai zama sanadin cigaban zumincin mu.
Har tsawon wata ďaya babu labarin doctor kota waya bare kuma ayi maganar dawowa.
Nikam inanan a6oye inata k'ok'arin zubar da ciki, duk abinda naji ance yana zubar da ciki saina sha a6oye, amma abanza wai man kaza, dan ciki ko gezau, saidai nasha azabar ciwon cikina.
Ahaka aka akai wata biyu da sati ďaya.
Awata ranar alhamis doctor yazo kano, saidai kuma yatarar da sabon tashin hankali, dan kowa ya ďauke masa wuta agidansu.
Kowa ya tambaya iman sai suyi masa banza harsu marwan da deexerh.
Hankanlinsa yatashi matuk'a, inda yaga sunk'i bashi wata amsa ta gamsarwa sai kawai ya tsare deexerh da marwan da bulala.
Tsoro yakamasu sosai dan ganin yanda yaburkice musu ďinnan zasu iya shan duka abanza, aiko suka sanar dashi komai, atake jikinsa yay sanyi, yanufi wajen mama hankali tashe.
Agabanta yashiga rantsuwar wlhy *BAN SAKETA BA!* mama, na rantse da ALLAH k'arya takemini.
Mama tayi masa banza, wuni guda yana magiya da rok'o amma kowa yak'i saurarensa, dayaga nan babu ci saiya nufi gidanmu, to gara nan abbah yayi masa nasiha da nuna masa muhimmancin yarda da k'addara.
Shidai doctor bashida wata magana sai *ban saketa ba*, tun suna kallon abun amatsayin wasa harya fara zarta tunaninsu, dan doctor neman zare musu yakeyi, awani daren litinin sai a asibiti ya kwana.
Wasa2 dai al'amira sun fara tsauri, doctor baisan waye akansaba, kuma indai idonsa biyu bashida magana saita *ban saketa ba*, wannan yasa hankalinsu yayansa yafara tashi suka fara tausayinsa kuma, dan abin yafara wuce makiďi da rawa.

Ahaka cikina yashiga wata biyar, nima kaina nazama mara lafiyar, kulum daga tunani sai kuka, duk sanda na kalli cikina sainayi kuka, har banason tuna inada ciki, duk halin da doctor yake ciki labari yana zuwa mini, dansu aunty salma suna zuwa ganinsa hakama su gwaggo.
Jikin doctor yay tsanani dole aka maidashi k'asar indiya, dan ciwon zuciya yana neman aikashi lahira, kowa yana tausaya masa.
Ban ta6a zuwa ganinsaba saidai kusan tare muke jinyar dan kullum zuciyata tana damuwa da halin dayake ciki.
Karna jaku da nisa, haka cikina harya cika wata tara, zuwa sanan jikin doctor da sauk'i amma ba'a dawo dashi 9ja ba yana indiya abinsa.
Awani dare juma'a na farka da nak'uda, cikin hanzari muka nufi asibiti, tun anasaran zan haihu acikin awa biyu har likitocin suka fidda rai, dan har washe garin ranar haihuwa shiru sai bak'ar azabar danake sha.
Har k'arfe sha biyun rana haihuwa shiru, zuwa sannan k'arfina yagama k'arewa, ko ďaga hannuna bana iyawa bare kuma nayi wani nishi, ganin halin danake ciki aka yanke shawarar yimini aiki.
Babu musu su abbah suka yarda, dadyn su deexerh yasa hannu a maimakon doctor, aka shiga dani ďakin tiyata.
Ancuromin yaro namiji k'ato mai kama da babansa kamar an tsaga kara, lallai yau naga farinciki wajen dangin doctor danawa dangin, kowa kamar yacinye yaron haka yakeji, haka nima kowa yana tausaya mini da addu'ar samun lafiya.
Duk wata hidima yayansa yayita, kuma shima ansanar dashi na haihu, yayi farinciki kuma yasha kuka, dan ranar saida ciwonsa yak'ara tashi, likitoci sunata faďa akan adaina gaya masa komai daya danganci 6acin rai.
Ina gadon asibiti

Please Login or Register in order to submit comment