Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko gsk?..
Dariya kawai Xoxo tayi batace komaiba.
Amota kam Dr Isma'il yashafa fuskarta iman, ahankali ta bud'e idonta, jin kanta acinyar mutum yasa ta ta tashi da Sauri.
Ido ta waro Dan ganin Dr Isma'il dake binta da kallo, ya ce, "kinsha barci?.
Batace komaiba sai duk'ar dakanta datayi saboda wata irin kunyarsa datakeji yau.
Shima ya lura da hakan shiyyasa yayi murmushi, itakuma tabud'e mortar da Sauri tafito..
Da gudu Reefat Tazo ta rungumeta kai iman Ashe kina ciki?, wlhy da harna yarda da zancen hafsat.
Murmushi iman tayi ta ce, " amarya kinsha k'amshi.
Bayan Reefat sun gaisa dasu Dr Isma'il, ta ce, "lah ya Nabeel da harda kai?, wlhy kuwa Aysha aii bammasan ke k'awarsu my hafsat bace.
Wlhy kuwa in k'awayenane, tunsanda kazo makarantarmu d'aukar Doctor naganeka bandai fad'a musu bane kawai.
Ayya to bari muma muk'arasa cikin gida ko?.
Okey to sannunku da hanya.
Yauwa kema sannu.
Dr Isma'il yamatso Kusada iman, ya ce, " kisamu ruwa mai zafi kiyi wanka zakiji k'arfin jikinki zuwa anjima zan kawo miki magani tunda kusane.
Kanta ak'asa tace to.

Koda suka Shiga gida Reefat sai tsiya takema iman, iman ta ce, "aii banibace abar yima surutu hafsat CE, saiwani 6oye manager take tsakaninta da Nabeel.
Dariya Xoxo tayi kawai Dan sunxo k'ofar Shiga falon su Reefat.
Tarba akaimusu ta mutunci Maman su Reefat taji dad'in ganinsu sosai.
Liyafa aka shirya musu sosai suka koma gidan makwafta Inda su Reefat suke zamna kunshi, Dan gidansu Reefat cike yake dam da mutane.
Saida suka fara yin wanka sanan suka zaunasukaci sukasha, aka baje kolin firar yaushe gamo, jisuke tamkar sun shekara BASA tare da juna.
Acikin firarrne iman takecewa wai Reefat ya akayi hakane?.
Idanun Reefat suka ciko da kwalla kubari kawai 'yan uwa, wlhy duk baffane da wannan aikin, wai tunda ba'asan randa za'a koma yajin aikinba to ayi auren kawai, dukda INA bala'in son yaa usman kuma kun sani amma wlhy banso hakaba, naso saina gama kawai.
Xoxo ta ce, " to kiyi addu'a ALLAH yasa haka shiyafi alkairi, Dan wlhy nimafa aurennan zanyi.
Gaba d'aya suke kallonta da mamaki.
Nan ta labarta musu yanda sukayi da Dr Nabeel amota, ya ce, "shifa Sam baixo da wasaba, suna komawa daga bikinnan zaizo gidansu wajen iyayenta daganan aturo manya.
Sunyi murna dajin haka danhaka suka rungume juna suna kukan dad'i.
Xoxo ta ce, " saura iman kema muna addu'ar ki koma kwanannan gaky, Dan muna buk'atar k'anin musayeef.
Hummm 'yana iska kunkuma dawo kaina.
Bawani iskanci anan, Reefat yaufa acinyar Dr Isma'il taxo.
Kai gaba?.
"ALLAH kuwa".
Iman wai haka?.
Matsalarkuce iman tafad'a tana kwanciya.
Kwashewa sukayi da dariya Reefat ta ce, " kice soyayya akasha amota?, lallai kallo ya wuceni.
Aii kuwadai kallo ya wuceki, shiru iman yayi musu.
Haka suka raba dare ranar suna hira.

6angaren su Dr Isma'il makuwa, komai daidai, tarba suka samu sosai dama mom d'in Nabeel tana nan tazo itada k'annensa.
Bayan sun huta Dr Isma'il yamatsa sai sunje an siyoma iman magani, Dr Nabeel ya CE, "kaima kasan rashin Sabon tafiya mai nisane yasata aman bawani abuba, kuma datayi barci normal zata tashi.
Badan yasoba ya hak'ura amma saida yakirata ya ce, tasamu farasitimol tasha.

_" washe gari 2:30pm aka d'aura auren Shareefat da yaa usman"_
To saimuce ALLAH yasanya alkairi.
Bayan angama d'aurin aure Dr Isma'il yaso ganin Iman amma hakan ya gagara, gashi yakira wayarta akashe, hakama ta Xoxo arufe, yasan sunacan sauna hidima, balle sune amararori k'irjin biki lol.

K'arfe 7:30pm akakai amarya d'akinta, k'arfe 8:30pm za aje liyafar cin abincin dare, Dan haka su iman suna zuwa gidan suka hau shiri na k'asaita.
Humm fad'a muku yanda suka had'uma aii 6ata lokacine ammafa sun kashe kalla, kuma dolene ido ya kallesu, babu Wanda zaiga iman ya CE, "ta ta6a aure barema harda haihu.
Hakama amarya tayi k'yau sosai cikin kwalliyar amare abin sai Wanda yagani komai zam zam.
Bayan sungama shiri abokan Ango suka fara kwasar k'awayen amarya Dan ance babu African time.
Dr Isma'il da Dr Nabeel gafe suka tsaya Dan babu budurwar dazasu d'auka saisu Xoxo.
Sukam sune k'arshe Dan tare suka fito da amarya, bayan amarya tashiga mortar da Ango ke zaune sukuma suka fara k'ok'arin Shiga wata motar guy.
Da Saudi Dr Isma'il yaymusu magana suka juyo, su bamasu lura dasuba sai yanzu.
Sunshiga motarsu Dr Nabeel suka tafi, Duk sunwani susuce da ganin kwalliyar su iman, dukda suma sunyi gayune cikin farar shadda d'inkin boda, yayi bala'in musu k'yau sosai, kowa yagani said k'yasa😉lol...................




*_"Kuyi hak'uri dajina shiru wani d'an uzurine yarik'eni."_*




*luv u oll my fan's*
*(((S)))..........2017*


*_BAN SAKETA BA!!._*





*_NA Bilyn Abdul_*




_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*





*miya kamata nayi?*
_Humm *Mad'igo wa'iyazubillah* Kai jama'a wanan rayuwar ko dabbobi basayinta wlhy, haba 'yar uwa mizakiji ajikin 'yar uwarki mace?, miyasa zaki bari shaid'an yayi tasiri akanki?._
_tawani 6angaren ina ganin laifin iyaye, wata yarinyar datakai shekara goma zaka fara ganin tana buk'atar aure, zuwa shekara 15 tayi nisa da sha'awa, amma zakiga wata uwar bata kulawa._
_dayawa wasu yaranmu sunada tsoron yin iskanci da maza, saboda iyaye sunfi tsoratar damu akan karmu yarda da namiji, basu cika kulawa akan gargad'in tarayya da k'awayeba, shiyyasa saikiga k'awa ta dilmiya yarinyarki wajen biyan buk'atar juna, saboda wanan hanyar mai sauk'ice_.
_zata samu biyan buk'atarta cikin sauk'i batareda an ganeta kai tsayeba, humm wata sa'in k'awanfa bala'ine wlhy_.
Muhad'u a page nagaba.
*ALLAH yasa mu gane*




*(page 28)*
Iman sai satar kallon Dr Isma'il takeyi yayi bala'in yimata k'yau, azuciyarta ta ce, "inama zai koma saka manyan kaya koda yaushe, wlhy da yaringa yin k'yau.....
Tanacan tana zancen zuci saitaji wani lallausan hannu ya rik'o hannunta, da sauri tad'ago matsakaita idanunta ta sauke akan Dr Isma'il, Ashe sun dad'e da isowa bata saniba.
Ta sauke idanunta ahankali, sanan tayi k'ok'arin zame hannunta amma hakan ya gagara.
Muryarsa mai amo da alamun sark'ewa ta sauka acikin dodon kunnenta, ya ce, ''kifito mana, tun d'azun su Nabeel sun shige da amarya.
Da sauri takalli gefenta babu Xoxo, Gavan motarma babu Dr Nabeel, tafito da sauri, tareda tambayar kanta wai har yaushe sukama iso da har bataji fitar Xoxo ba.
Dr Isma'il yak'araso inda take gaff tamkar zai rungumeta, idanunsa akanta, ya ce, " wai tunaninmi kikeyi ne haka?.
Shiru tayi tana k'yafta idanu.
Yasaka d'anyatsansa d'aya akan le6enta dayasha uban janbaki sai walk'iya yakeyi, da sauri ta d'ago tana kallonsa, d'an yatsansa ya nuna mata Wanda ya dangwalo janbakin, wannanfa?, yafad'a yana d'aure fuska.
Idanunta ta sauke k'asa batareda tace masa komaiba.
"Tambayarkifa nakeyi?.
Ak'ufule ta ce, " janbaki.
Humm janbaki ya maimaita ahankali, ha6arta yad'ago yana kallon fuskarta, ita kuma ta lumshe idanunta dakeda gashi gazar gazar sunji maskara duksun mik'e. Yad'an cije le6ensa, dama wanan kwalliyar ta Matan aure ce?.
Bud'e idanunta tayi ta sauke akansa, ban ganeba tafad'a tana ture hannunsa, baijanye hannunba, itama saita k'yalesa, amma ta maida kanta k'asa, tana kallon bak'i agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa.
Muryarsa cike da kishi ya ce, "wannan kwalliyar bata dace dakeba saudat saidai a d'akinki, amma kiduba taron jama'ar dake wajenan maza nawane dazasu kalleki, yabi jikinta da kallo doguwar rigace ta jan material bata kamata sosaiba amma dukda haka yaji kishi barinta tashiga wajen ahaka, Dan ALLAH kalli rigar dake jikinki.
Iman ta ture hannunsa da k'arfi sanan tabi jikinta da kallo tad'ago tana kallonsa miye laifin rigarnan Dan ALLAH?, nifa gsky kafara takurama rayuwata, lokaci yayi dazaka barni nasha iska mai dad'i, kwalliya kuma nibanga aibuntaba koso kake nazo wajen kamar wata korarriyane, cike da tsiwa take maganar Dan haka ta k'ara tunzura masa zuciya.
Takowa yayi zai matso Kusada ita ta matsa, ya matso, ta matsa, dahaka har suka dangane da wata mota, ta matse jikinta da motar tana k'ara d'aure fuska, shima fuskarsa tamau take kamar ba Dr Isma'il ba uncle d'in Deexerh.
Wani irin tsorone yaratsa zuciyar Iman, Dan batasan miyake shirin yimataba, muryarta na rawa tace doctor please kayi hak'uri Dan ALLAH.
dukda idanunta arufe suke wannan bai hanashi hararartaba, yamatsar da fuskarsa GAF da tata har sunajin saukar numfashin juna, cikin wata irin murya tamkar mai rad'a ya ce, " kina tunanin zan iya d'aga mini k'afa kishiga taron jama'arnan da wannan janbakin?.
Da sauri ta bud'e idanunta kafin tace wani Abu ya had'e bakinsu waje d'aya, janbakin yashiga tsotsewa cike da nuna kwarewa, Iman sai dukan bayansa take amma a banza.

Xoxo da Dr Nabeel suna zaune a tebir d'aya hira suke k'asa2, Xoxo tafara wayge2 waini inasu Iman ko har yanzu basu shigobane?...
Kafin Dr Nabeel yabata amsa wasu guys suka k'araso wajen, Nabeel yamik'a musu hannu yana fad'in a'a Auwal kun k'araso.
Eh wlhy d'an uwa, yaja hannunsa suka bar wajen, yayinda sauran abokan Auwal suka take musu bata, saida sukaje nesa da Xoxo sanan Auwal ya CE, Nabeel dama haka abokinka yake?.
Da sauri Nabeel ya ce, "wane abokin nawa?, ko Isma'il?.
" eh mana shi, bashine kukazo tareba.
Shine Cewar Dr Nabeel.
Hummm to wlhy gashi can a tsakanin motoci ya matse 'yar mutane yana sumbata.
'Yar mutane kuma?. Kai badai Isma'il ba, Dan bayida wannan halin, amma wane irin kayane ajikinta?.
Kama hannunsa Auwal yayi, kaga muje kagani sai, k'ila kafi yarda da zancenmu.
Dr Nabeel ya sauke numfashi yana kauda kai daga kallonsu Dr Isma'il, yaja hannun Auwal suka bar wajen.
Auwal ya kwace hannunsa haba Nabeel yanzu nan barinsa zamuyi harsai yakai da yimata fad'e?, kallifa yanda take dukan bayansa alamar batason abinda yake mata.
Tsaki Dr Nabeel yayi ya ce, "kai dallah malam matarsace fa.
Matarsa kuma?.
Eh Dr Nabeel yafad'a da k'arfi.
Tofa amma yarasa a Inda zai mata wanan abun sai anan kuma aii koda kukazo banganku da mataba.
Harararsa Dr Nabeel yayi, saika gammu tare zaka yarda ita matarsace?, to agidan su Aysha muka barsu, yaciro wayarsa a aljihu, ma'adanar hotuna yashiga saiga hoton Dr Isma'il da Iman da Musayeef suna dariya.
Kalla kagani uban 'yan rashin yarda.
Bayan yagani sauran abokan suka kar6a suka gani, wani ya CE, " kai ammafa sun dace wlhy.
Dr Nabeel ya kar6e wayarsa, saiku muje ciki idan sun shigo Ku kalli yarinyar kugani basuyi kama data hotonnanba ne?.

Ciki suka koma, Xoxo ta ce, "lfy dai, labari yabata, tayi dariya, ai tunda muka Shiga mota naga dama yana harararta.
Murmushi Dr Nabeel yayi ya ce, " kinsan mutumina akwai kishi, Nima na daurene kawai nabarki da kwalliyarnan wlhy.
Ta ce, "sorry sir, nidai amin hak'uri daga yau bazan sakeba.
Dariya yayi yana jifanta da wani shu'umin kallo, Xoxo tasa hannunta tarufe fuskarta saboda kunya.

Hummm su Dr Isma'il kam bama Susan wasu sun gansuba, saida ya tsotse janbakin tas sanan yacire bakinsa yana sauke numfashi a wahalce, itakam Iman sai hawaye takeyi tama k'asa wani motsi, yad'agota yarungume yana shafa bayanta alamar lallashi, kece kika jama kanji, ke kanji kinsan ni mutumne mai kishi miyasa zakiyi wanan kwalliyar?.
Ina rik'onki daga yau karki sake kinji, inba hakaba wlhy zanyi abinda yafi haka.
Yad'agota yana share mata hawayen, kinga karkuma ki 6ata kwalliyar k'awayenki suce namiki wani Abu daban.
Harararsa tayi tana turo baki gaba.
Yatsansa d'aya yasaka yabugi bakin Kad'an yana murmushi.
Yakama hannunta kinaga muje karsu Nabeel suyita nemanmu.

Wajen yayi tsit Dan ana addu'ane za'a fara abinda ya Tara mutane, takun takalmansune yasa gaba d'aya mutane suka juyo suna kallomso, Dr Isma'il yana rik'e da hannun Iman.
Auwal ya ce, " kai guys wlhy da gsk matarsace, ammafa babu maicewa ita ta haifi yaronnan, sunfa burgrni.
Sudai su Dr Isma'il wajen su Dr Nabeel suka k'arasa suka zauna, suma akayi addu'ar dasu.
Xoxo sai kallon bakin Iman takeyi, dariya ta taho mata taduk'ar dakai tayi abinta sanan ta d'ago.
Dr Nabeel ya kalli Dr Isma'il yana murmushi, yaje saitin kunnensa yace malam ka goge jambaki a le6enka.
Murmushi Dr Isma'il yayi, tareda saka hanki ya goge bakinsa.
Tunda aka fara abubuwa Iman kanta yana k'asa tak'i yarda ta had'a ido koda Xoxo, gani take kamar sunga abinda yafaru.
Ko awajen lik'i Dr Isma'il hanata sakewa yayi, da'aka kirata tabama amarya shawarama tare sukaje wajen, aiko sunsha hotuna, wasu sai fad'i suke kun dace gsky.
Haka aka gama taron Iman duk tana a takure saboda Dr Isma'il yabi ya katantaneta, karfe 12:00pm daidai aka tashi.
Daganan gidan Amarya aka wuce dasu.
Kowa yana zuwa yanemi makwanci amma bandasu Xoxo, hira suka dasa sabuwa.

Xoxo ta ce, "Iman wai d'azu mikuka tsaya yi awaje keda daddyn Musayeef?.
Babu komai tafad'a cikin rashin gsky.
Hummm kinsan dakuka shigo miya birgeni?, Iman ta harareta kinsanfa banason iskanci.
Babu wani iskanci, towaima miya kawo janbaki a le6en daddyn musayeef?.
Kije ki tambayeshi mana ba abokin saurayinki bane.
Xoxo da Reefat suka tuntsure da dariya harda tafawa.
Iman takaima Reefat duka 'yar iska kema gobe iyanzu kina hannun yaa Usman, ALLAH yasa yay miki sambad'e bad'e, tana gama fad'a taja bargo.
Duk iskancin dasuke mata bata sake kulasuba.
Na ce, " humm 'yamma tanan akwai shafta gsky, ko Yaya za'a rabu yayin tafiyarsu Iman?............












*Luv u I'll my fan's*
*((((S))))........2017*



[8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*






*_NA Billyn Abdul_*





_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com




*miya kamata nayi?*
_iyaye muringa kula da 'ya'yanmu, muringa kula kuma dawa suke mu'amullah, akwai had'ari yanzu sosai akan yaranmu maza da mata, Dan kowane yana iya fuskantar k'alubale daga 6ata gari, yara mazama wai yanzu suma saikiji ance anyi musu fad'e. Humm ya salam._
_wai Dan ALLAH ina akeso mushiga mu 6uyane, wannan wane irin masiface, yanzufa takai wai kishiya da kishiya zasu iya mad'igo, humm mata wai ina kishin damuke ik'irarin munayi?, kai rayuwa Yaya da k'anwa saikiga suna mad'igo, hasbinallahu wani'imal wakil, wanan wanne irin k'azantace, muringa tuna yanda ALLAH yayi da jama'ar *"ANNABI LU'DU A,S"*, ni d'alibar ilimice shiyyasa bazan kawo ayaba, amma kuje kuyi bincike Wanda baisan makomarsuba tofa zaiji._
*ALLAH yasa mugane.*



*_"cigiya 'yan uwa INA cigiyar 'yar uwata Riddallah 2days ta 6acema ganina😭."_*

*(page 29)*
Washe gari akayi walima da k'arfe 2:00pm Dan haka bak'in dake kusa suka fara kama gabansu, su Xoxo ma gobe idan ALLAH ya kaimu zasu tafi.
Su kad'ai aka baro gidan amaryar, sunata hirarsu da tsokanar juna kamar bazasu rabuba.
Har dare suna gidan, saida suka gyara mata ko ina sanan, abokan ango suka shigo hardasu Dr isma'il, bayan d'an hira da barkwanci irin na abokai suka mik'e zasu tafi.
Tofa yanzufa akeyinta, Dan su iman rungume juna sukayi suna kwasar kuka, Dan daga yanzu bazasu dawoba tafiyar asuba zasuyi, abokan angon duk sun tsaya suna kallon ikon ALLAH, sun birgesu sosai daga gani k'awancen nasu yanada dank'o.
Dak'yar suka rabu da juna, ya Usman yarungume Reefat yana lallashi, shima Dr Isma'il yacewa su iman kuyi hak'uri mutafi dare yanayi.
Bayanda zasuyi suka fito kowa yana share hawaye, koda suka Shiga motama kukansu suka cigaba.
Gidan su Reefat suka kaisu dansuyima mamansu Reefat sallama.
Kayan biki nagani nafad'a Mmn Reefat ta had'a musu, harda tsaraba ta musamman, taso su kwana anan amma Dr Nabeel ya ce, "tayi hak'uri tafiyar asuba zasuyi.
Bayanda zatayi haka tarakosu har Mota, daga nan ba gidan sukayi kai tsayeba zagayawa cikin gari Dr Nabeel yaytayi dasu harsuka d'an saki jikinsu, daganan yakaisu gidan dasu mom d'insa suke.
Nanma tarbarsu akayi sosai k'annan Dr Nabeel sai murnar ganinsu sukeyi, Ayeesh da Maimuna, sumadai 'yammatane Dan zasuyi sa'anni dasu Xoxo, mom d'in Dr Nabeel sai murna take, ta ce, "to ina matar ta Isma'il ina kuma ta Nabeel?.
Iman da Xoxo sukayi k'asa da kai sunajin kunya, Dr Nabeel ya ce, " mom ga Iman matar Isma'il yanuna iman.
Wanan kuma itace..... Saikuma yay shiru yana Sosa k'eya, su Ayeesh suka tuntsure da dariya, ya hararesu.
Masha ALLAHU 'ya'yana ALLAH yay muku albarka kunji, ALLAH yasa kuduka abokan arzik'in junane, Ameen su Maimuna suka amsa.
d'aki d'aya suka kwana dasu Maimuna sunsha labari sosai, dansu Ayeesh akwai surutu, 😉lol.
ana fitowa daga sallar asuba suka shirya, maimuna da Ayeesh sukace zasubi motarsu, hararsu Dr Nabeel yayi, ya ce, "tare mukazo dakune?, a'a maimuna tafad'a.
Ayeesh ta ce, " Yaya Dan ALLAH kabarmu, kinsan ALLAH kokimin shiru kona bigeki anan, dama kuntafi wajen mom tunkafin dare yamuku, Ku saima gobe zaku taho.
Babu yanda zasuyi haka suka hak'ura, dukda Magiyar da Dr Isma'il yay MASA akan yabarsu, ya ce, ''wlhy Isma'il bazasu bimubafa.
Haka suka Shiga mota su Ayeesh suna d'aga musu hannu, anan ma kayan biki sosai mom d'in Dr Nabeel ta had'a musu.
Dr Isma'il ne yake tuk'in yanzu, sharara gudu yake sosai yayinda iman da Xoxo sukayi barci kamar randa suka taho.
Wanan karon basu tsaya ko inaba, Dan abinci mom tad'an shiryo musu, sai wajen k'arfe uku suka tsaya sukai sallar azuhur da la'asar, daga nan suka sake d'aukar hanya, cikin amincin ALLAH karfe 5:15pm acikin kano tayi musu, gidan su iman aka ajiyesu su, Dan Xoxo saida safe zata k'arasa gida.
Gwaggo da deeni da musayeef sunyi farincikin dawowarsu, bayan sunyi wanka sukaci abinci aka zauna bama gwaggo labarin biki da yanda ya gudana, da hotuna.
Gwaggo taji dad'in yanda aka karramasu sosai.

A can kuwa saida Dr Isma'il ya sauke Dr Nabeel sanan yanufi gidansa, 6angaren mama yafara zuwa, bayan sun gaisa yashiga wajensu yayansa daganan yanufi 6angarensa, tun afalo yafara gamo da abin haushi domin falon kaca2 kamar ba'a sharewa, tsaki yaja yashiga d'akin iman Inda yamaida d'akinsa, kai kawai ya girgiza Dan nannmadai abin haushinne, yanda yabar d'akin haka yazo yasamu abinsa.
Zagewa yayi yagyara tsaf, sanan yayi wanka, harya kwanta baiji motsin Raihan ba, haushinta yakeji Dan haka yay kwanciyarsa.
Itakam bamata gidan, tun yamma suka Fita itada aunty sai k'arfe 9 na dare suka dawo, babu Wanda yace mata Dr Isma'il yadawo, Dan haka tana dawowa tashige d'akinta ta kwanta.

*washe gari*
Da Asuba yafita masallaci batareda ya kalli ko hanyar d'akintaba, saida gari yafara haske sanan yashigo, saida yaje suka gaisa da mama sanan yashigo.
Raihan ta tsaya cak tana kallon ikon ALLAH, shima binta yake da kallo fuska a d'aure, dayake ta karantu da ilimin Rayuwa saita basar da mamakinta tazo ta rungumeshi.
My one yaushe kadawo bansaniba?, baice mata komaiba, tad'ago tana kallonsa, ganin yanda yake hara rarta saita shiga aika masa da sak'wanni, Raihan irin fitunannun matan nanne, kwana ukunnan atakure tayisu ta daurene kawai.
Ogafa yafara yin sanyi, Dan abinda take MASA komai dakewarsa saiya kalleta, baimasan sanda ya d'auketa sukayi d'akiba, Dama ga garin dad'an sanyi sayin hadari dake tasowa, humm afito lafiya🙄.

Sai wajen shabiyu suka tashi tare sukayi wanka, Raihan sai salo takeyi ita matar so, (nace hummm), bayan sun shiryane yasata ta gyara falon da duk Inda yadace, 6angaren mama yaje sukaita hirarsu har aka kira sallar azuhur, daga nan yanufi masallaci.
Koda yadawo bainufi wajen mamaba saiya wuce 6angarensa, harya gota d'akin Raihan saiyaji magana k'asa2 Dan haka yadawo bayan, ak'ofar d'akin ya tsaya cak danjin furicin aunty.
Hummm ammafa auta kinyi k'ok'ari gsky, shiyyasa duk cikin k'annena nafi sonki, yanzu kina nufin yau da safe ya kusanceki?, kuma da maganin kikayi amfani?.
Wlhy kuwa aunty, Aida ya had'e girar sama data k'asa zaimin buyagi, naje na rungumeshi, narigaya na gano lagonsa na Shiga aika masa sakwanni, ai tuni yakwasheni muka tafi d'akinsa.
Da k'yau k'anwata, kidage amfani da maganinnan kamar yanda malam yace, ''saiya manta da waccan banzar dayake ik'irarin akanta ciwon zuciya ya sameshi, yanda mukayi nasarar fiddata agidannan haka zamuyi nasarar gogeta azuciyarsa.
Idanu Dr Isma'il yazaro waje..... Raihan taci gaba da fad'in, aii ni wlhy aunty har yanzu lamarinki mamaki yake bani, yanda har kika iyayin rubutun Yaa Isma'il kamarshi ya rubuta, kuma kowa ya d'auka da gsk shiyya rubuta sakin.
Dariya suka kwashe da ita suka ta6a kamar wasu k'awaye..........da k'arfi Dr Isma'il yadaki k'ofar d'akin, arikice suka d'ago suna kallonsa.
Wani kukan kura yayi yadamk'i Wuyan rigar Aunty ya sharara mata mari saubiyu, yacigaba da jibgar banza.
Ihun aunty da kururuwan Raihan yasa mama da mom da marwan isowa da gudu, sai janye Dr Isma'il suke amma bai daina dukan aunty ba.
Su mama sunrasa yanda zasuyi gashi ya fasa mata kai Dan dukanta yake ta ko ina, waya mama tasa takira Yaya.
Mansur komi kakeyi kazo gidan yanzunan babu lafiya, bata jira amsarsaba ta yanke wayar.
Cikin minti 20 saiga Yaya sanan Dr Isma'il Yakoma dukan Raihan yabar aunty tana sauke numfashi da k'yar.
Marinsa Yaya yayi, Isma'il wai bakada hankaline misuka yimakane?.
Hawaye yafara yanna nuna su aunty dake kwance suna jiyyar Kansu, bakinsa sai rawa yake alamar yanason yayi magana amma ya kasa, ya dafe k'irjinsa da sauri, luuuuuu yayi baya zai fad'i da sauri Yaya ya rik'eshi yafad'o a hannunsa.
Yaya ya girgizashi Isma'il! Isma'il!!, shiru, da sauri ya CE, marwan muje mota ya suma.
Mama tafashe da kuka, tana fad'in wayyo Isma'il kana ganin rayuwa kaidai Dan ALLAH karka mutu kabarni.
Marwan yana gyara mota za'a saka Dr Isma'il saiga Nabeel ya shigo, da sauri yak'araso yana tambayar lfy?.
Suma yayi cewar Yaya, Dr Nabeel ya ce, "Yaya amaidashi ciki saina dubashi bama sai Anje asibitiba.
Haka kuwa akayi aka maida Dr Isma'il d'aki, taimakon gaggawa Dr Nabeel yashiga bashi, bayan kamar Minti goma ya farfad'o.
ALLAH yasama akwai allurai da ake MASA, Nabeel yay masa allura yasamu barci, saida yak'ara kwantar musu da hankali sanan yatafi.

Mama takali su aunty da duk hankalinsu yake atashe tun d'azu, zuciyar Raihan tayi rauni sosai, bata ta6a ganin ciwon Dr Isma'il ba, batayi zaton haka yake shan wahalaba, tayi danasanin biyewa aunty, gashi tun ba'aje ko inaba komai ya rikice, tasamu Dr Isma'il kuma

Please Login or Register in order to submit comment