Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuji tsoron ALLAH kodan katange family naku fad'awa cikin bala'in fasik'anci, saimun gyara ALLAH zai gyara mana, sakawa 'ya'ya da k'anne sasari na hana Fita bazai hana ubangiji ya aiko wani k'ato har gidanka ya6ata maka rayuwar mata, 'ya'ya, k'anne, yayye, ba a yima ALLAH wayau d'an uwa._
*ALLAH yasa mugane*




*(page 35 & 36)*
Ayyeee mata kuk'ame k'am sabuwar rawa.
Iman Doctor Ku k'ame k'am kusami nutsuwa.........
Dariya iman tayi kai sisi ALLAH yashiryaki wlhy, ina kuma kika samo wanan wak'ar?.
Hhhhh sabuwar wak'ar gwanja ce amaryar, k'amshi, ya amarci.
Hummmm amarci kuma?.
Eh mana.
Yana wajenku.
Tofa mu asuwa, haryau banbar kwana agadon Umma ba, aiiko bana amsa sunan amaryaba.
Karki damu lokaci kad'an yarage kikoma kwana kusada....... Saikuma tayi shiru tana kallon Dr isma'il dayake kallonta.
A'a yakikayi shiru fad'i mana, Xoxo tafad'a tana dariya.
Iman takauda kanta daga kallo sa ta tashi tashige bedroom, 'yar duniya aiba kasa fad'a nayiba, doctor ne akusadani, kuma yakafeni da ido yanajiran mizan fad'a.
Hehehe 'yammatan gaya ga k'yau ga gayu, kice soyewa ake nakira, bari nabarki sai anjima.......
Kafin iman tace wani Abu Xoxo ta yanke wayar tana dariya.
"ALLAH yashiryaki iman tafad'a itama cikin dariyar.
Falo tayi yink'urin dawowa Dr yashigo d'aukeda musayeef dayayi barci, kad'an yarage suyi karo tad'anja baya.
Saman gado yad'orashi sanan ya zauna, iman dake tsaye tana kallonsu cike da sha'awa tayi murmushi.
Dr isma'il yad'ago yana kallonta, ya ce, " har angama gulmar?.
πŸ‘πŸ‘gulma kuma?, gulmarwa mukayi?.
Ya za'ayi nasani tunda kin gudo d'aki.
Hu'um to ba gulmar kowa mukeyiba mudai.
Murmushi yayi yana mai k'are mata kallo cikeda shauk'i.......garammm aka bugo k'ofa, da sauri iman tamatsa Dan k'ofar tad'an daketa kad'an.
Auntyce da Raihan, iman taimusu kallo d'aya ta d'auke kai, Dr Isma'il yatashi zaune yana kallonsu.
Shigowa sukayi cikin d'akin, (amamakin iman saitaga sun durk'usa ak'asa), tofa sabon salo iman tafad'a azuciyarta.
Raihan ta ce, yaa isma'il Dan girman ALLAH kuyi hak'uri Ku gafarcemu, Dan ALLAH kabama Yaya hak'uri shima ya yafema auntyna wlhy tana bala'in sonsa.
Wani kallo yakemusu, amma kuma bai fahimci zancen nasuba, baikuma tambayesuba.
Itadai iman tana tsaye tana kallonsu.
Aunty tajuyo tana kallon iman, iman Dan ALLAH kiyafe mana kema, munyi kuskure ki gafarcemu..... Tak'are maganar hawaye sunan sauna a kumatunta.
Sumba iman tausayi Dan haka tabud'e baki zatayimusu magana, Dr Isma'il ya ce, "my life karkice musu komai.
Shiru tayi tana kallonsa, yataso ahankali yakama hannunta, saman cinyarsa ya d'orata, dukda tanajin kunya haka ta dake ta zauna, yajuyo da fuskarta suna kallon juna.
My life ke harkin yarda da tuban wad'annan shaid'anun?, sunefa masu kulla raba aure, abinda ALLAH bayaso, dukda bansan abinda Yaya yayiba nasan yayi dadai wlhy, banaso ko a mafarki kiyafema Wanda ya rabani dake NA tsawon shekara hud'u, wand'anda suka jawo na kwanta a asibiti natsawon wata uku, wad'anda suka hana zukatan dangina nutsuwa, nasan basuyi nadamaba Dan har yanzu basu riski makarantar nadamaba.
Iman ta kad'an kai batareda tayi maganaba.
Shikuma yadaka musu tsawa, wlhy koku fitarmin ad'aki kokuma kufuskanci mummunan 6acin rai daga gareni, wlhy na tsaneku banason ganinku, shaid'anu kawai.
Sum sum aunty da Raihan suka fice, kowa zuciyarsa tana zafi.
Suna Fita suka kalli juna sukai murmushi, aunty ta ce, " sakarkaru sunfa zata da gsk Neman yafiyar mukazo.
Raihan tayi 'yar dariya bar kidahumai aunty.
Aunty ta ce, "ina fata kin saka?, kinsan malam ya ce, " bayaso asamu Marsala ana farko.
Nasaka aunty saura kuma nagobe, ai zasuci ubansune agidanan, sai sunyi Dana Sanin barinmu, aunty da Raihan suka ta6a tamkar wasu k'awaye.
(Ni Bilyn Abdul na ce, "hummmm
πŸ‘πŸ‘.)

Dr Isma'il da iman kam rakasu sukai da ido, iman har zuciyarta ta yarda sunyi nadama, Amma Dr yanaji ajikinsa akwai abinda suke shiryawa, badaicema iman komaiba akan hakan saiyayi bincike.

*bayan kwana uku*
Bayan kwana uku da dawowar iman, kullum tana zubama Dr k'arya tana fashin Sallah, saiya Fita saitayi sallarta, shikam ko kad'an baikawo k'arya takeba a ransa.
Yauma suna gama break yay shiri cikin watad'anyar shadda jaa yamurza bak'ar hula, iman natsaye tana kallonsa, saida yagama saka hular sannan yajuyo yana kallonta, murmushi sukaima juna, yamatsa daf da ita, my life nafa fara gazawa gsky.
Kallonsa tayi tana murmushi ta CE, ''akan mi ka Gaza?.
Akanki yafad'a yana rungumeta.
Ajiyar zuciya ta saki batareda tace komaiba.
Yad'agota daga jikinsa yana kallon fuskarta, ya ce, " bakice komaiba.
Mikakeso nace to?..
Kicemin bak'onki ya tafi.......
Kafin tabashi amsa musayeef da 'yan biyu suka shigo da gudu hannunsu d'auke da kayan sweet.
Dr Isma'il yasaki iman yana kallon su musayeef.
iye 'yan yara yara waya Baku?.
Cikin tsalle sukace aunty deexerh ce.
Kai ina aunty dee.... d'in?, tana wajen mama suka fad'a suna tsalle.
Iman ta ce, "lallai dee.... Tana fushi damu, harta dawo babuko waya.
Dariya Dr Isma'il yayi, ina bayanta tayi fushi sosai, kin dawo gidan uncle d'inta bata saniba, dama tagayamin kin shareta.
aii laifi tamin shiyyasa na shareta.
A to bari nayi shiru da bakina saikun had'u kenan.
Dariya iman tayi.
Ya ce, " bari nawuce ana jirana.
Iman tad'an ta6e fuska towaima wanan kwalliyar ina ta dosane?.
Gira yad'aga mata ya ce, "tad'i mana, kisan nasamo ta uku, iman ta had'e fuska sosai ta ce, to na mamajo saura ta hud'u.
Dariya yayi danganin yanda ta had'e fuska, ya shafa fuskar tata yana d'aga mata gira, karki damu itama tana hanya uwargidana, baijira cewartaba yafice da Sauri Dan Dr Nabeel yana jiransa.

Wasu hawaye suka zubo a kumatun imam itafa azaton da gsk yakeyi, bakin gado ta zauna zuciyarta na zafi.
Deexerh dake tsaye tun d'azu tayi murmushi Dan taji zancensu na k'arshe, ahankali tak'arasa Inda iman take ta zauna.
Imam tajuyo catake shine yadawo saitaga deexerh, Harar deexerh tayi tayunk'ura zata mik'e.
Dasauri deexerh tarik'o hannunta sorry my aunty Dan ALLAH ki saurareni mana.
Komawa imam yayi ta zauna, deexerh ta ce, " haba aunty na laifin mi nayi ake fushi dani.
Hawaye imam tashare Dan haryanzu maganar Dr yana cizon zuciyarta, ta ce, "a'a deexerh Niba auntyki bace tunda har kika iya 6oyemin uncle d'inki yayi aure.
Nasan dama komai dad'ewa kikaji labarinnan zakiyi fushi dani amma wlhy ban 6oye miki Dan wani abuba, danni ban d'auki Auren waccan sakaran a komaiba, amma kiyi hak'uri Dan ALLAH.
Murmushi iman tayi, shike nan na hak'ura.
Yauwa aunty na dee..... Tafad'a tana dariya, amma aunty nayi bak'inciki da ban nan randa kika dawo, amma marwan Duk yabani labari, nadad'e banyi farincikin dawowa gidan nanba kamar wanan karon.
Dariya imam tayi kai dee..... Banda k'aryafa?, ALLAH kuwa aunty, saidai nadawo da d'ammarar cin uban shegunayennan, sai sunbar gidannan kwanannan.
Imam ta zaro ido, kai dee.... A'a Dan ALLAH karkiyi musu komai, wlhy sunyi nadama ranarma saida sukazo Harnan suka bamu hak'uri.
Humm aunty kenan ke har kin yarda da tubansu?, ni nace miki k'arya suke, nasan halinsu sosai Dan aunty dakike gani ba k'aramar shaid'aniya baceba, kemafa kin zauna da ita kinga wasu daga cikin halayenta basai nabaki labariba, ke ganauce ba jiyauba..
Hakane kuma imam tafad'a, haka dai iman da deexerh sukaita hira har aka kira sallah suka tashi sukayi.

Bayan sun idar suka nufo fallo daniyar tafiya 6angaren mama, a fallo suka iske Raihan zaune tana kallo Dan yau takeso ta ida cika aikin malam so take kawai imam tafita ad'akinta taje ta aiwatar.
Deexerh tasaki wani wawan tsaki tanabin Raihan da kallon banza, aunty yanzunan har kinyarda kowanne datti yazauna miki afalo?.
Da Sauri Raihan ta kalleta dantasan da ita take, imandai batace komaiba, Raihan har zatayi magana saikuma tayi shiru, dee.... Tayi dariya mai bakin ja6a yakuma kika kasafad'a, fad'i maganarki karta kasheki.
Iman taja hannun dee... Suka fice, kai dee.... Kibari Dan ALLAH matar uncle d'inkicefa kuma 'yar uwarki.
Hummm wannan duk ada ne, ayanzu kam babu wata alak'a atsakaninmu, yanzuma tafara gaini Indai nice.
Suna fita Raihan ta share hawaye, zanyi maganinki kema, baridai nagama da wad'annan sakar Karun, hankalinta kwance tanufi d'akin iman, katifarta tad'a tasaka wasu layu ko k'yan gani babu, tatsaya gaban gadon tana wani sirkulle.
tana gamawa tajuyo zata Fita saifaman murmushi take Dan tasan daga yau imam tagama yawo.
Turus tatsaya baki bud'e tanabin Dr dake tsaye da kallo atsorace.
Takowa yayi cikin d'akin batareda yace komaiba, saida yaje gaban gadon sanan ya ce, "zoki cire abinda kikasamata agado.
Jikin raihansai rawa yake tazo tad'aga tacire layun data ajiye, ya ce, " nasan bayau kika fara saka mataba d'ebo sauran ma, da Sauri taduk'a k'ark'ashin gado saiga wani kasko da da tsokar nama an cacccaka k'ayoyi ajiki.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Dr yaketa ambata, gaba d'aya zufa ta jik'e MASA jiki, waya ya d'auka yakira yayansa. Yaya kana kasuwane?.
A'a isma'il INA gida yanzu babu dad'ewa nashigo.
Yaya Dan ALLAH ka tattaro 'yan gidanan kuzo kuga abinda Nagani INA d'akin imam.
Kagani kuma, minenen kagani??.
Yaya saidai kunzo kawai. Raihan dai tana duk'e ak'asa da 'yan kayan surkullenta sai hawaye takeyi, shikenan aunty tak'ara sakata amatsala itakam tashiga uku, wlhy batason rasa Dr Isma'il Dan tana bala'in sonsa.
Babu dad'ewa saiga gayyar 'yan gidan duka, kowa yashigo saiya rik'e baki, iman ta ce, "na Shiga uku ni saudatu wanan kuma daga INA Doctor?.
Baiyi maganaba saidai nuna mata Raihan yayi.
Jikake tauuuuu deexerh ta d'auke Raihan da wani wawan mari, shima Marwan yabata d'aya a d'aya kuncin, dukanta zasu farayi Yaya hace karsu daketa, Dr isma'il ya ce, " Yaya wlhy kabarsu su zaneta aii ita tajama kanta, kuma nidai gsky Yaya ayau zan saki jahilar nan, wlhy bazan iya jurewaba, kije na sakeki saki uku!!!!.
Wani ihu ta buga tareda rik'e kafafun doctor tana kuka, Dan Girman ALLAH ya isma'il kamin rai narantse da ALLAH bazan sakeba, wlhy aunty CE tasakani.
Yaya yay murmushi itama aii bazata tsallakeba, kema kibita na sakeki saki uku kema, saikuma kuje wani gidan.
Wlhy kummin daidai 'ya'yana ALLAH yay muku albarka, zama da wad'annan yaran aii masifa CE, mamace mai wanan maganar.
Dr isma'il ya ce, "aii wlhy mama banda Abba dakansa yafad'a mana iyayen yarannan 'yan uwansane nikam danace suba jininmu bane, tsinannu gadon tsiya gadon jaraba, wlhy minti talatin nabaku kubar gidanan.
Raihan da aunty kuka suke suna rok'on ayi hak'uri wlhy bazasu sakeba sunyi nadama.
Deexer da marwan suka kalli juna suka shek'e da dariya suka fice.
d'akunan su Raihan sukaje suka ringa Watso musu kayansu waje, duk abinda sukasan na kud'ine sun d'aukeshi Dan iyayensu suka siya, daga aunty har Raihan babu wacce aka kawo dako kofi daga gidansu, duksu yayane sukai musu kayan d'aki.
Kafin su fito duk su dee.... Sungama Watson Musu kaya waje, haka suka Shiga tattarawa suna kuka, Yaya yabasu kud'i ga kud'in mota nan sai abi wani sarkin.
Har k'ofar gida su dee.... Suka rakosu 'yan unguwar sai fitowa suke kallonsu, wasu sai tsine musu suke wasukam suna shima su Yaya albarka, Dan Ansan mugun halin su auntyn a unguwar.
Kowa baya jin tausayinsu bare goyen baya.
*_(ni bilyn Abdul na ce, "tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan doka Raihan da aunty)_*...............







*luv u oll my fan's*
*(((S)))......2017*
[8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*






*_NA Bilyn Abdul_*





_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com




*miya kamata nayi?.*
_duk matakan tsaro dazaka sakama family naka saboda kasancewarka fasik'i bazai hana ALLAH kuntata makaba kaima, Dan ALLAH ba ayi MASA wayau_.
_yanzu mud'auki waya k'aramar alhaki, anyi ittifak'i aduniya babu abinda bature yayi aduniya yakar6u kamar waya._
_zakaga duk talaucin mutum ya mallaki waya, waya tashiga hannun babba da yaro, mace da namiji, talaka da amai kud'i, waya tazama babbar fitina ga rayuwarmu, Dan 6arnarta tafi amfanin yawa, wlhy yanzu 'yarka tana cikin gida saita fad'a tarkon fasik'anci ta dalilin waya_.
_Yarinya tanada waya, zata iya Shiga duk Inda takeso hankali kwance, dama tanada sha'awar yin wani Abu Mara k'yau to amma bata samu hanyaba, saikuma ga waya ta mallaka, zakaga tana chart da k'awarta ta makaranta ko wata 'yar uwarta, 'yar uwarnan tata zata kaita group Wanda babu wata 6arna acikinsa._
_to matsalar da ake fuskanta a group bakowane nagariba, akwai gur6atattu Wanda suna 6oye kansune, to idan tsautsayi yafad'a akan 'yarka sai gur6atattunnan su d'auki No. d'inta sukai wani group nasu, (tunda dama haka sukeyi Idan suka kaika group d'insu inkai irinsune saika zauna idan ba irinsu bane kafita)......._
_kuyi hak'uri mu had'u a page na gaba._
*ALLAH yasa mugane*





*(page 37 & 38)*
Dr yatsaya kaida fata iman bazata Shiga d'akintaba wai ko akwai wani Abu dasu Raihan suka 6oye.
Iman ta langwa6e kai tana kallonsa, daddyn Musayeef ka kwantar da hankalimka, insha ALLAHU babu abinda zai faru, nad'azuma ba wayonmu yasa ka ganiba.
Hakane my life amma aii hanyar lafiya Abita da shekara ko.
Babu yanda zatayi dole tahakura suka Shiga d'akinsa akan da safe za'a bincike d'akin NATA.
Kayansa yacire yashiga wanka, itakuma tana zaune abakin gadon.
Musayeef yashigo d'akin yana d'ingishi, da Sauri ta ce, "kai kuma lfy kake d'ingishi?.
Gabanta yak'araso fuska ayamutse yana yarfe hannu, ya Nuna mata babban yatsan k'afarsa dayake jini.
Ya salam a ina kaje kaji ciwo?.
Aunty maa afalo nabige da kujela.
Ta sauke ajiyar zuciya tana d'aukarshi, saman cinyarta ta d'orashi takama k'afar zata duba doctor yafito daga bayi.
K'arasowa yayi Inda suke yazauna Kusada iman yana tambayar lfy?.
Kafar musaueef tanuna masa batareda tayi maganaba.
Woow! Shugaban hidima a INA kaji ciwo?.
Daddy a falo, yafad'a zaiyi kuka.
Kaga yi shirunka karkayi kuka, kaida zaka zama soja wanan d'an ciwon zakama kuka, ina zuwa..
Iman ta ce, " lallai su soja manya.
Dr Isma'il yazauna yana fad'in baki yardaba kenan??.
A'a nikam miye nawa ALLAH yakaimu lokacin.
Haka nikeson ji kawai.
Yagyarama musayeef wajen, ciwonma baida yawa amma sai jini.
Musayeef ya ce, "aunty maa yunwa nakeji.
Yunwa kuma musayeef?, ita saima yanzu tatuna babu Wanda yaci abincin rana agidan, Dr Isma'il dake bayansu yana saka kaya, ya ce, " badole yaji yunwaba inagama tun break d'in safe, wad'an nan shaid'anun sun mantar damu yunwar cikinmu.
Iman dai batace komaiba ta sauke musayeef daga cinyarta.
Kaga bari nafara maka wanka sanan saimuje kaci abincin.
Ya nok'e kafad'a alamar bayaso.
Ta harareshi kainifa banason ta6ara kamije namaka wanka.
Guduwa yayi Inda Dr yake, yarungume k'afafunsa yana fad'in daddy 6oyeni nifa bana son wankan.
Dr yarik'eshi yana murmushi, haba big boy rashin wankafa k'azantane, ko kanaso aringa cemaka k'azami.
A'a daddy.
Yauwa to jeka amaka wankan.
Nidai daddy saina fara cin abinci za'amin wankan.
Dr yad'ago yana kallon imam, aunty maa Dan ALLAH amana hak'uri muci abincin munajin yuwafa sosai.
Itama fuska ta marairaice Dan ALLAH karka biye masa, kallifa kayan jikinsa, ni bammasan inda yaje yay wannan dattinba.
d'aukar musayeef yayi yana fad'in mudai mun tafi saikin taho.
Rakasu da ido iman kawai tayi, yazatayi da uba da d'an.

Wanka itama tashiga, bayan tafito ganin lokacin sallar la'asar yayi tayo alwala, kayanta da Dr yad'ebo daga d'akinta yasaka a durowarsa taduba tad'akko zani da hijjab.
Tana cikin yin sallah, tayi raka'a ta farko tana ta biyu Dr yashigo d'akin tamkar anjehoshi, tsayawa yayi cak yana kallonta tamkar yau ya fara ganinta.
Ya ce, "hummm dama manya suna k'arya?.
Iman dai sallarta takeyi, saima yanzu ta tuna da shirinta, saurin kauda tunanin tayi tacigaba da sallah anutse.
Dr yafito daga bayi da Alama alwala ya d'auro, ya fice yana wata 'Yar dariya wadda iman batasan fassarartaba.
Koda ta idar da sallar duk jikinta yayi sanyi, tamanta wlhy har tayi saken da Dr yakamata, tagama shafa mai tayi 'Yar kwalliya, sanan tanufi 6angaren mama Dan taci abinci.
Musayeef yana ganinta yagudu cinyar mama, iman ta ce, " haba yaro zan kamakane aii.
Mama da deexerh sukayi dariya, mama ta ce, "mi mai gidana yayine?.
Mama wankafa zanma yaron nan shine yabiyo daddynsa suka fito wai yunwa yakeji, maimakon yaci abincin yadawo namasa wankan shine Yakama wata tashar.
Mama ta shafa kan musayeef asheni mijin nawa k'azamine ban saniba.
Deexerh ta ce, " a'a mama yanzu zamu cakire abinmu, musayeef zomuje ni nayimaka kaji.
Babu musu yabi deexerh.

β€’+β€’+β€’+β€’+β€’+β€’+β€’+β€’
Iman zaune abakin gado tanama musayeef shirin barci, Dr yafito daga bayi da'alama wanka yayi.
Musayeef ya ce, "daddy zaka koyamin game d'in d'azu?.
Dr ya d'aga masa kai, zan koya maka amma ba yauba yaro.
Um'um musayeef yafad'a a shagwa6e, nidai daddy yanzun.
Lallai yaro ka d'obo da zafi, yau baranar koyon game bace ba, Dan inada babban game adaren yau.
Iman ta kalleshi cike da rashin fahimta, shima ita yake Kalo, yad'aga mata gira, ta kauda kai tana girgizawa.
Musayeef dake danna wayar daddynsa shi adole game yake nema, yatako inda Dr yake yabashi wayar, daddy gashi kamomin.
Kaga jeka bama mamanka ta kamomaka nikam mai nake shafawa.
Musayeef yajuya wajen Iman shikuma Dr yacigaba da shirinsa.
Tana kamomasa game ya haye gadon yanayin abinsa.
Dr ya kalli Iman my life bazakiyi shirin barci bane?.
A'a ba yanzuba.
Sai yaushe?.
Sai anjima yanzu banajin barci.
Yawani kafeta da idanu, saikuma yayi murmushi aidama yau ba ranar barcinki bane, kedai tashi kiyi wanka kawai, danma saboda oga na k'yaleki datuni kin tsinci kanki cikin ruwan wanka.
Murmushi Iman tayi, tajuya tana kallon musayeef dayayi busy akan waya, ta ce, ni barinmuku d'akinma zanyi.
Baice komaiba yamik'e yay shiri cikin kayan barci.
Tana zaune yafice saigashi da fresh milk akofi, itadai kallonsa kawai takeyi.
Yazauna Kusada musayeef, my dear son tashi kasha madara.
Musayeef yathi zaune ya haye cinyar daddynsa.
Da Kansa yabashi madarar, yana gama sha yazame yay barci.
Cikin mamaki Iman take kallon Dr, yad'aga mata gira yana gyarama musayeef kwanciya.
Doctor wai mikabama yaron nan?.
Bai bata amsaba saida ya lilli6e musayeef da bargo, sanan yanufota, cak yad'auketa yanufi bayi, tafara zille2.
Bata ankaraba tajita acikin ruwa.
Wani d'an kukan ta6ara tasakar masa, yay dariya Saita burgeshi, dakansa yay mata wanka tanata rufe ido har aka gama, yanad'o kayarsa atawul.
Ta ce, "pls kasaukeni Dr yaron nanfa zai iya farkawa.
Hhhhh kwantar da hankalinki, Indai musayeef ne saikuma gobe idan ALLAH ya kaimu.
Cike da alamar tambaya ta kalleshi.
Yayi murmushi, dainamin tuhuma da ido, maganin barci nabasa kawai.
Ido Iman tazaro saboda mi?.
Saboda yau babu sauk'i, daddynsa da momynsa zasu angwance.
Kafin ta ce, " wani Abu ya had'e bakinsu waje d'aya.
Cikeda salo yake mata abubuwa, lallai tayarda mijinta yayi missing nata, komai a yunwace yake matashi, dukda tana cike da tsoro haka tadake ta hak'ura.
Yayinda akafara nisa sainajawo 'yammatan k'afafuna nayo wajeπŸšΆπŸ»β€.

************************
Bari mu waywayi su Raihan.
Tunda suka bar gidan basu nufi tashaba, gidan wata k'awar aunty sukaje.
Cike da mamaki take kallonsu, tofa Sadiya yana ganku rik'im2 dakaya?, incedai lfy?.
Inafa lfy Zubaida, kedai muje daga ciki.
Afalon zubaida suka zube, takawo musu abinci sukaci, dama yunwa sukeji.
Bayan sunci sunsha suka mik'e k'afa suna bama zubaida labarin komai.
Zubaida tarik'e Baki lallaima sadiya ya akayi kukayi sakaki haka, yo ALLAH na tuba bakuyima 'yan iska mai kankat.
Aunty ta CE, "kamar ya mai kankat?.
Wata dariyar mugaye zubaida tasaki, tagyara zama tashiga fanfasu sosai.
Zancen natadai bai yuce zuwa wajen malam da boka ba.
Sunkuma hau sun zauna daram, gobe asubar fari awani k'auye zata musu.
(Ni bilyn Abdul na ce " ajuridai zuwa rafi).

Wacece zubaida ne?.
Zubaida dai 'Yar sokoto CE, kuma k'awar aunty CE tun a sokoto, adaliln aunty ma tayi aure kano, Dan awajen bikin anuty tayi gamo da mijin dasuke tare yanzu.
Ko kad'an bayajin dad'in zama da ita, Dan zubaida halinsu d'aya da aunty jirgi d'ayane yad'ebosu.
Saboda bala'inta yaraba musu gida itada matarsa uwargidansa kenan.
Itadai ta haihu Dan yaranta biyu duk mata.
To yanzudai gashi tayima su Aunty hanyar malamai to kozasu dace, saimun bisu asannu sanan zamu tabbatar.......










*luv u oll my fan's*
*(((S)))............2017*
[8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu:

Please Login or Register in order to submit comment