Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin yawani shagwa6e fuska, kai habibina shagwa6afa, kaikayi musayeef yayi tawa zan duba?.
Musayeef kuma dolece tasa yake kwana damu, d'akinsa k'awayen deexerh ne aciki kaima kasani, d'akina kuma su Raihan suke kwana.
yarungumeta sosai to yanzu yaza'ayi nikam nakai k'arshe gsky.
Tad'an marairaice fuska, tareda shafa ciki, doctor ya ce, " fa na huta.
Shima hannunsa yad'ora saman cikin nata, to aii nine doctor d'in yanzu kuma nace na Shana.
Iman ta tuntsure da dariya, kai habibi wayonkafa yayi yawa wlhy, juyo da ita yayi sosai suna fuskantar juna, kallon juna suke ido cikin ido cikeda shauk'in so, ya sakarmata tattusan murmushi.
Sanan ya kauda kai yana fad'i. Kinga kwanta ki huta muyi wata magana.
Babu musu ta kwanta tayi filo da cinyarsa, rankwafowa yayi yana kallon fuskarta.
Ta ce, "INA jinka to.
Baiyi maganaba saidai tallafo fuskarta yayi da hannu d'aya, d'ayan kuma yana rik'e da hannunta sun d'ora saman cikinta, bata ankaraba taji bakinsa cikin nata.
Wata Sumba yake mata maicike da kashe jiki, itama maida masa take da murtani cikeda k'auna, sun shagala sosai da faranta ran juna aka turo k'ofar.
Raihan ce da aunty da mamansu, takirasu nanne danta kwantar musu da hankali akan suk'ara hak'uri da mutane, dolene aita kallonsu da abinda suka aikata abaya, amma idan sun danne sun hak'ura komaiba zai wuce sucigaba daneman gafarar ubangiji.
Turus sukayi suna kallon su, Maman su Raihan takoma da baya, amma aunty da Raihan sun kasa ko motsi bare d'aga k'afa.
Dr kam basu San da shigowarsu ba, sun tsunduma sosai wajan faranta ran juna, babu abinda kakeji sai saukar numgashinsu da k'arar AC.
Wasu zafafan hawaye suka wanke fuskar Raihan, dayanzu tana tareda mijinta suna soyayya, amma aunty taja mata fad'awa tarkon wahala, gashinan wadda sukayi Dan ita tadawo gareshi sunata shan soyayyarsu hankali kwance, harda ciki na biyu.
Shashshekar kukan Raihan ne yadawo da Dr hayyacinsa, yad'ago da k'yar yana kallon k'ofa, ganinsu Raihan tsaye saiya had'e rai, iman kam ta yunk'ura zata tashi zaune amma ya hanata, babu yanda zatayi dole ta hak'ura tabi yanda yakeso.
Lafiya dai ko?, yafad'a afusace.
Raihan da aunty auka tako har Inda suke suna kuka, suka durk'usa har k'asa suna rok'onsu akan su yafe masu, wlhy aunyi nadama, kuma har abada bazasu sakeba, Dan ALLAH su gafarcesu kozasu samu haske arayuwarsu tanan gaba.
Dr yabud'e baki zaiyi magana ransa a6ace iman tasa hannu tarufe bakinsa, a'a habibina Dan ALLAH kayi hak'uri mu kar6i tubansu, wlhy na yarda sunyi nadama, muma munama ALLAH laifi kuma ya yafe mana badan halinmuba, Dan ALLAH awanan karon INA rok'on arzik'i agareka ka yafe musu, nidai harga ALLAH na yafe musu kuma komai yawuce agareni, dawowatama gareka kad'ai ya Isa wankemin duk wani taumashe Dana samu na farinciki abaya, tacire hannunta asanyaye tana fad'in, karfa ka manta ALLAH yasaka maka harda k'arin ribar wanan, tanuna masa cikin dake jikinta.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali, ya jinjina kai shikenan na yafe musu ALLAH ya yafemu gaba d'aya.
Murmushi iman tayi ta ce, "ngd habibina.
Raihan da aunty suka Shiga godiya ga iman, ta ce, " babu komaiba wlhy, kutashi kuzauna muyi hirar zuminci ta yaushe gamo.
Abin yabama Dr haushi amma saiya danne, su Raihan suka zauna aka dasa hira, shidai bama sosai yake saka bakiba, daga k'arshema saiya jingina bayansa da kujera ya lumshe ido, hannunsa na shafa cikin iman.
Sunata hirarasu Raihan sai satar kallon Dr takeyi, akowane dak'ik'a jitake k'aunarsa tana sake nunkuwa a zuciyarta, amma tasan yayi mata nisa da zira'i dubu.

************************
Ranadai bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya, auyau juma'atu babbar rana aka d'aura auren Umar farukh da khadija deexerh ababban masallacin juma'a na anguwarsu, d'aurin auren yasamu halartar manyan mutane abokan Yaya Dana Dr isma'il, ga gayyar 'Yan sokoto, to saimuce ALLAH ya Sanya alkairi Dee... Yabada zaman lafiya da dank'on soyayya.

Tab amaryafa yau ranartace abin sai Wanda yagani, Shiga take ta kece raini kamar tauraruwa, hakama ango Umar abin sai Wanda yagane, sai washe baki yake yau ya mallaki abin sonsa, abokansa su Nawas sai tsokanarsa sukeyi, shikam yau dai dai yakejinsa gani yake yafi kowa sa'a.

Tab masu karatu yaufa ranarmuce nida 'yan gidana, Dan haka muka ware munata kwasar rawar Shoki, idan nai k'asa k'asa na kwaso saina manneta a idon damaπŸ˜‚, Alkur'an yau ranar tadabance.
'Yan *_"BILYN ABDUL H NOVELS_* fa babu sauk'i, Ashe duk sun iya rawar shoki, aiko sunata kwasota su iman Xoxo sunata manna mana lik'i, jar uban can, mawak'i gwanja ya haukace yaga ruwan kud'i sai kod'a amarya da Ango yake da iyayen amarya Dana Ango, Dr da iman susha washi kam babu k'arya.

Bayan munsha bidi'oin m aka saka amarya tsaka dangi namata fad'a, sai kuka takeyi, harda su aunty amasu nasiha (araina na CE, lallai su aunty anga duniya).
Bayan ankaita Yaya da mom sunmata suma aka kaita 6angaren su Iman, Dan babban uba yayi fad'a Dr kenan.
Tofa sabon salo nafad'a Dan ganin Dr isma'il yana sharar hawaye, bayason rabuwa da babynsa amma yazaiyi, daurewa yayi yayimata nasiha mai ratsa jiki, tanata kuka.
Dakansa Yakama hannunta har mortar daza'a kaita Inda abokan ango suke jira, yana sakata tafito da Sauri tana kuka, tafad'a jikin Dr tana fad'in itafa bazataba ta FASA auren.
Rungumeta yayi shima yana sharar kwallah, (na CE tofa kaga uba yana kuka 'yarsa zata gidan aure). Dak'yar ya lallashi Kansa yad'agota tareda sumbatar kanta, kiyi hak'uri kinji babyna wanan shine yak'in Matan, kowace mace haka akayimata, bakiga auntynki ba iman harta saba da gidanku, itama haka aka kawo mana ita tana kuka, momynki ma haka, gashi datayi hak'uri harta Haifa mana Ku, to kema ahankali zaki saba da Sabon family naki kinji.
Kai tad'aga masa tana shashshekar kuka, yashare mata hawayen yana murmushi, sanan Yakama hannunta yasake sakawa amotar, iman tashiga gefenta tareda k'anwar mom d'insu deexerh, aka saka dee... Atsakkiya.
Dr yarankwafo yana gayama iman magana akunne, ta jinnina kai tana kallonsa tace to.
Ya ce, "babyna ALLAH yabada sa'a kinji.
Su iman sukace amin.
Iman ta ce, " yauwa na manta musayeef na nan ad'akinka yana barci, karya tashi yayta kuka yaji gidan tsit.
Okey babu damuwa aii zuwa zanyi namayi wanka.
Daganan motocin amarya suka shilla, saida yaga 6acewarsu sanan Yakoma ciki,
A get yay gamo da marwan yajingina da Bango yanata kuka kamar wani mace, Dr ya girgiza kai tareda kama hannunsa suka Shiga ciki yana lallashinsa.
Na CE, "ALLAH sarki marwan abokiyar fad'a ta tafi sai hak'uri kuma aii........











*luv u oll my fans*
*(((S))).......murar
[8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*






*_NA Bilyn Abdul_*





_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*


https://mrsbilkisa.blogspot.com



πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š


*_(page 49 & 50)_*
Tawagar amarya ta isa had'ad'd'en gidan Umar farukh, har yanzu dee.... Kuka takeyi, motar da aka d'akkotace kawai tashiga cikin gidan, sauran duk awaje suka tsaya.
Iman takama hannunta har k'ofar falon, sanan ta ce, "kiyi addu'a kafin ki shiga.
Cikin sauke ajiyar zuciya dee.... Tayi addu'a sanan suka k'arasa cikin bedroom d'inta dayagama had'uwa masha ALLAH.
Sauran mutanema sun shigo sunata zagaye ko ina, kowa sai yabawa yake, dan su Dr sunyi k'ok'ari wajen had'a 'Yar d'iyar tasu.
Dee.... Kam tanacan kangado mak'ale da hannun iman, ita adole tayi wayau kar iman ta gudu.
Bayan kamar awa biyu akafara cewa su fito, mutane suka fara ficewa gudun karsu rasa mota.
Kafin kace kwabo gidan tsit, sai iman kawai datake k'ara mata nasiha, danuna mata wasu turarurruka da yanda zatayi amfani dasu.
Kai kawai take d'aga mata tana hawaye, bayan tagama nuna mata tayimata sallama.
Tab aiisai dee.... Ta k'ank'ame iman tana sake bud'e sabon shafin kuka.
Itama iman d'in sai kuka takeyi.
Aunty Zainab ce taji shirun yayi yawa Dan haka tabiyo baya, sun burgeta sun kuma bata tausayi, dak'yar ta 6an6are dee.... Daga jikin iman, ta zaunar da ita kan gado tana lallashi, cikin dabara da wayo suka gudu suka barta.

******************
Jiki a sanyaye iman tashiga gidan, 6angaransu tawuce itadasu Raihan, suka shiga d'akinta itakuma tawuce d'akin doctor.
Yana kwance rungume da musayeef, idonsa biyu amma ya lumshesu yana d'an girgiza k'afa.
Iman tayi sallama tashigo, ahankali ya amsa baikuma bud'e idanunba.
Jiki a sanyaye tazauna gefensa saitin cikinsa, ta shafa kan musayeef dake saman cikin doctor, tasauke ajiyar zuciya wadda tasa dole doctor bud'e idanu akanta.
Takauda kanta Dan bataso yagane kuka takeyi, yunk'urawa yayi yatashi zaune, yakwantar da musayeef saman gadon sosai, rungumo iman yayi jikinsa kema kukan kikeyi ko?.
Yashafa cikinta yana murmushin kuka, yanzunan nima idan mace kika haifamin haka za'a d'aukemin ita kamar yanda aka d'aukemana khadija a yau?, haka za'a kuma k'ara d'auke mana husaina wata rana?.
Kai iman dama haka iyaye sukeji aranar auren 'ya'yansu??, murmushi iman tayi tana zubar da hawaye, tasauke huci mai zafi daga bakinta, hakane doctor, haka iyayenmu sukaji alokacin dasuka Baku mu, suna sonmu suka hak'ura sukabi umarnin ALLAH.
Amma wanan baihana maza k'untata zukatan matansuba, baihana namiji raina iyayenmuba saboda yana gadarar shi mijine.......
Manneta yayi sosai ajikinsa yana fad'in kuyi hak'uri my life insha ALLAH U mu bazamu zama daga cikin wad'ancan mazanba kinji.
Haka yaytayi mata kalamai masu d'ankaren dad'i hartayi shiru, daga nan aka bud'e shafin soyayya.

🏳
Amarya kam tunda su iman suka tafi tak'ara tsananta kukanta, dama angon yana gidan, kuma bai gayyaci wani abokiba domin sayen baki.
Suna tafiya yashiga d'akin amaryar tasa, tuni tausayinta yakamashi, jiki amace yahau gadon, d'agota yayi yarungume, yana lallashi.
Sorry my Khadee kibar kuka plzz, kukanki yana cin zuciyata, yau ranar farincikinmu ce mun mallaki juna amatsayin zaman dindindin.
Namiki alk'awarin zan kula dake tamkar agidanku.
Itadai tana jinsane kawai, amma ita kad'ai tasan k'unar da zuciyarta take mata, ga tsoro fal ranta.
Da lallashi yasamu taci wani Abu, sanan sukayi sallah.
Hummm dagananfa oga Umar yanuna kwad'ayinsa afili, yayinda tuni idon dee..... Ya raina fata.
Tana ganin yafita zaicanjo kaya, tasakama d'akin key, shirin barci tayi tahaye gadon ta kwanta.
Bayan kamar minti20 saiga Umar yadawo, yanata6a k'ofa yaji GAM, komawa yayi d'akinsa yad'akko wani key d'in.
Barci yafara d'ibar dee..... Taji motsin mutum akusada ita, afirgice tabud'e ido, tako daddage zata kurma ihu, dasauri yasa hannunsa yarufe mata Baki, ninefa khadija yafad'a cikin kunnenta.
Jikinta na rawa ta ce, to Dan ALLAH nidai kafita.
Murmushi yayi yana rungumeta, habadai kinta6a ganin ango da amarya sun raba wajen barci?.
Tabud'e baki zatayi magana ya........ Hummmm saida safe my dee.... Asha amarci lfy.


Haka rayuwa tacigaba da shurawa, akwana atashi babu wuya wajen ubangiji.
Zuwa yanzu cikin iman yashiga watan haihuwa, haihuwa koyau ko gobe.
Reefat ta haihu tuni, tasamu mace maisuna Fateema Zarah, su iman sunje sunan suma, to ALLAH yaraya mana fateema.
Itama Xoxo cikinta yafito sosai, anan ana zubama Dr Nabeel shagwa6ar da'aka sabaπŸ˜‚.
Su dee..... Amarya, yanzukam andaina kuka, sai amarci da'akesha babu k'arya, tayi wani bul bul da'ita, Umar kam jiyake tamkar yacinyeta saboda so da k'auna, abin Nasu acan acan.

Yau tunda iman ta tashi takejin garin sama sama, gashi Dr bayama garin, yana wajen aiki.
Tana kwance akan kujera doguwa sai cije le6e takeyi, marwan yashigo da sallama rik'e da hannun musayeef daya d'akkosu daga makaranta, bata cikin hayyacinta ta amsa sallamar.
Atsorace marwan ya ce, aunty lfy kuwa?.
Murya asark'e tace marwan kiramin mom..... Aii kafin tak'arasa yayi waje, musayeef yazo gabanta yana kiran aunty maa miya sameki?, bakida lfy ne?, bata amsashiba Dan bazata iyaba.... Ahaka mom tashigo da gudu itada mama, hasbinallahu wani'imal wakil, iman haihuwa?, marwan muje fiddo mota.
Haka suka taimaka mata zuwa mota, dole da yaran aka tafi suma Dan gidan babu kowa.
Saida aka shiga da iman d'akin haihuwa sanan mom takira yaya ta shaida masa.
Cikin hanzari yabaro kasuwa.
Yana zuwa likita yana fitowa, yauwa yaya dama kaina fito nema wlhy, inagafa zamu bud'e tsohon aikintane na haihuwar musayeef kawai.
Babu damuwa Dr yaya fad'a ahanzarce, hannu yasaka musu amadadin Dr Isma'il.
Babu 6ata lokaci suka Shiga aikinsu.
Bayan wani lokaci aka fito da k'atuwa baby mace, masha ALLAHU suka Shiga fad'a suna amsar yarinyar kowa bakinsa har kunne.
Yaya ya ce, "maman fa?.
Itama tana cikin k'oshin lfy, mun kaita d'akin hutune.
Kafin kace mi, asibiti yacika da 'yan uwa da abokan arzik'i, su dee..... Amarya duk an iso, hakama Xoxo tazo danata kayan itama.
Dr imsa'il ma an sanar masa, farinciki kam aii ba'a magana, haukacema yaya yai da ihu awaya.

Satin iman biyu a asibiti aka sallameta, sukadawo gida cike da farinciki, zuwa sanan Dr yazo.
Shirin suma akafarayi, dafarko iman ta ce, " bazatayi taroba, Dr ya ce, "wlhy bai yardaba, ba'ayi haihuwar musayeef ba yanzuma ta ce, " baza'ayiba, aii wlhy suma kamar anyi angama.
Su dee... Ne 'yan zuga Dan kullum tana gidan, danma Dr ya ce, "karya k'ara ganin k'afarta sai ranar suna.
Badan tasoba ta hak'ura, amma tak'udiri anan zata kwana ana gobe suna.
Na ce, " humm.

Masha ALLAHU munsha suna yarinya taci sunanta Nafeesa, tom ALLAH yaraya mana nafeesat.
Bayan anci ansha anrak'ashe an k'walle kowa Yakama gabansa, xoxo da dee... Da aunty Salma kawai aka bari sune amarori k'irjin biki, saida suka gyara ko'ina sanan kowa mijinta yazo d'aukarta suka tafi.
Umar kam dayazo dee.... Ta tubure saita k'ara kwana d'aya, bayason 6acin ranta Dan haka yabarta sai goben, babu Wanda yasan yanda sukayi, tatsula k'arya wai shiyace tak'ara kwana.
(Haba dee.... Nagane wayonki sokike sai kun soya rago kawai, zan turo miki Rano ta tayaki Dan nasan tana son hanjiπŸ˜‚).

++++++++++++++
Iman zaune tagama shirya baby feena dakaya masu azabar k'yau, musayeef na saman gadon yana game d'insa na fama da wayarta, yanayi yanacin biskit, yauwa yarinyar daddy kinga ki kwanta ga yaa musayeef nan naje nayi wanka.
Musayeef ya ce, "aunty maa goyamin ita to kafin kiyi wankan.
A'a kabarta takwanta tagaji da goyo bari nayi wanka nafito kaga daddynka yakusa dawowa.
Tana Shiga wanka Feena tafara kuka, musayeef yajuyo yana mata magana cikin wasa baby feena ta daddy, yafad'a yana lakayar kumatunta, biskit d'in ya 6alla yasaka mata abaki.
Iman batasan hidimar dayakeba tazata feena tayi shirune saboda was an da musayeef yake mata.
Hankali kwance tayi wankanta ta fito, zuwa sanan biskit d'in ya narke abakin feena, shikam yak'ara saka mata wani azatomsa ta shanye, da sauri iman taja k'ofar bayi tarufe tak'araso gaban gadon tana fad'in na Shiga Tara ni saudatu musayeef mika batt?.
Adaidai nan Dr yashigo shima, iman tad'ago feena tana girgizata musayeef bakada hankali kabata biskit.
Da sauri Dr yak'aro gurin biskit kuma, wlhy habibi biskit yabata nikam naga takaina, kar6ar feena Dr yayi da sauri, bakinsa yad'ora akan na yarinyar yafara zuk'e biskit d'in daga bakinta, saida yatabbatar babu komai abakin sanan yamik'ama iman ita, kinga bata nono tasha.
Musayeef dake zaune yana kallonsu yayi shiru Dan yagane abinda yayi ba daidai bane, Dr yakalleshi oh kai musayeef haka zakayi naka rainon kai kuma?.
Wanefa raino, aii sainama zaneshi, haka kawai zai kashemin yarinya.
Musayeef najin zancen duka yasa kuka, daddy Dan ALLAH kabama aunty maa hak'uri karta dakeni, nibansan feena batacin biskit ba.
Jawoshi Dr yayi kaga karkayi kuka, amma daga yau karka sake bata kaji, ita bata fara cin irin wad'@nnan ba sainan gaba, nono ne kawai abincinta kaji.
Kai yad'aga masa, daddy bazan sakeba aii.
Yauwa d'an albarka.
Itadai iman tanajinsu bata tankaba, saida feena tak'oshi sanan tamik'ama Dr ita, shikuma yad'auketa yanna fad'in Ummm my sweet feena.
Iman ta harari musayeef kaikuma zamu gamu.
Dariya Dr yayi ya ce, "babu wani gamuwa aii mun baki hak'iri dai.
To ban hak'uraba.
Hummm to mikeso muyi miki yanzu.
Zaneku zanyi kawai.
A'a kiyi hak'uri, amma albishirinki?.
Goro tafad'a tana kallonsa.
Hafsat ta haihu yanzunnan namiji................








*luv u oll my fan's*
*(((S)))........2017*
[8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*






*_NA Bilyn Abdul_*





_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*


https://mrsbilkisa.blogspot.com


πŸ”šπŸ˜πŸ‘ŒπŸΌ

*_(page 50 to 60)_*
Wani ihun murana iman tasaki, shima musayeef ganin haka saiya fara tsalle, Dr kam dariya kawai yake musu.
Dandanan tashirya suka nufi gidan Xoxo.

Tana shiga suka rungume juna cikeda farinciki.
Iman tad'auki sargad'ed'en yaron fari tas masha ALLAH.
Kai tawan yarona yafiki k'yau.
Hhhh ALLAH ya kiyaye, kuma kunsan nagaba yayi gaba aii.
Dariya iman tayi ta ce, ''ki k'ara kallon madubi to, babu wani kalla dazanyi nasan nafi k'yau, Haka sukaita gardama suna tsokanar juna.

Ansha sunan baby Wanda yasami sunan muhammad, ya ALLAH karayamana Muhammad mai babban suna.
Sunakam yayisuna Dan munrak'ashe mun k'walle, su Rano ne 'yan suyar hanji, kunsan nantafi afana🀣, Dr yayi hidima sosai, to balle uban gayya Dr Nabeel Wanda bakinsa yak'i rufuwa, kad'an kad'an saiya lek'a maijego, safaman soyayya suke agaban mutane ko kunya babuπŸ‘πŸ»πŸ˜.



------------------------------------------
*Banyan wani dogon lokaci.*

Abubuwa dayawa sunfaru, masu dad'i da akasin haka, rayuwa tayi nisa sosai.
Zuwa yanzu Reefat tanada yaranta uku, hakama Xoxo tanada biyu, dee.... Ma ta silli6o mana 'yan biyu mace da namiji, Dr yasamu jika kamar yanda yake fata.
Anyi bikin marwan dawata yarinya Zuh'ra, harma da tsarabar ciki.
Su aunty da Raihan sunyi aure suma, sunan zaune acikin garin sokoto, suma yanzu komai daidai sun shiryu tareda tsaida zuciyarsu waje d'aya, sunan zuwa kano zuminci hakama su iman suna zuwa, aunty dai har yanzu bata haihuba, amma raihan ta haifi d'iyar mace.

Hummmm masu gayya da aiki kam yaransu hud'u yanzu, bayan musayeef, feena, an haifi ummukhursum, da Al'mustapha, Wanda take goyo yanzu haka.
Dr anzama babban soja kuma aikinsa yadawo kano, yana kula da iyalinsa yanda yakamata.
Musayeef yazama d'an saurayi masha ALLAH, yanzu rayuwarsa tafi yawa wajen mom da yaya, dansun kwaceshi.
Lokaci lokaci yana zuwa gaidasu gwaggo shida k'annensa, deeni ma anzama samari masha ALLAH, Dan shirin aurensama akeyi.
Hakama aunty Salma tana zaune gidanta lfy tareda 'yan yaranta biyar masha ALLAH.

*_BAYAN SHEKARA 25_*
feena tashigo dagudu tana kwala kiran aunty! aunty!!.
Dr da iman suka fito da sauri suna fad'in feena lfy dai ko?.
Bayan Dr taje ta mak'ale, daddy ya Musayeef ne zai dakeni Dan kawai nad'an d'ebo shamfo d'insa na wanke kai.......
Kafin tarufe baki musayeef yashigo rik'eda belt d'in wandonsa, ganin iyayen nasa tsaye yasa shima yatsaya yana Harar feena.
Dr yagirgiza kai, saboda tayi anfani da shamfo d'inka kabiyota zaka Daka?.

ALLAH daddy bafa yau tafaraba, hakama ranar itada husaina da Nawal d'in aunty dee.... Sukaje sukamin 6arna ad'aki, nahukura bance komai, shine danta rainani yau takoma d'ibarmin shamfo.
Iman ta hararesa to ba k'annenka bane, dansuyi amfani da kayanka shine kaketaman yima mutane wani babbotai, ALLAH ya shiryeka musayeef, taja tsaki takoma d'aki rik'e da hannun al'mustapha dayazama d'an saurayi shima.
Dr ya ce, "tom kayi hak'uri bazasu sakeba kaji ko.
Kai ya jinjina yafita, aransa kuma yana fad'in wlhy nakamata saina rankwashi kanta sau bakwai Dan Nasan bazata dainaba, itama husaina k'atuwa da ita tana biyema feena.
Wai kuma ahaka ake shirin auramin ita kanta na rawa, hummmm yarinya zan saitakine.
(Nikam Bilyn Abdul nayi dariya, wai yakaga musayeef da mata gwangwazoπŸ˜‚).

*_TAMMAT BI HAMDULLAH_*

```INA FARINCIKIN KAMMALA WANAN 'DAN LITTAFI NAWA.```
kuskuren danayi ALLAH ka yafeni, abinda nafad'a daidai ALLAH yasa ya amfanemu gabad'aya.

_Godiya mai tarin yawa ga masoyana abin alfaharina, bansan dawana baki zan godema masoyaba, amma zuciyata tana tsananin k'aunarku, kunacikin abubuwa muhimmai na rayuwata, ya ALLAH kabarmu tare, yak'ara dank'on zuminci atsakaninmu, ngd ngd sosai da k'ok'arin bibiyata._

*Bazan iya mantawa dakuba Dan tun farkon fara rubutuna kuna tare dani.*
deexerh.
sa'adatu sa'ad.
zulaiha.
my Ikilee.
Riddallah.
marak'isiyya (k'anwata).
Aysha Manshat.
Reefat yahaya.
Ayeesh.
'Dan mom.
Teema.
Adama gages.
Uwargida.
Sakina gages.
Hafsy.
Binta (kakus)
*_HOUSE OF NOVELS_* (gidan Abba Gana)
Kuntaka rawar gani sosai atafiyata, Dan shine gida nafarko dasuka fara karanta buk d'ina, shiyayasa bazan ta6a mantawa dakuba har k'arshen rayuwata, ALLAH yabar zuminci.
*_(Kaima Abba Gana ngd kana taka rawar gani arayuwata ta rubutu, ngd sosai)._*

_godiya gadikakanin groups na Novels ALLAH yabar zuminci ngd da k'auna kuda Admins naku, ALLAH yabar zuminci_

*_"yan Group d'ina abin alfaharina, ALLAH yabarmu tareβ€πŸ˜πŸ‘ŒπŸΌ."_*


*_taku har kullum BILKEESA IBRAHEEM (Bilyn Abdul)_*

_marubuciyar_
*_RASHIN SANI_*
*_AUREN K'ADDARA ko BIYAYYA?_*
*_K'ANWAR UWACE ko KISHIYAR UWA?._*
*_NIDA AMINIYATA_*
*_NAWAFF_*
*_SABON AL'AMAREE_*
*_KUKAN KURCIYA...._*
*_BAN SAKETA BA!_*


sai mun had'u asobon littafina mai suna_ *ABDUL-MALIK (Bobo)*
Shima zaizo muku danasa sabon salon na musamman.

Inafata zaku watsar daduk wani kuskure danayi kasancewata ajiza.

Inakuma Baku hak'uri wajen jinkirin akan rubutun littafinnan ngd ngd ngd.




Luv u oll❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣

😁 *Bilyn Abdul*πŸ‘ŒπŸΌ
[8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*






*_NA Bilyn Abdul_*





_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

🀝🀝🀝🀝🀝🀝🀝🀝
_Assalamu alaikum masoya na, godiya tamusamman agareku, k'auna mai yawa agareku, jinjina da fatan alkairi su tabbata agareku, banida bakin gode muku, lallai Ku wani 6angarene narayuwa da tarihina, duk inda masoyina yake ina alfahari dashi, kuma ina k'aunarku_

_ngd da d'umbin k'aunar dakuka nuna mini, ALLAH yasaka da alkairi yabar zuminci._

_naga sak'onninku, wasu na amsa wasu ban samu damaba saboda matsalar network dana fuskanta ajiya, kuyi hak'uri ngd sosai, kuma ina alfahari daku arayuwata._

_abaya nace muku Next Novel d'ina *ABDUL-MALIK* to yanzu ansamu canji saboda wasu dalilai, yanzu Next Novel d'ina shine *CIKI DA GASKIYA......*, insha ALLAHU zai zomuku anan kusa danasa sabon salon, Dan gsky ban ta6a rubuta Novel makamancin wannanba, Dan haka ina Neman addu'arku agareni gudun shiga had'ari._

_```masoyi abin sone, masoyi abin alfahari ne, masoyi abin tunk'ahone, masoyi abin k'aunane, inasonku fiye da tunaninku, ALLAH yabarmu tare_```

_nasan wasu zasuyita tunani saboda nace atayani addu'a a buk d'ina nagaba, kunsan rayuwa kowa da irin fahimtarsa, wasu zasu iya tunanin labarin nawa ya shafesu, kuma ko kad'an ba haka bane..... Bari nabarku karna cikaku da magana, saimun had'u a *CIKI DA GASKIYA, WUK'A BATA HUDASHI* zaizo muku cikin cikakkiyar Hausa kamar yanda yadace_.

SAIYA ZO...πŸ‘ŒπŸΌπŸ‘ŒπŸΌ

*_masoyi abin alfahareee_*❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*_CIKI DA GASKIYA.....!_*
*_CIKI DA GASKIYA.....!!_*
*_CIKI DA GASKIYA.....!!!_*πŸ—‘πŸ”ͺ

πŸ€™πŸ»πŸ€™πŸ»πŸ€™πŸ»πŸ€™πŸ»πŸ€™πŸ»πŸ€™πŸ»πŸ€™πŸ»πŸ€™πŸ»
Bilyn Abdul.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da

Please Login or Register in order to submit comment