Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

likitan dake taimaka min yaymin allurar amma abanza dan babu abinda ya canja agareni, har zuwa 'karfe huďu na yamma, saidai yalafa yadawo.
Awanan lokacin tuni Dr Isma'il yana gida yana hutawa, amma sai barcin ya gagari idanunsa, dan tunda yashigo kano gabansa ke faďuwa zuciyarsa tanata kwaďaita masa son ganina, dan ba 'karamin kewata yayiba acikin shekara ďayar nan..
Zumbur yami'ke yacanja kayansa zuwa shadda mai 'kyau ďinkin zamani, dan Dr Isma'il yanada 'kyau babu laifi, yafito falo yana ďaura agogo, auntynsa matar yayansa ta ce, "a'a angona sai ina kuma??.
Dr Isma'il yay dariya angon iman dai, kekam ga angonki nan akusada ke, ya nuna yayansa dake zaune yana masu dariya.
Ta ce, "wacece iman kuma??.
Dr Isma'il yay murmushi karki damu zaki santa kwanan nan, yanzuma sauri nakeyi amma kibini bashi idan na dawo zan sanar dake iman, yafice yana faďin yaya aunty saina dawo, yanaji tana kwala masa kira amma bai sauraretaba, motar yayansa ya ďauka yafice danshi bashida mota sai mashin, yayansa kuma baya masa shamaki da nasa motocin.
Yayansa ya tuntsure da dariya nikam kina bani mamaki keda Isma'il ke yanzu har kin yarda da zancensa ne??.
To ya bazan yardaba tunda bai ta6a kawo mana makamanciyar wanan maganarba.
Ito hakane ALLAH yasa da gsk yakeyi.

Dr Isma'il kuwa kaitsaye gidanmu yanufo, yay parking a kofar gida, yana tsaye gaban motar saiga deeni yadawo daga aika.
Dr Isma'il ya ce, "zomana abokina, babu musu deeni ya'karasa garesa, ya gaishesa.
Dr Isma'il ya ce, "dan ALLAH shiga gidanan kamin sallama damai gidan.
Deeni ya ce, "wai Abbah??.
Eh shinake nufi, ko kaima ďan gidanne ?, dan naga kana kama da Iman.
Ya ce, "lah ina kasan aunty iman??, Dr Isma'il ya ce, "anan gidan, to aii yanzuma itace batada lafiya dan har suma takeyi, aruďe Dr Isma'il ya ce, "suma kuma??, deeni ya ce, "eh suma, to yanzun Abbah na nan?, eh yana ciki, jeka ce masa Isma'il ne yazo gunsa.
Deeni yazo ya sanar da Abbah, Abbah yanajin Dr Isma'il ne da hanxari yafito, bayan sun gaisa Dr isma'il ya ce, "yanzu wani yaro yake sanar dani Iman babu kafiya?.
Eh hakane Isma'il.
Sun shigo gidan, sanda suka shigo inata mur'kususu ajikin gwaggo dan har wani shiďewa nake saboda azabar ciwo, gwaggo sai kuka take.
Dr Isma'il yakalli Abbah aruďe Abbah idan bazaka damuba na ďauketa muje asibiti mana.
Abbah ya ce, "babu wata matsala Isma'il......aibai bari Abbah ya 'karasa faďaba ya sunkuceni yay waje, amota yasakani Abbah yakaraso da hanzari yashige muka tafi asibiti, acanma ďaukata yayi, ďaki guda aka waremini nikaďai, ya shiga bani kulawa ta musamman, cikin 'yan mintina ya shawo kan matsalata harna samu barci................✍🏻







💕💚💕







Page~4⃣

..........Washe gari nadawo dai2 ina kwance agado gwaggo tana zaune akusa dani, aunty Salma kuma tana tsaye tana waya, Dr Isma'il yaturo 'kofa yashigo da sallama, rissinawa yayi ya gaida gwaggo, gwaggo tami'ke tafita dan tanajin kunyar sirikin nata, itama aunty Salma saitayi waje, Dr Isma'il yajawo kujerar da gwaggo ta tashi ya zauna kusadani ya tsuramin idanu Iman ya jikin naki?.
Cikin jin kunya na ce, "da sau'ki.
yanzun babu inda yake miki ciwo?.
na ce, "babu, ya ce, "Alhmdllh.
Ince dai kinci abinci ko?, naďan kalleshi ta gefen ido na ce, "a'a na koshi, ya ce, "mikikaci da har kika 'koshi?, na ce, "nasha tee ďazu.
Yay murmushi kice na shirya nemo maganin cin abinci matata batason cin abinci, da sauri na kalleshi, ya kannemin ido ďaya tareda ďaga gira, hannu nasa na rufe fuskata saboda kunya, ya ce, "inson mace mai kunya ashe ALLAH zai bani, na kuma cusa kaina cikin cinyoyina.
Yay dariya sanan ya ďauki filet, kulan da aunty salma tazo dashi ya buďe, ya ce, "iman lallai ke 'yar gatace, wannan irin farfesu haka, nidai kaina na tsakiyar cinyoyina nakasa ďagowa saboda kunyar maganganunsa.
Ya zuba farfesun yace nazo naci nasha magani.
Na ďago kaina cikin jin kunya na ce, "kawo to, ya ce, "waneni da barin gimbiya cin abinci da kanta, aii da hannuna zan baki, na ce, "A'a ngd zanci da kaina, ya ce, "nikuma ban yardaba, haka dole na hakura yabani da kansa, saidai cikin matu'kar jin kunya nake kar6a, shikam sai dariya yake mini.
Aranar aka sallameni muka koma gida..
Kunaga kutashi muyi sallar la'asar sanan saimu cigaba.
Bayan sun idar da sallar la'asar iman ta ďora labari.

Iman tabi Reefat da Xoxo da kallo tareda jan numfashi, wato 'yan uwa bayan kwana ďaya da sallamata Dr Isma'il yazo gidanmu, an masa tarba ta mutunci, dan su gwaggo suna son Dr Isma'il sosai.
Bayan sun gama gaisawa Dr Isma'il ya ce, "Abbah dama nazone nayi muku bayani akan ciwon iman.
Abbah ya ce, "ina saurarenka Isma'il.
Dr Isma'il yay 'kasa da kai sanan ya ce, "wato Abbah naďanyi bincikene akan ciwon iman, saina gano ta hanya ďayane kawai zata iya rabuwa da ciwon, hanyar kuma itace......saikuma yayi shiru, Abba ya ce, "inajinka Isma'il karkaji komai ka sanar dani, Dr Isma'il ya 'kara kasa da kai dan maganar tayi masa nauyi abaki, amma ya daure ya ce, "hanyar itace aii mata aure, ta wanan hanyar kawai nake ganin za'a samu mafita.
Abbah yay murmushi to aii Isma'il inadai hakane banida damuwa tunda lafiyarta muke bu'kata, inaga indai har iyayenka sun amince saisu turo, inyaso saita cigaba da karatun a ďakinta, dan haka nabaka dama kaje kayi shawara da nagabatanka, nima zanyi da gwaggonsu dakuma 'yan uwana.
Dr Isma'il ya ce, "to ngd ALLAH ya 'kara girma.
Abbah ya ce, "amin, yami'ke yana faďin bari na turo maka maman tawa.
Bayan Abbah yashigo ya ce, "naje falon ba'ki ana jirana, na ce, "to, hijjabi nasaka na nufi falon, yana zaune akujera mai zaman mutum ďaya, yana cikin farar shadda ďinkin boda amma babu hula akansa, yayi min 'kyau sosai, dan Dr Isma'il farine 'kyakykyawa, yanada suma mai 'kyau wadda take shan gyara, bayida saje saidai wani ďan gemu na gayu daya ajiye, wanda ya'kawata 'kyawun fuskarsa, dogone sosai yanada 'yar kiba daidai misali, akwaishi da yawan fara'a, dan a yanda nakula kamar ba miskili bane.
Da sallama na shigo 'kamshin turarensa ya bigi hancina, inason kamshin turaren tun sanda aka fara kaini asibitinsa, yaďanja gilas ďinsa kaďan zuwa 'kasan ido, yakuramin idanunsa matsakaita girma, na zauna saman carpet, yay saurin faďin a'a ban yardaba tashi ki hau kujera, cikin jin kunya na ce, "nanma ya isa.
To shikenan nima bari na sauka kasan tunda nan kikeson mu zauna, ganin zai zauna kasa nayi saurin hawa saman kujerar, ya tuntsure da dariya to shikenan gimbiya, nidai kaina yana 'kasa na gaisheshi, ya amsa cikin fara'a, sanan ya ce, "ya jikinki??.
Na ce, "aii ni na warke.
Ya ce, "zakidai warke in sha ALLAHU nan gaba kaďan.
Murmushi kawai nayi batareda nayi maganaba.

Ya gyara zamansa sosai, tareda 'kara daidaita nutsuwarsa, yayďan gyaran murya alamar maganar dazaiyi tanada muhimmanci.
Ya ce, "imaniii nasan kin sanni tunba yanzuba, tun sanda aka fara kaiki asibiti a matsayin patient ďina??, na ďaga kai alamar hakane, ya jin jina kai, to tun aranar naji kin kwanta min arai, nakamu da sonki na gsky, dalilin dayasa na sanar da majeed abinda ke raina kenan, shine ya shige mini gaba zuwa wajen abbah, banyi kasa aguywa ba wajen sanar da abbah sirrin zuciyata.
Alhmdllh Abbah ya fahimceni yakuma kar6eni amatsayin siriki, tunkuma a wancan lokacin ya mallaka minke, yakuma bani damar neman so awajenki.
Alokacin nayi wani nazari akanki, dan na lura ke yarinyace karama, wanan dalilin yasa na ce, "abarki sainan gaba, dama na sanar dasune kamar yanda addinina ya koyar dani, to saikuma wani uzuri yatasomin alokacin, natafi training ďin soja saboda tuni inason zama soja, saidai yayana yafison nazama likita, ina girmama bukatarsa dan haka nacika masa burinsa nazama likita, tonima sai ALLAH yacika min nawa burin nasamu damar zama soja ayanzu.
Ranar dana iso kano saina tarar bakida lafiya, danayi bincike akan ciwonki saina gano nine maganinsa, dan haka nazo yaunayima abbah bayanin komai.
Ya gyara zamansa to yanzudai zancen danake miki abbah yabani izinin turo iyayena su nemamin aurenki, shiyyasa nakeson jin tabakiki dan kar asoya mai amanta da albasa iman kina SONA kuwa???, nayi miki??, karki 6oyemin sirrin zuciyarki kinji..
Gsky naji kunyar zancensa dan haka na 6oye fuskata da tafin hannuna, Dr Isma'il yazare gilas ďinsa karkimin haka Saudat!!, ki daure kisanar dani kina SONA???.
cikin jin kunya naďaga kaina alamar eh.
Yasaki murmushinsa mai 'kayatarwa ya ce, "Alhmdllh, iman nagode da soyayyarki gareni, ALLAH yabarmu tare har abada, yakuma kaďe duk wata fitina dazata wanzu a tsakaninmu, ala66ana na ce, "amin ya rabbi.
Ya kalli agogon hannunsa idan bazaki damuba zan sanar dake koni wanene dan naga munada sauran lokaci.
Na ce, "babu damuwa.
Lemo ya ďauka ya tsiyaya acikin kofi, yasha kaďan sanan ya ajiye, ya ďauki gilas ďinsa yasaka, gilas ďin yana matu'kar kara masa 'kyau sosai.

♡☆♡

Nidai sunan Isma'il Muh'd Basheer, mu biyu iyayenmu suka haifa, yayana Mansur saini auta, mu 'yan asalin garin sakoto ne, aikine yakawo mahaifinmu kano, mamata kuma 'yar tarabace Jalingo kenan, bafulatanace ta asali, dan harta bar duniya hausarta bata fita sosai, tuni mahaifinmu ALLAH yay masa rasuwa saka makon haďarin mota dayayi daga kano zuwa sokoto, sanan ina wata 6 a duniya, Rasuwarsa ta girgiza maman mu dan haka takamu da ciwon zucuya itama babu daďewa tabi bayansa, inada wata 10 sanan aduniya, 'kanuwar maman muce tacigaba da ri'konmu, itama tana aure anan kano dawani abokin Abbanmu.
Sun nuna mana gata sosai wanda har muka manta da maraicin dake kanmu, dansu basu ta6a haihuwaba, sun taimaka mana munyi karatu mai zurfi, ina shekarar 'karshe a secondary ALLAH yayma uncle rasuwa, akabar mama da ďawauniyarmu, karatunmu tarbiyyarmu, cinmu shanmu, saidai abinda 'yan uwa suka taimaka mata.
Natashi mutum mai yawan laulayi na ciyo, ina yawan yin rashin lafiya akai2, idan ina cikin wanan halin mama takan ruďe itada yayana, hakadai rayuwa tacigaba da garawa har yayana ya kammala digiri ďinsa, bai tsaya neman aikiba ya tsunduma kasuwanci, nikuma sanan na kammala sacondary, kullum burina bai wuce nazama sojaba, amma awajen yayana da mama ba haka bane, burinsu nazama cikakken likita, dan haka burinsu ya danne nawa, nadage nazama likita domin na faranta musu, yayana yayi aure tuni, yanzu haka yanada yara biyu, Marwan da Hadeeza, (deexerh) saidai sun rabu da maman yaran, yanzu yana auren wata mata mai suna Ramla, agida ďaya muke zaune muduka, yayi mana gini kowa da 6angarensa saikuma na mama agefe, wannan shine tarihina a ta'kaice, ALLAH yasa kin gamsu.
Murmushi nayi ina satar kallonsa, na gamsu sosai, kuma tarihinka ya 'kayatar dani, ALLAH yajikansu mama ya yafe musu, yabamu hakurin rashinsu, ameen doctor yafaďa yanamai jin daďin addu'ata.
Ya kalli agogon hannunsa sanan ya mi'ke iman bari na wuce ko, magriba tana gabatowa.
Na ce, "to aii bakaci komaiba sai lemo, yayi murmushinsa mai 'kyawun gani, karki damu kasancewa dake kawai ya wadatar dani, na ce, "to na gode, naďan rakoshi bakin 'kofar falon ina faďin ka gaidamin dasu deexerh da marwan, saida yajuyo ya kalleni sanan ya ce, "zasuji insha ALLAHU.
bayan fitarsa daga gidan na lumshe idona ina murmushi da maida nannauyan numfashi, babu 'karya nima inason doctor Isma'il, domin kuwa ya cancanci asoshi, mutumne mai kwarjini a ayuka da kuma dangan taka, ga yawan fara'a, uwa uba 'kyawawan halaye, amma baza'a kirasa mutum mai tsananin 'kyauba, saidai tsaka tsaki.
Lalai na more da samun miji nagari, kamshinsa kawai ya wadatar dani burin kasancewa dashi har abada, saidai ina ba'kin cikin katsewar karatuna, dukda nanda wata shekarar zan kammala, amma ina bukatar rabuwa da wananan azababben ciwon dakansani tagumi tunkan kamawar wata, ALLAH dai yaza6a mana abinda yafi alkairi.
Kwala kiran sallar limance tasakani fitowa daga falon nanufi cikin gida..............✍🏻


Kuyi ha'kuri dani, wlhy ina busy🙏🏻😁









Luv u oll my fan's
(S)......2017
battery low🔋😜👌🏻
[8/6, 5:59 PM] mrs bilkisu: ________________________________
BAN SAKETA BA!!!.
________________________________
NA
BILKEESA IBARAHEEM
{bilyn Abdul}
________________________________
https://mrsbilkisa.blogspot.com






Sadaukarwa ga~Abdul {city phone's}


Page.....5⃣



💞💞💞💞💞💞

*invitation*! *invitation*!! *invitation*!!

U ar cordially invited to d wedding events of *Reefat Yahya*❤

*Walima* on 13th April 2017
Venue -Barr Yahya j Bobboi's residence @ marware ward Jada,
Adamawa state.
Time: 3:30pm

*Arabian night*
On 13th April 2017
Venue Atiku Abubakar science hall Jada.
Time: 9:00pm

*Kamu day* on 14th April 2017
Venue Atiku Abubakar science hall
Time: 3:00pm

*wedding fatiha* on 15th April 2017
Venue Barr.Yahya j Bobboi's resident marware ward Jada, Adamawa state.

Allah ya bada ikon zuwa💞💞💞
Sako daga bilyn Abdul😁👌🏻

_________________________________
WANNAN page ďin nakune.
KODA YAUSHE INA ALFAHAREE DAKU 👇🏻
Faty axlad maryam 'yar mama
humy luv first lady
hudallah salma Ali wada Sunher classic feedoh
Zeenur Fareedat musa
Kuďin nadabanne agareni, inafata alkairi da tarin basira da kwarin ido agareku, ALLAH yakara baku ikon nishaďantar damu da faďakar damu, yakuma karemu daga sharin ma'kiya baki ďiya.
(Maryam 'yar mama👌🏻❤)
MAHAUKACI ko BOYAYYAYEN MOSOYI!!!!!!???????. 🤔



Page.....5⃣

.......Babu 6ata lokaci aka shiga shirin bikinmu da doctor, domin iyayena basa son wata yacika al'adata tazo ba'a gidan mijinaba.
Aranar wata juma'a aka ďaura aurena da doctor Isma'il, mutane dayawa sunsha mamakin aurar dani da'akayi, saidai basuda dama tsogumi tunda gidansu doctor Isma'il ba wasu masu 'kazamin kuďi bane saidai rufin asirin ALLAH, wannan ya hana mutane ďafewa aka kuďi abbanah yagani, saidai hakan bai hanasu yawan hasashe da hange2n daliliba, saidai sun rasa tsani ko tubalin hangowa, dan masu iya magana nacewa wani sirri sai hanji kasanshi.
Da yamma akaje walima mai 'kayatarwa da birgewa, dayawa abokan Dr Isma'il sunyi mamakin ganina amatsayin matarsa, suna mamakin yanda akayi ya auri 'karamar yarinya haka, amma tunda basuda mai basu amsa sai sukayi gum, kamar ansakama kofar fada kwaďo.
Waleemar ta 'kayatar sosai, karfe tara na dare aka tashi, gida aka maidani sanan akayi shirin iza 'keyata makarantar samun ladan aljanna, wato gidan miji, nasha kuka sosai na rabuwa da iyayena dakuma ďan kanina Deeni.
An kaini gidansu doctor wanda zai zama familyna na biyu ayanzu, 6angaren mama aka kaini, dukda idanuna suna sinkife cikin hijjabi, ina a kwatan kwacin makauniyane, wanan bai hanani ďaukar sautin maganganun danginaba masu ambatar sunan wadda zata maye gurbin uwar mijinaba ayanzu, an dan'ka amanata ahannun mama, kuma ta kar6a tayi ammanar ri'keni amatsayin ďiya kamarsu doctor, to nimadai tawa zuciyar ta rungumeta amatsayin uwa tunda aure ya nisantani da gwaggota, bayan ďan faďa da nasiha aka kaini 6angarena wanda zai kasance fadata afanin sarautar gidan miji, masu kawoni basu wani ďauki dogon lokaciba suka fara kama gabansu dan komawa tasu fadojin domin kula danasu iyalin, kafin na farga gidan yayi tsit tamkar anyi ruwan sama anďauke, aunty salma kawai aka bari tana ďan gyaramin inda aka 6ata, itama zuwa wani lokaci tayimin halin ruwa, dankuwa bansan ta suďaďa ta ficeba saidai na riski shiru wai rai yayi halinsa.
Abu biyu suka giftamin awanan lokacin, wato tausayin kai, da jimamin rabuwa da iyaye gatan 'ya'ya, agefe kuma ga wani tsoro dayake neman titsiyeni sakamakon jin shiru danayi narashinjin rai mai motsi akusadani.
Ina nan cikin halin gajeren numfashi da dogon tunani, naji sallamar angon 'kamshi da gayyar abokansa masu masa rakiyar zuwa ďakin amaryar tasa, saidai afalo ya taka musu birki tareda mi'ka godiyar 'ko'karin dasuka nuna na fiddashi kunyar wanan rana, suduka sai suka shanya baki suna masa kallon sama da 'kasa, yayi murmushi yayinda shima yake maida musu murtanin kallon kwaji dashi, Raheem ya ce, "mutumina abin 'yar hakace ko?", doctor ya kaďa kai alamar babu shakku akan furicin abokin nasa da inda yadosa, to suma sun masa uzuri, dan dama daniyyar haka suka iso, tunda al'adarsuce haka, idan sun rako aboki basa fiya zazzarin shiga inda amarya take, daga bakin 'kofa suke tsayawa aja doguwar addu'a kowa yacika rigarsa da iska.
To shima sun masa addu'ar da fatan alkairi harda na dawowa suna awata tara masu zuwa, 'yar dariya kawai yayi yana musu sallama dafaďin ALLAH ya huce gajiya.
Ina zaune akan gado lullu6e cikin gyale jaa sai zabga 'kamshi nake wanda akasan amarya dashi, doctor yashigo da sallama cikin muryarsa mai shiga 6argon jiki da jini, tuni wata sabuwar nutsuwa tazo mini danjin ma'abocin 'kamshi yana kusantoni, acan kasan ma'koshi na amsa, cikin takunsa na burgewa ya 'karaso inda nake, ya ajiye ďan madaidaicin jakka mai kyawun gsk akusada gadon.
Gadon ya hawo yana faďin amarsu ta ango mai daďin suna, ta angonta Isma'il, ya zauna akusadani tareda yaye gyalen dana lullu6a dashi, ahankali yafurta "AMINCIN ALLAH YA TABBATA AGAREKI HASKE MAI HASKAKA ZUCIYA, IMAN MAI FASSARAR IMANIIIII!!!".
kasa nayi da kaina inaďan murmushi, yay 'yar dariya mai 'kayatarwa aikunya ta 'kare, tunda yau kin zama tawa ni kaďai, hannu nasa na rufe fuskata.
Iman Ta hurema Reefat idanu, ajiyar zuciya Reefat taja mai 'karfi, suka tuntsure da dariya gaba ďaya, iman ta ce, "kai Reefat gaba ďaya kin zuba min idanu, xoxo ta ce, "kamar tana hangen daren farkonku!."
To 'yammata aini ba haka nake nufiba, dama abinda kuke jira kuji kenan to bazan faďaba, aiko da kin cucemu dan nan muke jira muji, o, ke xoxo zan faďama momy aimiki aure kafin ki ida 'konewa wlhy, garama Reefat kaďan yarage ale'ka turaka😁👌🏻lol, ta faďa tana shiga bayi domin yin alwala.
Tayo alwala tafito, xoxo ta ce, "oh ke iman ashe kinsan hanyar.........saikuma tayi shiru dan ganin hararar da iman take watsa mata, suka tuntsure da dariya itada Reefat, yayinda iman ta kabbara sallah tana murmushi.
Bayan sun idar da sallah suka sake zama, Reefat ta ce, "dan ALLAH iman kibamu labarin komai karki rage mana, dan nasanki da shegiyar kunya.
Iman ta ri'ke ha6a kai Reefat ALLAH ya shiryaki, zandai faďi abinda bakina zai iya, amma ba komaiba, xoxo ta ce, "da wanan surutun mudai aci gaba".
Iman taci gaba da faďin, cikin sanyin murya na ce, "masa ina yini fuskata na rufe da tafin hannuna.
Ya ce, "a'a bazan amsaba saikin buďe fuskarki, dole na buďe fuskata sannan na gaisheshi, ya amsa cikin shau'ki ya ce, "ya gajiyar biki?, nai murmushi bance komaiba, yaďanja hancina miyasa kike da yawan kunya iman?, nanma shiru nayi dan gaba đaya atakure nake, kunyarsa duk ta gallebeni.
Mik'ewa yayi yana murmushi yafice, babu daďewa yadawo da filet ahannunsa da kofuna, saman kafet (carpet ) ďin dake gaban gadon yazauna, yajuye gasassaun 'yan shila daketa tashin kamshi, yazuba madarar akofuna.
Saudatttt!!! Yakira sunana ahankali, tareda ďanjan sunan, na ďago ina kallonsa tareda faďin na'am, ya ce, "taso kici abinci nasan kinajin yunwa.
Na ce, "na k'oshi".
Ya ce, "k'oshi kuma?, zadai ki k'oshi yanzu, yafaďa yana k'arasowa gareni, cak ya ďaukeni ya dire ak'asa sanan shima ya zauna, jikinsa yajawoni bari kiga ďura zan miki yanzu.
Na ce, "dan ALLAH kayi ha'kuri zanci da kaina, haka nayita tura naman nan ina kora madara badan nasoba.
Bayan mun gama ya ce, "yana zuwa, na ce, "masa to", yana fita nasakama k'ofar key.
wai kunsan wani abu??.
Sukace a'a saikin faďa.
Nifa duk wanan abun dayake faruwa babu tsoronnan da ake faďa na amarya ga angonta araina, danni wlhy bansan idan anyi aure mi'akeyiba, rufe ďaki danayi, nayi hakane dan inajin kunyarsa, amma badan ina tsoron faruwar wani abuba.
Su xoxo sukasa mata dariya, lallai 'yammata kin haďu.
Iman tayi 'yar dariya, ina gaya muku nacire kayana nasa na barci, na ďane gado na kwanta.
Cikin barci naji ana shafani, abinda baka sababa dan haka natashi afirgice tareda wage baki zanyi ihu.
Doctor yasa lallausan hannunsa ya rufe mini baki yana faďin iman nine fa, cikin rawar jiki na ce, "dan ALLAH ka dainamin wanan abun, wlhy gwaggo ta ce, "mini iskancine, kullum tanamin gargaďi, kokanaso na zubar da mutuncina??.
Doctor ya kunna fitilar dake gefen gadon, yakamo hannuna ya zaunar ya ce, "tokiyi ha'kuri nadaina yimiki zoki kwanta, na ce, "saidai na koma 'kasa, ya ce, "a'a yi kwanciyarki, nibari na kwanta saman kujera.
Haka yakoma saman kujerar dake a ďakin ya kwanta, nima na koma nakeanta atsorace, cikin ikon ALLAH babu daďeqa barci yay gaba dani dan akwai gajiyar biki a tattare dani.
Shikam doctor yakasa barci, yana mamakin dama azamaninnan da aka lalace akwai yaran dabasu san minene aureba, lalai shikam yayi babbar sa'a, idan yatuna abokansa dayawa, waďanda bayan aurensu suke masa tambaya akan suffofin mace mai cikakken burci, saboda kokwanto dasuka shiga akan nasu matan, yagodema ALLAH dabai kasance mazinaciba, bare ALLAH ya jarabceshi da auren mazinaciya, haka yayta tunane tunane har barci ya saceshi.
Kiran sallar farko ya farka, yatashi yaje bayi yay alwala, yayi raka'atainul fijir, saida aka kira sallar farko sanan yatasheni yafice masallaci.
Saida gari yaya sha sanan doctor yadawo, zuwa lokacin harna sake 6ingirewa akan sallayar dan barcin bai isheniba, yabini da kallo yana murmushi, akan la66ansa yafurta 'yarrigima kenan, ďaukata yay caj yadire agadon sanan shima ya hawo, ahankali yanutsani da jikinsa gudun karna tashi nayi masa mazurai, nikam nariga nayi nisa abarci bansan bikin dayakeyiba ma...............✍🏻







💕💚💕






Page.....6⃣

Karfe 8:00am nafarka sainajini ajikin doctor, da sauri nazare jikina daga nasa amma bai farkaba, dan haka na nufi bayi danyin wanka, harna fito na shirya cikin riga da siket na atanfa bai farkaba, ganin haka yasa na nufi falon dan inga tsarin gidan, na tsaya cak atsakiyyar falon inabin ko ina

Please Login or Register in order to submit comment