Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rawa tacigaba da mutau2n kwacewa, sai faman tsungulinsa takeyi amma ko'a jikinsa, aika mata da sakwanni kawai yake cikin zafin nama.
Da alama ya manta acikin mota suke, sunkai tsawon minti goma ahaka dakyar tasamu yasaketa, sai sauke ajiyar zuciya yake kamar d'an daya kwana uku baisha nonan uwarsaba.
Itama da sauri takoma d'ayar kujerar tazauna tana maida numfashi, jikinta sai rawa yakeyi, ALLAH yasotama ba'a gabansu deexerh yaymata wanan abunba, aidaba k'aramar kunya tajiba wlhy.
Ahankali ya rungume sitiyari yana ajiyar zuciya, bayan kamar minti uku, ya ce, "inasu deexerh d'in?.
Kad'an ta kalleshi taga yana rungume da sitiyari, taja ajiyar zuciya, Nima ban saniba.
Shiru yayi zuwa wasu 'yan sakwanni, sannan ya d'ago, bud'e motar yayi yafita, can yahango su deexerh zaune acikin runfar suna hira, yad'an d'aga murya yakirasu.
Atare suka juyo sanan suka mik'e, sunaji dad'in yanda suka gansa, suka k'araso suna MASA ya jiki, ya CE, " da sauk'i.
"Kushiga mutafi ko?, yafad'a yana Shiga motar.
Sums Suka Shiga ya tada motar, iman bata kalli kowa acikinsuba, wata iron kunyarsu takeji dukda basuga abinda Dr Isma'il yayi mataba.
Motar yayima key yaja suka tafi.
Yanzukam gudu yake sosai, motar tayi shiru babu mai magana.
Har suka shigo cikin kano bai sake kallo. Ko Inda iman takeba.
Juyowa yayi yakalli xoxo, k'awarmu INA muka nufa?.
Ta CE, " mije zan rink'a nuna maka.
Okey yafad'a yana satar kallon iman, wadda tunda suka taho kanta yana k'asa.
Da taimakon Xoxo suka Isa k'ofar gidansu, tayima Dr Isma'il godiya tareda addu'ar k'ara samun lfy.
Ya CE, "ngd, kigaida mutanen gida, zasuji tafad'a tana k'ok'arin fita.
Iman ma k'ofa takama Zata fice, yay saurin rik'o hannunta batareda yayi maganaba.
Tad'an d'aure fuska, nimafa anan zan sauka, sai anjima zan k'arasa gida.
Shiru yayi bai amsa mataba, Xoxo talek'o tana fad'in to Imam saimunyi waya, k'ila kuma gobe idan ALLAH yakaimu nashigo ma.
Iman ta CE, " to ngd sosai my Hafsy kigaidamin da momy Dan ALLAH. zataji, Nima ki gaidamin da my Musayeef da gwaggo da deeni da Abbah, duk zasuji insha ALLAHU, saikinxo d'in.
To sainazo, Ak'aramin godiya wajen daddyn Musayeef.
Hararta iman tayi.
Xoxo tabar jikin motar tana dariya.
Saida yatada motar sanan yasaki hannunta.
Daga nan gidansu iman yanufa.
Tunda suka tafi gabanta ke fad'uwa tana addu'ar ALLAH yasa kada kiwa yagansu, Dan zataji kunya sosai wlhy.
Ak'ofar gidansu yayi fakin, yana tsayawa deexerh tayi cikin gidan da gudu, shikuma yay saurin rik'e hannun iman dake k'ok'arin fita daga motar.
Bata juyoba bakuma tacigaba da yink'urin fitarba, muryarsa kasa2 ya CE, "ngd da taimakonki gareni, dabaki a kusa dabansan irin halin dazan tsinci kainaba ayau, ngd sosai.
Saidai zan k'ara tuna miki har yanzu akwai aurena akanki, *Ban sakeki ba!* Dan haka kicigaba da kula dakanki har lokacin da ALLAH zai bayyana gsky, Saudat kiguji abinda ALLAH zaikamaki da hak'in aurena, INA mana fatan Alkairi arayuwa, ALLAH ya albarkaci Musayeef da sauran k'annensa masu zuwa nangaba.
Kicigaba da sakani cikin Addu'arki Dan INA cikin wani yanayi na ciwon sonki, asanadin sonki nakamu da ciwon zuciya da hawan jini, ga matsananciyar sha'awa na damuna, akullum INA ADDU"AR ALLAH ya gaggauta bayyana gaskiyar halin damuke ciki, dukda kekam naga hankalinki akwance yake.
Amma nikam sai addu'a.
Tuni hawaye ya wanke fuskar iman, tausayi da tsananin son mijinta suka k'ara mamayeta, ahankali tazare hannunta tafice daga motar, tana k'ok'arin rufewa deexerh tafito itada Musayeef, da Sauri Dr isma'il yabud'e motar, ya d'auki d'ansa ya rungume yana maijin wani matsanancin facinciki da nutsuwa, saiyajima ciwon NASA yak'ara raguwa.
Jiki a sanyaye iman tashige gida tana share hawaye.
Tashin mortar Dr Isma'il taji, da Sauri tashare hawen idonta ta lek'a,.
Karaf idanunsu suka had'u yanuna Kansa da k'irjinsa ❤ sanan ya nunata ya had'e hannayensa🙏🏻, yatsu uku yad'aga mata, yaja motar da Sauri yabar wajen musayeef yana mata bey bey.
'Dan murmushi tayj Dan tasan abinda yayi mata yana nufin *"I luv u*.
K'ara share hawayenta tayi sanan tashiga gidan da Salama.
Gwaggo dake zaune tana gyaran alayayyahu ta amsa da far'arta, da Sauri iman taje ta shige jikin gwaggo tana mai far in cikin ganinta.
Itamadai cikin farin cikin ta tarbeta............




*Dan ALLAH idan damai ban saketaba saga farko yad'an turomin nayi missing d'in NAWA*.
09093044460






*luv u oll my fan's*
*(((S)))......2017.*
[8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!._*






*_NA Bilyn Abdul_*


_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*



*BARKA DA SALLAH*
*Bilyn Abdul H Novel's*
*Zumunta group*
*Online Hausa Writer's*
*Home of Novel's*
*House of Novel's*
*Muhad'a kammu mata*
*Hausa Novel-Farin ciki*
*Asmy fan's club*
*Billy Galadanci's Novel*
*'Dan/zabuwa 2010 Graduation*
*Fashion & Novel's*
*Miss Xahras Novel's*
*Hausa Novel's*
*Mmn Shureim Novel's*
*Talented Writers group*
*Hausa Novel's*
*Maryam G Novel's*
*Ciwon 'ya mace*
*House of Novel's 3*
*Manshat Novel's*
*Musan junah o,h,w.*
*Ikkiram's Novel's*
*Hausa Novel's*
*Mmn Useey Novel's*
*Feedo online Novel's*
*Hawwa H Novel's*.
*Faheemta Novel's Mrs jh*
*Hama Gee's Novels Chamber*
*Fareedat Novels*.
*Mmn Shaheed Fan's*
*MF&JH Hausa Novel's group*
*Feedo online Novel's*
*004 Hausa Novel's book's*.
_baridai naja birki an an da mik'a sak'on SALLAH, INA muku fatan Al'kairi arayuwa, nagode da k'auna._
Duk Wanda baiga sunansaba yamin Afuwa, badan bana sonsa bane saidan yawa dakuke dashi, duk inda masoyina yake INA Al'faharee dashi, ngd.
*luv u oll😘😘😁👌🏼*




https://mrsbilkisa.blogspot.com

*(page 18)*

Iman kinga yanda kikayi k'iba kuwa?, lallai makarantar nan babu wahala.
Kai gwaggo babu wahalafa kikace?, iman tafad'a tana turo Baki gaba.
Dariya gwaggo tayi, oh ni wai sai yaushe iman zakisan kin girmane?, kiyi shagwa6a musayeef yayi.
Dariya iman tayi tashige d'akin ta.
Kayanta tacire, sai wani faman murmushi takeyi Wanda Nima bansan namiyeba masu karatu.
Kayanta takai hancinta tana shinshinawa, talumshe idanu Dan jin dad'in kamshin turaren Dr Isma'il daya manne a kayanta. Gaban madubi tak'arasa tana kallon fuskarta, takai hannu kan la66anta tana shafawa ahankali, murmushi tayi Dan tuno irin kissing d'inta da Doctor tayi, afili ta CE, "ALLAH ngd maka daba agabasu Xoxo yayminba, nasan danasha tsokana.
Wayarta tad'auka tak'ara gwada Number Reefat amma bata shigaba, ta ce, " lallai Reefat soyayya tayi dad'i an manta damu.
Waje tayo tana fad'in gwaggo Dan ALLAH akwai ruwan d'umi agidanan?.
Eh akwai acikin kicin wanka zakiyi ko?.
Eh wlhy gwaggo gwara nayi naji dad'in jikina, ga garin akwai sanyi.
Hartaje k'ofar kicin d'in saikuma ta juyo, gwaggo wai miyasa kika Ba deexerh Musayeef ne?.
Kallonta gwaggo tayi, kijimin yarinya dawani zance, na hanata d'aukar d'an uwanta, kuma batacemin tare kuke da babansaba, to ko babu babansa itama aii ta Isa tazo ta d'aukeshi ko.
Amma gwaggo aidai sabari mugaisa ko?.
Uhmm kudai kuka sani, saiki kirashi kice yadawo miki da d'anki aii.
Da Sauri iman tashige kicin d'in Dan tasan bak'ar magana gwaggo tafad'a mata. Koda tajuyo ruwan tadawo gwaggo ta tashi, d'aki tawuce abinta tayi wanka, doguwar Riga tasaka jaa, bawata kwalliya datayi tafito tsakar gida.
Gwaggo ta ce, "ga abinci nan afalon Abbahn Ku, kid'ibo kici ko?.
To gwaggo iman tafad'a a sanyaye, Dan wlhy duk kewar Musayeef ta isheta.
Taci burin yau susha hira da *" Hasken idaniyarta"*.

A6an garden su deexerh kuwa suna zuwa gida ta sa6i musayeef suka nufi 6angaren mama, Dan tasan dukkan ahalin gidan suna can tunda yau asabar babu makaranta.
Dr Isma'il ma can yanufa, lokacin daya Isa falon ya kaure da murnar ganin musayeef, shima sai farinciki yake daganin 'yan uwansa.
Mama tafara fad'in oyoyo autana, da murmushi afuskarsa yak'arasa Kusada mama yazauna, ya gaisheta, cike da fara'a ta amsa masa.
Ina kasamo min mai gida na robar?.
'Yar dariya yayi danyasan Musayeef take nufi, ya ce, "gidan mukaje muka taho dashi.
Mama tarik'e ha6a auta banda fin k'arfidai.
Dariya yayi yana gaidasu Maman deexerh da aunty sadiya.
Yamik'e mama bari nad'an watsa ruwa nadawo, aunty baba mikika tanadar minine?.
Dariya Maman deexerh tayi, ta ce, " k'anina girki na musamman nayi maka, tunda kak'i kayi aure.
Dariya yayi, Idan kunaso nayi aure kuje kudawo min da momyn Musayeef kawai yafad'a yana ficewa.
Aunty tad'an ta6e Baki amma babu Wanda yaganta saini bilyn Abdul 'yar rahoto.
Mama da Maman deexerh kuwa da kallon tausayi suka bishi.
6angarensa yanufa yasa key yabud'e wani k'amshi yadaki hancinsa yashak'a ya lumshe idanu, yasan wanan aikin Maman deexerh ne, Dan waccan mai kama da karuwar bazata ta6a gyara MASA wajeba, (aunty yake nufi😜).
d'akin iman Nada yashige yakwanta Dan yanzu yamaidashi d'akinsa saboda yarink'a d'ebe masa kewarta.
Yaja fillo ya rungume tsam ak'irjinsa idanunsa ya rintse Dan tuna abinda yafaru d'azu amota tsakaninsa da imam, wani irin farin ciki yakeji, yak'ara matse filon yanaji tamkar iman ya rungume, muntuna kad'an barci yay awon gaba dashi.

Yana cikin barcinsa mai dad'i yaji Musayeef yana tadashi, yabud'e ido yasauke akan yaron.
Musayeef yay 'yar dariya, daddy katashi?.
Hannunsa yakamo yakwantar dashi agabansa, yarungumeshi, miyasa katadani INA barci Musayeef?.
Daddy dare yayi, katashi ka kaini wajen aunty Maa!.
Dr Isma'il yajuya yakalli agigon dake d'akin, 6:27pm, da Saudi yatashi zaune, innalillahi dama haka nadad'e INA barci?.
Musayeef ma tashi yayi zaune yana fad'in daddy inzo muje ka kaini waje Aunty maa d'in?.
Ma6allen rigarsa yafa cirewa yana fad'in Musayeef sai yanzu katuna da aunty maa d'in?, kabari sai gobe idan ALLAH yakaimu kaji.
Kusadashi yazo ya zauna yad'aukeshi yad'orasa asaman cinyarsa, haba my boy bakason zama dani sai aunty maa?.
Inaso mana musayeef yafad'a yana kallon babansa.
Sumbatar kumatunsa yayi yauwa my lovely son, yanzu kaga kazauna kajirani nayi wanka kaji ko?.
Daddy Nima zanyi wankan.
A'a kabari sai zamuyi barci, kaga ga wayata kayi game.
Cike da murna Musayeef ya CE, "daddy inaso zanyi game d'in, kamomin irin na aunty maa!.
Dariya Dr Isma'il yayi, game ya nemomasa yabasa sanan yanufi bayi domin yin wanka.
Wankan tsarki yayi Dan mafarki yaytayi yana tareda Iman, yad'auro Alwala yafito, sallaya yashinfid'a yafara rama sallolin da'ake binsa, Musayeef kam yana busy akan waya, game ya d'auke masa hankali gabad'aya.
Dr Isma'il bai tashi ba saida akayi sallar isha'i, yayi addu'oi yatashi, gadon ya haye yakwanta Kusada Musayeef daketa aikin game, tsayawa yayi yana kallonsa sai murmushi yake Dan ganin yanda yaron ya kware da iya game d'in, waya koyamaka game d'innan Musayeef?.
Ya CE, "daddy aunty maa mana, kullum idan bata tafi makarantaba sai munyi kafin muyi barci, daddy kaima kace mata ta koya maka.
Aii bazata koya minba nasani Dr Isma'il yafad'a yana marairaice murya.
ALLAH dady zata koya maka, nuna min Number ta nakirata tazo yanzu ta koya maka.
Dariya sosai Dr Isma'il yakeyi, shikam Musayeef yatubure sai ankira aunty maa Tazo ta koya game, hardasu kuka.
Ganin haka yasa Dr Isma'il kar6ar wayar danya kira iman, ALLAH ma yasoshi ya k'ar6i Number ta awajen deexerh, dayaga takansa da rigimar Musayeef.

Iman kam tana zaune abakin gado sunata hira da Xoxo awaya tamkar ba yau suka rabuba, sun dad'e suna hira harsaida katin Xoxo yak'are sannan, iman tacire wayar daga kunnenta tana dariyar maganar xozo ta k'arshe, danna number ta tayi da zummar kiran xoxo, sai bak'uwar Number tashigo.
Fuskarta cike da far'a tad'aga, azatonta Xoxo CE takirata da number wani d'an gidansu.
'Dagawa tayi tana fad'in shegiya sisi kud'inwa kuma zaki k'arema tanadi?, Dr Isma'il ya lumshe idanu danjin muryar Iman tadaki dodn kunnansa.
Ta CE, "hello my hafsy bak'ya jinane?.
Shiru Dr Isma'il yakasa amsawa, bayason ya amsa ta Yankee wayar, gashi shikuma bai gaji d'ajin muryartaba. Iman ta Yankee wayar tana fad'in inaga bata jina, kokuma bataso mai wayar ya ganota, kai ALLAH yashiryamin ke my Darling sis...
Kiran Number yayi bugu d'aya aka d'auka, hasnfree yasaka sanan yabama Musayeef wayar..
Cike da d'oki Musayeef ya ce, ''aunty maa!..
Ajiyar zuciya ta sauke, ta CE, " habawa yaro babu wani aunty maa, aii mun 6ata.
Tuni fuskar Musayeef ta Nuna alamun damuwa, ya CE, "yi hak'uri aunty maa mu shirya.
A'a nikam babu wani shiri dazamuyi, bakana ganinaba d'azu amma kabi daddynka.
Duk maganar dasukeyi Dr Isma'il yana jinsu. Musayeef yafara kuka yana fad'in Aunty maa bazan sakeba, mushirya.
Shiru tayi na minti biyu.... Tabud'e Baki zatayi magana saitaji muryar Dr Ismail tadaki dodon kunnenta, Aunty maa plzz kiyi hak'uri mu shirya, gabantane yafad'i rasss.
Yakuma cewa plzzzz!!, yanda yaja pls d'in saida tsigar jikinta ta tashi.
Akasalace ta CE, " na hak'ura, wani ihun murna Musayeef yasaki, yatashi yana tsalle akan gadon, iman dake jiyo ihun Musayeef da tsallensa sai a bin yabata dariya, tashiga k'yalk'yata dariya, tama manta da Wanda yake kusadashi.
Shikam Dr Isma'il tuni wutar dake taimakawa jikinsa aiki ta d'auke d'ifff, dariyar iman bak'aramin sakashi a shauk'i tayiba, yashala sosai a saurarenta.
Ta ce, "ALLAH ya shirya minkai Musayeef tafad'a muryarta na rawa alamar har yanzu dariyar Tana cinta, Dr Isma'il ya CE, " amin ya rabbii.
Gabantane yafad'i dama har yanzu yana rik'e da wayar?, da Sauri ta Yanke wayar tana dafe k'irji.
Dr Isma'il yabud'e Baki zaiyi magana saiyaji d'if, alamar an Yanke.
Musayeef yakara kunnensa zaiyi magana yaji shiru, yafara Kiran Aunty maa!, amma yaji tsit.
Akasalace Dr Isma'il ya CE, "ta kashe Musayeef.... Aii kafinma yak'arasa Musayeef ya kware Baki yana kuka, lallashinsa yafara yi amma fir yak'i, shi sai ank'ara kiranta, dole Dr Isma'il yashiga kiranta amma tak'i ta d'auka.
Ga musayeef sai kuka yake masa, test yay mata kamar haka.
*plss My live!, kid'auka wlhy Musayeef kuka yakeyi saboda kin kashe, Dan ALLAH badan Niba*
Iman tana kwance, tunda ta Yanke wayar, duk kiran dayakeyi tana kallo amma tayi burus da wayar.
Shigowar sak'o yasa ta d'auki wayar, bud'ewa tayi ta karanta.
Itama saita tura masa kamar haka.
*kayi banza dashi idan yagaji zaiyi shiru aii* ta tura itama.
Cikin hanzari yabud'e sak'on Dan kukan Musayeef yafara damunsa.
Yad'an cije le6e sanan Yakuma tura mata *Dan Girman ALLAH fa nace my live!*
Sanin girman ALLAH yasa ta yarda zata d'aga, kiranta Yakuma yi, saida takusan tsinkewa sanan tad'aga, hansfree Yakuma sakawa sanan yabama musayeef yana fad'in ishirunka my darling ga aunty maa d'in.
Da Sauri yakara akkune yana sauke ajiyar zuciya, iman ta CE, " oh kai Musayeef saboda na kashe waya katasa daddynka gaba kana masa kuka?, To mikakeson kafad'amin?.
Musayeef yasake share sauran hawayen fuskarsa, ya CE, "aunty maa kizo ki koyama daddy game.
Azuciyarsa ta CE, " kaji kuma wata fitinar, yakatseta da fad'in kinji aunty maa.
Musayeef inbada rigimadai yanzu yaza ayi nazo na koyama dadynka game, bakaga dare yayibane?.
Yafara tirza k'afa alamar zaiyi kuka, da Sauri Dr Isma'il yamaida maganarsa zuwa turanci, ya CE, "pls my live kice MASA zakizo, in ba hakaba kukan zai k'arayi.
Iman tace to kajirani ganinan zuwa yanzu.
Cikin murna ya CE, " to aunty maa.
Iman tayanke wayar tana fad'in musayeef rigima kenan........






*luv u oll my fan's*
*((S))......2017*
[8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*





*_NA Bilyn Abdul_*



_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com




*Miyakamata nayi?*
_kizama mai hak'uri arayuwa, mai tausayi Gana k'asa dakai, mai girmama manya, mai adalci, mai kunya, mai gudun zunubi komai k'ank'artarsa, mai gudun cutar dawani koda akan rashin Sanine, mai imani, mai gudun k'arya, mai Neman ilimi, mai yawan bautama ALLAH, mai yawan tsoron ALLAH._
_idan karik'e narik'e kika rik'e kuka rik'e, muka rik'e, inaga ZAMU zama cikin ceton fiyayyan halitta *ANNABI MUHAMMADU* tsira da aminci suk'ara tabbata agareshi._
*ALLAH yasa Mugabe*




*(Page 19)*
Koda suka gama wayar sai iman ta lumshe idanu, tareda rungume wayar ak'irjinta, jitake wani dad'i yana ratsata Wanda batasan dalilinshiba.
Bata tashiba har saida deeni yazo yakirata sanan taje kiran.

A6angaren Dr isma'il ma hakan take, tsintar Kansa yayi cikin tsananin farinciki Wanda yadad'e baiyiba, yayma musayeef wanka sukai shirin barci, haka ya rungume d'ansa sukasha barci mai dad'i abinsu.

_washe gare_
Dr Isma'il dakansa yayma Musayeef wanka, dayake ana yawan kawoshi gidan sai yakasance akwai kayansa, tawul ya d'aura masa ya ce, "maza kaje wajen mom tasaka maka kaya.
Dagudu Musayeef yanufi 6angaren su deexerh, Dr Isma'il yay murmushi yana binsa da kallo harya 6acema ganinsa. Ido yalumshe tareda zama bakin gadon, wayarsa yad'auka yafara sarrafata cike da k'warewa, haka kawai yaji yanason jin muyar Iman, yad'an dad'e yana tunanin idan ta d'auka mizaice mata, can yay wani tunani murmushi yayi tareda dialing d'in Number ta.
Alokacin iman na zaune tana maida numfashin gajiya, bayan tagama gyaran gidan duka tahad'a musu abin Karin kumallo.
Tabud'e idanu tareda fad'in wake kirana?, ko Reefat CE?, ko xox.......shiru tayi takasa k'arasawa Dan ganin number dake kiranta, tun adaren jiya ta haddace No d'in.
Wayar ta Yanke, Dr Isma'il yad'an cije le6e yana fad'in pls my live karkimin haka, yana maganar yana k'ara kiranta, yanzuma saida takusa k'atsewa sanan ta d'aga Dan atunaninta ko Musayeef ne.
Assalamu alaikum tafad'a tana zama abakin gadon, shiru na 'yana sakwanni, Dr Isma'il yakasa amsawa, bayaso yaymagana taji muryarsa ta Yanke.
Ta ce, " Musayeef Baka jinane?.
Muryarsa a sark'e ya ce, ''ba Musayeef bane daddyn sane, amma pls karki Yanke, zamuyi maganane Dan ALLAH.
shiru iman tayi tana sauke numfashi ahankali, muryar Dr Isma'il tana ratsata, azuciyarta ta ce, "bama saika rok'eniba Nima bazan iya kashewaba Dan bangaji dajin sautin muryarkaba.
Jin tayi shiru yasa yafara magana ad'an d'arare, my live kin bani dama?.
Iman ta lumshe idanu, sanan ta ce, " kafid'i maganarka idan ba hakaba zan kashe.
No my live pls karki kashe.
Batace komaiba sai ma kwanciya datayi visa gadonta.
Ya ce, "my live bakifa gaisheniba?.
Ajiyar zuciya tayi ta CE, " INA kwana?.
Lfy lau Rayuwata!, kin tashi lafiya.
"Lau."
Tafad'a atak'aice.
Ya ce, "baki tanbayeni Musayeef ba, kobakiyi missing nashibane?.
Karo nafarko datayi d'an murmushi, muryarta can k'asa ta ce, " idanma nayi yazanyi, tunda ka d'aukeshi.
Ya lumshe idanunsa shima yana murmushi, a'a idan kinason ganinsama yanzu saina kawo mikishi.
Humm na hutash sheka, kabarsa cikin 'yana uwansa suma suna buk'atarsa sosai.
Dr Isma'il yagyara kwanciya danjin yanda Iman ta saki jiki dashi, aikema kina buk'atarsa, saboda kin dad'e baki gansaba.
Hakane tafad'a tana k'ara rungume fillo ak'irjinta, nasan nayi missing NASA sosai, amma ai suma suna buk'atar kasancewa dashi, ni nikad'aice sukuma sunada yawa, so kaga sun rinjayeni sosai.
Ya saki wani lallausan murmushi Toni Nazo kiganni.
"A'a".
Miyasa ni ba'a son ganina?, kodanni ba d'anki bane?.
'Yar dariya Iman tayi tana juya kwanciyarta, nidai ban fad'aba.
Yanda take dariyar dukta kashe MASA jiki, ya ce, " kenan Nima ana missing d'ina?.
Ido tawaro waje tamkar yana gabanta, ta ce, "mizaisa nayi missing NAKA nikam?.
Maganarta yad'an ta6a zuciyarsa amma ya danne tunda Neman sulhu yakeyi da ita, ya ce, " amatsayina na daddyn d'anki!, masoyinki na har abada.
Shiru Iman tayi hawaye suna bin kumatunta, bata sharesuba bakuma tasake maganaba.
Jin tayi shiru Dr Isma'il ya ce, "hello kina jina?.
Muryarta dad'an rawa ta ce, " eh!.
Yanda ta amsa masa yasa yagane kuka take, Dan yasan Iman da halinta sosai.
Shima jiyayi kwalla ta cika MASA idanu, muryarsa a sark'e ya ce, "kema kinajin yanda nakeji ko Saudat, da akusa dani kike dakinji yanda zuciyata take bugawa da k'arfi kamar zata Faso k'irjina tafito, nayi kewarki sosai Iman, kullum sainayi wankan tsarki saboda barci danakeyi mai cike da mafarkinki, pls Saudat kigayamin gsky waya ya rubuta miki takardar sakin nan?, idan kece kifad'amin? zanmiki uzuree kuma zanyi yanda zanyi nagyara komai batareda asirinki ya tonuba, Dan ALLAH kifad'amin gsky, yak'are maganar yana hawaye.
Kuka sosai Iman takeyi har yanajin shashshekarta.
Suduka sunyi shiru kowa yana kuka, _(Nima masu karatu kukan nake saboda tausayinsu😭)._
'Diff iman ta Yanke wayar tanacigaba dakuka, da bak'incin maganar Dr Isma'il, wato duk tsawon lokacinanma ita yake zargi ta rubuta tankard ar sakin?, itakam tashiga uku, tunda take ko alabaran Novel's bata ta6ajin makamancin labarintaba, lallai tana cikin rud'u.
Ita tana ganin mijinta yasaketa, to Ashe shikuma kallon ita tarubata takardar sakin yake mata, shin wazata tambaya gskyar lamarin?, kodai da gsk Dr Isma'il *Bai saketa ba!* to waye yarubuta takardai?, Kokuma raina MATA hankali yakesonyi ne?.
Ta kuma kecewa dawani matsanancin kuka Wanda itama batasan tanayiba.
Da Sauri gwaggo tak'araso d'akin danjin kukan Iman, Innalillahi Iman bakida lafiya?.
Batabama gwaggo amsaba sai ma fad'awa datayi jikin gwaggo tafashe da wani Sabon kukan mai tsuma zuciya.
Lallashinta gwaggo tashigayi, itakuma tanata raira kuka, saida tayi mai isarta sanan tayi shiru, gwaggo tad'ago fuskarta tanamai share mata hawaye, iman miyasakaki irin wanan kuka haka?, ko wanine yamutu?.
"Girgiza kai iman tayi alamar A'a".
Tomiye yafaru?, kosaboda Musayeef d'in baya nanne?., nanma kai ta girgiza gwaggo tayi shiru tana kallonta, can ta CE, " to kifad'amin gsky, nasan dai ke bak'ya k'arya, dan haka gayamin mike faruwa?, koda taimakon dazan miki amatsayina na mahaifiyarki.
Iman tasake matso hawaye tabbas tasan batada kamar gwaggo, sai kuwa yayarta aunty Salma, saiko su Xoxo da Reefat da ayanzu take Musu kallon 'yan uwa suma.
Tagyara kwanciyarta ajikin gwaggo, ta CE, "gwaggo daddyn Musayeef ne, anan takwashe yanda sukayi tafad'ama gwaggo.
Shiru gwaggo tayi tana nazari, zuwa can ta CE, " iman wlhy bazan 6oye mikiba koni lamarin nan yana d'auremin kai idan nayi la'akari da halin da yaron nan yashiga bayan kin dawo gida, nidai gani nake kamar akwai wani kulli dabamu saniba, agefe kuma zamanki agida yana cin zuciyata, burin kowace uwa taga 'ya'yanta agidan miji k'ark'ashin inuwar aure, Iman shekararki hud'ufa kenan agida, tun cikin Musayeef yana k'arami gashi yanzu harya

Please Login or Register in order to submit comment