Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan kin rabama guys naki a titi?._
_randa kikayi aurefa akwai Matsala wlhy, duk d'an isaka baya son auren 'yar uwarsa 'yar iska, burinsa yasamu nitsatstsiyar mace kamila ya aura, kinga wanan kawai ya Isa ya nuna miki kin fad'i babu nauyi, idan aure kikeso karkiji kunya kisanar da iyayenki, idan bazaki iyaba samu wani a 'yan uwanki kisanar masa yasanar da iyayenki, wanan rashin kunyar tafi sauk'i akan kizubar da darajarki awajen wani sakarai Wanda baisan muhimmancin budurcinkiba, 'yar uwa tattali abinki kikaima mijinki domin yasaka ranar farkonku acikin muhimman kundin tarihinsa, duk mijin da matarsa takai masa budurcinta bazai ta6a mantawa da wannan k'yautarba har k'arshen rayuwarsa._
_wallhy 'yar uwa gsky nake gayamiki budurci mutunci, kuma, nagarta, donk'on so, tattalin so, k'auna ta musamman yake jawowa gadukkan macan data kaima mijinta._
*ALLAH yasa mugane*



*(page 32)*
*_8:00pm_* kowa yagama shiri za'akai iman, gayyace guda y'an rakiyya, Dan Matan anguwar dayawa sunshigo Dan rakiya abin kamar wasa.
Xoxo dake kusada iman zaune sun gama waya da Reefat sun bata labarin komai tanata murna, kira yashigo wayar Xoxo, takalli wayar tana murmushi Dan wringing na musamman tasaka masa, itadai iman sai binta take da kallo kawai, ga zuciyarta taf da fargaba.
Assalamu alaiki gimbiyata.
Wa'alaikassalam sarkina.
Dr Nabeel yay murmushi tamkar yana gabanta, ngd sosai dasamun sarauta, amma haryau baku maida mana amaryarmu bane?
Tab aii wanan amaryar ta gskce, saikunzo da motama, 'yan rakiya fal gida.
Kai haba?.
ALLAH kuwa.
Ku sauraremu gamu nan zuwa, kafin tace wani abu ya yanke wayar.
Iman ta ce, "karfa ya d'auka gskne sisi.
Oh keda wasa kika d'auka, kina ganin idan basuzoba saidai wasu mutanan suhau keke napep fa.
Iman ta ta6e Baki, kenifa daza'a fasa zanyi murna.
Dariya sosai Xoxo takeyi, haba 'yammata babu fashi yau saimun kaiki, ak'irjin Daddyn Musayeef zakiyi barci.
Duka iman takai mata ta kauce tana dariya, wlhy hafsy ke 'yar sikace, amma Dr Nabeel zaimana maganinki, kamar yanda yaa usman yay maganen Reefat.
Xoxo tamik'e tana fad'in Ashe za'a dad'e ba'ayi maganin nawaba.......
Sallamar aunty salmace ta k'atse Xoxo, tamik'ama iman kaya, kinga tashi ki shirya abbah sai fad'a yakeyi.
Iman takar6a tana turo Baki haba nikam naga takaina yau.
Bakiga takankibama sai anjima aunty Salma tafad'a tana Fita.
Dariya Xoxo tasaka, harda yima iman gwalo gsky ne auntyn mu, sai anjima zataga takanta.
Iman tamik'e tanufi Xoxo, itakuma tafita da gudu, zan kamaki aii humyim.
Xoxo tak'arasa inda aunty Salma take, saitin kunnanta ta gwargwad'a mata magana.
Aunty Salma tayi dariya dgsk hafsat?.
Wlhy kuwa aunty suna k'ofar gida, hannu aunty tabata suka ta6a, shiyyasa nakesanku 'yan k'annena kanku akwai kawo haske😉.
Xoxo tayi dariya, aunty aigara muje musu ashirye su tabbatar wa mak'iya da gsk mukeyi.
Tafawa suka sakeyi, ALLAH yamiki albarka k'anwata, yakaimu naki da Dr Nabeel.
Da Sauri Xoxo tafita tana dariya, dansu ummanta suna gurin, itama taxo za'a raka iman da ita.
Aunty Salma ta ce, "to jama'a ga motoci ankawo yakamata muyi harama.

Kowa yamik'e akayi waje, aunty Salma tashiga ta Tatar Xoxo ta gama d'aurama iman d'ankwali, kwalliya sosai Xoxo tamata dukda bataso amma Xoxo ta dage saida tayi mata, tayi k'yau kamar wata aljana, _(nikaina mace saida na k'yasa😉)_..
Kamar wasa saiga iman tana rabzar kuka, gwaggoma kukan takeyi, ahakadai aka lalla6a akyo waje da iman.
Dr Nabeel ya kalli Dr isma'il dake cikin mota zaune, bayaso agansa, ya ce, " Alhaji aii yau kad'auka sabuwar amarya za'a kaimaka.
Murmushi Dr isma'il yayi yashafa sumar kansa datasha aski da gyaran fuska, "o, kaida mika d'auka za'a kaimin?.
To kamabar wani tunani amarya gal aleda za'a kaimin.
Nabeel yay dariya, cikin musayeef kuma aruwa tasha ko?.
Rankwashi yabashi akai, to d'ansa ido koma ya akayi ina ruwanka......
Kafin Dr Nabeel yay magana su Xoxo suka iso rik'e da hannun iman daketa shashshekar kuka.
Nabeel yabud'e musu suka Shiga, shima yashiga yatada motar, shiru Dr isma'il yayi Dan bayaso agane dashi akazo, amma tuni k'amshin turarensa yacikama Iman hanci.
Bata kawo yana motarba, azatonta motarsace shiyya turaren Yakama motar, har lokacin shashshekar kukanta takeyi.
Dr Nabeel ne gaba, mota biyar ta 'yan rakiya suna binsa abaya.
Tunda suka shiga cikin gidan suke rangad'a gud'a kamar ankawo sabuwar amarya, ananma gidan cike yake Da makwafta, Dan tarba tamusamman mama da mom suka shirya musu.
Yauma tarihi ya maimaita Kansa, saida aka fara kaita 6angaren mama, mama ta rungume iman tana hawayen dad'i, itama iman kukan takeyi,, an dank'a amanar iman a hannun mama akaro na biyu, wanan karonma mama ta kar6i Amanna tareda addu'ar fatan alkairi ga iman, sannan tabada k'yauta abama iman wadda babu Wanda yasan komiye aciki.
d'aukarta akayi daganan har 6angarensu mom, itama dai amanar iman aka bata itada Yaya, suma sun kar6a.
Su aunty dai anzama 'yan kallo, bak'inciki fall ransu saidai babu damar koda tarine mai k'arfi😜.
Daga nan 6angarenta aka kaita, tofa anafa kallo yakoma sama.
Jar ubancan kai, kai masu karatu, kunga wani sabon salon gyara da akayima 6angaren kuwa?, hu'ummm nabaku dama kutambayi Xoxo labarin tsaruwan da 6angaren yayi😉.
'Yan rakiyadai sunata tofa albarkacin bakinsu, har tsakkiyar gadonta aka kaita, gadone na alfarma, mai musalta muku tsaruwarsa sai Xoxo dasuka kasance amara kirjin biki, lol.
Bayan 'yar nasiha da aka k'arayima iman, 'yan rakiya sukayo waje, umman su Xoxo kawai aka bari ad'akin da aunty Salma, Umma ta koro Xoxo waje, fitowa tayi tana zum6ura Baki, mumadai ankusa daina korarmu idan za'ayi wanga zance, shiyasa Zarah Bukar ta ce, "bata zuwa rakkiyar amarya da manya, Ashe da gskyarta.
Tana tsaye tana kunkunai Dr Nabeel ya iso gareta, humm wanan bayajin kunyar gamo da Umma ne.

Abubuwa su Umma sukabama iman, wasuma suna d'akin tashiga bayi tayi amfani dasu, aka bata wasu tasha, sanan suka fito, itakuma taja filo tarungume tana kuka.
ALLAH yasa Musayeef yazo yanzu, Dan ita rabonta dashi tunkafin taje gidansu Xoxo, yau data dawo akace yana nan gidan.
Bayan kamar minti15 gidan yay tsit, kowa Yakama gabansa, taso Xoxo tashigo su k'ara yin magana, amma Umma ta korata.

*************************
Har k'arfe goma Dr isma'il bai shigoba, itakam bata daina kukanba, Dan ita azatonta yana wajen Raihan, datayi shiru ta kalli agogo saita k'ara fashewa da kuka.
Dr Isma'il kam yana d'akinsa kwance, yama rasa irin murnar dazaiyi, tashi yayi yay wanka yashiga gyaracan goge can tamkar wani mace.
Yarasa kayan barcin dazaisa, candai idonsa yatsaya akan wasu fararen kayan barci masu taushi, wandone iya gwuywa da riga mai bud'ad'd'en k'irji, yabaza turare na d'aukar hankali.
Ledar da Dr Nabeel yabasa yad'auka yanufi d'akin iman.
Wasu hawaye suka wanke kumatun Raihan dake bakin k'ofa tana kallonsa, takoma cikin d'akinta dagudu tana kuka.
Shikam dama baisan tanayiba yatura k'ofar iman ahankali yashiga, bakinsa d'auke da sallama.
Wani k'amshin dad'ine yabugi hancinsa, yashak'a ya lumshe idanunsa, ahankali yabud'e ya saukesu akan iman dake kwance tana kuka, Dan shigowarsa saita k'arajin sabon kuka.
Cikin takun nutsuwa yak'arasa gaban gadon, ya ajiye ledar ak'asa sanan yahaye saman gadon shima.
Gabanta yaje ya kwanta yana fusakantar ta, da Sauri tamik'e zaune tana hararsa.
Wani murmushin gefen baki yasaki, Wanda ya kashe zuciyar iman, taisaurin duk'ar da kanta k'asa Dan murmushinsa ya tsayar da hawayenta cak.
Hannunta yakamo yarumtse anasa, Amincin ALLAH ya tabbata agareki my life.
Bata tankashiba saima k'ok'arin zare hannunta takeyi.
Bai bata damar hakanba, yakuma damk'e hannunta sosai Wanda yakejinsa kamar auduga dan laushi.
Muryar iman can k'asa ta ce, "INA musayeef?.
Murmushi yak'ara yimata yana murza hannunta, lallenta yaymasa k'yau sosai, muryarsa cike da salo ya ce, " gadai daddyn musayeef atare dake, musayeef kuma yana wajen mom d'in Deexerh.
Shiru tayi babu amsa.
Yatsunsa biyu yasa yad'ago ha6arta, sai kawai tamatso hawaye.
Yad'an rintse ido yabud'e, ahankali ya ce, "har yau bakibar kukan rabuwa dasu gwaggonba ne?, yakamata kiyi shiru haka nan, tun amota kike kukafa.
Aii kamar ya zugata saima ta fashe masa da kuka.
Jawota yayi yarungume yana lallashi, my life please ya Isa haka, inko bakiyi shiruba nima zan fara miki kukan, yafad'a yana d'ago fuskarta.
Yanda ya yamutse fusaka kamar yaro saiya bata dariya.
Ta murmusa.
Shima yasaki lallausan murmushi yana kallonta.
Matsawa tayi baya tana turo baki gaba.
Yagyara zamansa wauni gudunama akeyi kenan?, duk'ar dakai iman tayi tana wasa da zoben hannunta.
Yakuma matsowa daf da ita ta matsa baya, ya matso tamatsa, suka dangane da jikin gado, murmushi yayi ya ce, " to munzo k'arshe sai Yaya kuma?.
Kallonsa tayi da runannun idanunta datasha kuka, ta ce, "saina barmaka d'akin.
Hhhhh duk Inda kikaje yau zan bikine aii.
Mik'ewa tayi danufin barin gadon, yajawota tafad'o jikinsa, zobe yaymata da hannunsa yarungumeta tsam ajikinsa.
Tafara mutsu mutsun kwace kanta, yakuma matseta, cikin kunnenta ya ce, " yaufa babu wata hanyar ku6ta Dan mak'ogwarona abushe yake da k'ishirwa.
Tad'an kalli fuskarsa akaro na farko, wani shek'in angwanci taga fuskarsa tanayi, takawar da kanta daga kallonsa, jitayi zuciyarta tana wani zafi saboda kishi, aranta ta ce, "namiji munafiki.
Yalura da canjin fuskarta, ya sumbaci yuyanta dake wani tashin k'amshi mai rikitashi, my life baki yarda da maganata bane?.
Baki ta ta6e tana k'ok'arin tashi, yazanyi na yarda bayan kaima Kasan ba haka bane, harma mai amarya yayi k'ishirwa.
Hannunta yaruk'o Dan harta mik'e daga jikinsa, ta kauda fusakarta data jik'e da hawaye.
Dawo da ita yayi saman cinyarsa, yajuyo da fuskarta suna fuskantar juna, saita rintse ido tana k'ara zubo da hawaye.
" aransa ya ce, "kishi".
Afili kuma saiya huro iska daga bakinsa, yana hura mata akan idonta, nan take hawayen suka tsaya, kafin ta bud'e ido ya had'e bakinsa maicike da k'amshi danata, sannan yaymata k'yak'yk'yawar runguma wadda babu maganar kwacewa...................



*_hummmm masu karatu........... Baridai na shiru kawai🙊._*





*luv u oll my fan's*
*(((S)))..........2017*
[8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*






*_NA Bilyn Abdul_*





_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com


*_"wanga page nakine k'anwa Marak'isiyya alkairin ALLAH yakaimiki, nayi missing naki sosai, yakamata kidawo haka nan"._*



*(page 33 & 34)*

Cike da wani irin salo yake sumbatarta, lakwas tayi takasa yunk'urin kwacewa, shikam saiya k'ara k'aimi cike da nagarta.
Sunkai tsawon minti18 ahaka sanan yazare bakinsa, idonsa yayi jajur, yarungumeta tsam yana hawayen farinciki, itama kukan take danji take zuciyarsa nafaman bugawa da k'arfi, hannu tasaka saitin zuciyar tasa ta danne wai ko zata dainajin bugun.
Ahankali yad'agota yana murmushi, tacire hannunta daga k'irjinsa, yakama hannun nata yamaida ak'irjinsa, karki cire my life, kusantowarki gareni yasa zuciyata ta canja salon bugu ayau, jinake tamkar zata Faso k'irjina tafito, inasonki dayawa my life, bazan iya yafema wad'anda suka rabamuba har tsawon shera hud'u da Rabi, dolene su fuskanci hukunci da horo mai tsanani........ Lallausan hannunta tasaka tarufe masa baki, tayunk'ura ahankali ta tashi zaune sosai akan cinyarsa.
Share masa hawayen tashiga yi yayinda itama idonta kezubar hawayen, tanason Dr Isma'il sosai, shiyyasa bazata iya jure ganin saukar hawayensaba, shikam aii saiya k'ame k'am, Ashe har yanzu iman d'insa tana sonsa?.
Muryarta cike da taushi ta ce, "karka damu _Zuciyata_ muyarda da k'addara bana son zubar hawayenka, kad'auka mukeda nasara tunda gani nadawo gareka, iman takace kai kad'ai, kuma zan cigaba da kasancewa taka har a aljanna insha ALLHU RABBI.
wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke ahankali, yakuma rungume iman tareda nuna mata wani sabon salon soyayya na musamman mai tsadar gsk, _(nidai bilyn Abdul kauda idona nayi gefe Dan lamarin yagirmi wayona),_ humm. So makahone.
Ganin zai wuce gaba yasata rik'e hannunsa, duk jikinta yayi sanyi lakwas, ya tsura mata rinannun idanunsa wad'anda suka k'ank'ance, muryarsa a sark'e ya ce, " tashi muyi sallar godiya ga ubangijin talikai.
Tsorone yashigi iman data tuno da Daren farkonsu, tasha wahala, nantake kanta yakawo mata haske, tayi k'asa da ido tana k'arema k'irjinsa kallo, muryarta dad'an rawa ta ce, "nifa ina danja.
Ban gane kina danja ba?.
Cusa kanta tayi a k'irjinsa cike da kunyar abinda zata fad'a, muryarta can k'asa ta ce, " ina fashin sallah.
Shiru yayi na 'yan sakwanni, lallai danja kam, gsky kika fad'a Dan an6ata masa show daya dad'e yana shiryawa.😜
Jin yayi shiru yasa tad'an d'ago dantaga lfy, murmushi yasakar mata, Wanda takeda tabbacin iyakarsa fuska, ta maida kanta tana gumtse dariya, Dan yabata dariya wlhy, ta ce, "yanaji kayi shiru?.
Manneta yayi sosai da jikinsa, acikin kunnenta yarad'a mata wani abu, Wanda Nima banjiba.
K'ara cusa kanta tayi tana wata irin dariya maicike da amo.
Shikam saita k'ara narkar dashi, gudun kar ayi abin kunya yasashi d'agota, my life dariya kikemin ko??, hummm zan ramane aii, tashi kici abinci.
Tashi tayi zaune tana kauda kai, nifa ba dariya nake makaba, humm to mikikeyi?, babu komai.
Shikenan zamu had'une aii.
Dakansa yabata naman gasashshiyar kaza mai dad'i, sukaci suka k'oshi suka d'ora da sassanyar fresh milk.
Koda zata saka kayan barci saita shige bayi, murmushi kawai yayi, yaja filo yarungume.
Can k'arshen gado ta lalla6a ta kwanta, azatonta yayi barci, batasan yana kallontaba yayi shirune kawai.
Saida takwanta tayi addu'a, sanan yajuyo had'e da rungumota yana fad'in 'yammata aii tuni an wuce wanan k'arnin kokin mantane.
Shiru tayi batace komaiba Dan kunya.
Dukda baisamu abinda yake k'ulafucinba tasha jagwalgwala sosai, dan saida ta gwammace dama batayi masa k'aryarba, sai wajen k'arfe 2 yabarsu suka runtsa.


Da asuba yatashi dak'yar yashiga bayinta, saida yayi wankan sanan yay alwala, bai tada iman ba dan yasan bata sallah, d'akinsa yanufa yasaka jallabiya yanufi masallaci.
Iman kuwa yana fita tabud'e ido, gwalo tamasa sanan tasakko daga gadon tashiga bayi, alwala tayi tazo tayi sallar asubahi, tamaida kayan barcinta ta haye gadon kamar komai bai faruba.
Saida gari yafara haske suka dawo daga masallaci shida marwan da Yaya, kowa 6angarensa yanufa.
Sanda yashigo d'akin iman takoma barci Dan bai barsu sunyi barci ishashsheba da daddare.
Kwantawa yayi shima tareda rungumeta sai barci.

*_7:48am_* iman ta farka, ahankali ta zare jikinta daga NASa gudun karya tashi ta saka masa filo, falo tafito, dukda babu wani datti mai yawa saida ta k'ara gywarashi, tabaza k'amshi, d'akinsa tashiga, tabi ko ina da kallo, ancanja komai bawanda tasani bane, tagywara d'akin tabaza k'amshi nanma, anan tayi wanka tad'anyi kwalliya sanan tanufi d'akinta.
Ahankali take komai dankar ta tadashi, tasaka kaya dasuka kara fidda tsarin halittarta, siket ne da Riga na atanfa, kai telan nan ya iya fidda d'inki gsky, ta nad'a d'aurin d'ankwali mai tsari sanan tafeshe lungu da sak'o najikinta da turare.
Ahankali Dr Isma'il yabud'e ido yana kallonta, tunsanda take d'aurin d'ankwali yake kallonta, tajuyo danufin fita saitaga idon doctor akanta, lallausan murmushi tasaki tana fad'in dama katashi?.
Baiyi maganaba saidai ya mik'o mata hannunsa alamar yanason tashi, matsawa tayi gaban gadon ta kama hannunnasa, ahankali yatashi zaune har yanzu idonsa akanta.
Ita kallon nasama kunya yake bata, ta daure ta ce, "kallonnanfa ya Isa haka.
Kamo hannunta yayi yazaunar saman cinyarsa, akunnenta yay magana wadda tasakata saurin saka tafin hannunta ta rufe fuska, da sauri tamik'e daga jikinsa ta gudu........ Yakatseta dafad'in ni wazaimin wankan?, ashagwa6e yay maganar.
Da d'an gudunta ta ida fita daga d'akin, yay 'yar dariya, my life sarkin kunya, mik'ewa yayi yashiga bayinta, tawanke bayin tsaf sai k'amshin dad'i yake, ga ruwan wanka anhad'a Wanda yakeda tabbacin nasane.
Wankan yafarayi zuciyarsa cike da tunanin iman, gabad'aya yarinyar ta canja masa, komai nata yak'ara girma musamman ma k'irjinta, duk motsin datayi saita kuma rikitashi, yakuma nutsa kansa cikin ruwan yana murmushi.

Iman tana fita sukaci karo da Raihan tafito sanye da kayan barci, da alama yanzu ta tashi, har iman tayi niyyar wuceta saikuma tadawo baya tana murmushi.
Taje gaban Raihan ta tsaya fuskarta fes, ta ce, " Raihan kin tashi lfy?.
Wani k'ududun bak'in ciki yatokare zuciyar Raihan amma saita dake, itama ta CE, "lfy lau. Ashe kin dawo?.
Iman tayi murmushi danjin tambayar rainin wayo daga Raihan, tad'an dafa kafar Raihan tana cigaba da murmushi, nadawo Raihan cikin huncin ALLAH, mammallakin zuciya da abinda ta sak'a, tad'aga mata gira, ina fata kema bazaki tafiba zaki zauna murayu tare, harmu haifo k'annan misayeef k'yautar ALLAH...... Tana gama fad'a tayi gaba tana wata irin dariyar rainin hankali, saida taje dai dai k'ofar shiga d'akin doctor sanan tajuyo, cikin wani salo ta ce, *_" BAN SAKETA BA!."_* tadafe saitin zuciyarta sannan tayima Raihan jinjina da hannunta d'aya👍🏻😉tad'an gira sannan tashige.
Sagade Raihan tayi tanabin iman da kallon harta shige d'akin Dr, zuciyarta cike da d'aci, wai waccan 'yar yarinyarce take gaya mata bak'ar magana a fakaice?.
Hummmm iman kikira kanki sorry kawai, fuuuuuu tashige d'aki, tafasa kuka tareda fad'awa kan gadonta daya had'a kwana uku babu gyara.

Iman kam tana d'akkoma Dr kaya tana faman murmushi kamar wadda akayima albishir da aljanna, k'anan kaya ta d'akko masa masu k'yau, tafeshesu da turare sanan fito.
Tayi murmushi Dan ganin babu Raihan, tayi zaton zata fito ta isketa aii.
Dakinta tawuce, agurguje tagyara ko'ina tabud'e d'akin da k'amshi, sanan tadawo falo ta zauna.
Fitarta babu dad'ewa Dr tafito, yabi d'akin da kallo yana mai jin dad'i, iman akwai tsafta, amma awannan karon tazo masa da sabon salon k'amshi na musamman.
Tsaf yashirya tamkar wani matashin saurayi, babu Wanda zaiga Dr ya ce, "iayi aure harda d'a, falon yanufo shima.
Musaueef yashigo falon da d'an gudunsa, cak yatsaya yana kallon iman, fuskarsa d'auke da mamaki, tayi masa murmushi tareda bud'e hannayanta alamar yazo.
Zuwa yayi yashige jikinta yana 'yar dariya, aunty maa yaushe kikazo?.
Bata bashi amsaba sai faman murmushi take zabgawa na jin dad'in ganinsa, ta ce, " I miss u my derling.
Dr Isma'il yana tsaye yana kallonsu fuskarsa d'auke da murmushi.
Iman tashare 'yan kwallan dasuka taru mata agefen ido najin dad'i, tad'ago Musayeef daga jikinta ta sumbaci kumatunsa sanan tamik'a masa nata, shima sumbatarta yayi.
Sai asanan yaga dadinsa, dagudu yasaki iman yanufi Dr dake tsaye.
Dr yatsugunna tareda ware hannunsa musayeef yazo yashige.
" daddyna!."
"Musayeef d'ina!."
Shima yafad'a cike da jin dad'i.
Yad'agosa yana dariya, katashi lafiya?, lfy lau daddyna, da k'yau na gwaggo.
Musayeef ya ce, daddy!.
Ma'am, Dr Isma'il ya amsa.
Daddy itama aunty maa tadawo gidanmu.
Saida ya kalli iman suka had'a ido tayi k'asa da kanta tana murmushi, sanan yadawo da dubansa kan musayeef, kai ya d'aga masa tareda lumshe ido yana murmushi.
Yeeeeeeee musayeef yashiga fad'i yana tsallen Murna, Dr da iman kallonsa suke sunata dariyar jin dad'in ganin farincikin tilon d'ansu.
Raihan dataji ihun Musayeef tafito tawani doka uban tsaki tashige cikin, babu Wanda ya kulata danshi Dr ko kalloma tata isheshiba, da ita da babu duk d'ayane agurinsa.
Mik'ewa yayi yad'auki musayeef suka k'arasa Inda iman take zaune, zama yayi Kusada ita yad'ora musayeef kan cinyarsa.
Kinga yanda musayeef yake farinciki momynsa tadawo ga daddynsa.
Murmushi iman tayi batareda ta ce, komaiba.
Musayeef ya ce, "aunty maa ina uncle deeni da gwaggo da abbah.
'Yar harara tamasa ta ce, "sai yanzu katuna dasu?.
Musayeef ya kalli daddynsa, daddy aii dai Kaine kace zaka kaini ko?.
Kai yad'aga masa ya ce, " insha ALLAHU big boy. Dariya sosai musayeef yakeyi wadda tasaka iyayen NASA dariya suma.
Iman tamik'e kunga bazan iya wannan shiritarba bari naje na gaida mama dasu Yaya.
Shima Dr mik'ewa yayi d'auke da musayeef muma Baza a barmu abaya ba aii, muje muyi breakfast ma.
Haka suka rankaya abin sha'awa kamar kasacesu ka gudu, sunsan su yayama suna 6angaren mama, Dan haka suka nufi can kai tsaye, ilai kuwa suna can.
Sunbama su mama sha'awa, marwan ya ce, "family ya had'u dee.... CE kawai babu, dariya akayi harda su Dr dake shigiwa.
*_(Ni bilyn Abdul na ce, " tofa, mi marwan yake nufi, bayan babu aunty da Raihan agurin, naga suma duk suna cikin family🙊😜)_*.

Gaisuwa aka shigayi, kowa saiji da imam yake, itakam kunyarsuma takeji, ta ce, "marwan yaushe dee...... Zata zo?.
Aina San weekend d'innan saitazo, dan taji haushi kin dawo bata nan, murmushi iman tayi ta ce, ALLAH yakaimu lfy.
Ya CE Ameen.
Sun dad'e anan anashan hira, sannan suka koma 6angarensu.
Suna zama wayar iman tahau wringing, takalli wayar.
My sweet hafsy tagani, tasaki murmushi tareda d'agawa...................



*_" kuyi hak'uri idan nadad'e INA typing wayar k'amewa takeyi"_*





*luv u oll my fan's*
*(((S)))...............2017*
[8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*






*_NA Bilyn Abdul_*





_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com



*miya kamata nayi?*
_6arna NATA yawa a bayan k'asa, amma anrasa miye tushenta?._
_hummm akwai tushe tushema ba tusheba, misali idan na d'auki yanda al'ummarmu suka maida zina a yanzu._
_zakiga uba mai cike da kamala ariga da fuska, amma idan yaje office shida sakatariyarsa saidai addu'a, zai makad'awa matarsa k'arya yatafi k'asar waje kasuwanci amma yana hotel da 'yammata, k'ilama harda k'awar 'yarsa, ko k'awar matarsa, ko k'awar k'anwarsa._
_to jama'a Dan ALLAH, indai maganarnan da ake fad'in Wanda yayi zina da uwar wani sai anyi da tasa mizai hana matar magidancinnan fad'awa tarkon zina, tunda k'ila harda matar wani yakeyi, mizai hana 'ya'yan magidancinnan fad'awa zina, tunda yayi da 'yar wani, mizai hana k'anwar magidancinnan fad'awa zina, tunda yayi da k'anwar wani, mizai hana yayar magidancinnan fad'awa zina tunda yayi da yayar wani._
_kunga tadalilin mutum d'aya mutane dayawa sun fad'a tarkon 6arna, shikad'ai ya wargaza family d'insu, Dan abin zaita bibiyarsune har 'ya'ya da jikoki._
_wa'iya zubillah, Dan ALLAH magidanta

Please Login or Register in order to submit comment