Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna ganin irin wannan tashin hankali.. Umma abin yayi yawa.. This has to end Umma.. Ni kad’ai ce ya kamata nayi abinda ya dace.. Umma ki sanar da Malam Liman ni Sadiya na amince ya aurar dani ga Alhaji Isyaku... Zan rabu da Sabeera rabuwa Ta har abada.. Bazan k’ara kallon cikin idonta ba.. Watak’ila Wannan shine hukuncina a rayuwa.. Hukuncin abubuwan da nayi ma Abba a lokacin da yake raye.” Ta k’arashe cikin tsananin kuka... Umma ta rungumeta su duka biyun suna masu fashewa da wani irin kuka mai tab’a zuciya.
**

Koda labari ya iski Alhaji Isyaku cewa Sadiya da mahaifiyarta sun amince da batun auren Zo kaga Farin ciki wajensa, jinsa yake sabon ango.. Lallai tarkonsa ta d’anu ko banza zai mallaki wannan kyakkyawan yarinyar da ya jima yana kwad’ayin kasancewa da Ita.. Bayan isha ya shirya tsaf yasha wankansa ya fesa kwalliya da babbar riga ya nufo gidansu Sadiya.

Da k’yar Umma ta shawo kanta tace taje su gaba taji da mai yazo.
Haka badon taso ba ta zira hijab d’inta ta fito.

Yana ganinta fari’arsa ya k’aru “Assalamu alaki kyakkyawa ma’abociya annuri..” Ya fad’i yana mai k’arasowa.
Sanin darajan sallama yasata ta amsa ciki ciki kanta na duk’e k’asa.. Ta soma k’ok’arin duk’awa da niyyan gaishesa.

“A’a tashi tashi kayanki.. Haba ai saidai ni na duk’a miki Gimbiyata.”

Takaici ya turnuk’eta, ta rintse idanunta a hankali tanajin zuciyarta na mata zafi.

“Ki saki jikinki. Kuma ki saka a ranki cewa ni masoyinki ne..”

“Masoyi kuma Baba..? Kodai b’atan kai kayi ne.? Ni ce fah Sadiya k’awar Sabeera wacce ka datse alak’armu da Sabeera sabida banida kamun kai.. Ko ka mance ne..?”

Murmushin da yafi kama da yak’e yai kana yace “Yaro dai yaro ne. Toh banda abinki Sadiya ai ba komai yasa bani k’aunar alak’arku da Sabeera ba Sai dan bana so ku shak’u ku samu kusanci da juna gudun kar randa duk nazo miki da wannan batu nawa da ya jima a birnin zuciyata kice bazaki iya ba sabida k’awance da d’iyata da kuke.. Idan kika cire wanann ni babu wani abinda zaisa na rabaki da Sabeera.. Ki yarda dani Sadiya, ni wllhi ba sabida komai na rabaku da Sabeera ba sai dan kar ta zamto mana cikas a tsakaninmu.. Banaso ta zamto shamak’i ma soyayya ta dake..” Ya d’an nusa yana mai gyara zaman babbar rigarsa “Wato Sadiya na jima Ina k’aunarki saidai bansan Ta yanda zan tunk’areki da wannan batu ba har sai zuwa wannan lokaci..”

Sadiya dake dubansa cikeda tsananin mamaki, dan itakam kunya ma take ji masa, murmusawa tai tace “Sai wannan lokacin ka sami dama. Lokacin da banida wani zab’i da ya wuce na amince da buk’atarka koda ace bana so. Shin ko ba haka bane Baba.?”

Saurin katseta yai da fad’in “Ko d’aya.. Ba haka bane.. Kuma dan Allah ki daina kirana Baba, mud’in zamu kasance k’ark’ashin inuwar ma’aurata ne, matata zaki zamto nan da kwanaki biyu rak, dan ni asabar d’in nan mai zuwa nake so a d’aura Kinga yau Alhamis ne already..”

A zabure ta d’ago tana dubansa “Asabar mai zuwa fah kace.!”

“K’warai kuwa Amaryata, rashin jan lokacin yafi a’ala, shi dama jan lokaci a aure Baida wani alfanu..”

“Ka sani auren nan da zanyi sadaukarwa ne ga ahalina amma ba don inaso ba.” Ta fad’i idanunta na raurau.

Murmusawa yai yana mai kuma gyara tsayuwarsa “K’warai kuwa nasan da hakan, kuma ina mai tabbatar miki da sannu zaki soni ki k’aunace ni.. Idan har da gaske auren sadaukarwa zakiyi toh kuwa ya kamata ki amince ayi auren nan as soon as possible.. The earlier the better. Sabida ahalinki zasu huta da tashin hankalin Tabawa harma da Malam Aminu.. Bai kamata ayi Jinkiri ba a situation d’in da ahalinki ke ciki.. Bugu da k’ari Nifa d’aukeku zanyi Cak daga garin nan dan ku mance komai ku mance duk wasu tashin hankali da kuka fuskanta cikinta.. Amma ke ya kika gani..? Ki tuna you are doing this for your family.” Ya k’arashe yana mai zuba mata idanu.

Hawayen da take rik’ewa ne suka soma gangaro mata. Ta shiga jinjina kai tana furta “Yes.. Yes I’m doing this for my family.. For the sake of my Family... Zan sadaukar da komai nawa ciki harda Farin cikina sabida Su.. Sabida ni ce duk na ja masu halinda suka tsinci kansu ciki..” Kuka ya hanata ci gaba da magana.

Juyawa yai yana sakin murmushin cin nasara kafin ya maidoda dubansa gareta “C’mon Baby ki daina kukan nan haka, wllhi har cikin zuciyata nake jin zafin zuban hawayenki.. I promise you kukan ki ya k’are Baby.. Da zaran kin auren zan mantar dake komai.. Zan baki irin rayuwar da kika jima kina mafarkin samu... I’ll spoil you and pamper you kinji Baby na..”

Jin kalaman nasa take kaman Ana hura mata wuta cikin kunnuwarta, babu kunya babu tsoron Allah Wai Baban Sabeera ke jero mata wad’annan kalamai hardasu kiranta Baby.. Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana girgiza kai tace “Wancan rayuwar mafarkin Sadiya ce a baya.. A halin yanzu babu abinda nake so face peaceful world for my family. I want my family to have peace.. Iyakacin abinda nake so yanzu shine peace.. Zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ahalina.. Mafarkina da buruka na sun jima da mutuwa.. An birnesu tareda mahaifina.. Kuma ina neman wani alfarma a wajenka.”

Ya jinjina kai yace “Kin wuce neman alfarma Gimbiyata, abinda kike so kawai zaki fad’a ayi.”

Sadiya tace “Kar ka biya Tabawa har sai randa akazo d’aura aurenmu domin akwai rayuwa akwai mutuwa bamu San mai zai faru kafin ranan ba..”

Ya murmusa yace “Idan dan wannan ne banida matsala. Yanda kikace haka za’ayi Amaryata.. Wllhi na k’agu ki zamto tawa..”

Katsesa tai da fad’in “Ni zan shige gida..”

“A’a tsaya mana..” Yai maganar yana zaro kud’ad’e cikin aljihunsa.

Saurin girgiza kai Sadiya tai tace “Bazan karb’i komai daga hannunka ba.. Na gode..” Bata tsaya sauraron sa ba tasa kai ta shige cikin gida.

Yabi bayanta da kallo zuciyarsa fari k’al, kad’a Kai yai yace a fili “Bari dai naita lallab’a ki har ki shigo...” Yana ida fad’in haka ya gyad’a Kai yana mai kuma Washe baki ya shige.

**

Washe gari sassafe Tabawa tai kiran Asabe mai kayan Koli.

Tabawa ta k’irgo kud’ad’e cikin wanda Alhaji Isyaku ya bata, Ta mik’awa Asabe Mai kayan Koli tace “Kina jina dik abinda na sanar dake haka zaki sanar da matarsa.. Asabe koda wasa kar ki ce ni na sanar dake..”

Asabe Ta jinjina kai tana tura kud’in cikin posar ta. “Haba Hajiya Tabai, indai dan wannan ne ai bakida matsala, da Asabe fah kike zancen..”

Tabawa ta murmusa cikeda jin dad’i tace “Yauwa tawan.. Idan har hak’ata ta cimma ruwa zan k’ara miki wani abu..” Asabe Ta Washe baki cikeda farin ciki.. Tuni ta aza kayanta na Koli aka ta nufi layin gidan Alhaji Isyaku.

Tabawa tabi bayanta da kallo zuciyarta fari k’al. A fili take furta “Alhaji Isyaku kenan ai wllhi bazan bari ka auri yarinyar nan ba, auren nan saidai ayi dani Koda zaka biya masu bashin amma bakada mata sai ni Tabawa. Zan d’aga masu hankali dan ka biya masu bashi sannan zan sa matarka da d’iyarka su d’aga masu hankali suk’i amincewa da buk’atarka bayan ka biya masu bashin..” Tana ida fad’in haka ta bushe da muguwar dariya kafin ta shige gida.

**
Maman Sabeera na zaune parlor tana kallon shirin good morning Nigeria da ake nunawa da sanyin safiya a tashar NTA Asabe mai kayan Koli tai sallama.

Iyatu mai masu aikatau ce ta amsa mata sallamar tace ta jira ta shiga ta tambayi Hajiya idan zata sayi wani abin.

Asabe tace “Dakata ba saye da sayarwa ya kawoni na ba.. Alhaji na gida Ko ya fice..?”

Iyatu tai jim kafin tace “Ai Jiya Alhaji bai dawo gida ba inaga wajen aiki ya kwana..”

Asabe ta zaro ido waje tace “Bai kwana gida ba..? Ikon Allah Toh ki shiga kice mata magana nazo mata dashi mahimmiya kan maigidanta.”

Iyatu ta dubeta da mamaki amma sai ta jinjina kai tace “Shikenan.” Lokaci guda ta shige ta nufo parlor ta tadda Maman Sabeera ta sanar da ita abinda Asabe mai Kayan Koli ta fad’a mata.

Mamaki ya cika Maman Sabeera jin Wai magana Asabe tazo mata dashi kan mijinta. Ta nusa tana tinani kafin taceda Iyatu “Kice mata Ta shigo.”

Iyatu ta jinjina kai kafin ta fice yin iso ma Asabe.

Jim kad’an Asabe ta shigo d’aikeda kayan Kolinta, ta nemi waje daga k’asa ta zauna tana gaida Maman Sabeera.

Maman Sabeera Ta dubeta da mamaki tace “Asabe kikace yau ba talla kikazo ba.. Toh wani magana ne ya kawo ki kan maigidana.?”

Asabe Ta d’an Tab’e baki tana ‘yan waige waige tace “Hmm ai Hajiya abinda nazo dashi yau yafi k’arfin talla.. Amma Hajiya jiya Kinsan yanda mijinki ya kwana..?”

Da tsananin mamaki Maman Sabeera ke dubanta ganin basu saba irin wannan batu ba, iyakaci ta shigo da kayan kolinta ta tallata ta fice. Amma yau Asabe tazo mata da batu mai girma.
Girgiza kai kad’an Maman Sabeera tai “Ban.. Fahimceki ba Asabe.. Mai kike nufi..?”

Asabe ta kuma gyara zama tana duban Maman Sabeera “Hajiya wllhi wllhi abinda zan fad’a miki Sai ya firgitaki.. Idan dai har bakisan yanda mijinki ya kwana jiya ba kuma bakisan da wa ya kwana ba ni zan sanar dake dan na sani..”

Zuciyar Maman Sabeera yaci gaba da bugawa cikin sauri, mijinta ya saba kwana cikin Abuja idan dare ya masa sabida tsananin holdup da cinkoson Abuja yakan sa wataran ya kwana ga yanda k’asar Ta koma babu tsaro, wataran yakan ce aiki ya rik’esa zai kwana cikin Abuja da safe ya dawo. Amma koda wasa bata tab’a saka ma ranta cewa mijinta na ha’intarta ba tuni ta kyautata masa zato tinda ma kafin ya kwana cikin Abujan Sai ya kirata ya sanar da Ita cewa zai kwana aiki ya rik’esa gudun Karma zargi ko abu mai kama da haka ya shiga tsakaninsu. Cikin rashin yarda da batun Asabe Ta mik’e tana nuna ma Asabe k’ofa “Kinga Asabe tashi kawai ki fice.. Kafin ranmu gaba d’aya ya b’aci.. Tashi ki fice min a gida ni bana shiga gulma da gutsiri tsomen unguwar nan.. Tashi ki fice min a gida kuma kar ki sake dawowa idan da irin batun nan zaki Zo..”

Asabe Ta murmusa tace “Hajiya wllhi Allah na rantse miki da Allah daren jiya mijinki na unguwar nan kuma nasan da wa yake tare.. Ni ganau ce ba jiyau ba, na gansa da yarinyar nan Sadiya kuma yau kusan kwanaki uku kenan yana zarya k’ofar gidansu.. Ina mai tabbatar miki d’aukanta yayi suka fice suka kwana tare.. Ai dai Kinsan wacece Sadiya a unguwar nan Sadiya Sady Pretty da tai k’aurin suna wajen rab’an maza masu abin duniya.. Toh ta fad’o kan mijinki zata k’wak’wale abin hannunsa.. Dan wllhi jiya tare na gansu kaman zai mata sijadda dan biyayya..”

Bibbiyu Maman Sabeera ta soma gani, hazo hazo da wani irin duhuwa ne suka gifta k’wayar idanunta. A yayinda Sabeera da fitowarta kenan daga kitchen rik’eda mug dik taji tattaunawarsu a kunnuwanta.. Wani irin k’ara ta saki had’ida sake mug d’in dake hannunta ya watse saman tiles..



SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*18*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*









Da kuka Sabeera ta k’araso gabansu tana fad’in “A’a badai Babana ba.. Badai k’awata Sadiya ba.. Mama kar ki yarda da maganar wannan matar I’m sure k’arya take.. Ki tashi.. Tashi ki fice mana daga gida..!” Tai maganar tana k’ok’arin finciko Asabe dake duk’e wajen ta zuba masu ta mujiya.

Maman Sabeera kam tama kasa tantance abinda ke faruwa. Kaman daga wani duniyar take sinkayo kukan Sabeera da maganganunta.

Asabe ta mik’e tana fad’in “Idan k’arya nake maku ku tare mutanen lungunsu ku tambayesu ko kuma kuje da kanku dan ance zuwa dakai yafi sak’o. Nidai na gama nawa tinda sanar daku.. Ya rage naku ku yarda ko kar ku yarda. Allah bamu alheri.” Tana ida fad’in haka ta mik’e ta aza bahon kayan Kolinta aka Ta nufo waje, tuni Ta cika ma rigarta iska aka bar Sabeera da Mamanta babu mai iya ba ma wani hak’uri. Cikin muryar kuka Sabeera ke duban mahaifiyarta tana fad’in “Mama k’arya take kar ki yarda da ita.. Wllhi nayi imani Sadiya bazata tab’a aikata haka ba.. Nasan Sadiya nasan halinta wllhi sharri ne kawai irinta mutanen unguwar nan.. Mama dan Allah Kema kice min baki yarda ba..!”

Maman Sabeera bata iya furta koda kalma ba sai hawaye dake zarya saman k’uncinta. Cikin sauri ta mik’e ta nufi d’aki tana jin kukan da gaske na zuwa mata. Sabeera tabi bayanta da sauri tana kiranta amma inaa bata ko tsaya ba balle ta saurari Sabeera ta shige d’aki kayanta.
Silalewa Sabeera tai a wajen kukanta na k’aruwa itama. Hiran wasu course mates d’insu take tinawa data sinkaya wataran a makaranta cewa akasari ba duka ba iyaye da suka faye tak’ura da tsanani ka bincika ta yuyu shima watsewarsa yake da yaran wasu baiso ayi da nasa shiyasa yake masu mugun tsanani. Tai saurin toshe kunnuwanta tana girgiza kai dan bata so ta amince da hakan.. Wani tinanin ne ya kuma d’arsuwa mata a zuciya.. Ita kad’ai ta aminta da Sadiya, itace bata mata kallon da sauran mutane suke mata a unguwar.. Ta yarda da ita d’ari bisa d’ari sannan ta saka ma ranta cewa Sadiya ba mutuniyar banza bace but Maiyasa yanzu take jin shakku akan hakan.. Kardai da gaske Sadiya cin amanarta take.. Take taji zuciyarta na wani irin bugawa, gwara taji labarin mahaifinta na neman wata daban badai Sadiya k’awarta data d’auki yarda ta d’aura mata ba.. Waima tsaya mahaifinta ya mata iyaka da Sadiya ta ya za’a ce su biyu d’in suna tare.. Cikin sauri ta shiga girgiza kai tana furta “No.. no .. no I can’t take this anymore.. I need to find out myself..” Tana ida fad’in haka Ta mik’e Ta nufi nata d’akin dan shiryawa.

Cikin kuka Maman Sabeera ta kirawo k’awarta Ramatu a waya tana sanar da ita tashin hankalin da suka wayi gari dashi, a fujajan Ramatu tace gata tafe maganar yafi k’arfin ayita a waya dan dama basuda nisa unguwar tasu.

Sabeera kaw tuni ta fice dikda mahaifinta ya mata iyaka da waje balle gidansu Sadiya tin bayan abinda ya faru. Ta’aziyan mahaifinsu ne kawai Mamanta Ta mata cover suka tafi tare. Tafiya Sabeera take a layin tana jin zuciyarta na mata wani irin d’aci, babu addu’an da take cikin zuciyarta face Allah yasa duk abubuwan nan da taji k’arya ne babu gaskiya ko guda a ciki.. Bata jin zuciyarta zata iya d’aukan cin amana daga babban aminiyarta irin Sadiya wacce ta d’auki yarda da komai ta d’aura mata. Tana tafe tana tinanin tazo wuce shagon Maman Emeka ai kuwa saiga wasu ‘yanmata ‘yan unguwar a k’ofar Kantin sun Sai bredi da dangin abin kari kumallo.. D’ayar ta tab’a d’ayar tana nuna mata Sabeera dake had’a hanya zata nufi lungun gidansu Sadiya.

Cikin azama suka nufo Sabeera suna kiran sunanta, taja Ta tsaya tana dubansu da idanunta da tuni sun kod’e sunyi ja dan kuka..

“Laa Sabeera ina kika nufa..? Kardai gidansu Sady Pretty..” Ta d’an tab’e baki kad’an yace “Ai kuwa ko Jiya naga Babanki k’ofar gidan yana zance kuma kaman Sady Pretty na gani..”

D’ayan ta cab’i zancen da fad’in “Ni da naga motar Babanta bakin lungun ma nayi zaton Sabeerar ce ashe ashe dai Baba ne..”

Cikin tsananin huci Sabeera ke dubansu, ta kasa magana sai dubansu da idanu da take.. ‘Yanmatan suka dubi juna kafin d’ayar ta tab’e baki ta janyo hannun ‘yaruwar tata tana fad’in “Kinga k’awata Zo muje.. Allah dai ya kyauta k’awancen cin amana..”

Tamkar wacce aka dasa dutse haka Sabeera ta tsaya a wajen.. Shikenan dai Wato ta tabbata da gaske Mahaifinta saurayin Sadiya ne.. Kuma ko da wasa bata tab’a hasasho hakan ba, bata tab’a tunanin hakan ka iya kasancewa ba.. Da k’yar take d’aga k’afafunta tana ganin hanya na rabe mata bibbiyu.. A haka Ta k’araso gidansu Sadiya.

Sadiya da Umma na zaune tsakar gidan tana duba k’afar Umma da har yanzu yake d’an mata ciwo, tamkar wacce aka jefota haka sukaga Sabeera akansu..

Zuciyar Sadiya yai wani irin tsinkewa yayinda Sabeeran ta zuba mata idanu.

Umma ce tai k’arfin halin cewa “A’a Sabeera kece tafe.. Sannu da zuwa.. K’araso ki zauna.”

Ko gizau Sabeera batai ba saima duban Sadiya da take. Umma ta dubi Sadiya ta kuma dubi Sabeeran da irin kallon da take ma Sadiya. Kafin Umma tai wani aune Sabeera ta k’araso ta duk’a yanda Sadiya ke duk’e suna fuskantar juna saidai kan Sadiyar a k’asa yake.

“Ki fad’a mun gaskiya da bakinki.. Shin da gaske ne..? Sadiya da gaske ne abinda nake ji tsakaninki da mahaifina..?!”

Izuwa lokacin hawaye sun soma ambaliya saman fuskar Sadiya, ta kasa d’agowa ta dubi Sabeera sai hawaye dake zarya saman fuskarta.

Cikin zuban hawaye da tsananin d’aga murya Sabeeran ke ci gaba da fad’in “Talk to me Sadiya.. Tell me the truth.! Ki fad’a mun gaskiya.. Wacece ke a wajen mahaifina..! Ki fad’a mun Sadiya..!!” Ta k’arashe tana damk’o kafad’un Sadiya tana mai jijjigata da iya k’arfinta hawaye na ambaliya saman fuskarta a yayinda kukan Sadiyar ma ya k’aru.

Umma dake gefe ta kasa tab’uka komai sai hawayen da itama taji suna zubo mata.

Cikin muryar kuka ba tareda ta d’ago ta dubi Sabeeran ba take furta “I’m sorry.. I’m sorry Sabeera.. Please forgive me.. Dan Allah ki yafe mun..!”

Take jikin Sabeera ya sake gaba d’aya.. Maiyasa Sadiya take bata hak’uri.. Kenan da gaske ne.. Kenan maganganun da mutane suke fad’i gaskiya ne.. Sadiya da mahaifinta... Ji tai Ta kasa k’arasa tunanin sabida wani irin jiwa dataji na neman kaita k’asa. Take taji wani irin k’arfi yazo mata.. Ta hankad’a Sadiyar da k’arfin gaske Wanda saida ya kaita k’asa.. Sadiya ta buga kanta had’ida gwiwan hannunta da tuni ya karje ya soma jini.. Babu shiri Umma ta mik’e da k’yar dikda k’afarta dake mata ciwo Ta nufi kan d’iyarta.

Sabeera ta kuma yowa kan Sadiyar tana kuka sosai take fad’in “Sai na kasheki kafin ki zama matar Babana..!” Tayo kanta tana k’ok’arin fuzgota saidai tuni Umma ta raba tsakaninsu ta tallafi Sadiyar dake kuka sosai tana duban Sabeera dake k’ok’arin funcikota..

Cikin kuka Sabeera ke furta “I trusted you.. I believed in you.. I never doubted you.. I never judged you.. Duk abinda mutane zasu fad’i akanki Sadiya dai dai da rana guda ban tab’a yarda ba.. Ashe duk ba haka bane.. Ashe ked’in da gaske macijiyace mai bak’in guba.. Ta yaya zaki min haka.. Ta yaya zaki aminiyar data aminta dake irin haka Sadiya..!” Ta kuma yowa kanta tana kuma janyota tana fad’in sai tayi ajalinta.

Daidai lokacin Baban Sabeera ya shigo da shopping bags hannunsa, nan ya tadda wannan hargitsi dake tashi cikin gidansu Sadiyar.

Da tsananin mamaki yake duban Sabeera dake k’ok’arin kaima Sadiya duka Umma na tarewa.

“Ke Sabeeraa.!!” Ya fad’i cikin daka tsawa yana mai fuzgo Sabeeran had’ida d’aura mata mari maiji da lafiya..

Sabeera ta tsaya Cak tana duban mahaifin nata cikeda tsananin mamaki hannunta guda dafe da k’uncinta.

Sadiya kaw tuni ta rungume mahaifiyarta tana kuka sosai..

“Dan gidanku ashe bakida hankali.. Ashe ke shashasha ce ban Sani ba.. Uban wa ma ya baki izinin fitowa daga gida.. Matar nawa zaki daka dan bakida kunya bakida hankali Ko..!”

Baki sake kurum Sabeera ke duban mahaifinta da kalaman da yake, tana ganin kaman mafarki take ba gaskiya bane.. Tanada tabbacin ba don zafin sauk’ar marin dataji a k’uncinta ba zata iya cewa mafarki take ba gaskiya bane..

A guje Sadiya dake tsananin kuka ta shige parlor yayinda Baban Sabeera yai yunk’urin bin bayanta yana fad’in “Baby.. Baby kiyi hak’uri dan Allah I’ll deal with her myself..”

Cikin hawaye Umma Ta katsesa da fad’in “Ya isa dan Allah..!” Tai saurin bin bayan Sadiya tana ambato sunata ga k’annenta da tuni sun fito suna kallon abinda ke faruwa.

Baban Sabeera kaw hannunta ya damk’o yana fad’in “Shige muje ki sanar dani ubanda ya koya miki rashin kunya..”

Haka ‘yan lungun sukaita lek’e wasu na k’us k’us d’in an fara dan kaf lungun gidansu Sadiya ne bai rabuwa da hatsaniya da tashin hankali.. Daga wannan sai wancan..

Sadiya kam kulle kanta tai a d’aki tana kuka sosai kaman ranta zai fice.


A b’angaren Maman Sabeera kaw Ramatu tazo sun k’ule a d’aki suna tattauna lamarin tareda neman mafita.

Ramatu Ta nusa tace “Ai wllhi Rahina Kema da naki, idan b’era da sata daddawa da wari.. Ni tin yaushe nace ki raba ‘yarki da wannan yarinya Sadiya mai shegen kyau kaman aljana.. Wannan yarinyar tana shigo miki gida Ta shnatak’e kaman gidan Ubanta, santaleliyar yarinya irin wannan kice min mijinki bazai d’aura idanu kanta ba..”

Maman Sabeera tace “Wllhi Ramatu ban tab’a kawo haka ba tinda naga bama ya son alak’arsu.. Kuma ni ban tab’a yarda yarinyar lalatacciya bace kaman yanda ake cewa _Never judge a Book by its cover_ toh ban tab’a munana ma yarinyar nan zato ba dan wataran wanda kake zaton mutumin kirki ne bashi ne mutumin kirkin ba, wanda kayi zaton na banza ne sai kaga shine mutumin kirkin.. Ni da har ina sha’awanta ma Abdallah (yayan Sabeera dake karatu k’asar waje..) Amma ni koda wasa ban zaci Wai Alhaji zai d’aura idanu kanta ba...Yayi aurensa ni bazan hanasa ba ya auri ko wacece amma kam banda Sadiya k’awar Sabeera... Ina zan Kai wannan d’imbin bak’in ciki da tashin hankali ga uwa uba Sabeera taji komai..”

Ramatu ta tab’e baki tace “Rahina zama fah bai ganki ba, tashi zakiyi muje har gidansu yarinyar nan muci uban uwarta da kyau dan itace tsararmu ba d’iyarta ba.. Ki daina wannan simi simi d’in nan naki ki tashi ki karb’a ma kanki da yaranki ‘yanci idan kuma ba haka ba ki zuba ido ki zama ‘yar kallo cikin gidanki.. Kinaji kina gani yarinya ‘yar cikinki Ta k’unsa miki bak’in ciki. Keda gidanki yafi k’arfinki.”

“Ramatu sanin kanki ne ban isa na hana namiji son mata ba dan a halittarsu ne amma damuwar shine kar ya nemi na banza, yayi auren dan shine mafi a’ala tinda Allah ya huwace masa daman auren mace sama da guda. Sannan ni idan zai auren ya auro ko wacece amma tsakani ga Allah banda Sadiya.. Idan ni zan iya jura Sabeera fah.. Sabeera bazata iya jura ba.. Ni wllhi tashin hankalin da ‘yata zata shiga nake tunani.. Yaran nan fah bacci ne ke rabasu sanda suke makaranta kafin su tafi yajin aiki har karatu tare suke..”

Ramatu Ta katse Ta da fad’in “Ni dan Allah kin isheni, kin cika ni da surutun da babu gaira babu dalili.. Dik kin San da wannan shine kika d’add’agoni ko karin kummalo banyi ma mijina ba.. Dama Kinsan wa’azi zaki kirani kimin shine baki sanar dani tin a waya ba.. Ni wllhi indai hakane kar Ki sake neman shawari daga wajena.. Kije can ki k’arata da sanyin zuciyarki aita cutanki bak’in ciki ya turaki rami.. Idan kin canza shawri kya nemeni.. Ni Kinga tafiyata..”

Bata ida rufe baki ba sukaji kukan Sabeera na tashi Babanta rik’e da Ita yana fad’in ta gama rashin kunya daga yau..

A tare Maman Sabeera da Ramatu suka nufo parlorn.

Sabeera ta fad’a bayan mahaifiyarta a guje tana kuka.. Yayinda Babanta yaci gaba da aza babbar riga yana k’ok’arin ciro igiyar decoder yake fad’in “Har ni zakije ki wulak’anta.. Kije kici wa matar da zan aura mutunci sabida bakida hankali.. Yau zakiji a jikinki..”

Ramatu kaw yab’e baki saitin kunnen Maman Sabeera Ta rad’a mata“K’awata ni na wuce kafin mijinki ya had’a dani yace ni ce uwar zigi..”

Maman Sabeera da tuni Hawaye ya wanke mata fuska Ta tare d’iyarta tai tana fad’in “Wllhi bazan Barka ka daketa ba..” Lokaci guda ta tura Sabeerar d’akinta ta maida k’ofa ta rufe.. Tare k’ofar d’akin tai tana hawaye alamun bazata barsa ya shige ya daki Sabeera ba..

Sai sakin huci yake yana duban Maman Sabeera yana fad’in “Rahina ki bani hanya na koya ma yarinyar nan tarbiya.. Tarbiyar da kika kasa bata..”

Cikin zuban hawaye Maman Sabeera ke dubansa, lokaci guda take furta “Wane tarbiya kake magana..? Wane tarbiya ne zaka bata wanda na gaza bata..? Tarbiyar rufeta a gida ka hanata fita Ko k’ofa dan kana tsoron kar a lalata maka Ita Ko mai..?”

Da tsananin mamaki yake dubanta “Rahina kike fad’awa magana irin haka.. Kina cikin hankalinki Rahina..? Dan kawai nazo da batun zan k’ara aure sai ki nemi ki jefeni da sharri..!”

Cikin zuban hawaye Maman Sabeera

Please Login or Register in order to submit comment