Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yanzu ita da Mr Inspector Wai har zasu zamto manyan abokai irin yanda Aunty Larai ke fad’i..? Ta kuma duban fuskarta a madubi kafin zancen Aunty Larai ya kuma zuwa mata cewa Great Mission d’inta shine rayuwar aure dake gabanta, dan aure ibadah ne kuma bautan Ubangiji ne. Duk abinda Ta gani cikin gidan aure ibadah take.. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin ta isa ta kwanta hoton fuskar mijinta cikin idanunta.

A ranan da yammaci Aunty Larai tazo da mai lalle Ta zana mata bak’i da ja hannu da k’afa.. Sosai k’unshi yai kyau ya amshi fatarta musamman da shike fatar tata ta d’auki gyara sosai.

Idan ka ganta kaman wata sabuwar Amarya ga wani k’amshi na musamman da take duk yanda Ta gifta..

Habeeb ya dubeta yace “Aunty Sadiya kunyi kyau sosai kaman ana bikinki..”

Gaba d’aya suka d’an dara Habeeb na kuma cikasu da sururtu. Kafin dare mai kitso tazo tai mata dan harta wanke kai da drying saida Aunty Larai tai mata.

Safiyar Washe gari litinin Aunty Larai ta sanyata ta shirya tsaf cikin wani embroidery atampa mai kyaun gaske ruwan cikin k’wai wanda ya tafi da kalan jikinta, d’inkin riga da skirt ne da ya masifan mata kyau cikin kayyakin da su Aunty Larai suka d’inka mata a nan cikin foundation d’in. Dama tin kwanakin baya Aunty Larai ta d’au measurement d’inta ashe Mu’azzam ne ya bama Aunty Larai tai mata d’inkuna masu kyau na zamani.. Sai gani kawai tai Aunty Larai dasu Farida ‘yanmata masu koyar da sana’ar d’inki a foundation d’in suna shigo da kayayyaki kama daga laces zuwa atmapopi hardai irinsu Dubai materials d’in nan.

Aunty Larai tasa Farida tai mata light makeup a fuskarta. Dik yanda Sadiya bataso ba haka dole akai mata mai sauk’i dama ita ba gwanar kwalliya ma fuska bace tin tana amsa sunan Sady pretty.. Kaidai barta da gayu ma jiki sai ka rantse d’iyar wata hamshak’i ne.. Dama bata faye fente fuska ba.. Yau d’in Sai abin ya zama na musamman abinka da wacce bata saba ba. Tayi kyau har ta gaji, Farida ta d’aura mata d’ankwalin daidai da kanta. Sai santin kyaun da ta k’ara suke.. Ita dai batace komai ba sai fad’uwa da gabanta keyi dan ko Aunty larai bata sanar da ita ba tanaji a jikinta Inspector ne zaizo, ga Umma ta kauda kai abinta bama ta saka masu baki cikin al’amaransu.. Toh kodai baiyi tafiyar bane.? Ta tambayi kanta tana duban kanta a mirror bayan an ida shiryata. Tabarakallah Masha Allah shine kawai abinda taji zuciyarta na ambata. Ta fito tsaf da ita kaman wata sabuwar Amarya.

Tana tsaka da tinanin wayar ya soma ruri. Ta juya tana duban wayar kan gado gabanta na kuma fad’uwa. Tasan idan bashi d’in ba babu mai kiran wayar Dikda cewa ba da lambar da ya sanya mata ba yake kiran.

Ta k’arasa a hankali hannunsa sai k’aran awarwaro yake kafin ta d’auki wayar.

Bata furta komai ba daga d’aya b’angaren ta sinkayo muryarsa cikin sallama.

Ta lumshe idanunta a hankali tana tinanin yaushe rabon da taji Muryarsa. Sallamar tasa ma a zuciya Ta iya amsawa.

Shiru kaman babu mai kuma cewa komai. Nan ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Are you ready for your next mission..?”

Murmushi ne taji yazo mata wann karon.. Sai ta d’an murmusa tana rufe fuskarta da hannu guda.

Mu’azzam yaji sautin murmushin nata ta cikin waya. Shima murmushin yai kafin yace “Ki fito ina jiranki a parlor.”
Daga haka k’it ya katse kiran.

Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana kuma duban kanta. Mayafinta kalan kayan dake aje saman gado ta d’auka ta yafa kaman mai tsoron ganinsa ko kuma wacce basu tab’a had’uwa ba haka nan taji.. Ta kasa fita saima komawa da baya da tai tana sauk’e ajiyan zuciya a hankali.

Kusan minti biyar ta kwashe kafin ta daure ta fito cikin taku a tsanake.

Tin daga nesa yake dubanta dan musulmin k’amshin da take ne ma ya soma yima k’ofofin hancinsa sallama.

Cak ya daina shafa wayar da yake ya mik’e tsaye yana dubanta sanda take k’arasowa.

K’afafunsa ta fara hangowa itama nan ta fahimci yau d’in shigar manyan kaya yayi.. Ta d’ago idanunta a hankali tana dubansa. Jampa ce jikinsa kalan ruwan k’asa sai hularsa Wanda ya dace da shigar tasa.. zata iya cewa wann shine karo na farko da ta gansa da idonta cikin manyan kaya tin bayan hoton aurensu da ta gani shida Safeenah a gidansu. Sosai shigar ya amshesa ita zata iya cewa irin wann shigar ma yafi amsar Sa. Ko kuma dan ta kwana biyu bata gansa bane shiyasa taga hakan bata dai sani ba. Kaman wacce aka tsunkula Ta kuma maida kanta k’asa tana jin kaman bazata iya ci gaba da tafiya ba sabida irin kallon da yake mata.





SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*45*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*





Kasa k’arasowa tai saima tsayuwa da tai daga can nesa kanta a k’asa. Gabanta na wani irin fad’uwa musamman da ta jiyo sautin footsteps d’insa alamun yana k’arasowa.

Saida ya tako kusanta kafin yaja ya tsaya yana kuma k’are mata kallo lokaci guda yana tsarkake mahaliccinta.. Cikin ransa yake fad’in Maiyasa suke kiranta Pretty...? Beauty ta cancanci su kirata ba Pretty ba domin kuwa she’s truly beautiful.. Ya k’arashe zancen zucin nasa yana mai kuma k’arasowa kusanta, dab kusanta ya tsaya yana duban tsakiyar kanta sabida ratan tsawo dake tsakaninsu.

K’amshin dake jikinta na kuma tasowa yana bugan k’ofofin hancinsa, hannayensa ya bud’e had’ida rungumeta cikin jikinsa idanunsa a lumshe. Itama d’in lumshe idanunta tai tana jin wani irin salama had’ida nastuwa na ratsa zuciyarta.

Sun d’an jima a haka kafin ya rik’o hannunta suka zauna saman kujera. Ta d’an duk’a ta gaishesa kanta a k’asa.

Ya tsareta da idanu yana duban Bak’on Al’amari a wajenta. Gaba d’aya shi gani yake ma kaman an canzata.

Ya amsa ba tareda ya janye idanunsa daga kanta ba. Suka d’auki lokaci a haka Sai k’are mata kallo yake, har ta soma gundura tana tinanin bazai kuma cewa komai ba, dan tasan mai hali baya fasawa. Nan kuma ta sinkayo muryarsa yana fad’in “It seems to me you’re ready.. For your next mission.. Kin shirya komawa GIDAN ARO..”


Sai sann ta d’an dubesa kafin ta maida kanta wani b’angaren, d’an juyowa tai tana dubansa murmushi saman fuskarta kafin ta jinjina kai tace “Of course Inspector.. I’m super ready to carry out my next mission.. But only for Inne..” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.

D’an tsimewa yai kafin yace “Aw sabida Inne zaki yarda ki bini ba wai dan kina son bina ba.. Didn’t you miss me at all..?”

Sunkuyar da kanta tai tana murmushi. Sai kuma ta girgiza kai alamun a’a.

Kafeta da idanu yai sai kuma yace “Idan bakiyi kewata ba bazaki min Duka wad’ann kwalliyan ba..”

Dubansa ta kumayi, sai ta murmusa kad’an itama tace “Unfortunately ba sabida kai nai ba Inspector.”

“Toh sabida wa kikayi.?” Ya tambaya yana dubanta.

“Inne of course..” Ta basa amsa kai tsaye.

Mamaki ya cikasa ganin bataji haushi ba, yasan da da ne da yanzu hiran ya k’are yana sako mata zancen mission.

Ya jinjina kai kad’an kafin yace “Ki shiga ki masu sallama we are leaving now.. Akwai yanda zamu biya.”

Ta d’an d’ago tana dubansa a d’an tsorace wann karon “Da gaske kake yanzu zamu tafi..? To.. To.. Bakaci komai ba.. Should I bring something for you..?” Duk sai ta wani daburce lokaci guda.

“Calm down.. I’m not hungry.. I’m ok..” Ya fad’i yana mai kamo hannayenta da zanen k’unshi ya k’ara masu kyau.

Jiki a sanyaye take duban yanda ya sakale yatsun hannunta cikin nasa “I thought you said Kin shirya ma mission d’inki na gaba.. Why are you panicking then..?” Ya k’arashe yana mata wani salo cikin tafin hannunta.

So take ta cire yatsun hannun nata daga nasa amma ta kasa, ga tsareta da idanunsa da yai. Saida ya tabbata ya kashe mata jiki lak’was kafin ya d’anyi gyaran murya yace “Jeki masu sallama na k’agu a fara wann mission d’in..”

Gabanta ya fad’i tai saurin d’agowa tana dubansa, sai gani tai yankashe mata idanu guda “Go now.” Ya fad’i murya a hankali yana mai mata alama da idanu.

Jiki a sanyaye ta mik’e ta nufi ciki yayinda Mu’azzam ya d’au wayar salulansa

Tana shiga ciki maimakon ta sanar dasu d’aukanta yazo, sai ta soma masu kuka. Ta duk’a saman cinyar Umma tana kuka.. Aunty Larai ta duk’a tana lallashinta had’ida bata baki “Haba Sadiya saikace tafiyar da bazaku dawo ba, dukda duka bazaku shige sati biyu ba.. Tashi abinki kayayyakinki ma an fitar miki tintini.. Tashi kar ki b’atawa mijinki lokaci kinji koh.”

Ta d’ago tana duban Umma, kwantattun hawaye ta hango cikin idanun Umman. Basu iya furta komai ba Sai rungume juna da sukai.

“Allah shi maku albarka.. Allah ya tsareku daga dukkanin abin k’i ya azurtaku da zuri’a d’ayyiba.. Tashi kije Sadiya na yafeki duniya da lahira.. Allah yajik’an mahaifinki ya miki albarka..” Ta k’arashe suna masu kuma rungume juna cikin hawaye.

Haka su Aunty Larai dasu Habeeb suka rakota har waje kaman kar su rabu da juna.

Mu’azzam ya bud’e mata front seat ya kuma musu sallama kafin Sadiya ta shige kanta a k’asa.

Nan suka d’auki hanya sun Aunty Larai dasu Habeeb suna masu waving.

Tana hangosu ta mirror tana jin wasu hawayen na kuma zuwa mata.

Yana hankalce da ita saidai bai furta komai ba har sukai nisa da tafiya.

Hannunta dake aje saman cinyarta taji masa hannun guda akai d’aya kuma yayi amfani dashi wajen rik’e steering wheel. Zata janye taji ya d’an rik’e da k’arfi still idanunsa naga kwalta ba tareda ya dubeta ba.

Babu yanda Ta iya dole haka hannunta guda ya kasance cikin na Mu’azzam dake driving da hannu guda.
**

Da k’yar ta iya tashi tana murtsuke idanu, alarm d’in da Ta saka ne ma ya tada Ita dan a ranar take shirin komawa Office.

Bathroom ta fad’a Tai wanka kafin ta tana drying kanta, sai lokacin ta zira Doguwar riga da hijab tai sallar asuba. Dan dama tin da Mu’azzam ya tasheta tai Sallah sai ta gudo nata d’akin tai kwanciyarta. Harda kulle k’ofa tai dan karma idan ya dawo ya shigo ya tada ita ya tambaya ko tayi sallan. Ta d’an tsuke baki tace “Haka kawai ba gashi yanzu nayi sallar ba, da ace ina can d’akinsa na tabbata da yanzu ya katse min bacci na yace lallai Lallai dole dole Sai na tashi sallah. Dik San bacci na kusanka my Halal zan iya yafe baccin safe a jikinka..” Ta k’arashe tana mai ci gaba da shirin fitarta. Nan ta duba time taga har 9:30am.

A gurguje ta ida shirinta ta nufi nasa d’akin Dikda tasan by then ya tafi office. Kaman yanda tai tunani d’akin nasa tas tas kaman basu kwanta saman gadon ba.. Har Ta juya zata fice Ta dawo da baya tana duban side lamp dake kunne.. K’arasawa tai zata kashe lamp d’in nan taga drawer d’in kaman a bud’e ga wani abu kaman picture ya sako kai. Zuciyar Safeenah yai wani irin yankewa.. A hankali ta ida bud’e drawer d’in zuciyarta naci gaba da bugu.. Bata ida jin tashin hankali ba saida ta ciro hoton gaba d’aya.

Halal d’inta ne da wannan ‘yariskar yarinyar a park, saikace wasu masoya fuskokinsu cikeda annashuwa.. Zuciyar Safeenah yaci gaba da tsinkewa tana tinanin kenan Mu’azzam raina mata hankali yai ko me.. Kenan ba auren mission yai da yarinyar nan ba..? Take zuciyarta ya bata amsa da fad’in dama bai tab’a ce miki ga kalan auren da yai da Ita ba.. Takarda kika tsinta wanda yarinyar ta bar masa nan kika fahimci cewa auren mission yai da Ita.. Sassauta ma kanta Ta soma da fad’in “Enough Feenah ke shaida ce Babu abinda ya shiga tsakanin mijinki da wann ‘yariskar.. Kuma ma ta iya yuwa wann dik cikin mission d’in ne.. Da ace yana tare da wann yarinyar da bai zauna dake tsawo satittika har biyu ba tareda ya tab’a miki koda zancenta ba balle ya kawo miki Ita gidanki..” Tsayuwa kuma tai tana duban hoton kafin ta girgiza kai, kaman zatai kuka take furta “Toh amma Maiyasa ya aje hotonsu haka..?” Take taji zuciyarta na bata amsa da fad’in Because he loves her.

K’ara Safeenah ta saki ta shiga kekketa hoton tana watsi dashi a tsakiyar d’akin.. Tana tsaka da wann bori wayarta ta soma ruri.

Mommy ce mai kiranta, rabon da suyi waya da Mommy tin randa Mommy tazo gidan tace sai Mu’azzam ya saki Safeenar.

Ta d’aga wayar tana kuka.. Had’iye kukan tai sakamakon abinda Mommy Ta soma sanar da Ita

“Safeenah kina ina ..?”

Safeenah tace “Ina gida Mommy..”

Mommy ta jinjina kai tace “Ba wannan amsar nake so ki bani ba.. Kina ina Maras mutuncin mijinki ya d’auko kishiyar ki ta bariki zai tafiya da ita..”

Zuciyar Safeenah yai wani irin tsinkewa. Lokaci guda Ta shiga girgiza kai tana fad’in “A’a Mommy you must have have got this wrong.. My Halal fah baya tare da ‘yariskar can.. Dama auren mission sukai kuma babu abinda ya tab’a had’asu..”

Bata kai aya ba Mommy ta katseta da fad’in “Rufe mun baki shashashar banza..!Toh ki zauna a wajen ke ga mai Halal koh. Aiko zai shayar dake halaliyar mamaki.. Gashi nan ya kawo yarinyar suna jiran Daddynki a side d’insa kuma daga nan Fufore suka nufa tare.. Ki zauna Safeenah kar kizo ki k’watar ma kanki ‘yanci..!” Daga haka Mommy Katse kiran tai tana huci.

Safeenah ta soma ganin duniyar na juya mata.. Itace Mu’azzam zai mata haka..? Zai d’auki wata ‘yariska Karuwa yace zai tafiya da ita.. Kuma ma wai all this while dama suna tare..? Ta soma sakin huci tana jin k’irjinta na mata zafi.. A fujajan ta nufi closet d’insa tana dubawa nan kuwa taga alamun ya d’ibi wasu kayan yayi shirin tafiya.. Safeenah taci gaba da sakin huci.. Tasa kai zata fice sai kuma ta tsaya cak, juya ta kumayi a nan closet d’in nasa Ta hangi d’aya drawer da ya mance a bud’e wanda bindiga ce cikin drawer d’in. Cikin sauri ta duk’a ta suri bindigar ta shiga juyata cikin hannunta, lokaci guda take furta “Wllhi yau ko ni ko wann ‘yariskar.. Amma kam Tabbas yau za’ayita Ta k’are.. Ko ni ko tsinanniyar can..!” Tana ida fad’in haka Ta nufi nata d’akin ta d’auko car keys d’inta a fujajan, sai sauri take tana had’e stirs tana sakin huci, office d’in da bata je ba kenan Ta d’auki hanyar gidan Mahaifinta.

**
Assad na shirin fitowa kenan yana zaune yana shan tea yaji ana masa knocking a apartment d’insa.

Mamaki ya cikasa Toh waye wann mai nemansa da farar safiya. K’arasawa yai yana duba ko wanene.

Da mugun mamaki yake duban Maleeka dake tsaye k’ofar apartment d’insa tana hawaye ga akwati gefenta.

Ya d’an girgiza kai kad’an yana dubanta “Maleeka.. Lafiya..?”

Maleeka ta kuma fashewa da kuka mai ban tausayi.

Assad ya lek’a bai ganta da kowa ba, ya kuma dubanta ya dubi akwatin dake gefenta. Ya d’an kuma girgiza kai kafin yace “Maleeka meke faruwa..?”

Cikin kuka Maleeka ke fad’in “Assad bani da yanda zanje.. Mai gidan da nake haya ta mun wulak’anci ta koreni.. I’ve no one to run to, savings d’ina na watan nan na tura gida wa Mamana dake jinya.. Assad please help me..” Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana d’ago hannayenta alamun rok’o kaman zata duk’a a k’asa.

Fuzar da fuci yai kad’an kafin ya d’an matsa gefe ya bata hanya.

Tin kafin ya mata izinin shiga Maleeka ta shige tana kuka.

Zama tai saman kujera tana ci gaba da kuka kaman ranta zai fice.

Assad ya zauna d’aya kujeran yana dubanta cikeda tausayawa.

Bai hanata kukan ba saida tai mai isarta kafin ya d’anyi gyaran murya yace “Garin yaya haka Ta faru..? Kan mai zata koreki daga gidan.. Ince akwai ‘yanmata da yawa da kuke haya a gidan..?”

Maleeka ta jinjina kai tace “So take ta dinga samun kud’i damu.. Maza take kawowa gidan ni kuma nak’i amincewa..”

Murmushi yai a tak’aice kafin yace “Kina jami’ar tsaro har za’a miki barazana irin haka.. Haba Maleeka saikace bakisan right d’inki ba.. Ki tashi yanzu mu tafi mu filing case akanta.”

Girgiza masa kai tai still tana hawaye “Assad kasan yanda al’amra suke a k’asar nan.. Duk isanka da sanin ‘yancinka idan bakada abin duniya Toh fah kai na kowa bane.. Assad matar nan da manyan k’usoshin gwabnati take huld’a ta Ina zan fara shari’a da Ita.. Ga mayafiyata last week an Aiko mun jikinta ya tsnanta da Wanne zanji da shari’ar da bazan iya ba ko da jinyar mahaifiyata..” Ta k’arashe tana kuma fashewa da kuka. Dama Iyayen Maleeka ba Abuja suke na itama aiki ne ya kawota iyayenta a can garinsu Kwara suke kaman yanda iyayen Assad suke Nasarawa Lafiya.

Ya d’anyi jim yana dubanta cikeda tausayawa. Fuzar da fuci yai kafin ya mik’e ya nufi kitchen ya kawo mata mug da flask harda bread yace tasha tea. Tai masa godiya kafin ya zauna ya d’auki tea d’insa yana sha.

Lokaci guda yake furta “Zamu San yanda za’ayi ki kwantar da hankalinki.. Amma zamanki a nan bazai yuwu ba, kinga dukanmu musulmai ne kuma a shari’a bai kamata mu zauna haka ba.. D’aki d’aya ke gareni nima sai parlor.. Kinga zamanki a nan bazai yuwu ba amma nasan bazamu rasa yanda za’ai a sama maki wani rent mai sauk’i ba...”

Ta jinjina kai tana hawaye..” Wannan gaskiya ne.. Kuma na gode maka, banida abinda zan saka maka dashi..”

Ya girgiza kai kad’an yana jin idanunsa na masa nauyi.. Lokaci guda yake furta “Kar ki damu ai yima kai ne.. Ki gama karyawa sai mu fita muga yanda za’ai..” Bai kai aya ba maganarsa ta sark’e.. Kan kace mai ya silale cikin kujerar tamkar wani sumamme.

Wani irin jahilar dariya Maleeka Ta fashe dashi dan lokacin da Assad ya tashi yaje kawo mata abin karin kumallo ta zuba masa pills cikin tea d’insa.. Ta kuma murmusawa tana dubansa kafin ta soma fad’in “Da kyau Detective Assad, Sarkin taimako da tausayi.. Yanzu sai muga ta yanda zaka tsere wa makirci na..” Tana ida fad’in haka ta kuma fashewa da dariya kafin Ta isa ta janyosa da k’yar ta shigar dashi d’akinsa.. Kwantar dashi saman gado tai kafin ta shiga b’alle botiran rigarsa.. Tana gama cire masa ta cire nata tufafin itama kafin ta haye saman gadon, ta kwanta cikin jikinsa ta dinga d’aukansu pictures da wayarta..

**

A first parlorn Daddy suka zauna, bai ma soma tunk’aran side d’in Mommy da Ita ba dan yasan abin bazai wanye da kyau ba. Ya mik’e da zummar Fita.. Tai saurin mik’ewa itama tana dubansa idanunta sunyi rau rau “Ina zaka kuma..?” Ta tambaya tana dubansa.

Murmushi ya sakar mata kafin yace “Ki kwantar da hankalinki nan gidanmu ne.. Babu wanda zai cutar dake..”

Ta d’anyi shiru sai kuma tace “I thought kace garinku zamuje..?”

Baikai ga bata amsa ba Musaddiq ya shigo da sallama. Suka gaisa da Mu’azzam yana fad’in yanzu zai shirya jirgin sai 12noon Daddy yace yana zuwa yana rounding meeting d’insa a Company ne..

Mu’azzam ya jinjina kai yace “Sai Kai sauri ka shirya kasan bana San delay.”

Musaddiq ya jinjina masa kai yana mai sara masa.. Lokaci guda yakai dubansa ga Sadiya wace ta b’ace kaman bata a wajen.

Ya d’an k’araso ya duk’a yana gaisar da Sadiya cikeda barkwanci yana fad’in “I’m Musaddiq Gamji.. Mijinki babban Yayana ne kuma my only confident.. Duk wata matsalata wajensa nake kawowa dukda cewa wasu lokutan yanada wuyan sha’ani.. Nasan Kinsan halin kayanki..”

Murmushi kawai Sadiya take tana jinjina barkwancin Musaddiq.

Janyosa Mu’azzam yai yana fad’in “Kasan banson b’ata lokaci Ka tashi kaje ka shirya kafin Daddy ya k’araso..”

Musaddiq ya sara masa yana fad’in “Yes Officer.. Right away..” Lokaci guda ya shige yana murmushi.

Mu’azzam ya d’an girgiza kai kafin ya mik’e da zummar ficewa.

Nan itama ta mik’e tana dubansa a d’an tsorace “Are we leaving now..?” Ta tambaya kaman mai shirin yin kuka. Dan harga Allah haka kurum taji sam bata sake a gidan ba.

Agogon hannunsa ya d’an duba kafin yace “Daddy zai k’araso in a bit.. Idan kun gaisa zamu wuce in sha Allah.. Ki jirani a nan Ina zuwa..” Daga haka ficewa yai cikin sassarfa.

Sadiya Ta koma saman kujeran ta zauna zuciyarta na kuma yankewa yanda Kasan wacce aka kawota gidan yankan kai haka take ji.. Sai rarraba idanu take.

Tana nan zaune Meema Ta shigo hannunta rik’eda tray murmushi saman fuskarta, tsaf Sadiya Ta gane Meema sune dai sukaje zasu bugeta kwanaki a GIDAN ARO.. Sannan sune ‘yanmatan da suka kuskure Ummanta da Mota.. A tak’aice dai ta gane Meema k’anwar Matar Mu’azzam ce.

Tana ganin Meema ta nufota tai saurin mik’ewa tsaye dan batasan da mai tazo mata ba dukda cewa kayan motsa baki ne ta hango saman parantin dake hannun Meemar. Sannan bata mance last meeting d’insu ba.

Meema tace “Kiyi hak’uri ki zauna banida niyyan cutar dake..” Tai maganar murmushi saman fuskarta tana mai dire tray d’in gaban Sadiya.

A hankali Sadiya ta koma ta zauna Dikda cewa zuciyarta bai gama aminta da Meema ba.

Meema Ta zauna kujeran gefenta, murmushi saman fuskarta take duban Sadiyar “Sunana Meema Gamji.. Ni cousin d’in mijinki ne Ya Mu’azzam.. Kuma k’anwar matarsa Safeenah.. Nasan kin ganeni dan ba yau bane farkon had’uwarmu..”

Sadiya ta jinjina kai a hankali tana duban Meemar.

Meemar ta kuma gyara zamanta kafin tace “Naga shigowarku Keda Ya Mu’azzam nace barin Zo na rok’eki Gafara akan abinda muka miki nida ‘yaruwata.. Nasan baki sanar da Ya Mu’azzam cewa ga abinda muka miki ba, dan kin sanar dashi na tabbata da mun yabawa aya zak’inta.. Dan Allah ki yafe mana..” Ta k’arashe tana duban Sadiyar.

Girgiza kai Sadiya tai a hankali kafin tace “Babu komai.. Kar ki damu Ya wuce ai.. Kuma ko wacece akai mata irin abinda akai ma ‘yar uwarki zatayi fin haka.. Ni ban k’ullaceku da komai ba..” Ta fad’i a tak’ice still ba’a sake ba.

Meema Ta murmusa tace “Naji dad’i sosai, kuma mun gode.. Kisha lemo mana..” Ta k’arashe tana k’ok’arin zuba drink d’in.

Sadiya Ta saki murmushi kad’an tana girgiza kai “A’a a k’oshe nake.. Na gode..”

Meema bata fasa zuba drink d’in ba take fad’in “A’a zaki sha wani abu.. Yau ce fa rana ta farko da kikazo gidan nan.. Kuma gidan nan gidansu Ya Mu’azzam ne..” Tana maganar tana mik’owa Sadiya glass cup d’in.

Murmushi kawai Sadiya tai ta amsa tana mata godiya ba tareda ta sha ba.

Tuni Meema Ta soma janta da fira.
**

Mu’azzam kaw yana ficewa d’akin Musaddiq ya shige yanda Musaddiq d’in ke shirya suitcase d’insa.

Yana tsaye daga gefe yana karantar Musaddiq dake ciro kaya yana linkewa yana shiryasu cikin Jaka, lokaci guda Musaddiq d’in ke jefo masa fira yana amsawa jefi jefi.

“Damina ake bazaka d’auki kayan sanyi ba..?” Mu’azzam ya fad’i daga nan yanda yake jingine jikin gini hannunsa hard’e a k’irji.

Jinjina kai Musaddiq yai yace “Na gode da ka tina min..” Lokaci guda ya soma ciro kayan sanyi harda huluna. Hularsa da yake son sakawa wanda bai gani bane ya sanyasa tsayawa yana tinani yana kuma duba shelf d’in hulunan nasa.

Mu’azzam ya tsaresa da idanu kafin yace “Kana neman wani abu ne..?”

Musaddiq ya d’anyi shiru sai kuma ya girgiza kai yace “No.. No babu komai..” Jiki a sanyaye ya mik’e yana zipping jakan nasa.

Mu’azzam dake ta faman karantarsa yace “Are you sure babu komai..? You look tense of a sudden.”

Murmushi Musaddiq yai yace “No babu komai.. Shall we..” Ya k’arashe yana duban Mu’azzam d’in had’ida janyo suitcase d’in nasa.

Mu’azzam ya jinjina masa kai kafin suka soma takowa, wayar da ya shigo masa ne yasa Musaddiq yin gaba ya bar Mu’azzam d’in a baya yana amsa waya.

**
Safeenah na k’arasowa ta hangi motar Mijinta Mu’azzam a gidan. Watau dai da gaske Mu’azzam na gidan tareda wann ‘yariskar.. Cikin huci Safeenah ta d’auko bindigar ta nufi gidan tana hure huren hanci.

K’ofar side d’in Daddy data hango a bud’e ya tabbatar mata suna b’angaren Daddy kenan. Cikin huci Ta nufi sashen Daddy rik’eda bindigar.

A tare Sadiya da Meema suka mik’e cikin tsananin firgici ganin Safeenah da sukai kansu rik’eda bindiga.

Meema ta tare Sadiya ta shiga girgiza kai tana duban Safeenah “Addah Feenah no.. Please don’t do this.. Mai kike tunanin kinayi..?”

Safeenah na huci tana duban Sadiya da takai k’ololuwa wajen razana, lokaci guda take nunata da bindigar tana fad’in “Meema ki kauce min idan ba so kike ki bi sahunta ba..!”

Meema ta kuma girgiza kai tana d’ago hannu a hankali tana k’ok’arin nufo Safeenar “Addah Feenah please.. Don’t do this.. You are

Please Login or Register in order to submit comment