Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saman gado tana kuka tana fad’in Ina her Halal yake.

Daddy ya k’arasa ya rungume kan Safeenah dake zaune saman gado cikin jikinsa. Lallashinta ya dinga yana k’ok’arin calming nata kafin ya zauna gefenta.

Cikin kuka Safeenah ke ci gaba da fad’in “Daddy I love him.. I can’t live without my Halal..”

Mommy dake gefe tsawa ta darara mata da fad’in “Kika sake ambato wani my Halal a nan sai na halarta ma tafin hanuna fuskarki.. Sai na shata miki mari Safeenah. Shashasha kawai wacce bata San yanda ke mata ciwo ba.”

Safeenah Ta kuma fashewa da kuka yayinda Daddy ya aikawa Mommy mugun kallo “Fita ki bamu waje Hajara.” Ya fad’I yana duban Mommyn.

Cika kurum Mommy take tana fuci kafin tai k’wafa tasa kai fuu ta fice.

A k’ofa Ta had’u da Dr rik’eda file d’in Safeenar.. Ta dubesa tace “Yaya..?”

Likita yace “Report d’in Safeenah ne..”

Mommy Ta nuna masa hanya tace “Muje ka sanar dani ni ce nan mahaifiyarta.”

Dr ya d’an dubeta sai yace “Mijinta fah.?”

Mommy tace “Sun rabu basa tare. Zaka iya sanar dani komai..”

Ya d’an jinjina kansa kad’an kafin ya nuna mata hanya yana fad’in “After you.”

Mommy tasa kai Dr ya take mata baya.

A cikin d’aki kaw yanda Safeenah ke kwance Daddy yaci gaba da mata nasiha da fad’in “What were you thinking Safeenah.. Shin Kinsan matsayin wanda duk ya kashe kansa a addini.. Kafuri fah ya mutu Safeenah.. Shij kinaso ki mutu kafura..? Mai zai sa ki hallak’a kanki kan soyayya. Kwanakin baya kin tasamma halak’a matar Mu’azzam yanzu kuma kina yunk’urin halak’a kanki.. Kan wani dalili Safeenah..!”

Cikin kuka take fad’in “Daddy tambayata kake kan wani dalili bayan kasan dalilin son Mu’azzam ne.. Ni dai Daddy gwara na mutu kan na rasasa..”

Daddy ya girgiza kai yace “Mu’azzam doesn’t love you Safeenah. Learn to accept this.”

Safeenah Ta kuma girgiza kai tana hawaye “My Halal loves me Daddy.. He loves me.. I know he does.. Kawai dai wancan muguwar ce ta rabamu.. Daddy you need to help me please.. Dan Allah ka masa magana Daddy.. Yana jin maganar ka.. Dan Allah Daddy kace ya maidani..” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka.

Daddy ya lumshe idanunsa a hankali yana mai tura hularsa baya kad’an. Harga Allah ya soma gajiya da halin Safeenah akan Mu’azzam. Ya kula tana ma Mu’azzam son da bazata iya yakicesa cikin zuciyarta ba. Daga wnn sai wancan.

A can office d’in Dr kuwa da tsananin mamaki Mommy ke dubansa, ta d’an girgiza kai tace “Kace she’s 4 weeks pregnant.?”

Dr ya jinjina kai yace “Gwaji ne na jini wanda ko cikin Kwana guda ne jikinta zai nuna.

Mommy tai shiru tana jinjina kai tana tuna tarewar Safeenah gidan Mu’azzam wata guda kenan harda kwanaki. Muryar Dr ta sinkayo yana ci gaba da fad’in “Luckily cikin bai fice ba amma yana iya zuwa da tangard’a sai a kula da ita sosai kar irin abinda ya faru da ita yanzu ya kuma faruwa.. Dan komai ka iya faruwa.”

Mommy Jiki babu kuzari ta jinjina kai tace “Za’a kula da ita Dr. Kuma haka bazai sake faruwa ba.. Amma Likita inaso maganar nan ya tsaya tsakaninmu kar kowa yaji harda ita Safeenar duba da yanayin halinda take ciki.. Nafi so na sanar da Ita a naste.”

Dr ya jinjina kai yace babu komai dik yanda tace. Lokaci guda ya mik’awa Mommy result d’in. Ta cukukuye ta tura cikin jaka kafin ta fice daga Office d’in tana sakin huci tana muzurai.

Cikin zuciyarta take fad’in “Lokacin ramuwa yayi Mu’azzam zaka d’and’ani k’unci wanda baka d’and’ana a baya ba. Idan sunana Hajara sai na sauk’e maka wann d’anyen kan naka.. Sai na nuna maka kai k’aramin maras kunya ne.” Ta kuma yin k’wafa kafin tasa kai ta shige.

**

A can Fufore kuwa tun bayan tafiyar Mu’azzam Ta dawo d’akin Mamy da kwana. Tare tare suke gudanar da komai itada Mama Hindu da Ajidde..

Yau ma ruwan addu’a data kawo Malama ta bata zamzam ce tace ta Bawa makusancinta ya karanta mata ayatul Shifaa a ciki a bata Ta sha.. Saidai babu Mu’azzam wanda yake d’anta sann babu Daddy da yake mijinta. Sadiya ta amsa tace zata karanta mata Ta bata tasha tinda damuwar shine a karanto ayoyin da yak’inin Allah ya bata lafiya.

Nan kuwa ta karanto ta tofa mata ta bata tasha saura ta shafe mata a fuskarta.

A ranar da dare suna kwance suna bacci taji kaman gadon Aunty Nuratu na motsi. Ta mik’e a hankali daga saman katifar da take kwance.. Kaman wasa motsin na kuma yawa matar da ko hannunta bata iya motsawa.

Sadiya ta mik’e tana karanto addu’o’i saman harshenta. Nan ta hangi kaman Mamy d’in ce ta mik’e zaune. Zuciyarta yai wani irin yankewa.. Ta soma lalumar haske zata kunna wutar d’akin.. Tana kunna wutan sai kuma taga tana nan kwance harta abun rufauwarta na nan kaman bata motsa ba. Tai k’ok’ari tai k’arfin hali ta matso kusanta ta karanto mata amanarrasulu da ayatul kursiy da kuma k’ul’au’zai.. Ta tofa mata kafin tai zaune gefenta tana dubanta dan gaba d’aya ji tai baccin ya tafi daga idanunta..

Washe gari da safe haka ta dinga mamakin abinda ya faru daren jiya wanda kaman mafarki ne tai haka take gani. Koda Ajidde tazo Sadiya ta sanar da ita abinda ya faru amma tafi tunanin watak’ila mafarki ne tai.

Ajidde ta jinjina kai tace “Ince baki sanar da kowa ba..?”

Sadiya ta gyad’a mata kai alamun eh.

Jinjina kai Ajidde tai tace “Yauwa Malama tace idan anga wani canji kar ayi Saurin fad’a wa mutane.. Yanzu yau in sha Allah zan sanar da ita abinda kika fad’a mun.. Allah yasa a dace matar nan ta sami lafiya.. Al’amarinta akwai ban tausayi.”

Sadiya ta karkato tana duban Aunty Nuratu. Sai kuma ta furta Ameen a hankali. Ta maidoda dubanta ga Ajidde dake saka tsakin habbaussauda cikin gaushi tace “Idan ana buk’atar wani abu ki fad’a mun kinji.. Ajidde ta murmusa tace “Kar ki damu zan sanar dake in sha Allah..”

Sadiya ta sakar mata murmushi tace “Barin duba Inne..”

Jinjina mata kai Ajidde tai tace “A dawo lafiya.”

Suka sakar ma juna murmushi kafin Sadiyar ta fice.
**

Bugu biyu a na uku Shemau ta d’aga dan Safeenah ce mai kiranta.

“Ina jnki Safeenah tin shekaran jiya nake neman layin ki.. Sai yau kika samu sararin kiran wayata.”

Safeenah Ta fuzar da fuci kad’an tana duban hannunta da aka saka mata drip tace “Aunty banida lafiya ne.. Ko Kinsan Jiya a asibiti na yini Ina shan drip..”


Aunty Shemau Ta zaro idanu tace “Mai ya faru..?”

Safeenah tace “Mommy bata baki labarin abinda Mu’azzam ya mun ba..? Aunty na tsani matar Mu’azzam zanyi komai Dan Ta fice daga rayuwarsa.”

Shemau ta jinjina kai tace “Wann sadaka yallar ai ba banza ta bar Mu’azzam ba.. Zan taimaka miki Safeenah.. Zata fice daga rayuwar Mu’azzam na miki alk’awari..”

Musaddiq yai tsaye Cak yana sauraron wayar Aunty Shemau da Safeenah.




SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*52*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*






Shemau Ta numfasa tace “Kina jina, naji Inne na maganan za’a turo Driver ya d’auketa, kuma naji tana magana da Mama Hindu ko za’a sama mata yarinya ‘yar tayin zaman Mota cikin ‘yanuwa. Nasan duk tsiya cikin satin nan za’a turo direban..”

Safeenah ta katseta da fad’in “Aunty ai bazamu bari ta dawo ba.. Ni kawai ki taimakeni kar ta dawo Gidana Dan girman Allah Aunty Shema.. Ayi mai yuwa kar Ta kuma tako mun k’afa cikin gida Ta fita da fitar Ta kenan..” Ta k’arashe tana fito da idanu waje kai kace Shemaun na dubanta.

Shemau tai shiru tana nazari Ta tuna exactly abinda Mommy Ta fad’i mata kenan lokacin da za’a kawo Aunty Nuratu jinya cewa Ta fice kenan daga gidanta fita ta har abada. Ta nusa kad’an tace “Yanzu meye abinyi Safeenah..? Mai kike so ayi Kinsan dai tafiya ya zama dole babu fashi tinda har Inne ta amince da hakan..”

“Ni kawai kiyi duk abinda zakiyi dan kar ta dawo..”

Da Mamaki Shemau tace “Toh kasheta kike so ayi..?”

Cikin sauri Safeenah har tana girgiza kai take fad’in “A’a ni bance ki kasheta ba Aunty.. Kawai ki illata shegiya yanda bazata samu damar dawowa ba yanda ma bazata kuma amfanarsa ba. Ki karya mun k’afar munafuka ko ki lak’a mata wani babban sharri.. Ki tura namiji d’akinta kiyi kururuwa ki had’a mata jama’a nayi imani idan Mu’azzam yaji haka ya rabu da Ita kenan rabuwa ta har abada..”

Shemau ta numfasa kad’an cikin zuciyarta tana ayyana cewa Wato anama Safeenah kallon shashasha idan akan D’ansandan nan ne tsaf zatai tunanin makirci iri daban daban dan burinta ya cika.

Ta d’an nusa tace “Feenah Kinsan had’arin abinda kike fad’i kuwa.. Idan plan d’in yai backfiring fah ba ke kad’ai ba harta ni zan sami matsala bada Uncle d’inku kawai ba harta da Inne sai na sami matsala dan na tabbata ko Mu’azzam bai kulle ni a cell ba Inne zata koreni.. Ta inama zan gayyato mata kwarto cikin gidan gonar nan..? Bayan Kinsan kalan tsaron dake cikin gidan gonar.

Safeenah ta d’an rausayar da idanunta cikeda k’osawa tace “Aunty bamuda wani zab’i kawai kisan yanda zakiyi ki lak’a mata wann sharrin shi kad’ai ne zaisa Mu’azzam yaji ya washeta bai ko k’aunar jin mai irin sunanta balle ya ganta.. Haba Aunty Shema ki tausaya min na karkato da akalar hankalin mijina gareni..”

Aunty Shemau ta nusa tace “But Safeenah kinsan fah komai a rayuwar nan yanada price..”

Safeenah Ta jinjina kai tace “K’warai kuwa na sani Aunty.. Wllhi idan kika mun haka.. Idan kika taimakeni tsinanniyar nan Ta fice daga rayuwar Mu’azzam ni kuma zan miki komai ko mai kika umarceni na miki zan miki shi without giving it a thought.. I’ll do whatever it takes dan na tabbata Karuwar nan Ta b’ace b’at daga rayuwar my Halal.. Please Aunty Shemau ki taimakeni Kimin wann..”

Aunty Shemau ta jinjina kai dan ta tabbata yanda Safeenah tace d’in zatayi komai “Toh shikenan Safeenah.. Zan taimakeki zan gayyato mata kwarto har cikin d’akinta yazo mana da sauk’i tinda a d’akin uwar Mu’azzam take kwana, Kinga idan Ta fice sai mu turosa ya shiga da safe tana dawowa a kamata dashi a d’akin. Ni kuma zan tara mata jama’a.. Kinga tun kafin labari ya isa ga Mu’azzam jarabebbiyar Kakarku zata kori shegiya dangin mayu..”

Safeenah ta sauk’e ajiyan zuciya cikeda jin dad’i tana mai sakin murmushi “Aunty kin gama mun komai nan gidan duniya idan har kika mun wann.. Ki fad’a ko me kike so daga wajena kin same shi babu tantama.”

Shemau ta murmusa cikeda jin dad’i tace “Zan fad’a miki abinda nake so ki mun.. But for now bari mu cire Sadiya cikin hoton..”

Suka shek’e da dariya a tare kafin sukai sallama.

Cikin sand’a Musaddiq ya bar wajen yana nanata iyaka abubuwan da yaji suna fita daga Bakin Aunty Shemau. Ya fahimci sunaso Su k’ulla wa matar Mu’azzam sharri ne itada ‘yar uwarsa Safeenah. Ya girgiza kai kad’an ba tareda yace komai ba. Zama yai saman kujera ya d’aura hab’arsa saman hannayensa da ya dunk’ulesu waje guda tinani fal zuciyarsa.

Aunty Shemau kaw suna ida waya da Safeenah ta nufi sashen Sadiya.

A k’ofa suka had’u da Sadiya zata shashen Inne.

Ta sakar mata murmushi tana dubanta “A’a Amarya kar dai fita zakiyi..?”

Sadiya ta murmusa kad’an kafin ta d’an risina ta gaida Aunty Shemau.

“Dama sashen Inne na nufa Aunty..”

Aunty Shemau ta murmusa kafin tace “Koda yake ma ina kika sani a garin nan balle ki fita.. Kuma dai ya kamata ki d’an fita kiga gari kafin ki gama hutunki ko yaya Kikace..?”

Murmusawa ta d’anyi kad’an tana gyara zaman mayafinta ba tareda tace komai ba. Sai kuma tace “Aunty Mu shiga ciki ki sha ruwa na barki tsaye.”

Aunty Shemau ta murmusa tace “Aiko ba a k’in tayin shan ruwan gidan Amarya.. Ruwan gidan Amarya zak’i ne dashi..” Ta k’arashe cikeda barkwanci.

Sadiya dai sai murmushi kurum take. Lokaci guda ta juya ta bud’e masu k’ofa suka shige Parlorn.

Aunty Shemau Ta soma bin parlorn da kallo sai kace ranan ta soma shiga. Tai zaune saman kujera k’afafu d’aya bisa d’aya ta d’aga kai sama tana ‘yan kalle kalle “Wai! Dank’ari lallai an kashe Kud’i a parlorn nan.. Kaga kaya kaman order d’insu akai daga waje.. Gidan Amarya dai dik yanda yake akwai santi. Sai ya tuna min lokacin da na raka Aunty Hajara mukai sayayyan kayan auren Safeenah a Dubai da Qatar.. Ni wasu abubuwan ma sunmin kama da na Safeenah..” Ta k’arashe tana kuma dube dube.

Jikin Sadiya ya d’anyi sanyi dai dai lokacin da take aje drinks gaban Aunty Shemau.

Shemau taci gaba da fad’in “Ai iyaye gaskiya suna k’ok’arin kashe Kud’i wajen aurar da yaransu mata. Duk dukiyar nan da ake kashewa wani sa’in sai kiga aure bai kya ba.. Shiyasa ni bana goyon bayan kashe kud’i da gidan mata suke a aure.. Ka gama kashe kud’i ka sai ma d’iyarka kayan d’aki na gani a fad’i ba shi zai hana namiji ya faskara mata rashin mutunci ba. Dai dai da warmers na zuba masa abinci sai an saya.. Yana cin abincin yana danna wa ubanta ashar.. Namiji kenan k’anin ajali..” Ta k’arashe tana kurb’an drink d’in.

Ta d’anyi gyaran murya kad’an kafin tace “Ai ke kinada sa’a da naki iyayen basu wahala kan namiji ba.. Duk wann kayan alatun danginsa suka zuba abinsu.. Ai naga tulin kud’ad’en da Inne tasa aka fitar sanda za’a gyarawa Mu’azzam wann b’angaren da shike lokacin da sunan Safeenah aka gyara sashen nan.. Da yanzu komai nata ne a nan.. Saidai kana Naka ne Allah na nashi.. Na Allah shine daidai dama ya tsaga rabonki ne.. Yo ba dole ma a shak’e gidan nan da kaya masu kyau da tsada ba sabida ansan Safeenah da son k’yale k’yale da gayu..” Tai maganar tana kurb’ar drink.

Jikin Sadiya yai matuk’ar yin sanyi da jin irin abubuwan da Aunty Shemaubke fad’i.. Ta sadda kanta k’asa d’ago sai tanaji kaman ita d’in ta tauye hakkokin Safeenah da yawa. Na farko Ta soma tarewa gidan Safeenar tin a can Abuja kafin Safeenah Ta shiga gidan yanzu gashi gidan da aka gina ma da sunar Safeenar ya zama nata.. Anya wann ba rashin adalci bane..? Bata kaiga nemo amsa ba ta sinkayo muryar Aunty Shemau naci gaba da fad’in “Kinga randa ya tasamma maki halin nasu na maza abin bazai ma iyayenki ciwo sosai ba..”

Gaba d’aya jikin Sadiya a sanyaye yake, kanta a k’asa tana sakin murmushin da daga gani kasan na yak’e ne.

Aunty Shemau taci gaba da fad’in “K’ila al’adarku ce maza ke yin kayan d’aki..?”

Sadiya ta d’an girgiza kai cikin rashin sakewa tace “A’a Aunty Al’ada iri guda mukeda shi.. Gidan mata keyin kayan d’aki.. Nawa iyayen ne basu da hali..Kuma ni marainiya ce banida kowa sai mahaifiyata da k’annena..”

Aunty Shemau tai rau rau da idanu ta taso da sauri ta dafa Sadiya tana fad’in “Allah sarki ‘yar nan.. Kiyi hak’uri Bansan haka abin yake ba.. Kiyi hak’uri kinji.. Allah sarki ashe dai ked’in marainiya ce.. Allah sarki bansan haka ba..”

Sadiya ta murmusa kad’an Wanda yafi kama da yak’e tace “Babu komai Aunty.. Ki daina bani hak’uri dan Allah..”

Aunty Shemau tace “Yo dole na baki hak’uri Amarya am.. Bansan ke marainiya bace.. Amma a halin yanzu ke ba marainiya bace dan tinda kika shigo ahali irin wann maraici ya k’are miki..”

Ta murmusa kad’an tana sadda kai.

Aunty Shemau ta tsareta da idanu cikin zuciyarta tana fad’in ‘kaji munafuka yanda take wane sanne kai’
A fili kuwa gyaran murya ta kumayi tana d’an dafa Sadiyar “Amma naji kince Bakida kowa..Sai mahaifiyarki da ‘yanuwanki. Toh ina ahalinki suke.. Dangin mahaifiya ko na mahaifi..?”

Zuciyar Sadiya yai wani irin yankewa dan batasan Ta yanda zata soma sanar da Aunty Shemau Dangin mahaifinta sun gujesu tun kafin a haifeta sabida zab’an mahaifiyarta da yayi a matsayin wacce zata zamto abokiyar rayuwarsa. ko kuma dangin mahaifiyarta da batasan duniyar da suke ba.. Bata kai ga bata amsa ba sallamar Mama Hindu ya katse su.

Hamdala tai cikin zuciyarta dan zuwan Hindu ya ceceta daga amsa tambayar Aunty Shemau.


Mama Hindu Ta sanar da Ita Inne ke kiranta. Cikin sauri kaman wacce take jira Ta mik’e tana amsawa.

Aunty Shemau ta d’auki sauran drink d’in da Sadiya ta had’a ta kawo mata tana sha tana fad’in zata Zo a koya mata irin wann drink d’in dan ta lurar hannun amaryar tasu nada albarka. Sai santin drink d’in take.

Sadiya tace “Aunty bari akai miki dama na had’a maku ne dasu Inne.. An kai na Inne tintinin dama na k’ofarki ne ban kai ba nace sai zuwa anjima zan kai..”

Aunty Shemau ta d’auka tana fad’in “Allah Sarki Amarya mai ruwan zak’i.. Toh bara na hutasarki na tafi dashi, ai kaw Uncle Salman na son irin wad’ann fresh drinks d’in da babu wani chemicals ciki babu preservatives..”

Mama Hindu ta amsa jug d’in daga hannun Aunty Shemau tana fad’in bari ta kai mata.

A tare suka jera suka nufo sashen Inne da Shemau da Sadiyar.

Suka gaida Inne gaba d’ayansu dan a parlor suka taddata.

Inne Ta dubi Shemau tace “Wai har yanzu ‘Yan biyu basu ida hutun nasu bane bazasu dawo haka nan ba.”

Shemau ta murmusa cikeda jin dad’in Inne na kewar jikokinta “Dama satin dama za’a d’aukosu Inne..”

Jinjina Kai Inne tai tace “Allah ya kaimu.. Ai gwara su dawo haka nan.. Da k’iriniyar tasu a waje yafi.. K’aramin k’afa a waje da dad’i..”

Shemau sai murmusawa take cikeda jin dad’i tana fad’in “Za’a d’auko Su Inne..”

Inne Ta dubi Sadiya tace “Kinyi magana da mijin naki ne..?”

Sadiya ta girgiza kai kad’an tana sadda kai k’asa “A’a Inne bamuyi magana yau ba..”

Inne Ta jinjina kai tace “Taw, nasan zai kiraki ya sanar dake... Adnan yana hanya yau.. Zuwa gobe in sha Allah zai d’aukeki zaku koma.. Sai ki fara shiri ko..”

Ba zata Sadiya taji batun.. Sai bata ce komai ba ta amsa ma Inne da fad’in “Toh Inne.. Can k’asan zuciyarta kaw dikda tana son kasancewa da mijinta dan tayi kewarsa amma wani b’angare na zuciyarta sam bai son rabuwa da Mamy.. Ta saba sosai da ita d’an zaman da sukai tare dan tare suke kwana sann kusan rabin d’awainiyar da Mama Hindu ke mata Sadiyar ke mata su yanzu.

Shemau kaw ji tai kaman an dab’a mata mashi.. Abin yayi kusa bazata samu Ta cimma Alk’awarin da taima Safeenah cikin gaggawa ba.. Ya zama dole Ta b’ullo da dabara.. Ya zama dole kafin wayewar gari tai executing plan d’inta.

D’an murmusawa tai tana fad’in “Allah Sarki Amarya zata tafi Ta barmu da kewa.. Gashi bata zaga taga dangi ba.. Dama Mu’azzam ya kamata ya zaga da ita toh gashi baya nan.. Har lokacin tafiyarta tayi..”

Inne ta d’anyi shiru sai kuma ta jinjina kai tace “Haka ne.. Ya kamata ta d’an zaga ta gaida dangi ta masu sallama.. Shemau sai ki mata rakiya zuwa yamma..”

Shemau ta jinjina kai cikeda jin dad’i “Tau Inne zan zaga da ita In sha Allah..”

Inne Ta dubi Sadiya tace “Tinda gobe zaku juya da yamma idan rana tai sanyi sai ki shirya Shemau ta rakaki gari kiga dangi koh..”

Sadiya Ta jinjina kai tana amsa dama Inne da “Toh Inne.” Lokaci guda Ta mik’e tana fad’in bari ta duba Mamy.

Inne ta jinjina mata kai tana mata izinin tafiya.

Suka bi bayanta a kallo daga Innen har Shemau. Murmushi saman fuskar Inne take fad’in “Yarinyar a natse take.. Modibbo yai sa’an iyali.. Allah ya nuna min d’iyoyinsu kafin ya amshi rayuwata.”

Shemau Ta murmusa tace “Zaki ga d’iyoyinsu in sha Allah Inne..”

Inne ta murmusa tace “Allahu yashaa.”

Shemau Ta amsa da Ameen kafin Ta mik’e tace bara ta duba taci kaman shigowar motar Uncle Salman k’ila ya dawo.

Inne ta jinjina mata kai tana mai gyara zaman k’afarta dake d’an mata ciwo. Ta bud’e murya tace “Ki fad’a wa Salman d’in Ina nemansa.”

Shemau Ta amsa da “Tau Inne.”

**

ABUJA

_National Police Headquarters (Force Criminal Investigation and Intelligence Department FCID)_


Carko carko sukai shida Yusuf bayan sun fito daga Babban meeting d’in da ya k’unshi manyan ‘yansanda daga cikinsu. An kuma d’aukan statement d’in Assad an basu kwanaki k’alilan su zak’ulo Danger yanda ya shiga ya fita.

Mu’azzam ya fuzar da fuci a karo na babu adadi yana shafan sumarsa, dole yai interrogating Assad koda bai yarda cewa Assad d’in mai laifi bane dan a halin yanzu abin ya fi nasa k’arfin ya isa yanda baiso ya isa ba.. Idan yana son wanke Assad dole sai ya kamo asalin b’eran dake cikin Department d’in.

Jikin Farin allo da hotunan mutane da case d’in ya shafa ya k’arasa ya manna hoton Assad jikinsa a matuk’ar mace.. Ya janyo arrow yai linking hoton Assad dana Danger yana jin kaman hannunsa na shaking.. Abotansu da abubuwan da sukai going through a rayuwa kawai yake tunawa kama daga lokacin da police academy har zuwa nasarori da k’alubale da suka fuskanta a aikin na D’ansanda.

Yusuf ya dubesa cikeda tausayawa kafin ya k’araso yana basa k’warin gwiwa.

“Komai zai shige.. Zamu wanke Assad, bazai losing aikinsa ba saidai ma ya samu k’arin yarda da matsayi.. In sha Allah zamu fitar da gaskiya daga cikin k’arya.. Nasan zaka iya Mu’azzam.. Kar ka karaya.. Kar ka nunama Azzalumai gazawarka.. Zaka kawar dasu da yardar Allah.”

Duban Yusuf kurum yai da idanunsa da suka kad’a sosai kafin ya maida dubansa fa hoton Assad da aka had’a da na Danger.

Ya d’an shafi sumarsa kad’an kafin yace “Kaje wann asibitin.. Mai ka samo so far.?”

Yusuf ya d’an ware idanunsa yana mai fuzar da fuci kad’an yace “I couldn’t find anything until now.. Na sa an min playing CCTV footage tin daga ranan da ka kai samples d’in asibitin amma wann ranan da ka kai samples d’in security Cameras d’in asibitin sun sami matsala..”

Mu’azzam ya dubesa yace “Kenan ba’a sami footage d’in wann ranar ba.?”
Yusuf ya jinjina kai alamun Eh..

Murmusawa yai da gefen bakinsa yana jinina kai kad’an “Na wann ranan ne kawai ya zama missing.. Why..? Maiyasa sai a ranan zai sami matsala..? Don’t you think this is too much of a coincidence..?” Yai maganar yana d’an bubbuga table d’in da marker dake hannunsa.

Yusuf ya jinjina kai yace “I thought as much.. Nayi tunanin haka nima..”

Mu’azzam ya d’an sosa hancinsa kad’an kafin ya dubi Yusuf yace “K’arya suka maka.. Wann footage d’in na nan kawai basu maka playing d’insa bane.. Wani wasa suke so su buga, but believe me we’ll turn the table on them.. Wann Rat d’in da muke nema shi ya shiga wann asibitin Yayi Sabotaging DAN Samples.. Idan muna so mu kamo b’eran nan sai mun fitar da wann footage d’in daga hannun securities d’in. I’m pretty certain footage d’in na nan biyansu akai dan Su b’oye dan na tabbata by now b’erayen sun san muna hunting d’insu.”

Yusuf yace “What if sunyi deleting..?”

Mu’azzam yai shiru yana nazarin Yusuf sai kuma yace “Ai asibiti ne bazasu goge record haka kawai ba.. Sannan sunsan test d’in is somehow related to police case. Dole akwai abinda sukai.. Nafi tunanin biyansu akai.. Amma kar ka damu zamu buga wasan sai mun samo wann footage d’in.”

Dai dai lokacin Maleeka ta shigo Office d’in. Mu’azzam ya mik’e daga saman table d’in da yai zaune bisa ya dubi Yusuf yace “I’ll interrogate Assad..”

Yusuf ya jinjina masa kai kafin ya shige.. Maleeka kaw sai dubansa take k’asa k’asa zuciyarta ba wane irin yankewa sabida taga irin firgitaccen duban da Mu’azzam d’in ke mata.

Yana ficewa Ta dubi Yusuf tace “Bansan mai naima Inspector Gamji ba. Ko kallo ban ishesa ba.. Na rasa shi wane irin mutum ne sam da yakeda tsananin ra’ayi.. Ba hurumin kowa yake shiga ba koda aiki tare ya had’aku idan ba dole ba Sai yaga dama yai involving naka.” Ta k’arashe tana zuba files d’in hannunta saman table.

Yusuf yaci gaba da tattara reports d’in dake saman table d’insa yace “I don’t blame him idan ya zab’i yai minding business d’insa.. Nowadays mutane ba abin yarda bane.. Kana tare da mutum ne bakasan yana cin dunduniyarka ba.. Excuse me..” Ya fad’i yana d’aukan folder d’in.

Tabi bayansa da kallo cikeda takaici dan Ta kula magana ya fad’a mata a dunk’ule..

Zuciyar Maleeka yai wani irin tsinkewa sanda wani tunani ya d’arsu mata cikin zuciyarta. Yanzu idan teburin ya juya fah..? Idan aka fahimci Assad baida laifi kenan fah itace zata tafi kurkuku alhali babu abinda ya had’ata da Danger tinda Ita dai masu Chief take

Please Login or Register in order to submit comment