Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Gidan da tai zaton bazata kuma dawowa cikinsa ba. Gidan da tai masa lak’abi da GIDAN ARO. Zuciyarta ne ya yanke sanda ta tuna tangamemen hotonsa da Safeenah da ake soma hangowa idan ka nufi staircase. Ta d’ago idanu tana duban spot d’in da hoton yake.. K’irjinta ya kuma bugawa sakamakon ganin nasu hoton da tai.. Hoton da aka masu suna zaune a park farkon fitarsu mission da sukai tare. Ya matso da bakinsa kusan kennenta yana fad’a mata dik abinda suke acting ne cikin mission ne Ita kuma Ta saki murmushi wanda tasan yak’e ne kawai amma sai gashi a hoton baiyi kama da acting ba. Komai looks real kaman dai soyayya ce ta gaskiya. Ta saki murmushi a hankali still idanunta na kan hoton.

Juyowar da zatai ta gansa tsaye bayanta fuskarsa babu yabo babu fallasa. Sai ta d’an sha jinin jikinta ta sadda idanunta kad’an.

Ta soma takowa a hankali ta K’araso gaba gareshi. Still idanunta a k’asa take furta “Fushi kake dani.?”

Bai ce mata komai ba Sai dubanta da yake.

“I’m sorry.. Bansan maganar zai b’ata maka rai ba.. Kai hak’uri kaji..” Ta k’arashe muryarta na rawa kaman zatayi kuka.

D’an takowa yai ya matso dab da ita sosai kafin ya kamo hannayenta, ta d’ago idanunta kwantattun k’walla tab cikinsu tana dubansa. Murmushi ta hango saman fuskarsa wanda ba lallai ka fahimci hakan ba sai idan domin kai akayi.
Ya juyar da ita had’ida rungumarta ta baya ya d’aura hannayensa saman cikinta, su duka biyun suna fuskantar hoton nasu.
“Did you like my surprise..? Tsarin gidan ya miki..?” Ya tambaya yana rank’wafo da kansa kad’an zuwa wuyanta.

Mr Inspector kenan komai nasa burgeta yake. Wato bazai amsa mata ba saidai ya nuna mata a aikace. Ta lumshe idanunta kad’an kafin ta jinjina masa kai ba tareda Ta iya furta koda kalma ba.

Ya murmusa kafin yaci gaba da fad’in “Nan gidanki ne.. Everything here is yours.. Komai da komai dake cikin gidan naki ne.. Including me..” Ya k’arashe cikin wane irin siga mai kashe mata jiki.

Hawayen da suka jima mak’ale cikin idanunta suka gangaro.. Ba komai ta tuna ba face farkon zuwanta gidan da ya jaddada mata cewa gidan tamkar dai GIDAN ARO yake a wajenta wanda za’a iya sallamanta ko yaushe.. ta zauna cikin shiri sann kar ta baje kolinta dan ga duk mai hankali da hangen nesa ba’a baje koli a GIDAN ARO. Sannan dik abinda aka ce maka na aro ne akwai ranan da za’a karb’i wann abun. Hausawa sunce Kayan aro baya rufe katara.. Sann dik daren dad’ewa zaka mayar da abinda aka ara maka..

Juyo da ita yai suna fuskantar juna, ya saka yatsarsa guda yana goge mata hawayen dake gangaro mata.

“Baki son gidan ne.. Ko tsarin ne bai miki ba..?”

Ta Ware idanunta tana dubansa “Komai yayi mun... Thank you for this wonderful surprise.. But do you know something..” Ya tsareta da idanu, yayinda taci gaba da fad’in “Kaid’in kafi mun duk abinda ka zuba cikin gidan nan.. Soyayyarka da k’aunarka a gareni sun isheni..” Ta jinjina kai kad’an hawaye naci gaba da gangaro mata “A baya wad’ann k’yale k’yaleni sune mafarki na kuma sune burin Sadiya.. Nayi zaton Sune kad’ai suke haifar da soyayya.. Nayi zaton idan babu su babu wata kalma da ake kira So.. Saidai bayan had’uwata da kai na yarda akwai wann kalma da ake kira So koda babu k’yale k’yale na rayuwar duniya wacce za’a tafi a barta a nan duniya.. Ba kaman mutane guda biyu da suka rayu domin Allah suka so juna dan Allah.. A ranan k’iyama Allah ya tadasu tare.. Shin akwai soyayyar da tafi wann..?” Murmushi da hawaye gauraye saman fuskarta. Yayinda Mu’azzam ya k’ura mata idanu yana jin kalaman nata har cikin b’argo da tsokarsa.

Ta kuma murmusawa kafin taci gaba da fad’in “Akwai abubuwa da dama da Allah zai baka a duniyar nan kasan cewa ya gama maka arziki.. Kaman dai arziki na lafiya wacce babu arzikin da ya kaita bayan kaancewarka musulmi mai kad’aita Ubangiji.. Bayan naga Mamy da halin da ta tsinci kanta ciki na jarabawa Tabbas na yarda k’yale k’yale na duniya ba komai bane face rud’i ne na d’an wani lokaci da yake k’ayadadde.. Mafarki na ne a baya na kasance cikin daula da tarin arziki... Amma a halin yanzu na shafe wann mafarkin.. Kaine mafarki na.. Kuma kaine cikan burina Mr Inspector... Ina fata na rayu dakai a nan gidan Duniya wanda yake GIDAN ARO ne.. Sannan a rayuwa na gaba Ina fata Allah ya kuma tadani da kai k’ark’ashin Inuwa guda a gidan Gaskiya.. I love you so much my Detective..” Ta k’arashe tana mai rungumarsa.

Rungumeta yai yana mai lumshe idanunsa shid’inma siririyar Hawaye ta gangaro masa “I love you.. I love you more my Beautiful Stubborn head.” Ya k’arashe yana mai kuma matseta jikinsa.

Soyayya suka dinga nuna ma junansu wanda ya tabbatar masu cewa sud’in sunyi kewan juna sosai da sosai. Babu kaman Mu’azzam wanda har saida Sadiyar Ta tausaya masa taga wautanta da tace zata kwana gida bayan shafe kusan sati da yai baya tare da ita.

**

Coin d’in ya dinga juyawa yana tuna lokacin da yake k’arami cikin stuff d’in mahaifinsa ya sami exactly irin wann coin d’in wanda tsakiya an rubuta _Black African Team_ mai hakan yake nufi.. Ya akai ya sami exactly irin wann coin d’in a wajen Habeeb k’anin Sadiya..? Kodai su Danger ne suka yasar da Coin d’in a gidansu Sadiya Habeeb ya tsinta..? Toh kenan wann coin d’in ta iya yuwa nada alak’a da su Danger kenan..? Toh amma idan wann coin d’in nada alak’a dasu Danger ya akai ya sami irinta a cikin kayan mahaifinsa..? Gaba d’aya kansa ya k’ulle.. Anya coin d’in iri guda ne..? Babu abinda zai had’a mahaifinsa dasu Danger.. Ya dafe kansa kad’an kafin ya furta a fili “Su waye su Danger.?” Ya bama kansa amsa da fad’in “Sune mutanen da suka kashe mun k’anwa Ikram..” “Toh idan wann coin d’in nada alak’a da mutuwar Ikram kenan ta iya yuwa mutuwar mahaifinsa ba accident bane..? What if shiryawa akai..? What if su Danger Sun jima suna bibiyan ahalinsa..? What if mutuwar Daddynsa shiryayya ne..? Zuciyarsa yai wani irin yankewa. Ya shiga girgiza kai yana dafe kansa wanda gaba d’aya ya masa nauyi komai ya cunkushe masa. Tunanin yanda ya aje wancan coin d’in ya soma.. Ya zama dole yai comparing coins d’in ya tabbata idan sunada kamanceceniya. Da wann tinanin ya aje coin d’in gefen bedside ya janyo sadiya dake bacci zuwa cikin jikinsa, ya lumshe idanu yana shak’an k’anshinta mai sanyi wanda ya sauk’ar masa da natsuwa cikin zuciyarsa.

**

A can Fufore kaw Shemau k’arfe shad’aya na dare ta soma bugun k’ofar gidan k’awarta Baddo.

Da k’yar Baddo ta k’araso ta bud’e k’ofa cikeda tsoro dan dama mijinta baya nan yayi tafiya ga yanda duniyar ta zama kowa kaffa kaffa yake da rayuwarsa.

A razane Baddo take k’ok’arin tura k’ofa tana karanto addu’o’i dan Ta zaci mahaukaciya ce ko gamo tai cikin daren.

“Baddo nice Shemau dan Allah kar ki rufe k’ofar.. Ki ceceni Baddo banida yanda zanje. A cikin uku nake..!”

Baddo ta dafe k’irji tana duban Shemau cikeda tsoro dan bata ma ganeta ba saida Shemaun tai magana “Shemau kece haka..? Mai zan gani ni Baddo..”

Kuka Shemau Ta fashe mata dashi tana fad’in “Baddo ki taimakeni.. Wllhi cikin tara nake bama uku ba..”

Baddo ta shiga salallami tana tafe hannaye tana duban Shemau cikeda tsoron duniya..



SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*55*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*






Baddo ta canza position d’in taguminta yafi sau abinda yafi “Ni babu abu guda dana fahimta Shemau. Kinaso kice mun tin jiya da dare abin ya faru.. Toh a ina kika kwana..?”

Gajeren tsuka Shemau tai “Duk wann ba lallai kiji ba Baddo tinda Allah ya taimaka na wayi gari.. Da ace jiya kika ganni nayi imani Bazaki ganeni ba.”

Baddo tace “Yanzun ma da k’yar na ganeki wllhi saida kikai magana.” Ta ida maganar tana aje mata plate d’in indomie da ta dafa mata.

Shemau ta janyo plate d’in ta soma nad’an abincin hannu baka hannu k’warya.

Baddo ta rapka uban tagumi tai zaune gefe tana kallon Shemau matar Alhaji Salman Gamji yanda ta fice a hayyacinta cikin lokaci k’ank’ani. Ta gyara zama tana kuma canza position d’in taguminta “Wai ni mi ya faru dake ne.. Mai ya jefaki cikin wann ukun..?”

Shemau ta dubeta sai kuma tace “Safeenah ce ta jefani cikin wann bala’in.”

Baddo ta girgiza kai tace “Safeenah kuma..?”

Shemau ta janyo ledar pure water ta huda tana zuk’a saida ta shanye tas kafin ta dubi Baddo tace “Yo Safeenah Ta jazamin da na d’auki shawarinta..”

“Kika d’auki shawarinta kaman yaya..?”

“Kinga Baddo ke k’awata ce kuma rugarmu d’aya tare muka taso.. Kin sanni na sanki babu wata ‘yar b’oyo a tsakaninmu dan haka zan fayyace miki dik abinda ya faru.” Ta gyara zamanta tana karanto ma Baddo duk abinda ya faru tin daga kan plan d’insu da mijinta na amfani da Safeenah da sukaso suyi har kawo yanda teburin ya juye zuwa kan Shemaun. Dik Ta sanar da Baddo saidai bata sanar da ita duk abubuwan da sukai da Mommy ba.

Baddo Ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Toh meye laifin Safeenah a nan..? Ai idan akwai mai laifi kece number one sai ko mijinki.. Shi da kikai abin sabida shi gashi bai gani ba ya cazga maki rashin mutunci ya kwance miki zani a kasuwa.. Ki gode ma Allah ma da ba kan idanun yaranki abin ya faru ba.. Dama shiyasa akace idan zaka gina ramin mugunta ginata gajeriya mai yuwa kaine zaka rufta ciki.. Yanzu ina ribar abinda kika so aikatawa ma wacce bataji ba bata gani ba.. Gashi ke kin kwan ciki kin rufta ciki wanda kikayi domin shi bai gani ba saima tozartaki da yayi a bainar duniya..”

Shemau ta katseta da fad’in “Salman baida laifi shawarin shashashar nan ne Safeenah da na d’auka ya kaini ya baro ni.. Banda ma b’atan baseera irin nawa mai zai kaini d’aukan shawarin da ya fito daga bakin Safeenah wacce batada ta cewa sai abinda aka tsara mata.. Zafin kishi ne kawai ya d’ibi Salman kuma nasan idan ya sauk’o zai fahimci cewa bani kawo masa maza cikin gida.. Tsaf zan wanke kaina a idon mijina dan har abada bazamu rabu ba..”

Baki sake Baddo ke dubanta kafin tace “Aw bayan wann mummunan wulak’anci da ya miki kina tunanin komawa gidansa.”

Da tsananin Mamaki Shemau ke duban Baddo “Toh ina zan koma..? Inada wajen komawa ne..? Ruga kike so na koma a titi kike so na k’arashi gantali na.. Nan gidan duniya bayan Salman da ‘ya’yana su waye nake dashi..?”

Baddo ta jinjina kai tace “Haka ne.. Dan ko kin koma ruga bana jin Inna Fini zata amsheki.. Kin wahala hannun matar K’anin mahaifinki.. Kin taso marainiya babu mahaifa.. Allah ya rufa miki asiri ya yaye miki wahalarki da k’uncinki kikai aure gidan masu arziki..”

Shemau ta jinjina kai tace “K’warai kaw Salman shine Gata na dan haka ko meye ya umarcen na masa zan masa matuk’a zan iya aiwatar da wann abin. Ina tsaka da shan wuya hannun Inna Fini ina kawo mata tallan Fura da nono cikin gari Salman ya hangoni daga cikin motarsa ya saye abinda nake saidawa ya kuma bini har rugarmu ya auroni dukda mahaifiyarsa bata so auren ba. Da shike yana k’aunata ya auroni ya tsame ni daga k’angin bautan gidan Inna Fini da Baffa. Akasi yanzun ma aka samu da rashin fahimta na tabbata zai fahimceni dan wllhi bazan koma hannun Inna Fini ba.. Ina nan cikin gari har ya hak’ura ya maidani kan ‘ya’yana.. Babu kalan bak’antani da Inna Fini da Baffah basuyi ba a idanunsa amma ya toshe kunne yace yaji ya gani zai aureni.. Har cewa sukai ni mayyace ni na cinye uwata zan lashe masa dangi amma dukda haka bai fasa k’udirinsa na aurena ba.. Toh ina kike tunanin zan koma Baddo bayan ma na riga na saba da rayuwar jin dad’i.”

Baddo ta girgiza kai tana murmusawa kad’an kafin tace “Tabbas Duniya karatu ta biya miki Shemau, bayan duk wann uk’uba da kika sha a rayuwa har zakiyi tunanin ki cutar da wani D’anadam bayan ke Allah ya cireki daga cikin wahalan..? Haba Shemau.. Ai idan wani zai mugunta wllhi ke bazakiyi ba sabida Kinsan abin Kinsan ya akeji idan aka cutar dakai.. Nayi matuk’ar mamaki da kikaso cutar da wata..”

Shemau tace “Baddo ya kike so nayi bayan wa mijina nake hakan.. Mutumin da ya zamto Gata da sutura a gareni.. So kike na juya masa baya ko me.?”

Baddo ta katse ta da fad’in “K’warai kuwa babu biyayya ma wani abin halitta wajen sab’awa Ubangiji koda miji ne ko mahaifa.. Zalunci haramun ne Allah ya haramta ma kansa zalunci sann ya sanya shi ya zamto haramun a tsakanin Al’umma.. Idan mijinki yace sai Kun cutar da wani sai ki nusar dashi idan yak’i ganewa ke dai kar ki aikata duk hukuncin da ya d’auka akanki sai ki bar wa Allah lamuranki da sannu zai samar miki mafita amma ba wai ki bisa duk ku zama mugaye ba dan ya taimakeki a baya.”

Shemau ta d’anyi shiru sai kuma tace “Mijina fah ba mugu bane Baddo shi hakkinsa kawai yake nema wajen Yayansa Marwan wanda yayi kane kane akan hakkin nasa.. Yayansu yayi yarjejeniya a rubuce cewa ya mallaka ma Salman assets d’insa da dukiyarsa toh Marwan bai baiwa Mu’azzam ba sann bai baiwa Salman ba mai yake nufi idan ba handamewa yai ba.. Kinga kuwa mijina fad’a kawai yake akan abinda yake nasa ne.. Mahaukaciyar d’iyarsa ce da muka saka cikin plan d’in Ita Ta b’ata komai. Bansan wani b’atan baseera ne yakaini amfani da shawarin Safeenah ba..”

Baddo Ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Koma dai menene sharrinku ne Allah ya maida maku kanku.. Ke kanki kince baki San wani b’atan baseera ne yakaiki d’aukan shawarin Safeenah ba.. Hakan kad’ai ya isheki ki gane ishara Allah ya nuna miki idan kinada rabon gyarawa amma idan kuma Bakida niyyan gyarawa wann ke ya ragema.”

Shemau ta dubeta had’ida tab’e baki kad’an kafin tace “Kinga ni bacci ma nake ji, kar ki damu ko a nan parlor zan kwana dan nasan gidan naki d’akuna biyu ne d’aya naku d’aya na yara.. Yo gidan ma babu AC bansan ya zanyi nayi bacci ba..”

Baddo ta tab’e baki tace “Ke kika San wann.. Ni mijina ma baya nan.. Bara na kawo miki abin shimfid’a.” Ta k’arashe tana mai mik’ewa.

Shemau tace “Yama fi da baya nan.. Kafin ya dawo zan koma gidana.. Ina zan iya wann rayuwa..” Ta k’arashe tana mai gyara kwanciyarta.

Baddo dai girgiza kai kurum tai ta shige abinta ta bar Shemau nan kwance tana lissafi.
**
ABUJA

Musaddiq na shirin kwanciya Safeenah ta turo d’akin ta shigo sai sakin huci take.

Da mugun mamaki yake dubanta kafin ya jinjina kai kad’an yace “Kin dai San ni ba k’aramin yaro bane da zakike shigo min d’aki kai tsaye.”

“Bafa zan k’yaleka ba Musaddiq sai ka amsa min tambayata.. Ka fad’a min Idan tareda shegiyar matar Mu’azzam kuka dawo.?”

A tsananin kufule yake dubanta, yana tuna sharrin da suka tasamma d’aura ma Sadiya itada Shemau. Yai k’wafa kad’an kafin yace “Ki fice mun a d’aki Feenah..”

“Bazan fice d’in ba ank‘I a fice Ai dama gaskiyar Mommy ne tare kuke k’ulle k’ullenku kaida Mu’azzam.. Shiyasa kullum bayansa kake bi baka ganin laifinsa kaima.. A gaban idonka ya zab’i wancan Karuwar ya k’yaleni ina’yaruwarka harda wani binsu ka take masu baya kuyi tafiya.. Kai a dole ga mai rik’e masu jaka ko..”

A kufule wann karon yayo kanta yana nunata da d’an yatsa “Be thankful.. Ki gode ma Allah ban sanar da Mu’azzam abinda kuka tasamma yima matarsa ba Keda Aunty Shemau.. Kuma wllhi idan baki daina shiga hidiman gidan Mu’azzam ba zan miki abinda baki tab’a tsammani ba Safeenah.!”

Baki sake Safeenah ke dubansa “Eh lallai Musaddiq na yarda k’wayan Naka basa fad’a maka daidai.. Ni kake nuna ma yatsa kaman zaka daka.. Kawai ka dakeni sai nasan ka cika masoyin Mu’azzam.. Laifin Mommy ne da tuntuni bata jefa ka a Rehabilitation centre ba..”

“Nida ke waye yafi buk’atan tafiya Rehab.. Dalla Malama fice min a d’aki..” Ya k’arashe yana mai janyota ya turata waje.

Har zai maida k’ofar ya rufe ya dakata kad’an yace “Sai Ki kira Ally d’in naki ki mata jaje..!” Yana ida fad’in haka ya maida k’ofar ya rufe akan fuskar Safeenah.

Huci kurum take tana murza tafin hannunta.. Kardai plan d’insu backfired.. Taiyita kiran layin Aunty Shemau bai shiga.. Toh meye ne ya faru..? Wato kenan Sadiya ta dawo gidanta.. Ai kuwa sassafe zata tafi gidan ta gane ma idanunta hakan. Tai k’wafa kafin tasa kai ta wuce cikin tsananin b’acin rai.

**

Ni’imtaccen k’amshi ne mai gauraye da natsuwa ya tadashi daga baccin nasa.

Ya mik’e yana karanto addu’an tashi a bacci fuskarsa d’aukeda murmushi. Cikin zuciyarsa banda hamdala da gode ma Ubangijinsa baya komai. A haka ya mik’e ya nufi bathroom yayo wanka ya fito ya soma shirin fita Office.

Tin daga staircase yana sauk’owa yasan matar gidan gwana ce wajen tsafta, ko ina need Sai k’amshi dake tashi ga na room fresh gana turaren k’una dake tashi a natse cikin electric burner, ga na abinci na bada nasa kalan shima.. Gidan sai ya bada wani kalan k’amshi na musamman.

Can ya hangota cikin kitchen tana tsaye jikin working base tana chopping onions saman chopping board. Tana sanye ne cikin maroon top da ya kama jikinta d’amas Sai black three quarter wanda shima yai fitting d’inta. Sumar kanta ta tupkesa waje guda tayi ponytail style dashi. Tayi kyau sosai har kaman bazai iya janye idanunsa daga barin dubanta ba, just like a berbie.

Ya soma takowa a hankali ba tareda ya bari tai noticing d’insa ba, abinka da yankan albasa bama ta lura na zuwa ba hankalinta kacaukam naga abinda take. Chapp taji hannun mutum saman cikinta. Ta d’an saki k’ara a razane.

“Good morning Beautiful..!” Ya fad’i still tana nan rik’e cikin jikinsa.

“You scared me... I almost chopped my fingers.” Ta fad’i kaman zatai kuka.

Murmusawa yai yana kuma shigar da kansa cikin wuyarta “Every little thing scares you..” Ya k’arashe yana juyo da ita suna fuskantar juna. Hannayensa saman k’ugunta yayinda Sadiyar ta d’ingile k’afafunta ta zuba nata hannayen saman shoulders d’insa dan kar ta b’ata masa jiki da onions.

“You look fantastic.. I love you..” Ya fad’i yana bata light kiss.

Murmusawa tai kad’an kafin tace “Thank you... Handsome.”

Ya murmusa yana mai lakatan hancinta kad’an “K’amshi ya cika mun ciki tin daga upstairs.. Mai ake dafa mana ne..?”

Ta d’an marairaice fuska tace “Kai Handsome nothing special fah.. Kawai chicken Sandwitch ne served with black tea..”

“Sounds delicious.. But I think I’ll just have the tea.. Sauri nake suna jirana a office..”

Tai rau rau da idanu tace “Kai dan Allah Bazaka tsaya ka karya ba.. Kaga fah I’m almost done, onions d’in nan kawai zan zuba..Oh no no I’m sorry.. Bansan da wuri zaka fita ba.. I should have waken up earlier..” Tana maganar tana k’ok’arin rounding up.

Hannayenta ya kamo yana fad’in “Relax Beautiful.. It’s okay.. Na gode da kika tashi as early as you can bayan gajiyan hanya da kika kwaso.. You don’t need to stress yourself.. Badon Ina sauri ba zan tsaya naci, na riga na makara ne.. Ban saba makara ba suna can suna jirana..” Ya d’an kashe mata idanu guda kafin yace “But I guess ke kika sa na makara..”

Ta zaro idanu waje tace “Ni kuma..! How am I at fault.?”

Ya janyota jikinsa kad’an yana mata wasu salon kafin yace “Because last night I slept beside you shiyasa na makara..”

Ta rufe fuskarta kad’an cikeda kunya. Daidai nan wayarsa ta soma ruri.. Yusuf ne mai kira yai saurin cirota a aljihu yana fad’in “See, suna jirana.. I’ve to go now.. Take care I love you.” Ya fad’i yana manna mata peck a cheek d’inta.

Ta biyosa tana fad’in “Toh tea d’in fah bazaka sha ba..”

“Kiyi hak’uri na makara I’ll make it up to you next time..” Ya k’arashe yana mai shigewa Mota.

Ta d’ago masa hannu tana masa waving. Ya sakar mata murmushi yana d’an kashe mata ido guda lokaci guda ya juya kan motar ya fice.

Ta juyo ta komo cikin gidan tana fad’in “May Allah always be with you my Inspector..” Haka ta k’arasa cikin gidan taci gaba da abinda take. Dik Sai ta kasa cin breakfast d’in itama. Kusan duka ta juye ma Patrick. Ruwan tea d’in da Aunty Larai ta bata kawai taita sha.

**


_Police Headquarters_


Motar prison ne ta k’araso aka fito da Assad hannayensa rufe cikin handcuffs. Hajiyarsa ta fashe da wani irin kuka Shaheed k’aninsa na rik’e da ita kaman zata duk’a k’asa sabida kuka. Shaheed sai tausan ta yake cikin k’arfin hali. Ya rik’ota Ta zauna saman wasu kujeru dake a k’ofar wajen.

Mu’azzam ya hangosu daga nesa tausayin mahaifiyar Assad fal zuciyarsa, da k’yar ya k’araso wajensu yana jin zuciyarsa na masa wani irin rauni.
Baima san mai zai soma fad’i ba, baisan da wasu irin kalamai zai lallashi mahaifiyar Assad ba.

Cikin kuka take duban Mu’azzam tana fad’in “Ya fad’a da bakinsa.. Ya amsa cewa yaci amanar aikinsa.. Maiyasa zai aikata haka.. Maiyasa Mu’azzam..Mai yake nema da tsanani a duniyar nan.. Bai duba maraicinsa ba bai duba d’iyarsa da yake fafutukan amsowa daga hannun matar can a Kotu ba..” Kuka ya hanata ci gaba da magana.

“Hajiya Assad baida laifi.. K’age aka masa.. Baici amanar k’asa ba.. Baici amanar aikinsa ba.. Inada tabbacin abokina ba D’antadda bane.. Kuma zan tabbatar ma kowa hakan da izinin Allah. Ki kwantar da hankalinki kinji.. In sha Allah komai zai wuce.. Allah zai fidda Assad daga wann bak’in k’ulli da aka masa..”

Hajiya bata iya amsa sa ba sai kuka da take.

Ya dubi Shaheed yace “Take her home.. And make sure ta sami hutu.. Zan kula da case d’in Assad..”

Shaheed ya jinjina kansa yana mai amsa ma Mu’azzam d’in. A tare shida Shaheed suka kai Hajiya Mota Shaheed na rik’eda Ita tana cazgan kuka tana kama k’irjinta. Kai da gani kasan ba lafiya take ba.

Shaheed ya dubi Mu’azzam yace “Mun gode K’warai Inspector da d’awaniyarka.. Allah ya saka maka da alkahiri.”

Mu’azzam ya dafa hannun Shaheed yace “Kar ka mun godiya.. Banyi rabin abubuwan da Assad ya mun a rayuwa ba.. Nida Assad are practically brothers so dan na masa wani abu ba favor bane dole akaina nayi.. Ka kula da mahaifiyarku na maka alk’awari in sha Allah D’anuwanka zai fito.”

Shaheed ya jinjina kai a hankali yana kuma godiya wa Mu’azzam d’in kafin ya shige ya tada Mota.

Maleeka dake tsaye daga can gefe akan idanunta komai ya faru. Babu abinda ya d’aga mata hankali kaman ganin mahaifiyar Assad da tai cikin yanayi na tashin hankali.. Sai ta tuna nata mahaifiyar dake kwance gida tana jinya wanda duk kud’ad’en da take samu daga wajen su Chief ma ita take turawa. Hawaye guda d’aya ya gangaro mata.. Meye laifinta dan ta amshi kud’ad’e ta tura ayima mahaifiyarta dake tsananin jinya aiki.. Shin kowa bazai komai domin ya ceci mahaifiyarsa ba.. Tai saurin juyawa ta shige building d’in. Restroom ta shige tana cazgan kuka. A fili take furta “Meye laifina.. Meye laifina dan naso taimakon mahaifiyata..?”

Zuciyarta ya soma tuhumarta “Idan wanda kika d’aura ma sharri ya rasa nasa mahaifiyar fah ke taki ta rayu shin wane riba kika samu a cikin hakan.. Shin kin mance duk kalan abubuwan alkahiri da Assad ya miki..? Shin kin mance gwagwarmayar da kuka sha tare.? Shin kin mance barkwancinsa musamman a lokutan da kike tsananin son ganin Inspector Gamji ya kula ki.. Assad was there for you.. Yana k’ok’arin kwantar miki da hankali dukda yasan Abokinsa baki ishesa kallo ba balle ki shiga cikin jerin matan da yake so.. Shin duk kin mance abubuwan da Assad ya miki Maleeka.? Why Assad..? Why him.. He’s a good guy.. A kindhearted wanda a koda yaushe baida burin da ya wuce ya kyautata ma mutane.. Assad bai cancanci haka ba. Ta rintse idanunta hawaye na gangaro mata. Daidai lokacin wayarta ya soma ruri.. Ta saka hannu ta d’auka k’aninta ne yake kira daga gida..

Daga yanda taji muryarsa tasan babu lafia. Cikin kuka take tambayarsa meke faruwa.. Nan take ya sanar da ita Mahaifiyarsu

Please Login or Register in order to submit comment