Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakinki kuma kar ki sake zagar mun mata, a yanda take a nakashe tafimun ke sau babu adadi.. Kuma da sannu zaki gani Allah zai bata lafiya ta dawo cikin gidan nan.. Tamkar bata tab’a jinya ba..!”

Ya dubi Safeenah yace “Shige muje..”

Babu musu Safeenah ta janyo suitcases d’inta tabi bayan Daddy. Aka bar Mommy baki sake tana duban bayansu har suka fice.. Yau itace Marwan yake cewa nakasasshiyar can ta fi masa ita, matar da ma cushe aka masa ba cewa yai yana sonta ba tun fil azal.. Lallai tun kafin ta makara gwara ta tura Shemau ta koma ta duba mata wanne hali Nuratu ke ciki.. Da wannan tunanin Mommy ta haura sama tana kiran Shemau.

Shemau tana jin Mommy na kiranta tai rounding up wayar da suke da mijinta Salman.

Ta dubi Mommy dake sakin huci ta tambayeta ya akai. Mommy ta sanar da ita komai cewa Daddy yakai Safeenah gidan Mu’azzam dukda irin cin kashin da Mu’azzam d’in yai masu, harda cewa da Daddy yai Nuratu tafi masa Ita.

Tab’e baki kad’an Shemau tai tace “Ai kuwa gwara ki tabbata Nuratu bata sami lafiya ba dan da alama mijinki ya fara sonta tin kafin ta warke daga jinya.. Ina ji miki tsoro kar ta dawo Gidanki a kan k’afafunta bayan an fitar da ita a kwance.”

Mommy ta sauk’e fuci tace “Kin mance cewa gidan mijina tamkar dai GIDAN ARO yake a wajenta.. Ai yanda aka fitar da ita a kwance Saidai a turata rami a haka.. Gidana ya haramta a gareta.. Yanda idan aka mutu ba’a sake dawowa Gidan Duniya haka itama yanda Ta fice daga gidan nan bata kuma dawowa.. Shemau ya kamata ki koma gida tinda dai Safeenar ta tare ki duba mana halin da nakasasshiyar cen ke ciki.”

Shemau ta jinjina kai tace “Gawa zakice dan kullum jikinta dad’a gaba yake yanzu haka wayar da nayi da Salman abinda ya sanar dani kenan cewa jikin Nuratu yak’i dad’i har Inne ta fara tinanin ko mai magani za’a canza..”

Mommy ta zaro ido dafe da k’irji tace “Shemau kar ki bari a canza mai magani.. Asirinmu zai tonu.!”

Shemau ta murmusa kafin tace “Baki da damuwa hakan bazai tab’a yuwa ba.. Bazan bar hakan ta kasance ba. Yanzu Salman yace zai taho Abujan gobe Ina tsammanin Business trip ne, zai kwana biyu sai mu koma tare. Kinsan nace miki Su Husna sunata shirin waec ga twins ma na barsu wajen mai aiki gwara na koma sai naci gaba da saka mana idanu kan Nuratu.”

Mommy ta jinjina kai tace “Hakan yayi.. Allah yasa kafin gobe muji Labarin nakasasshiyar nan ta mirgina..”

Suka saki shewa suna masu tafe hannaye.

**

Assad yana k’arasowa yai masa knocking da yatsar saman glass, lokaci guda Mu’azzam d’in ya danna unlock Assad ya ya bud’e ya shiga.. Kallo d’aya yaiwa Mu’azzam d’in ya basa tausayi.. Kai da gani Kasan abubuwa sun taru sun masa yawa k’arfin hali kurum yake.

Assad yace “Ya jikin Mamy..?”

Lumshe idanunsa kad’an Mu’azzam yai a hankali kafin yace “Munyi waya da Inne da safe tace mun jikin nata da sauki an gode Allah..”

Assad ya jinjina kai yace “Allah ya bata alfiya yasa kaffara ne.. Allah ya tashi kafad’unta..”

Mu’azzam ya amsa da “Ameen ya Allah..”

“Safeenah fah..? Wanne kake ciki da nata batun..?”

Ya d’an tab’e bakinsa kad’an kafin yace “I still don’t know.. Ban Sani ba Assad..”

Assad ya fuzar da fuci kad’an cikeda tausayin Mu’azzam d’in kafin yace “Kar ka damu Mu’azzam Ubangiji yana jarabtar bayinsa ta ko wacce hanya.. Ba wai yak’ika bane yake aiko maka da jarabawa daki daki, daga wannan sai wancan.. Kai hak’uri sannan kai addu’a Allah ya baka ikon cin jarabawarka Brother..”

Mu’azzam ya d’an kaikaito ya dubi Assad d’in kafin ya jinjina kai a hankali ba tareda ya iya furta koda kalma ba.

Assad yace “Ta ina zamu fara yanzu..?”

Mu’azzam ya d’ago yana dubansa kafin yakai ga basa amsa wayar Daddy ya shigo masa.

“I’ll take this call, Daddy ne mai kira.”

Assad ya jinjina masa kai ba tareda yace komai ba.

Mu’azzam ya d’aga da sallama yana mai gaida Daddyn.

Daga d’aya b’angaren Daddy ya amsa cikin sakin fuska kafin yace “Baka gida ne, gashi munzo bamu taddaka ba sai gateman.”

Ya d’an dubi Assad kafin ya girgiza kai cikeda mamakin jin Daddy yana gidansa “No bana gida Daddy. Ai na fice..”

Daddy ya jinjina kai yace “Toooh da kuwa gashi na taho da Safeenah ce zan had’aku gaba d’aya harda d’aya matar taka nai maku nasiha.”

Jin abinda Daddy yace ya sanya Mu’azzam ware idanu babu shiri yana jin wani abu na neman toshe masa mak’oshi.. D’an girgiza kai yai kafin yace “Daddy you mean, ka kawo Safeenah yanzu haka..?”

Daddy yace “K’warai kuwa Mu’azzam, na kawo maka matarka dan zaman nata a gida can baida wani alfanu.. Kyaun mace mai aure ta kasance a d’akinta shine cikan mutuncinta.. Sannan kaima shine cikan Kamalarka..”

Mu’azzam ya jinjina kai a hankali kafin yace “Haka ne Daddy..Amma yanzu bana gida and.. Bazan dawo gida nan kusa ba..” Yai maganar cikeda jin nauyin Daddy.

Daddy ya d’anyi jim kafin yace “Tooh lafiya dai koh..?”

Mu’azzam ya jinjina kai kaman Daddy na ganinsa “Eh.. Eh wani aiki ne ya taso mun shisa zan d’an makara.”

Daddy yace “Af Toh ai babu komai, nan gaba sai na had’aku na maku nasiha.. Ina ita matar taka take..?”

Mu’azzam ya dubi Assad dan baisan mai zai sanar da Daddy ba.. Baisan ta yanda zai soma fad’a masa cewa Sadiya ta gudu daga gidan ba. Ya d’an shafi fuskarsa kad’an kafin yace “Bata gida inaga taje can wajen mahaifiyarta..”

Daddy yace “Allah sarki toh shikenan.. Allah Ubangiji ya zaunar daku lafiya ya had’e maka kan iyalanka.. Allah shi maku albarka gaba d’ayanku..”

Mu’azzam yanata amsa masa da Ameen kafin Daddy yai masa sallama yana mai sanar dashi ya bar Safeenah a gidan shi kuma ya koma gida.

Suna ida wayar Mu’azzam ya dubi Assad yana mai kuma tura yatsun hannunsa cikin sumarsa.

Assad ya d’an girgiza masa kai alamun meke faruwa.

Mu’azzam ya d’aura duka hannayensa saman steering yana mai kuma fuzar da huci, idanunsa naga glass na gaban motar yake furta “Daddy yakai Safeenah gidana..”

Assad ya murmusa yace “Kaga mai tagwayen mata.. Baka Farin ciki da hakan ne..?”

Da wutsiyar idanu ya dubesa kafin yace “If she’s still my wife it’s because of Daddy..”

Assad ya d’an girgiza kai kad’an yace “Mu’azzam, Safeenah batada wani laifi.. Kawai dai she got trapped ne.. Gashi Allah ya wanketa. Su Danger sunso saceta ne suka sace Ikram. At least ka godewa Allah da ya wanke Safeenah.. Ko Babu komai ‘yaruwarka ce kuma matarka ce

Still da wutsiyar idanu yake dubansa kafin yace “Ka mance text d’in BAD ne.. I’m pretty sure D’aniskan Lauyan nan shine BAD.. Ban kuma yarda da sak’on BAD ba har Sai na isa k’arshen binkicen nan.”

Assad ya jinjina kai a hankali kafin yace “Ta ina zamu fara yanzu.?”

“Suleja..” Mu’azzam ya basa amsa kafin yaci gaba da fad’in “Babu yanda zatai tunanin zuwa sai nan, na tabbata can zata tafi ta nemi mahaifiyarta da ‘yanuwanta.”

Assad ya jinjina kai kafin yace “Let me drive..”

Mu’azzam ya murmusa yace “Kai haba rangwancin nawa ai bai kai nan ba.” Yana maganar yana tada motar had’ida d’aukan hanya.

**

Daddy yana tafiya Safeenah ta dinga zagaya gidanta tana imagining kalan cin amanarta da Mu’azzam yai a cikin gidan da wannan ‘yariskan yarinyar. Tai tsaye tana duban Parlorn sai taga kaman tana hangosu saman kujera Mu’azzam na zaune yarinyar tayi matashi da cinyarsa. Tai saurin rintse idanunta tana jin zuciyarta na mata wane irin zogi da k’una. Can taga kaman ta soma hangosu yana mata cakulkulkuli tana dariya tana zillewa.. Har kaman shewarsu takeji cikin kunnuwarta suna wasanni irinta masoya a parlorn gidan dikda kuwa tasan mislkilanci irin na Mu’azzam.. Ta sak’i k’ara tana mai toshe kunnuwarta “Enough Feenah..!” Ta daka ma kanta tsawa da fad’in haka “This is just your imagination.. Mu’azzam would never do something like this musamman da k’aramar yarinya irin wannan.. Asiri tai masa kawai shiyasa ya aurota ba tareda sanin kowa ba..!” Ta k’arashe zancen nata tana sakin huci kafin ta haura upstairs.

Ta jima tana duban hoton su itada Mu’azzam na ranan aurensu dake lik’e a hanyar matakalan. Lokaci guda Safeenah ta isa jikin hoton tana sakin murmushi tana shafa hoton a hankali musamman b’angaren Mu’azzam. Sunyi kyau har sun gaji, sannan sun dace da junansu.. Ta kuma sakin murmushi har lokacin shafa hoton take “Hakan ya nuna tabbacin ni ce a zuciyarka My Halal.. Da ace wancan ‘yariskar tanada matsayi na tabbata da baka aje hoton nan a nan ba.. I’m the Queen of your heart Mu’azzam.. And I won’t allow any woman ta sace mun wannan matsayin a wajenka.. I’ll do whatever it takes to make sure banyi sharing d’inka tareda wata ba.. You are mine.. Alone..!” Tana ida fad’in haka ta nufi nata d’akin tana k’are ma d’akin kallo.. Kaman babu wanda ya zauna ciki, komai tas tas harda hotonta gefen bedside Mu’azzam ya aje. Ta kuma sakin murmushi tana duban hoton saidai hango kaya jere cikin wardrobe da tai ne ya sanya zuciyarta tsinkewa.. Ta isa ta bud’e ta shiga firfito da kayayyakin tana watsi dasu wasu tana kekketa su da hannayenta musamman da taga dik dangin English wears ne..
“I curse you.. I curse you.!! I curse you..!!” Haka ta dinga fad’i tana keta kayyakin tana watsi dasu. Taci gaba da sakin huci kafin ta nufi bathroom d’in tana k’are masa kallo.. Harda kayan wanka dasu shampoo.. A fili ta furta “Shegiya Karuwa.. Idona idonki sai na kasheki..!” Ta tattaro kayan wankan danginsu shower jell dasu Shampoo ta dinga matsesu tana zubar dasu cikin toilet seat saida ta zubar dasu kaf tai flushing d’insu tana sakin huci kafin ta fito ta nufi ta nufi nasa d’akin. Haka kurum taji gabanta yayi wani irin yankewa sanda ta hangi saman gadon.. Muasamman data lura saman gadon is kind rough alamun an kwanta ba’a gyara ba.. Take wani tunanin ya soma d’arsuwa zuciyar Safeenah.. Tai saurin rintse idanunta tana bud’e hannayenta take furta “Enough Feenah.. Nothing happened, kawai dai ya kwanta ne ya tashi bai gyara gadon ba.. And that’s all.. Yanzu sai ki gyara masa and play a perfect wife role..” Ta d’an rausayar da idanunta kafin ta haye saman gadon tana mai tattaro pillows d’in..

K’amshin da hancinta ya jiyo mata cikin pillows d’in shi tasa zuciyarta kusan bugawa, dan k’amshin shower jell da Shampoo d’in da ta gama juyowa cikin toilet taji.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Tare fah suke Kwana kenan.. D’akin mijinta wanda ko tarewa basuyi ba.. Gashi ya tare da wata Karuwa tana can baki sake.. Take taji kuzarin jikinta sun tafi gaba d’aya.. Ta koma ta silale tana jin wane irin kuka gauraye da k’unci na taso mata.. Haka ta dinga kuka tana fatali da kayayyakin dake cikin d’akin.. Saida tai mai isarta kafin Ta danni kanta da fad’in “Feenah kuka bai ganki ba.. You need to be strong if you want to get your husband back.. Think Feenah..!” Ta soma kame kanta tana tinanin abinyi tinda dai yanzu babu Meema mai bata shawari. Murmushi ta saki still hawaye na gangaro mata sanda ta tuna abinda zatai. Nan kuma ta hango takarda yashe a k’asa.. Ta rarrafa ta d’auki takardan tana juyawa, rubutun da ta gani jiki shi ya bala’in kashe mata jiki ya kuma haifar mata da bugawan zuciya. Na farko na Mu’azzam ne yana umartan Sadiyar da tai wankan tsarki dukda babu abinda ya faru.. Sai note d’in da Sadiyar ta bar masa a k’asa na cewa bazata tab’a yafe masa ba kan abinda yai niyyan mata sannan mission d’in ya k’are..

Safeenah ta gyara zama sosai tana nazarin rubutun, idan taso fahimtar wani abu kenan zaman mission wann ‘yariskar tai a gidanta..? Toh kodai da gaske ba zaman auratayya sukeda Mu’azzam ba..? Kardai auren yarjejeniya ne shiyasa yace wa Daddy zaiyi bayani..? Toh amma wane irin mission kenan..? Ta kuma tambayar kanta.. Toh koma dai menene mission d’in ta tabbata kusantar yarinyar yasoyi kenan.. Mu’azzam d’in da tai masa shaida babu ruwansa da mata ashe hauka take gashi har zai ma wata da k’arfi ita tana can tana bibiyarsa ko kallo bata ishesa ba.. Zuciyar Safeenah yaci gaba da harbawa cikin sauri.. Babu abinda ya tsaya mata kaman cewa da Mu’azzam yai cikin note d’in ‘Thank you for taking care of me last night’. Safeenah ta shiga keta takardan tana kuka tana birgima a wajen.

**

Suna isa gidansu Sadiya suka tadda kaman Kufai, babu kowa sannan babu alamun kowa wajen, Mu’azzam yai tsaye yana tina farkon zuwansa layin wanda bincike ya kawosa, ya tuna had’uwarsu Ta farko a lokacin da suka bangaji juna, ya tuna jifarsa da ultra pad da tai, ya tuna randa ya aureta ya kuma sunkuceta ya tafi da ita.. Haka ya dinga tina every bit na abubuwan da suka faru tun bayan had’uwarsa da ita.. Saman dakalin k’ofar gidan ya zauna yana mai d’aura hab’arsa saman hannayensa da ya had’e waje guda.

Assad da k’arasowarsa kenan bayan yabi layi layi yana tambaya ko sunga Sadiya amma babu wanda yace yaga Sady Pretty sannan Mahaifiyarta ma da ‘yanuwanta har yau basu san yanda suke ba, babu wanda ya kuma ganinsu a unguwar.

Assad ya k’araso kusan Mu’azzam d’in yana mai girgiza kai “Mu’azzam negative..! Babu wanda ya ganta, da alama batazo nan ba.. Sannan k’awarta Sabeera sun bar gari..” Ya k’arashe cikin sanyin murya.

D’agowa Mu’azzam yai ya dubesa kafin ya jinjina kai a hankali ya mik’e yana kuma duban gidan.. Inama ya ganta a gabansa, inama ya ganta tana fitowa daga cikin gidan.. Ya kuma fuzar da fuci kad’an kafin yace “I’m not leaving this place har Sai na ganta.. Nan kawai zatai tunanin zuwa. I’m hundred percent positive.. So you go Assad.. Ni zan tsaya a nan..”

Assad ya d’an girgiza kai kad’an yana mai zama gefen Mu’azzam d’in nan saman dakalin.

Wayar Mu’azzam ne ya soma ruri, ya ciro daga aljihunsa yana duba mai kiran, ba kowa bane face Safeenah.. Bai d’aga ba sai maida wayar da yai cikin aljihu. Bata fasa kira ba.

Assad ya dubesa yace “Bazaka d’aga ba.. It might be something serious..”

Gajeren tsaki yai yace “Assad, don’t you think I have a lot on my plate already. Banida lokacin haukar Safeenah..”

“She’s still your wife Mu’azzam.. She’s your responsibility.. Ya kamata ka d’aga kaji meke faruwa.”

Ya d’an fuzar da fuci kad’an kafin ya d’aga kiran.

Kukan Safeenah ya soma jiyowa tana fad’in Tasan komai duk kalan cin amanarta da yai shida wancan ‘yariskar da sunan mission.

Ya lumshe idanunsa kad’an kafin yace “Look Feenah.. I don’t have time for your stupid tantrums.!”

Katsesa tai da fad’in “Bakada lokaci na amma kanada lokacin shirya mission a bayan ido na hardai ka tasamma raping d’in ‘yar mutane. Ko kunya bakaji ba kana da mata kaman Safeenah Gamji amma kaje kana k’ok’arin aikata fyad’e wa k’aramar yarinya.. Kodai shima cikin mission d’in naka ne..?”

Assad kaw matsawa gefe yai yana amsa wayarsa wanda ya soma ruri.


Da Mamaki Mu’azzam yace “Mai kika ce Safeenah..?!”

“Kaji sarai abinda nace, Wllhi ko ka dawo gida ka kula dani ko na sanar da Daddy ga irin auren da kayi Kasan sarai Daddy bazai lamunci irin wannan auren ba musamman idan yaji cewa auren mission ne.. Sannan harda fyad’e ka tasamma yi a matsayinka na jami’in tsaro.”

Gyara zamansa yai kafin yace “First of all kar ki sake cewa na tasamma yin fyad’e wa matata ta sunna.. Secondly, don’t you dare threaten me Safeenah, for as far as I know, I didn’t do anything wrong.!”

Safeenah ta jinjina kai tace “I’m not threatening you, I’m only saying the fact.”

Mu’azzam ya fahimci cewa Safeenah Ta tsinci note d’in da suka bari ma juna ne shida Sadiya. Hakan yasa ya jinjina kai yace “Okay, well.. Go ahead and tell Daddy.. Kije ki fad’a ma duk wanda kikaga dama cewa ni Mu’azzam Gamji nayi auren mission sannan idan kinje fad’a kice na tasamma kusantar matata wacce nai mata mummunan fahimta daga farko.. And after na fahimci cewa she’s a total opposite of duk abinda nake zato kanta sai na fasa kusantarta dan ba a haka ta cancanci nazo mata ba, because she deserves nothing but the best.!” Daga haka katse kiran yai Safeenah na kuma fashewa da wane irin kuka wanda batayi irinsa a baya ba.

Daidai lokacin Assad ya k’araso yana fad’in “Shall we inform our team members ko zasu tayamu da search d’in..?”

Girgiza kai Mu’azzam yai yace “Ni a halin yanzu ban yarda da kowa ba Assad, especially mutanen da muke aiki dasu, bayan abubuwan da suka faru nasan ba zakaga laifina ba idan na zargi kowa.”

Assad ya d’an shafi kansa yace “Haka ne Mu’azzam, toh yanzu kana nufin ba komai zamu sanar dasu ba gameda case d’in..?”

Ya jinjina kai yace “Ko Yusuf ne bazamu sanar dashi komai ba for the mean time har Sai mun fahimci waye mai mana zagon k’asa..”

Assad ya jinjina kai yace “What do we do now..?”

Mu’azzam Baikai ga basa amsa ba wayarsa ta soma ruri.. Unknown number shine ya bayyana saman screen d’in. Ya dubi Assad ya kuma duban wayar dake ci gaba da ruri.. Lokaci guda ya d’aga wayar.

Daga d’aya b’angaren dariya aka fashe dashi kafin mutumin ya furta “Detective Gamji.. It’s been a long time.. Did you miss me..?” Sai aka kuma fashewa da dariya...




SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*



*36*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*





“Danger.!” Abinda Mu’azzam ya furta kenan yana jinjina kai a hankali.

Dariya ya kuma kecewa dashi kafin yace “Correct.. Ashe dai baka mance ni ba.. Koda yake ta yaya zaka mance Abokin shan shayinka..!”

“I’ll catch you.. Believe me I will..!” Mu’azzam yace yana sakin murmushi mai zafi.

Danger ya kuma k’yak’yata dariya kafin yace “If I were you ba wann maganar zanyi ba yanzu.. Zai fi kyau ka bada mahimmanci ga neman matarka da kake..!” Ya kuma fashewa da dariya kafin ya katse kiran.. Yana katse kiran ya karairaya SIM card d’in yai watsi da ita.

K’iris ya rage zuciyar Mu’azzam bata buga ba.. Mai Danger yake nufi.. Badai Sadiya tana hannunsa ba.. No no no. Baiso yayi tunani haka.

Zagaye wajen ya soma yana shafe fuskarsa da tafukan hannayensa, Assad yai saurin bin bayansa yana tambayarsa mai Danger yace masa.

Mu’azzam yai tsaye yana fuzar da fuci a hankali yana kuma shafe fuskarsa cikin tsananin damuwa “Assad that Maniac was asking me about my wife.. Assad what if..?” Sai kuma ya kasa k’arasawa yana jin harshensa na masa rawa cikin bakinsa..

Assad ya kame kansa yana mai karanto innalillahi wa inna’ilaihi raji’un a hankali. Lokaci guda Mu’azzam ya isa jikin mota yana mai kifa kansa cikin rashin sanin mai zai aiwatar.

Assad ya dafa Sa kad’an yace “Let’s not think of the worse.. Bata tareda shi in sha Allah..”

D’agowa yai yana duban Assad da idanunsa masu gauraye da tashin hankali, yana pointing Assad da ‘yar yatsa yake fad’in “If he lays a finger on her, I’ll kill him without showing any mercy..” Daga haka bud’e Mota yai ya shige Assad ya zagaya mazaunin mai zaman banza ya shige yana addu’an Allah yasa Danger bai d’auke Sadiya ba.

Suna tafe wayar Mu’azzam d’in ta kuma ruri, wani bak’on lamabar ne. Yana d’agawa Danger ya soma fad’in “Don’t think of tracking me down Mr Officer, dan bazaka tab’a samuna ba.. Amma idan kana so ka samu matarka zaka nemi ni koda bazaka sameni ba. Ni kuma zan sanar dakai conditions d’ina..!”

Babu shiri Mu’azzam ya paka motar gefen kwalta yana fad’in “Why can’t you face me. You coward..!”

Dariya ya kumayi kafin yace “You haven’t changed one bit.. You are still a short tempered police Officer..” Yana maganar yana dariya irinta rainin hankali.

Lumshe idanunsa Mu’azzam yai dan yasan yana fad’in hakan ne to provoke him. A halin yanzu baida burin da ya wuce ya ceci matarsa daga hannun wann d’an ta’addan “Wani salon wasan naka ne wannan..?!” Abinda kawai ya fad’i kenan.

Danger ya kuma murmusawa kafin yace “Karka damu I play fair idan har zakabi abubuwan da zan gindaya maka.. Amma idan bakabi ba.. Believe me abinda ya faru da k’anwarka zai faru da matarka..After all, she’s as beautiful as your sister..”

“If you touch her. I swear I’ll kill you.!” Mu’azzam ya fad’i idanunsa naga kwalta.

Dariya Danger ya fashe dashi kafin ya katse kiran.

Kifa kansa Mu’azzam yai saman steering wheel yana sakin numfashi a hankali.

Assad yai saurin dafasa yana tambayar Mu’azzam d’in. Ga duhun dare da ya soma shiga Sai kiraye kirayen sallar magrib ake.

Duk maganar da Assad yake masa bai basa amsa ba har suka tsaya wani masallaci sukai sallah. Yana nan calm kaman babu abindake faruwa harta Assad saida yaji mamakin hakan. Suka nufo motar bayan sun fito daga masallacin still Mu’azzam baice komai ba.. Suna shiga Mota suka d’auki hanyar cikin Abuja amma ga mamakin Assad Sai gani yai Mu’azzam murza kan motar ya canza hanya tamkar wanda aka tinzirasa. Yana ida kwana ba tareda ya dubi Assad ba yace “Get out Assad”

Assad ya dubesa da mamaki kafin ya girgiza kai yace “No, a halin da kake ciki bazan Barka kai kad’ai ba Mu’azzam.. I know you so well, so bazan Barka kai kad’ai ba.”

Murmushi yai da gefen baki still idanunsa naga waje guda “Ka fita Assad.” Ya sake fad’i yana damk’e kan steering d’in sosai.

Assad ya kuma girgiza kai “Bazan Barka kai kad’ai ba Mu’azzam..”

Jinjina kai Mu’azzam yai yace “Fine.. Ka zauna kai kallo..!” Daga haka ya ja motar suka soma falfala gudu saman kwalta. Basu zarce ko ina ba sai daban su Danger da Sagir k’ofar shagon Danger yanda Danger d’in yace Sagir sayen sigari ne kawai ke kawosa basuda wata connection.

Suna isa yai parking Assad Sai dubansa da mamaki ganin babu kowa babu alamun mutum a k’ofar shagon Danger, tamkar dai anyi shara.

Assad ya girgiza kai kurum yana duban Mu’azzam d’in “Kana tunanin zamu sami Danger a nan ne.?”

Mu’azzam bai ce masa komai ba Sai k’urama k’ofar shagon idanu da yai.

Assad bai kuma cewa komai ba sai kwantar da kansa da yai cikin kujera had’ida lumshe idanunsa.

Kusan minti talatin suka kwashe a wajen babu ko tsuntsu da ya gifta. Assad ya d’an fuzar da huci yana duba agogon dake d’aure hannunsa. Ya bud’e baki kenan da niyyan magana suka hango wasu matasa sun nufo shagon.

Mu’azzam zai bud’e Mota Assad yai saurin rik’osa yana fad’in “Mubi komai a sannu Mu’azzam..”

Da tsananin mamaki yake duban Assad kafin yace “That Maniac has my wife yet kana cewa na bari ayi komai a natse..? Assad Wai shin ka mance cewa Sadiya itace target d’in Su Danger.. Ka mance cewa nemanta suke ruwa a jallo.. Ka mance cewa ta dalilin nemanta da suke kowa nata ya shiga had’ari..? If you can’t be at any help kar ka kuskura kai tunanin dakatar da ni..!” Daga haka sauk’a yai ya nufi matasan Assad yai saurin bin bayansa, kamo Mu’azzam d’in yai suka d’an lab’e suna sauraron tattaunawar matasan yanda suke jajen sun d’ebe kwanaki basa ganin Danger bai bud’e shago gashi akwai wata nau’i na k’waya a wajensa kawai suke samu.

D’aya matashin yai tsaki yana fad’in kodai ya daina zuwa nan ne gaba d’aya.. Aiko zai rasa customers.. Muje kawai dallah..”

Ganin zasu shige yasa Assad fitowa daga yanda sukai kwanton b’auna suna sauraron tattaunawarsu. Tuni d’ayan ya arce dan sun zaci ‘Yan kamen Drugs ne..

Assad ya juyo yana duban d’ayan wanda tuni Mu’azzam ya damk’o kafad’arsa ya sharb’e k’afafunsa ya zube k’asa.

Saurayin ya shiga d’ago hannaye yana rok’onsu yana fad’in wllhi basu saye k’wayan ba kuma shi ba D’anta’adda bane.

Assad yace “Munsan kai ba D’antadda bane amma kana Ta’ammudi da miyagun k’wayoyi, zamu iya kulleka akan haka Kasan da wannan.?”

Saurayin wanda duka duka bai fi shekaru 20 ba ya shiga jinjina kai yana kuma rok’on Su k’yalesa..

Assad yace “Zamu sakeka idan ka amsa mana tambayoyinmu..”

“Na rantse da Allah Yallab’ai wllhi Allah shine shaidana ni zan fad’i gaskiya, ina sayen abu wajensa amma ni ba D’antadda bane..”

Mu’azzam baice k’ala ba Tunda Assad ya soma tambayar mutumin. Kafin Assad ya ankara sai gani yai Mu’azzam ya janyo saurayin ya jefasa cikin Mota. Assad yai tsaye kurum yana dubansa cikin rasa mai zaice. Bayan Mota Mu’azzam ya bud’e ya jefa saurayin ciki kafin ya d’auki hanya.. Assad yai saurin take masu baya saidai bai cimmasu ba mai taxi kurum

Please Login or Register in order to submit comment