Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dubesa da mamaki har suka isa mota Mu’azzam d’in ya bud’e ya shige yayinda Assad d’inma ya bud’e d’aya b’angaren ya shige.. Shi yanzu harga Allah tsoro Mu’azzam ke basa bayan wannan birkitaccen auren da yai yanzu yanzu..
Assad zuba masa idanu kurum yai yanda yake kwasansu saman kwalta tamkar zasu bar gari.

**

Tabarma Umma ta shimfid’a wasu Malam Liman, ko daga yanayin da tagansa ciki ta fahimci akwai matsala mai girma, saidai ta jingina hakan da Sace Alhaji Isyaku da akace anyi.

Ta zauna daga d’aya b’angaren suka gaisa, bak’ar ledar viva aje gaban Malam Liman.

Saida ya d’anyi gyaran murya kafin ya soma fad’in “Watau Uwani ita rayuwar nan da kike gani komai rubutacce ne tun kafin a samemu, Idan Ubangiji ya k’addari faruwar abu Toh fah bawa bai isa yaja da hakan ba.. Sannan inaso ki sani mutum baya tsallake matarsa, muddin matarsa ce toh ko a ina take kuma ko menene sanadi sai yaje ya cinma matarsa a duk yanda take..”

Jikin Umma yakai matuk’a wajen yin sanyi. Ta jinjina masa kai a hankali tana mai furta “Haka ne Malam.”

Malam Liman yaci gaba da fad’in “Alhamdulillah naji dad’i da kika fahimci haka Uwani.. Sannan akwai magana mai girma da nake tafe inaso na sanar daku daga ke har Sadiya. Nasan Kunji cewa an d’auke Alhaji Isyaku yau a k’ofar gidansa bayan ya fito zai halarci wajen d’aurin aurensa da Sadiya.”

Umma ta jinjina kai a hankali tana jin k’irjinta na tsananta fad’uwa.

Malam Liman ya d’an kifa kansa kad’an yana ganin girman maganan da zai fad’a masu, ya d’an muskuta kad’an yana gyara zaman rawaninsa “Toh Uwani aure dai bai yuwu da Alhaji Isyaku ba..”

Umma ta dubesa da mamaki sai ta d’an murmusa tace “Allah sarki Malam ai Babu komai haka Allah ya nufa, dama kullum cikin kai masa kokenmu muke muna rok’onsa yama zab’in abinda yafi alkhairi ya kuma dubi lamarinmu.. Na tabbata idan bai k’addari wannan aure ba k’udirarsa da Buwayarsa su suka dakatar da aukuwan wannan aure, inada tabbacin hakan shine abinda ya zab’arwa d’iyata.. Mun kuma gode da jarabawar da yake aiko mana daki daki.. Fatana Allah ya nufa muci wad’annan jarabawa.. Malam kar ka damu nasan kayi iyaka k’ok’arinka wajen ganin an sauk’e mana wannan nauyi na bashi dake bisa kanmu, Ubangiji ya saka maka da alkhairi duniya da lahira.. Idan Allah ya nufa zai turo mana wani hanyar da zamu samu mu biya wannan bashi dake kanmu..”

Malam Liman ya d’an share k’wallan da ya zubo masa, lokaci guda yake furta “Sadiya d’iya ce a wajena Uwani, ki daina min godiya ni babu abinda nayi mata.. Sannan idan babu damuwa inaso ta fito itama domin abinda zan fad’a maku yanzu ya shafi rayuwarta kacaukam. Sannan zai iya canza rayuwarta gaba d’aya..”

Wannan karon bugun zuciyar Umma ya k’aru. Ta dubi Habeeb dake zaune daga can gefe yana ‘yan wasansa abinka da yaro tace “Habeeb shiga ka kira Addarku..”

Habeeb ya jinjina kai kafin ya mik’e ya shige ciki kiran Sadiya.

Jiki a matuk’ar sanyaye Sadiya Ta fito, ga zuciyarta data tsananta yankewa tinda Habeeb yace su Malam Liman da Umma ke kiranta.

Sadiya ta fito sanye da hijabinta ta duk’a daga can gefe kusan Umma ta gaida Malam Liman.
Malam Liman ya amsa zuciyarsa cikeda tausayin yarinyar, bazai gushe ba yana mata add’uan samun Farin ciki mai d’orewa cikin gidan aurenta. Yana fata wannan aure nata da ya had’a da Mu’azzam ya zamto alkhairi gareta da mahaifiyarta harma da ‘yanuwanta.

Malam Liman ya dubeta yana jin rauni sosai had’ida tuhumar kansa “Halimatu.!” Ya ambato asalin sunanta wanda babu mai kiranta da wannan sunan sai mahaifinta.

“Na’am.. Baba..!” Taji bajinta na furta haka ba tareda tasan dalili ba, saidai tafi danganta hakan da cewa ya kira sunanta ne da sigan da mahaifinta ke kiranta shiyasa ta kirasa da Baba itama.

Malam Liman yaji dad’in ambatonsa da Baba da tai, a hankali ya soma furta “Inaso ki sani, da ace inada halin da zan sauk’e wannan bashi da basai kin kaiga sadaukar da Farin cikin ki ba kin auri wanda baki so.. Halimatu kin d’aukeni a matsayin mahaifi..?”

Sadiya ta dubesa sai kuma ta dubi mahaifiyarta, a hankali ta jinjina masa kai.. Malam Liman ya share hawayen da suka gangaro masa “Bansan ya zaku d’auki al’amarin ba.. Amma inaso ku Sani ina mai neman yafiyarku.. Musamman ke Sadiya.. Ki yafe mun kan had’a aurenki da nayi ba tareda saninki ba bayan kin d’auki matsayi mai girma kin bani.. Ki yafe ni d’iyata banyi haka dan wulak’anci ko cin zarafi ba saidai nayi haka ne gudun kar dama na k’arshe ya kufce mana.. Sannan inaso ku Sani ni d’an adam ne ajizi wanda yake kuskure.. Kar ku dubeni a matsayin malami ko limami.. Ku dubeni a matsayin D’anadam kuma Bawan Allah mai kuskure..”

Izuwa lokacin hawayen Sadiya ya k’aru.. Girgiza Kai take tana fad’in “Baba Liman dik abinda ka yanke akaina zanyi na’am dashi kuma zaka sameni Ina mai maka biyayya kaman yanda zanyiwa mahaifina.. Zanji dad’i matuk’a ace na samu damar yi maka biyayya irin wacce banyiwa mahaifina ba a lokacin da yake raye.. Hak’ik’a zanji dad’in hakan.. Duk hukuncin da ka yanke kayi daidai nasan bazakayi abinda zai cutar dani ba..”

Malam Liman da abokin tafiyarsa suka share hawayen da ya gangaro masu, da k’yar Malam Liman ya saita kansa kafin yace “Halimatu a yau sanda mukayi zaton Alhaji Isyaku ya janye aurenki ne gudun kar ya biya bashi na bada aurenki ga wani..”

Umma da Sadiya suka dubi juna cikin tsananin sanyin jiki..

Malam Liman ya mik’a wa Umma dubu d’ari sadakin Sadiya dasu Mu’azzam suka biya “Wannan shine kud’in auren Sadiya..”

Sadiya Ta kuma duban Umma cikeda kad’uwa. Cikin rawar murya Umma tace “Malam ko zamu iya sanin wanene mijin nata.?”

Malam Liman ya d’an gyara zamana kafin yace “Mu’azzam Abubakar Gamji. Shine sunan mijinki Halimatu.”

“Mu’azzam Abubakar Gamji.!” Sadiya ta nanata a hankali zuciyarta naci gaba da tsinkewa.. Take ta tina tattaunawarsu da Mu’azzam da ko minti talatin baiba kalamansa na k’arshe take tunawa _Idan Sunana Mu’azzam Abubakar Gamji ne zaki maimaita abinda kika fad’i_

A hankali Ta furta “The Corp!”
Sai kuma ta mik’e tana jin wani irin kuka na zuwa mata.. Babu shiri ta shige d’aki a guje tana mai k’unshe bakinta da kuka gadan gadan ke shirin fitowa.

Umma ta dubi su Malam Liman tace “Malam kuyi hak’uri zan shiga na kula da Sadiya.”

Malam yace “Babu komai.. Ga kud’in Tabawa nan sun biya idan yaso sai a had’u tareda ku da shaidu a biya Tabawa kud’inta.. Babu sauran maganan bashi..”

Jinjina masa kai kurum Umma tai kafin sukai sallama ta shige wajen d’iyarta da sumewa ne kawai batayi ba sabida firgici.


Malam Liman suna ficewa ya dubi abokin tafiyarsa suka tafe hannu.

Abokin Tafiyarsa yace “Kai Malam Wato dai harta ku malamai kuna d’an tab’a wuru wuru..”

Malam Liman yace “Kai Munkaila rayuwar nan tayi wuya fah, ai muma Malamai sai mun d’an had’a da cida addini bacin haka bazamu kai labari ba. Kai badon zan sami nawa kason ciki ba maizaisa na dage nayita wa’azi ina rok’on a biya masu bashin da suka ciwo, bashinma da ashararancinsu na buki kawai sukai dashi.. Ai tsuntsun da ya jawo ruwa shi ruwa yake bugu Munkaila, ni ko tausayi basu bani ba kuma nima kasuwancina nai dasu..Yanzu kaga kud’ad’en nan Tabawa tamin alk’awari akwai Kaso na ciki shiyasa dole na aurar da yarinyar nan ma koma wanene.. Yo zanyima d’iyata irin wannan auren ne..? Mutane suzo bagatatan babu bincike babu komai a d’auki d’an mutum sukutum a basu.. Kai ina ka tab’a jin anyi irin wannan aure idan ba don zan sami kaso na ciki ba.”

Suka kuma k’yak’yata dariya a tare Munkaila na fad’in “Nima kuma zan sami nawa ba..”

Malam Liman yace “Bani son zari Munkaila ka jira na dafe nawa tukuna..”

Munkaila yana murmushi yake jinjina kai kafin suka wuce.
**

Wani uncompleted building sukazo, Assad sai dubansa yake cikeda tsananin mamaki dan shi har wannan lokacin ya gaza yarda da abinda abokin nasa ya aikata.

“What are we doing here..?” Assad ya fad’i yana duban Mu’azzam d’in.

Mu’azzam bai kaiga basa amsa ba saiga su Yusuf team mate d’insu da kuma wani abokin aikinsu a CID mai suna Jabir sun fito daga building d’in.

A tare Yusuf da Jabir suka k’araso suna sara ma Mu’azzam da Assad..

Baki sake Assad ke dubansu, ya kuma dubi Mu’azzam kafin ya sake duban Yusuf yace “Wai ba yanzu na kiraka nake sanar dakai abinda ke faruwa ba..”

Murmusawa kurum Yusuf yai yana mai mik’a masu hannu alamun musabaha. Jabir ma ya k’araso suna gaisawa.

Mu’azzam ya dubi Yusuf da hannunsa ke d’aure alamun an kuskuresa da bindiga yace “Wait.. What really happened.. Why are you wounded..?” Yai tambayar cikeda kulawa yana duban Jabir d’in.

Jabir ya d’an murmusa yana duba hannun nasa dake d’aure da bandage yace “This.? It’s nothing Sir, just a scratch.”

Mu’azzam ya girgiza kai yana duban Yusuf da Jabir d’in.. Lokaci guda ya kuma duban Yusuf yace “What really happened Yusuf..?”

Yusuf ya soma basa labarin abinda ya faru “Bayan ka turamu Mu d’auke Alhaji Isyaku, koda muka isa k’ofar gidansa munga wasu mutane Sun shiga motarsa.. Muka bi bayansu Toh Sai suka tsere mana, a nan ne abductors d’in suka kuskuri Jabir da Bindiga..”

Da tsananin mamaki Mu’azzam ke dubansu kafin yace “Kuna nufin wasu sun rigamu, wasu suna targeting Alhaji Iskyaku.?”

Yusuf ya jinjina kai yace “K’warai kuwa wasu sun rigamu.. And I’m suspecting zasu iya zama yaran Danger..”

Mu’azzam yace “Kun kub’utar da Alhaji Isyakun..?”

Suka jinjina masa kai a tare Jabir na fad’in “Yana cikin building d’in nan, saidai bamu fara interrogating nasa ba muna jiran isowarka.”

Mu’azzam ya jinjina masu kai kafin yace “Muje ciki..”

Saurin rik’osa Assad yai, ya dubi su Yusuf yace “Officers ku k’arasa ciki muna zuwa..”

Suka jinjina kai kafin suka shige ciki.

Aka bar Assad da Mu’azzam tsaye a wajen..

Huci kurum Assad yake yana duban Mu’azzam wanda shima fuskar tasa tamau take.

Assad ya fuzar da fuci kafin ya d’ago yana duban Mu’azzam cikin tsananin b’acin rai “What the hell have you done Mu’azzam.. What has gotten into you.. Bayan auren yarinyar can da kai ashe kai ka d’auke Alhaji Isyaku.. Maiyasa na kasa gano hakan ma..? Mu’azzam anya lafiya kake.. Maiyasa zaka auri yarinyar nan idan ba sonta kake ba.. Kafi kowa sanin cewa marriage is a serious commitment.”

Katsesa Mu’azzam yai cikin tsananin b’acin rai “You know perfectly well that I didn’t marry that girl because I wanted to be with her.. Abu d’aya ne yasa na aureta because she’s the key to finding my real sister’s murderer.!”

Cikin b’acin rai Assad ya katsesa da fad’in “Kan wannan dalilin ne zakai making huge decision na aurenta..”

“Yes Assad..!!! If that’s what it takes me to do.. Then I’d marry her just to find my real sister’s murderer.. Ka fahimta..!” Ya k’arashe idanunsa na firfitowa waje tsananin b’acin rai.

Assad ya fuzar da huci yace “Don’t you think you’re ruining the girl’s life aurenta da kai ba tareda kana sonta ba Sai dan ka cimma burinka na binciken da kake..”

“Her damn life has already been ruined tin lokacin da ta zab’i kasancewa da wannan d’aniskan criminal d’in..! And just to remind you, dama ‘yar tasha ce rayuwarta lalatacce ne tuntuni..!”

Assad ya shafi kansa yana mai fuzar da huci kafin yace “Toh shi kuma Alhaji Isyaku daka d’aukosa ka ajiye sa nan fah..? Ta yaya zaka aikata abu makamancin wannan Mu’azzam, karfa ka mance you’re still on your suspension, sanin kanka ne mutumin nan can file a case against you d’aukosa da kai ka ajiyesa a nan, sannan baka tinanin Yusuf da Jabir zaka iya jefasu cikin matsala.. And.. waima da ka aje mutumin nan mai zai maka.. kanaji sunce anyi abducting d’insa sukai bata kashi da ‘yanta’addan suka k’wacesa.. Idan na fahimta Alhaji Isyaku baida masaniya akan abinda ke faruwa he’s only caught in the middle of all this a matsayinsa na wanda zai auri yarinyar.. Ya kamata ka saki mutumin nan ya tafi Mu’azzam kafin ka janyo ma kanka wani matsalar bayan wanda kake ciki.”

Mu’azzam dake dubansa da rinannun idanunsa yace “I thought I told you, idan banzanyi k’ark’ashin umarnin NPF ba I’d do it my way.. And this is my way of doing things Assad.. Kafi kowa sanin hakan.!”

Assad ya d’an shafi kansa kafin ya d’ago cikin tsananin b’abin rai yace “Baka tinanin mutumin nan Danger ke targeting d’insa.. He’s innocent Mu’azzam you can’t keep him here.. You’ll be charged with kidnapping..”

Assad Bai Kai aya ba Mu’azzam dake tsananin huci ya katse sa da fad’in “Assad, If I keep doubting everybody then my real sister’s killer will never be found.!”

“Then what..! So is it okay to abduct an innocent person if it means finding the killer..?” Assad yace cikin tsananin b’acin rai.
Ya d’an sassauta murya yana duban Mu’azzam d’in “I know how frustrated you can be to wait for justice to come through.. We can’t take laws to our hands Mu’azzam.. You’re a police officer, you should know better..!”

Da tsananin mamaki wannan karon Mu’azzam ke dubansa, ya bigi bonnet d’in Mota kafin yace “What the hell has happened to you.? Because you used to be so determined on solving this case.. Tell me Assad.. Are you backing off now..?!” Ya k’arashe cikin tsananin zafin zuciya gumi na karyowa daga sumarsa zuwa goshinsa.

Girgiza kai kurum Assad yai dan ya gama yarda Mu’azzam yayi nisa.. Zai dik abinda zai domin ya gano waye ya kashe masa ‘yaruwa.

A hankali Assad ke furta “Just don’t do anything that you’ll later regret Mu’azzam.. Please..! Let’s do everything the right way.. Hanyar da doka ta aminta dashi..”

Da gefen idanu Mu’azzam ke dubansa kafin yace “I’ll interrogate that man.. Zaka shigo ne ko zaka tafi..?”

Assad ya girgiza kai kad’an yana mai fuzar da huci kafin yabi bayan Mu’azzam d’in, suka shige cikin ginin yanda Alhaji Iskyaku ke zaune saman kujera Jabir da Yusuf na tsartsaye b’angarorinsa guda biyu..


Mu’azzam na shigowa ya janyo kujera da k’afarsa ya saita Ta gaban Alhaji Isyaku kafin ya zauna suna duban juna.



SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*23*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*









K’ura masa idanu Mu’azzam yai yana duban yanda Alhaji Isyaku ke rarraba idanu kaman an jefa mage a tukunya.

“Alhaji, nasan ka gane ni, domin kuwa munje gidanka a satin da ya gabata Nida abokin aikina domin gudanar da bincike..”Ya k’arashe yana d’ago kai had’ida duban Assad dake tsaye saman kansa.

Alhaji Isyaku yai saurin jinjina kai yana duban Mu’azzam d’in harma da Assad “Eh K’warai Yallab’ai.. Na ganeku.”

Mu’azzam ya jinjina kai kafin yace “Good, bazamu cutar dakai ba.. Hasalima mu Jami’an tsaro ne, inada Tabbacin ka fahimci cewa bazamu cutar dakai ba bayan abokan aikina sun Kub’utar dakai daga hannun wad’anda sukai garkuwa dakai..”

Cikin sauri Alhaji Isyaku ke jinjina kai yana fad’in “Wannan haka ne Rankaidad’e, wllhi kud’in aurena suka sace nid’in sabon ango ne Yallab’ai..”

Fuzar da huci Mu’azzam yai cikeda takaici kafin yace “Wannan ba matsalata bace Alhaji, tambayoyin da zaka amsa mana yanzu sune damuwata.. And I suggest that you cooperate with us dan muji dad’in gudanar da aikinmu kuma kaima mu maidaka gida a mutunce.”

Alhaji Isyaku ya zuba masa idanu kafin yace “Maiyasa baku kaini police station ba kuka kawo ni nan wajen..?”

Mu’azzam dake murza hannayensa kad’an yana duban Alhaji Isyakun gajeren murmushi ya kumayi kafin yace “Kasan da cewa yarinyar dake yunk’urin aura ‘yantadda suna bibiyarta..?”

Alhaji Isyaku ya zaro idanu waje yana mai tuna kalan tashin hankali da iftila’in da ahalin Sadiya ke ciki dik dalilin tsohon saurayinta Sagir.. Idan ya fahimta Wato yarinyar suke hari shiyasa sukai yunk’urin d’aukesa. Yai saurin d’ago kai yana fad’in “Yallab’ai wllhi tsautsayi ne ya sanyani neman auren yarinyar nan.. Wllhi bansan komai ba.!”

Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Baka San komai ba..? Then Maiyasa ka firgita..?”

“Yallab’ai satan mutane ya zama ruwan dare a k’asar nan dole na firgita..!” Alhaji Isyaku ya fad’i jikinsa na rawa.

Mu’azzam ya jinjina kai yace “Wannan shine dalili...?” Shiru ya gifta gumi na tsartsafo ma Alhaji Isyaku yana kuma zaro idanu waje, lokaci guda yanajin babu abinda zai kuma had’asa da Sadiya balle yai tinanin aurenta..

Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Alhaji idan muka kaika ofishinmu dole sunanka ya shiga record sannan hakan ka iya shafan reputation d’inka harmada sana’arka.. And once you’re proven guilty dole a maka ka a kotu akumayi shari’a dakai.. Amma ni na maka alk’awari idan ka sanar damu iyakacin gaskiyar abinda ka sani zamu sakeka tin daga nan basai mun tafi ofishinmu ba.. Just cooperate Alhaji and tell us how you’re connected to this man.!” Ya k’arashe yana mai aje masa hoton Danger saman hannunsa.

Da mamaki Alhaji Isyaku ke duban hoton kafin ya d’ago yana duban Mu’azzam, lokaci guda ya girgiza kai yace “Rankaidad’e wllhi kaji na rantse maka bansan wannan mutumin ba.. Wllhi Allah shine shaidata ban sansa ba ban kuma tab’a ganinsa ba sai yanzu daka nuna min hotonsa.”

Mu’azzam ya jinjina kai kafin yace “Amma kanada masaniyar mutumin nan sunanka ya soma ambata mana a lokacin da muke bincikensa.. Ta yaya zaka ce baka sanshi ba bayan shi d’in ya sanka..”

Alhaji Isyaku ya girgiza kai yace “Wllhi wllhi Allah d’aya ne ban sanshi ba, bansan yaya akai ya sanni ba.. Koda yake ba abun mamaki bane dan ya sanni dan ni mutum ne mai huld’a da mutane da dama. Sannan Allah ya rufa mun asiri a unguwarmu inada tabbacin idan ka shigo layin gidana na d’aya daga cikin gidajen da ake kwatance dasu.. So ba abun mamaki bane dan ya kama sunana Rankaidad’e..”

Mu’azzam ya tsaresa da idanunsa da suka gama kad’awa sukai jazir “Alhaji zan sake tambayarka nicely ka sanar dani abinda ke tsakaninka da mutumin nan.!”

Jin zai fice a giya yasa Assad saurin kamosa suka fice daga wajen.

Dukan garu Mu’azzam d’in yai da hannunsa yana duban Assad “What now..! Mai kuma na aikata..? I was only questioning the man..”

Fuzar da huci Assad yai yace “Baka aikata komai ba Mu’azzam, amma kana shirin aikatawa, ka d’auko mutumin nan ba bisa k’aida ba kana interrogating nasa, and not only that. you’re forcing him to admit to the crime he’s not committed. Bayan cewa koda ya aikata laifin yanada damar da zai k’i yin magana har sai an barsa ya gana da lawyer d’insa..Anya Mu’azzam ka d’auko hanyar da zai b’ulle.. Don’t allow your anger to consume you.. Kabi komai a sannu.. I’m positive mutumin nan Iyakacin gaskiyarsa yake fad’i babu abinda ya Sani. Kaman yanda na fad’a maka he’s caught in the middle ne sabida auren yarinyar da ya tassama yi, Toh haka d’in ne.. Instead mu tsaya muna b’ata lokacinka kan tuhumarsa da neman mutanen da suka tassama kidnapping d’insa mukai.. Dan na tabbata babu abinda zamu samu wajen mutumin nan..”

Mu’azzam ya d’ago fuskarsa data rine zuwa ja sabida tsananin tashin hankali, lokaci guda ya shafi goshinsa da hannunsa guda kafin yace “Kai baka tunanin mutumin nan had’a baki sukai da mutanen da suka tassama sacesa.. Baka tunanin hakan na iya kasancewa cikin plan d’in Danger.. Danger is a very dangerous person Assad, he’s capable of everything.”

Assad ya jinjina kai yace “Na sani Danger is Dangerous, amma tambayar da zan maka a nan shine idan bakinsa d’aya da Danger Maiyasa zai sacesa.. Sannan idan bakinsa d’aya da Danger bazasu amshe kud’ad’en dake hannunsa ba..”

Mu’azzam ya zuba masa idanu kaman mai nazarin sai kuma ya murmusa yace “Kana magana as if you can’t read criminal minds and how smart they can act.. Yanzu dashi da Danger duk zasu iya shirya haka dan su karkatar da hankalin jami’an tsaro dan kawai abun yayi kaman Su d’in suna bibiyar Alhaji Isyaku ne sabida Auren Sadiya da yake yunk’urin yi.. I believe ka amince zasu aikata fiyeda haka.”

Assad ya nusa yace “Everything is possible in a situation like this saidai hanyar da ka d’auko zai iya sakamu cikin matsala gaba d’aya.. Maimakon muyi solving case d’in zamu iya b’ata komai da wannan hanyar daka biyo ba bisa k’a’ida ba..” Shiru Assad ya d’anyi yana mai tsaresa da idanu kafin yace “But wait, idan har kana tinanin Danger da mutumin nan bakinsu d’aya ne Maiyasa ka hana mutumin auren yarinyar..? Sannan Maiyasa kai ka aureta.. Kana tunanin zasu iya cutar da ita ne..?”

Shiru Mu’azzam bai basa amsa ba sai mugun kallon da yake aika masa. Lokaci guda Assad yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “Now I get it.. Ka aureta ne to give her protection..!”

“O C’mon just shut up Assad..!”

Assad yaci gaba da fad’in “Yes gaskiya ne Mu’azzam dan ka bata kariya daga sharrin su Danger ka aureta.. Because she’s there target.. Ko baka fahimci hakan yanzu ba I’m positive gaba zaka fahimci haka.”

Da mugun mamaki Mu’azzam ke kallonsa yanaji yanda yake k’ok’arin k’irk’iro wani zance, kan mai zai bama wannan yarinyar protection Iyakacin abinda ya Sani shine he still needs her for his mission ne. Gajeren tsaki yai yana mai girgiza kai yake furta “You are not serious Assad. Bansan ya akai kake aiki k’ark’ashin NPF ba. You should be a clown and not a police officer..” Yana ida fad’in haka yasa kai ya koma cikin building d’in yanda Alhaji Isyaku ke zaune.
Assad ya take masa baya yana mai girgiza kai kad’an.

Suna k’arasowa Mu’azzam ya dubi Alhaji Isyaku yace “Alhaji zamu k’yaleka ka tafi.. Zamu maidaka Gida.. Motarka tana nan a waje wad’annan abokan aikin nawa sun taho maka da Ita nan.. Amma still idan kanaso zaka iya reporting ‘yanta’addan nan da suka tasamma saceka suka kuma sace maka kud’ad’enka.”

Alhaji Iskyaku Yai saurin girgiza kai yana mai zaro idanu yace “Ni wllhi bana fatan abinda zai had’ani da ‘‘yanta’addan nan, yo a k’asa irin wannan da aka maida satan mutum kaman an d’auke ‘ya’yan kaji ai abun na gode ma Allah ne da bai k’addari zan sha wahala hannun mutanen nan ba.. Kuma tinda na tsira Alhamdulillah.. Sannan wannan yarinya ko a k’afa aka d’aura mun ita zan kwance na gudu dan na kula tsautsayi da bala’i ke bibiyarsu.. Ban tab’a jin k’aran harbe harbe ba saida nace zan aureta.. Na gode maku matuk’a da ceton rayuwata da kukai..”

Assad ya mik’a masa hannu sukai musabaha kafin yace “Kar ka damu Alhaji, hakan aikinmu ne.. Kula da al’umman k’asa tsare masu rayuwarsu lafiyarsu harmada dukiyarsu.. Kuma kar ka damu da izinin Allah zamu gano mutanen da suka maka wannan aika aika and they will answer to the law. Ku daina karyar ma jami’an tsaron k’asar nan da fad’in cewa sun gaza Gwabnati ma sun gaza.. NPF tana iya k’ok’arinta a kullum domin taga Ta kawo k’arshen ta’addanci da rashin tsaron da ya addabi k’asar nan..A koda yaushe ku saka a ranku cewa mu ‘yansanda abokanku ne ba mak’iyanku ba.. Dukda cewa da yawa sun mana shaida cewa akasarin mu gurb’atattu ne ba haka abin yake ba domin kuwa akwai na k’warai a cikinmu.. Kaman dai ko wacce irin Sana’a akwai gurb’atattu akwai na K’warai..”

Alhaji Isyaku ya jinjina kai a hankali yana duban matashin D’ansandan. Lokaci guda ya kuma masu godiya kafin suka nufo waje gaba d’aya.

Suna fitowa waje Alhaji Isyaku ya kasa key ma Mota, jikinsa dik sai rawa yake.. Gani yake kaman ‘yantaddan zasu kuma dawowa.

Ya lek’o da kansa ta glass yana fad’in “Rankaidad’e ko zaku taimaka min dan Allah.. Wllhi ban iya tuk’a motar.”

Assad ya dubesa kafin ya dubi su Mu’azzam sai kuma yace da Alhaji Isyaku “I’ll drive you home Alhaji.”

Alhaji Isyaku cikeda jin dad’i yake godiya wa Assad “Na gode matuk’a yallab’ai, aikam bazan iya tuk’a mota ba dan har yanzu tsoro bai sakeni ba.. Gani nake kaman idan ina tafiya ‘Yantaddan nan zasu dawo.. Na gode na gode k’warai.”

Assad ya dubi Mu’azzam yai masa alama da hannu kan cewa zai kai Alhaji Isyaku gida. Jinjina masa kai kurum Mu’azzam yai kafin suka soma fitowa tareda su Yusuf suka nufi motocinsu suna basa update abinda ke faruwa a CID.

Shiru Mu’azzam yai yana nazarin abducting Alhaji Isyaku da aka tasamma Yi wanda baida haufi idan har Alhaji Isyaku baida wani connection da Danger Toh ko shakka babu masu bibiyan yarinyar ne suka kuskuresa. A fili ya furta “Danger..! Zan kamaka dik yanda ka shiga ka fita.. Da k’udurar Ubangiji.!”

K’aran shigowar sak’o cikin wayarsa da yaji ne ya sanyasa ciro wayar aljihu yana dubawa. Lamba ce Babu suna, sannan abinda kawai aka rubuta jikin sak’on shine _BAD_

Ya nanata alphabets d’in a

Please Login or Register in order to submit comment