Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zauna yana shafe fuskarsa da tafukan hannayensa yana jin bugun zuciyarsa na k’aruwa.. Meke faruwa dashi..? Badai sha’awan yarinyar nan yake ba.. Kai never..! God forbid..! Ya kuma lumshe idanunsa, ji yai zaman d’akin na neman gagaransa. Ya mik’e ya bud’e k’ofar balcony yana shan fresh air na damina.. nan yaji k’aran hadarin dake sararin samaniya na k’aruwa. Kan kace mai an soma ruwa kaman da Bakin k’warya. Ya mik’a fuskarsa waje ruwa na zubo masa saman fuskar nasa, idanunsa a lumshe ko zai daina ganinta amma babu abinda ya canza Ita d’in dai yake gani.. Ya yarda sha’awanta yake sannan bai tunanin zai iya rik’e kansa har gari ya waye.. Toh amma ta yaya zai had’a jiki da fasik’a irinta..? Wata zuciyar tace masa ai kai ba fasik’anci zakayi da ita ba ka biya sadaki, ka fanshe sadakinka tinda dama Ta saba a biyata kud’i ta bada jikinta.. Kai Naka ta halattacen hanya zakayi akwai igiyan aurenka har guda UKU akanta wanda sun halatta maka Ita. Ya bud’e idanunsa yana fuzar da fuci a hankali.. Toh amma ta yaya zai soma tunk’aranta da batu irin wannan aima sai ta rainasa ta maidashi D’anhannu irinta.. Ya saka hannayensa biyu ya shafi sumarsa da suke wet ya maidasu baya.. Zuciyarsa tana fad’i masa this is the perfect opportunity for you Idan baka so ta fahimci wani abu ya shiga tsakaninku kaje mata a cikin barci bazata fahimci komai ba.. Besides tinda an samu suspect shikenan zaka rabu da ita bazata kuma dawowa cikin rayuwarka ba.. Da wannan tunanin Mu’azzam ya dawo cikin d’akin. Yana tina suffarta da kuma ni’imtaccen k’amshin da yaji cikin jikinta.. A cikin baccin ya dinga sarrafa sassan jikinta yana mamakin mace da ta gama yawon ta zubar jikin nata bai sake ba, komai zamzam kaman dai na sabuwar budurwa wacce bata tab’a sanin wani d’a namiji ba.. Tin daga nan jikin Mu’azzam ya soma yin sanyi yanajin zuciyarsa na masa wani irin rauni.. Bai ida shan mamaki ba saida yazo shiganta yaji kirif babu alamun ta tab’a tarayya da wani d’a namiji.. Cikin tsananin sanyin jiki ya tsaya cak ba tareda ya ida nufinsa ba.. Ya d’ago yana duban fuskarta wanda har lokacin idanunta a lumshe suke alamun bacci take.. Take yaji bugun zuciyarsa ya k’aru.. Toh kodai idan mace tayi tarayya da wasu mazan bayan wani lokaci idan ta jima batayi ba tana komawa budurwa ne..? Da kansa ya bama kansa amsa da fad’in no never.. Sabo Sabo ne.. Koda ace baisan halitta ‘ya mace practically ba ya sani a karance.. A hankali yaji bakinsa na furta “She’s verging..!” Cikin tsananin sanyin jiki ya mik’e kaman wanda aka zare ma laka. Ya shiga janyo mata tufafinta yana maida maida mata. Ya janyo bargo ya kuma rufa mata bayan ya gyara mata kwanciyarta. Yai zaune had’ida mata K’uri yana duban fuskarta lokaci guda yana jin wani abu mai kaman tausayinta can k’asan zuciyarsa.. Kalaman b’atanci da ya dinga fad’a akanta yake tunawa da irin wulak’ancin da ya dinga yi mata.. Toh kenan batabi mazan bane kokuwa dai sharri ake mata..? Toh Wai shin meke faruwa ne..? Ya kuma tambayar kansa yana dubanta. Tabbas ya shiga rud’u da rashin sanin abinda zai yarda dashi.. A hankali ya mik’e daga kan gadon ya nufi bathroom ya d’auro wankan tsarki. Ya dawo cikin d’akin har lokacin baccinta take. Drawer ya isa ya d’auki takarda da pen yai rubutu saman takardan ya linke ya ajiye mata nan gefenta.

Sadiya kaw maganin bai saketa ba Sai wajajen k’arfe bakwai na safe, Ta mik’e taji idanunta sun mata nauyi.. Nan ta ganta a d’akin Mr Inspector saman gadonsa.. Take ta soma tuna abinda ya faru a daren jiya, ya sanyata zaman d’akinsa da sunan baida lafiya.. Tai saurin mik’ewa tana k’ok’arin sauk’owa daga saman gadon, nan taga takarda ya fad’o.. Ta mik’a hannu ta d’auko tana addu’an Allah yasa takardan saki ne ya ajiye mata. Allah yasa Ta gama mission d’inta kenan.. Da wannan tunanin ta warware takardan. Zuciyarta ne yai wani irin tsinkewa sakamakon abinda ta gani rubuce cikin takardan

_Thank you for taking care of me last night. Dare ne mai cikeda rud’ani.. Dukda cewa babu abinda ya faru, but still kiyi wanka ki tsarkake jikinki_ Sai aka rubuta Mr Inspector daga k’asan note d’in.

Jikinta ne ya d’auki rawa, ta k’unshe bakinta da duka tafukan hannayenta tana girgiza kai.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Mai ya faru da ita.. Mai Mr Inspector ya aikata mata.. Tasha magani ya sakata bacci.. Kenan Mr Inspector yayi attempting raping d’inta alhalin tana bacci.. K’ank’ame jikinta ta soma hawaye na zubo mata, cikin tsananin rawar murya take furta “Monster..! Monster.. How could you..? You are a monster..!!!” Ta fashe da wani irin kuka tana k’ank’ame jikinta. Ya mata abinda bazata tab’a yafe masa ba. Ta mik’e tana kuka ta nufi nata d’akin ta fad’a bathroom.. Haka tai wankan tana kuka tana darje illahirin jikinta.. Sosai take kuka tana jin tsanar Mu’azzam wanda bata tab’a yin irinsa ma wani bil Adam ba.

Bayan tayi wanka tayi alwala tai sallah har lokacin kuka take tana jin zuciyarta na mata wane irin zafi.. Ya bud’e mata jikinta, sannan ya kalle mata jikinta harma yayi abinda yaga dama da jikinta alhakin tana bacci.. Cikin k’unan zuciya hawaye na zubo mata take furta “He’s a Rapist.. He tried to rape me while I was asleep.. How could he..?!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin wani kukan. Ta mik’e tana goge hawayenta. Lokaci guda ta koma d’akin nasa Ta d’auki pen d’in da paper d’in da ya rubuta mata note d’in. Can k’asan rubutun tana hawaye Ta soma rubutu itama.

_I’ll never forgive you for what you did last night.! Aside from being a Kidnapper you are also a rapist, Mr Inspector. You are a Criminal, baka cancanci zama D’ansanda ba. Kai d’in D’antadda ne.. Zan iya yafe maka komai, all the insults wulak’anci and all.. But abinda kayi daren jiya abu ne da bazan tab’a yafe maka ba.. Har abada. The game is over, and the mission is accomplished. Mr Inspector_

Ta ajiye masa nan kafin Ta mik’e ta nufi gate tana hawaye.



SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*33*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*






Zaune ta tadda D’ansandan saman benchinsa, yana ganinta ya mik’e yana sara mata “Good morning Ma’am.” Ya fad’i cikeda risinawa.

Sadiya tai k’ok’arin saita kanta kafin tace “Morning..”

Shiru ya d’an biyo yana sauraron mai zatace.

Kanta ta d’an dafe kana tace “Magani nake son zuwa saye zaka bud’e mun k’ofa yanzu.”

Ya d’an dubeta yana girgiza kai “Ma’am I’m really sorry.. I was instructed not to let you out.”

Ta tsaresa da idanu tana dubansa tana kuma kame kanta “I told you magani nake so, ko so kake na mutu maka a wajen nan.. Kai D’ansanda ne kafi Kowa sanin mai hakan ke nufi idan na fad’i maka a wajen nan.. So you better let me out now..”

“Ma’am I’m sorry.. Idan na barki kika fice, Boss won’t sapere me. Kiyi hak’uri ki koma cikin Gida..”

“Am I a prisoner da bazaka barni na fice ba.?” Ganin ya kifa Kai k’asa bai amsata ba ya sanyata dafe kanta tana ‘yank’ararraki kad’an tana k’ok’arin duk’awa k’asa alamun tana jin jiki.

Police d’in ya matso a daburce yana tambayarta “Ma’am are you alright... Do you want me to call Boss..? Ma’am..”

Bata amsa Sa ba Sai kame kanta da cikinta take tana fad’in idan bazai barta Ta fice ba shi yaje ya nemo mata maganin.. Yanda takeyi dole kayi tunanin da gaske batada lafiya.

Cikin daburcewa ya mik’e yana k’ok’arin zaro wayarsa da niyyan kiran layin Mu’azzam.

Sadiya ta kannare ido tana dubansa daga nan yanda take kwance nan ta soma fad’in “Hey what are you doing.? Can’t you see I’m in pain. Just go to any nearby pharmaceutical and get me medicine.. Wayyo cikina.. Kaina.. I can’t breath..!” Abubuwan da ta dinga fad’i kenan daga nan yanda take kwance wanda ya kuma birkita mutumin. Gashi ya gaza samun layin Mu’azzam.. Dole ya fice yana fad’in bari ya nemo mata magani. Yanda ya fice haka ya bar k’ofan a bud’e ko tinawa ya kulle baiba.

Aiko sanda ta tabbatar ya fice ya bar ma layin sannan ta mik’e tana hamdalah. Ba tareda Wani b’ata lokaci ba tasa kai Ta fice daga GIDAN ARO. Ta juyo tana duban gidan bayan ta fice, hawayen da ya gangaro mata ta goge kafin tace “Wannan shine k’arshe bazan kuma dawowa cikinka ba in sha Allah.!” Tana ida fad’in haka tasa kai Ta soma sauri sauri tana mai ficewa daga layin gaba d’aya.

**

Assad ya shigo Coffee shop d’in yana mamakin kiran da Mu’azzam d’in yai masa yace Su had’u nan da sassafe irin haka.

Assad ya k’araso sukai musabaha still mamaki saman fuskarsa. Mu’azzam ya tambayesa abinda za’a kawo masa. Nan yace a kawo masa coffee d’in shima. Yai zaune yana duban Mu’azzam d’in yana jira yaji da mai zai fara. Bayan an kawo wa Assad nasa order d’in ya sinkayo muryar Mu’azzam na fad’in “Nasan ka tab’a aure zama baiyi dad’i ba Kun rabu da matar..”

Assad ya dubesa da mamaki jin yau kuma da wannan batun yazo, shi ya zaci ma wani ci gaba suka kuma samu daga binkicen da suke.

Assad ya jinjina kai yace “Haka ne.”

Mu’azzam ya kuma sipping hot coffee d’insa kafin yace “Kanada experience, kasan halittan mata kenan.”

Yanzu kam aje cup d’in dake hannunsa Assad yai yana duban abokin nasa da tsananin mamaki wanda a baya sam bai irin wad’ann zantukan.

Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Inaso na maka tambaya a matsayinka na wanda yakeda experience.”

Assad ya jinjina kai yace “Umhum ina saurarenka.

“Idan mace ta gama yawonta da biye biyen maza, after some time ta jima batabi mazan ba tana koma sabuwa ce kaman dai budurwar da bata tab’a sanin wani d’a namiji ba.?”

Bagatatan Assad yaji zancen wanda har saida ya kusan fuzar da coffe d’in da ya shiga bakinsa sabida dariyan da yazo masa.. Da alama abokinsa ya shiga missed call.. Ya k’unshe bakinsa yana darawa a hankali dan Yanzu kam ya gama gane Ina tambayoyin Abokin nasa suka nufa.

Mu’azzam ya aika masa mugun kallo cikeda takaici “You are not serious, you know. Ya ina tambayarka abu kana wani dariya..”

“Toh kuka kake so nayi.. Abun ne abun dariya.. Budurci guda d’aya ne ai.. Halitta ne da Ubangiji ya Karrama ko wace d’iya mace dashi, wacce ta watsar da wannan karamci nata tin a titi bazata kuma samunsa ba, bazai dawo ba duk gyaran da za’ayi kuwa.. Bazata tab’a zama kaman wacce ta Martaba wannan karamci nata ta rik’esa da kyau ba.”

Mu’azzam ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yana mai sipping coffee. Lokaci guda Assad yaci gaba da fad’in “Shiyasa shaidar zina dai takeda matakai daki daki..Ku guje ma mummunan zato ma bayin Allah.. So tari wanda ka munana masa zato shine na k’warai d’in. Sannan so tari wanda ka kyautata masa zato shine na banzan. Amma ko yaushe ana so mutum ya kasance mai kyautata zato.. Ku guje ma d’aukan maganganun mutane domin shi d’anadam a Kullum aibunka yake nema ya yad’a, Sai ya yad’a aibunka sau d’ari kafin ya fad’i alkhairinka guda d’aya.. Ga aibun a tattare da shi amma shi bazaiga nashi ba sai yaje yana hangen na wani.. Allah yasa mu gane ya kuma datar damu.”

Mu’azzam ya amsa da Ameen. Yana mai ci gaba da shan coffee d’insa. Time ya duba yaga Wai har tara na safe Ta d’an gauta ya kamata Su k’arasa Office.. A tare Suka mik’e Mu’azzam yai settling bill d’insu kafin suka nufo waje.
Babu b’ata lokaci suka nufo ofishinsu.

Suna isowa suka tadda Daddy a k’ofan Ofishin nasu. Assad ya dubi Mu’azzam “Wa nake gani kaman Daddy..? Allah sarki ni wllhi duk yafi bani tausayi a al’amarin nan.. Mutumin nan yana k’aunarka Mu’azzam, kaga yanda ya juya ma d’iyarsa baya yak’i ya bama k’arya goyon baya dukda cewa yanada halinda zai iya sakawa a kashe case d’in nan a rufe case d’in gaba d’aya sabida d’iyarsa amma baiyi haka ba.. Gaskiya na jima banga mutum mai dattako da kiman Daddy ba.”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “K’warai Daddy mutumin kirki ne.. Bai cancanci d’iya irin Safeenah ba.. Unfortunately bamu zab’en ahali, farkawa muke kawai mu ganmu tareda mutanen da Allah ya hukunta zasu zama ahalinmu.. Sannan ko wanne ahali sunada nasu k’alubalen da suke fuskanta.. Mu kuma irin namu k’alubalen kenan.. Mu k’arasa..”

Assad ya jinjina kai kafin suka nufo yanda Daddy ke zaune. Gaisawa sukai gaba d’aya kafin Assad ya Shige ya basu waje.

Daddy ya dubi Mu’azzam wanda jinkinsa ya d’anyi sanyi da ganin Daddyn.. Ko Babu komai Safeenah d’iyar Daddy ce jininsa ce dole zaiji wani abu can k’asan zuciyarsa dukda kuwa k’arfin halin da yai.

Mu’azzam yace “Are you here to see Safeenah.? Mu k’arasa sai a kira maka ita..”

Daddy ya girgiza kai yace “Ba Safeenah nazo gani ba Mu’azzam.. Kai nazo gani..”

Mu’azzam ya d’an gyara zamansa yana duban Daddyn.

Daddy yaci gaba da fad’in “Mu’azzam bazan hanaka hukunta Safeenah akan laifinta ba idan har an kamata da laifin.. Amma inada wata alfarma guda d’aya da nake son rok’a daga gareka.”

Mu’azzam ya d’an d’ago ya dubesa “Alfarma kuma Daddy.. Ai ka wuce alfarma a wajena Daddy.. Umarni kawai zaka bani..”

Daddy ya murmusa cikeda jin dad’i kafin ya jinjina kai yace “Allah ya maka albarka Mu’azzam.. Alfarmar da nake nema wajenka shine, dan Allah kar ka saki Safeenah har sai an gama bincike an sameta da laifi.. Kamin wannan alk’awarin cewa bazaka rabu da ita ba har sai an tabbata Tanada laifi.. This is the least I can do for my daughter bayan juya mata baya da nayi..” Ya k’arashe yana duban Mu’azzam d’in cikeda kulawa.

Cak Mu’azzam ya tsaya ba tareda ya iya amsa Daddy ba, saima sadda idanunsa k’asa da yai.

Daddy yai gyaran murya yaci gaba da fad’in “I know it’s not easy, ace kana shari’a da matarka.. But please do this for me.. For our family Mu’azzam.. Kar ka saki Safeenah until she’s proven guilty.. Ina rok’onka ne a matsayin mahaifin Safeenah.. Please Mu’azzam..!”

Ganin Daddy na k’ok’arin had’e hannayensa biyu waje guda alamun rok’o yasa Mu’azzam saurin kamo hannayen Daddy ya hanasa aikata hakan. Yana girgiza kai yake fad’in “Dani da Safeenah Kai Babanmu ne gaba d’aya Daddy.. Yanda zaka umarce Safeenah tai abu ko Musaddiq haka nima zaka mun.. Daddy bazan saketa ba kaman yanda kace.. Safeenah zataci gaba da zama matsayin matata..”

Daddy ya sakar masa murmushi yana k’ok’arin maida k’wallan dake k’ok’arin ciko idanunsa “Na gode Mu’azzam.. Thank you for this.. Allah Ubangiji ya maka albarka ya kuma maka jagora.”

Mu’azzam ya amsa da “Ameen Daddy..”

Daddy ya mik’e yace “Alk’ali ya sanar da Court Hearing d’in ne..?”

Mu’azzam ya girgiza kai yace “Muna sauraro tukuna Daddy.”

Daddy ya jinjina kai kafin yace “Ni zan wuce Company.. Sai na ganka a gida..”

Mu’azzam ya jinjina kai yana mai rakiyawa Daddyn har zuwa yanda motarsa ke ajiye driver na jira. Suka kuma yin sallama kafin Mu’azzam ya dawo cikin ofishin nasu.

Yana shigowa Assad ya K’araso yana fad’in “Barr Ameer Dikko, Safeenah’s lawyer is here.. Yana son ganawa da Safeenah..”

Sunan Ameer da Assad ya fad’i in full shine yai ringing a k’wak’walwar Mu’azzam. Barr Ameer Dikko.

Duban Assad yai kafin ya kuma duba Barr Ameer dake nufosu cikin takunsa na k’asaita.

Ya k’araso yana gaisar da Mu’azzam cikeda izgilanci irin yanda ya saba. Mu’azzam bai ce masa komai ba Sai aiaka masa muguwar kallo da yake yana nanata sunansa cikin zuciyarsa.

Assad ne yai masu jagoranci gaba d’aya zuwa interrogation yanda Safeenah ke zaune tana jira. A d’an Kwana guda da tai cikin Cell har kamanninta ya canza abinka da wacce bata saba da wahala ba. Farin fatar ta dik yayi wani irin jajaja alamun wahala da rashin sabo.

Ameer ne ya soma shiga suka gana kafin daga bisani Mu’azzam ya shigo. Safeenah na ganinsa ta fashe da kuka tana fad’in “My Halal I can’t believe you are doing this to me.. Please ka k’yaleni na tafi gida.. This place is hell..”

Ameer kaw takaici ya cikasa ganin yanda Safeenah ke shagwab’awa Mu’azzam tana wani kiransa her Halal.

Zama yai gefe yana mai aikawa Ameer mugun kallo. Bai amsa Safeenah ba still idanunsa na kan Ameer yake furta “Barrister Ameer Dikko is your enemy.!”

“Barr Ameer Dikko is ruining your home.!”

“Barr Ameer Dikko is very BAD”

“Barr Ameer Dikko you’re BAD”

Cikin rashin gane kalman nasa suke dubansa daga Ameer d’in har Safeenah.

Ameer ya girgiza kai yace “Ban fahimceka ba Inspector..?”

Murmushi Mu’azzam yai kafin yace “Ba Lallai ka fahimta ba amma Iyakacin abinda na sani YOU ARE BAD..”

Ameer ya kuma dubansa kai a k’ulle, lokaci guda Mu’azzam ya ciro wayarsa cikin aljihu yana nunawa Ameer sak’onnin BAD da akaita turo masa kwanakin baya. Ameer ya dubi sak’onnin da tsananin mamaki yana kuma duban Mu’azzam. Safeenah ma mamaki ne saman fuskarta cikin zuciyarta tana furta mai hakan yake nufi.

Mu’azzam yaci gaba da furta “Ko Wanene mai turo mun wad’ann sak’onnin gargad’i yake mun akanka BAD.. And that means yasan Kun jima kuna k’ulla wani abu kenan kaida Safeenah.. Let’s say Ikram Ta fahimci wani abu taakaninku da Safeenah.. And you two silenced her sabida kar ta sanar dani.. Am I right..?” Ya k’arashe yana dubansu su duka biyun.

Zuciyar Safeenah yai wani irin yankewa. Ta shiga girgiza kai tana fad’in “No.. Wllhi wlhi babu komai tsakanina da Ameer.. Wllhi bansan mai wannan sak’on ke nufi ba..”

“Ai dama bazaki sani ba. Amma shi wanda ya turo min wani clue yake so ya bani game da ku biyun..” Mu’azzam ya fad’i yana tsare Safeenar da idanu.

Ameer ya girgiza kai wannan karon yace “Excuse me Mr Office. Mai kake k’ok’arin fad’i.. What are you trying to accuse us of.? BAD everyone can be BAD.. You can also be BAD... Bad is just a word.. So don’t try to complicate things here..”

Murmushi Mu’azzam keyi wann karon yana duban Ameer d’in “We shall see.!”

Safeenah dake girgiza kai tana hawaye lokaci guda Ta soma fad’in “Wait Mu’azzam wllhi zan fad’i gaskiyar abinda ya faru.. Kar ka fara zargina da cin amanarka balle aurenmu ya lalace.. Wllhi zan fad’i komai koda bazaka yarda dani ba.”

Mu’azzam ya jinjina kai yana mai gyara zamansa lokaci guda yai alamawa Maleeka cewa ta shigo ta tattari bayanan Safeenah. Maleeka kaw kaman wacce take jira, nan take ta shigo.. Ameer sai aika mata mugun kallo yake a sace, yana tinanin idan ba Ita ba babu wanda zai tura ma Mu’azzam sak’on BAD dan yasan duk wanda ya tura sak’on so yake ya raba Mu’azzam d’in da Safeenah.. Maleeka ita kad’ai ce takeda wanann Motive d’in.

Mu’azzam ya dubi Safeenah yace “Ehen go ahead ina sauraronki.”

Safeenah ta soma fad’in “Kafin ranan aurenmu nayi receiving phone call daga wani mutumi, he told me he was an investor, yana son sayan Dairy milk da companyn mu ke producing... Ni kuma banso muyi losing client since ni ce ke rik’eda fannin saye da sayawarwa na Company d’in.. I didn’t want to disappoint Daddy.. I wanted to be perfect in his eyes.. Dikda cewa lokacin na kusan aure amma sai nayi accepting business proposal d’in.. Yai fixing date d’in da zamu had’u Mu tattauna kasuwancin, ranan ya fad’o daidai da ranan aurenmu.. Nace mishi bazai yuwu mu had’u mu tattauna kasuwancin wannan ranan ba amma sai yace mun shi baida lokaci daga wannan ranan, saidai a fasa kasuwancin.. Bana so muyi losing client nace masa babu damuwa zamu had’u mu tattauna kasuwancin.. Toh a ranan nayi receiving wannan text message d’in saidai banje location d’in ba dan zuciya na bai kwanta ba maiyasa zaice mu had’u a wani waje ba a Ma’aikatanmu ba.. Ban tab’a business da wani outside the company ba.. Shiyasa zuciyata bata aminta ba.. Kwatsam saiji nayi an tsinci gawan Ikram a wannan location d’in.. Wllhi wllhi Iyakacin abinda na sani kenan Mu’azzam.. Bansan ya akai Ikram ta tafi wannan location d’in da aka turo mun a matsayin meeting place ba..!” Ta k’arashe cikin kuka sosai.

Mu’azzam da yai mata k’uri Maleeka na gefe tana tattara bayanan cikin k’aramar littafi.

Mu’azzam ya kuma duban Safeenah kafin yace “And you expect me to believe your story..? Ta yaya zan San you’re not making it all up..? Idan gaskiya kike fad’i mai ya hanaki fad’i tuntuni..?”

Safeenah ta girgiza kai tace “Wllhi gaskiya nake fad’i wannan shine abinda ya faru.. Naji tsoron kar ka k’i amincewa dani ne shiyasa ban fad’i ba..”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “And shi mutumin da zaku k’ulla kasuwancin tare baki da contact dashi ne ko kuwa contact d’in ne ya yanke.?”

Ta girgiza kai tace “I don’t even know him..”

“How is this possible..?”

Tana bada amsa yana kuma rikitata da wasu tambayoyin.

Ta kuma girgiza kai tace “I lost contact with him tin wancan lokacin.. Na karya SIM card d’ina bayan na canza layi dan naji tsoro sosai da aka ce an sami gawan Ikram a wannan location d’in wanda bansan ya akai taje wajen ba.”

“We are in a Global world Safeenah.. Tracking mutumin bazai tab’a yin wahala muddin kin tab’a samun contact dashi.. Unless kuma bakinku d’aya ne Keda shi.. Maybe Kun datse duk wata hanya da zai nuna kun tab’a samun connection dan kawai ku rufe laifin da kuka aikata ke da shi na kisan Ikram.. Admit Safeenah.!” Ya k’arashe cikin tsananin tsawatarwa.

Ameer yai saurin dakatar dashi wannan karon “Inspector ya kamata ka gyara kalamanka...”

Yusuf ne ya katsesu da fad’in “Someone has just confessed to the crime.”

Mu’azzam ya juyo yana duban Yusuf, gaba d’ayansu dake cikin d’akin ma duban Yusuf suke.

Mu’azzam ya girgiza kai yace “Mai kace..?”


Yusuf yace “Wani mutumi ya zo yanzun nan sannan ya amsa laifin kisan Ikram...”


Mik’ewa tsaye Mu’azzam yai yana tambayan Yusuf “Where is he..?”

Yusuf yace “Gashi nan a office d’in Chief ana tattara bayanansa..”

Cikin sauri Mu’azzam yasa kai ya fice yayinda Yusuf ya take masa baya. Maleeka ma bin bayan abokan aikin nata tai.


Safeenah Ta dubi Ameer tace “Mai hakan yake nufi..?”

Ameer ya tab’e baki kad’an yace “Ta yaya zan sani..? Ai ke zan tambaya.. Kwatsam Ana tuhumarki saiga wani ya amsa laifin..? Watak’ila wancan investor d’in ne da kukai deal tare..”

Safeenah ta mik’e tana huci “Ai kuwa wllhi sai na shak’e D’anbanza naji uban da yasa ya sakani a wannan ukun..”

Ameer ya tare k’ofa yana dubanta kafin yace “Not too fast Safeenah.. Ki tsaya kiji da mai yazo.”

Harara Ta aikawa Ameer kafin tace “And who do you think you are da zaka dakatar dani.. Wanda yayi crime d’in ya bayyana kansa hakan yana nufin zan zama free sannan zan koma gidan Mijina.. Babu wata alak’a tsakanina dakai dan haka kar ka sake kallon ko yanda nake ne balle kace ka sanni..!”

Shaye da tsananin mamaki Ameer ke dubanta “Safeenah.! Ni kike gayawa magana haka dan wani ya ceceki ya amsa laifin..?”

Dakatar dashi tai da fad’in “Correction Mr Lawyer. Dama ban aikata laifin ba kuma nasan Allah bazai barni na biya abinda ban aikata ba.. Da wannan b’ata lokacin da kake da ka fara processing releasing papers d’ina ne dan ni ba mai laifi bace.”

Ameer ya jinjina kai yace “I see, toh dai kar ki mance ko da wani ya amsa laifin nan akwai wanda ya tura sak’on BAD wa mijinki a gefe.. Mu’azzam bazai kuma yarda dake ba musamman idan ya tina BAD.!” Ya k’arashe yana murmushi.

Zuciyar Safeenah yai wani irin yankewa ta dubesa tace “You are behind this Ameer..!”

Ameer ya murmusa yace “Maiyasa zan tura masa sak’on BAD bayan nasan hakan na nufin d’aure kaina zanyi wajensa.. Ai duk wanda ya tura masa sak’on BAD wani ne da ya fahimci recently ina damunki da waya sannan kuma yana so ya rabaki da Mu’azzam maybe dan shi ya samu kusanci da Mu’azzam d’in..” Yai maganar yana kashe mata idanu guda kafin yace “Aff! I mean ita.. Dan nasan definitely mace ce..!”

Zuciyar Safeenah yaci gaba da yankewa. Ameer ya barta nan tsaye tana tinanin waye yasan tana waya da Ameer yake so ya sanar da Mu’azzam ta wannan hanyar. Waye mafi kusanci da ita wanda yasan komai nata..? Take taji bakinta na furta “MEEMA.!”



*SameenaAleeyou📚*
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*



*34*






*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*






Mu’azzam yana shigowa ya damk’o mutumin da duka hannayensa biyu yana tambayarsa ma wa yake aiki. Assad da Chief suka janyesa bayan ya kaima mutumin

Please Login or Register in order to submit comment