Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya fad’i yana zuba sugar cubes a cikin tea.

Ya tsareta da idanu kafin ya d’auki mug na tea yana kurb’a. Wane b’angaren take duba ba shi d’in ba.

“You look good..” Ya fad’i yana dubanta.

“Thank you..” Ta basa amsa cikeda k’osawa murmushin da za’a iya kiransa da yak’e saman fuskarta. Lokaci guda ta kuma d’aure fuskar tana mai duban wani b’angaren.

Ya d’auki fork kafin ya janyo chips da liver sauce dake cikin bowl ya soma ci a hankali still idanunsa akanta “This food is delicious.. You made it..?”

D’an gyara murya tai kafin tace “Well, actually yes.. But only the sauce.”

Jinjina kai yai kad’an kafin yace “So you can cook like this..? I thought zama a gaban motar samari kawai kika iya..” Yai maganar yana cin abincin ba tareda ya dubeta.

Ta had’iyi maganar nasa tana mai kauda fusk. Saidai ba shid’inba bazai zauna bai yab’a mata magana ba. Wai ya zaci zama gaban motar samari kawai ta iya tsaban wulak’anci. Babu wanda ya kuma tanka kowa cikinsu saima cin abincinsa da yake peacefully.

Ya d’anci da yawa kafin ya d’auki tissue yana goge bakinsa.. Daidai lokacin wayarsa Ta soma ruri.

Ya d’aga yana murmushi ganin Inne ce mai kira. Saidya tanaji yanda yake fira gwanin ban sha’awa da Kakarsa.. Tanata mamakinsa dan Ita sam batai zaton na magana haka ba.. Koda yake Ta lura da selected people yakeyi dan ta kula sosai sabo mai tsanani ya shiga tsakaninsu shida Habeeb. Tana tsaka da tinanin ta sinkayo Muryarsa yana fad’in “Alright Inne.. Zan fad’a mata cewa kina gaisheta..” Ya kuma murmusawa kafin yace “Soon zan kawo maki ita in sha Allah..” Daga haka sallama sukai kafin ya dubi Sadiya da Ta b’ace shiru tamkar bata a wajen.

“Inne tace tana gaisheki.. And she wants to meet you soon..”

“Inne..?” Ta fad’i tana dubansa.

Jinjina mata kai yai yace “She’s my Grandmother.. Tace inada sa’a nayo mata kishiyoyi har biyu lokaci guda.” Yai maganar kaman ba daga bakinsa barkwancin ya fito ba.

Murmushi ne ya kufce mata wanda yafi kama da yak’e kafin tace “Amma ka mance baka fad’a ma Inne ba.. Cewa you create your own luck yourself.. And aurenmu na mission ne.. Ba mai d’orewa bane..”

Shiru yai yana dubanta kafin ya gyara zamansa yace “Look here.. Kalleni..” Ya fad’i yana tsareta da idanu.

Dukda gabanta dake tsananin fad’i hakan bai hanata k’ok’artawa Ta juyo tana dubansa ba. Sai kuma ta sadda idanunta a hankali tana jin bugun zuciyarta na k’aruwa.

“Sadiya..” D’agowa tai tana dubansa for the first da taji ya ambaci sunanta cikin wane irin siga da zata ce Ta tsinci kanta cikin yanayi mai wuyan fasaltuwa.. Mu’azzam yaci gaba da fad’in “We’ve been wearing each other out for quite some time now.. I don’t want to have another stressful conversation with you..I want to try and make peace with you.. Let’s try to do this.. Mu mance duk abinda ya faru and start a fresh..”

Jiki a matuk’ar sanyaye take dubansa, ji tai kaman ba shi bane mai maganan amma sai ta kauda kanta gefe tana jin wani abu kaman rauni na tasowa daga can k’asar zuciyarta. Lokaci guda wulak’anci da munanan maganganun da ya dinga jifarta dasu suna zuwa mata.

“Don’t you think you are asking for too much.. Mr Inspector.?”

Bai bata amsa ba Sai mik’ewa da yai yana gyara zaman d’amararsa “Don’t say a word.. Zamuyi magana da dare idan na dawo.. But for now.. Just come with me..” Bai jira cewarta ba ya shiga janyo hannunta.

Ta soma girgiza kai tana fad’in “But.. But wait.. Where are you taking me to..?”

“Don’t worry I won’t kidnap you again..” Ya bata amsa daidai sanda suka fito zuwa k’asar bishiyar da ya aje motarsa.


Jikin k’ofar motar ya tsaya ya d’an jingunu kad’an yana dubanta a hasken ranan hantsi yana jin wani abu mai kamada shauk’i cikin zuciyarsa.. Dik sai ta kuma tsarguwa da irin duban da yake mata.

“Do we have to stay here all day Inspector..?” Ta fad’i tana kuma ‘yan juye juye..

“ zamuyi magana da dare idan na dawo..And it’s about us.. Da makomar aurenmu..” Yana ida fad’in haka ya d’auko shopping bag k’arami mai kyau ya mik’a mata.

Bata amsa ba ta tsaya tana dubansa gabanta ya fad’i.. Watak’ila sakinta zai tinda dama auren nasu na mission ne kuma mission d’in ya k’are.

“Karb’a mana..” Ya fad’i yana kuma mik’o mata.

Ta d’an d’ago tana dubansa kafin tace “May I know what’s inside..?” Ta tambaya tana dubansa.

“You will see..” Ya fad’i yana mai kamo hannunta ya saka mata bag d’in cikin hannun nata.

“Make sure you on the phone.. I’ll call you later..” Ya fad’i yana shigewa cikin motar.

Ta d’ago bag d’in tana duba jin abinda ya fad’i kenan waya ya bata. Tai K’uri tana duban motar nasa.. Ta glass ya fito da kansa ya sakar mata murmushi kafin yace “It was a lovely breakfast.. Thank you..”

Bata iya furta komai ba Sai dubansa da take.. Har ya maida kansa cikin motar ta dakatar dashi “Inspector.”

Ya kuma ciro kansa yana dubanta.

“Thank you.. For saving me and my family..”

Murmushi ya sakar mata da gefen bakinsa kafin yace “You don’t need to thank me.. It’s my sworn duty as a police officer..” Ya bata amsa da fad’in haka kafin ya maida kansa cikin motar ya soma tafiya.

Tai tsaye tana dubansa har motar tasa Ta b’ace ma ganinta kafin Ta sauk’e ajiyan zuciya, ta kuma d’ago jakar tana juyawa maganganunsa na Yawo a kunnuwarta cewa Ta kunna wayar zasuyi magana.

Tana isa d’aki ta kulle k’ofar ita d’ayarta kafin ta soma bud’e jakan. Wani note ne Ta soma cin karo dashi. Ta d’auka a hankali tana warwarewa.. Saida ta nad’e k’afafunta kafin ta soma karantawa

_You have no idea with whom you are dancing..! MISSION CONTINUES..._

Rausayar da idanu tai tana mai girgiza kai “I knew it.. Bazaka tab’a canzawa ba Malam Inspector.. Ka canza salon wasan Naka kenan.. Zamu gani waye ya iya rawan tsakanin ni da kai..” Ta k’arashe tana mai juya takardan cikin hannunta.

Sauk’e ajiyan zuciya tai kafin ta linke takardan tana kuma ciro kwalin wayar.

**

Daga cikin restaurant d’in yanda Ameer ke zaune ya d’agowa Meema hannu alamu ta k’araso table d’insa. Meema ta d’an janye shades d’in dake idanunta kafin Ta k’arasa teburin Ameer d’in.

Yai mata K’uri yana dubanta har Ta zauna saman kujeran.

“Good morning..” Ameer ya fad’i still idanunsa akanta.

Ta saki murmushi da gefen bakinta kafin ta jinjina kai tace “Morning..”

“What do you want to have..?”

Ta girgiza masa kai “No I’m good.. Kar ka damu.. Magana kawai nazo muyi ba jimawa zanyi ba..”

Ameer ya mik’e yana fad’in “A’a zaki sha ko tea ne ko coffee it’s still morning ai..” Yana maganar yana d’aga kai yana neman inda waiter d’in ya tafi.

Meema tace “Da baka tak’ura kanka ba.. But since you insist, coffee will do.” Ta k’arashe tana mai d’aura k’afa d’aya bisa d’aya.

Tuni Ameer ya shige neman waiter d’in yana fad’in mata yanzu zai dawo.

Ta jinjina masa kai ba tareda tace komai ba.

Barin Ameer wajen keda wuya wayarsa ta soma ringing. Sunan Maleeka CID shi Meema ta ga ya bayyana saman screen d’in Ameer.. Meema Ta zaro idanu sosai tana kuma ganin sunan.. Tabbas Ta gane Maleeka abokiyar aikin Ya Mu’azzam ce.. Kenan tasan Ameer ne kodai dama Ita ce ta turawa Ya Mu’azzam sak’on BAD tinda dama Meema tasan Maleeka na son Mu’azzam dan itace cop d’in da suka tab’a zuwa har ofishinsu suka ci mutuncinta itada Addah Feenah.. Toh idan kuwa haka ne.. Yanzu ta fahimci duk abinda ya faru, kenan Ameer da Maleeka sunsan juna probably suna aiki tare domin cimma muradin junansu.

Har wayar Ta katse Ameer bai dawo ba, can ya dawo hannunsa rik’e da disposable cup. Ya ajiye gaban Meema yana fad’in “Your coffee..”

“Thank you..” Ta fad’i tana sakin murmushi da yafi kama da yak’e.

“Ina sauraronki.. Mecece tattaunawar da kike so muyi..?”

Meema ta sauk’e ajiyan zuciya dan ta riga ta sami abinda take nema tinda taga Maleeka na ma Ameer waya. Gudun kar ya fahimci wani abu yasa Ta murmusa tace “It’s about my sister.. She’s living a happy life now with her husband.. Bana fatan abinda zai b’ata mata wannan Farin ciki da take ciki.. Nazo nan ne na rok’eka on behalf of my entire Family.. Dan Allah Barr ka k’yale Safeenah haka.. Ka fita daga rayuwarta ka barta da mijinta.. Ka tuna cewa kai musulmi ne sannan kasan matsayin musulmi dake bibiyan matar aure.. Kuma kaima bazaka so a bibiye matarka ba. Dan Allah ka rabu da ita haka nan.. “ Ta k’arashe tana had’e hannayenta biyu alamun rok’o..

Murmushi Ameer yai kafin yace “Safeenah ce ta turoki nan kizo ki gaya min wad’ann kalaman..?”

Saurin girgiza kai Meema tai tace “No.. Addah Feenah bata San nazo nan ba.. Kawai rad’in kaina ne na tsara haka.. Sabida Ina k’aunar ‘yaruwata da kuma ci gabanta.. Kuma da Allah na had’aka ba da kowa ba.. Ka dubi girman Allah ka yada makaman yak’inka na neman auren Addah Feenah.. Ita d’in matar wani ce a halin yanzu..”

Shiru yai kaman mai nazari yana duban wani b’angaren kafin ya murmusa yace “I love your sister like I never loved someone before.. Ina tsananin k’aunar Safeenah wanda yasa zan iya aiwatar da komai domin naga na mallaketa.. Amma tinda kikazo har nan kikace haka.. Zan gwada dannar zuciyata idan zata iya amincewa.. But I’m still not sure idan zan ita cire Safeenah cikin sauk’i daga zuciyata..” Daga haka mik’ewa yai ya saka glasses d’insa kafin ya cire suit d’insa da ya lank’aye jikin kujera ya saka a jikinsa “Zan wuce chamber.. Dik yanda mukayi da zuciyata zakiji ni..”

Murmushi Meema ta sakar masa kafin Ta kuma masa godiya.. Ameer yasa kai ya shige.

Yana ficewa Meema Ta sauk’e ajiyan zuciya kafin tai saurin zaro wayarta Ta shiga dialing layin Safeenah dan ta sanar da ita ha wacce ta had’ata da mijinta.

Saidai kiran duniya Meema tayi Safeenah bata d’aga wayarta ba.. Ta lumshe idanu a hankali dan tasan zai wuya Safeenah Ta d’aga kiranta tinda tana tsananin fushi da ita.

**

An gama dressing ma Assad kenan ya shigo.. Suka sakar ma juna murmushi kafin Mu’azzam ya k’arasa ya mik’a masa hannu sukai masabaha.

“Detective, How are you feeling now..?” Ya tambaya yana duban Assad d’in.

“Much better, Sir..” Assad ya basa amsa murmushi saman fuskarsa.

Gaba d’aya murmushin suke kafin Assad yace “Ya meeting d’in naku da DIG ya kasance..?”

Mu’azzam ya fuzar da fuci kad’an kafin yace “Believe me, It was so stressful..!”

Assad ya murmusa kad’an kafin yace “Ba damuwa an karb’o Sady yanzu sann ga kuma Safeenah.. Zasu had’u Su d’auke duk stress d’in nan I believe..” Ya kuma murmusawa kafin yace “Mission zai ci gaba kenan.. I still can’t believe that Mu’azzam Gamji is finally falling in love..”

Da wutsiyar idanu Mu’azzam ke dubansa kafin ya d’an tsime yace “You should stop watching those Indian movies.. They are filling your head with nonsense..” Ya k’arashe yana wani tsimewa.

Assad ya murmusa yace “Mudai mun zuba ido mun zuba kunne muga yanda mission zata kaya..”

Kauda zancen Mu’azzam yai da fad’in “Wai ina Shaheed ne..?”

“Ya fice d’azu amma yace ba jimawa zai ba..”

Ya jinjina kai kad’an kafin yace “Maleeka tazo ta dubaka..?”

Assad ya d’anyi jim kafin ya girgiza kai yace “Yusuf dai yace min jiya Sun shigo ina bacci.. Why.. Maiyasa ka tambaya.?”

Mu’azzam ya k’urama waje guda idanu kafin ya d’ago ya dubi Assad yace “Haven’t you noticed anything suspicious tareda Ita..?”

Assad ya girgiza kai yace “Ban fahimta ba..?”

Mu’azzam ya tako kad’an kafin yaci gaba da fad’in “Randa muka fita operation d’in nan.. Something was off with her.. She looked quite disturbed.. Kaman tana b’oye wani abu..?”

Assad ya murmusa yana mai d’an girgiza kai kafin yace “Wacce Ta ceci rayuwarka ne zaka mata wannan zargin.. You owe her a huge debt of gratitude.. She saved your life Mu’azzam..”

K’ura masa idanu Mu’azzam yai kafin yace “Da alama har yanzu baka fahimci abinda na gano ba.. Naji she saved my life.. But Maiyasa babu wanda yaga mai harbin cikin kai da Yusuf sai ita..? Sannan muna isa wajen aka soma attacking namu alamun informant d’insu ya sanar dasu muna hanya..”

Assad yai shiru yana nazari kafin ya dubi Mu’azzam yace “Kana tunanin tana aiki dasu Danger.. And she could be the mole in our group..?”

Ya jinjina kai a hankali kafin yace “Possibly..” Ya gyara tsayuwarsa kad’an kafin yace “Kawai ban yarda da ita ba Assad.. Inaji a jikina itace mai mana zagon k’asa..”

Assad ya d’an sauk’e ajiyan zuciya kad’an kafin yace “Ban tab’a kawowa koda tunanin Maleeka zatai abu mai kama da haka ba..”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “We are still not sure.. But they say mugu baida kama..”

Assad yace “Haka ne..Kace wani abu..” Ya k’arada yaushe ne DNA result d’in B.A.T zai fito.?”

“In three days time.. Nan zuwa gobe kenan..”

Assad ya d’an gyara daga yanda yake kishingid’e yana fad’in “Nima dai bazan wuce kwana biyu a nan ba.. Na riga na warke.”

“Hey don’t rush Detective.. Ka bari ka ida samun lafia babu abin hanzari.. Duk da cewa yau a meeting d’inmu da DIG mutuminka neman duk wata hanya da za’ai watsi da case d’in nan yake.. Amma babu abinda zai achieving bazan bashi wann satisfaction d’in ba..”

Assad yace “Jaja will never backdown.”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “Ka barshi idan b’era na Yawo mage na Yawo zasu had’e wata rana..”

Assad yace “Kenan idan Jaja na kare ‘yanta’addan nan zai iya yuwa yana aiki tareda Maleeka.”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “Exactly.. Nasan kamasu redhanded zai matuk’ar wuya but believe me, we will play myth games.” Ya k’arashe yana jinjina kai a hankali lokaci guda Ya duba agogon dake d’aure hannunsa na hagu “I’ve to go now na maka hira da yawa ai..”

Assad ya murmusa yace “Mai iyalai.. Aima kayi k’ok’ari.. Thank you very much..”

Girgiza kai kurum Mu’azzam yai kafin yace “Don’t let me punch your wound.”

Assad ya darara kad’an daidai lokacin Shaheed k’anin Assad ya shigo suka gaisa yana takama Mu’azzam d’in.

**

Babu yanda Meema batai ba Patrick ya barta Ta shiga wajen Safeenah amma fir ya hana yace Safeenar ce tace ita bata San da zuwan wata Meema ba, bama ta da k’anwa mai wann sunan.

K’arshe Safeenar da kanta Ta fito tana yatsina fuska take duban Meemar daga gate yanda Patrick ya hanata shiga.

Meema da Ta hango Safeenah ta kuma saurin matsowa jikin gate d’in tana fad’in “Addah Feenah please let us talk.. I have something important to tell you..”

Patrick ya dubi Safeenah yace “Ma’am, should I let her in..?”

A yatsine Safeenah ke duban Meema kafin ta dawo da dubanta ya Patrick tace “Don’t you dare.. Kai ko mai kamanninta ce tazo kar ka barta Ta shigar mun gida.. I don’t know her.”

Meema baki sake take duban Safeenah kafin tace “Addah Feenah ni kike kora haka daga gidanki har kina cewa ko mai kamanni na kar a bari ta shiga..? Addah Feenah ni ce Meema fah.. Your sister..”

Safeenah ta juyo tana aika mata mugun kallo “I don’t remember having a sister like you..”

Ta maidoda dubanta ga Patrick tace “Kai kuma idan ka barta ta shigo a bakin aikin ka.. Idan ta matsa sai ta shigo ka kwance mata karnukan nan..” Daga haka Safeenah sa kai tai ta shige cikin gida abinta.

Aka bar Meema baki sake tana duban Safeenah har ta b’acewa ganinta.

Fuzar da fuci kad’an Meema tai kafin Ta wuce ta shiga mota ta bar wajen.

Tana isowa gida ta tadda Kiki tana jiran k’arasowarta. Jiki babu laka Meema ta zauna cikin kujera tana kwance belt d’in takalmin dake k’afarta.

Kiki Ta dubeta tace “Ehen, ya kukayi da Adda Feenah..?”

Meema ta tab’e baki kad’an tace “She wouldn’t listen to me.. Tama hanani shiga Gidanta.. Tayi instructing security man d’insu cewa idan na shiga ya kwance min karnuka..”

Baki sake Kiki ke dubanta “Addah Feenah ce ta miki haka.. Anya kuwa Meema..?”

Meema ta kuma tab’e baki tace “Kinsan dai na daina tsara zance.. Wllhi gaskiya nake fad’a miki.. Addah Feenah shut me off..”

Kiki ta jinjina kai cikeda Mamaki “Yanzu kece Wai Addah Feenah ta kora daga gidanta..”

Meema bata kai ga bada amsa ba suka sinkayo muryar Mommy tana fad’in “Wacece Safeenah ta kora..?”

Kiki Ta dubi Mommy tace “Mommy Wai fah Meema ce Addah Feenah ta hana shiga gidanta.. Can you imagine..”

Mommy ta jinjina kai tace “Ai Safeenah ta zama sallamammiya.. Ku k’yaleta bata cikin hayyacinta.. Gata ga namiji idan ya gurza mata guda d’aya k’wakk’wara zata dawo cikin hankalinta.. Sannan ne zata nemi ahalinta..” Mommy tana ida fad’in haka tai k’wafa kafin tai shigewarta zuciyarta fam takaicin Safeenah.

Meema da Kiki suka dubi juna kawai ba tareda sunce komai ba.

**

Tana jin shigowar motar Mu’azzam Ta mik’e tana gyara kwalliyarta. Abincin da tai googling Ta girka Ta shiga jerawa saman dining table.. Tayi kyau kam dan kyau dan Safeenah akwai iya gayu ma jiki da kwalliya. Saidai fah kana iya hango kwantattun k’ura cikin gidan Dikda kuwa ta daure tayi picking wanda idanu ke iya gani.

Mu’azzam na shigowa Ta tafi Ta D’ale jikinsa tana masa sannu da zuwa.

Ya sakar mata gajeren murmushi yana mai amsa gaisuwarta.

“My Halal.. Nayi kewarka da yawa.. I thought zaka dawo da wuri.” Ta k’arashe tana turo baki.

Murmushi ya sakar mata a d’an gajiyye kafin ya kai dubansa ga dining table yaga komai a shirye.

Da mamaki ya juyo yana dubanta “You cooked all this..?”

Ta jinjina masa kai tana juya idanu “Of course..”

Ya d’an rage girman idanunsa yana dubanta “For real..?”

Ta d’an turo baki tana juya idanu “Haba my Halal na maka girki instead kaji dad’i shine kake doubting d’ina..”

Ya jinjina kai yace “Naji dad’i.. I’ll take a shower first Sai na sauk’o muci abincin..” Ya k’arashe yana mik’a mata k’aramar shopping bag irin wacce ya bawa Sadiya.

Safeenah ta Ware idanu tana amsa “Wow.. Menene wann. A surprise gift.?” Ta k’arashe tana ciro kwalin sabuwar wayar.

Mu’azzam yace “Nasan bata kai naki kyau da tsada ba.”

Rungumesa tai tana fad’in “Duk abinda ya fito daga wajenka is priceless a wajena.. Thank you My Halal.”

Ya sakar mata murmushi kafin yace bari yai wanka.

Ta jinjina kai cikeda jin dad’i tana mai take masa baya.

Da k’yar ta barsa yai wanka da kansa. Shiryawa ma ita ta tayasa.. Suka nufo parlor a tare ta mak’alesa tsam cikin jikinta. Safeenah Ita Ta janyo masa kujera ya zauna kafin Ta soma serving nasa.

Kallo d’aya yaima abincin yaji ya k’oshi, bai dai ce komai ba har ta soma serving abincin.

“Do you want me to feed you..?” Ta fad’i tana mai zama kujerar gefensa.

“Kar ki damu I can feed myself.” Ya fad’i yana janyo plate d’in.

Spoon d’aya yai ya dakata..

Safeenah ta tsaresa da idanu tana duban reaction d’insa. Yinin ranan a YouTube ta k’are tana checking recipes d’in da zata girka masa.

Da k’yar ya had’iyi abincin da ya saka bakinsa yai saurin janyo ruwa ya tsiyaya a cup yana kwankwad’a “It’s too spicy.. Wann abincin baza’a iya ci ba Safeenah.. Ga gishiri ga yaji.. Ya kuma janyo ruwa yana sha yana hura iska ma bakinsa.

Safeenah tai saurin matsowa kusansa ta amshe glass cup d’in Ta aje saman dining table tace “Nasan maganin yajin..” kafin yai aune ta rufe masa baki da nata.. Daga nan bata yarda Ta bar jikinsa ba har saida Ta tabbata an isa yanda take so.

K’ara shiryawa yai cikin k’anan kaya kafin ya kuma ficewa.

Safeenah fitowa tai daga bathroom taga baya nan.. K’aran ficewar motarsa kurum taji.. Tai saurin janye labule tana lek’e tana mamakin Toh ina ya kuma ficewa..?

Kodai wajen wancan ‘Yariskar ya tafi ne..? Toh amma ai basa tare yanzu dama auren mission ne sukai ta tabbata Mu’azzam babu abinda zai da wann yarinyar tinda har Ta gama zamanta cikin gidan babu wani abinda ya shiga tsakaninsu.. Bazata saka ma ranta wani damuwa ba yanda Ta samu yanzu suke zaune lafiya tana samun kula da tarairaya daga mijinta.

Sauk’owa k’asa tai tana duban abincin da suka kasa ci. Tai tsaki a hankali tana yatsina fuska “Kai Kai Feenah anya zaki iya wann d’awainiyar..?” Ta tambayi kanta tana duban gidan. Tsaki tai kafin ta isa dining table d’in ta shiga d’iban abincin tana juyewa cikin dustbin. Tanayi tana mitan bazata iya wann wahalar ba. K’arya da ciwo gwara taci gaba da yo masu order idan yaso sai tace ita ta girka.

**

Duba d’aya Sadiya tai masa ta sadda kanta.

Yai gyaran murya kad’an kafin yaci gaba da fad’in “Bazan k’ara tilasta miki komai ba, kuma bazan kuma d’aukan ki bada amincewarki ba.”

Ta d’an girgiza kai kafin tace “Amma ai kai da kanka kace auren mission mukai kuma gidanka tamkar dai GIDAN ARO yake a wajena.. Maiyasa zan koma bayan an gama mission d’in.”

Idanunsa k’ar akanta “Nayi alk’awari ma Inne zan kai mata ke.. Bani d’in bane mai son tafiya dake..”

Murmushin da yafi kama da yak’e tai kafin tace “Maiyasa ka kasa sanar da Inne gaskiya cewa Auren Mission kai dani.. Kuma mission d’in ya k’are.”

D’an kauda kansa gefe yai yana fuzar da fuci kad’an. Ya kuma dubanta yace “Wai ke baza’ayi peaceful conversation dake ba. Dan ma ana son tafiya dake.. Ba don Inne tace a kai mata ke ba Maiyasa ma zanyi tafiya dake bayan inada wata matar.. Kema Kinsan bake kad’ai gareni ba..”

Ta d’an juyar da fuskarta kad’an kafin tace “Maiyasa bazaka tafi da matar taka ba.. Tinda kanada ita..”

“Bakiji mai nace miki bane.. Badon Inne ba bazanje dake ba. Ita ke son ganinki kuma na mata alk’awari zan kai mata ke.. Nasan bazaki bari na sab’a wann alk’awarin da nai mata ba.”

Ta d’an dubesa kafin tace “Is this my new assignment..? Is this another mission..? Idan mun dawo mission d’in ya k’are..?.”

“Mai kike so ayi yanzu.?” Ya tambaya yana dubanta.


“Zanje sabida kace Inne.. Amma idan na dawo mission d’in ya k’are.. Kuma inada condition d’aya kafin na bika..”

Ya tsareta da idanu yana dubanta Wai sai ta gindaya masa sharud’a kafin Ta yarda Ta bisa.

“Meye condition d’in naki..?”

Muryarta ya sinkayo tana fad’in ”Sai ka rantse min da Allah zaka sakeni da zaran mun dawo kuma zaka fice daga rayuwata gaba d’aya.”

Da tsananin mamaki Mu’azzam ke dubanta Wai sai ya mata rantsuwa zai saketa kafin Ta yarda ta bisa.

Umma da Ta fito daga d’aki zata nufi kitchen Ta sinkayo tattaunawar nasu Sadiya na fad’in sai Mu’azzam ya rantse zai saketa kafin Ta amince ta bisa garinsu. Fasa shiga kitchen d’in tai Ta k’araso parlorn da sallama. Mu’azzam ya risina ya gaisheta.

Ta amsa tana aika ma Sadiya mugun kallo nan take tambayarsa jikin Mamynsa Ta kuma sanar dashi sunyi waya da Inne jiya da dare tace jikin Mamyn nasa da sauk’i. Mu’azzam yanata amsa mata cikin girmamawa yana fad’in aima yanaso yaje ya dubasu idan abubuwa suka d’an lafa.. Umma tace “Aikam ya kamata.. Allah dai ya bata lafiya yasa kaffara ne.”

Mu’azzam yanata amsawa da Ameen Umma yayinda Sadiya keta dubansu tana mamakin yaushe har sukai Sabo haka har Umma tasan ‘Yan gidansu suna gaisawa a waya. Bata ida tinanin ba Ta sinkayo muryar Umma na Ta taso suyi magana.

Jiki babu laka Sadiya tabi bayan Umma dan taga irin duban da Umman tai mata.


Tana shigowa d’akin taji sauk’an mari mai kyau a fuskarta.

Ta kame fuskarta tana kuka.

Umma na huci take nunata da yatsa “Ashe Bakida mutunci.. Ashe ke mahaukaciya ce ban Sani ba.. Mijin naki kike cewa yayi rantsuwa zai sakeki dan kawai yace yana so ya d’aukeki.. Ashe baki d’auki darasi kan abinda ya faru dani da mahaifinki ba.? Toh idan ya sakeki d’in sai muga ina zaki tafi dan nan ma alfarmarsa kikeci.. Yanzu Sadiya ashe duk karatun da duniya ta biya miki baki d’auki darasi ba.!”

Cikin kuka Sadiya ke fad’in “Umma fah baki San mai ya mun bane sanda ya d’aukeni. Yace mun ‘yar tasha ya kirani da sunaye masu muni har had’ani da Karnukansa yai yace ni Kariya ce.”

Umma ta kuma kai mata bugu tana fad’in “Sai mai dan yace miki haka.. Wa ya ja ma kansa.. Ke har kinada bakin magana bayan rufa miki asiri da yayi.. Mutumin da ya biya miki bashi ya tsare miki mutuncinki da na ahalinki ya kub’utar dake da ahalinki wannan mutumin kike k’ok’arin wulak’antawa.. Ashe idan baki gode masa ba har zaki wulak’antasa.. Ke bandama taimakon Ubangiji ina zaki samu miji irin Mu’azzam.. Har kina wani gindaya masa sharud’a shi bai

Please Login or Register in order to submit comment