Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

not a murderer.. Kar kiyi abinda zaki zo kina danasani for the rest of your life.. Please Addah Feenah..”

“Komin shiru nace Meema ko na had’a dake.. Dama dukanku munafukai ne bakinku d’aya duk son mijina kuke.. Mijina is mine.. Nawa ne ni kad’ai.. Zan fara daga ita kafin na dawo kanki Mema.!” Ta k’arashe tana kuma nuna Sadiya da bindigar.

Daidai lokacin Mommy ta shigo a firgice.

Ta shiga girgiza kai tana fad’in “A’a Safeenah.. Mai kikeyi haka..?”

Cikin zuban hawaye Safeenah ke fad’in “Wllhi sai na kasheta Mommy.. Bazan bari ta shiga tsakani na da my Halal ba..!” Ta kuma saita Ta da dindigar.. Daidai lokaci Mommy Ta soma takowa a hankali tana yunk’urin k’wace bindigar.. Buge hannun Safeenah da Mommy zatai yai daidai da harba bindigar.

Mu’azzam da Musaddiq da fitowarsu kenan daga sashen Musaddiq d’in nan sukaji sautin harbi daga sashen Daddy ga motar Safeenah pake a gefe ko rufe marfin motar batai ba. A tare suka nufi b’angaren Daddy a guje.




SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*46*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*






Safeenah bata saki bindigar ba dukda rawa da jikinta keyi.

Sadiya da Meema da suka tak’ure waje guda rik’eda juna idanunsu duka biyu a rintse dan basu San wa aka harba cikinsu ba. Su dai kawai sunji sautin fitan harsashi.. Muryar Musaddiq ne ya sanyasu bud’e idanunsu har lokacin suna rik’eda juna. Nan sukaga yanda harsashin ya huda jikin gini.

Musaddiq ya nufo Safeenah yana fad’in “Feenah bani bindigar nan..”

Nunasa tai da bindigar tana ci gaba da huci take fad’in “Don’t come near me Musaddiq.. Stay back.. Kar ka matso kusana..!” Tai maganar tana nunasa da bindigar.

Daidai lokacin Mu’azzam ya nufota yana fad’in “Bai nan.. Bani bindigar nan Safeenah..!”

“What if na hanaka..? Mugu kawai.. Macuci.. Maci amana..! Azzalumi.. Mai ha’intar aure... Da kai ya kamata ma na fara kafin na k’araso kan ‘yariskar da kake cin amanata da ita..!” Ta k’arashe tana saita Mu’azzam d’in da bindigar.

Da rinannun idanunsa yake dubanta ba tareda yayi ko gizau ba. Shine Safeenah take gaya masa maganganu son ranta irin haka.. Ya jinjina kai still yana dubanta. Ba laifinta bane.. Laifinsa ne da ya bari taga girmansa.

Cikin dakewa ya kuma fad’in “Hand me over that gun..!” Ya fad’i yana dubanta.

Safeenah ta kuma girgiza kai tana hawaye, lokaci guda take furta “Bazan bada ba.. You choose between ni da wannan ‘Yariskar..” Ta k’arashe tana mai nuna Sadiya da bindigar.

Izuwa lokacin zuciyarsa ta gama kai k’ololuwa wajen tafarfasa ya nufota a zafafe yana fad’in Ta basa bindigar.

Saitasa tai da bindigar tana huci take fad’in “If you take one more step.. I swear I won’t hesitate to shoot you right in the head..And believe me, I mean it..!” Tai maganar sai sakin huci take tana nunasa da bindigar cikin tsananin zafin kishi wanda ya rufe mata idanu ruf bata ganin komai.

Izuwa lokacin kam ya tabbatar ma zuciyarsa k’wak’walwar Safeenah ta samu matsala, ba daidai take aiki ba. Yai mata K’uri yana dubanta da idanunsa da tuni sun kad’a.

Cikin huci Safeenah dake pointing nasa da bindiga take fad’in “Ka zaci Allah bazai toni asirinka bane.. Kana can ka ajiye wann karuwar a wani waje without my knowledge.. Toh Allah ya kamaka yanzu sai ka zab’a ko ni ko ita.. Idan ka cika kai Mu’azzam Gamji ne ka zab’a yanzun nan wacece zakai zaman aure da ita.. Ni Safeenah ko wannan ‘Yariskar..!” Ta k’arash still tana nunasa da bindiga.

“Haka kika ce..?” Ya fad’i yana dubanta.

Safeenah Ta jinjina kai tana fad’in “Eh haka nace.. You choose between us..” Tana maganar zuciyarta na k’arfafa mata gwiwa da fad’in Mu’azzam yana matuk’ar k’aunarki tinda har ya kasa sanar dake yana tare da yarinyar.. Hakan na nufin yana shakkun b’acin ranki ne.. Bazai iya rayuwa babu ke ba. Wannan ya tabbatar miki da irin k’aunar da yake miki.. Bata ida tunanin nata ba ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Na sakeki Safeenah..!”

K’ara ta saki tana mai d’aura hannayenta biyu aka dai dai lokacin Musaddiq yai azama ya fincike bindigar daga cikin hannunta.

Sadiya ta saki Meema ta nufo mijinta Wanda shid’inma tuni ya nufota. Rungumeta yai tana mai fashewa da wani irin kuka jikinta har lokacin bai daina rawa ba.

Safeenah Ta kuma fincika daga rik’onda Musaddiq da Mommy sukai mata tana fad’in “Wllhi Mommy sai na kasheta.. Mommy kina gani My Halal ya zab’i wannan ‘Yariskar sama dani.. Wllhi sai na kasheta..” Sai ihu take tana fincika tana fad’in su saketa..

Daidai lokacin Daddy ya shigo ya tadda wann hatsaniyar.

Mommy ta fashe da kuka tana salati tana fad’in “Ehh Lallai Mu’azzam ka tabbata.. Ka cika tabbatacce.. Ko mutuwa na kunyan idon uwa.. Ni tinda nake ban tab’a ji anyi saki gaban uwa ba.. Na shiga uku ni Hajara..” Ta dubi Daddy kafin taci gaba da tafe hannaye tana fad’in “Kazo kaga abinda D’an matarka ya aikata ma d’iyarka.. Ya zab’i bare sama da jininsa..”

“Enough please Mommy..!” Musaddiq ya dakatar da Ita cikeda takaici. Lokaci guda yake ci gaba da furta “Aiko bai saketa ba Cikin gida biyu ‘yarki zata kasance a guda d’aya.. Kodai Ta tafi gidan Yari ko ta tafi asibitin mahaukata dan babu hankali tattare da Safeenah. Balle ma ita ta buk’aci hakan da kanta.”

Safeenah ta kuma kurma ihu ta tsalle tana fad’in atafau bazata yarda ba babu wanda ya isa ya rabata da halal d’inta..

Meema ta k’araso kusanta sanda zata fice, tana duban Safeenar a yatsine. Murya can k’asa tace “Ai saidai kiyi hak’uri Addah Feenah dan Ya Mu’azzam ya zama haram a gareki yanzu kam..”

Safeenah ta zabura zata kamo Meema. Tuni Meema ta fice ta basu waje. Musaddiq ya shiga karanto ma Daddy abinda ya faru yana nuna masa jikin garu yanda Safeenah ta huda da harsashi. Ya k’ara da “Daddy what Safeenah needs is a Dr.. A psychiatrist m.. Likitan mahaukata take buk’ata Daddy.. She’s not well..”

Haba nan fah Safeenah ta hayayyak’osa tana fad’in lafiyarta lau sune mahaukata da suke tunanin zata rabu da Halal d’inta.

Musaddiq ya girgiza kai yana mai jan gajeren tsaki kafin ya dubi Mu’azzam yace zai jirasu a Mota.

Jinjina masa kai kurum Mu’azzam yai kafin Musaddiq d’in ya fice.

Daddy ya dubi Mu’azzam da Sadiya wacce ke tsaye gefensa kanta a k’asa kana gani zaka fahimci har lokacin a razane take. Daddy yace “D’auki matarka ku tafi Mu’azzam kar ku rasa flight d’inku.”

Safeenah Ta kurma wani irin razannan ihu tana fad’in babu yanda zasu tafi wllhi.

Ta tafi a guje tana k’ok’arin rik’o Daddy dake haurawa upstairs tana fad’in “Daddy wllhi sakin k’arya ne.. Wllhi My Halal bai sakeni ba.. Mommy ce ta masa dole..”

Haba nan fah Mommy ta hayayyak’ota da fad’in “Ni zaki ma sharri Ina mahaifiyarki..! Allah yasa ba ni kad’ai bace wajen.. Daidai kenan yanzu Kinga ranan zab’en namiji akan mahaifiyarki.. Gashi ya zab’i matar da yai auren bariki da Ita ya barki.. Yanzu zaki dawo cikin hayyacinki Safeenah..”

Mu’azzam dai bai kuma bi takansu ba ya janyo hannun matarsa suka fice suka bar Mommy da Safeenah sai rantse rantse suke gaban Daddy..

Safeenah tana fad’in Mommy ce ta zugota tazo Mommy tana fad’in hakkin abinda tai mata ne ya kamata.

A guje Safeenah tabi bayansu kaman sabuwar kamun hauka.. Mu’azzam zai shige Mota Safeenah ta rik’o rigarsa tana fad’in “My Halal.. Dan Allah kace sakin wasa ne.. My Halal you know I can’t do without you.. Please Mu’azzam kar ka tafi ka barni..!” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka.

Kallanta yai ya kalli yanda Ta rik’e masa riga kafin yace “A hukumance abinda kikayi za’a d’aureki akan hakan, Kinyi attempting murder.. Kin sake cin albarkacin Daddy bazan jefaki a cell ba.. Kaman yanda dama zaman auren da kikayi albarkacinsa kika ci.. Sakar min rigata.. You are not my wife..!” Yana ida fad’in haka ya finciki rigarsa yai shigewarsa Mota.

Safeenah tabi motar a guje tana fad’in my Halal.. Inaa tuni motar ta fice daga gidan.

Ihu ta kuma zundumawa ta nufi cikin gidan tana kuka tana fad’in wllhi sai ta bisu ta dawo da halal d’inta saidai ai duk abinda za’ayi.

Zata shige Mota kenan taga Daddy tsaye gabanta ya kai k’ololuwa wajen had’e rai.

“Give me the keys..” Ya fad’i yana mik’a mata hannu.

Girgiza kai take tana hawaye “Daddy please ka barni na bi mijina.. Daddy wllhi sharrin shaid’an ne.. Daddy zafin kishi ne bansan abinda nake aikatawa ba.. Daddy na tuba dan Allah ka barni nabi Mu’azzam.. Wllhi mutuwa zanyi Daddy idan har ya rabu dani.. Please Daddy dan Allah ka ceceni.. Daddy I’m your Daughter please..!” Ta k’arashe tana mai duk’awa had’ida rik’e k’afafun Daddy tana kuka sosai.

Abinka da d’a da mahaifi, Zuciyar Daddy ta raunana.. A hankali ya mik’a hannu ya kamo Safeenah ya tada ita tsaye.. Safeenah ta kuma fashewa da kuka tana mai fad’awa jikin mahaifinta. Bai hanata kukan ba, saida tai mai isarta kafin ya kamo hannunta suka nufi parlornsa. Zaunar Ta saman kujera yai yana dubanta cikeda tausayawa.. Shi kansa ya fara tsoron kardai Kwanyar Safeenah ya tab’u ne.

Ruwa ya mik’o mata yace tasha.. Babu musu ta amsa ta kafa kanta ta shanye still hawaye na gangaro mata.

“Safeenah inaso ki nastu ki nitsa hankalinki waje guda.. Safeenah da halayya irin wannan bazaki tab’a samun kwanciyar hankali a gidanki ba.. Bindiga Safeenah.. Kisan kai zakiyi akan wata ta auri mijinki..? Waye yace miki shi mijinki ne ke kad’ai.. Waye ya baki wann guarantee d’in..?!” Ya d’an k’arashe cikin tsawatarwa

Safeenah batace komai ba Sai kifa kanta da tai tana hawaye.

Daddy ya jinjina kai kafin yaci gaba da fad’in “Mu’azzam yana d’aga miki k’afa, yana duba girman zumunci.. Amma ba don haka ba abinda kika aikata yau da ya kulleki a gidan Yari.. Why Safeenah.. Maiysa kike nema ki haukarta da kanki babu gaira babu dalili.. Kan rayuwar duniya da k’alilance ba tabbata za’ayi ba.. Idan kikayi hak’uri wataran babu ke ko Babu abokiyar zaman taki ko ma Babu mijin da ake ta faman tada jijiyan wuya akansa.. Rayuwar duka batada yawa Safeenah.. Har yaushe zakije ki jefa kanki a halak’a sabida soyayya.. Ai so ba hauka bane Safeenah..!” Ya d’anyi fasali yana dubanta. kafin ya d’ago yatsa yana nunata “Toh ki kula.. Ki sani rayuwar duka batada yawa.. Yau idan mune gobe ba mu bane.. Idan kuma baki natsu kin daina wann haukar naki ba Ina mai tabbatar miki ni da kaina zan d’aukeki na kaiki mental facility kin jini koh..?!”

Safeenah ta d’ago tana dubansa “Daddy asibitin mahaukata kuma..? Daddy wllhi da hankali na.. Kawai son mijina nake... Daddy na saba dashi bazan iya rayuwa babu shi ba.. Dan ka barni na bisu Daddy..”

Mik’ewa Daddy yai yana dubanta cikin tsananin b’acin rai “Idan kika sa k’afa kika fice daga gidan nan.. Ki nemi wani mahaifin amma bani ba Safeenah..!” Daga haka Sa kai yai ya haura upstairs..

Safeenah tai mutuwar zaune tana duban mahaifinta har ya haye sama.. Wani irin sabon k’unci da kuka ne taji sun taru sun bugi k’irjinta lokaci guda.. Ta mik’e ta fice ta nufi side d’un Mommy tana kuka kaman ranta zai fice..

Saidai tana zuwa Mommy ta haura sama ta k’yaleta ita kad’ai.. Tabi bayan Mommy da sauri tana kiranta.. Ko kallo bata ishi Mommy ba balle ta tankata. Tanaji Mommy ta banko k’ofar d’akinta da k’arfin gaske ta rufe akan fuskar Safeenar.

Juyowa tai ta dubi k’ofar d’akin Meema dake bud’e. Nan ta hangi Meema saman gadon tana karatun novel.. Suna had’a idanu Meema ta mik’e ta k’araso ta tura k’ofar d’akinta ta rufe..

Silalewa Safeenah tai a wajen tana kuka mai tsuma zuciya.

**

Assad kaw bashi ya farka ba Sai wajajen can bayan azahar, ya mik’e ya gansa kwance a d’aki babu riga jikinsa, daga shi sai shorts.. Mamaki ya cikasa.. Yai saurin janyo rigarsa yana rufawa, yana dafe kansa da yai masa nauyi lokaci guda yana tuno abubuwan da suka faru.. Innanlillahi wa inna’ilaihi raji’un kurum zuciyarsa ke iya nanatawa.. Meke faruwa..? Mai ya faru dashi. Take ya soma tuna cewa Maleeka tazo tana neman taimakonsa.. Toh ya akai ya k’are a d’aki kuma undressed.. Cikin sauri ya mik’e yana duba lokaci.. Wai meke faruwa ne..? Mai ya faru..? Tambayoyi da dama cikin zuciyarsa da ya gaza samo amsoshinsu.

A fujajan ya fice parlor yana dubawa ko zaiga Maleeka a parlorn. Babu Maleeka babu alamarta saidai ga kayan karin kumallon da suka ci nan..

Cikin sauri ya suri wayar salulansa ya soma dialing layin Maleeka.

Ringing d’in wayar nata yaji a k’ofar parlorn, Ya tsaya cak yana sauraro.

D’ago kan da zai ya hangota ta shigo cikin parlorn muguwar murmushi saman fuskarta, Ta canza shiga wann karon cikin wasu sutura masu bayyana tsaraici.

“Wai har ka tashi a baccin..?” Ta tambaya tana fari da idanu had’ida bank’aro k’irji.

Shaye da tsananin mamaki kurum yake dubanta kafin yace “What really happened Maleeka..? Tell me mai ya faru..?” Yai tambayar cikin tsananin kad’uwa.

Murmusawa ta kumayi tana k’ok’arin matsowa kusansa. Ya dakatar da Ita ta hanyar d’aga hannu “Don’t dare.. Don’t you dare..!” Ya fad’i cikin d’acin rai.

Ta murmusa kafin tace “Idan kana son sanin komai.. Bani cell phone d’inka..!” Girgiza kai yai yace “Ke koda wasa don’t try me..”

Murmusawa tai kafin tace “Ashe ka mance da wa kake tare.. Ka mance profession d’aya garemu.. I won’t say a word.. I won’t explain anything to you.. Until you hand me over your phone..!” Ta k’arashe tana sakin huci.

Yana son yasan mai ya faru.. Baisan wani tuggu ta k’ulla masa ba.. Baida wani zab’i face ya mik’a mata wayar.

Ta saka hannu ta fuzge wayar nasa.. Aiko nan taga ya danna record Wato zai recording conversation d’insu ya sami evidence against her. Ta katse recording d’in tana sakin murmushi “Do you think I’m that fool Assad.. You might be my senior at the police academy.. Amma a wajen aiki you are my mate.. Nasan yanda abubuwan suke gudana..” Ta k’arashe muguwar murmushi saman fuskarta.

Zuciyarsa taci gaba da tsinkewa sanda Maleeka take nufosa.

“Kar kizo kusana najasa kawai..!” Ya fad’i yana sakin huci..

Dariya tai kafin tace “Na yaushe kuma Assad.. Ai mun riga da Munyi Abinda Zamuyi..”

Dakatar da ita yai da fad’in “K’arya kike makira fasik’a.. Nayi imani babu abinda nayi dake..!”

Dariya ta fashe dashi wann karon kafin Ta dubesa tace “If I were you.. I wouldn’t be so sure..”

Cikin tsananin huci Assad ke furta “Na fad’a k’arya kike munafuka..!”

Ta kuma darawa kafin tace “What if I have a concrete evidenc that clearly shows ni da kai munyi abinda zamuyi.. Kamar dai haka..!” Ta k’arashe tana nuna masa fuskar wayarta hotonsu su biyu kwance saman gado babu tufafi ya bayyana a fuskar wayar.

Zuciyar Assad yai wani irin yankewa.. Ya shiga gani duru duru.. Jiri na neman kaisa k’asa.

Hannunsa na rawa haka ma muryarsa yake nuna hoton yana fad’in “Menene wannan.. Menene wannan Maleeka..?!”

“This is our photo Darling..Making love..” Ta k’arashe tana mai kashe masa idanu guda.

Girgiza kai ya soma cikeda jinjina kaidi irin na mace “What..!” Ya furta yana dubanta. Lokaci guda yaci gaba da girgiza kai yana fad’in “That’s not me in the picture.. Bani bane photoshop ne..!”

Ta murmusa kafin tace “Unfortunately kai ne cikin hoton nan.. Kai bama hoto guda d’aya bane ka gansu.. Hotuna ne.. Harda videos..” Ta k’arashe tana sliding pictures d’in..

Tsananin kad’uwa had’ida tashin hankali suka had’u ma Assad.

Maleeka taci gaba da fad’in “Kai jami’i ne na bincike.. Kasan hoton da aka had’a ka kuma San hoto na gaskiya kaman dai wann.. Munada na’urar da zai nuna cewa da model d’in wayar nan tawa akai hotunan nan.. Hotunan nan na gaske ne.. Kai kafi kowa sanin haka.. Sannan fuskarka da jikinka sun fito sun bayyana b’oro b’oro.. Babu wanda bazai ganeka ba cikin hoton nan koda kuwa yau ne ya soma ganinka.!”

Gumi mai tsananin zafi yaci gaba da tsartsafo ma Assad.. Ya shiga girgiza kai yana nunata da yatsa “How could you.. How could you Maleeka.. Banyi niyyan komai ba face taimaka miki.. Maiyasa zaki mun haka.. Mai kike nema a wajena..?!”

Ta dara kad’an kafin tace “Now you are talking detective..” Gyara tsayuwarta tai kafin ta soma fad’in “I know you don’t want this videos and pictures to go viral on social media.. Na tabbata bazakaso sunanka ya b’aci ba.. Na tabbata bazaka so ka rasa aikinka da ahalinka ba.. Harma da d’iyarka wacce take hannun matarka da kaketa fafutukan k’watota daga hannun matar taka a kotu.. Assad idan Kotu sukaga pictures da videos d’in nan Alk’ali bazai baka rik’on d’iyarka ba kaman yanda kake so.. Wait Idan ban mance ba kace mahaifiyarta Wato tsohuwar matarka batada kamun kai batada tarbiya hasalima ka kamata da kwarto ne shiyasa kuka rabu.. Kana son amso d’iyarka daga hannunta sabida zata lalata maka d’iya shiyasa kake so Kotu ta karb’ar maka rik’on d’iyarka ya dawo hannun mahaifiyarka.. Toh ina mai tabbatar maka idan Kotu sukaga wann shaida kaida d’iyarka har abada.. Sannan ita kanta mahaifiyarka zata gujeka.. Kai k’arshe ni kaina zan k’ulla maka sharrin da bazaka iya fidda kanka ba.. Dama NPF kam ka saka ma ranka an koreka an gama bayan tuggun da zan k’ulla maka.. Kai bama kora kad’ai ba zaka k’are a kurkuku..!”

Duban Maleeka kurum yake yana mamakin Ta yaya mutum zai zama mugu irin haka.. Mai ya mata da tsanani da zata shirya masa irin wann gadar zare..

Girgiza kai ya soma yana fad’in “Maleeka why.. Mai na miki..?!” Yai maganar cikin rawar murya yana nuni da k’irjinsa.

Maleeka ta tsefe idanu tana dubansa “Baka mun komai ba Assad.. Laifinka d’aya shine zama aminin Mu’azzam da kai.. Dole ce ta saka ni na aikata maka haka..”

Ya girgiza kai hawaye na gangarowa daga idanunsa guda “Maleeka don’t do this please.. Na rok’eki.. Kar ki aikata mun haka.. Ki dubi girman Allah ki dubi girman sharrin da kike k’ok’arin k’ulla ma ran da bata San hawa ba batasan sauk’a ba.. Kar ki cutar da ran da baki da iko akanta..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya.

Maleeka ta murmusa kafin tace “Babu kalaman da zakayi amfani dasu wad’anda zasu sa na fasa k’udirina Assad.. Babu gudu babu jada baya.. Wanna shine kad’ai hanyar da zan wanke kaina daga zargin da abokinka yake mun.. Ka saka ma ranka kalan taka k’addaran kenan..!”

Ya girgiza kai yace “Ban fahimceki ba.. Mai hakan yake nufi.. Mai kike so nayi..?”

Ta murmusa kafin tace “Inspector Gamji your best friend, your only confidant.. Ya bani Assignment cewa na nemo masa wanda yake masa zagon k’asa a CID.. Nasan kanada masaniya akan binciken da yake gameda B.A.T. Ta yuwu ma tare kukeyi tinda yanzu aikin team d’inma kuna classifying nashi.. Dan haka Ina so ka amsa laifin cewa kai kake wa Mu’azzam zagon k’asa.. Ya bani sati biyu kafin ya dawo daga tafiyar da yai na kawo masa wanene B.A.T... A cewarsa B.A.T shine Spy d’in Danger a cikin CID.. Zaka amsa laifin cewa kai kake aiki da Danger sann duk tsawon lokacin nan kai ne kake masa zagon k’asa.. Wato dai zaka amsa cewa kai ne B.A.T..”

Lumshe idanunsa Assad yai hawaye masu zafi suka gangaro masa.

“Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..!” Abinda harshensa ya iya furtawa kenan.. Fatan bakinsa suka bud’e da k’yar..

Muryarta ya kuma sinkayo tana fad’in “Zab’i ya rage Naka Assad.. Kodai ka amsa laifin ka rufawa Kanka da mutuncinka asiri ka tsare mutuncin ahalinka, harma da d’iyarka da mahaifiyarka.. Ko kuma kak’i amsa laifin na yad’a wad’ann hotuna a kafafen sada zumunta mutuncinka ya zube.. Sannan ka rasa Farin cikinka Wato d’iyarka... Sannan ka shafawa zuri’arka harma da d’iyarka bak’in fenti wanda bazai tab’a gogewa ba a tarihin rayuwa..”

Daga haka Sa kai tai zata wuce.. Har Ta kai k’ofa ta dawo da baya ta aje masa wayarsa saman kujera, kafin Ta dubesa yanda yai zaune ya k’ura ma waje guda idanu, hab’arsa d’aure saman hannayensa biyu.

Maleeka tace “You have 2 good weeks to decide Detective.. Kodai ka zab’i kasancewa da Abokinka ka rasa mutuncinka da d’iyarka harma da ahalinka.. Ko kuma kai confessing wa Mu’azzam cewa kai ne ke masa zagon k’asa ka tsira da mutuncinka.. Zab’i ya rage naka..!” Tana ida fad’in haka tasa kai zata Shige.

Kukan kura Assad yai ya fuzgo wayarta yana k’ok’arin goge hotunan.

Dariya ta fashe dashi kafin tace “Kayi a banza.. Kana abu kaman kana mance cewa inada tunani irin naka.. Profession d’aya ke garemu.. Assad nayi saving d’insu a multiple files inada su a wajaje daban daban.. Zab’i ya rage Naka... Kar ka mance kana da lokaci kafin Mu’azzam ya dawo..!” Tana ida fad’in haka ta funciki wayarta kafin ta fice zuciyarta Wasai..

Tana ficewa ta kirawo wayan Chief tana sanar dashi yanda abu ya kasance.

Chief ya murmusa Cikeda k’asaita “Na fad’a miki.. Ni nasan bazaki bamu kunya ba. Yanzu bamuda sauran damuwa akan Inspector Gamji da Assad.. Shikenan mun tarwatsa abotansu.. Ina mai tabbatar miki yanzu Mu’azzam zai zamto baida tudun dafawa a CID tinda amininsa mafi kusanci dashi zai tafi gidan Kaso... Daga wann lokaci case d’in zai fice daga Zuciyar Mu’azzam idan har abokinsa mafi kusanci dashi zai zamto suspect na gaba.. Kinga cikin Sauk’i za’a k’arasa wanann jarabben case da ya tsaya mana a mak’oshi ya mana banga banga..” Ya kuma murmusawa yana fad’in “Good job Officer.. Kinsan aikinki.. Dole BAT ya baki kyauta na musamman bisa jajircewa da kikai..”

Ta murmusa kad’an kafin tace “Na gode da yabo Sir.. Amma Sir Ina son sanin wanene asalin BAT.. Shin menene had’insa da case din nan..?”

Murmusawa Chief yai kafin yace “Zai fi miki idan kika tsaya a nan ba tareda Kin kuma kutsawa ciki ba..”

Maleeka ta d’an girgiza kai kad’an kafin tace “Har yanzu baku gama yarda dani bane.. Chief ina son sanin Wanene BAT.. Ina son sanin ma wa nake aiki..?”

Chief ya murmusa kafin yace “Har yanzu dai zan k’ara shawartanki kar ki nemi sanin wanene Jemage domin kuwa bakinksa baya banbance abu mai kyau da najasa, komai ta baki yake. harta najasa ta baki yake fitarwa.. Jemage baida gaba sai baya..!” Ya k’arashe cikin tsoratarwa.

Maleeka ta d’anyi jim kafin tace “Chief kana nufin BAT wai Jemage kake nufi ba abbreviation na sunan wani bane..?”

Murmusawa Chief yai kafin yace “You love asking crucial questions Maleeka and you never give up akan bincike.. Ked’in material ce Babba.. Zakiyi amfani ma CID sosai da ace zaki zamto mutumiyar k’warai...” Daga haka katse kiran yai ya barta tana tinani.. Ta fuzar da fuci kad’an tana nanata kalmar Jemage.

**

FUFORE..


Su Inne dasu Aunty Shemau gaba d’aya suka fito tarbansu, duk wanda ke cikin gidan ma saida Inne ta sanyasa fitowa domin a tarbi kishiyarta amaryar Mu’azzam d’inta.

Ajidde ce kawai bata a wajen amma har su Mama Hindu duk sun fito.

Gaban Sadiya Sai fad’uwa yake sanda suka soma fitowa daga motar. Ita da Mu’azzam ne a baya sai ko Musaddiq da driver a gaba.

Tana fitowa ta hango Dattijuwar sai sakin murmushi take idanunta tarau akanta sauran mutanen na lale lale.

A hankali Sadiya ta sadda idanunta k’asa sanda taji hannun Mu’azzam saman nata. Tai k’ok’arin zame hannunta amma yak’i saki.. Ta d’an d’ago idanunta ta dubesa kaman mai shirin kuka alamun ya sakar mata hannu.. Bai sakar matan ba sai ma d’auke kansa da yai alamun ta daina b’atawa kanta lokaci dan bazai cire hannunta cikin nasa ba.
Babu yanda ta iya ta maida kanta k’asa.

Musaddiq ya tafi da sauri ya rungume Dattijuwan yana fad’in yayi kewarta wanda Sadiya keda tabbacin cewa itace Inne.

Inne ta d’an dunguri k’eyarsa tana fad’in “Toh maza kayar dani sai kaji dad’i.. Fitananne..”

Musaddiq ya d’an shafi kansa yace “Haba mana Inne tarban da zaki min kenan..”

Ta tsaresa da idanu tana karantar k’wayan idanunsa ko da ya tafi Abuja ya koma shan wasu abubuwan.. “Shige ka jirani zanzo na bincike ka..” Ta fad’i tana turasa kad’an.

Daidai lokacin Mu’azzam da Sadiya suka k’araso.. Mu’azzam ya bawa Inne light hug yana fad’in “Nayi kewarki Inne na..” Murmushi itama tai kafin ta d’an turasa tana fad’in “Ka dank’aro mun kishiyoyi dole kace haka.. Bani waje na fara gaisawa da kishiyan tawa kafin kai.” Ta k’arashe tana mai nufo Sadiya.

Sadiya tai saurin duk’awa da niyyan gaida Inne.. Saidai Inne bata bari ta isa k’asa ba ta kamota tana fad’in “A’a na yafeki.. Tashi abinki ni k’awarki ce ba kishiya ba..” Tai maganar tana mai rungumar Sadiyar.

Ita kaw Sadiya daketa sakin murmushi sanne kanta tai da mayafinta jikin Inne dan kunya..

A haka Inne na rik’eda Ita suka nufi cikin gidan.

Shemau ta rakasu da idanu kafin ta

Please Login or Register in order to submit comment