Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake yana duban Chief Inspector wanda yayi imani biyansa akayi ya kare mai laifi..

A hankali yake takowa gaban Chief kafin yace “Sir, I know my job.. I know exactly what I’m doing.. I only need a little more time to prove to you that..”

Katsesa Chief yai da fad’in “All the decisions are taking by me Inspector Gamji..! Now I’m ordering you to process his release immediately...!”
Cikin tsananin daka tsawa Yai maganar..

Mu’azzam dake ci gaba da sakin huci ji yake kaman ya shak’o wuyan che of inspector ya matsesa Sai ya fad’a masa uban wa yake karewa.. Assad ya kula da hakan, a hankali ya soma k’ok’arin janyo Mu’azzam yana fad’i cikin rad’a “Control yourself, don’t do anything foolish..”

K’ok’arin saita kansa Mu’azzam yai kafin ya jinjina kai yace “Yes, Sir.. Permission to leave, Sir.”

Chief ya jinjina kai yace “Good.. Dismiss now..”

Sara masa Mu’azzam d’in yai kafin yasa kai ya fice daga office d’in zuciyarsa na masa wani irin zafi...Shi kad’ai Sai wani irin tsuma yake.. Yana isowa ofishinsu buga benci yai yana sakin huci.. Maleeka ne da wasu abokan aikinsu guda biyu.. Suna ganinsa a haka duk suka mimmik’e.

Cikin tsananin huci yake furta “Out.. Everyone out..!” Babu shiri duk suka fice daga ofishin suna duban yananyin da yake ciki mai ban tsoro..

Assad ya turo k’ofar ya shigo kafin ya maida ya rufe yana mai fuzar da huci a hankali, lokaci guda yake furtawa cikin tsananin b’acin rai “What do you think you’re doing Mu’azzam.. What exactly is wrong with you.. You almost got yourself into trouble back there.. Ko kasan a gaban wa kake.. Chief ne fah Mu’azzam.. Ba case d’in nan kawai ba, harta aikinka zaka iya rasuwa Mu’azzam.. C’mon get a grip.!” Cikin b’acin rai Assad Ke maganar

“Shut up..! Just shut up Assad..!” Yai maganar yana mai d’ago kansa dake kife kafin ya k’araso gaban Assad d’in su duka biyun suna sakin huci...

Mu’azzam yaci gaba da fad’in “To hell with everything.. I don’t give a damn about his so called position.. I’ve always known mutumin nan is a corrupt police officer.. Nasan akwai wanda yake karewa.. Sanin kanka ne Assad sabida mutumin nan da gurb’atcciyar zuciyarsa wanda cin hanci da rashawa suka masa katutu munsha losing cases da Dama.. Criminals sun sha tsallake laifukansu. Da irin wannan mutumin a police force baza’a tab’a cin galaba ba.. Sune ‘yansandan da suke b’ata mana suna kuma suke walak’anta aikinmu takai matakin da Uniform d’in mu baida wani daraja a idon mutane.. But I promise you.. Ka rubuta wannan ka ajiye Assad, idan b’era na Yawo mage tana Yawo wata rana zasu had’e.. Sai na kawo k’arshen cin hancinsa da rashawarsa.. Kuma sai na kamo wannan mutumin da yake karewa..”

Daga haka bai kuma cewa komai ba ya bud’e k’ofar yai ficewarsa, yanda yake tafiyar kad’ai zai tabbatar maka ransa yakai k’ololuwa wajen b’aci..

Daga bakin cell d’in Danger ya tsaya suna aika ma juna kallo.. Danger sai sakin murmushi yake yana shafa hab’arsa.. Lokaci guda yake furta “Mr Inspector.. It looks like nida Kai bazamu d’auki dogon lokaci a nan muna sha coffee ba..”
Ya d’anyi fasali yana mai girgiza kai had’ida tab’e baki kad’an kafin yace “Too bad you don’t smoke da mun had’e a mashaya.. So get off my neck already..!”

Baikai aya ba Mu’azzam dake tsananin huci ya zira hannunsa guda ta cikin k’arfen cell d’in ya fincikosa yana fad’in “This is not yet over.. I’ll make sure you rot in jail, you criminal..”

Cikin sauri Assad ya shiga janyesa, sai sakin huci yake.. Lokaci guda sergeant guda ya k’araso ya bud’e cell d’in Danger.. Aka fito dashi aka nufi bakin kanta dashi yanda Su agogonsa da wasu kayansa suke.. Sai sakin murmushi yake yana kashe ma Mu’azzam idanu..

Mu’azzam bai iya zama cikin wajen ba sai ficewa da yai cikin sassarfa.. Kafin Assad ya cimmasa har yayi key wa motarsa..

Yana isa gida baibi takan kowa ba ya nufi part d’insu shida Musaddiq dake cikin gidan..
Safeenah dake zaune balcony d’in d’akinta tana ganin shigowar motarsa ta mik’e.. Dama dawowarsa take jira, taci gayunta cikin navy blue Dubai material mai d’aukan idanu.. d’inkin fitted gown akai mata da ya mugun mata kyau ya zauna jikinta sosai.. Dikda bata faye fad’in kwankwaso ba amma ya mata kyau dan ko babu komai Safeenah tanada kyaun fuska da hasken fata.. D’aki ta komo ta isa gaba dressing mirror tana kuma k’yalk’yale fuskarta da kwalliya.. Ta sakar ma kanta murmushi ganin yanda tai kyau kafin Ta nufi b’angaren Mu’azzam...

Shi kaw yana fad’awa d’aki bathroom ya shige ya sakar ma kansa shower.. D’umin ruwan na ratsasa yana tuno abubuwan da suka faru dashi a ranan.. Na farko buge juna da sukai shida wannan ‘yar tashan yarinyar da jifa masa ultra da tai a fuskarsa... Sai kuma Chief Inspector da yasa aka saki Danger.. Lokaci guda ya bud’e idanunsa ya saka hannayensa biyu ya maida sumarsa da ruwa ya jik’a zuwa bayan kansa.. Fuzar da fuci yai yana mai kuma lumshe idanunsa.. Bai Sa a ransa zai losing hope ba.. Binciken mutuwar Ikram yanzu ya fara koda hakan na nufin zai rasa komai nasa ne including his job as a police officer...

Safeenah da tin shigowarta d’akin Ta fahimci wanka yake dan tana iya jin zuban ruwa daga cikin bathroom d’in hakan yasa Ta zauna saman gado tana mai mik’e k’afafunta alamun tana jiran fitowarsa.. A nan saman gadon ta hangi suit d’insa da ya cire..

Murmushi ta d’anyi kafin ta mik’e tana furta “Maza Feenah tashi Ki fara gudanar da duty d’inki as a wife..” Tai maganar tana sakin murmushi kafin ta isa ta d’ago suit d’in nasa..
Jin kaman da abu gefen rigar ya sanyata kuma shafawa tana jin kaman soso.. Nan dai ta zira hannunta ta ciro abun..

Cak Ta tsaya tana juya ledar cikin hannunta.. Daidai lokacin Mu’azzam ya fito daga bathroom d’aure da towel saman kunkuminsa, hannunsa rik’e da k’arami yana tsane sumarsa..

Kallo d’aya yai mata yaci gaba da abinda yake, tana tsaye tana kallonsa ba tareda ta janye idanunta ba.. Zai iya cewa zama a turai yasa Safeenah take wasu abubuwan kaman dai k’arancin kunya, amma yasha mamaki da har Ta gansa a haka bai Ko d’ad’areta ba saima ci gaba da dubansa da take.. Ganin ko tarewa basuyi ba..
Ya d’an kuma satan kallonta still bai daina abinda yake ba, sai sannan yaga abinda ke rik’e hannunta...

Baice da Ita komai ba saima k’ok’arin nufan closet da yake..

Cikin sauri ta take masa baya har lokacin tana rik’e da pad d’in...

“Mu’azzam what is this doing in your pocket..?”

Ya d’an dubeta kad’an ba tareda yace komai ba yaci gaba da abinda yake...

Zata kuma magana ya soma takowa gabanta, ganin yanda ya had’e rai yana nufota ya sanya gabanta wani irin fad’uwa ta shiga matsawa baya baya cikeda tsoro... Saida ta isa jikin gini kafin ta daina matsawa har lokacin pad d’in na rik’e hannunta..

Rank’wafo da kansa da yai kaman zai sumbaceta yasa Safeenah saurin rintse idanunta tana jin sanyin ruwan dake jikinsa had’ida hucin numfashinsa..

Saitin kunnenta yake fad’i tamkar mai rad’a “I hate it when someone messes with my stuff..” Daga haka zare ultra d’in yai cikin hannunta ba tareda ya kuma cewa komai ba..

“But I’m not someone.. I’m your wife.. And dan na tambayi ina ka samo ai banyi laifi ba..”

“Safeenah Zo ki fice min a d’aki..” Ya fad’i yana nuna mata k’ofa.

Idanunta suka kawo ruwa, zuciyarta ta shiga mata zogi, meke shirin faruwa da aurenta tin baaje ko Ina ba.. Auren data d’au alwashin protecting d’insa no matter the costs..

“But you know this is not fair..” Ta fad’i cikin rawar murya irinta mai kuka..

“Get out please...” Ya kuma fad’i yana nuna mata hanya..

Jinjina kai tai kafin ta tako gabansa tana goge siraran hawayen dake gangarowa saman fuskarta “Wannan shine dalilin da yasa kak’i mu tare har yanzu.. Do you have another woman in your life..?”

Da tsananin mamaki yake dubanta, shine Safeenah take kallo tana fad’a masa magana haka, mai ta d’aukesa mai Ta maidashi.. Idan baiyi k’ok’arin rik’e kansa ba yanda ransa yake b’acen nan zai iya mata komai l..

K’ofa ya kuma nuna mata “Leave now..!”

Zata k’ara bud’e baki kenan taji ya fizgota da k’arfin gaske ya nufi k’ofa da Ita.. Har waje ya fitar da Ita kafin ya maida k’ofan ya rufe..

Safeenah taji wani irin kuka na zuwa mata, durk’usawa tai wajen tana cazgan kuka.. Allah ya gani bazata iya sharing mijinta da wata shegiya a waje ba... Da wannan tinanin ta tashi ta nufi side d’insu..

A k’ofar parlor Ta had’u da Meema zata fito waje..

Meema ta dubi Safeenah da har lokacin da ragowar hawaye a fuskarta..

“Addah Feenah lafiya.. Ya na ganki haka.. Keda kika koremu d’azu kikace kwalliya kike wa Ya Mu’azzam mu fice mu baki waje.. Ya kuma naga Fuskar Ki haka..?”

Harara ta raka Meema dashi “Mind your own business..” Ta fad’i tana mai shigew..

Meema ta tab’e baki kad’an kafin tabi bayanta tana fad’in “Aaaa badai Meeman ba, I don’t mind my own business.. Duk abinda babu ruwana a gidan nan shi nake shiga.. I love to meddle with other people’s lives..” Tana ida fad’in haka ta nufi bayan Safeenah..

Kafin Safeenah Ta rufe k’ofa Meema ta shige..

“Addah Feenah Wai meke faruwa ne.. Sai fah kin fad’a mun.. You know bazan k’yaleki ba har sai naji komai..”

Feenah ta isa saman gado ta zauna tana jin hawaye na kuma zuwa mata, cikin muryar kuka take furta “I thought babu ruwansa da mata.. I thought baida lokacinsu.. But then I was wrong..” Kuka ya hanata ci gaba da magana..

Meema ta tab’e baki kad’an tace “Dama ke Addah Safeenah wani namiji ne mai lafiya zaice babu ruwansa da mace.. Wllhi k’arya ce kawai.. Ai haka aka haliccesu da son mata.. Ke yanzu jinki Ya Mu’azzam zaik’i amincewa da tariyarki ne idan baida me d’ebe masa kewa.. Ahap.. Allah yasa ma ba a Gidanki yake cin amanarki ba dai..”

Cikin kuka Safeenah ta katse Meema da fad’in “Enough Meema.. Ya isheki haka.. I know my husband is not like that..”

Tab’e baki Meema tai kafin tace “Aw really..? Shisa naga kinzo nan kina kuka ai.. Addah Safeenah you need to face reality.. Your Husband is a cheater.. Abinda ya kamaceki shine ki tashi tsaye, and fight for what’s rightfully yours kafin kiyi latti.. That’s if you really love him..!” Ta k’arashe tana ware idanunta fuskar Safeenar..

Shiru Safeenah tai kaman mai nazari sai kuma tace “What do i do now Meema..?”

Meema Ta tab’e baki kad’an tace “Baki sanar dani abinda ya faru ba ta yaya zan samo miki solution..”

Safeenah ta karanto mata tiryan tiryan abinda ta gani wajen Mu’azzam da yanda suka kwashe..

“Tabb amma wllhi Adda Feenah gayen nan ya raina miki hankali.. D’an anjima ma ce miki zai is a piece of evidence na wani binciken da yake.. Wllhi mata yake bi idan ba haka ba babu abinda zai had’asa da ultra.. Kinsan me..?”

Safeenah Ta girgiza kai alamun a’a..

Meema ta jinjina kai tace “Kin bincika wacece budurwar tasa ni kuma na miki alk’awarin shirya miki wulak’ancin da zaki mata wanda ko kallon yanda mijinki yake bazata k’ara ba koda kuwa Colleague d’insa ce a wajen aiki..”

Safeenah tai saurin d’agowa tana duban Meema, lokaci guda ta shiga jinjina kai tana fad’in “Itace.. Junior colleague d’insu ce a police Academy bani mancewa dik tare sukayi da best friend d’insa Assad.. And yanzu kuma tare suke aiki a CID.. Ta jima tana son Mu’azzam..”

Meema ta dara kad’an tace “Ahap wllhi itace take neman rabaki da mijinki..”

Safeenah tace “Toh amma ai shi baya sonta, kuma ita d’in ba ajin Mu’azzam bace..”

Gajeren tsuka Meema tai tace “Wllhi idan kikayi magana Sai naga kaman Bakida experience na rayuwa.. Shi namiji ina ruwansa indai zai samu abinda yake nema.. Wllhi Ko kaffara bazanyi ba itace tinda kullum suna tare wajen aiki..”

Safeenah ta jinjina kai tana huci “Wllhi sai na mata mugun wulak’anci.. Sai nasa ta soma jin kunyar kanta a ofishin nasu.. Sai naci mutuncinta a bainar jama’a..!” Ta k’arashe tana sakin huci..

Meema ta murmusa tace “Good. Now you’re talking like my real sister.. Ni ko a sch ban tab’a losing battle ba.”

Safeenah tace “Mai zan mata Meema ta fita daga rayuwar mijina..?”

Meema ta matso kad’an tace “Kawo kunnenki kiji..



SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*





*08*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*







Umma tana kallo Abba ya ida shirya yaransa Ashiru da Habib, tambayan duniya ta masa ya sanar da ita yanda zai kaisu yak’i kulata, ko kallon arziki ma bata ishesa ba balle ya amsata.. Har saida suka gama shiryawasu tsaf kafin yace suje waje su jirasa. Yaran sukai kaman yanda mahaifinsu yace..

Abba yai gyaran murya yana duban Umma “Uwani.”

Ta d’ago a raunane tana dubansa. Lokaci guda yaci gaba da furta “Bazan bar yarana suna ganin tashin hankalin da kuka janyo ma kanku Keda d’iyarki ba, a shekarun Ashiru da Habibu sunyi k’anana su dinga ganin ana sintiri cikin gidan nan ana Fad’a da mahaifiyarsu ana fad’in sai ta biya kud’ad’en data amsa, sannan bazan bar yarana sunaji ana cewa ‘yansanda na sallama da mahaifiyarsu ba.. Tsuntsun da yaja ruwa dama shi ruwa yake duka.. Kuma abinda ka shuka ko shakka babu shi zaka girba. Ashiru da Habib sun gama yini a gidan nan, idan Kinga mun dawo toh dare ne Yayi amma sam bazan barsu su yini a layin nan ana cewa ga abinda mahaifiyarsu da ‘yaruwarsu sukai ba.. Kunje can Keda d’iyarki ku warware abinda kuka sak’a..”

Umma cikin rawar murya take furta “Haba Abban Sadiya yanzu ficewa zakayi ka k’yalemu.. Idan ‘yansandan sukace zasu tafi damu fah..? Dan Allah ka tsaya ka zamo mana rumfa ka zamo mana Katanga.”

Da tsananin mamaki yake dubanta kafin ya murmusa yace “Wanda Allah ya zama gatansa shikeda cikakken Gata Uwani.. Amma yau naji dad’i da kika yarda duk talaucin miji da rashinsa akan iyalansa shi Katanga ne kuma rumfa ne..? Ashe yau kin amince ki tabbatar da hakan Uwani.. Na gode ma Allah da ya nuna mun wannan rana da kika furta hakan da bakinki kafin na bar duniya.. Ko kin mance abubuwan da kike fad’a mun a baya, cewa ni ban isa ba a gidan nan.. Idan inaso na zamto isasshe a gidana na maku abinda ranku ke so. Toh Alhamdulillah ban maku abinda ran naku ke so ba amma ku kunyi da kanku dan haka a wannan fanninma na kasa Uwani, saidai ku kuyi da kanku.. Ubangiji ya fiddaku..” Yana ida fad’in haka yasa kai zai fice..

Sadiya dake mak’ale bayan k’ofa tana sauraren tattaunawan iyayen nata wane irin kuka ne taji na taso mata, tai saurin fitowa daga mab’oyarta ta nufi Mahaifinta.. Durk’usawa tai ta kamo k’afarsa tana kuka tana fad’in “Abba dan Allah ka yafe mun.. Abba nayi imani hakkinka da rainikon da muka maka nida Umma shike bibiyanmu.. Dan Allah ka yafe mana Abba, kar kayi fushi damu ka yafe mana.. Wllhi na tuba Abba bazan sake ba..”
Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana mai rungume k’afar mahaifin nata...

K’uri yai mata kaman zai magana, sai kuma ya duk’a ya zame hannayenta daga rik’on da tai masa, lokaci guda yasa kai ya fice daga gidan..

Sady ta d’aura hannu aka tana kuka da duka zuciyarta tana fad’in ta shiga uku..

Ficewan Abba da kaman wasu mintoci wani yaro ya shigo ya sanar dasu ‘yansanda suna sallama a waje..

Sady ta kuma fashewa da sabon kuka tana fad’in “Shikenan Umma k’ila kud’ad’en da Sagir yayita bamu na shan jini ne.. K’ila ma kud’in kan mutane yayita bamu bamu sani ba Umma.. Na shiga uku ni Sadiya ina zan saka kaina..”

Umma ta girgiza kai tace “Aikin gama ya riga ya gama Sadiya, shige muje mu sami ‘yansandan dan ko bamu fita ba zasu shigo su samemu..”

A b’angaren Sadiya Ita bama fitan bane, ganin wannan D’ansandan ne bata sonyi wanda kallonsa kad’ai ba komai yake haifar mata ba face tsananin fad’uwan gaba.. Addu’a take Allah yasa kar tayi tozali dashi..

Aiko tayi sa’a domin kuwa yau d’in babu wancan D’ansanda Sai d’aya abokin aikin nasa da sukazo tare jiya saiko wata mace wacce itama tayi shiga cikin bak’ak’en kaya..

Shi wannan Officer d’in kam nada kirki ba kaman abokin aikinsa da sukazo jiya ba, haka Sadiya tace cikin zuciyarta dan ko yanzu ma a natse yake masu tambayoyi shida abokiyar aikin tasa..

Tambayar k’arshe ne da yayi masu yasa Sadiya da Umma duban juna..
Assad yana hankalce dasu, d’an gyaran murya yai kafin yace “Zaki iya gane mutumin da ya turo a matsayin Uncle d’in nasa..?”

Umma Ta girgiza kai tace “Gaskiya nikam bazan ganesa ba, dan sau d’aya na gansa kuma da Mahaifin ita Sadiyar sukai magana..”

Maleeka ta d’an matso kad’an tace “Bazaki iya suffanta mana yanda kamanninsa yake ba..? Kiyi dogon tinani da nazari..”

Girgiza kai Umma ta kumayi alamun a’a.. Sadiya dake gefe ta bud’e baki tace “Officer idan kuka sami wannan mutumin zaku k’yalemu..?”

Assad ya dubeta kad’an yace “Kinga mutumin ne..?”

Jinjina masa kai tai kad’an tana furta “ Eh na gansa kuma zan iya ganesa.. A tsakar gidan nan sukai magana da Abba ni kuma ina lab’e kitchen ina hangensu.. Zan iya gane kamanninsa...”

Jinjina kai Assad yai yana mai zira hannayensa cikin aljihu “Da kyau, yanzu zaki bimu can ofishinmu dake headquarters, akwai masu ilimin zana kamanni cikin bayanan da aka masu wanda su aikinsu kenan.. Zamuje ofishinmu tareda ke zaki masu bayanin kamannin wannan mutumin su kuma zasuyi sketching d’insa..”

Sadiya jin ance zaa tafi da ita police station ya sanyata zaro idanu waje tana duban mahaifiyarta “Umma Wai tafiya dani zasuyi..?”

Maleeka da kanta ke kife tana rubutu cikin wata ‘yar k’amar littafi mai yanayi da jotter d’agowa tai Ta dubi Sadiya tace “Kar ki d’aga hankalinki ba tsareki za’ayi a can ba, wasu tambayoyi kawai zaki amsa mana sai kiyi bayanin wannan mutumin..”

Assad ya murmusa kad’an ganin yanda tsoro ya cika Sadiyar yace “Ki daina tsoronmu.. Police are your friends kinji koh.. Had’in kanki kawai muke buk’ata domin mu cire gurb’atattu cikin al’umma..”

A hankali Sadiya Ta jinjina kai har lokacin tsoro bai bar saman fuskarta ba..

Umma Ta matso da sauri tace “Rankaidad’e dan Allah zan iya raka d’iyata.. Dan Allah ku taimakeni ku barni na tafi tareda d’iyata..”

Shiru Assad yai yana dubanta kafin ya jinina Kai a hankali yana mai nuna masu yanda motar take pake..

Gaba d’aya suka d’unguma suka tafi police headquarters..

Zuciyar Sadiya sai tsinkewa take, ta d’aga idanu tana duban dogon ginin.. Oh yau kuma Ita Sadiya ce a ofishin ‘yansanda, abinda takeji take kuma ganina finafinai sai gashi yau yana faruwa da ita.. Tabbas a rayuwa kar kayi ma k’addaran wani dariya domin bakasan da mai gobe zata Zo maka ba.. Tana ganin yanda mutane ke shige da fice. Assad na gaba yana masu jagora yayinda Maleeka ke take masu baya.. Sady dai sai rabe raben idanu take tana kallon kanta a wajen da bata tab’a tsammanin zatazo ba..

Suna tafe ta hangosa yana tsaye k’ofan wani Office kansa kife yana duba wani file.. D’ago kan da zai suka had’a idanu.. Take taga annurin fuskarsa ya kuma d’aukewa, Ta lura mutumin kaman haushinta yakeji, Ta kula baik’i ya sami wani dalilin da zaisa ya jefata kurkuku ba.. Take ta shiga b’oyewa bayan Maleeka tana k’ok’arin b’oye fuskarta tana lek’ensa.. Tana ganin Assad ya isa garesa yana nuna masa wani k’aramin d’aki mai kaman office.. A tare suka shige Assad d’in nayima Maleeka alama da hannu kan su k’araso..

Office ne madaidaici mai d’aukeda table guda biyu, d’aya table d’in wani mutum ne zaune da computer gabansa wanda take tinanin shima d’ansandan ne.. Sai d’aya table d’in kuma wani mutum ne zaune da takardu gabansa da k’aramar cup wanda pens ne da dangin abin rubutu ciki.
Umma bata shigo office d’inba saiko Sadiyar. Addu’a take Allah Sa kar wannan mutumin ya shigo.. Aiko bata ida addu’an ba Ta gansa ya shigo yana amsa waya.. Assad yai mata nuni da wani kujera yace ta zauna.. Babu musu ta k’arasa ta zauna.
Mutumin dake gaban computer shike tattara bayanan da Sadiya keyi cikin computer d’in yayinda d’aya Mutumin dake zaune gaban table d ya shiga shirya takardunsa alamun yana jira ta suffanta masu kamannin Kawun Sagir..

Assad yai mata umarni data fara bayani..

Yanda take masu bayanin a tsorace yasa mutumin bai fahimci komai ba, tana kuma d’agowa idan ta dubi Mu’azzam sai ta kuma daburcewa ta rasa bayanin da take..

Assad ya lura da hakan, ya d’ago yana duban Mu’azzam ya kuma dubi Sadiya dake satan kallonsa.
D’an sosa kunnensa kad’an Assad yai kafin ya dubeta yace “Are you alright..?”

Girgiza masa kai tai alamun a’a..

“What’s the matter then.?” Ya tambaya yana dubanta.
Satan kallon Mu’azzam da ta kumayi yasa Assad murmusawa kad’an kafin ya k’arasa yanda Mu’azzam yake ya d’an janyo Mu’azzam d’in da har lokacin waya yake yana tsaye jikin window.. Cikin dabara Assad ya fiddashi daga cikin office kafin suka samu full attention d’in Sadiya..
Ai kuwa suna fidda Mu’azzam daga office d’in suka samu full attention d’in Sadiya, tai masu bayanin kamannin Kawun Sagir tiryan tiryan..

Mai zana hoto ya zano kamannin data fad’i.. A daidai lokacin Mu’azzam da ya ida wayan da yake ya turo k’ofa ya shigo.. Bai wata wata ba ya isa table d’in yana duba zanen wanda ba fuskan kowa bane ya bayyana face Danger..

Wani irin huci kurum Mu’azzam yake yana dunk’ule hannunsa, lokaci guda ya bugi table d’in yana furta “I knew it.!” Lokaci guda ya fuzgi takardan ya fice daga office d’in cikin tsananin b’acin rai sai sakin huci yake kaman zai kifa k’asa...
Cikin sauri Assad yabi bayansa dan yasan komai ka iya

tsakanin Mu’azzam da Chief Inspector.


Hankali tashe Assad ke k’ok’arin taresa ko kula Assad baiba har saida ya daki k’ofan Office d’in Chief..
Chief na cikin waya yana kwance cikin kujerarsa mai juyawa sai ganin Mu’azzam yai akansa yana sakin huci kaman wani mayuwancin zaki..

Babu shiri Chief ya katse wayar da yake yana duban Mu’azzam da tsananin mamaki
“How dare you barge into my office.. Who do you think you are..!” Cikin tsananin b’acin rai Chief yake maganar yana duban Mu’azzam dake tsaye gabansa idanunsa babu alamun tsoro..

Lokaci guda Mu’azzam ya d’ago Sketch d’in yana nunama Chief “Do you still have any reason to depend this criminal..?!”

Ko ba’a fad’a maka ba tsoro ya bayyana a fuskar Chief Inspector amma Sai ya dake yace “Kai k’aramin maras kunya. Kasan da wanda kake magana.. Naga irinka dubu kuma na gama dasu..”

Baikai aya ba Mu’azzam ya katsesa da fad’in “Bakaga irina ba kuma kafin kaga irina sai na tabbatar na gama dakai..”

Wannan karon murmushi Chief yai yace “Mind your language boy.. Bakada hujjan cewa na kare mai laifi domin kuwa dani da kai bamu San wanene Danger bamusan he’s connected to crime d’in nan ba sai yanzu...” Ya murmusa kad’an kafin yace “Har yanzu kaid’in yaro ne a gidan nan.. Har yanzu bakasan yanda Al’amara ke gudana a gida irin wannan ba.. You’re lucky, you’re from well known and respective family, I should’ve thrown you out cikin k’ask’anci . Now, get out of my office befor you lose everything .. Including your career as a police officer..!” Ya k’arashe muguwar murmushin saman fuskarsa..

Daidai lokacin Assad ya shigo a rud’e yana neman afuwan Chief on behalf of friend’s behavior..

Mu’azzam kaw har lokacin huci kurum yake yana duban Chief Inspector da idanunsa da tuni sun gama rinewa..

Chief ya dubi Assad d’in yace “Take him out.. Fitar dashi daga nan..!”

“Don’t touch me.. Don’t you dare touch me..!” Mu’azzam yai kashedi ma Assad kafin ya dubi Chief yace “Wata rana zamu had’u..! Alk’awari ne..!” Daga haka juyawa yai ya fice zuciyarsa na masa tsananin k’una..

Assad zai magana Mu’azzam ya d’aga masa hannu alamun dakatarwa “Not now Assad.!”

Fuzar da fuci kurum Assad yai kafin yabi bayan Mu’azzam d’in...

Su duka hud’in suna tsartsaye sunyi carko carko.. Suna kuma duban hoton Danger da ya bayyana cikin sketch d’in..

Assad ya nusa yace “What do we do now.. Danger must be in a hide tinda yasan dole za’a nemesa... Bazai tab’a zama nan kusa ba.. Allah Sa ma bai gudu ya bar gari ba..”

Yusuf yace “Ba Lallai Danger yasan ana nemansa ba, so ba lallai ace tsakanin jiya zuwa yau ya gudu ba..”

Muryar Mu’azzam suka sinkayo yana fad’in “We will track him down before yayi making move.. I know by now informer d’insa ya sanar dashi muna nemansa..!”

Gaba

Please Login or Register in order to submit comment