Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita hanyar samun kud’inta.. Tuni Umma ta hure ma Sadiya kunne cewa ta dinga karb’o masu kud’i hannun samaruka, hakan yasa Sadiya bata raina samari hardai zata samu ta tatsesa ta rariki rabonta.. Kowa a unguwar yayi shaida ma Sady pretty da Ummarta indai akan tara samari barkatai ne da amsan abin hannunsu.. Babu yanda Malam Ibrahim mahaifin Sadiya da suke kirada Abba baiyi ba wajen ganin ya karkatar da Uwani da kuma mummunan d’abi’ar data d’aura d’iyarsu amma abu yaci tura.. Tsaf Uwani take tsefe masa ruwan bala’i tace bazata zauna tanaji tana gani d’iyarta ta k’are a auren matsiyaci ba kaman yanda ita ta k’are.. A haka har Sadiya ta sami gurbin karatu a Jami’ar babban birnin Tarayya.. Idanun Sadiya sun kuma bud’ewa yanda Ta soma gogayya da manyan ‘yanmata masu ji da kansu da kuma yaran masu hannu da shuni.. Tuni Sadiya Ta kumaji Lallai batada miji sai mai Kud’i ko d’an mai kud’i musamman ganin yanda daga shigarta samaruka sukai mata chaa sabida kyaun halitta da Allah yayi mata.. Idan tayi wanka ta shiga makaranta sai ka rantse d’iyar wani hamshak’i ne, daga nan duk wasu situru da abubuwan more rayuwa da take amfani dasu maza Ke bata su.. Daidai da registration da kud’in samari tayi.. Hoto kuwa idan zatayi posting a social media saidai ta tafi can layin bayansu gidan su wata k’awarta Sabeera a nan take hoto dashike mahaifin Sabeera yanada d’an rufin asiri dan babban d’an canji ne cikin Abuja amma gidansa na nan Suleja.. Gida mai d’an karan kyau ya cancad’a.. Kullum Sady pretty tana gidansu Sabeera dan dama tare suka sami gurbin karatu a nan Jami’ar Abuja, course d’aya suke tare suke tafiya tare suke dawowa, a motar gidansu Sabeera ake kaisu a d’auko su wasu sunyi zaton ma ‘yan gida d’aya ne wasu kuma sukanyi zaton Sady ce d’iyar mai Kud’i Sabeera ce ‘yar k’wak’warta.. Bugu da k’ari Sabeera irin ‘yanmatan nan ne da abun hannun iyayensu bai rufe masu ido ba, Sam abun duniya bai d’ad’areta ba kaman k’awarta Sady pretty.. Sady sam bata bari k’awaye suzo gidansu saidai Su had’e a gidansu Sabeera.. A haka Sabeera Ta zamto Aminiyar Sady, sau tari Sabeera takanyi nasiha ma Sady kan irin rayuwar data d’aukar ma kanta amma ko a jikinta takan ce lokacinta gwara taci duniyarta da tsinke.. Bazata bari kyaun da Allah yayi mata ya zamto a wofi ba tinda basu da kud’i zata iya amfani da kyaun da Allah ya bata ta sama masu rayuwa mai inganci itada iyayenta..

Duk wasu kayan more rayuwa da Sady zata kawo gidan Abba baya amfani dasu bai kuma fasa masu nasiha ba musamman ga Uwani mahaifiyar Sadiya.. Ita kam Sadiya ya mata nasihar ya mata fad’an har duka yasha mata amma babu abinda ya canza dan Tuni mahaifiyarta ta hure mata kunne.. K’arshe Umma ce masa tai idan dai bazai bar mata d’iya ta sakata ta wala ba toh wllhi zata kwashe yaran ta tafi taredasu kuma bazai sake ganinsu ba Eritrea zasu koma da shike dama Mahaifiyar Sady ‘yar asalin k’asar Eritrea ce, haka nan take kyakkyawa kaman mutanen k’asar Eritrea masu kusanci da Ethiopia dan a wajenta Sady ta samo tsantsan kyaun halitta da Allah yayi mata, saidai Ita Sady har ta d’ara mahaifiyar tata.

Sosai Malam Ibrahim ya samu matsala da Umma akan Barin Sadiya da tai sakaka tana Yawo dan har Dattijan unguwa sun gaji sun soma masa magana, yayi dik yanda zaiyi ya hana hakan abu yaci tura..K’arshe dai shine yace saidai Sady ta fiddo da miji a mata aure kafin ta k’arasa shekararta ta farko a jami’a.. Ana haka ta had’u da wani saurayi mai suna Sagir a Yanargizo.. Nan da nan Sagir ya samu gurbi mai girma a zuciyar Sady dan sosai yake mata b’arin kud’i kuma yace da aure yake nemanta.. Sady ta gama sakankacewa ta yarda ta amince Sagir masoyinta ne Tuni tace masa ya turo ayi maganar aurensu dan Dama Abbanta ya saka mata takunkumi.. Nan Sagir yake sanar da ita cewa iyayensa US suke basa zama a Nigeria.. Shima abinda ya kawosa zuwa yayi dan ya nemi mata ‘yar k’asar Nigeria ya aura ya d’auketa su koma can US suci gaba da zama.. Haba nan fah Sady da Umma suka kuma susucewa akan Sagir.. Ya turo masu wani mutumi guda d’aya a matsayin Uncle d’insa akai maganar aure.. Sagir yace kar suji komai shi zaiyi komai na aure, nan suka kuma jin dad’i.. Nan da nan zance ya d’auka Sady zata auri d’an gidan k’usa bama cikin Abuja suke zama ba cen k’asar Amurka suke da zama shida iyayensa neman macen aure ya dawo dashi gida Nigeria, iyayensa zasu Zo da zaran ya samu mata an soma shagulgulan biki..

Hakan yasa Uwani cin alwashin yin Bikin kece raini ga Sadiyarta, Ta shiga ciwo bashi dan tayi Bikin kece raini, Bikin yaran masu hannu da shuni Bikin nunuwa a shafukan sada zumunta na yanar gizo..
Ana biki kwatsam aka nemi ango aka rasa har rana mai kaman Ta yau basu san abinda ya faru da ango ba.. Ga wayar salulansa ta dena shiga.. Tun Sady na damuwa har dai Umma tace ta daina damuwa k’ila America ya koma dan ya taho da iyayensa tinda an soma shagulgulan biki.. Sabeera ma cewa tayi k’ila US d’in ya tafi kuma ba lallai wayarsa Ta shiga ba.. Hankalin Sady sosai ya tashi, taci kuka tana fad’in Maiyasa bazai kirata ba da zaran ya saka layinsa na k’asar Amurka, Sabeera tace k’ila surprise yake son mata.. Abu kaman wasa babu Sagir babu dalilinsa har zuwa ranan d’aurin aure da aka rasa ango aka rasa mai karb’awa ango aure.. Toh daga nan ne fah Umma da Sadiya suka fara shakku da yinin wane irin mutumi suka jajib’o...

Umma Ta nusa tana duban Abba da har ya ida alwalansa yana d’auraye slippers d’insa da sauran ruwan butar har lokacin karan goge bakinsa na cikin bakinsa..

“Abban Sadiya yanzu bazakace komai ba.. Kana jin yanda ake shigo gidan nan sahu sahu ana d’aga min hankali sai na fidda kud’ad’en dana ciwo bashi..”

Sai sann ya d’ago ya dubeta “Toh ki biyasu kud’insu mana sai su daina miki sintiri a gida..” Ya fad’i yana k’ok’arin mik’ewa.

Ta k’walalo idanu waje “Ina zan iya kashin tulin kud’ad’en nan Abban Sadiya..?”

“Aw dama Kinsan Bakida hanyar samu Kika ciwosu.. Kan wane dalili.? Dan ki birge mutane..? Ai sai ki jira mak’aryacin da ya yaudareku d’in yazo ya biya miki bashin dan nikam Kinsan Ko kud’in haya na shekara da nake biya idan an had’a bazasu isa ba..”

Umma ta dafe fuskarta da hannu tana salallami tana furta “Oh ni Uwani na shiga uku, Sadiya kin d’ebo mana ruwan dafa kanmu..”

Tana jiyo muryar mijinta na kiran Ashiru da Habib suzo su shige masallaci...

Umma ta nufi d’aki yanda Sadiya Ke kwance tana aikin abu guda..

“Ki tashi ki daina wannan koke koken mu soma tunanin yanda zamu samo mafita.” Umma Ta fad’i tana mai zama gefen katifar da Sadiya Ke duk’unk’une tana zuban hawaye, sautin kukan ma ya daina fita.. Idanunta sunyi luhu luhu haka nan ma fuskarta tayi jajazir, tsinin hancinta shima yayi ja har kaman ya k’ara tsawo.. Kallo guda zakai ma Sadiya ka fahimci cewa tana cikin tsananin tashin hankali wanda tinda tazo duniya bata tab’a shiga irinsa ba.

“Umma.. Sagir..” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka, sai kuma ta kasa ci gaba da magana sakamakon kukan da ya dad’a taso mata

Nan ta kifa kanta tana mai isarta yayinda Umman tai tagumi Ta zuba mata Ta mujiya..

**


Suna tafe saman kwalta Assad naci gaba da jefo masa tambayoyi wanda akasari ba samun amsarsu yake ba shidai kawai damuwarsa su isa wannan location d’in da Danger ya basa..

Wayar Mu’azzam d’in Ta soma ringing.. Yai saurin ciro wayar a aljihu yana duban mai kiran nasa, a d’an kasalce ya k’arawa a kunnensa dan yasan mai kiran nasa matsala zai kunno masa.. Shiru yai ga dukkan alamu yana sauraren d’aya b’angaren ne..

A hankali ya lumshe idanunsa yace “Tell me your location..?” Alright alright I’ll be on my way.. Don’t call a cab just wait for me there..” D’if ya kashe wayar yana mai fuzar da fuci..

“Pull the car over Assad.”

Assad da kacaukam hankalinsa kega kwalta d’an kaikaitowa yai yana dubansa “Wait what..?”

“Stop the car, zan sauk’a a nan.. I need to go back..”

“You mean to the station..?” Assad ya kuma tambaya yana k’ok’arin parking motar gefen kwalta..

Yana k’ok’arin ficewa daga motar yake fad’in “No..MUSADDIQ ne... Daga yanda yake mun magana nasan ba cikin hayyacinsa yake ba..”

“Musaddiq kuma..? Na kwana biyu banji kana tare tare da gagaransa ba.. What really happened..?”

D’an tab’e baki Mu’azzam yai kafin yace “How would I know.. Abunda na sani kawai shine ya kasa karb’an k’addarar cewa Ikram ta tafi kuma bazata tab’a dawowa ba.. I’m afraid rashin Ikram ka iya jefa Musaddiq halinda ya riga ya bari a baya..” Ya k’arashe damuwa saman fuskarsa..

Cikeda tausayawa Assad yake duban abokin nasa, yasan d’awainiya ne da dama zasu kuma hawa kan Mu’azzam d’in...

Daidai lokacinda cab ya tsaya.. Mu’azzam ya shige yana fad’in “Kaje kayi sauri ka isa location d’in zamuyi waya..”

Baki sake Assad Ke dubansa yana kuma juya ‘yar k’aramar Doguwar takardan mai d’aukeda address d’inmu.. D’an girgiza kai kurum yai kafin ya shige ya d’auki hanya...

**

-Star lake street, Maitama_


Tsaye tayi saman kan matar dake kwance saman gado wacce idanunta Ke bud’e tarau saidai gefen jikinta guda tamkar a shanye yake, bakinta dake karkace miyau na fitowa.. A tak’aice dai kallo guda zakai mata ka fahimci matar tana cikin tsananin jinya ne...

A hankali matar dake tsaye kanta ta duk’a tana mai ci gaba da k’are mata kallo, lokaci guda ta saki murmushi tana mai ciro tissue paper dake ake gefe cikin kwali ta shiga goge mata miyau d’in dake fitowa daga cikin bakinta. Lokaci guda take furta “Na shafe tsawon shekaru ina jinyar kishiya.. Shin zan samu riba nan gaba..? Shin hak’ata zata cimma ruwa.. They say everything in life has a price, Nuratu.. Could this be my punishment..?” Tai fasali tana mai duban matar wacce ta kirata da Nuratu kafin ta saki murmushi tace “No wait.. How could this be my punishment bayan ni ban aikata komai ba.. Kece kika aikata mun komai Nuratu.. Kece kika d’auke komai daga gareni.. A baya ked’in matar d’an uwan mijina wacce na miki lak’abi da kishiyar Dinga sannan Hausawa sunce ita d’in tafi zafi.. Kin kasance wacce tafi soyuwa cikin dangi musamman wajen Inne Mahaifiyar mazajenmu..” Ta k’arashe maganar tana mai disposing used tissue paper d’in kafin ta d’auko wani tana mai kuma goge wanda yake gangarowa, lokaci guda take ci gaba da furta “Nayi zaton idan mijinki ya mutu zaki fita daga rayuwarmu.. Zaki koma yanda kika fito.. But then I was wrong.. Ashe mutuwar mijinki ba komai zai k’ara mana ba face kusanci da juna..” Kukanta ya k’aru sanda taci gaba da fad’in “Kin aure mun miji Nuratu.. Kin aure mun miji bayan naki mijin ya mutu.. Kin zamto shalele mafi soyuwa a wajen mijina.. How could you.. Ta yaya zaki aikata mun haka..? Ta yaya Nuratu..” Tasa hannu tana goge hawayen da ya wanke mata fuska kafin taci gaba da fad’in “This is what you deserve.. Keda mijina bazaku tab’a kasancewa ba balle har Kuji dad’in yin rayuwar aure tare.. Bazan tab’a bari hakan ta kasance ba Nuratu.. Ked’in bazaki tab’a warkewa daga wannan ciwo ba.. Kar ki mance da furucina... Dama na gaya miki gidan mijina tamkar GIDAN ARO yake a wajenki... Babu Ke babu sukuni balle samun natsuwa a cikin gidan mijina.. Na fad’a miki aron gidan na baki na d’an wani lokaci.. Zaki fita daga gidan domin kuwa akwai babban shiri da nake miki.. Zaki fice daga wannan gidan kaman yanda na miki alk’awarin cewa shid’in GIDAN ARO ne a wajenki..” Tana kaiwa nan ta kece da wata irin dariya hawaye na fito mata.. Saida har dariyar nata ya koma tamkar kuka kafin ta kifa kanta gefen majinyaciyar tana kuma sakin kuka mai ban tausayi.

K’amshin turaren mijinsu da yaima k’ofofin hancinta sallama ya tabbatar mata cewa shid’in ne ya shigo.. Nan fah ta dad’a narkewa tana sakin kuka mai ban tausayi..




SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:34 AM] My mom: *GIDAN ARO*



*03*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Ya d’auki mintoci yana tsaye kansu kafin ya duk’a a hankali ya zauna gefen majinyaciyar, yai amfani da hannunsa guda ya dafa matar dake duk’e tana sharb’an kuka “Hajara kukan nan ya isa haka, shi majinyaci ba kuka yake buk’ata daga wajenmu ba.. Abinda yafi buk’ata shine addu’o’inmu.. Kiyi hak’uri ki daina kukan nan kinji..”

Ta d’ago fuskarta da tuni hawaye ya wanke ta janyo tissue paper tana share majinan da yazo hancinta alamun taci kuka.
“Daddy gaba d’aya hankalina ya gaza kwanciya, ace ko yaushe ahalin nan cikin tashin hankali muke.. Babu k’asar da ba’a fita da Nuratu ba amma jikinta yak’i dad’i kullum ciwon nata ma kaman k’ara gaba yake.. An gama Bikin SAFEENAH da MU’AZZAM Ko tarewa basuyi ba wani tashin hankalin ya kunno aka tsinci gawan Ikram..” Ta kuma saka hannu tana share hawayen dake mak’ale cikin idanunta, a hankali takai hannunta ta dafa saman na majinyaciyar, cikin rawar murya take furta “Poor Nuratu, bata San da labarin mutuwar d’iyarta ba.. I’m sure duk randa ta farka daga wannan jinyar nata ta tadda wannan mummunan labarin zata shiga tashin hankali ne maras misaltuwa.. Na kasa daina tunani, mai Ikram tayima wannan mutumin ya kasheta , sannan Maiyasa shima ya kashe kansa.. Da ace shi D’an Garkuwa da mutane ne da ya nemi Ransom.. Ikram yarinyar kirki ce mai tsananin kamun Kai balle ace biye biyen maza take.. Ko shakka babu mutumin nan saceta yayi...Bazan tab’a mance rawar data taka a rayuwar D’amu Musaddiq ba.. Ikram Ta zamto tamkar wata fitila data haska rayuwar Musaddiq, bani mance lokacin da ya dawo daga k’asar England bai dawo da takardan komai ba.. Baiyi karatun ba Sai yawo da abokan banza.. Bani mancewa har kusan koranshi kayi a gidan nan.. Amma Ikram da Mu’azzam basu cire rai akanshi ba.. Mu’azzam ya shawo kanka ka yafewa Musaddiq, sannan Ita kuma Ikram ta taimakawa Musaddiq wajen ganin rayuwarsa ta inganta.... And now that she’s gone.. I don’t know what’s going to happen to our son..” Ta k’arashe cikin tsananin kuka..

Alhaji Marwan Gamji ma hawayen da ya kasa rik’ewa ne ya sauk’o masa yana k’ok’arin dannewa..Ya rungume matarsa yana fad’in “Ya isa Hajara.. Allah yana nan da sannu zai daidaita mana al’amran ahalinmu kinji Ko.. Everything will go back to how it was before kinji koh..”

Ta kuma fashewa da kuka tana fad’in “Ta yaya Al’amara zasu koma kaman yanda suke da bayan babu Ikram a halin yanzu, Ikram ta tafi yanda bazata sake dawowa ba. Al’amara bazasu kuma kasancewa kaman da ba.. Ikram Fitila ce a cikin gidan nan, kowa tasan yanda zata zauna dashi.. Na shak’u da yarinyar nan fiyeda yanda na shak’u da Karimatu da Meema, kusan kullum tare muke yini nida ita wajen jinyar mahaifiyarta.. I saw how dedicated she was to her ailing mother.. Yarinyar kirki wacce ko wace uwa zatayi fatan samun irinta.. Bata tab’a banbanceni da mahaifiyarta ba.. Ikram rashinta zai bar gib’i Babba a gidan nan...” Ta k’arashe cikin tsananin kuka..

Hannu yasa yana mutsuke gajeren hawayen da ya mak’ale masa, lokaci guda yake furta “Wanda duk yayi ma Ikram wannan abun shine aiki yake gabansa domin kuwa itakam Ta sami shaida.. Sannan ita duniya dama takenta kenan GIDAN ARO, dik yanda ka kaiga sonta Ko k’inta wataran dole ka barta.. Yi k’ok’ari ka tanadi guziri mai kyau a GIDAN ARO domin ka inganta gidanka na lahira wacce itace tabbatacciyar GIDA...”

Mommy ta d’an dubesa kafin tace “Wai kaima baka yarda wannan mutumin da aka tsinci gawarsu tare shi ya kasheta ba.?”

D’an jan numfashi kad’an Daddy yayi yace “To be honest, I don’t know what to believe... Maiyasa mutumin nan zai kashe Ikram sannan ya kashe kansa..?”

Mommy tace “Maybe baiso a kamasa dan yasan dole a kamasa shiyasa da yayi garkuwa da Ita ya kasheta sannan ya kashe kansa..”

Daddy yai shiru kaman mai nazari sai kuma ya d’an girgiza kai yace “Still it doesn’t make any sense.. Maiyasa zai kashe kansa dan tsoron kar ya tafi gidan Yari..?”

Mommy tai shiru tana nazari itama..

Fasali ya d’anyi kafin yaci gaba da fad’in “Inada tabbacin Muazzam bazai huta ba har Sai ya zak’ulo su Wanene Keda alhakin mutuwar Ikram.. Sannan Ina fata kafin zuwa wannan lokaci Nuratu ta sami lafiya domin taga yanda za’a hukunta ko su wanene suka aikata ma d’iyarta haka..”

Wani irin bugawa k’irjin Hajiya Hajara yai lokaci guda.. Ta d’ago tana duban mijin nata Wanda da gani har cikin zuciyarsa yayi maganar.. A hankali ta shiga jinjina kai tana furta “Wannan gaskiya ne.. Ko su wanene suka aikata ma Ikram haka sun cancanci a gurfanar dasu gaban shari’a..”

Ta d’an nusa kad’an kafin tace “Yau ‘yan Fufore Sun koma gidan Sai ya dad’a mana girma da shiru..”

Jin baice komai ba ya sanyata kuma gyara zama tace “Jiya muke magana da Shema’u akan ciwon Nuratu, take ce min har yanzu Aunty Nurah dai shiru jiki yak’i dad’i nace mata wllhi anyi magani k’asashe da dama amma Allah bai nufa an dace ba.. Toh shine take ce min an gwada na gida.? Nace mata Ai baka faye yarda da maganin gidan nan ba.. Tace min akwai wata mata datayi shigen irin ciwonta, maganin wata bafulatana aka gwada dake wata Ruga cen gaba da Fufore.. Shine take ce min Ko za’a gwada nace mata gaskiya saidai idan na maka magana naji abinda zakace.. Magani kuma dace ne ba’a San yanda maganinta yake ba..” Ta k’arashe tana mai tsaresa da idanu cikeda kulawa..

Knocking d’in da akai a k’ofar d’akin ne ya katse masu tattaunawar tasu, Mommy Ta d’an janye jiki daga cikin nasa, tai k’ok’arin saita kanta kafin ta bada izinin shigowa..

Wata budurwar yarinya ce da bazata gaza shekaru 16 ba ta turo k’ofar ta shigo..

Yanayin da suka ganta ciki ya sanyasu zuba mata idanu suna jiran suji yau kuma menene ya faru a gidan

“Kiki lafiya..?” Mahaifiyar tata ta tambaya

Alhaji Marwan Gamji kaw cewa yai “Come here baby.. Zo ki fad’a min mai ya faru..”

Cikin sanyi ta K’araso ga iyayen nata.. Ta dubi wannan ta dubi wannan..

Duban mahaifiyar tata tai tace “Mommy it’s Addah FEENAH.. Tace ita gidanta da Ya Mu’azzam zata tafi tinda ‘yan karb’an gaisuwar Ikram sun watse, ‘Yan Fufore sun koma itama zata tafi nata gidan..”

Ta juyo tana duban mahaifin nata “Daddy you need to stop her, nida Meema mun ce mata Bride bata Kai kanta gidan Groom shine tace zataje ta sami Inne ta kaita tinda ita bata koma Fufore ba..”

Mik’ewa yayi yana fad’in “Ina Safeenan take..?”

“She’s in her room, probably parking her stuff..” Kiki ta fad’i tana matsawa kusan mahaifiyarta dan bama mahaifin nata hanya..
Cikin sauri yasa kai ya fice..

Kiki ta dawo da dubantaga mahafiyarta tana yatsina fuska tana duban Aunty Nurah dake kwance..

“Wai Ke Mommy bazaki daina damuwa akan matar nan bane.. Matar nan fah kishiyarki ce amma ko asalin danginta iyakacin abinda zasu mata kenan.. Ni ban tab’a ganin kishiya irinki ba Mommy wacce take ma kishiyarta jinya. Ko a sch idan ina labarin Mommy ta ita take ma step mom d’ita jinya mamaki suke sha sai suce Lallai Ke ta daban ce..” Tai fasali tana mai zama gefen mahaifiyar tata kafin taci gaba da fad’in “And Mommy tun tasowarmu a haka muke ganin matar nan, ciwonta bai gaba bai baya Ke kuma sai faman wahala kike da ita dik tulun maids d’in dake gidan nan basu isa jinyar nata ba sai kin saka hannu..”

Murmusawa Hajia Hajara tai tana duban d’iyar tata “Kareema kenan, yaro dai yaro ne.. Bazaki fahimci komai ba yanzu sai nan gaba.. Mamarki kirki ne da ita bazata iya ganin wasu suna shan wahala ta k’yalesu cikin wahala ba.. Nuratu da kike gani ba kishiyata bace kawai, tamkar ‘yaruwa haka na d’auketa domin kuwa idan baki mance ba a baya Yayan Babanki mai rasuwa take aure.. Kinga nida Ita mun jima da sanin juna tun kafin Daddynki ya aureta..”

Kiki Ta d’an turo baki tace “Amma Mommy Maiyasa da nata mijin ya mutu ta aure miki naki mijin..? Mommy nan gidanki ne bai kamata ta aure miki miji ba..”

Murmusawa Mommy ta kumayi kafin tace “Nurah batada kowa a k’asar nan, batada dangi a nan.. Mijinta ne kad’ai danginta sai kuma yaranta, shiyasa koda mijinta ya mutu nawa mijin ya aureta..”

Shiru Kiki tai tana sauraren mahaifiyar nata kafin ta tab’e baki tace “Even so Mommy, she shouldn’t have married your own husband.. Ita ta aure miki miji ga kuma d’anta Ya Mu’azzam ya aure Addah Safeenah.. Um nidai duk bana son irin wannan had’e had’en kusancin tai yawa... Shikenan namu family d’in sun k’are a cycle d’aya..Ni gwara ma da Addah Ikram Ta mutu nasan itama da yanzu an soma maganan nata auren da Ya Musaddiq.”

“Ke Karimatu..!” Mahaifiyar tata ta daka mata tsawa wanda ya sanyata zabura babu shiri..

Mommy taci gaba da fad’in “Kina jina.. Koda wasa koda wasan wasa kar na kuskura na kuma jin wannan kalma ya fito daga bakinki balle har kiyi gangancin furtata cikin gidan nan kinji koh..!” Ta k’arashe tana mai nunata da ‘yar yatsa cikin tsananin b’acin rai..

Kiki baki a ture ta mik’e tana fad’in “Fine Mommy, kema kinfi son wannan matar da yaranta sama damu yaranki.. Kaman yanda Daddy yake nuna yafi sonsu.. This is not something new a gidan nan.. Dama Daddy ya saba nuna yafi sonsu tun kafin Ikram ta mutu..”

“Kimin shiru da maganar Ikram nace and kindly leave this room kafin na b’ata miki rai..”

Fuu ta fice fuska a kumbure kaman zata kurma ihu..

Tana ficewa Mommy ta dafe k’irjinta tana Sauk’e ajiyan zuciya.. Ta maidoda dubanta ga Nuratu da fuskarta ke duban wani b’angaren.. A hankali ta sauk’e ajiyan zuciya kafin tasa kai ta fice...

Tana fitowa d’akin Safeenah ta nufa yanda ta tadda Safeenar duk’e saman carpet tana fuskantar Daddy dake zaune bakin gadonta, kanta a k’asa da alama hawaye take..

“Daddy I’m sorry.. Kawai inaso na kasance da mijina ne.. Please understand me..” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya..

Cikin kwantar da hankali yaci gaba da fad’in “Na fahimceki Safeenah.. But don’t you think yayi sauri ayiwa Mu’azzam maganar tariya yanzu..I mean, he recently lost his sister.. And he’s looking into the matter right now...Kuma Kema ‘yaruwarki ce..”

Cikin muryar kuka Safeenah Ke fad’in “Daddy gani nake kaman Mu’azzam kufce min zaiyi.. Daddy kaga da k’yar ya yarda akayi aurenmu sabida jinyar Aunty Nurah toh mai kuma zai faru yanzu da Ikram ta rasu.. K’ila yace ya fasa auren ma gaba d’aya Daddy..” Ta k’arashe wani kukan na taso mata..

Cikeda tausayin d’iyar tasa yake dubanta dan yasan yanda take tsananin k’aunar Mu’azzam..

Hannunsa ya mik’o ya kamo nata kafin ya soma magana cikin kwantar da hankali “Safeenah an riga anyi aurenku da Mu’azzam kinji.. Shid’in mijinki ne, babu abinda zai rabaku ki kwantar da hankalinki kinji koh..”

Izuwa lokacin sosai take kuka tana fad’in “Daddy you don’t understand.. Daddy Mu’azzam ba kaman kowa bane. Bata soyayya yake ba balle aure, baida lokacinsu Daddy I’m sure of it, yafi bada mahimmanci ga jinyar mahaifiyarsa da kuma aikinsa na d’ansanda.. Ba don Inne ta dage sai anyi aurenmu ba nasan k’ila da ba’ayi ba.. And yanzu da ya sami dalilin da zaice ya fasa.. I know him zai iya cewa ya fasa auren.. Daddy please kar ka bari aurenmu da Mu’azzam ya sami matsala..” Yanda take maganar gaba d’aya tamkar mai son fad’in wani abu duk ta daburce tama rasa mai take fad’i.. Shi kansa Daddyn da mamaki ya soma dubanta..

Cikin sauri Hajiya Hajara ta k’arasa ta rungume Safeenah dake sharb’an kuka tana sunbatu..

Shigowar Meema a birkice tana fad’in “Mommy..! Mommy kizo ga cen Ya Mu’azzam ya dawo da Ya Musaddiq.. And... he looks high..”

Wani irin zafi Alhaji Marwan yaji zuciyarsa na masa, take ya shiga karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Yai saurin ficewa daga d’akin cikin tsananin damuwa...

Mommy Ta dubi Meema dake tsaye daga bakin k’ofa tana duban yanda Safeenah ke cazgan kuka ta bud’e murya tace

Please Login or Register in order to submit comment