Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi yasa ya dafa guiwowin ta cikin rawan murya yace,
"Bazan iyaba Ummul bazan iyaba ina son cikina bazan zubda gudan jinina da kaina ba bazan yi kisan kaiba".
sai ya kuma mik'e yana yarfa hannunshi,
ganin haka ta mik'e itama tana yarfa hannun ta tana kuka tana binshi a baya tare da cewa,
"toh ni dai ka maidani gida,
na gaji da zaman gidan nan ka maidani gun Nenne na".
jin hakan yasa yayi ajiyan zuciya dan yasan indai ya maidata gida bata isa tace a zubda cikin ba dan tana jin tsoron su Adam hakan yasa cikin kauda kai yace,
"shirya mu tafi".
Hannu ta yarfa cikin dire k'afafunta tace,
"ni a shirye nake mu tafi kawai".
"toh".
yace sannan ya shige d'akin shi,
wonka yayi ranshi cike da takaici,
yana fitowa ya sameta a bakin gadon shi,
bai kulata ba ya zauna gaban dressing mirror mai ya fara shafawa yana murza fatar jikin shi,
a d'aya gefen kuma Ummul ce ta mik'e cikin tura baki tazo bayan shi hannun shi ta rik'e cikin jin bacci da kasala ta manna kanta a bayan shi a hankali tace,
"Hamma mu tafi bacci nake ji".
juyowa yayi ya jawota jikin shi cikin sanyi ya ruggumeta tsam a jikin shi yana shak'ar k'amshin ta,
hannun shi ya cusa cikin rigarta yana shafa cikinta zuwa kan kirjinta murya can k'asa cikin daburcewa yace,
"Ummul kiyi hak'uri kiso d'anki kiso gudan jinina ki barni in rab'i jikin ki ina begenki ki bani hak'k'ina".
shiru tayi ta lafe a jikinshi tana jin yadda yake murje kirjinta da shafa cikin ta,
ido ta lumshe cikin sanyi da kasalar daya k'ara sakar mata ta ruggume k'ugunshi ta manna kanta da fatan cikin shi,
a hankali tace,
"Hamma Umar tashi mu tafi,
banda lafiya zan koma gun Nenne na ni a cire cikin".
ranshi a b'ace ya d'an tureta sannan ya shirya tsab fuskarsa a tsuke suka fito,
rufe gidan yayi sannan suka shiga mota,
Kai tsaye hanyar potaskum ya nufa da ita.

A gida kuwa Aliyu ne dasu Nanne ke zaune a parlour ,
Aliyu dake zaune a 1 str hannun rik'e da wayar ya Sadik yana game a wayar,
itako Nanne tana kishingid'e a kan doguwar kujera suna hira da Ya Sadiq dake zaune rik'e da remote yana kallon TV suna d'an hira kad'an -kad'an,
Suna isa harabar gidan Hamma Umar na tsayawa Ummul ta bude motar cikin kasala da jin bacci ta shige cikin gidan,
kai tsaye tai parlour Nanne Sallamar ta ce tasa Nanne tashi zaune tana murmushi ta bud'a mata hannu, Ummul cikin shagwab'a ta fad'a jikin Nanne tace,
"Nanne na ina kwana?". lafiya lau Ummul na,
ya Damaturun ?". Sallamar Hamma Umar ce ta katse su,
cikin sakin fuska Nanne ta amsa mai tana mai sannu da zuwa,
Cikin nitsuwa da cikar kamala ya shigo parlour kanshi a sunkuye zama yayi a k'asa gaban Nanne yace,
"Nanne ina kwana ? ya gidan?".
murmushi tayi cikin jin dad'in ganin su ta amsa da,
"lafiya lau Farouk ya hanya, ya aiki?".
Kai yasake sunkuyar wa k'asa yace "Alhamdullah".
sannan Ya Sadiq da Aliyu daya matso jikin Hamman na shi cikin so da kauna suka gaida shi ya amsa musu cikin sakin fuska tare da cewa,
"Ina Adam fa?".
Sadiq ne ya dan kalleshi tare da cewa,
"Yanzu ya tafi d'akin shi, barin kira shi".
Kai ya jinjiga yace,
"kyale shi zamu wuni ai".
Ummul dake kwance kan cinyar Nanne kuwa tuni tafara bacci cikin kasalar da take tare da ita,
sukuwa hira suka ci gaba dayi.
Can jimawa kad'an Hamma Umar ya mik'e tare da cewa,
" Nanne bari inje mu gaisa da Hajjajo".
Cikin zumud'i Aliyu yace,
"Ko kaje ma yanzu tana sallar walaha, kasanta kamar tubabbiya, nima koroni tai".
Dariya suka d'anyi duk kansu ban da Nanne da ta ran kwashi kan Aliyu tace,
"tadai fika da surutun ka mara amfani ai ita hanyar tsira ta kama kaifa maiyin game ".
Jin hakan yasa Hamma Umar d'in ya sake zamewa ya zauna k'asa tare da tok'oshe k'afafun shi sannan yayi k'asa da kai,
a hankali ya furta,
"Abba basu dawo ba? Munyi waya jiya yace suna maiduguri".
Nanne dake shafa bayan Ummul ne tace, "Bai dawo ba, muna dai sa ran sai gobe insha Allah".
Addu ar dawowa lafiya yayi masa,
sannan suka amsa da, "Amin".
Itako Ummul ta bud'e lumseshshun idonun ta da kyar tai mik'a a hankali ta kuma lafewa jikin Nennen tata
ture ta Nannen tayi tare da cewa,
"to d'aga min cinya in duba mai sunan ki ko ta idar sai kuje ku gaisa".
Tana mikewa Ya Sadiq ya bi bayan ta yana cewa Aliyu,
"Tashi muje mu k'arasa gugar Hajjajo".
Fitarsu ne ya bawa Ummul damar tasowa ta matso gaban Hamma Umar d'in cikin kasala da mayen bacci ta durkusa ta had'a hannu wanta biyu guri guda tace,
"Hamma narok'e ka dan Allah kayi hakuri ka rabani da cikin nan wallahi banaso cikin nan bana son haihuwa da kai".
Idon shi ya rumtse da karfi tare da furza numfashi mai nauyi jiki a mace ya sa hannun sa ya lank'ayo kugunta ta fad'o jikin shi ya sa hannun shi ya Kara matsota sosai har numfashin su na had'ewa ya d'ago idanun shi ya tsura mata su cika sanyi ya sauke numfashi tare da lumshe ido ya kamo lips inshi yana tsotsa murya can k'asa yace,
" Ummul khairina kiyi hakuri kibar mana d'anmu ya rayu a cikin ki kibarshi yaji d'umin cikin mahaifiyar shi".
sake narkewa tai a jikin shi tasa hannu ta tallafo fuskar shi tace,
"Haba Hamma dan Allah kaji tausayina mana nifa kasani bana sonka,
ka zubda cikin nan dan Allah".
Kanshi ya cusa cikin kirjinta yana goga fuskarsa akan dukiyar fulanin ta yana wani irin numfashi mai d'auke da tsan tsar k'una da rad'ad'i ga kuma sha'awar dake cin jinkishi da zuciyarshi murya na rawa yace,
"Naji amman indai kina son a zubda cikin nan to ki fad'ama Adam da Abba idan sun amince shike nan sai a zubar ".
Cikin tarin takaici Adam dake kokarin shigowa parlour yayi sallama tare da shigosa yana jin wani irin bak'in ciki da takaici ji yake kamar ya abka kan Ummul din har sai ya sumar da ita tunda ita bata gane nasiha tafi gane bugu,
Itako Ummul tana jin muryar Adam d'in take yuk'ura tabar jikin Hamma Umar wanda ke zaune jiki a kasalance ,
Itako Ummul ganin yanda jikin Adam yai sanyi ga gumi na tsatstsafowa daga duka jikin shi yasa suka tabbatar da yaji zancen da sukeyi dan haka Ummul ta rink'a jan baya-baya Vikings tsoro tana kallon idanun shi yadda yake watsa mata harara gaba d'aya jikinta sai kerma yakeyi da sauri tajuya tayi cikin tsoro ta shige bedroom d'in Nanne ta turo kofa ta rufe ta haye gado tana tunanin yadda zasuyi da ya Adam,
Shi kuwa Hamma Umar mik'ewa yayi cikin kasala da rauni yaje gaban Adam d'in hannu yasa ya dafa kafad'ar Adam yace,
"kar inji wannan a bakin kowa".
Cikin mamaki Adam ya zuba mishi ido tare da gyed'a kai dan abin ya d'aure masa kai,
Shiko Hamma "good". Kawai yace ya fice yabar shi baki bud'e yana mamakin yanda Hamman nasu yazama,
kai tsaye b'angaren Hajjajo yayi, yasame su dukkan su, cikin ladabi ya gaida Hajjajo, ita ko tana tsokanar shi yana murmushi yace,
"Nanne bari inje gun Ammi".
Itama fuska a sake ta amsa da,
"ka gaidata, kace zan biyo muje gaisuwar".
"toh". yace sannan ya fice ya tafi haka ya fita ya kama hanyar gidan su Ammin shi,
Adam kuwa yana ganin Hamman nasu ya fita,
yazo ya tsaya kofar dakin Nanne yana ta fada da alwashin koyama Ummul hankali yana,
"wallahi ki bud'e k'ofarnan in kuwa kikak'i zan balla k'ofar na kuma shigo na tattakaki tunda baki da mutunci".
tana jinshi sai rawan jiki take da tsoro tana k'ara b'uya a cikin blanket tana,
Dan Allah kayi hak'uri ya Adam".
a harzuk'e ya koma kan kujera ya zauna.

a gidan su Ammi Kuwa yana isa yai paking a k'ark'ashin bishiyar kofar gidan ya fito yashige cikin gidan,
da Inna yafara had'uwa tafito daga kichin tana ganin shi tayi murmushi cikin jin dad'i da k'aunar jikan nata tace,
"kaga Ummaru faruq, mai tagwayen suna, kaga d'an Ammin shi da Nanne yayan shehu Usmanu, angon Rabi'atul Adawiyya likita bokan turai".
Duk kirarin da Inna keyi ya na tsaye ya na kallon ta yana shafa sajenshi ganin ba zatayi shuru bane ya katseta da cewa,
"To ya isa haka zo muje inbaki tukuici dan kinyi aikin maroka".
hannun ta ya kama suka shiga cikin parlour inda Ammi ke zaune tana ninke y'an kayayyakin data data woke,
sai murmushi takeyi tana jin dad'i da shauk'i da k'aunar d'an nata dariya ta d'anyi dan jiyo kirarin da Inna kewa d'an nata,
suna shiga yasamu ya zauna a gaban ta ya cire hular shi kamar ko yaushe in yana gaban Ammin nashi , ya kwantar da murya yace, "Ammi na ina kwana?". hannunta takai ta shafa kanshi tace,
"lafiya lau, ya aikin, ina Ummul dina?".
K'ara matsawa jikin ta yayi yace,
"lafiya lau Ammi na tare muka zo da ita bacci tai kafin in fito shiyasa bamuzo tare ba".
sai kuma yasa hannu ya karb'i zanin hannun ta yaci gaba da ninkewa,
Ido Ammin ta zubawa d'an nata tanajin kaunar shi na ratsata tace ,
"Umar inajin dad'in yanda kake tafi da rayuwar auren ka da k'anwarka amanar ka". Ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe ido yana jin dad'in yadda Ammin nashi ke Al'fahari dashi da kuma yadda take gamsuwa da rik'on amanar daya d'auka, murya can k'asa yace "koyarwarki ce Ammi ina alfahari dake ko yaushe".
Tattare kaya yayi yaje ya jere kowanne a mazauninshi sannan ya fito yad'akko abin yankan farce ya dawo ya russuna gaban Ammin sa, itako hannu ta mik'a mai yafara aikin shi na yankemata farce Kamar yadda ya saba dai-dai sanda ya gama yankan ffarcen Ammin nashi akayi kiran sallah dan haka yai alwala yawuce masallaci dan gabatar da sallah azhar,
bayan an idar da sallan ne ya koma cikin gida gaban Ammin nashi ya zauna tare da zaro woyarshi yace,
"Ammi bari in kira autanki ayi hira dashi".
"toh".
tace tare da yin murmushi.

A b'angaren Ummul kuwa tun tana zaune har ta kwanta bacci b'arawo ya saceta shiko ya Adam da ya Sadiq daya shigo bayan fitan Hamma suna nan zaune a palour Nanne suna jiran fitowarta, baccin da tayi ne yasa bataji tafiyar su masallaci ba bare taking dawowarsu , Anan sukaci abinci cewarsu ko shekara zatai a d'akin suma zasu shekara a gurin.



Ya Usman Kuwa mutan india, yana zaune a k'asan capet ya kifa kan shi a kujera hannu shi dafe da kirjinshi yana wani irin kuka mai cin rai da k'ona zuciya kamar yadda kukan ya zame mai sabo duk da ga tarin magungunan da ko ya shasu baya jin sauk'in zogin da zuciyarsa keyi kullum son Ummul da k'aunarta K'aruwa suke a zuciyarshi,
kukan yakeyi kamar yadda ya saba har numfashin sa na fizga, Kid'an da wayar shi keyi ne yasa ya dago rinannanun idanun shi yakai hannu ya janyota daga kan table d'in dake tsakiyar palour, har kiran ya yanke yanata kallon ta yana k'ok'arin saita kan shi gudun kada yad'au kiran yayi abinda B'iyayen nashi zai gane yana cikin damuwa,
Shiko Hamma Umar dake zaune gaban Ammi yace,
"barin in sake kira". Bugu d'aya Usman ya amsa da,
"Amincin Allah da rahamar sa gareka d'an uwana jinina".
ba Hamma Umar ba hatta Ammi da tasawa wayar ido saida ta lumshe ido dan jin dad'in kalmar autan nata, aiko ita ta amsamai da,
"Amincin Allah ya tabbata gareku y'a y'an albarka".
wannan kalmarce ta tabba tarwa Usman da Hamman shi na tare da Ammin su, sai da ya k'ara dai daita kanshi sannan yace, "Ammina, Hammana, da y'ar tsohuwa Inna ina wunin ku?".
Kafin su amsa kuwa ya sake katse su da cewa,
"ina nan lafiya lau, dan nasan yanzu Hamma na zaita bincike ni da tuhuman ina shan magani".
dukkansu sun manta da amsa gaisuwar tasa suka fashe da dariya sannan Inna tace, "wato dai angona kana nan da halinka na ban dariya ko?".
sai da yayi gyaran murya sannan yace, "waye angon ki? kinga barni karki cikani da surutu gwara nayi magana da Ammina dan nayi missing voice d'in ta".
Ammin ce ta katse shi tace,
"Meyasa bazaka dawo ba in dai hakane, muna buk'atarka a kusa damu".
Sai da ya sauk'e ajiyar zuciya sannan ya furta, "Afwan ya Ammi na ki tanadi abun dad'i dan nan da sati biyu zan taho".
bai gama rufe bakin shiba Hamma Umar ya d'an juyo ya kalli wayar cikin nutsuwa da murmushi d'auke a fuskar shi ya ce,
"Ajiye wasa B'iyayena, da gaske hakan zaka dawo?".
Murmushi mai sauti yayi yace,
"Insha Allah".
Shima murmushin yayi cikin tsananin farin ciki da k'aunar d'an uwan nashi yace, " Alhamdullahi Usman yau naji dadin jin zaka dawo, Allah ya dawomin da kai lafiya nayi kewarka matuka".

Da haka sukaita hira cikin so da k'aunar juna har lokacin sallah la asar sannan sukai sallama kowa yatashi dan gabatar da sallah shiko Hamma daga masallacin gida ya nufo dan ya sallami su Ammi shi.




Yunwa ce ta tashi Ummul da rawar jiki da kyar ta mik'e ,a daddafe tai sallah la asar sannan ta zira kunnenta a bakin kofa, shirun dataji ya bata damar bud'e kofar ta leko kanta bakowa babu motsin kowa a palour dan haka da fito kai tsaye tai kicin, abinci ta zubo ta dakko ta fito kenan sukai arba da ya Adam jiki na rawa tai k'asa ta ajiye plate d'in ta durkusa jiki na kerma tace,
"Ya Adam". Damgota da yayi ne yasata sakin wata irin gigitacci yar k'ara tana,
"kayi hak'uri yaya, nadena, bazan sakeba". Aiko saukar marukan da taji yasa ta k'walla k'arar data janyo hankulan mutanen gidan ciki harda Hamma Umar wanda fitar shi daga mota kenan,
da Nanne dake b'angaren Abba tana d'an gyare-gyare,
da Hajjajo wadda suke zaune palour ita da Ya Sadiq da Aliyu da gudu sukayo b'angaren Nanne Hamma Umar ne a gaba, shigowar shi tai dai dai da marin da Ya Adam ya k'ara mata,
a fusace ya janye Ummul bayanshi cikin fushi ya d'ago hannunshi tas, ya kifawa Adam mari ,
hakan yasa kowa k'amewa a inda yake sannan kowa da irin tunanin shi, Hamma Umar d'inne ya katse shiru cikin tsananin takaici yace, "metayi maka?".
Kanshi a kasa yana rik'e da kumatun daya sha marin yace, "Hamma inaso inmata fad'ane akan maganar d'azu".
Hannu Hamma Umar d'in ya d'aga ya dakatar dashi da cewa,
"waya saka? na kawoma k'ararta ne?". Ya Sadiq ne ya matso kusada Hamma Umar d'in yace,
"Hamma".
Dakatar dashi yai yace, "ya isheni, kuban waje".
fita su kayi dukkan su sukabi bayan Nanne da Hajjajo wanda tunda Hamma Umar ya mari Ya Adam d'in suka fita suka barsu,
batare daya juyaba yasa hannu ya dawo da Ummul dake manne a bayan shi tunda ya karb'eta daga hannu Ya Adam ya ruggume ta tsam

Please Login or Register in order to submit comment