Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inaso ki nunamai soyayyar da kikemai inaso ya amfana da ita ta hanyar yimai addu a Ummu ki dena zubda mai hawaye".
kai ta rink'a gyad'awa cikin rauni da tsananin nadama,
saita kuma juya ta kalli Abba dake tsaye yana kallonsu ido cike da k'ollah,
sannan ta dawo da kallon ta ga Ya Adam dake murza yatsunta a hankali tace,
"Ya Adam Abbana yamin zab'i mafi al'khairi zab'i mai cike da al'kairai a rayuwata amma ina shaid'an ya hanani ganewa nayiwa iyayena taurin kai gashi zan dauwama cikin nadama da dana sanin rashin biyayya haka zan k'are rayuwata na kasa yiwa iyayenmu d'a'a kaitona Allah ya wadaran halina bani da wani abun koyi lallai duk yarda tayiwa iyayenta ba dai-daiba tana tare da nadama ya Adam na tsani kaina na cutar da Hamma na na b'ata ran mahaifanmu".
sai kuma ta kife kai wani irin matsanan cin kukane ya kwace mata wanda ya hanata k'arasa kalaman ta ta kife kanta a gwiwar Ya Adam jiki na rawa tana cewa,
"Wallahi ina son shi, inason Hamma Umar Yazanyi Hamma Umar yaga soyayya da kaunar da nakemai,
ya Adam kullum Hamma Umar yana cewa Ummul zaki soni, zakisoni lokacin da soyayyar bazata amfane muba ashe wannan lokacin ne Hamma na yake ganemin dana sani dana nuna mishi so da yake son in nuna mai lallai wannan shine kuskure mafi muni da yarinya tayi dan iyayenta sun mata auren dole".
kuka takeyi sosai tana cike da madama,
Aliyu ne yataho jiki ba kwari yasa hannu biyu ya d'agota ya durkusa gabanta a hankali yace,
"Aunty Ummul kiyi hak'uri, Hamma yace nine abokin shawararki abokin kukanki kuma me rarrashinki kiyi hak'uri kidena kukan nan kinga kinsa Ammi da Nanne kuka ga Abban mu shima yanayi kinga Hamma junior zaiji sautin kukan mu ki dena auntyna dan Allah".
Cikin galabaita da ajiyar zuciya ta kwantar da kanta a cinyar Aliyu tana sheshshe k'ar kuka tana nannad'e kafafun ta,
hannun Aliyu yasa yana shafa bayanta yana bubbugawa tare da share mata k'ollar cikin lallashi da haka bacci yayi gaba da ita,
su kuma Abba ya zauna yayi ta musu nasiha Usman kuma sai ajiyar zuciya yake sauk'ewa yana ruggume da farouq,
a haka rayuwa tayi ta juyawa rana d'ad'd'ayace
basa zama suyi kuka a hankali mutuwar ta fara shiga jikinsu,
lokaci yaja kwanaki sun tafi tuni Farouq ya cika kwana arba'in.


A bangaren Mustapha kuwa a kullum koda yaushe tunanin shi nakan Ummul da yaronta dan haka ranar Asabar suka shirya da umman shi suka nufo potiskum dan duba lfy Ummul da jaririnta, dai dai lokacin da motar Mustapha na shirin shiga harabar gidanne motar Dr Bashir ta sako kai dan fitowa wanda shima zuwa ganin Ummul da yaronta ya zame masa jiki a duk lokacin da baida aiki,
daga cikin mota suka gaisa da Mustapha sannan ya wuce cikin gidan shiko Dr bashir ya fita,
Kayane na gani na fad'a da suka had'a da sabulai man shafawa powder, pampers, wipers da sauran kayan jinjiri Mustapha ya lodo kamar me bud'e shagon mother care, duk na Umar faruq wanda Aliyu ke kira da junior,
Bayan ya gaisa da su Ammi da Nanne Aliyu yamai jagoranci zuwa palourn bak'i sannan ya kawomai abin sha sannan ya fita,
a cikin d'akin Kuwa Ammi ce ta maida hankalin ta kan Ummul dake zaune bakin gado cikin sigar lallashi da bada umarni da kulawa
tace,
"Ummu na ki kaiwa Mustapha yaron nashi ko".
Dakai ta amsa tad'au katon hijab ta saka sannan Umman Mustapha dake rik'e da Farouq ta mik'a matashi ta karb'a ta fice,
sukuma sukaci gaba da jajantawa juna irin jarrabawar da suka fuskanta.

Mustapha dake zaune yana latsa wayar shi sallamar Ummul tasa ya aje wayar a gefe yamik'e tare da amsa sallamar yamik'a hannu ya karb'i Farouq dake ta bacci sannan ya koma ya zauna yad'an dago kai yana kallon Ummul dake tafiya kamar mara lakka a jiki har ta sami kujerar dake fuskan tar wadda yake zaune ta zauna tai k'asa dakai tana wasa da yatsun hannun ta sannan yamai da kallon shi ga Umar faruq,
Shiru ya ratsa na y'an muntina sannan Ummul tai k'arfin hali tace,
"ina kwana".
Saida taji shirun yayi yawa sannan ta d'ago kanta a hankali tasauk'e idanun ta kan fuskar Mustapha dake rungume da Umar faruq kallon yaron cikin tsananin k'auna da tausayawa maraicin shi, lokaci d'aya tausayi shi ya rufeshi tuno Hamma Umar kawai sai idanun shi ya fara zubda k'ollah,
da sauri ta maida kanta k'asa ganin
hawayen Mustapha sai wani irin raunataccen kuka mai zafi ya kubce mata,
Mustapha da kyar ya dai-dai ta nutsu warshi sannan yace,
"Khairi dan Allah kiyi hak'uri banyi haka dan na saki kukaba please ki dena zubdawa Hamma Umar hawaye Insha Allah muna zata mai rahama gatan da zakiyi mishi addu'a ce".
ai kamar ya dad'a tunzura ta tacigaba da kukan da sauri ta mik'e ta fita daga palour cikin kuka a zahiri ko fuskar Mustapha bata son gani ji take sanadin shine tayi duk wani kuskure da taurin kai shiyasa da zaran ance mata yazo sai ta resa meke mata dad'i,
gashi shima in yazo kullum sai Farouq ya sashi Kuka tana fitan,
Mustapha yasake rungume Umar Faruq ya lumshe idanuwa yanajin kaunar yaron na ratsa duk wata gab'a ta jikin shi,
Dasu Ya Adam sukaita hira har lokaci yaja sannan yaje sukai sallama dasu Ammi suka kama hanyar damaturu.





Yau asabar wanda yayi dai-dai cika watanni 4 da Farouq yayi,
misalin k'arfe takwas Usman yafito daga b'angarensu sanye da farar jallabiya yanufi b'angaren Nanne kai tsaye d'akin Ummul ya shiga yasame su zaune da alama nono Ummul keba Umar Farouq ta yadda yaga tai maza ta sauke rigarta,
k'asa yayi da kai ya tsugunna ya kuma gaida Ammi sannan ya dago kai ya kalli Ummul yace,
"kawo shi".
mik'a shi tai batare da ta dago kantaba yasa hannu ya karb'e shi sannan yace,
"kinci abinci ne?".
Kai ta girgiza alamar a a d'an juyawa yayi ya kalli Ammi kafin yayi magana Ammin tace, "kaga abincin nan zataci kenan yaron yafarka daga bacci,
to nabashi ruwa yasha nace taci sannan ta ba shi nonon,
amma saina ga hankalin ta bai kwanta da hakan ba, shiyasa nabata shi yasha tukuna".
Murmushin karfin hali yayi ya kalli Ummul ya jijjiga kai ya juya rungume da yaron shi, a parlour su ya zauna ya kwantar da Faruq kan cikin shi ya zubamai ido saikuma ya fashe da kuka mai cin zuciya da k'unar rai yana kad'a kai wanda hakan yazama al'adarsa yana dawowa daga aiki zai d'auki Faruq yaje yasashi a gaba yaita aikin zubda k'ollah yana tuno d'an uwanshi Hamman shi abin begenshi.

Ammi ce zaune tana kallon farcen hannun ta taga yanda suka fito sukai tsayi nan da nan ta tuna gudan jininta wanda tunda yayi wayo shike yanke mata farce dan haka ta manta da lokacin da ta yanke farce ta a rayuwar ta, hannu tasa ta d'auko abin yankan farce sannan ta koma ta zauna kan carpet ta fara gwada yankewan sai abin ya murd'e mata lokaci d'aya begen Farouq d'inta ya rufeta mutuwar ta dawo mata sabuwa kawai sai ta kifa kai jikin gado tasaki matsanan cin kuka mai cike da tausayi.

A part d'in su ya Usman Kuwa,
ya Adam na kwance rigin gine ya d'ora dan lelensu Umar Faruq a kan cikin shi shikuma Ya Usman ya zuro hannu yana daga kwance yakama k'afar faruq yanata murza k'asan k'afar a hankali shiko Farouq sai dariya yake yana wulla hannaye,
Ya Sadiq ne ya shigo sanye cikin farar shadda yanata zuba kamshi yai sallama suka amsa sannan yace,
"Ya Adam dan Allah kabani junior zamuje unguwa".
Kai Adam d'in ya d'an d'ago yakalleshi yace "ina zakuje?".
cikin mik'a hannun yace,
" D'azu dana fita zan sayoma Nanne turare ne naga wani takalmi na yara me kyau shine nakeso inkoma da Farouq in sayo masa".
aiko yana rufe baki Ya Usman ya mik'e yace,
"muje nima zanje,
kuje mota bari inje gun Ummul koda akwai abinda takeso a seyo mata".
Yana fad'in haka ya nufi cikin gidan,
Shigar dayayi tambayar Ummul ne yasa yaga Ammi ita kadai a d'akin ta kifa kai hannunta rike da abun yankan farce tana kuka mai cin rai,
cikin rauni da sanyin jiki ya zame ya zauna kusa da ita yasa hannu ya karb'i abin yankan farcen kawai sai ya fashe da kuka mai ban tausayi ya kasa yanke mata farcen da rufe idonshi sai ya rink'a tuno yadda Hamman shi ke yanke mata farcen.
shirun da Adam da Sadiq sukaji suka gaji da jirane yasa suka shigo dan duba me ya tsaya yi,
aiko samun su sukayi suna kuka ba me rarrashin wani cikin su ganin haka,
Sadiq ya zube guiwowin shi a kasa ya dafa kafad'ar Usman shima Adam ya rab'a yazauna bakin gadon sannan yafara bawa Ammi da usman hakuri da lallashin har saida suka samu suka hakura,
sannan Usman yakama hannun Ammin shi ya yanke mata farce sannan yankan farcen Umar farouq,
daga ranar yanke music farcen ya zame mashi abun yi duk k'arshen sati.




Ranaku na shud'ewa wattanni sun tafi har Farouq yayi wata 7 B'ngaren Ummul kuwa kullum cikin kuka dasa mutane kuka tana fad'in irin yadda takejin Hamma Umar da soyayyar shi mai k'arfi a zuciyar ta yayinda ya Adam ya Sadiq Aunty Halima dake zuwa daga gidan ta duk kwanaki biyu suka dage wajen kula da y'ar uwarsu dan samar mata da farin ciki.

Kamar kullum yauma zaune suke a palour nanne suna ta hira Aliyu zaune gaban Ummul yana b'are mata lemo yana bata labarai masu ban dariya su ya Sadiq na tayashi, Nanne ce ta fito daga bedroom nata ta zubawa yaran nata ido cikin kulawa tace to ina Yayan ku Usman? ya Sadiq yace,
"yanzu yad'au Faruq yafita dashi".
ajiyar zuciya tayi tace, "daman yanzuma fitowa nayi ince a d'aukeshi daga koyan tsayuwar kar ya gaji".
Da haka ta wucesu tanufi bangaren su Usman,
abinda take zato ta gani,
Usman zaune yasa Farouq dake ta wutsil wutsil a gaba yana aikin kuka,
zama tai gefen shi a hankali tace,
"haba Usman, nad'auka zaka sassauta wannan damuwar da kake, nad'auka nasihar da mukaima jiya nida Inna da Hajjajo zata sa ka sassauta wa ranka, dan Allah kayi hak'uri ka ruggume k'addararka ka dena kukan nan haka, addu'a Hamman ka yakeso daga gareka a yanzu ba kukaba, kagafa d'anka yanzu yayi wayo yana buk'atar wasa ,
kuma kaga yafi sabo dakai kaduba yanda yake kallonka ya gane muryarka dayaji yake woige-woigen neman ka amma kuma saika sashi gaba ka rink'a kuka".
D'an d'aga kai yayi ya kalli Umar Farouq da girman sa da wayon shi keba kowa sha'awa dan yarone bulbul dashi fari tas kamar balarabe ga dimple dake kumatunshi inka gan shi kace yayi shekara amma watan shi 7 ne,
shi Kuwa Usman sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya d'auki yaron ya rungume yana shafa bayan shi,
Ita Kuwa Nanne kanshi ta shafa tace,
"Allah yayi maku albarka".
hawaye ya zubda masu zafi sannan yace,
"Amin Nenne".



Haka rayuwa taita tafiya da Ummul da dad'i ba dad'i dakuma samun kulawa ta musamman daga iyeyenta yayunta kaninta da uwa uba ya Usman wanda duk lokacin shi natane ita da yaron shi wanda komai nashi ke kanshi inko yajiyo kukan shi har yana gudu da tun tub'e dan so da k'auna, sau da yawa yakan cewa su Adam idan suna hira,
"inajin nafison Faruq junior a kan kowa a duniya ciki harda Hamma na dan so kala da yawane a kan Junior son da nakewa mahaifinshi ma ya dawo kanshi".


Daga b'angaren Mustapha kuwa abin ba a magana da duk k'arshen sati yana hanyar potiskum yayin da mahaifiyarshi ke rakoshi bayan sati biyu ko uku, Dr Bashir ma ba a barshi a bayaba domin kuwa baya wuce sati bai ziyarci Ummul da Umar farouq ba.

Haka abin yake agun Inna da daddy abun saidai hamdala dan kuwa Ummul da d'anta suna ganin gata tako ina matsalar Ummul d'aya rashin abin kaunarta hasken idanuwanta Hamma Umar wanda har yau bata dawo dai-dai ba ita da Usman Ammi kuwa yanzu tasa dangana a ranta.




Ranar wata asabar misalin k'afe hud'u na yamma ne Mustapha ya iso gidan su Ummul kamar yadda ya saba duk sati, da Aliyu yafara had'u a farfajiyar gidan yana zaune kan kujerar roba yana karatu cikin girmamawa yataso ya karb'i lodojin hannun shi yakuma gaida shi sannan yamai jagora zuwa palour sannan ya wuce ya sanar da Ummul,
ba afi minti ashirin ba Ummul ta shigo sanye da hijabita k'ato har k'asa tana rike da Umar faruq da yaketa zullowa yanason sauka tai sallama ya amsa mata cikin kulawa sannan tasami kujerar gefe ta zauna, Farouq ko yanata kiciniyar sauka Mustapha yai d'an murmushi yace, "sauke shi mana".
Bata d'aga kantaba ta sauke Farouq aiko kamar yana jira ya rarrafa da saurinshi kasancewar shi mai kuzari da lafiya kuma yana ji da k'arfi ya je wajen Mustapha,
aiko shima hannu ya bud'e yana zuwa ya d'auke shi yana dariya
tare da d'agashi sama yana sumbatar goshin sa,
Sheshshek'ar kukan Ummul ne ya tsagaitar da Mustaphan daga wasan da yakema Farouq ya d'ago kan shi cikin damuwa da kid'ima a hankali murya can k'asa yace,
"Khairi wallahi da kin san yadda nakeji akan kukan nan naki wallahi dakin taimaka min kin dena".
sai kuma yayi shiru tare da cire glass d'in idon shi ya mik'awa Farouq da yaketa kokuwar karb'a sannan yaci gaba da cewa,
"Ummul bana jurewa banajin dad'i kuma bana iya bacci ko cin abinci aduk lokacin da natuna wannan kukan da kike, kiyi hak'uri khairi dan Allah ki daure".
Haka yayi ta aikin rarrashi kamar yadda ya saba duk sati dako duk yanda zaiyi Ummul bata cewa komai sai aikin kuka a haka ya zauna

Please Login or Register in order to submit comment