Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasha".
Itama Anty Shuwa ɗaure fuska tayi ba wasa tace,
"Kuma wannan ma yanzu zaki shanye shi ba,
ni banson shirme ki amsa kishs kawai".
Bubbuga ƙafa tafarayi a ƙasa tana yarfa hannu da ƙunƙuni ƙasa-ƙasa dai-dai lokacin shigowar Usman da Adam da Sadiq sun dawo daga gaida Inna,
Dasauri Usman ya ƙaraso cikin palour yace,
"Wai meye, Halima ce ko?".
Ɗauke kai Aunty shuwa tayi kamar bata jiba itako Aunty Halima cewa tayi,
"kai ya Usman to bani bace itada Auntyn ta". ɗan juyawa yayi ya kalli Aunty Shuwa data ɗaure fuska babu alamun wasa tace, "kyaleni da ita, abu nabata wai bazata shaba ta k'oshi".
ɗan leƙa cikin kofin yayi sannan ya tambaya,
"Magani ne?".
"eh maganin ciwon ciki ba".
Inji Halima,
ganin yadda yajuyo yana kallonta yasa Nanne tashi ta fice dan ta gane sarai Usman ya gane maganin menene ake batan,
dan tasan halin shi zai iya faɗan komai,
a hankali ya ƙarasa inda take zaune yace, "Ummu na yi haƙuri kisha mana kinji kinga yanada amfani".
Noƙe kafaɗa tayi alamar taƙi a hatsale Aunty Shuwa tace,
"Matsamin dan Allah intafi ana baki kinawa mutane yanga wazai amfana? ni ko Halima ko ke?".
Dasauri yamiƙe ya karɓi kofin ya tsura mata ido fuskar shi babu alamun wasa yace,
"Ke wallahi sai kinsha ko in ɗura maki, wannan ai shirme ne,
au tukun ma wai shin ko dai baƙin ciki zakimin?".
da jin haka Ammi ma ta tashi ta fice tabarsu ganin taƙi karɓa yace, "Sadiq riƙe min cup ɗin Allah saina ɗura maki zakiwa mutane asara da baƙin ciki inke bakya so ni inaso kuma dole kishi".
Yana faɗa yana matsowa kusa da itan sanin halinshi yasa ta miƙa hannu Sadiq ya miƙa mata kofin tana ɓata fuska takai bakinta,
"Gwara miki dan wallahi ba abinda zai hana in d'ura maki shi". Saida ta shanye tas sannan tasauke kofin tana dama fuska kamar zatai amai,
kallon Aunty Shuwa yayi wacce kunya ta rufeta har ta kasa ɗaga ƙafarta wato Usman yama gano me ake bawa Ummu,
shiko ko a jikin shi yace daga yanzu in taƙi sha dan Allah ku kirani".
Yajuya zai fita Hajjajo datake kallon ikon Allah tace,
"fitsararre".
Juyowa yayi kafin yaba ta amsa idon shi yasauƙa kan Ummul da taketa kakarin amai kallon ta yayi tare cewa,
"Kada kiyarda ki amayar da abinnan dan sai an ƙara maki wani".
Ficewa yayi suko duk sukayi shiru suna kallon juna itako tashi tayi tafice tana buga ƙafa.




Yau asabar da misalin ƙarfe 10:30am na safe dubban jama a suka shaida daurin auren USMAN IBRAHIM UMUR SHUWA da amaryar shi RABI'ATU HASSAN UMAR SHUWA ciki da abokan Hamma Umar wanda dayawa suka sami gayyata daga Dr Bashir da kuma Mustapha shima da mahaifinshi,
Ango kuwa Usman lokaci ɗaya tunanin ɗan uwanshi ya faɗo mai a take ida nunshi suka fara zubda ƙolla mai tsananin zafi yana tuna a yau ds Hamman shi na raye da zaifi kowa farin ciki da yau zaiga gata mai tarin yawa cikin kuka yake gaisawa da abokan Hamman nashi,
bayan ya shiga cikin gida kuwa Ammin shi ya tasa a gaba suna wani irin kuka mai cike da ƙuna a zuciya da kyer aka samu Abba da Hajjajo suka tausasu.

Haka abin ya kasance a cikin gida mata nata nasu hidimar ga matar Dr Bashir da matar Mustapha da Ummanshi,
ita kuwa Ummul yau mutuwar Hamman ta takuma dawo mata ruggume Farouq tayi ta durƙusa gaban Adam da Sadik tana kuka mai tarin nadama da dana sani,
Shima yaro ganin yadda mahaifiyarshi ke kuka sai ya fashe da kuka mai ƙarfi
ayyah Adam shma gaba ɗaya ya kasa control en kanshi sai hawaye cur-cur ya kasa magana
Aliyu kuwa jawo Farouq yayi ya riƙeshi gam a jikin shi suna kuka,
Sadik ne da Anty Shuwa sukayi ƙarfin halin lallashin su da yi mudu nasiha,
saidai Amaryar kam da kyer aka samu aka rarrasheta saboda kuka da takeyi mai tsanani dan tunawa da masoyinta Hamma Umar.

Haka jama'a sukayi ta tayasu murna har zuwa dare aka fara watsewa.

Ango yanata sintiri dan yana son ya lallashi Ummul enshi da kanshi kuma shima yana buƙatar ta tausayawar ta a gareshi dan yau gaba ɗaya begen Hamman shi yake,
karo na 3 yashigo yasami Nanne da Ammi sai Aunty Shuwa da Aunty Nafisa yasami gefe yazauna gaisawa sukayi tare da ƙara yimai addu'a kai yafara sosawa yakalli Aunty Shuwa cikin rauni yace, "Ina take?".
Haɗe fuska tayi sannan kuma abin nashi ya bata dariya ya kuma bata tsusayi a hankali tace,
"To anace tanada bak'i".
D'agowa yayi ya kalleta sannan ya saci kallon Ammi daketa ƙoƙarin maida ƙollar ta a hankali yace,
"Dere yayi fa kuma zamuje wani wuri da ita Ayyah dan Allah a bani matata".
Ammi ce ta karb'i zancen da cewa,
"A,a baza a baka ba Usman,
ainan ba gidan ka bane kuma da bakinka kace sai kaje course kadawo zata tare".
Da hannu ta nuna mai hanya alamar ya tafi, marairaice fuska yayi kamar zaiyi kuka yace, "Nanne".
Bai ƙarasaba tace,
"Jeka kayi wanka ka huta babu mai hanaka matarka".
Ɗan murmushi ya ido cike da ƙollah yatashi yafice yana ƙoƙarin cire babbar rigar jikin shi, Ammi ta kalli Nanne tace,
"Bafa zan yarda da wannan tsarin ba". ƙasa Nanne tayi dakai cikin girmamawa tace,
"Kiyi haƙuri Addana dan tun ɗazu Abban su yace kada a hanashi matar shi ,
dan duk su biyu kukan da sukeyi na abu ɗaya ne tuno Umar ne kuma su duka kowa zai tsaida hawayen shi dan ɗaya yayi shiru,
kuma ai banga laifin hakan ba tunda mutune dayawa suna aure su tare gidan iyaye nasu kinga shima yanada damar hakan kuma kinga yama kusa yin tafiyar".

Aunty Shuwa ce ta kalli Ammi tare da cewa, "Ammi ki kyale ɗan Abba yasha sha anin shi dan wallahi dagashi har Ummul sun ban tausayi ga yadda ƙaddara ta haɗasu bawan Allah Farouq shima yau yayi kukan rashin Uban da bai saniba".
Itako Ammi baki ta d'an rumtse hawaye na bin fuskarta tace,
"Hmmm to Allah yayi musu albarka Allah ya jiƙan Umar Allah ya mishi rahama Allah ya raya abun da ya bari".
"Amin Amin Ameeeeeeeen ya rabbil izzati"
suka amsa baki ɗayan su,
Aunty Nafisa matar Daddy wacce tunda aka fara magana tayi shiru tace,
"Au shiyasa naga Adam da Halima sunata shirya Ummul ɗin".
Ammin ce ta miƙe tana tafiya tace,
"eh mana ai duk bakinsu ɗaya har da Adam kamar mace,
nidai baruwana kuma bame takuramin yarinya.


A ɗakin su Usman kuwa Adam ne da Nuru sukayi ta lallashin Usman,
miƙewa sukayi
jin muryar Anty Halima wacce ta shigo ruggume da Farouq Ummul na biye da ita a baya,
A hankali tace,
"Ga Farouq tun ɗazu yake kuka sai a kawoshi gun Abeen shi".
hannu Usman yasa ya karɓeshi sannan ya ruggemeshi
suko Anty Halima da Adam da Nuru fita sukayi suka bar part ɗin gaba ɗaya.


Shiko Usman suna fita yasa hannun ya ruggum.....



*By*
*GARKUWAR FULANI*
[11/29, 9:44 PM] El-hajj🤣: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMRI*

Page 3⃣7⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



*MOH ALLAH WUJI FURƊA TA FULLO BE FULAKU KOSAM EH DAN GOL*



*Wannan shafi naki ne ke kadai k'anwata ta kaina Queen Hafsi Allah bar zumunci da k'auna dear 🤝*








*H*annu yasa ya jawa Ummul ɗin ta faɗo jikin shi cikin sauƙe ajiyan zuciya ya haɗasu da Farouq ya ruggume su tsam a jikin shi yana jin wani irin yanayi mai cike da tarin rauni,
tabbas wani abu sai mutuwa inba mutuwaba ya za'ayi ya auri Ummu matar ɗan uwanshi gaba ɗaya begen ɗan uwanshi ya rufeshi zuciyarshi ta cika da rauni a hankali wani irin kuka ya kufce mai,
kuka mai cin zuciya har jikin shi na rawa sai ƙara ruggume ta yake yana sheshsheƙa hawaye na bin fuskar shi,
itama Ummu sai kara lafewa tayi a jikin shi tacigaba da kukan dama tun safe take yinshi,
Kuka suke sosai bame rarrashi wani a cikin su sai ruggume juna sukeyi suna kuka mai cike da ƙuna a zuciya,
sun ɗau lokaci mai tsawo suna cikin yanayin tuno da jigonsu gaba ɗaya zuƙatansu sun cika da rauni,
Cikin kukan Ummu ta ɗago kanta fuska cike da ƙollah ido ta ɗan firfitar ganin yadda numfashin ya Usman ke fusga yana neman ɗaukewa sai karkarwa yake ida nunshi sunyi jazir ƙirjinshi na bugawa da ƙarfi ,
janye jikinta ta tayi hankali ta miƙa hannun ta karɓi Farouq dake ta bacci daga hannun shi tamatsa a hankali ta kwantar dashi akan 2 seater,
sannan tadawo jikin shi ta ruggume shi a hankali takamo hannun shi ta jashi suka zauna kan 3 seater,
ruggume shi tayi cikin kuka da rawar murya tafara magana a hankali tace,
"Hamma Umar baida wani fargaba daya wuce ya ganka cikin tashin hankali,
kullum burinsa ya ganka cikin farin ciki,
fatan Hamma Umar baya wuce samun lafiyar ka ya Usman,
ko a lokacin da zai rasu sunan ka dana Ammi ya kiramin amman Allah bai bashi damar karisa min maganar da yake son faɗa minba sai yayi kalmar shahada,
Abunda ban saniba wata ƙil amanar ku zai barmin ko cemin zai na kula da kune ban saniba".
Tana kaiwa nan suka daɗa rungume juna suka sake fashewa da kuka jiki na rawa ya kuma matseta a jikin shi murya na rawa yace,
"Ummu na ni kam Hammana yabar min amanar ki keda Farouq randa yayi zuwanshi na karshe a gidan nan,
saida duk ya bar mana wasiya amman a lokacin bamu ganeba,
Ummu kituna meyace min nida Adam".
sai kuma ya sake matsota jikinshi yana zubda ƙolla sannan yaci gaba da cewa,
" Hamma na cemana yayi,
"Da inada damar tafiya da Ummul duk inda zanje,
da ko ina zanje zan tafi da ita,
sai dai kach bani da damar yin tafiya da ita dole in barmaka ita Usman kaine ɗan uwana kuma dole ka kula da family na,
Ummu
kin tuna abinda yacewa Adam
yace Adam zantafi da ita amman zata dawo in tadawo duk maison ɓata min rai ko tozar tani to ya ɓatawa Ummu rai niya ɓatawa!
Ummu kin tuna abinda Hamma yacewa Aliyu,
yacewa Aliyu kai kuwa Aliyu a zatona kaine abokin kukan ta kaine abokin shawarar ta Aliyu ko duk zasu dakarmin Ummul a zatona kai zaga zame mata katanga abun jingina azatona kai mai tayata kuka ne".

Sai kuma ya sake ruggumo Ummun cikin tarin ƙunci ya sauƙe nannauyan ajiyar zuciya yace,
" Kin tuno me yacewa Sadik
Cemai yayi
"Sadiq inta dawo ka kasheta don dole zata dawo badon ina soba dole zata dawo cikin ku ba yadda na iya,
ya kuma cewa Nanne Ummul fa madadin mutum 3 ce ni Usman da Ammin mu dakuma ɗan cikin ki ya ware kanshi a lissafi ashe zai tafi ya barmune bamu saniba tafiyar da bazai dawoba ashe duk maganganun shi wasiyace a garemu,
Ummu dana sani dana hana Hamma na tafiya a wannan ranar,
ashe shike nan mun rabu har abadan,
ashe shike nan yayi zuwanshi na ƙarshe a gidan nan,
Ummu ki tuna a ranar Hamma yace min,
Usman nauyin farin cikin Ahlina yana kanka in bananan".
Sake matsota yayi yaci gaba da kuka har yana shiɗewa,
Cikin tsana nin kuka itama ta ruggumoshi tana cewa,
"Ya Usman kayi hakuri mubar yiwa Hamma na kuka muyi mishi addu'a zaifi farin ciki damu, kabar kukan nan Hamma bayason kukanka nima banason kukan ka,
ya Usman ina sonka ina son farin cikin ka ka dena kuka".
Cikin kukan ya tallabo kanta ya kalleta da kumburarrun idanun shi ya sakar mata murmushin dayafi kuka ciwo a hankali yace,
"Allah ya ɗaiyaba min Ummuna,
nima ina sonki".
Itama murmushin tayi wanda hawaye ke bin fuskarta a hankali tasa tafin hannunta tashare mai hawayen,
shima haka yasa hannu ya share mata nata ya ruggumo ta yana sauƙe nannauyan numfashi a hankali yace,
"Ummuna zan dawo miki da farin cikin ki keda Farouq ko Hammana zaiyi farin ciki dani".

Shiru tayi tana kallon shi cikin jin tausayin shi,
Shiko ido ya lumshe cikin sanyi yasa hannun shi yana shafe fuskarta tare da gashin kanta hannun yasa ya ƙara jawota jikin shi cikin salon lallashi yasa hunnun shi yana shafa jikinta yana sunsunarta tare da goga sajen shi a kumatun ta,
a hankali ya rinƙa fese mata iska mai sanyi cikin kunnen ta,
hannun shi yarinƙa cusawa cikin rigarta yana yiwa kirjinta wani irin salo mai wuyar faɗuwa yana sunsunar wuyanta yana wani irin numfashi gaba ɗaya ya gigitata ya gigita kanshi,
itama sai sake narkewa take jikin shi tana mika tana ɓoye fuskarta a jikinshi cikin tsananin kunya,
haka suka kasance cikin yanayin rarrashin juna da kyar ta zame jikinta,
ta koma gefe tana gyara rigarta da ya cukuikiye a hankali takai dubanta ga agogon dake manne a palour 12 dai-dai
shiru tayi a wurin tana satan kallon shi yadda
ya kife kanshi a jikin kujerar yana maida numfashi gaba ɗaya yayi wani iri,
da kyar itama ta saita kanta a hankali tace,
"Ya Usman tashi ka rakani zan koma cikin gida kar Ammi ta farka taga Farouq baya kusa da ita".
riƙo hannun ta yayi murya na rawa yace,
"a,a dan Allah kibar shi mu kwana anan". miƙewa tayi tana girgiza kai,
"a,a gaskiya nidai tafiya zanyi wallahi ni kunya nakeji bazan iya kwana anan ba".
Shima miƙewa yayi ya kamo hannun ta ya lonƙoso kai yace,
"Ki taimaka min habibty zan shiga wani hali in kika barni cikin wannan yana yin ina buƙatarki kusa dani,
ki kaishi saiki dawo in kinga kowa yayi bacci kinji plssss".
Dakai ta amsa mai alamar "Toh".
dan ya Usman yana bata tausayi kuma tana tsoron karta kuma irin kuskuren da tayi a baya A hankali ta ɗauki Farouq ɗin ta fita kai tsaye ta wuce ɗakin su inda ta samu tuni Ammi tayi bacci.

Kwantar dashi tayi akan gado a kusa da Ammin,
sannan taje tayo wanka tashafe jikinta da turaruka masu ƙamshi da sanyaya zuciya sai kuma
itama tazo ta kwanta gefen shi,
Addu'a tayi ta tofa mashi ta tofe kanta sannan ta kwanta tajanyo wayarta ta buɗe data dan taga ya Usman nata kiranta kuma bata son ɗagawa kar Ammi ta tashi,
tana buɗe datan
saƙon shi ta gani,

"ina jiranki a kofar Nanne ki fito mutafi kinga kowa yayi bacci".

Amsa tamaida mai,

"kayi haƙuri kaje ka kwanta saida safe".

"gaskiya bazan iya baccin ba kizo ki taimaka min in kuma bakizo ba kuka zanyi tayi har gari ya waye, daman ni nasani ba mai sona sai Hammana".

Jiki na rawa ta kashe wayar gaba ɗaya ta lallaɓa dan kar Ammi tafarka ta fice,
a bakin ƙofar palour ta taddashi tana fita yasa hannu ya ɗauketa cak ya ruggume ta a jikin shi,
bai sauketa ko inaba sai sai akan gadon shi,
A hankali ya kontar da ita cikin wani irin yanayi ya konta gefenta a hankali ya jawota jikin shi yana maida numfashi hannun shi ya cusa cikin rigar baccin jikin ta yana mata wani irin salo mai taɓa zuciya a hankali yake sarrafata da salo mai cike da so da ƙauna haɗe bakinsu guri guda yayi yana mata wani irin tattausan kiss,
hannun shi nakan kirjin ta yana murzawa dukkansu sun rikice sunyi nisa cikin duniyar masoya a haka sukai ta fama har bacci ya ɗaukesu suna ruggume da juna cikin happy.

A zabure Ummu ta farka,
aiko tare suka mike yana daɗa matseta kamar zaa kwace mai ita,
"Ya Usman kabarni intafi kafin kowa ya farka kaga an fara kiran salla ".
Wani irin kallo yake mata kamar zai haɗiye ta baice komaiba ya saketa,
dasauri ta fice bayanta yabi da kallo badan yasoba banɗaki yashiga yayi wanka sannan ya fito ya fara nafilillin shi.


Gari na wayewa misalin 8:00 Usman ya shirya tsab yaje yagaida Abba da Hajjajo sannan ya shiga ɓangaren Nanne, a kitchin yaji motsin Nanne dan haka ya tsaya ya gaidata sannan ya wuce ɗaki, zaune yasami Ummul a kan sallaya Ammi kuma na bakin gado ta zuba mata idanu, kamar jira take ya shiga tana ganin shi ta zuba mai ido cikin son gano halin da ɗan nata ke ciki,
Shiko Usman a hankali yazo ya

Please Login or Register in order to submit comment