Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallonta har zuwa k'arfe 3 a lokacin ta farka ido ta zuba mai ganin yadda yake kallon ta,
cikin baccin ta juya gareshi tasa hannu biyu ta ruggumo shi,
murmushi yayi sannan ya gyara mata konciyar,
sai can k'arfe 4 kuma ta sake farkawa nan ma har yanzu baiyi bacci ba kallon ta yakeyi kamar zai had'iye ta,
nan ma juyi tayi a jikin shi cikin sanyi ta shafa sanjen shi har zuwa k'irjin shi a hankali ta sauk'o da hannun ta har kan mararshi cikin magagin baccin tace,
"Hamma har yanzu bakayi bacci ba,
me kake so ne? ".
hannun ta ya rik'o a hankali yace,
"Pakala nake so kuma naga kin gaji gashi baki da Lafiya ko zaki iya da buk'atuna?".
a hankali tace,
"Uhum".
jawota yayi ya ruggume cikin jin dad'i yace,
"Nagode Khairi Allah ya miki al'barka amman yanzu kiyi baccin ki sai na dawo masallaci sai ki bani kafi shayi tunda yanzu biyar ta kusa".
kai kawai ta juya sannan taci gaba da baccin shikoh tashi yayi yaje yayi wonka sannan yazo ya d'anyi nafila ana kiran salla ya tafi massalaci,
bayan ya had'a mata ruwan wonka ya kuma tasheta,
itama wonkan tayi sannan tazo tayi salla ta d'an tab'a karatu zuwa k'arfe bakwai ta koma ta konta,
shiko bakwai da rabi ya shigo gidan yana shiga ya lek'ata ganin tana bacci ya wuce kitchen kasan cewar yau Monday sauri sauri ya had'a musu breakfast sannan ya shirya musu komai kan dinning table,
wonka yaje yayi a gaggauce yana fitowa k'ugunshi d'aure da towel ya nufi d'akin Ummul da nufin ya tasheta tazo taci abinci ya kuma bata magani,
yana shiga ya wuce bakin gadon a hankali ya yaye blanket da ta rufe jikin ta,
murmurs yayi ganin daga ita sai borgon duk zanin jikin ta d'in ya gudu hannu yasa ya shafo kirjin ta wanda hakan ya tayarmai da buk'atarsa,
kawai sai ya rab'a gefen ta ya konta cikin sanyi ya fara lalubarta,
koda ta bud'e ido batayi yunk'urin hanashi ba,
haka ya murzata har saida ya samu gamsuwa sannan ya ciccib'e ta ya wuce da ita toilet nata,
tare sukayi wonka,
sannan suka fito d'akin shi ya koma ya shirya tsab sannan ya fito,
koda ya fito parlour yayi mamakin ganin bata fitoba,
dan haka ya wuce d'akinta yana shiga ya sameta sai rawan sanyi take kar-kar gaba d'aya zazzab'i mai zafi ya rufeta duk jikin ta kamar wuta,
da sauri ya ruggumeta cikin tsananin k'auna da kulawa yace,
"Ummu na sannu zazzab'in nan yana bani tsoro wallahi".
ita dai ba magana sai hawaye da rawan sanyi ganin haka,
yaje ya had'a mata tea sannan ya kwaso magungunan ta yazo ya bata,
a Karo na forko kenan Ummul ta karb'i maganin tasha ba musu sannan ta shanye tea d'in ya kuma k'aro mata tea d'in tashanye tsab,
sannan ya kontar da ita ya d'an rufe mata jikin ta kis ya manna mata a goshin ta sannan ya shafa fuskarta a hankali ya zaro babbar woyarshi ya ajiye mata gefen pillown ta cikin kula yace,
"Ummu na fitar nan ta zame min dole ne badon hakaba da bazan fita in barki baki da lafiya ba amman karki damu yanzu zan dawo bazan dad'eba,
ga wayata na ajiye miki zan fita da k'aramar dan zan kiraki inji ya jikin".
kai ta gyad'a mai,
jiki a mace ya juya ya fita koda yaje dinning table d'in ya kasa cin komai haka ya fita,
tana jinshi ya rufeta ta baya tanaji har ya tashi motarsa sai kuma taji ya kashe motar,
jim kad'an sai ta kuma jin ya bud'e k'ofar parlour nasu ya shigo,
tana ganin shi yazo ya tsaya kanta yana ta kallon ta,
sai kuma ya shafa fuskarta ya fita,
a karo na uku ya kuma dawowa ya zauna gefenta a hankali yace,
"Ummu ina sonki ciwonki na tayar min da hankali".
kai ta juya a hankali tace,
"meyasa kakeke ta zirga-zirga ka tafi mana ko meyasa kake kallo na?".
mik'ewa yayi ya shafa fuskarta cikin sanyi yace,
"wallahi kinmin kyaune yau d'in bana son d'auke idanuna a kanki".
murmushi tayi tace,
"Hamma kaima sai kaga yadda kayi kyau wallahi kamar oggo".
murmushi yayi yana fita tare da cewa,
"ai yau nake oggon Ummu yayan Usmanu d'an Ammi da baban Ibrahim jikan Hajjajo da Inna dan gatan Abba da Daddy da Nenne yayan Adam da Sadik da Halima da Aliyu".
binshi tayi da kallon har ya fita,
yana fita fita ya shiga motarsa ya tafi kai tsaye asibitin su ya nufa jikin shi a mace gaba d'aya ya rasa sukuni.

A gida kuwa Usman ne ya kalli Adam dake gefen shi cikin sanyi yace,
"Adam zan tafi damaturu zanje naga Hamma na tun shekaran jiya bamuga junaba yanzu zan tafi".
cikin sanyi Adam yace,
"Ni dai bazani ba sai Hamma ya huce ".
haka yayi shirin tsab ya fito ya sallami su Nenne da Hajjajo sannan ya fito ya bud'e motarshi ya shiga.

Ita Kuwa Ummul Hamma Umar na fita wani irin zazzab'i mai zafi ya rufeta a take taji wani irin yunk'u ri... ..





*By*
*GARKUWAR FULANI*
[11/18, 9:44 AM] El-hajj🤣: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 2⃣9⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇






*JAMU NA HOLARE BALD'E*





*Y*unk'uri tayi cikin gala baita dan aman da takeyi tun bayan fitan Hamma Umar d'in nata amai d'in take tayi har jikin ta na rawa gaba d'aya ta gala baita intayi yunk'uri sai taji zuciyarya taja ta tsinke ras gaban ta na fad'uwa,
a wahalce ta tashi cikin layi da rawan sanyin zazzab'in dake bibiyarta tattare wurin da tayi amai d'in tayi ta goge filin sannan ta kashe A/C dan sanyin da taji ya rufe ta sannan ta sassake labulayen windows nata har ta konta ta kuma mik'ewa da kyar taje ta rufe k'ofar bedroom nata d'in sannan ta dawo ta konta ta gudundune cikin blanket tana jin yadda d'an cikin ta ya tattare ya dawo k'asan k'ahon zucuyarta,
yayi cus ya dena motsi,
itako lokaci d'aya wani irin fargaba da razani da tsoro mai tsanani ya rufeta haka kawai taji jikinta kamar an rufamata d'anyen fata duk zuciyarta ta raunata a hakan cikin kad'uwa da ciwon wani irin bacci ya saceta.

Shiko Hamma Umar da yake Federal Medical center duk da dama ba kullum yake zuwaba sai akwai imergency dan shi aikin shi duba govnr ne,
so yauma imergency ne ya kawoshi,
aiki sukayi cikin sauk'i shida abakin shi Dr Bashir Ibrahim,
k'arfe takwas da mintu hamsin da biyu suka fito kai tsaye office nasu suka nufa dan office en a jere suke,
suna tafiya Dr Ibrahim na bin bayan Dr Umar Ibrahim Umar d'in da ido ganin gaba d'aya yau komai yake jikin shi a mace duk motsin da zaiyi sai yace,
"Sauri nake zan Koma gidana Ummul bata da Lafiya,
kuma inaso muje gida nayi kewar Usman".
murmushi Dr Bashir yayi cikin sanyi yace,
"Dr Umar anya ko kana son kanka kamar yadda kake son Usman da Ammin ku da Ummul? ".
kai ya gyad'a mai a hankali yace,
"ina jin tausayin su ne".
a dai-dai tsakiyar farfajiyar asibitin suka tsaya sukayi shiru suna kallon juna cikin kasa kunnuwa yayin da gaba d'aya illajirin mutanen dake wurin sukayi cirko-cirko suna baza ido da kasa kunne.

Ta kasance yau Monday 27 February 2014 ranar da mutanen garin damaturu bazasu tab'a mantashi a kund'in tarihin rayuwar su da garin ba musamman zuriyar Alhaji Umar Shina
k'arfe tara dai-dai na safiyar wannan rana *BOKO HARAM* sukayiwa garin Damaturun diran mikiya inda sukayiwa garin zobe wanda forkon shigarsu ta layin uguwarsu Hamma Umar suka shigo wato gidan Ummul kenan dake nyanya line dake gujba road damaturu,
yayin da suna shiga suka rink'a sake bomb da harbe-harbe duk wanda suka kama suyi mishi kisan gillah,
lokaci d'aya garin damaturu ya hargitse ya birkice sai gudu akeyi ana neman tsiratar da rai,
😭😭😭suko tsinannun Allah ta ala sai bi suke gida diga suna kashe Al'Ummar Annabi sannan sun datse hanyoyin shiga garin duk motor da tazo su tsare su kashe a bakin mashigar garin,
a haka har suka kusan to gidan Hamma Umar.

Shiko Hamma Umar a asibitin inda suke tsaye a take saiga motoci da mata maza manya da yara suna shigowa cikin asibitin da gudu dan b'oye rayukan kansu,
abin mamaki sai Hamma Umar yaga gaba d'aya mafi akasarin masu shigowa asibitin yan uguwarsu ce duk mak'o tansu ne kab a cike cikin tsoro da firgici,
ya kutsa cikin su,
Dr Bashir ne ya rink'a binshi a baya yana cewa,
"Dr Umar ina zaka je Dr tsaya mana".
hannun shi ya fizge cikin tashin hankali da firgici yace,
"Ummul! Ummul! Ummul! Bashir banga Ummul ba bashir kalli nan duk mak'otanmu ne gashi sun gudo banga Ummul a cikin suba".
sai kuma ya rink'a kutsawa cikin mak'otan nasu yana tabbayarsu d'aya bayan d'aya,
" ina Ummul kunga Ummul ne?".
amman duk sai suce basu ganta ba,
hakan yasa cikin tsoro da fargaba yayi parking lot nasu motarshi ya nufa,
Dr Bashir d'in ne da sauran mak'otan nasu suka bi bayanshi cikin tarin tsoro suka rik'eshi a firgice Dr Bashir yace,
"Dr Umar ka nitsu ina zaka je kana ga wad'anda suke canma sun gudo nan kaikuma kace zaka koma can plxx Dr Umar karka koma".
ture Dr Bashir yayi cikin rawan jiki da murya yace,
"Ummul bata da lafiya ga tsohon ciki bazata iya guduba kuma kasan kashe masu ciki sukeyi plxx Dr Bashir barni inje".
Dr Bashir kam kai ya rink'a juyawa rik'e da hannun Hamma Umar d'in,
mak'ocinsa ne ya matsoshi cikin rud'u yace,
"Dr karka koma uguwarmu wallahi suna can suna ta kashe mutane".
hannun shi ya fizge da k'arfi ya shiga motarshi yana cewa,
"kace ana can anata kashe mutane Ummul kuma na can sannan kuce kar naje".
yana kaiwa nan ya figi motar cikin firgici ya nufi uguwar tasu,
yana zuwa ya samu uguwar a hargitse duk ko ina sai jini da gawarwakin mutane gaba d'aya jikin shi sai rawa yakeyi cikin tausayawa rayuwar mutan k'asarmu ta Nigeria ya rink'a ratsawa gefe-gefe yana kaucewa gawakin har ya samu ya isa cikin gidan nashi bai had'u da suba,
parking yayi ya fito da gudu ya nufi kan y'ar barandar da zata sadashi da k'ofar shiga parlour nasu,
key yasa ya bud'e k'ofar ya shiga hannun shi rik'e da woyarshi yana ta kiran Usman tun a cikin mota amman har yanzu da yake kiranshi a karona 13 bai d'aga ba har kiran ya katse,
ganin haka ya zira woyar a aljihun shi ya k'arisa bakin k'ofar bedroom d'in
Ummul d'in,
turawa yayi jin k'ofar a rufe yasa cikin tashin hankali ya fara magana da d'an buga k'ofar yana cewa,
"Ummu ! Ummu! Ummuna ina kike? Ummu na kizo ki bud'e min k'ofa Hamman kine".
ita ko Ummul wacce tun sanda harbe-harben Boko Haram d'in suka tasheta a baccin daya saceta gaba d'aya jikin ta ya fara b'ari kar-kar d'an cikin ta ya k'ara komawa saman k'irjin ta numfashin ta ya rink'a korar juna sai wani irin zufa ke tsatstsafo mata tako ina,
ta kasa ko motsi dan fargaba da bugawar zuciya tana jin yadda mak'onta su ke guduwa amman ta kasa tabuk'a komai,
sai yanzu da taji muryar Hamman nata ne ta yunk'ura cikin rawan jiki taje ta bud'e k'ofar,
yana ganin ta ya bud'e mata hannunshi,
da sauri ta fad'a jikin shi,
wani irin ruggume juna sukayi wanda basu taba jiyawa junan su irin wanan ruggumar ba,
Hamma Umar kam da k'arfi ya matseta a jikinshi kamar wanda yaga mutuwa na biye da ita,
itama da iya k'arfin ta tasa hannunta ta ruggumeshi murya na rawa tace,
"Hamma mu buya".
kai ya jinjina cikin rawan murya ya tallabo konta ido ya tsura mata cikin nata idanun yace,
"Ummu naji tsoro karsu kashe min ke shiyasa na dawo Ummu na ina sonki inajin tsoron rabuwa dake zomu fita mu tafi asibitinmu yanzu na shigo layin nan basa nan sun gudu bayan sun kakkashe mana yan uwa musulmai".
sai hawaye car-car a idanu su,
a hakan ya jawo hannun ta ko mayafi basu tuna d'aukaba tunda yanaga mota zasu shiga,
janta yake tana binshi a baya gaba d'aya jikin ta na rawa bata da kuzari ko kad'an
a haka har sunzo k'ofar fita parlour sai kuma duk suka juya suna kallon cikin gidan nasu,
sai ya kuma kamo hannun ta suka fito woje,
taku d'aya sukayi a na biyu suka tsaya cak a tsakiyar barandar tasu,
jikin Ummul rawa yakeyi har d'an cikin ta na yin k'asan maranta kuka ta saki cikin rawan murya ta nuna zugan Boko Haram da suka cika harabar gidan nasu wanda sunkai su 8 gaba d'ayan su rik'e da bindigogi da wuk'ak'e cikin tsoro ta k'ara rik'e hannun Hamma Umar d'in murya na rawa tace,
"Wayyo Allah na Hamma na nashiga uku zasu kashemu".
juyowa yayi cikin karfin hali ya kalleta murya a carke yace,
"Ummu na Insha Allah zan kareki bazasu kashe min keba zan kareki keda d'anna Allah yana tare damu".
suna cikin haka suka k'araso gabansu cikin rashin imani d'aya daga cikin su yace,
"Kai meya dawo da kai?
bayan kana ganin kowa yana guduwa kai kuma yanzu muna ganin ka ka dawo munga shigowar ka cikin gidan shine muka biyoka muje meya dawo da kai?".
Allah sarki Hamma Umar cikin jarumta yace,
"Matata na dawo in d'auka".
harara suka watsa mishi cikin izzati sukace,
"ita bata da k'afane da bazata gudu ba"?.
cikin rashin karaya yace,
"Bata da lafiya ne bazata iya guduba"".
jin haka suka matso gaban su cikin rashin imani suka fizgo Hamma Umar d'in suka shak'e wuyanshi suna cewa,
"Ai gwara daka dawo kaga zamu samu mu kashe ka mu rege arna".
ita kam Ummul tunda suka fuzgo shi ta saki k'ara mai k'arfi ta matso kusa dasu cikin bushewar zuciya ta rink'a kaiwa wanda ya shak'eshin duka tana,
"ka sake shi mugaye kawai azzalumai kuku bashi raine da zakuce zaku kasheshi mugaye Hamma na ba arne bane kune arna kafuran Allah ta ala".
shiko Hamma Umar da k'afafunshi ya rink'a harbin na gabanshi da suketa dariyar mugun ta naushin su yakeyi sosai har ya kada uku daga cikin su,
ganin hakan wand'a ya shak'enshi ya sakeshi cikin zalumci ya kalli sauran yace,
"Ku kasheshi".
nan sukayi kanshi gaba d'ayan su,
Ummul kuwa kuka ta farayi da burburwa tana neman agajin Allah,
shiko Hamma Umar kamar wasa ya rink'a dambe dasu Allah cikin ukonsa sai gashi ya jikkatasu duk da taron dengin da sukayi mishi,
bai bar kare kanshi ba,
ganin haka babban nasu yace,
"ku sake shi".
ba musu suka sake shi,
hakan yasa Ummul ta taso da sauri tazo kanshi zata fad'a jikin shi sai babban nasu ya rik'eta ya bank'are hannayen ta cikin ta ya fito fili,
K'ara ta saki da k'arfi tana cewa,
"Hamma Umar".
shima Umar cikin razani ya taso yayi kanta,
dan sauri babban nasu yace,
"wato Kai jarumi mai k'arfi ko,
toh mun fasa bazamu kasheka ba,
a gaban ka zamu kashe matar taka mu fasa cikin nata mucire abinda yake ciki,
kai kuma zaka zama ganimar yak'inmu zamu musuluntar da kai kaima ka zama mayak'i d'an Boko Haram ".
yana gama fad'in haka yace kai zo ka farka cikin nata,
da sauri wanda yake bayan Hamma Umar d'in ya zaro wuk'a,
ganin haka
cikin rawan jiki da murya Hamma Umar ya sake guiwawin shi k'asa yana rawan murya yace,
"Kuji tsoron Allah ku sani Allah na ganin ku mutuwa kuma tana matakata ko wanne mai rai sai ya d'and'ane ta,
ku dena kafurtani *Ni Musulmi ne* karku kashe min mata karku cutar min da d'ana".
dariyar mugunta suka saki baki d'ayan su suna k'ara bank'are Ummul ganin haka Hamma Umar d'in ya yunk'ura da k'arfi zai jawota,
a dai-dai lokacin wanda yake bayan shi ya zaro wuk'a da nufin farka cikin Ummul,
cikin rashin imani da tsoron Allah yasa wuk'ar a wuyan Hamma Umar a gaban Ummul suka d'anneshi sukayi mishi yankan rago 😭😭😭😭😭,
Allahu Akbar Hamma Umar Allah sarki Ummul cikin wani irin firgita da gigicewa da fita hankalin ta tasaki wani irin k'ara mai firgatar da duk wani bani Adam dake wurin,
juyowa tayi da k'arfi ta rink'a dukan wanda ya rik'etan dukanshi take a haukace tana,
"Wayyo Allah na wayyo Hamma na Wayyoni Ummul naga ta kaina mugaye azzalumai Allah ya isa nima ku kasheni ku kasheni nace ku kasheni ko".
dariya sukasa a mugunce wanda take dukan ya tureta ta zauna k'asa dirsham yace,
"ai bama kashe mata sai maza".
shi kuma wanda ya yanka Hamma Umar d'in yana rik'e da kafad'un Hamma Umar d'in k'ara sa wuk'an yayi a kan wuyan nashi zai k'ara yan kawan a dai-dai lokacin kuma jiragen helkobta na sojoji dake shawag'i a fad'in garin damaturun suka gilma ta kan gidan su Hamma Umar d'in kuma sun ga halin da suke ciki ganin haka boka Haram d'in suka hankad'o matashi a kanta sannan suka juya a guje suna fita,
a gigice ta matsoshi cikin tsananin ihu da rud'ewa,
shiko Hamma Umar cikin azaba da fizge-fizge dan jinin shi dake ta zuba amman da yake basu iso mak'ok'oron maganarshi ba a hakan yasa hannu cikin wahala murya can k'asa numfashi in ya fita baya dawowa yace,
"Ummu na ki dena kuka matso matso in mutu a jikin ki Ummu na na yafe miki duk abinda kikayi min".
sai kuma ya rink'a mimmik'e k'afafunshi jikin shi duk na rawa jinin shi nata zuba,
ita kuwa Ummul matsoshin ta kumayi kanshi ta d'ago ta d'ora kan cikin ta cikin kuka tace,
"Baza ka mutuba Hamma karka mutu ka rufamin asiri".
a wahalce cikin magagin fitar rai murya na caccarkewa can k'asa yake,
"Ummu karki sha komai kibar cikina ki haifamin shi,
Ummu na kice kina sona".
K'ara ruggume shi tayi a gigice tace,
"Hamma bazan sha komai ba Hamma na ina sonka ina sonka Hamma na".
sai kuma tayi shiru jin yadda ya had'a tafin hannun ta da nashi ya damk'e da k'arfe sai kuma yayi murmushi cikin sanyi da tafiyar numfashi da kyer take jin abin da yake fad'a,
"Alhamdulillah Ummu".
sai ya kuma saketa a hankali yace,
"Am..! Amm...! Ammina Us...! U,,, Usman".
sai kuma yayi mik'a a hankali yace,
"LA'ilaha'illahu MuhammadS'A'W".
daga nan sai Ummul ta jishi yayi shiru ya sake ko ina,
nauyin shi ya k'aru fuskarshi tayi haske sai d'umin jininshi da takeji yana ratsa fatar cikin ta har zuwa cinyoyin ta,
Daga nan lokacin rayuwar Ummul ko ta shiga wani yanayi kukan da takeyi ya tsaya cak,
sai ta k'ara ruggumoshi a jikinta ta rik'eshi gam,
ta kasa kukan sai tayi zuru da idanun ta,
tana cikin haka taji motocin sojoji kai tsaye gidan suka shiga dan sojojin dake cikin jiragen ne sukayi musu umarni su shiga,
suna shiga kai tsaye gaban ta suka je,
babban sun ne ya durk'usa gabanta a hankali yace,
"Sannu baiwar Allah me sunan ki".
shiru batayi magana ba bata kalleshi ba idonta na kan wuyan Hamman ta da fuskarshi,
a karo na uku sojan yace,
"baiwar Allah kiyi magana mana musan taimakon da zamuyi miki me sunan ki? me sunan mamacin? ku yan inane ina za, a samu yan uwanku? ".
duk bata amsa mishi ba,
ganin haka yasa hannu zai jawo gawar Hamma Umar dake jikinta sai ta k'amk'ameshi da k'arfi,
abu kamar wasa da kyer suka kwaceshi a jikinta,
yana karbar shin ne I'd card 💳 d'in Hamma Umar d'in ya fad'o daga aljihun sa,
ganin I'd card d'in ne yasa ya d'agoshi ya duba cikin mamaki yace,
"Dr Umar Ibrahim Umar shine doctor Alhj Ibrahim Gaidam govnor jihar nan".
jin haka yasa da sauri ya ruggume gawar Hamma Umar d'in cikin sanyin jiki yacewa sauran,
" ku taho da ita mu tafi gidan govnr dasu".

Haka kuwa akayi kai tsaye suka wuce g Government house dasu,
ana shiga dasu kai tsaye har parlour Alhj Ibrahim gaidam suka wuce,
mutuwar da ta girgiza illahirin mutanen gidan domin ko kwana biyu baiyi ba da zuwanshi,
kuka cur-cur suka rink'ayi anan cikin gidan govnr kuwa akwai abokin Mustapha ganin Ummul yasa ya kira Mustapha ya shaida mishi,
suna nan a zaune Ummul bata gane komai tasa gawan Hamman ta a gaba bata kallon kowa,
Shi kuwa Mustapha lokacin da aka gaya mishi rasuwar yana gidan mahaifinshi dake bayan government house d'in cikin kid'ima ya d'auko Umman shi suka taho tare,
suna shiga parlour Umman Mustapha ta matso jikin Ummul a hankali ta kamota,
ita kuwa Ummul bata kalleta ba sai k'ara rik'e hannu Hamman nata tayi,
a hakan taji muryar Mustapha tabbas taji muryarsa amman bata gane me yake fad'i ba,
daga gidan govnr Alhj Ibrahim Gaidam d'in ya bada umarni a d'auki gawar Umar d'in a kaita gidan sarkin garin nasu wato Mai martaba Alhj Umar Bubaram ibin Wuriwa Bauya,
haka kuwa akayi aka kwashesu aka nufi gidan sarkin dasu inda suna zuwa aka shigar da gawar sannan aka d'auki motacin sojoji guda 5 aka had'asu da motor Mustapha wanda Umman shi ke zaune a baya tana ruggume da Ummul wacce ta zazzaro ido tun sanda aka kwace gawar a hannun ta,
a haka suka nufi patiskum bayan sun biya asibiti sun sanar nan ma Dr bashir da sauran abokansu suka mara musu baya a zaton su a can za, a sallaceshi, suna isa cikin pataskum d'in kai tsaye gidan su Abba suka nufa.



A gidan kuwa tunda gari ya waye basu da wani nitsuwa kowa jiki a mace,
har zuwa 11 na rana Adam dake konce a parlour Hajjajo cikin kasala ya mik'e ya fita ba tare da yayi mata magana ba,
itama Hajjajo tana ganin shi amman batayi mishi magana ba,
shiko Adam parlour Nenne ya lek'a inda ya samu Sadik na konce kan 3str Aliyu na zaune gefen Nenne amman su duk sunyi shiru,
koda ya l'ek'a sun ganshi ya gansu amman ba wanda yayi magana,
parlour su ya wuce yana zuwa ya samu Usman na zaune a tsakiyar parlour sai rawan sanyi yake,
da sauri ya matso gaban shi baki na rawa yace,
"Hah Usman baka tafi damaturun bane? baka da lafiya ne?".
cikin rawan sanyi da mutuwar jiki yace,
"Adam ban tafiba Adam bazan iya tuk'iba sanyi nakeji har cikin hanjina zuciyata na bugawa".
cikin fargaba yace,
"Usman baka da lafiya ne?".
kai ya rink'a juya mishi a hankali yace,
"Lafiyata lau amman bana jin dad'in yanayin yau kuma sanyi nakeji ina son inje gum Hamma na dan Allah Adam muje ka tuk'a motor muje gun Hamma".
ba musu yace,
" toh biri in d'auko hula mu tafi".
"Yauwa to kayi sauri mu tafi".
"To" yace sannan ya shiga cikin d'akin da nufin d'auko hular,

A dai-dai lokacin kuma motacin sojojin suka tsaya a k'ofar gidan,
suna tsayuwa Umman Mustapha ta kamo Ummul sukayi cikin gida,
suma sojojin sukabi bayan su amman su sai suka tsaya a harabar gidan gamida cewa Ummun Mustapha in sun shiga tace ana sallama da mai gidan,
shiko Mustapha gidan Ammin su Hamma Umar ya wuce dan yasan gidan nata.

Ummun Mustapha na tallab'e da Ummul suka shiga cikin gidan a tsakiyar gidan ta tsaya a hankali tace,
"Assalamu alaikum ".
sai kuma tayi shiru
a parlour Nenne Kuwa cikin bugawar zuciya Nenne ta amsa mata tare da cewa,
" ku iso".
Sadik Kuma da Aliyu mik'ewa sukayi da nufin zasu fita su basu wuri,
Aliyu ne a gaba yana fita Sadik na binshi a baya,
Umman Mustaphan kuwa kallon Ummul tayi a hankali tace,
"Mu shiga ko Ummul".
jin sunan Ummul ne Aliyu ya juyo da sauri,
sai kuma ya zaro ido cikin rawan jiki ganin gaba d'aya rigar jikin Ummul d'in tana jik'e jilak da jini ,
a razane yayi wani irin k'ara,
sai gashi ya fad'a k'asa a sume,
k'aran da Aliyu yayi ne yaja hankalin mutanen gidan baki d'aya a guje suka firfito,
Abba na fitowa ya kalli Aliyu a sume sannan yaga Ummul a tsaye jini na d'iga shima sai ya fad'i k'asa a sume,
Adam kuwa yana fitowa Abban yaje ya kamoshi dan shi baima lura da Ummul d'in ba,
Nenne Kuwa gaba

Please Login or Register in order to submit comment