Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'aya jikin ta rawa yake kar-kar kamar mazari sai zufa ke zubo mata,
Ya Sadik kuwa tsayuwa yayi tamkar an dasashi,
ita kuwa Ummul sai yanzu ta d'ago kanta ta kalli ya Sadik d'in nata a hankali tayi taku taje gaban shi tana zuwa ta fad'a jikin shi,
Sadik daya gama sakewa shima sai zamewa yayi ya zauna k'asa dirsham yana tallabe da ita,
ita kuwa Ummul kifuwa tayi jikin ya Sadik din tana jizon lips d'inta da zuwa yanzu sun kuburo sintim sintim,
cikin karfin hali Nenne tace,
"Baiwar Allah make faruwa ina Umar?".
shiru Umman tayi sannan ta kamo hannun Nenne suka zauna a kan kujerun dake wurin sannan ta kalli Sadik a hankali tace,
"Sadik kawo Ummul nan".
kai ya juya cikin kuka yace,
"bazan iya ba".
kukan Sadik yasa Nenne ma ta kife Kai ta fara kuka Adam ma kukan ya fara cikin tashin hankali yace,
"Dan Allah ki gaya mana meke faruwa Ummul ina Hamma Umar ?".
cikin sanyi Umman Mustapha tace,
"Kullu nafsin za'ikatil maut".
sannan ta dafa kafad'un Nenne taci gaba da cewa,
"Lallai Umar namune amman Allah ne ya bamushi kuma ya fimu sonshi yau kuma ya kira Umar,
Umar ya amsa kiran mahaliccin mu".
gaba d'aya a tare suka mik'e cikin razani da kad'uwa,
Usman kuma dake tsaye gefen Adam,
kai ya rink'a juyawa da k'arfi sai kuma ya kalli Ummul dake jik'e da jini gabanta yaje ya durk'usa cikin razani yace,
"Ummul gaya min inji a bakinki shi zaisa na yarda Ummul jinin waye a jikin ki?
Ummul gaya min ina kika barmi d'an Uwana Ummul wannan jinin waye a jikin ki? ".
Ba magana sai zamowa tayi daga jikin Ya Sadik ta fad'a jikin Usman d'in a hankali tasa hannu ta shafo jinin a hankali ta gyada mishi kai,

cikin wani irin yanayi Usman ya mik'e tsaye sai kuma ya,........



*By*
*GARKUWAR FULANI*
[11/18, 9:44 AM] El-hajj🀣: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 3⃣0⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



*Wannan littafi nawa gaba d'ayan shi sadaukarwane wa Hamma Umar, Dr Umar Ibrahim Umar shuwa Allah ya jik'anka da rahama😭😭😭*


*Alhamdulillah Da forko zanyi amfani da wannan damar na mik'a sak'on godiya ta a gareku yan uwana Musulmai bayan na godewa mahaliccina tabbas lallai musulmi dan uwan musulmi ne kuma akwai soyayya da tausayin juna da k'auna a tsakanin mu musulmai hak'ik'a naga hakan kuma lallai in abu mara dadi ya samu dayanmu kamar ya samemu ne baki d'aya kamar yadda mutuwar Hamma Umar ta ratsa zuk'atanmu baki d'aya nida kaina Aysha ban san adadin addu'oin da bawan Allah nan ya samuba a cikin kwana biyun nan fatana Allah ya amsa addu'oinku gareshi Usman Ammi da Ummul suna godiya a gareku Ummul kuma tana neman addu'arku dan tun shekaran jiya bata da lafiya saka makon abun da ya zame mata sabo Ummu na Allah ya baki lfy🀝😍😘*



*Abu na biyu ina baiwa masoya na hak'uri daga jiya da daddare zasuga suna magana bana amsa musu to na canza number ne sakamon yawan da Jama,a sukamin duk ta inda na lek'a kafafen yanar gizo-gizo sai naga sak'on ni bila adadin hakan yasa dole na canza number dan samun sauk'i toh dan Allah duk wacce taga tayi mgn ba amsa toh na canza number ne ngd matuka Allah bar zumunci da k'auna sisters bada ku na gajiba da bada amsa na gaji amman ku kam ana mugun tare domin kun zamani na zamma ku na godewa Allah daya bani ku masoyana tabbas jama'a rahamace Allah ne yamin wannan rahamar kuma ngdwa Allah na Alhamdulillah*






*Y*a rink'a juya kai yana b'ari kar-kar kamar mai farfad'iya wani irin zufa ya keto mai daga tsakiyar kanshi har kan d'an babbar yatsar k'afarshi hatta cikin gashin kanshi sai d'igowa yake tol-tol,
Hajjajo kuwa wacce tun ihun da Aliyu yayi ta fito amman ganin Abba a sume Aliyu a sume ga Ummul jiki duk jini,
a take sai jijiyoyin ta suka sassake k'afafun ta suka kasa rik'e ta jiri ya rufeta cikin tashin hankali ta fad'i k'asa dirsham hawaye na bin fuskarta ta kasa tashi sai yanzu ta mik'e da kyar ganin halin da Usman ya shiga,
tana xuwa ta kamo hannun shi tana k'ok'arin zaunar dashi amman ina sai taji jikin shi kamar an dasashi ganin haka cikin muryar kuka tace,
"Usmanu! Usmanu! Usmanu ! ka ambaci Allah shi zai kawo mana agaji Usmanu kar kabar zuciyarka ta mance da Allah Usmanu wannan shine jarrabawarmu a wannan shekara a wannan wata a wannan rana muyi rashi mai girma ban sani ba waya kashe mana Umar".
sai kuma ta k'ara rik'o hannun Usman d'in sannan cikin kuka ta kalli Adam dake yayyafawa Abba da Aliyu ruwa,
a firgice Aliyu ya farfad'o cikin k'ara tare da rarumo Sadik dake gefen shi,
karan da Aliyu yayi ne yayi dai-dai da farfad'owar Abba a razane ya mik'e dai-dai lokacin kuma sojojin dake harabar gidan suka shigo dan jin k'aran da Aliyu keyi,
suna shiga Usman suka kama suka rik'e sabida ganin yadda yake tsaye,
zau nar dashi suke k'ok'arin ya,
cikin hard'ewar harce ya janye hannayen shi gaban Abba yaje ya tsaya hannun Abba ya kamo ya rik'e harce a nad'e maganarsa bata fita sosai kuma yadda bugun zuciyarshi tayi k'asa haka muryarshi numfashi a cushe ya nuna Ummul dake zaune ta zama mutum mutumi sai ida nun ta da sukayi jazir tamkar rushi sai lips nata da suka kumbura,
a hankali yace,
"A..! Ab...! Abb!...
Abba wai jinin Hamma nane a jikin Ummul Abba kace ta gaya ma inda ta barmin d'an uwana Abba kalli matar nan wai cewa take d'an Uwana ya resu Abba wai Hamma fa suke cewa ya rasu".
kife kai Abba yayi tamkar yaro ya rink'a kuka yana durk'ushe a gaban mahaifiyarshi,
Aliyu kuwa kuka yakeyi da shid'ewa Nenne ma kuka takeyi da tsananin k'una ya Sadik kuwa kanshi ya rink'a murzawa yana kuka cur-cur Adam kuwa ruggumo Usman yayi yana kuka tankar ranshi zai fita,
Umman Mustapha ma tuni kukan take,
ganin haka sojojin suka kama Abba suma kansu kuka suke dan tausayawa rayuwar wannan family,
cikin hikima sukayi wa Abba bayani,
suka k'ara da cewa,
"yanzu haka gawarshi tana gidan sarki ya kamata kuje ayi mishi sutura".
Abba jikin shi sai rawa yake cikin kuka yace ,
"Mu tafi".
juyawa sukayi har zasu fita Adam yaga yadda Usman yake tafiya numbfashin sa na yankewa ganin haka ya kamoshi da sauri a cikin kuka yace,
"Usman ka zauna a gida Abba kace Usman karya je".
Abba ya bud'i baki zaiyi Magna kenan Usman d'in ya d'ago ida nunshi da suka koma tamkar zasuyi aman wuta murya a nad'e yace,
"Gun Hamma na kuke cewa kar naje idan banje gunshi ba ina zan shiga a duniyar nan wai yau ni kuke cewa kar naje gun d'an Uwana idan banjeba me zanyi".
daga jin Maganar Usman an san baya hayyacin sa,
haka yasa Adam ya rik'eshi suka shiga motocin sannan sojojin suyi gaba suko suka bisu a baya dan an hana zirga-zirga a garin suma dan da sojojin ne,
Mustapha kuwa kai tsaye gida su Ammi ya nufa dan yasan gidan sun tab'a zuwa shida Hamma Umar d'in.

Ammi kuwa tunda garin wannan ranar ya waye ta kasa yin komai gaba d'aya jikin ta a mace yake,
a haka ta jawo radio ta kunna wanda yayi dai-dai da saka harbe-harben da yan BH sukayi a garin na damaturu sannan mai bayanin yaci gaba da fad'in uguwannin da suka fara shiga da kuma irin b'arnanr da sukayi,
jin an kira uguwarsu Hamma Umar ba k'aramin tashin hankali da firgici ya sawa Ammi ba a take taji wani irin sanyi yana ratsata har cikin hanjin cikinta tsoro mai tsanani ya rufeta ido cike da k'ollah tib ta kalli mahaigiyarta cikin muryar kuka tace,
"Inna ta uguwar su Farouq suka fara shiga Inna kinji sunfa kakkashe mutane".
Itama Inna gaba d'aya jikin ta rawa yake cikin hargitsi tace,
"Kira min wayar Umarun kira minshi maza Amina".
jiki na rawa tayi ta kiran Hamma Umar d'in amman tuni abinda Ammi bata saniba an kashe mata d'anta,
ganin Umar baya d'aga woyar sai kukanta ya k'aru sai kuma ta rink'a kiran Usman ina shima baya d'agawa hakan yasa hankalin ta ya tashi ta rink'a kiran mutanen gidan Abban amman duk basa d'agawa haka yasa ta koma ta zauna dirsham kan taburma a gaban Innarta d'in ta zauna kenan,
Mustapha yayi sallama,
shi kuwa Mustapha ganin tana kuka sai yayi zaton taji batun rasuwar Umar d'in sai ya tsuguna gefenta cikin kuka kamar yaro yace,
"Ammi kiyi hak'uri hak'ik'a munyi rashi mai zafi amman Hamma Umar yafi but'atar addu'armu a kan kuka Addu'a zakiyi mishin Insha Allah muna zatama mai rahama Allah ya karb'i shahadarsa".
Ita kam Ammi tunda taga Mustapha jikin ta ya rink'a b'ari kar-kar ta kasa tashi amman jin ya ambaci Hamma Umar yasa ta mik'e da sauri cikin razani a kid'ime zanin ta ta rink'a d'aurawa tana kuncewa tana sake d'aurawa sai karkarwa takeyi ganin haka cikin kuka Inna ta kamota ta rik'e tana cewa,
"Innalillahi WA innailaihi rajiun".
haka ta rink'a maimatawa har akayi sa'a itama Ammi cikin kukan daya kufce mata ta rink'a cewa,
"LA haulawala k'uwta illabillahi aliyul azim hasbunallahuwani'imam wakil Allahu Akbar Allah Akbar innalillahiwa Inna ilaihirajiun Allah mai girma yau kuma da k'unar dana wayi gari kenan Mustapha yau kuma Boko Haram sun yanke min naman jikina kenan Mustapha ina Usman Mustapha Usman yana cikin wanne irin hali?".
sai kuma ta kife kanta kan ciyar Innarta ta saki wani irin kuka mai cike da k'unci a zuciya,
itama Inna sai kuka shima Mustapha ya kasa barin kukan,
a haka Uncle ya shigo ya samesu wanda dama Abba ne ya kirashi ya gaya mishi,
abin tausayi shima Uncle sai yasa yar uwarshi a gaba suna kuka tamkar yara Ammi kam kuka take har numfashin ta na tafiya,
a hakan Uncle ya daukosu ya kawosu gidan Abban sannan shida Mustapha kuma da sauran abokan Hamma Umar dana ya Usman da abokan Adam Sadik da abokan Abba duk suka d'ugguma damaturun,
suko Inna da Ammi suka wuce cikin gidan.


A damaturu kuwa suna isa suka samu ana shirin yiwa mamacin wonka suna shiga Usman ya wuce kai tsaye inda yaga an mik'e gawar a shimfid'e ta a k'asa Adam ma da Abba da Sadik da Aliyu gaba d'aya sai sukasa gawar a tsakiyan su,
shiko Usman hannu yasa ya d'ago gawar fuskar ya tsurawa ido cikin wani irin yanayi mafi rauni da muni ya rink'a kallon wuyanshi da aka yanka, ruggume gawar yayi da k'arfi,
a hankali ya rink'a juya kanshi yana wani irin numfashi Adam kuwa kuka yake kukan tausayin Usman Sadik ma kukan yake Aliyu Kuwa a k'asa ya kife kanshi yana kuka,
Shiko Usman cikin hard'ewar murya da juya kai yace,
"Sun cuceni sun cuci rayuwata sun rabani da mutun mafi soyuwa a gareni ina ma ina wurin in fanshi ran Hamma na da nawa ran Ammi sun cuceki sun kashe miki lafiyayyen d'anki suka bar miki ni wanda zama danima larurace".
sai kuma ya kalli Abba cikin wani yanayi da yafi kama da wanda baya hayyacin sa yace,
"Ashe duk hirar da nike da Hamma na watsiyace ashe yana barmin abinda har in mutu bazan manta bane Abba Adam Sadik Aliyu ko jiya da dere Hamma na yace ince ku gafarceshi fad'an da yayi a kan Ummul".
sai kuma ya ruggume gawar ya fara magana kamar zai bashi amsa cikin bushewar zuciya yace,
"Hamma na ba jiya nake cema in na mutu zaka zama gatana na ko?".
sai ya kuma kallin fuskar Hamman nashi yace,
"Hamma na ka tuna kace min zaka zama gatana bazaka zubdamin hawaye ba zaka min wonka kamin sutura sannan zaka dauwama dimun wa da'imun kana min addu'a har sai randa kabar numfashi,
to Hamma na Insha Allah zanyi maka wannan gatan har zuwa lokacin da nima zan biyo bayan ka".
sai kuma ya kalli Adam yace,
"Adam taya ni in yiwa Hamma na wonkan k'arshe a duniya".
Adam yana kuka da majina suka kamo gawar suka matso inda aka tanadi abubuwan buk'ata dan yin wonkan gawar,
Abba kam da Sadik zama sukayi suna ganin duk ta inda aka juya kan Hamma Umar sai yayi lagwas shiko Aliyu kuwa kuka yake da zafin rabuwa da d'an uwa,
shiko Usman nad'e k'afafun wondonshi yayi cikin bushewar zuciya ya rink'a wonke wuyan nashi da sauran wuraren da jinin ya taba sannan yayi mishi wonka yadda addinin musulunci ya tanadar,
bayan sun gama ya shiryashi tsab cikin likkafanin shi aka kawo makara motor da babu taya motar da ta zame mana dole shigarta bayan an sashi a cikine aka fitar dashi akayi mishi sallah bisa koyarwar annabi sannan aka d'auki Hamma Umar aka nufi gidanshi na gaskiya da shi,
inda Usman da Adam su suka sashi a makoncin sa,
Allah Akbar ko wanne d'an adam k'arshen sa kenan,
an gama binne shi ne ya Usman ya d'aga hannu yayi ta karanto addu'oi bayan sun gama ne aka fara juya baya ana tafiya,
a dai-dai lokacin ne Usman yaji wani irin suka da zogi a kahon zuciyarshi wanda ya fara ganin duniyar tana juya mai,
da kyar yake d'aga k'afafun shi har suka fita cikin mak'abartan suka shishishiga motocin su suka nufi Potiskum.


A gida kuwa Ammi da Inna suna shiga suka samu Anty Halima da matar Daddy da sauran yan uwansu duk sun taru suna zaune a barandar Nenne,
Ammi na shiga Nenne ta ruggumota suka had'a kai wuri d'aya suna wani irin kuka,
Halima kuwa da Anty Shuwa gefen Ummul suke zaune wacce tunda tazo batayi magana ba sai idonta da yake a zazzare,
cikin kuka Halima tace,
"Allah sarki Ammi wayyo ya Usman Ummul tashi ki cire rigar nan Ummu kar kiyi Ammi taga wannan jinin zai iya kawar mata da hankalin ta".
shiru bata kula Halima ba sai kallon Nenne da Ammi take Hajjajo da Inna ma kuka suke kamar zasu shid'e,
Ammi kuwa da Nenne sunyi kuka har idanu su sun rufe,
sai can Ammin ta kalli Ummul dake gefensu tana ta zaro ido tamkar idanun zasu firfito,
a hankali Ammin ta kalli Ummul d'in da k'aton cikin ta wanda jikin ta duk Jini,
kife kai tayi ta kuma sakin kuka,
amman Ummul sai kallonta takeyi kamar bata santaba ganin haka cikin kuka Ammin tace,
"Nenne kuka rahama ne kuka wani sauk'ine a garemu kusa min Ummul tayi kuka inba haka ba zai zauna a zuciyarta ku samin yarinyar nan tayi Kuka Ummul ki zubda k'ollah".
amman ina Ummul Allah bai bata damar kukaba,
har Allah yasa su Abba da Usman dasu Adam Sadik da Aliyu suka dawo,
suna shigo wo gidan Usman yazo ya kife kanshi a jikin Ammin shi yana magagi harce a nad'e yace,
"Ammi sun kashe miki lafiyayye sun bar miki nakasheshshe wanda rayuwarsa bata da tabbas Ammi zan kai kararsu".
cikin kuka ta ruggumeshi tace,
"Usman ya zamuyi da *RUBUTACCEN AL, AMARI* wanda Allah ya tsara mana Usman ina zaka kai kararsu waya gansu".
harce na k'ara nad'ewa yace,
"Allah Ammi Allah ya gansu kuma zan kai k'ararsu gun adalin sarki Allah zan had'asu da Allah ya bimin hak'kin jinin yan uwana musulmai Allah zaiyi mana hisabi dasu zubarmin da jinin Hamma na da sukayi Ammi babu kotu ko lauya ko alkali da zaiyi wannan shariyar sai Allah dan haka zan dawwama ina kai kararsu gun Allah zasuga saka makon aiyu kansu a ranar da gabbansu zasuyi bayanin rayukan da suka kashe Allah ya isar mana ana cutar damu musulmai a k'asarnan ana kashemu tankar kiyashi Allah ya isa! Allah ya isa! Allah ya isa jinin d'an uwana".
gaba d'aya sai gidan ya kuma cika da tasbihai dan samun sanyin zuk'atansu ita kuwa Ummul sai binsu take da kallo,
Aliyu ne wanda tunda suka shigo yake kuka sai yanzu Sadik ya kamo hannunshi suka k'araso cikin gidan suna shiga Aliyun ya fad'a jikin Ummul d'in yana kuka mai tarin k'una shi kuwa Sadik cikin rawan murya yace,
"Ammi mun kai Hamma Umar gidanshi yanzu addu'arki yafi buk'ata".
daga wannan kalmar Ummul bata kuma sanin inda takeba ko a wanne halin takeba,
ta sume cit suma mafi munu domin harda k'ok'olwarta tayi sanyi,
daga nan aka kwasheta akayi asibiti da ita Dr Bashir shike duba lfyar ta,
yayin da Usman Kuwa yake ganin suma hutune a wannan halin da yake ciki ba kuka ba suma sai tarin k'unan zuciya ga fargabar halin da Ummul take ciki.


Har tsawon kwana uku Ummu bata farfad'o ba hakan yasa yan uwa cikin wani sabon tashin hankali ganin haka Dr Bashir ya bada shawaran a fiddata woje,
haka kuwa akayi cikin kwanaki aka shirya fita da ita k'ark'ashin d'aukar nauyin gwamnatin jihar tasu aka fidda ita,
Egypt inda aka kai tsaye suka wuce Magrib Medical Center Cairo,
ita da Ammin Hamma Umar sai ya Adam tare da jagorancin Dr Bashir,
koda suka je Ummul saida tayi kwana 8 a sume sannan ta farfad'o koda ta farfad'o d'in kuma bata magana sai kallon mutane kawai,
duk bincike anyi da magani amman ba magana a haka aka sallamesu dan doctors sunce a koda yaushe zata iya magana,
an sallamesu da sharadin watan haihuwar ta na tsayuwa su dawo dan bugun zuciyarta yayi k'asa sosai bazata iya haihuwa da kantan ba,
a haka suka dawo gida dan hankalin mutanen gida ya konta.


randa Hamma Umar ya cika sati uku da rasuwa a ranar suka dawo,
suna dawowa koma yazo yanawa Ummul magana amman ba amsa,
bata ko d'ago kanta ta kalli kowa sai in Ammi ce tayi magana,
haka gaba d'aya farin cikin su ya koma ciki.

A daren ranar ne bayan duk an shiga an konta Ammi na zaune da Usman a gefen Ummul da ta konta tana kallon su ba magana,
Usman ne ya kalli Ammin cikin rauni yace,
"Ammi cikin kam baida matsala ko? ".
Ammin ta bud'e baki kenan zatayi magana Ummul tayi wani irin gigitaccen......




*By*
*GARKUWAR FULANI*
[11/18, 9:44 AM] El-hajj🀣: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 3⃣1⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*MOH ALLAH WUJI FURD'ATA*

*DEDDE Na Ummu uwata ta kaina mahaifiyata abin k'aunata abin Al'faharina yau kuma kirarinki da kikemin na yarintata na tuno lallai bani da tamkarku kida Abba na domin a yau Kirarin da kikemin zai iya kasan cewa a horkon ko wani shafina na littafaina inada kike cemin*

*KIN KINI KAN KAD'A DAMONI NA DAMONI GID'D'O MO FINA LARA GAID'O MO FINA SUKOYO LADDE ALLAH YAMAD'UM! KI D'OIDI YALETE! KI B'IB'B'E SAMMMETE! B'ENDUKI YAMETE! YORIKI TENETE! DAMONI NA DAMONI GID'D'O MO FINA LARAMO GAID'OMO FINA SUKOYO LADDE ALLAH YAMAD'UM ALLAH WANNE BARKA BOD'D'I DEDDE Allah fintine ba seto arana*
*wata kalmar sai a bakin Fulani*
*Wani Abu sai Uwa da Uba wannan kirarin duk ni kadai Aisha Aliyu garkuwa mahaifiyata da mahaifina kemin da sanya min albarka tun ina karama har zuwa yau Ya Allah ka sakawa iyayena da mafi kyawun sakamako ya Allah ka yiwa iyayena jagoranci har cikin jannatul firdausi DEDDE NA DA ABBAN ina sonku fiye da kowo har kaina Allah ya barmin ku😍😘😍😘*

*T*ayi wani irin firgitaccen zabura cikin tsananin
razana ta yunkura da karfi zata tashi tana wani irin gurnani,
ganin haka cikin karfin hali da firgici Ammi da ya Usman sukai saurin rik'ota suna mata addu'a,
ita kuwa gaba d'aya jikinta rawa yake kar-kar hatta d'an cikin ta sai motsi yake da k'arfi ta zazzaro ido tana waige-waige kamar me neman wani abu,
dakyar ya Usman ya kamo kanta da hannu biyu ya kwantar da ita a kan cinyar shi dan yadda take fisge-fisge Ammi bazata iya control enta ba,
ita kuwa Ammin sai shafa bayanta takeyi a hankali kwalla cike a idon ta tana furta, "hasbunallahu wa ni'imal wakil".
Shiko ya Usman yana ruggume da ita a jikin shi gaba d'aya jikin nashi sai kerma yake a karo na forko da yaji rauni da tausayin kanshi da kanshi ga tau

πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 3⃣2⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡





*MOH ALLAH WUJI FURD'ATA*

*Kin kid'i kankad'a damoni na damoni giddo mo fina laramo gaid'omo fina sukoyo ladde Allah yamad'u benduki yamete ki b'ib'b'e sammete joruki tenete ki d'oidi yalete*




*U*sman ya d'ago jajayen idanuwan shi yazuba matasu sannan ya mik'e yana layi yaje bakin gadon ya sa hannuwanshi biyu a d'auko Umar faruq ya rungume sosai a jikin shi yana zubda hawaye mai tsanani da zafi da k'una a zuciya yana shafa kan yaron dake cike da suma bak'ik'k'irin daya kwanta luf,
ita kuwa Ummul cikin kuka taci gaba da cewa,
"Hamma Umar ne rayuwa ta nafi sonshi a kan kowa a duniya, shikad'ai nakeso shine komai nawa na rasa a lokacin da nake tsananin buk'atarshi".
Tana magana ne cikin matsanan cin kuka, bakajin komai a gun sai shashshek'ar kuka da duk wanda kegun yakeyi,
shiko Usman yana k'ollah ne idanuwan shi na kan Umar faruq yana mai wani irin kallo kamar a lokacin yafara ganin halittar jariri,
Itakuwa Ummul cikin kuka taci gaba da cewa,
"Ammi wallahi ina sonshi,
bazan k'ara son wani mutum a duniyar nan bayan Hammana,
ina kaunar shi fiye da kaina Inamai matsanan cin so da duk duniya bamai iya fahimta".
sei ta kuma jan gwiwoyinta data zuba k'asa har gaban Ya Adam dake ta faman zubda k'ollah tace, "Yaya na kafi kowa yimin fad'a bakamin wasa amman na kasa ganewa,
kuma baka son damuwa ta, nasan kayi iya k'ok'arinka ka d'orani ka turbar gaskiya,
amman taurin kaina da rud'un shaid'an yasa nak'i gane abinda nasan gaskiya ne gashi hakan ya jazamin nadama ta har abadan na cutar da kaina da kaina naga illar rashin yiwa iyaye biyeyya, nagode dakaita k'ok'arin nunamin hanyar gaskiya".
Hannu yasa ya kama hanna yenta duka biyu ya d'an matsesu sannan yace,
"Ummul nasan kina son shi naga sonshi a idonki amma

Please Login or Register in order to submit comment