Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

filon da yake kai a hankali yafurta, "Shhhhmm Ummuna Insha Allah sana iyshu ma'aki ma'a habbah=insha Allah zan rayu dake tare da soyayya".
jin haka yasa tafara sauke numfa shi tana murmushi tana kuma hura mai iska a kunnenshi a haka yafara bacci ita kuwa taci gaba,
"Kayi bacci cikin nutsuwa hannuna na riƙe da naka kanka yana cinyata hannuna ɗaya na yawo a cikin suman kayin ka zuwa kunnen ka, ina son kayi bacci kar ya saka ciwon kai".
Shirun dataji dakuma jiyo saukar numfashin shi a hankali yasa ta kira shi ta tabbatar da yayi bacci dan jin bai amsa kiran da tayi mai ɗinba,
haka yasa ta katse wayar ta konta cike da tunani har bacci ya d'auketa.


Gari na k'arasa wayewa Ammi tazo ta tasheta dan tayi break saida tayi wonka tai kwalliya sannan taje tagaida Nanne,
bayan sun gaisa tace,
"Ga abincin Usman can ki ɗauka ki kai mishi".
Amsawa tayi sannan tajuya ta je ta had'a mai komai akan tire ta ɗauka ta fita hannun ta riƙe da hannun Faruq.


A ɓangaren Usman ma yana tashi yashige yayi wanka ya shirya tsaf ya feshe jikin shi da turaren hugo mai ƙamshi yana fitowa palour kunnuwan shi suka jiyemai abinda yafi son ji,
Sallamar da tayi ya amsa sannan ya buɗe hannuwan shi ya ɗan tsuguno da fara a fuskar shi yace,
"come on Daddy boy".
da gudu Farouq yaje ya faɗa jikin shi shima yamaida hannun shi ya rufe sannan ya ɗagashi sama yana kissing ɗinshi tako ina cikin ƙauna shima yayi kiss ɗin shi a kumatun shi cikin gwaranci shi yace,
"Ana Ubbuka Abee". Dariya yayi yana saukeshi ƙasa yasa hannu yana lakace mai hanci yace,
"Ana hubbuka ya bunayya".
Wucesu yayi yaje ya haye kujera yaɗau remote d'in tv yafara wasa.
Shi kuwa dawo da kallon shi yayi kan Ummul dake kokarin ajiye tiren a tsakar palour ya zuba mata manyan idanun shi, tana ajiyewa tasami guri a ƙasan a tsakiyar carpet tazauna sannan ta kalleshi ta ɗanyi murmushi yadda taga ya ƙure ta da ido dakai tamai alamar yazo ya zauna,
aiko kamar rakumi da akala yataho da hannu ta nunamai inda zai zauna,
saida tasa hannu taɗau flate tafara zubamai abincin sannan ta ɗan kalleshi cikin sanyin murya tace,
"katashi lafiya?".
Shima lumshe idanu yayi sannan ya buɗesu ya namata wani irin kallo murya can ƙasa yace, "Inafa lafiya Ummu na bayan a baccin ma zuwa kikayi,
kikayita jagolgoleni duk kin turmusheni kin sani cikin wani yana yin".
ya ƙarishe maganar yana kashe mata ido ɗaya da ɗan ɗaga mata girar sa,
kunya sosai maganar shin ta sakar mata sunkuyar dakai tayi ta ajemai abincin da tea data haɗa mai a gaban shi tace,
"Kacinye duka sai in baka kyauta".
Ɗan ɗago kai yayi yace,
"kefa?". kai kawai ta girgizamai alamar a a,
kallon ta yayi cikin tsigar so da ƙauna yasa hannu ya ɗauko ɗaya cup ɗin ya haɗa tea mai kauri sannan ya ɗan kurb'a cup ɗin ya miƙa mata a hankali yafurta,
"Ki shanye ba zafi sosai".
karɓa tayi tana kallon idon shi shiko lips d'inta da suka sha jambaki sai shek'i suke ya kurawa ido a hankali yace,
"Wannan janbakin dada hali zan tsotse shi dan ya rufemin pink lips d'inkin nan masu kyawun gani".
Baki ta ɗan tsuke tana ɗan yimishi kallon ƙasa-ƙasa bai jira tayi magana ba yace,
"l'ilam uhibbuki hubban azeem=kisani ina sonki so na hak'ik'a, bansan wanne irin murna zan yiba idan aka ɗaura mana aure,
bansan wsnne iri so nake mikiba Ummu na, Anti faƙat fee hayatee=kekad'aice a rayuwata".
Ɗan ɗago kai tayi tace,
"Kamar cewa nayi kaci abinci ko?
sannan ka tsaya surutu nikuma nafiso inga ka kaci abincin sannan kasha maganin ka".
Karya wuya ya ɗanyi cikin wani sabon salon shauƙi yace,
"Aaahhhh hubby zanci amma kinga wannan kallon? hmmmm". sai kuma ya haɗiye maganar da yayi niyar furtawan
sannan yaja flate d'in yafara cin abincin cikin nutsuwa,
Farouq daketa tsalle kan kujera ne ya sub'uce kamar zai fad'o dasauri suka tashi dukkan su sukayi gunshi hannu kowanne yakai dan riƙoshi aiko hannunsu ya haɗe wuri guda gun ɗaukan Farouq ɗin,
Shiko Usman haɗe hannun ta dana Farouq ɗin yayi ya riƙe ya na murzawa a hankali itako ƙasa tayi da kanta,
sun daɗe a haka sannnan suka koma suka zauna ya k'arasa cin abincin,
itako ta tattare kayan ta ɗauka suka fita tare,
suna fita suka haggo Dr. Bashir yafito daga motar shi,
Cikin gida Ummul ta shige b'angaren Nanne shikuma Usman ya k'arasa gurinshi riƙe da hannun Farouq,
suka gaisa ya tsuguna yakamo hannun Farouq ya ɗaukeshi,
Usman ne yamai jagora har palour baƙi yazauna yana wasa da Farouq shikuma ya juyo yafito yana fitowa yaci karo da Abba na shirin shiga palour ɗan russunawa yayi yace, "sannu da fitowa Abba".
Kallon shi yayi yace,
"Dr na ciki ko?".
"eh".
yace sannan yasake cewa,
"To ka jirani a palour Hajjajo zamuje gidan Daddy inna fito".
da "to". ya amsa yawuce parlorn Hajjajon.

Shiko Abba da sallama ya shiga palour suka gaisa cikin girmamawa, a hankali Abba yawa Dr Bashir bayani sannan yabashi hakuri akan abinda ya faru dakuma nuna mai jin dad'in shi akan yadda ya nuna soyayyar shi ga Ummul dakuma burin kulawa da Farouq,
shiko Dr har zuciyarshi yaji daɗin yadda Abban yamai bayanin yakuma yi addu'ar al'khairi har zuciyar shi yakejin ya haƙura da ita kuma zaici gaba da kulawa da ɗansu Farouq, dahaka sukayi sallama ya fita ya tafi.



Inda yayi parking motar shi anan Mustapha yayi parking kusa dashi yana fito suka gaisa cikin mutunci sannan shi Dr ya tafi,
shiko Mustapha ya nufi cikin gidan,
Aliyu ne ya tarbi Mustapha sannan ya kaishi palour ya zauna shikuma yashiga dan sanarwa auntyn shi Ummul zuwan shi.

Gabanta na faɗuwa kanta a ƙasa ta shiga palour tasami guri tazauna cikin nutsuwa dajin kunya ta gaidashi kallonta yake kamar ya ɗauketa ya tafi da ita dan so da ƙauna,
cikin wani irin salo murya a raunane yace, "Andawo lafiya?
ya ibada Allah yasa karb'ab'b'yace".
"Alhamdulillah, Amin". tace sannan suka ɗanyi shiru na wani lokaci da kyar tabuɗe baki tace,
"Ya Mustapha daman inaso zamuyi magana sannan ina fatan zaka fahim ceni?".
Gyara zama yayi yace, "Haba khairi kinsan ina gane duk abinda yafito daga bakinki kuma ina yarda da shi kuma kin san maganar ki abar fahimtace a gareni,
fad'i maganarki".
sake sunkuyar da kanta tayi tafara magana a hankali,
"Dafarko zan maka godiya da irin kulawar da kake bamu kuma naji dad'in hakan sosai bani da abin cewa sai dai ince da kai jazzakallahu bil jannatul firdausi,
abu na biyu kuma inaso in baka hakuri akan maganar da kayimin kafin nayi tafiya".
Tuni zuciyar shi tafara bugawa da ƙarfi sai sake ƙureta da idanu yayi,
Ita ko kai a sunkuye taci gaba da cewa,
"Haƙiƙa kai cikakken masoyine kuma mai soyayya dan Allah sannan mai ɗaukan ƙaddara da yarda da ita a duk yadda tazo maka dan naga hakan a baya kai namiji kayi biyeyya ga iyayen ka ka ruggumi ƙaddararmu abin da ni mace ya kamata nayi shi amman taurin kai da zugar shaiɗan sun hanani ruggumar ƙaddara ta nayi ta cutar da masoyi na gashi yanzu rayuwata zata ƙare cikin nadama da dana sanin rashin bin umarnin iyaye kai kuwa na tabbata zaka samu farin ciki a rayuwarka tunda kayi biyeyya ga zaɓin iyayenka,
Ya Mustapha inaso in faɗamaka na amince da auren ya Usman saboda dalilai da dama amma nasan zaka fahim ceni kuma ka kasance mai yimin addu'a a koda yaushe".
shiru ta ɗanyi har zuwa wani ɗan lokacin muryarta ta fara sarƙewa cikin zubda ƙollah murya na rawa tace,
"Zan auri ya Usman ko dan na sa farin ciki a zuciyoyin iyayena,
zan auri ya Usman cikin aminci ko dan na goge laifin da nayiwa iyayena a baya na ƙin yarda da zaɓin su,
zan auri ya Usman ko dan na reba Farouq da agolanci na kuma kasance tare dashi dan duk inda nayi aure ya Usman zai karɓe min Farouq,
zan auri ya Usman dan zaiyi farin ciki farin cikin ya Usman kuwa shine abu mafi soyuwa a zuciyar Hamma na,
zan auri ya Usman ko dan na kula dashi da lafiyarshi wanda kullum shine fargabar Hamma na,
zan auri ya Usman ko dan ƙaunar da Ammi take min,
zan auri ya Usman dan mu rayu tare mu cirewa Farouq maraicin mahaifin shi,
zan auri ya Usman ko Allah zaisa Hamma na yayi farin ciki dani,
zan auri ya Usman don Allah da zuciya ɗaya,
Mustapha na cutar da Hamma na akan soyeyyar ka amman Hamma bai taɓa fushi dani ba bare yayi fushi da kai Mustapha yanzu bana son kowa a duniya sai Hamma na ya Mustapha inama-inama Hamma na zai dawo gareni inama tafiya yayi ta dawowa inama ace ni suka yanka suka barshi a raye na tabbata da shi zaimin wonkan gawa da shi zai sani cikin ƙabarina ya Mustapha a gabana suka yanka Hamma na yankan rago ya Mustapha Hamma na ya sadaukar da rayuwarshi a kan tawa ya Mustapha wallahi wallahi tallahi ina son Hamma Umar ina sonshi ina sonshi,
kaito na ni Ummu tabbas naga illar rashin yiwa iyaye biyeyya kaitona da zuciya ta kaitona da taurin kaina kaito na da ƙin yarɗa da ƙaddara ta a haka zan ƙare rayuwata cikin dana sani da nadama ashe maganar da Hamma na ke cemin gaskiya ce yana cemin
tabbas wata rana zaki soni fiye da kowa a duniya amman ban sani ba ko son zai amfanemu ashe gaskiyarshi a ƙurerren lokacin zan soshi,
ya Mustapha washe gari za'a kashe min Hamma na na fara sonshi na yarda dashi bisa gaskiya amman suka zo suka rabani dashi".
sai kuma ta kife kai tana kuka cur-cur cikin sauti mai cike da rauni da nadama,
Shiko Mustapha gaba ɗaya duk ya ruɗe tausayin ta na ratsashi tabbas ranshi ya cika da raunida kukanta ya raunata zuciyar shi lokaci ɗaya hawaye suka rinƙa zubo mai a take yashiga matsanan ciyar damuwa cikin rawan murya yace,
"Haba Khairi na fahimce ki kuma nagamsu naji daɗi daya kasance ɗan uwana ne yazama zaɓinki domin kuwa inajin duk wani ɗan gidan nan a matsayin ɗan uwana na jini,
kuma ina ƙaunar su, har kullum burina shine dawo maki da farin cikin da kika rasa,
a koda yaushe fatana in sa hawaye ya dena zuba a idanuwan ki Ummu tabbas Hamma Umar mutunne mai cikar daraja,
nasan kukan da zakiyi shi zaisa kiji sanyi, amman dan Allah ki daure ki dena zubda mai ƙollah kiyi ta mishi Addu'a kiyi fatan Allah ya sadaku a al'janna,
ni dama fatana in kawarwa Farouq tunanin maraici,
Allhamdulillh nasan zaku sami haka a gurin Usman sama da abin da zaku samu a gun kowa, kuma na yarda da ƙaddararmu a karo na biyu dana kuma neman aurenki ban samuba Ummul na haƙura dake amman ki sani ke nafara so a rayuwata,
nima nagode da kulawar ki gareni ƙanwata".
Hakanan yaci gaba da yimata hira da nasiha a matsayin yayanta duk da bayajin dad'in zuciyar shi da jikin shi amma yana ɓoyewa dan kada itan ta damu itako da eh ko a a kawai take amsamai har yadauki ɗan lokaci sannan sukai sallama yatafi jiki ba ƙarfi.


A palour Hajjajo Ummul tayi sallama sakamakon kiran da Abba ya aika Aliyu yayi mata,
dukkansu suka amsa sallamar tasami gefen da Hajjajo take tazauna a ƙasa gaida Daddy da Abba tayi sannan Hajjajo da Usman sai ya Adam,
Daddy ne ya kalli Usman da sigar tsokana yace,
"To angon yafara bud'e mana taron da addu a". Kanshi a ƙasa yana dariya k'asa-k'asa ya ɗaga hannu sukai addu'a suka shafa sannan Daddyn yaci gaba da cewa,
"Mamana wannan taron nakine,
yanzu Abbanku yazomin da sadakin su sannan yace suna so ayi auren cikin ƙan ƙanin lokaci dan haka nace a kirawoki kiji da kunnenki sannan inbaki sadakin ki".
Kanta na ƙasa batace komai ba Daddy yasa hannu yaciro kud'in ya miƙa mata tare da cewa,
"Gashi mamana yi bismillah ki karb'i sadakin ki".
Sake sukuyar dakai tayi ta b'oye fuskarta a cinyar Hajjajo kunya kamar ta tsaga ƙasa ta shige,
hakan yasa Daddy da Abba dariya irin ta manya sannan Abba yace,
"To wani ya wakilceta". Hajjajo ce takai hannu takarɓa tana cewa, "kubani idan bataso". duk dariya sukayi sannan sukayi addu'a suka tashi Abba yafi kowa murna yanata sanyasa y'artashi al'barka.



Kamar kullum idan dare yayi Usman ke zuwa su sha hirarsu da Ummul enshi yauma haka yana dawowa daga masallaci,
wanka yayi ya sha kwalliya sai zuba kamshi yake Adam dake kwance kan kujera a palour yanajin fitowar shi daga bedroom yasa dariya k'asa-k'asa aiko kamar a kunnen shi yajuyo yace,
"Me kakewa dariya?."
,hannu yasa ya toshe bakin da hannun shi yana b'oye dariyar yace, "Kai malam nifa abu nake kallo a waya".
Kwafa yayi yafice sai palour Nanne.

Da Ammi yafara haɗuwa tana fitowa zatayi ɓangaren Hajjajo ɗan raɓawa gefe yayi itako ta kalleshi cikin kaunar ɗan nata tace,
"hmm Usman manyan gari".
Sunne kai yayi ƙasa yana sosa ƙeya,
sannan ta wuce,
shima ya shige,
a palour suka zauna sunata zuba soyayya yanata rikita ta da kalamanshi masu daukar hankali cikin hirar sukai amfani da wayar ta suka kira Garkuwa kiran na shiga shiya fara magana,

"Barka da dare Anutyn Ummu".

"Barka dai ,ya kuke yasu Ammi da su babana Aliyu Auta?".

da fara'a yace,
"Suna lafiya lau kowa na gaidaki".

"Na gode matuƙa".

"Daman cewa nayi bari nayi maki godiya akan irin shawarwarin da kike bawa Ummuna sannan in sanar dake yau ta karb'i sadaki na sannan ansaka rana nan da sati biyu".

"Alhamdullah gaskiya naji dadi sosai nakuma tayaku murna Allah yasa ayi a sa'a,
bani ita nayi mata murna".
hannu biyu tasa tarufe ido tana murmushi shiko sai cewa yayi,
Kin ganta tana jinki tarufe ido wai kunya takeji,
Anutyn Ummu gaskiya kiyi mata faɗa ta rege kunyar nan gudun karta takura mana rayuwa kuma dan Allah ki mata nasiha ta rege kuka dan naga tana jin maganarki".
Murmushi tayi sannan tace,
"Ummu yau kuma ni ake kunya to shike nan saina jiki anjima a online dan zamu tattauna inason karin bayani akan labarin kinga zamu fara".

Da haka sukayi sallama sosai Usman yaketa zuba godiya,
Basu jimaba ya rekata ƙofar ɗaki ta shige shima yatafi ɓangaren su.



Shirye-shirye aka fara domin kuwa sati biyu kawai aka saka ranar auren dan haka Aunty Shuwa da Aunty Halima suka zage gurin gyara Ummul da taimakon Ammi da Hajjajo kullum cikin tsumata suke da tsumakansu na shuwa'arab sosai suke tsumeta naci dana sha dakuma na zama a ciki suna murjeta tuni ta murje ta ƙara fari da kyau ko ina na jikin ta ya ciko tib sai sheƙi takeyi fatar nan tata kamar ta jariri kuma ita da kanta tasan ta tsumi da tsumin mutan Yobe.

Wata ranar asabar da tayi dai-dai da saura kwanki bakwai d'aurin auren Aunty Shuwa ta jiko abunda suka saba bawa Ummul kullum tafito palour Hajjajo inda suke zaune ita da Aliyu da Aunty Halima sai Nanne da Ammi da uwar gaiya Hajjajo,
aiko tana ganin ta da cup ta ɓata fuska ta marairaice kamar zatayi kuka tajuyar da kai tace,
"Ni gaskiya nagaji wallahi cikina a k'oshe yake yanzufa Aunty Halima taban wani

Please Login or Register in order to submit comment