Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikin shi,
cikin sanyi yace,
"Allah ya d'ayyiba".
kai ta d'ago ta zura mai ido cikin murmushi tace,
"Ya Usman ina son ka".
ido ya bud'e da sauri sannan ya k'ara matsowa kusa da ita a hankali yace,
"Da gaske kina sona?".
kai ta gyad'a mai tare da kad'a harce tace,
"ehh mana ina sonka".
kai ya juya cikin k'arfin hali yace,
"Allah ya d'aiyiba nima ina sonki so na hak'ik'a,
Ummu ina sonki zan aureki mu reni Farouq da hannun mu,
ina sonki ina shawa'awar rayuwa da ke a k'ark'ashin inuwar aure bisa sunna Ummu ina sonnnn ki zan dawo miki da farin cikin ki nima ki tallafawa rayuwa ta".
Ido ta zazzaro tare da fuska tsuke cikin zubda k'ollah murya a carke tace,
"Na shiga uku ya Usman".
sai kuma ta mik'e da sauri ta gudu d'akinta ita da Ammi,
a haka tasu hirar ta watsent a palour Nanne,
inda ita ko Nenne duk taji abin da suke cewa dan tana cikin kitchen,
shiko a nan ya zauna ya kasa tashi inda ya sametan,
sai lokacin sallah la'asar yatashi tafiya masallaci,
sai ya shiga d'akin nata dan yasan Ammi tana parlour Hajjajo,
yana shiga ya d'ago ta yasa hannu ya shafa fuskarta yakai yatsan shi kan lips d'inta ya lumshe idanuwan shi da suka canja launi sannan ya juya ya fice tare da cewa,
"Ina son ki Ummu so irin na aure ban saniba ko nima zaki tsanene kamar Hamma sai randa na mutu ki soni".
yana fita itema tashi tayi tashige toilet wonka takeyi tana kuka ta rasa matsayin Usman a gareta shike tayata batun kartayi aure yau kuma shike cewa zai aureta me sunanta inta aureshi ta auri yaya ta auri k'ani yau ya Usman ke mata zaurancen saida Hamman ta ya rasu take sonshi a haka tayi ta kokenta,
sannan ta fito dan yin Sallah.

Ranar wata lahadi Ummul na kwance a cinyar Aunty Halima datazo tun safe tanayi mata kitso,
Aliyu ne ya shigo ya zauna gaban Ummul yace,
"Aunty Ummul Dr Bashir yazo yana palour yana jiranki, kamar bazata amsaba saida ta d'au lokaci sannan ta ce,
"ina zuwa, ina Farouq fa?".
cikin jin dad'i Aliyu yayi y'ar dariya yace,
"ai muna ball yana ganin motar yatafi da gudu saida na rik'eshi motar ta tsaya yana fitowa na sakeshi yatafi da gudu gunshi".
Aunty Halima ce ta d'anyi murmushi tare da cewa,
"ya ganeshi kenan?".
Sadiq ne dake kwance kan kujera yana latsa wayar shi yace,
"ai Farouq ko sau biyu kazo gidan nan a na uku sai yanuna ya ganeka,
balle Hamma Bashir da duk sati sai yazo indai yana gari".
murmushi sukayi baki d'aya sannan ita kuma Ummul ta
d'auko hijabi tasaka tafita.

zaune tasame shi a k'asan carpet yabud'e ledar da yazo da ita yana b'arewa Farouq sweet din dayasaba kawo mishi,
sallama tai tasami guri ta zauna sannan cikin nutsuwa ta ca,
"ina wuni?".
da fara'a d'auke a fuskar shi ya d'ago kai yace,
"lafiya Ummul khair ya mutanen gida?".
Kanta a k'asa tace, "suna lafiya".
shiko Farouq cikin kici-kici yasa hannu ya k'ara d'aukan sweet d'in nashi sannan ya mik'e cikin gwarancin sa na yarinta yace,
"Abpa Ayeeh".
gaba d'aya ya sasu dariya har Ummul saida tai d'an yi murmushi balle Dr Bashir dayaketa kyal-kyalawa shiko cikin gudu dib-dib da kuzari yayi waje abin shi yana,
"Abppa Ayeeeh jo cuwit".
Cikin son yaron Dr Bashir ya dawo da kallonshi ga Ummul yace,
"Wai me yace ne?".
k'asa tayi da kai a hankali tace,
"cewa yayi Bah Ali". dariya yasa keyi yace,
"Aliyu zai kaiwa kenan?".
da kai ta amsamai, murmushi yayi tare da sauk'e numfashi sannan ya tashi yakoma kan kujera ya zauna ya dai-dai ta nutsuwar shi sannan ya fuskanci Ummul cikin kulawa da wata irin murya da shima ya rasa inda ya samota yafara magana, "Ummul khair yau zuwana yanada banbanci da kowanne zuwa da nakeyi, sabida wannan zuwan ina tafe da magana mai muhimmanci wadda ta dad'e a zuciyata tana hanani sukuni".
tunda ya fara magana Ummul ta tsinci kanta cikin fad'uwar gaba mai tsanani,
shiko bai gusheba yaci gaba,
"Kiyi hakuri ki daure da kisaurari kalamai na sannan kuma zan baki lokaci da zakiyi tunani akai,
amma dan Allah Ummul kada kisa damuwa a ranki akan abinda zakiji sannan dan Allah ki tausa shi zuciyar ki saboda kukanki yana k'onamin zuciya".
saida yad'anyi shiru kamar mai tunani sannan yace,
" Ummul ina sonki, inason kizamo uwar y'a y'ana, ina sha awar zama dake a k'ar k'ashin inuwar aure".
Duk kalaman da yake yak'i kallon Ummul, itako tuni jikin ta ya mutu tunaninta ya tsaya cak tanajin wani irin zafi a ranta. Katseta yayi da cewa, "kiyi tunani akan maganata zan dawo naji amsa".
yana fad'in haka ya mik'e jiki a mace shida kanshi ya tuno abokin shi a haka ya fice,
yabarta tana share k'ollah,
yana fita a farfajiyar gidan yaga Usman da abokinshi Nura cikin jin dad'i suka fara gaisawa anan Ummul ta fito daga palour ta wucesu tunda ta wuce Usman hankalin shi ya koma kanta dan yadda ya ganta ya tabbatar akwai matsala dan haka sunayin sallama da Dr Bashir ya kalli abokin shi Nuru yace,
" kajirani a d'aki ina zuwa".
Bai jira amsar Nuraba ya shige cikin gidan da sauri,
A bakin k'ofar parlour Nenne ya tsaya cake Dan abinda kunnen shi yajiyo maine ya hanashi k'arasawa ciki ya jingina jikin k'ofar yana sauraren Ummul data fad'a cinyar Aunty Halima tana cewa,
"ku gaya musu banason kowa bazan auri kowaba bazan iyaba dan Allah kuce su kyaleni".
Ya Sadiq dake kwance kan kujera ne ya mik'e zaune cikin b'acin rai yace, "wlh banason wanda muna zaman mu zaizo ya tada hankalin yarinyar nan, mutane basusan damuwar mutumba
ke kuma Ummul ai aure wajibi ne a gareki zaman shekara biyu da wata 9 ya isa haka dole kiyi aure kam".
sai kuma ya taso ya matso inda Ummul d'in take ya d'ago kanta yace,
"kyaleshi Ummuna kiyi shiru kinji".
sannan ya mik'e zai fita Usman dake lab'e yana sauraronsu juyowa yayi da sauri cikin k'unar zuciya yanufi b'angaren su yana tafiya da kyar.

A palour ya sami Nura da Adam suna hirar ball yayi sallama ya fad'a kan kujera ya fidda dogon tsaki ya lumshe ido, Nuru ne dake kusa dashi ya dafa kafad'ar shi yace, "aboki na ya a kayi ne? ". d'ago kai yayi ya kalli Nura sannan ya maida kallonshi ga Adam daya zuba mai ido yace,
"Wai dan Allah yazanyi ne mekuma yake shirin samuna wacce irin rayuwa zanyine?".
Adam cikin yanayin tausayawa d'an uwan na shi yace,
"Wai tambayoyin nan na meye haka? me a kayima?".
saida ya rik'e kirji sannan yace,
"Adam wai Dr Bashir ne yacewa Ummul yana sonta".
Adam da shima yaji bugun zuciyar shi ya k'ara k'arfi yace,
"Usman dan Allah ka ka gayawa Abba ko kuma kabarni in fad'a musu Abban kana son Ummul Insha Allah nasan nanda wata biyu Abba zai aurama ita."
da sauri suka d'ago kai cikin sanyi dan ganin wanda ya shigo......

*Sadaukarwa ga Dr Umar Ibrahim Umar Shuwa( Hamma Umar)*

*By*
*GARKUWAR FULANI*
[11/27, 1:17 PM] El-hajj🤣: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 3⃣4⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇





*RESA TUM MARA TUM HEB'A TUM SEYA TUM JOD'E BE GAYOMA WOD'I NAFU*





*I*do suka zubawa Daddy tare da shafa Kai da sauri Usman ya sauk'e kanshi k'asa,
Adam kuma ya yunkura zai tashi sai kuma ya koma ya zauna ganin shiko Daddy ya saki labulen daya d'ago ya juya ya fice,
batare dayace musu komai ba,
saida suka tabbatar da ya tafi Adam yatashi ya lek'a sannan ya dawo yazauna cikin zolaya yace,
"Allah yasa Daddy yaji zancen da mukai".
Nura ya gyara zama cikin wasa yace,
"basai in fara kiran abokina da angoba". dukan wasa Usman yakaimai yana murmushi.

Shiko Daddy kai tsaye gidan shi ya wuce haka ya kwana da tunanin abinda yaji yaran nasu na tattaunawa wannan yasa gari na wayewa tun da suka fito daga masallaci suka d'unguma b'angaren Hajjajo,
samunta sukai tana lazimi a kan sallaya ganin haka suka samu gefe suka zauna har takai inda zata tsaya ta d'aga hannu sama tai addu'a suka shafa tare sannan suka gaisa cikin so da k'auna, kallonsu tayi da alamar tambaya,
Daddy ne ya sake tonk'oshe k'afa yafara magana cikin nutsuwa yace,
"Ummie jiya bayan nafita daga nan sai naje b'angaren yaran nan dan zan aiki Adamu to ina zuwa kunnena yaji Adam yanata rok'on Usman,
wai yabar shi ya fad'a mana yanason Ummulkhair".
da mamaki Hajjajo ke kallonsu shiko Abba cikin jin dad'i yace, "Alhamdullah Masha Allah,
in haka ta kasance tabbas muna farin ciki dan naji dad'in wannan magana sosai".
Sannan ya maida duban shi ga Hajjajo da itama da ganinta kasan taji dad'in maganar yace,
"Ummie kinji ko? yanzu izininki kawai muke nema dan aiwatar da abinda ya dace tunda dama ita Ummu tak'i kowa kuma inaga shak'uwarsu da Usman zatayi tasiri wurin sa ta amince dashi".
Ita love Hajjajo sunkuyar da kai tayi tana b'oye k'ollar data fito mata wadda ta fito da manufofi biyu tace, "namuku izini,
kuyi duk abinda ya dace,
Allah yai muku albarka yasa k'udirin mu yazamo alkhairi amman a nemi yardar Ummu dan yanzu ita ba budurwa bace ku bata dama tayi zab'in da ranta keso gudun kar a maimaita abinda ya faru a baya".
had'a baki sukai suka amsa da, "Amin".
sannan Daddy ya kuma gyara zama tare da cewa,
"Insha Allah baza a maimaita abinda ya faru a baya ba dan tabbas munga illar auren dole da illar auren cushe duk da muna da damar da zamuyi mata zab'i kuma mun mata amman zuciyarta bata soba gashi sai a k'arshe rayuwar ta katse mana cikin nadama ita kuwa sanin din kafiyarta ta d'auke farin cikin rayuwar".
cikin sanyi Hajjajo tace,
"Allah ya tsare na gama".
"Amin Amin Ameeeeeeeeeeeeeeeen ya rabbil izzati ".
suka amsa a tare, Matsowa Abba ya sakeyi kusa da d'an uwan shi yace,
"Hussain ina nemawa yarona Usman auren yarinyarka Ummulkhair". Hannunshi Daddy ya rik'o cikin jin dad'in yadda d'an uwan nashi kemai kara akan yaransu yace,
"Nabaku nabaku Ummulkhair bisa amana da k'auna Allah yasa ayi cikin sa'a kuma Allah ya sanya alkhairinsa".
Hajjajo da Abba suka amsa da, "Ameen".

Haka sukai ta tattauna yanda zasu tsara,
daga k'arshe Abba ya d'auko wayar shi ya latsa yasa a kunnen shi,
Usman dake zaune kan sallaya yaji wayarshi na k'ara yamik'a hannu Adam dake kan gado kwance yasa hannu yad'au wayar ya mik'amai dasauri Usman ya amsa kiran yasa a kunne ya russuna kamar yana ganin me kiran yace, "Assalamu alaika,
Abba ina kwana?". Adam dajin Usman yace Abba ya mik'e daga kwanciyar da yake ya zauna tsakiyar gadon ya zubawa Usman ido wanda ya saurara yana jin abinda Abban ke fad'a yana jiran karin bayani,
"To". Usman yace sannan ya sauke wayar ya kalli Adam yace, "Abba na kiranmu a palour Hajjajo".
daga haka ya tashi ya ajiye wayar yafice,
cikin happy yayi d'an k'ara tare da cewa,
"yes". sannan ya sakko daga gadon yafita cikin zumud'i da addu ar Allah yasa abinda yake zato ne.

A palour Hajjajo Usman yayi sallama suka amsamai yasami k'asa gefen Abba ya zauna sannan Adam ma ya shigo yasami gefen Daddy ya zauna,Usman ne yafara gaida Hajjajo sannan yakuma gaida iyayen nashi sannan Adam ma yayi tashi gaisuwar sai kuma suka saurara cikin nutsuwa Abba yafara magana dacewa,
"Usman banji dad'in yadda kuka waremu kaida d'an uwanka Adam kuke b'oye damuwarku ku kad'ai ba,
duk da nayar da komai lokacine kuma ga lokacin yayi dan haka inaso ka shaida sannan d'an uwanka ya shaida kamar yadda mahaifiyata ta shaida d'an ni mahaifinka na nema maka auren y'ar d'an uwana Ummul khairi".
sanyi, dadi, fad'uwar gaba gabaki d'aya suka ziyarci zuciyar Usman da haka ya kasa jin komai da gane komai da suke fad'a,
Abbane ya dawo dashi daga duniyar daya tafi ta hanyar dafa kafad'ar shi yace,
"Allah yamaka albarka Allah ya baka ikon kula da d'an d'an uwanka". Cikin nutsuwa da kwantar da kai k'asa Usman murya a sanyaye yace,
"Daddy nagode Allah ya saka da alkhairi". sai kuma yakai dubanshi ga Adam da dad'i ya cikawa ciki yanata murmushi yace,
"Adam katayani godiya gun Abba".
Shiko Adam washe baki yayi kai kace shi akaima kyautar matar yace,
"Daddy mun gode Allah ya k'ara girma".
Usman yasake matsawa kusa da Abban yai k'asa da murya cikin biyeyya da yace,
"Abba nagode Allah ya k'ara arzik'i,
amin godiya gun Daddy".
sai kuma ya d'anyi shiru kai ya kuma sunkuyarwa a hankali yaci gaba da cewa,
"Sannan inaso in nemi wata alfarma agurin ku".
Abba ne ya sa hannu ya shafa kan Usman yace,
"a shirye muke mu samar maka da farin ciki kada ka damu ka fad'i duk abinda kake so insha Allahu zamuyi maka danko munada yak'inin bazaka nemi abinda bazamu iyaba". sauke ajiyar zuciya yayi sannan murya na rawa yace,
"Abba dan Allah kumin alfarma kubani dama in nemi yardar Ummul,
da kaina kar ayi mata dole a bari ta amince dani da kanta,
Daddy inaso inganta cikin farin ciki sannan hakan shizai bani damar k'arasa kula da ita da yarona cikin jin dad'i, ina nufin zatafi jin dad'i idan anyi komai da yardar ta".

Shirune ya ratsa palour na y'an mintina sannan Daddy yai gyaran murya tare da cewa, "Usman Allah yayi maka albarka, hak'ik'a wannan kalaman naka sunkai ayi maka uzuri kamar yadda ka buk'ata kuma hakan ya dad'a tabbatar mana da cewa kaine kad'ai zaka iya dawo mata da farin cikin ta,
Allah yamaka albarka Allah yabaka ikon kulawa da iyalinka".
"Amin". Suka amsa sannan Abba yace,
"to duk abinda zance Daddyn ku yafad'a dan haka indai babu wata maganar sai kuje kuyi abinda zakuyi,
Allah yayi muku Albarka ya jikan yayanku yakai haske kabarin shi".
duka suka amsa da, "Amin".
Daddy yace to Adam kayi mana addu'a mu tashi,
daga haka taron ya tashi kowanne zuciyar shi na cikin nishad'i.

Suna fita Adam ya kama hannun Usman yace,
"congrat bros". Murmushi yayi yace, "nagode".
Adam yasake matse hannun Usman dake rik'e a hannun shi yace, "nidai naso kabari ayi auren nan kasan yadda Ummul take balle yanzu yaza ai kace saida amincewar ta".
a hankali ya janye hannun shi ya shafa kanshi ya

Please Login or Register in order to submit comment