Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalli Adam cikin lumshe ido da sauk'e sassanyar numfashi yace,
"Adam hak'ik'a inason kasancewa da Ummul ina son rayuwa da ita k'ark'ashin inuwar sure, amma kasani a yanzu soyayya hud'u nake mata, nafarko inamata so irin na ma a bota soyayya da kauna wanda Allah ne ya dasamin hakan a zuciyata,
na biyu inason Ummul soyayya ta yaya da k'anwarsa, na uku itace abinda Hammana yafiso da k'auna, sannan itace tafara haifamin d'ana jinina,
kaga wad'annan suke jana kuma suke bani tabbaci da kwarin gwiwar insha Allah zanyi nasarar samar mata farin cikin data rasa a baya".
ajiyar zuciya yayi sannan yacigaba da cewa,
"Zan jure duk wata damuwa akan haka,
nasan burinka insami farin cikine amma inaso kacigaba da tayani addu'a Allah ya sanya sona a zuciyar Ummu".
Magan ganun Usman ne suka kashe wa Adam jiki ya sa hannu ya rungumo shi suka rungumi juna suka juya zasu tafi b'angarensu Keenan,
muryar Nanne c ta tsai dasu suka juyo inda take,
ita ko cikin jin dad'in ganin su a haka tace, "y'ay'an Abba me kuka samu ne? na ganku a cikin nishad'i".
K'asa sukai suka tsuguna a tare suka ce "ina kwana".
Ammice ta amsa da, "lafiya lau". Kasancewar indai Ammi naguri Nanne bata amsa gaisuwar da za ai daga farko,
sannan suka sake gaida Nanne ta amsa cikin sakin fuska tace, "kuje abinku muma zamu gaida mai sunan Ummul ne".
Da haka suka shige sukuma suka kama hanyar b'angarensu.

Dab da zasu shigene Usman yasaki hannun Adam daya rik'o yace, "kaga jeka ni bazan iya komai ba saina dubo Noor hayati name da my son".
dariya Adam yasa harda rik'e ciki,
shiko Usman ko kallo bai ishe shiba ya juya yai tafiyar shi.

Hargowar Farouq yajiyo tun kafin ya shigo,
yana k'arasowa ya sauke idanuwan shi kan Ummul dake zaune a bakin gado rik'e da rigar Farouq a hannu ta shagwab'e fuska kamar zatai kuka,
inda take kallo shima ya kalla Farouq ne tsaye ya mak'ale kafad'a ya turo baki gaba yana zare ido, abin nasu dariya yaso bashi amma saboda gudun rigimar Ummul ya b'oye dariyar yazauna bakin gadon kusa da Ummul yace, "meya had'aku ne?". Kafin tai magana Farouq ya taho yafad'a jikin Usman yace,
"Abee imma ne".
k'ara rungume shi yayi a jikin shi yace, "Ummuna wai menene?".
Itama k'ara shagwab'e fuskar tai tace,
"tun dazu kowanne kaya na d'auko sai ya gudu yace bashi ba ni har nagaji".
Murmushi Usman yayi yana jinjina aikin gaban shi na rarrashin y'an shagwab'a biyu sannan yasa hannu yakarb'i rigar daga hannun Ummul yace,
"yaron kirki yi hakuri kasa wannan yanzu anjima kad'an sai in canja maka wasu ko?". d'aga kai yayi yace cikin gwaranci, "ambuma". hannu Usman ya mik'o ya mak'ale yatsu guda biyu yace,
"e". aiko dariya Farouq yasaka sannan yasa yatsanshi tsakanin na Abeen nashi ya raba yatsun da Usman d'in ya had'a,
sannan ya mik'a kai Usman ya sakamai rigar yajuya ya fice da gudu,
ido suka rakashi dashi sannan Ummul tasuke ajiyar zuciya tai k'asa da kai tace,
"Ina kwana".
Ido ya zuba mata na tsahon 20 second sannan yace,
" waya ce maki a haka ake gaida masoyi?".
d'an turo baki tayi ta turo lips d'inta gaba ta mik'e zata fice daga d'akin,
cikin zafin nama ya rik'o hannunta abinda yajine ya ratsa dukkan sassan jikin shi yasa yayi saurin sakin hannun nata itako tacigaba da tafiya,
ganin hakan ya dafe kirjin shi da hannun shi d'aya yace,
"washh". da sauri ta juyo ta dawo kusa dashi ta zauna tad'ora hannunta akan nashi tai rau-rau da idanu kamar zatai kuka tace, Ya Usman meke damunka? k'irjin ko? ". zame hannun ta yayi daga nashi yace,
"so, soyayyarki ce take damuna Ummul soyeyyar kice take son min illah a zuciyata da jikina". Yanda ya kafeta da idanuwan shi masu zuba kasala yasa tai k'asa dakai ta marai raice fuska cikin sanyin murya tace,
" dan Allah kadena min haka kaga kaban tsoro nazaci ciwo kakeji". murmushi yayi cikin jin dad'i tare dayi mata wani solon kallo mai cike da k'auna sannan yace, "Ummuna bakyaso inji ciwon ne?".
Dakai ta amsamai alamar "eh".
sannan ta tashi zata fice,
da sauri ya taso yasha gaban ta ita kuwa ta rink'ayin baya-baya har ta isa jikin gini,
ido ya tsura mata cikin laso lips enshi murya can k'asa yace,
"Ina sonki so mai tarin yawa ina son rayuwa dake da Farouk na wuri d'aya ki kijik'ana ki tausayawa tuzurun yayanki Ummul na gaji da zama ba mata na matsu da yin aure ki tausayi min nida Farouq kar muyi maraici biyu ba Hamma na kema kuma kiyi nesa damu baza muji dad'in rayuwa ba".
k'ara matsowa kusa da ita yayi cikin yin k'asa da murya yace,
"Ummuna ina son aure wallahi na fa gaji da zaman gidan ina son mace kusa dani hak'uri na ya fara gazawa kiyi hak'uri ki yarda dani ki bani dama zan dawo miki da farin cikin ki kinji Ummuna".
rab'awa tayi gefen shi cikin jin tsananin kunya da tsoron ya Usman d'in dan ta lura baida sauk'i ficewa tayi ta barshi a d'akin,
shiko murmushi yayi yamik'e yafice.

A ranar bayan ya tashi daga aiki,
kai tsaye ya wuce Ahlul bhait communication ya seyowa Ummul d'inshi waya k'irar Iphone 6,
sannan ya nufi gida yanajin farin ciki sosai a ranshi dan ya tabbatar ta woyar zai k'ara samun damar isar da sok'onnin soyeyyarshi.

A gida kuwa yana isa kai tsaye part d'in kakarsu ya nufa,
zaune ya samesu a palour Hajjajo yana shiga ya d'an rusuna ya gaida Hajjajo da Ammi da Nanne,
sannan ya zauna a k'asan carpet,
Sadiq ne yafara gaida shi sannan Aliyu Ummul ce k'arshe sannan ya dubi Nanne yace,
"Ina Farouq fa?
Murmushi Nenne tayi sannan tace,
"Sun fita yanzun nan da Adam,
kasan shi dason yawo". hannu yasa cikin ledar daya shigo da ita yaciro kwalin wayar ya mik'awa Aliyu dake kusa dashi yace mik'ama Ummul saika saka mata sim card d'in ,
murna Aliyu yake yasa hannu biyu ya karb'a ya mik'ama Ammi ta juyata tace,
"to angode Allah yayi albarka".
sai ta mik'ama Nanne tace,
" Gashi asamana albarka Ummu na tayi woya".
hannu tasa ta karb'a tayi godiya sannan tamik'a ma Hajjajo,
da sauri Hajjajo takama kwalin da kokawa,
sai kuma Aliyu yayi saurin kwacewa yace, "ke tsohuwa karki mana b'arna fa ya Karo'arma sai da dambe".
Yamutse fuska tai tace,
"garani ai".
dariya sukayi sannan Ammi ta tashi tana gaba Nanne na binta suka fice,
Cikin zumud'i Aliyu ya had'a waya yana washe baki ya mik'awa Ummul dake zaune tana wasa da yatsun ta kaita girgizamai alamar bataso,
Shiko Usman da tunda ya shigo ya keta satar kallon ta sai yayi saurin kauda kansa kamar baiga me sukeba yatashi yafice,
Shi kuwa Aliyu dawowa yayi kusa da Ummul d'in yace,
"Haba Aunty meyasa kike hakane?
yanzu dayaga kinnuna bakya so ai bazaiji dad'i ba,
kuma bakya ganin zata d'ebe miki kewa da tunani,
aduk lokacin da kike ke kadai,
dan Allah ki karb'a kisa albarka".
Batace komai ba sai idanu data zubamai tana zubda k'ollah cikin sanyi ta fara kuka murya can k'asa tace,
"Aliyu kai gani kake akwai wani abu da zai mantar dani Hamma Umar ne Aliyu gani kake woya zata ciremin dana sanin dana saka rayuwata a cikine Aliyu gani kuko a shekara uku zan manta yadda aka rebani da Hamma Umar ne Aliyu bayan qura'an ba wani abu da nake rik'ewa inji sanyi a raina waya zata tuno min da Hamma na dan ita ce kyautar da ya bani a randa zai rasu zai fita ya ajiye min woyarshi k'asan pillow na yace min Khairi na ga wannan zai d'ebe miki kewa kuma zan rink'a kiranki inji ya jikin ki".
sai ta kuma fashewa da kuka ta rik'o hannun Aliyu murya na rawa tace,
"Inama woya zata iya had'ani da Hamma Umar da na gaya mishi ina sonshi so na hak'ik'a ina sonshi son da bana yiwa kaina da zan dauwama ina mishi zantu kan so amman ina Hamma na yayi min nisa Aliyu ina son Hamma Umar wallahi ina sonshi Aliyu nayi nadama a rayuwata nayi laifi mai munu ina ganin sakayyar rashin yiwa iyaye biyeyya ina ganin illar taurin kai ina ganin munin tsanar masoyi da nabi zab'in iyayena da bazanyi dana sani ba da bazanyi nadama ba".
Cikin zubda k'ollah Aliyun yace,
"Abun da Hamma Umar yafi so shine ya Usman Anty Ummu in kinso ya Usman Hamma Umar zaiyi farin ciki ki yarda da Ya Usman ku had'u ku reni Farouq ku rabashi da agolanci ki karb'i kyautar ya Usman ko dan kar ranshi ya b'aci kin san matsalar sa dan Allah ki amshi woyar kinji ko".
shiru tayi ta tsura mai ido dan Aliyu kamar k'awa yake a gareta kuma abokin shawara kuma abokin kuka kamar yadda Hamma Umar ya fad'a ganin tayi shiru ne,
shiko yasake cewa , " kin yarda?".
saida ta k'ureshi da ido sannan cikin kosawa da nacinshi tace,
"eh".
Hajjajo da kamar jira take Ummul ta amsa tamik'e tace, "gulmammiya kawai kin sa kanki cikin nadama da taurin kanki".
sannan itama tayi shigewar ta bedroom d'inta tabarsu a wurin ita da Auta,
Aliyu ya k'ara matsowa kusa da Ummul yace, " kinga idan na bud'e miki Whatsapp zaki rink'a chat damu, sannan facebook kirink'a ganin labaru kinga ai zakiji dad'i".
Kallonshi kawai take yana dannawa yace kinga ga number ki nasaka maki number duk y'an gidan nan harda Abba,
itadai ta zuba ido tana kallon cikin wayar a haka ya seta komai harda whatsapp da facebook ya sanya mata hoton Farouq akan dp ta sannan ya kira mata Aunty Halima tana d'auka yace,
"number aunty Ummul ce,
kisa asata a groups da kike dan d'ebe mata kewa".
Itama murna tayi sosai sannan tai addu'a take tabada number Ummul da aka sata a group na Hausa novel Aliyu ma yayi adding nata a family group nasu wanda shine admin,
har magariba ta samesu agun sannan suka tashi suka fito a hanya Aliyu ke cewa Ummul,
"Idan kinje kin nutsu zakiga number ya Usma saiki kira kice kin gode kinji Anty na?". Bata cikiyi wa Aliyu musuba dan shiya zama kamar k'awarta haka yasa ta gyad'a mai kai alamar toh.


K'arfe 9:30 na dare Ummul tana kwance ganin zata fara aikin ta na tunani da kuka da take duk darene yasa ta janyo wayar ta kunna sannan ta lalubo number ya Usman ta danna kira aiko bugu d'aya ya d'auka daman yanada niyyar kiranta sallama yayi ta amsamai sannan shiru ya biyo baya,
a hankali ta katse shirun da cewa,
"ya Usman nagode". wata irin ajiyar zuciya ya sauke,
tare da lumshe ido a hankali yace,
"Nima nagode da kika amshi keutata,
Ummu ina sonki ina son auren ki kiyi hak'uri ki yarda da k'addararki ta sirens dan inba mutuwa ba ba abinda zaisa ni Usman k'anin Umar nace zan aureki da haka shima wannan ki sanyashi a cikin littafin k'addarar rayuwarmu Ummu na ina sonki ki shigo rayuwata ki zame min gurbin Hamma na nima na zame miki gurbin sa,
Ummu wallahi da gaske ina murad'in yin aure na gaji da zaman kad'aici ina son samun me d'ebemin kewa da kawarmin da buk'atuna ko zan samu sukuni a rayuwa ta Ummu ina da buk'atar ki kusa dani". saurin cire wayar tayi daga kunnenta ta katse kiran,
tana jin zuciyarta na bugawa da k'arfi salon maganganun Ya Usman d'in nata suna bata tsoro dan a hankali ta fara fahimtar yana yin irin tasa halittar Kuma,
Kamar zata ajiye wayar sai kuma ta bud'e data,
aiko sak'onni sukayi ta shigowa saida ta bud'e na sauran groups d'in sannan ta dawo kan wanda taga sakon shi sunfi yawa mai suna 'COOL NOVELS ' na Hayatu Baba Zubairu, ta bude magan ganu tarink'a gani anayi a group din daga dukkan alamu a kan novel suke tattaunawa,
wata tace daga cikin members na group d'in tace,
"Gaskiya Meenal ta Hamma Haiydar ce". wasu suce,
"A barwa Dr jabeer".
wasu suce General Aliyu ai shine jarumin amman kuma Allah yasa kar Abdul yaci nasarar ketawa Meenal haddi". Saida tayi ta dubawa sannan taga suna maganane akan wani novel dataga antura page d'aya mai suna, *'BANDIRAWO'* na marubuciya nan *AYSHA ALIYU GARKUWA,* fita tayi tayiwa Aunty Halima magana data tura mata novel d'in saboda ta faro daga farko,
aiko nan da nan ta turo mata, saida takai k'arfe 1:50 tana karantawa har ta iso inda aka tsaya sannan ta tashi tayo alwala tayi nafiloli day'an addu o i sannan ta kwanta.

Tunda ta karanta littafin *Bandirawo* tafara tunani da kuma son taga itama labarin rayuwarta yazama littafin da jama a da dama zasu karanta kuma su ilmantu da sanin illolin rashi biyayya ga iyaye da rashin karb'ar k'addara sannan da sanin muhimmancin mutum mai hakuri da illar cutar da masoyi sannan jama a da dama zasuji labarin d'an kad'an daga cikin illar da boko haram sukayi ga zuciyoyin al'umar dake arewa maso gabashin Nigeria tana son yan mata su d'auki darasi a rayuwar ta tunda ita kam ta rigada tayi kuskure da nadamar yin tirjiya ga zab'in iyayenta amman tana son labarin ta ya zama izina ga yan mata da su guji yiwa iyayen su tirjiya dan nadama zata biyo baya tana son taga irin muhawarar da mutane zasuyi a kanta da abin da ta aikatawa Hamma Umar tana son taga an fad'i laifinta ko zata k'ara dauwama cikin dana sani da yiwa Hamman ta addu'a.

Aliyu tafara bawa shawara sannan sukaiwa Ya Sadiq da Adam shawarar hakan shima ya gamsu amma yace mata ta sanar da ya Usman kafin ta ai watar da komai dan shine babba kuma shi zai bada shawara mafi dacewa dan haka tai niyyar sanar dashi buk'atar ta.


Ranar asabar misalin k'arfe sha d'aya na rana Ummul tayi wanka tad'au doguwar rigarta ta saka tai rolling kanta da mayafin rigar ta feshe jikinta da turare mai kamshi sannan ta zauna bakin gado ta d'auki wayar ta a hankali tai dialing number Ya Usman sannan ta kara a kunnen ta,
Usman dake zaune gaban laptop yana d'an danne danne ya d'aga wayar yasa ki murmushi mai sauti dayasa Adam dake latsa wayar shi juyowa yana kallon shi, ciki jin dadi ya amsa kiran ya karata a kunne yayi k'asa da murya yace,
"Assalamu alaiki ya noorul hayati na". Ummul ta amsa da, "Wa alaikassalam, ya Usman ka fitane?". saida ya sake kashe murya yace,
"waneni infita banyi sallama da ruhina ba,
inzone?".
Dasauri tace,
"a a ina zuwa".
bata jira amsar shiba ta katse wayar ta tashi ta fito.

Juya kai Usman yayi ya harari Adam cikin wasa yace,
"meye ka zuban ido, kake wata dariya kamar mara gaskiya".
k'asa da kai Adam yayi yana danne dariyar dake shirin fitowa da k'arfi yace,
"ni menace?".
tsuke fuska yayi yace, "Daman me ka isa kace,
fita zaka yi daga d'akin Ummuna zatazo".
Adam baisan lokacin da dariyar ta kwace mashi ta fitoba,
shiko Usman yunk'ura wa yayi ya kawomai dukan wasa Adam ya kauce yace,
"kuda zakuyi maganar ku a palour ina ruwana ina nan".
Kai ya kad'a yace,
"Allah saika fita d'an sa ido kawai".
Wayarshi ya d'auka yasauko daga gadon yana dariya yace, "intai tsami naji".

"inba tagi tsaminba kuma kai sai kayi tsamin ko".
Adam yana fita yasami Ummul bakin k'ofa tana sallama ya amsa cikin kauda kai sannan suka gaisa ya wuce yanufi b'angaren Nanne.

Usman yana jin ta ya fito yana amsa sallamar ya k'arasa

Please Login or Register in order to submit comment