Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[1/14, 4:57 PM] Sis Asma: 🏉KAMAR SU CE DAYA🏉
COPY BY ZAINAB BUTALAWA



1-5





Official








By
AsmaBaffa












BISMILLAH







Alhmdllh Allah ya kawo mu sabon Novel dina fans KAMAR SU CE DAYA.
Allah yasa ku ji dadinsa kamar sauran Novels dina da suka gabata,ina fatan zaku bibiyeni readers ba sai an gama anyi Doc ba Nafi son wanda za ana bina page by page ana min sharhi muna nishadi da zumunci.kamar yanda muka fara lfy Allah Sa mu gama lfy mu amfana da juna da sakon da Novel din ke isarwa.







FCT Abuja unguwar sai wane da wane a Abuja ma sai ka Isa kake zama cikinta ba kowanne me karamin kudi ke iya zama ciki ba sai ka sharaha ka gawurta kuma ka tumbatsa ka fetsara a Naira zaka iya zama cikinta,ba wanda zai zaton cewar a kasar nan akwai unguwa me tsari da kyau irin nan ba ko a turai sai haka,shi yasa ma kafin kaga bakar fata a unguwar zaka dade kusan duka fararen fata ke zama a wannan unguwa irin su Ambasadors,consilor na embassy da Sauran masu zama a kasar Nigeria lokaci zuwa lokaci,wani tsantsararren gida da kusan ma yafi da yawa kyau a layin,wasu motoci ne sunfi biyar tafka tafka suka shararo zasu shiga wannan gida wawakeken gaske tsayawa fada muku tsaruwar wannan gidan kadai zai cinye mana Pages duka ma,remote Driver me jan motar gaban ya danna sai ga gate ya dage sama,suka shiga wannan gidan wanda ko ina motocine na alfarma,gidane na nunuwa a duniya,tunda motocin suka shiga ko ina ma'aikata da Securities sun dai daita sahunsu suna jira me gidan nasu ya fito,sai da aka dauki kusan 30mnt bai fito ba har an kosa da jira su kam da Alama sun saba da hakan.

Kofa aka bude masa ko ina ka juya Sojoji ne a gidan ana tsaro,kafa daya ya zuro hakan ma ya dade bai fito ba sai daga bisani ya zuro kafar dayan ya fito a gadarance cikin Isa da takama yana shan kamshi yana basarwa,wow Tabbas wannan Bature ne ko balarabe babu abinda ya hadashi da suffar bahausa ko jinin Nigeria,domin ta ko ina ba kalar nan bane,cikin turawa da Larabawa ma sai an dage da gasken gaske za a samu me kyan wannan matashi,domin wasu ma da dama zasu ce Aljani ne,za a iya karade kasar nan kowa zai iya cewa Bai taba ganin me kyau irinsa ba,kamar Aljani haka yake,tun daga dirinsa da baiwar sura cikar zati da haiba baza ka gama rudewa ba sai ka kalli fuskarsa,dole kayi kabbara ga Allah,iya saninka wannan Matashin ya zarta saninka a baiwar kyau idan ya shugo waje ko waye sai ya raina kansa Bai isa ya matsa kusa dashi ba, hancinsa codede zarkadede,dan bakinsa cut dashi pink kamar yasa jambaki,idanunsa Dara Dara shanyayyu kamar bacci zai yi,sumarsa me uban yawa baka me santsi tasha gyara Naira tayi kuka a kanta,ga wani hadaddun Saje da gemu nasa, kafafunsa da yatsunsa abin kallo,girarsa kuwa har hadewa take sabo da baki da yawa,gashi fari kar kar dashi ba irin fari na jigari jigari ba farin bature ne dashi domin yafi Balarabe fari,amma kyansa da cikar hallitar kamar Balarabe,ba zai wuce 32years ba.

gaisuwa ake kwasa cikin harshen turanci amma ko saurarensu baiyi ba fuska ba rahma ya shiga cikin palon tare da danna code din kofar cike da takama da gadara, sai ka shiga palon zaka San ma a duniya kake ne wai ko a Aljanna domin kyansa da tsaruwarsa ya wuce hankali,kamshi ne da sanyi ke tashi kawai,
Wata budurwa ce kyakyawar gaske ke zaune a palon ta nitse cikin kujeru kafa daya kan daya tana cin Apple tana kuma danna kafcececiyar wayarta,tana ganinsa ta Mike tare da Fadawa jikinsa cikin harshen turanci take masa sannu da zuwa,dan murmushi yayi kadan,cikin hausar daya fara koya Bai iya ba yace yau...Shi..ni...kinka Jo?wai yaushe kika zo yake nufi,Budurwar tace since in the morning,ci..danna...mini... English,(ki daina min English). Kansa ya nuna da yatsa ni...sho nace na gane..hausa, dariya tayi ita dai hausar sabon saurayinta na bata dariya,ba haka ake cewa ba Honey,cewa zakayi ina so na iya hausa ki daina yi min turanci.Ok na gano shi(na gane) na gane zaka ce,

Wuyansa ta sakalo cikin salo ta fara aika masa da kiss ya fara biye mata kenan yaji kamar an rike masa harshe tam,da kyar ya finciketa daga jikinsa yana huci kamar zaki,bata gane ba Sam ta kara rungumeshi nan take taji anyi jifa da ita gefe can har sai da kanta ya bugu da bango,ihu ta saki tare da rike keyarta ta dago tana kare masa kallo,honey lfy kake kuwa?jiya fa muka hadu ka bani address kace nazo mu dan huta muna mu'amula daga nan ma sai ka koyi hausa duk cikin turanci take kora masa bayani,cike wulakanci da isa,izza da gadara cikin lalacacciyar Hausarsa wacce a dole sai ya koya yace ni...ni...ba Jan iska bane,ta tari numfashinsa to kai ba dan iska bane ni kuma itace?, cike da takaici yace ni bana cinye mata,nan take ta kwashe da dariya sabo da hausar abin dariya,shi kanshi sai da yayi murmushi,wai haka hausawa suke cewa,

Tace to ai ba haka zaka ce ba na gane baka sex amma zamu iya Romancing ko? Baki ya tabe tare da cewa nop...ni bana con ina tabo mashe ne,cin can me na Shana?tace a'a Bana con noanoa irin naki,tunani ya fara na Kalmar da zai ce yace ayi maka surgery noanoa naka naki yana kamar da tsayi har cikinka ni na fada ma fact that komi ma Bana con shi na taba masha,ina feeling Bana so temper na yana rising,what do u people called it?I wanna know?Harara Ruky baby ta watsa masa sabo da ta gano tsab ci mata mutunci yakeyi baya son ta dan dai ba Jin hausa sosai yake ba,wai ayi mata plastic surgery a breast yake nufi nata ya zube,kuma baya son komai ba dan iska bane shi,tsaki taja tare da mikewa ta fice fuuuuuuu tare da shiga motarta ta bar gidan,tana cewa ita dashi har Abada dama haduwarsu ta farko kenan a resturant,dan iska har ita zai ciwa mutunci amma tana mamakin karfinsa yanda ya jefar da ita kamar Aljani daga tabashi taji wata iska ta fisgeta ta makata a bango,kai gaskiya Aljanune da shi,taya kamar ta zai ce mata boobs nata har ciki,ita da bata da girman su ma har magani take Sha dan su kara girma sai dai idan idonsa ne ya nuna masa haka,Ruky sai masifa take tana driving dama kallonsa tayi kalar kyau da gani gwarzon namijine gashi me kyau,ga kudi idan suka saba gaskiya ta more yanda zai dinga biya mata bukatunta na masha'a kuma zai tafi da ita kasar su ma suci gaba da Jin dadinsu ga Naira wannan ya cuceta dakikin banza a haka kamar gwarzo Ashe lagwani ne.

Shi kuwa wannan Matashi tana barin gidan wani farin ciki ya ratsashi kamar an masa bushara da Aljanna,bedroom ya wuce wanka ya fesa sama sama ya shirya kansa Ashe musulmi ne sai gashi yana sallah sosai karatun Quranin sa abin saurarone sabo da dadin muryarsa ba a cewa komai sai masha'allah,yana idarwa ya fara azkhar ya dade sannan ya gama ya fada saman bed tare da jawo wayarsa ya latsa number lovely M,hello Sweet heart cike da shagwaba kamar zai yi kuka ya fara magana kamar wata mace haka yake shagwaba har yafi matan ma,Sweet heart am tired of this country gaskiya,My Son na fada ma ka daina min turanci Hausa zaka yi min so nake ka iya min yaren hausa, ur mother's tongue shi yasa nace ka fara aiki acan sabo da so nake ka iya yarena kuma ina so ka saba da kasar sabo da soon zamu dawo kasar Nigeria gaba daya da zama tunda Abbanka ya rasu me zamu zauna muyi,idan kana son yan uwanka kazo ka kawo musu ziyara,amma bazan zauna a kasar nan ba Nigeria zan dawo gwara ma ka saba,ya aikin? Alhmdllh sweetheart da wa'ala aiki,not wa'ala wahala,tun kana karami NA'IM nake koya ma Hausa amma ka kasa koya amma bari zamu dawo Nigeria ne zaka iya dole.,My love pls ba dadi kasar nan me zamu dawo muyi?tunda ina da kudi kema kina da shi me zamuyi kuma pls Sweetheart idan kina so na zauna ki dawo kasar to I missed u, miss ur food badly Dear.
Oh! My son ka jirani zan dawo duk abubuwanka zan taho dasu ba sai ka dawo ba, kai kam ka dawo Nigeria kenan,ka jirani nan da 3wks zaka ganni Insha'allah,Kukan shagwaba ya fara mata shi sai dai yazo ya taho da ita,kashe wayar tayi cike da farin ciki.

Asalinsa Babansa musulmin Balarabe ne tsantsa kasar Lebanon Al'awwal Mahmud,aiki ya hadasu a airport da Mummy Hajiya Zuwaira kyakyawa fara tas itama,sonta ya kamashi haka ya dage da kyar iyayenta dake Kebbi suka yarda ya aureta,Hausa Fulani ce sosai, Allah yasa itama iyayenta masu kudi ne gaba da baya,
Al'awwal dan sarkin Lebanon suna da dukiya me tarin yawan gaske,Bayan rasuwar Babansa aka bawa Al'awwal Sarauta Bai dade kan kujera ba Allah ya masa rasuwa,lokacin Na'im za a bawa sai dai yayi kuruciya da yawa sai yace shi baya son Sarauta ya barwa kanin babansa,tun kafin Al'awwal ya rasu ma basa Zama a kasarsu wato Lebanon a Manchester city suke zaune dake Amurka,danginsu kaf suna Lebanon kuma alhmdllh suna zumunci sosai, bayan aurensu Na'im shine Babba sai kannensa Irfan,Hunaif sai auta Aisha,duk a uk suke zaune can suke makaranta,Irfan da Na'im sun gama har Masters,Hunaif yanzu ya fara University,Aisha tana secondary schl,Hunaif da Aisha baza a dawo dasu Nigeria ba sai sun gama karatu zasu dawo sai dai suzo Hutu.

Kasarsu daya ta rage tal a duniya wato ta bangaren uwa Dada Babar Hajiya Zuwaira Mummy, Zuwaira mutuniyar kirki ce ga son yan Uwa da dangi,kuma ga taimako tana son kasarta da hausawa shi yasa tunda mijinta ya rasu tace baza ta kara aure ba yaranta zata rike ta dawo gida Nigeria kusa da yan Uwanta,Arzikinsu yayi yawan da duk wani dan uwan Zuwaira dake kauye tuni sun maidasu cikin birni,Dada kakarsu Babar Mummy ma gidanta daban a cikin Abuja da yan aikinta, sauran kuwa duk suna Kebbi cikin city suna Jin dadi,maza da mata Zuwaira tana nema musu aiki tana biya musu kudin makaranta,ta ko ina Zuwaira halayenta sunyi bata da makusa,haka ma mijinta Al'awwal Abban su Na'im kafin ya rasu mutumin kirki ne na gaske.

Na'im da yan uwansa suna da tarin ilmin addini dana zamani,kuma alhmdllh suna aiki dashi kasancewar sun samu tarbiyya sai dai yanayin Zamansu a kasar waje dole suna abubuwa da basu dace ba da Rayuwar tamu kasar ko nace rayuwar musulmi,baya ga haka dama dole a samu dan Adam da laifi dole ne sai dai wani yafi wani.
basu dauki mace Nada banbanci da maza ba Sam,yanda zasuyi kawance da namiji haka sukeyi da mace,gwara ma Na'im shi baya neman mata sai dai tarin frnds mata kamar me hadadde wayayyu masu kudi amma kuma yana son yayi Sex,yana so yayi rayuwa dasu yana da karfin sha'awa amma abin haushi ya rasa dalili da mace ta rabeshi da niyyar Jin dadi sai yaga ta fadi ko ta bugu da jikin bango,kuma nan take zaiji ya tsaneta sai yaga ta rikide ta koma mummuna me suffa marar kyau,duk abinda ke birgeshi a jikinta sai yaga sun koma abin kyama,abu daya ne ke rage masa Zafi Shan giya sama sama bada yawa ba,sabanin su Irfan basa Shan giya sai dai suna dan having sex da mata amma bada yawa ba sai lalura ta taso,
Aisha kuwa zaman turai yasa mata ta saba da shaye shayen kwayoyi da syrup, sai Lesbian da ta fara jefa kanta ciki, amma dukkansu suna addini sosai kuma kowa yasan laifin da dan Uwansa ke aikatawa.

Na'im Babban likitan kwakwalwa ne a Abuja Mummy ta bude masa katafaran Hospital na gani na fada wanda babu kamarsa likitoci ko ina a ciki,sannan kuma consilor ne a cikin Embassy na kasar lebanon dake Abuja,sune masu yarda a baka visa kasarsu sune masu interview cikin lebanon Embassy, haka kuma yana kula da dukkan business da companies nasu dake kasar Nigeria,shi ke kula da komai na dukiyarsu dake Nigeria,Irfan kuma me Kula dana kasashen ketare,Hunaif ma yana taimakawa.
Na'im duk yafi yan uwansa kyau da komai ma,jinin Sarauta jinin kudi,gadon Arziki,ga kyau shine kadai ke nuna Sarauta a jininsa take,kana ganinsa kasan ya hada jini da Sarauta, matsalarsa Shan giya kadan,tarin kawaye mata amma fa masu class ba karamar wacce ta isa bace zata iya ganin Na'im har su hadu ba, ba a haduwa dasu wajen kananan yara masu karamin karfi,

Matsala ta biyu bashi da mutunci idan yaga dama yanzu zai wulakanta mutum,ga isa takama da gadara,baya saurarar rayuwar wasu bare har ka bata masa rai ko kuma ya wulakanta talaka yaushe ma ya shiga harkarka da har zaku samu matsala,kuma ko uban me zakayi bazai ce ka daina ba wai shi Bature ba ruwansa rayuwarka ce,yasha kama Aisha da mata suna Lesbian Bai taba ce mata ta daina ba kyau ba,haka kannensa ko me zakayi Good for u rayuwarka ce,
Akwai barnar kudi wajensa yanzun nan sai yayi wasa da dollers ba abinda ya dameshi mahaukaciyar kyauta yakeyi baya karama,ko zakka idan zai fitar to sai wanda ya bawa ya washe,kyautar kudi a wajensa ba komai bane,ko ina a motarsa kudine,haka kayansa ma a aljihu ma har cikin takalmi idan yaga dama Dollers zaka gani ya fyalla ta a cikin takalmi ya baka kyauta,
Watarana mutunci watarana babu sai tsiya,haka ma'aikatan sa duk sun San halinsa da kallon Banza watarana watarana fara'a.
Hospital idan yaje tab ai duk patient din da sukayi dace ya dubasu da kansa ba sauran Doctors dake aiki karkashinsa ba to zai wahala patient ya biya kudi kyauta zai masa komai komai girman cuta.
Shi yasa yanzu sunansa ya koma Me Imani,Doctor me Imani,baya Jin hausa sosai sai dai akwai me karasa bayani yanda zai gane idan yana mu'amula da hausawa,shi yasa ma ya dan iya hausa da yawa,a hospital har so ake yazo aiki ranar Monday da Tuesday yake zuwa suna Shan dariyar hausar tasa,wanda basa Jin hausa ya musu turanci amma Mummy dukkan ma'aikata da tasa aka Eba a Hospital Hausawa sunfi yawa sabo da kishin kai, kusan Kullum sai yaje wajen Dada kakarsa sun gaisa tana kara koya masa hausa.wannan kenan nan gaba zaku ci gaba da Jin halayen Na'im wanda ban fada ba sai gaba zaku jisu yanda suke,amma wannan sune Manyan.


Hanyar Abuja Can cikin daji akwai wata ruga ta yan Fulani usul ciki,amma duk da haka rugar a kusa da gefen titi take,tana da girma ba laifi,harda makaranta primary da secondary tare da islamiyya,Fulanin dake wannan dajin ko hausa kadan suke ji basu iya sosai ba amma suna Jin hausar,
Wata Dattijuwa ce kyakyawa me cikar haiba ta fito domin zuwa asibiti dake Suleja Hanyar Abuja kusa dasu,Dattijo yana rike da hannunta da Alama mijinta ne sai sannu yake mata,haka suka shiga mota har suka karasa wannan asibiti,bayan an duba Lafiyarta an tabbatar rashin haihuwa ce ta kawota tunda likita yace baza ta taba haihuwa ba haka ma mijinta shima,cike da tawakali suka siyi magunguna suka fito wajen me gadin wannan asibiti suna hira dashi sama sama,me gadi ya kalleta tare da cewa Hajiya idan baza Ku damu ba ko zaki iya rike min yata guda daya danake da ita?tunda bakya haihuwa kuma na yaba da halayenku zan baku tarihina idan kun amince sai na bar muku yata kyauta Ku riketa Amana.
Sunana Ahmad wanda akewa lakani da Tall Man a cikin Garin Borno muke da dangina tare da dangin matata wacce Allah yayiwa rasuwa kwanan nan,Matata yar Asalin Nijar ce buzuwace gaba da baya amma danginta kaf suna Borno a unguwarmu,Yan uwanta da kuma kanin babanta sai sauran danginta amma iyayenta dama sun Dade da rasuwa,Bayan munyi aure da shekara biyu Allah ya bata ciki ta haifa min yata sunanta Salma watan Salma 7 a duniya Allah ya karbi rayuwar matata Khairat wacce Hawan jini ya kama da karfin gaske,
Bani da Uwa bare uba nima bani da yan Uwa mata sai maza a zamanin nan idan na bawa dan Uwana namiji rikonta matar zata iya gallaza mata tunda ba shine zai zauna da ita ba,haka idan nayi aure ban san wa zan aura ba,haka na hakura na bawa dangin matata Khairat yata Salma,amma yau Salma shekarta biyu a duniya wahalar rayuwa take Sha a hannunsu rayuwar yanzu ba imani ba tausayi,

idan kun yarda muje garinmu kuga gidanmu ayi yarjeniya da dangina da dangin matata kusan juna sai ku tafi da Salma wajenku Ku rike ta Amana,sai Ku dinga kaita wajen dangin ubanta dana uwarta suma zumunci kawai amma na baku ita halak malak Allah yayi jagora kune iyayenta daga yau,Murna wajen wannan dattijai ba a magana,kamar wasa ya dauki Hutu washe gari suka tafi har Borno state,Dukka sun gaisa da danginsa dana Khairat Babar Salma,hannu biyu suka karbesu amma da gani Salma a cikin wahala take ba a kula da ita Sam,haka yayi musu bayani ya dauki Salma da kayanta na sawa ya bawa wannan dattijai da sharadin zasu dinga kawo Salma ana gaisawa da danginta suna zumunci,cikin dangi babu wanda yace kar ayi haka su zasu rike kowa mukus yayi harda fatan alkhairi,cike da murna dattijai suka koma gida suka nuna Ahmad Tall Man baban Salma ga kowa dake da alaka dasu a rugar Fulani duk da cewar yan uwan nasu suma kusan duk sun kare sai kadan daga ciki sai makwafta da abokan arziki,

Kamar wasa tsakani da Allah suke rike Salma ko yarsu baza taji dadi haka ba sabo da gatan da suke nuna mata,ubanta Tall Man idan yazo ganin yarsa dadi yake ji ba kadan ba yana shi musu albarka,haka mutanen gari ma,Salma sai abinda take so shi yasa ta taso cikin shagwaba da tabara ta gaske,amma suna bata tarbiya ta gasken gaske, tana da shekara biyar suka sata a schl tana ilmin addini dana zamani,kamar yanda alkawari yace suna kai Salma Hutu cikin danginta tayi Hutu acan,duk Hutu a Borno take yinsa Affa da kansa yake kaita can abin sha'awa.

tana da shekara takwas Ahmad Tall Man mahaifin Salma ya rasu sakamakon ciwon Koda daya kamashi ba tare da doguwar jinya ba,masu rikon Salma sunyi kuka sunyi zaman makoki,Salma tana primary 4 aka fara ganewa kamar tana da tabin kwakwalwa,sai aganta tana ta maganganu ita kadai,ko aga tana dariya ita daya,wani lokacin kuma tayi ta kuka tana shagwaba,sai ta dinga kallon waje daya,watarana kuma tayi ta wasa tana maganganu kamar da wani takeyin maganar,sai aga tana shafa iska ko ta rungumi iska,a schl ma haka takeyi,watarana kuma aji tana ta rawa tana cashewa kamar tana Jin kida har karkata kunne takeyi,bata da kokari a sauran Subject da dama banda English da French,amma fa Idan anzo exam,a class duk tambaya zata amsa amma kuma bata da kokari kan kowanne subject sai dai English kadai sai French idan ana musu,har kure malamai takeyi indai akan yare ne to baka isa ka kureta ba.

Haukar Salma bata kara ta'azzara ba sai da ta shiga js1 nan aka fara kiranta da living things,sabo da bata iya ba,ance what is living things?Salma tayi sauri ta mike cikin iyayinta tace Living things cike da shagwaba,tace living things is a living things that live on earth with a life,akwai aka kwashe da dariya sabo da Salma kowa yasan a exam kadai take kokari ta cinye du ana mamakin hakan,
Gata dakikiya a class amma da anzo sauran Subject sai ta koma jaka sentence daya baza ta iya kawowa ba bare ta bada definition na abu, sai languages, wani lokacin ma gani za ayi ta tsurawa waje daya Ido tana murmushi ko tana Surutu kasa kasa,kayi mata dariya taci ubanka tana da karfi idan tsokanarta kayi amma idan ita ta tsokaneka to sai ka mata duka baza ta iya komai ba,wasu har suna cewa Aljanune da Salma living things, Sunyi wani Sabon Malami komai sai yace collaborate,shine kullum Salma ta rike aikinta tace Collaboration,shike nan wannan sunan ma yabi Salma,Salma Collaborate ko Salma Living things.

Salma tana da hakuri da Hankali,bata Harka da kowa daga iyayenta da suke riketa shike nan kowa nata ne ba ruwanta da duniya da abinda ke cikinta,Salma me tsananin kyau ce na gasken gaske,fara ce ba fara can ba normal farinta yake,hanci me kyau dan dai dai dashi,bakinta dan karami me dauke da kananan hakora masu
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On KAMARSU CE DAYA
avatar
abdulkadir-lawan-yusuf

2 months ago

Reply

Littafi me ma'ana

Please Login or Register in order to submit comment