Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐🌟🌟⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐






*WACECE NI*








🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation












✍🏼by

*fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
wattpad teemacool2020



1⃣&2⃣



Zan iya mutuwa akan son ka my love and only man kada ki fasamun kaina da dadadan kalamenki abar kaunata

zan kasance mutum na farko da yataki sa'a samun mace Kamar ki,

please Kiyi mun alkawari bazaki taba gujemun ba cikin kowane Hali kika sameni

ta lumshe ido Tana imagining picture na shi da yaturo mata cikin wani hadedden suit Ya matukar karban shi guy ne ajin farko a kyau da kamala..

cikin tattausan murya ta ce in sha Allaah zaka sameni da rike gaskia kuma zan karbeka aduk halin da na tsinceka

yaji dadin kalamanta sosai har cikin ranshi...cikin murya kasa kasa tace my hubby yanzu lokaci yayi da mu fuskanci juna tunda yanzu kusan 5 months muke soyayya ba tare da sanya juna cikin ido ba

nifa na matsu da ganin wannan kyayyawar fuska Mai saje da murmushi a ko yaushe ba karamin sa'a na ci ba da samun mutum Kamar ka...

Ya danyi Jim sannan Ya ce you have me my love and I also love u with all my heart in sha Allaah u will be the mother of my children...

amma zan nemi alfarmanki bazan iya samun daman zuwa ba saboda wasu dalilai zan kwatanta maki inda zamu hadu idan bazaki damu ba sai muhadu,

bataji dadin hakan ba amma da yake sonshi Ya rinjayeta sai ta amince.

ta mushi alkawarin gobe zasu hadi, yaji dadi sosai yayi ta yi mata godiya sannan suka katse wayan bayan Ya manna mata kiss ta cikin wayen har jikinta sai da ya amsa

Aunty na kenan badai wannan guy din ne yadauke maki hankali tun dazu nake maki magana amma hankalinki duk baya kaina,

sai lokacin tajuyo tare da fadin ke waye sa 'anki da zaki damu mutane da tambaya...nasamu wuri na zauna tare da fadin Kiyi hakuri big sister ba nufi na kenan ba...

na lura sosai tana soyayya da wani da suka hadu a instagram ayanda naji take fadawa friends dinta sunan shi *yusuf*

Na nutsu da karatuna hints ne Amman gaskia writer din akwai basira

sosai kuma yana burgeni fatana kawai Allaah yanuna mun shi ko da at once ne in my life time,

zanyi farin ciki da ganinsa nayi Nisa sosai cikin karatu sai na tsinkayi aunty *maryam*

na Kira na zaratun da gudu na iske ta a falo ta shirya sosai gaskiya kwalliyarta yaburge ni,

na'am aunty ki shirya yanzu zaki rakani unguwa abin da ta ce kenan

Sauri sauri nagama shiri na sanya hijabi na nadau waya ta,sannan nace anty na shirya ta dau car keys ina biye da ita,

tabude motor muka shiga kusan tare wakar celline Dion

cikin wakar ta every night in my dreams inabin wakar ahankaliTafiya muke Yi ana kwatanta ta mata location din tana bi har muka iso wani layi muna yin kwana sai ga gidanda aka kwatanta mata

muna kofan gidan sai naga Tana yatsina fuska😒
tare da fadin Anya nanne gidan kuwa a sannan ne na juwo domin ganin gidan

gaskiya low class gida ne..tare muka sauka a motor sannan muka shigo gidan tsohon gini ne
kofan dakin da yake fuskantar mu muka nufa Muna knocking aka bamu umarnin shigowa

saurayi ne matashi handsome ke zaune akan ♿ wheelchair kallon kallo muka tsaya Yi da shi yayin da shi hankalin shi akan aunty *maryam*

yana murmushi tare da fadin my dear welcome to my world,really appreciated to have such a beautiful lady.

have a sit tare da nuna mana kujera ko kallo aunty *maryam* bai ishe ta ba.

cikin karaji da bakin ciki take kallon shi tare da fadin dama kai ne na bata dukkan lokaci na da tunani na akan ka?

wallahi nayi asarar haihuwata akan bata lokaci na a kanka Allaah ya isa tsakani na da Kai

tajuyo gareni cikin fada take mun magana da cewa ke kuma Dan ubanki tashi mufita

kin wani zauna sai kace kin samu gidan ubankiDa wuri na tashi har Tana ingiza keyata muka fito waje yayin da *yusuf*

kuma ke bimmu akan wheelchair cikin fadin haba my love me namiki?

da yayi zafi haka ki fadamun wallahi a shirye nake dan bada hakuri please don't treat and funished me on this way

coz I can't do without you
Cikin karaji ta ce please *yusuf* or whatever you call ur self don't deceive to call me my love

nemi wata can da bata San ciwon kanta ba amma ba ni ba Dan

Allaah kajimun mutum fa saboda tsaban yaudara rainin Hankali ka dubeni da kyau ras da ni

me zanyi da musaki can ka karata or try another girl not me ,

taja hannuna mukabar gidan *yusuf*

kam bakin shi bai gaji da roko ba har mukabar gidan,

har ga Allaah banji dadin abinda auntie na tayi mushi ba .
wlh he didn't deserve this treatment...har muka

dawo gidan fada da masifa ta ke

nikuwa na tsuke baki na nayi shiru dan kar abin yarufta ta kaina🤐

Muna shiga gida ko zama bamuyi ba sai ga kiran *yusuf*

Tana dagawa ta ce wai Kai wane irin mayene kashedi na kuma this is the last time da zanyi warning dinka

kadaina kiran waya ta na ce banayi OK....

sai ta kashe wayan tare da fadin Bari ma inyi block na shi inhuta da kuda,

ta ajiye wayan tayi cikin gida da sauri na dau wayen na copy number *yusuf*

cikin waya ta na ci gabada kallon series da aka saka lokacin da muka shigo film na Mexico ne

amma an fassara da harcen larabci (min ajli ilaina)

ina tunanin abubuwan da suka gabata yanzu ina kuma yin mamaki da yadda Auntie na taci mutuncin mutumin

da suka shude watanni suna soyayya abin da nakasa fahimta shi ne ko dai bai gayamata halin da yake Ciki ba..
koma yayane gaskiya bata kyauta mashi ba yakamata ta saurare shi atleast sai ta share shi

na tsinci kaina da tausayi mashi😢
Nadau waya ta na danna number da nayi serving dazu ina tunanin kiran shi

bedroom na shige rike da wayan a hannuna



*please vote share and comment*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐



*WACECE NI*




Writing by

*fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
wattpad teemacool2020


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*Readers nayi matukar farin ciki da comments*



*page* 3⃣


Ina shiga bedroom wayan manne a bisa kafada ta sau biyu yayi ringing sai yadaga tare da sallama cikin amsa masa da sallaman,

sannan na ce *zaratun* ce sister *maryam* dazu tare muke da ita na Kira ne inbaka hakuri bisa abinda auntie tayi maka gaskiya banji dadin shi ba...

Muryan shi can kasa kasa dagaji kasan yana cikin damuwa Ya ce


gaskiya nayi matukar farin ciki bisa ga kulawarki gareni wallahi ina cikin mawuyacin Hali
Na kuma damu da

*maryam* bansan meye so ba akanta nafara sani,i am even confused I don't know how to explain how I felled,

ko dan yanayin da ta riskeni ne taguje but I am not default,

doctor na ya tabbatar mun zan warke Inci gaba da sabuwar rayuwa

Cikin tausaya mushi na ce kayi hakuri in sha Allaah komai zai daidai ta may be she wasn't in her mode,
Ya ce dan Allah ki taimaka mun ki sha mun kanta wallahi am dying for your sister,

and I will like to hear her voice again,
kayi hakuri ka bata lokaci na kwana biyu sai ka Kira ta nasan 'yar uwata sosai she is difficult person to deal with,

amma zan wuce maka gaba dan ganin komai Ya daidaita

Na katse wayan sannan na fito falo na iske sis na zauna kusa da ita,

na Kira sunan ta da sanyin murya
Nifa banga abin damuwa ba atleast da kin tsaya kin saurare shi ko dan shakuwa da kukayi da juna
A masayinki na barrister bai kamata Kiyi judging Nashi by his physical appearance ba

Ki bashi dama na biyu dan Allah ki saurare shi ki san abin da yake damun sa
Kinga ta hakane zai gane baki guje shi don darurar da ke damunsa ba
Sai ki barwa Allaah zabi
Kafin ma inkarasa magana,
ta katseni cikin tsawa tare da fadin sannu uwata lallai kam kin girma dole ki tsaramun yadda zan tafiyantar da rayuwa ta
me kike nufi ne so kike in kuma sauraron shi ya kuma batamun Lokaci,

duba fa kigani akan shi na rabu da dukkan masoyana
AI shi ma ma yaudari ne tunda muka hadu da shi bai taba gayamun shi musaki ne ba
Sai ma kasheni da kyawawan picture na shi
No wonder bai taba turomun picture da yake tsaye ba
cikin girgiza Kai ta ce now I guess

*yusuf* ka yaudara ni bazan kuma manta ka ba a shafikan rayuwa na
Tana cikin wannan

zancen sai ga kawarta *Bilah* ta shigo tare da sallama kasancewar bamu rufe kofan ba,

saboda dukkan mu hankalinmu a tashe yake,

da murnan ta da hayaniya ta shigo tare da fadin Betsy how far how is guy doing kasance cewar ta sanar mata yau zasu hadu da *yusuf*

Cikin yatsina fuska ta ce ke dai kawata kyaleni da abin da yake damuna
Cikin rausayar da ido da mamaki cike cikin idanun ta ta ce ban ganeba
Kar dai ki cemun yahoo boys he is not real?

tajuyo Tana fuskantar ido cikin ido...

ta ce hmm kawata ai gwara yahoo boys the man am talking about is crippled can u imagine ta karasa magananta cikin jimamin abin
*Bilah* cikin rashin fahimtar maganan sis ta ce bangane ba kawata dan cireni a duhu kina nufin *yusuf* din ne ke zaune bisa keken guragu

Does that mean bashi da kafa am sorry to say gurgu kenan kike nufi, if I didn't mistaken

cikin girgiza Kai ta ce wallahi ko daya bakiyi kuskure ba in ta Kaita maki ,
Muna zuwa gidan da ya kwatanta mana toh kafin nashigo gidan jiki na ke bani
bisa yanayin gidan ma tukun balle da muka shiga
ko minti daya nakasa yi saboda am desperately shocked
*Bilah* ta nisa cikin dogon numfashi

Ta Kama hannayan ta duka biyu, sannan ta ce
Haba dear na, Meye na daga hankalin ki akan wannan this is the same person you madly in love with
As for me if love is involved his situation is not Matter...
Wannan darura ne kuma zai iya fadawa kan kowa

hey *Bilah* hold it ba fa shawara nake nema ba,

idan ke zaki iya toh ni bazan iya ba so watch your mouth...cikin

murmushi ta ce yi hakuri kawata duk mubar wannan zancen tun da na lura baki so

Allaah ya zaba mana mafi alkhairi
Duk muka amsa da Aameen
ni da Nike tun zuwan *Bilah* ban furta komai ba sanin da nayi magana ta zai kawo matsala sai na tsuke baki na

ina cikin tunanin rayuwar ta mu gaskiya akwai tsarkakiya da ban Al'ajabi da jimami buri na kuwa bai wuce sanin abin da na fito nema ba...

Ina cikin tunanin sai na tsikayi kiran *yusuf* ba kadan ba kiran Ya tsora ta ni,
saboda *Aunty maryam* Sam batasan nadau number wayarsa ba

da hankali nadau wayar nasanya akunnena tare da mikewa tsaye don shiga bedroom waye ne ke kiranki tambayar da tamun Ya girgiza ni,

ban kuma san amsar da zan bata ba, kawai nace kawata ce tare da shigewa ciki ban tsaya naji Mai take fadi ba....






*comment vote and share*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐



*WACECE NI*





✍🏼 Written by


*fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
wattpad teemacool2020


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation






*page* 4⃣



Ina shiga bedroom tare da amsa sallamar *yusuf* cikin fadin don Allaah karufamun asiri *auntie* fa batasan munyi waya da kai ba

Kuma sanin hakan zai iya ruguza komai na ce kabamu kwana biyu within that time may be ta sauko kaga bazamu sha wahalar shawo kanta ba
So kayi hakuri ka daina Kirana ...

cikin
marairaice murya yace nasani Lil sis kuma na gode da kulawarki gareni
Bazan kuma kiranki ba,na maki alkawari sai bayan kwana biyu da kika bukata.

Na nisa, sannan na ce toh thanks sai munyi waya na katse wayan.sannan najawo laptop dina na bude na sanya password, yana gama yin booting sabbin sakonni ne suka dinga shigowa ..banbi ta kansu ba nayi typing through amazon don haka bansamu wahalar samun web site din ba.

finding na, sun jeromun kusan tube number dubu da wani abu, cikin jerin numbers din tube number 489 dama shi nake nema, kuma Alhamdulillah sai gashi na samu cikin sauki...

na sake searching 489 din sai ga bayanai da sunan bearer din tube sun kawomun komai na kwafesu...sai da nayi
nazari sosai akai sannan na rubuta bayani Kamar haka...

My name is zaratun I was born in San Francisco my mother was Nigerian by birth. I am looking for tube 489 bearer whenever you are please Dad I am in need of you please...you can reach me on my fb page or through my email

sai da nagama nazarin rubutun sannan na dinga watsawa dukkan website din San Francisco Birmingham sannan local and international social media Kamar fb, YouTube, twitter da duk whatsApp group da nake ciki na diaspora....

Na mike tsaye tare da cire riga na na daura towel sai da nayi scrubbing jiki na da milk and honey scrub sannan na shiga bathroom na sake shower akaina domin yanayin garin akwai dan zafi na matsa milk and honey gold shampoo sai da na wanke sosai, sannan na kuma wanke wa da conditioner.
duka products na oriflame ne.
organic products ne suna da kyau ga kamshi ga gyara jiki yayi smooth ga yanayin jikina color African American ne....
na gama wanka sai na dauro alwala nafito daidai *Auntie* kuma ta shigo tare da fadin ki fito muyi sallah magariba ta gabato sosai nace toh gani nan fitowa,sauri sauri na shafa Mai loving care gaskiya kamshin mai din yana burgeni..

dogon riga Marar nawi nasanya tare da hijabi sannan na fito falo jam'i mukayi, bayan mun idar da sallah sai ga cook tana tambayar inyi serving abincin ne ko sai anjima zaku ci?

na dago kaina ina fuskantar *Auntie* Kiyi amma kayan ganye Sufi yawa kadan zaki zuba. tace toh,tare da zuwa darning table...
Muna cin abinci ina bata labarin duk abubuwan da nayi tun shigana bedroom ta danyi murmushi,tare da fadin wish you best of luck Allaah kuma yawuce maki gaba.
na ce Aameen aunty ki tayani da addu'a in sha Allaah my Lil kullum kina cikin addu'o'i na

naji dadin kalamanta sosai...
Na kama hannayenta duka biyu na fuskance ta ido cikin ido sannan na ce *Auntie* na please ki saurari *yusuf* mana koda na minti biyu ne idan yaso sai ki basa hakuri, Kinga idan kikayi haka zaiji dadi koda rabuwar ne ta wannan hanya zaifi kyau....

Tayi shiru Kamar bazata mayarmun answer ba. tadai tsareni da manyan idanunta har na tsorata, sai naji ta ce, my Lil gaskiya kina da tausayi I love that, but don't you ever to talk to me about that man again. I don't want to hear even his name, wannan shi ne kashedi na karshe da zan maki.you knew am older than you kuma kinsan,nasan abinda nakeyi so you have to be careful...daga wannan
bata kuma Kara cewa komai ba.
Nima nayi shiru sannan na ce kiyi hakuri zan kuma kiyaye bazan kuma yi maki maganar shi ba...munyi shiru sai na

Mike nazo na kwanta akan 3 setter na dau waya ta tare da danna number uncle *Anas*, naci sa'a ringing na farko yayi receiving ina murna na ce gaskiya my uncle yau naci sa'a....

daga can uncle ma murmushin yake Ya ce Ya hayatie kina raina kuma ina kan danna wayar ne sai kuma ga kiranki
na tura baki Kamar ina gaban shi cikin murya Kamar zanyi kuka na ce missing you and home a lot wallahi,
duk na gaji da garin ma domin ina cikin kyawarku gaba daya...

shima cikin jingina Kai ya ce muma Muna missing dinku, zaku ganmu idan yara suka samu hutu. kafin nan zan danyi tafiya na dawo ku Kular mun da kanku....na ce in sha Allaah kuma ka tayani da addu'a Muna Kai naga post naki sosai da sosai nagani kuma ana comments Allaah yasa sakon ya 'iso gunda ake bukata....

Na ce Aameen uncle nagode sosai my regards to all ya ce toh sannan Ya katse wayan.....
na juwo na ce uncle *Anas* yana gaisheki cikin girgiza Kai ta ce ina ansawa gaskiya munyi missing dinsu suyi kokari su zo mana....


Asalin labarin birnin maiduguri garin shehu
Alhaji modu tayyib sanannen mutum ne, Wanda Ya rike mukamin ambassador,ba sau adadi daga wannan country zuwa wannan country.Allaah ya arzurta shi da yara uku kawai, mace daya da maza biyu Wanda suka haihu da hajja fanna babban dansu shi ne *mustapha* sai *Anas* da karamarsu *yakaka* *abduram*
wadda ta kasance ita ce mahaifiya ta.....

family mu kaf 'yan maiduguri ne, suna zaune a unguwar shehuri north,

amma alhaji modu tayyib baitaba zama ko na wata daya ba a maiduguri kasancewar sa jakadan kasashe ma bambanta
ambashi high
commissioner to U. S. A
a garin San Francisco suka zauna...a lokacin
mahaifiya ta bata wuce shekara bakwai ba...kasancewar *mustapha* da *Anas* an maida su Nigeria don yin haddan Quran. yakasance *yakaka* ta zama ita daya a gidan sai ma'aikata
ranar da kaf family mu bazasu mantawa shi ba shi ne ranar da ba'asan ko wayene ba da bakaken kaya fuska arufe ba'asan ta ina yashigo gidan ba *hajja fanna* da ta ganshi ta yunkura tare da karma ihu sai alhaji modu Ya sanya hannu ya toshe bakinta, daga ita har shi ganin mutumin suke cike da tsananin tsoro. shiko mutumin rike yake da silent 🔫 pistol Ya seta daidai kan............

*wannan part na labari true life story ne daga nan har labarin zaratun sun faru da gaske ne sai dan gyara da nayiwa wadansu wurare*

gaskiya comments dinku shi zai karamun karfin gwiwa

share

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐



*WACECE NI*


✍🏼 by


*fateema Muhammad Suleiman*
[email protected]
teemacool2020




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*Readers nayi matukar farin ciki da comments*
*Wannan shi yasanya ni* *kwarin gwiwar cigaba da rubutun Ana tare*



*page* 5⃣&6⃣

Babu Wanda yaji Harbin bindugar sai fadowar mijin na ta tagani, jina-jina cikin jini,babu mutumin babu dalilin shi awurin Kamar layar zana ya bace bat...

Tashin hankali da rudani da kuma kidima kam, hajja fanna ta ganshi a wannan rana da ta kasa mantawa a rayuwar ta.

Jami'an FBI sunyi matukar buncike, amma ankasa gano wanda yayi wannan kisa.

Ankai gawar asibiti domin gudanar da binciken likitoci sun cire blade kuma sun baiwa jam'i an tsaro .

sannan akawuce da shi mutuary...
Embassy sun sanya hannu domin maido shi Nigeria.

bayan anyi arrangements din zuwan tare da iyalan shi,
Duk wani mai imani idan yaga *hajja* *fanna* dole Ya tausaya mata ckin kwana uku duk ta zube Kamar ba ita ba dama haka rayuwa take.

Mr *suhaib* wani makocin su mutumin Pakistan ne, kuma suna zumunci sosai.

kasancewar *yakaka* da yaran shi suna makaranta daya kuma sa'ani ne da yarinyar shi mai suna *vaishali* sunyi matukar shakuwa da juna.


tunda akayi mutuwar da taga mahaifinta cikin jini taki zama agidansu...

Sai gashi rana daya kaddara zata rabasu daga yaran har manya kuka sukeyi...

Mr *suhaib* ya nemi da hajja *fanna* tabar musu *yakaka* ta gama primary six sai a maido ta Nigerian,tunda 'yan watanni yasaura musu sugama.

idan yaso dukkansu sai su zo Nigeria da iyalansa don suma suna son ganin yanayin Nigeria din...


Ta ce toh amma zan nema izinin iyayenta acen idan sun amince da haka ni bani da matsala.

Mr suhaib yaji dadin bayanan ta yayi mata godiya tare sake ban hakuri, sannan Ya koma gidansa...


hakan kuwa akayi anbar *yakaka* awajen Mr *suhaib* domin hajja fanna ta gamsu da tarbiyansa tun zamansu da shi bashi da matsala, kuma suna kula da addini sosai...

sun barta da sharadin tana gama primary school za 'a maido ta Nigeria.

mr *suhaib* Ya jinjina Kai tare fadin cewa in sha Allaah mune ma zamu kawo maku ita da kammu...
Haka rayuwa ta kasance akwana a tashi babu wuya awurin Allaah...


*Yakaka* sun zana jarabawar shiga jss class
Kamar yadda *suhaib* Ya alkawarta sunyi shirin maido ta Nigeria.
Daga shi har iyalansa sunyi shirin yawon bude ido kasashe kafin su zo Nigeria...


jirgin ruwa zasubi sun fara yada zango a Jamaica,italy,maxico sannan suka wuce Australia.

duk acikin babban jirgin ruwan vaishali da yakaka wadda suka canja mata suna da *Aazeen* a cewarsu Mai kyau duk sun girma shekarunsu sha biyu, amma zaka dauka sunkai sha biyar.
'yan matan gwanin ban sha' awa,da daukan rai...

yau asabar duk suka shirya zasu dauki kananan jirgin ruwa kowa da abokin tafiyarsa.

yakasance *vaishali* da *Aazeen* jirgin su daya sai wanda zai tuka

Please Login or Register in order to submit comment