Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zajir yana watsamata kallon tsana..

"" wani kallon tuhuma tajefi bash dashi, "shikuwa mak'e k'afad'a yyi alamar ko ajikinsa".
Cikin takunsa na k'asaita had'e da isa yanufota...tana ganin haka ta fara ja da baya dan guduwa dan tasan halin yarima in and out..
" wata muguwar damk'a yyi mata ganin zata shige mota ,tana juyowa ya wanke ta da maruka lafiyayyu guda2wanda Saida jinta na wucin gadi yad'auke."
Wata mummunan shaka yyi mata Wanda atake idanunta suka fara ruwa ta sark'e da tari ba k'akk'autawa ,Wanda shikanshi bash yatsorata daganin irin wannan shak'ar da yarima yyiwa salma."
Saida yatabbatar ta jigatu yacika ta had'e da hankada ta kanta yabugi marfin motar,tasaki wani uban ihu....
"Cikin kakkausar murya ya nunata da yatsa yace ,natsaneki ,banason ki bana k'aunarki dana aureki gara natabbata bbu aure arayuwata. inaso kisani yasmeen ta fi k'arfinki ,yasmeen yar gatan ubangiji ce baki isa kiyi mata komai ba ,saidai sharrinki yakoma miki!
Wawiya fasik'a ke a tunanin ki na had'a yasmeen da wata y'a mace ?" Kinyi kuskuren da jakar brain d'inki kike tunanin yiwa yasmeen sharrin zina,inaso kisani nayarda da mamata dari bisa d'ari tanada tarbiyayya bakamar keba da Kika zubda darajarki atiti Kika zama kingi."koda kinci galaba akan wannan mugun gudirin naki to bazan rabu da yasmeen ba mata d'aya tamkar da 1000,bana aikata abu sainayi binkice,dan binkicen ne yasaka nagano yes kina nemanmu da sharri yanxun kuwa nazo hukuntaki,inafatan kin fahimta".
Zare ido kawai salma keyi dan duk ta ji yafitar mata arai ga zafin maganganunsa na cin fuska ga kuma wai zai hukunta ta ,kuma haushinta guda agaban bash aisai yarainata yaje yana yayata ta."
Bata gama tunanin ta ba taga yarima na k'ok'arin bude dan bucket d'in dke hannunsa
atsorace tace meye aciki?"wata uwar harara yyi mata yace acid ne zan zubamiki afuska in lalata fuskar da dama bleaching yagama watsawa kixama abintsoro ga lalatattun mata irinki....
Atsorace tace pls wlh natuba kada kamun haka na rok'ek'a wlh nafita arayuwarku...tsaki yarima yyi atsawace yace kadama ki fita indai kincika y'ar halak!amma fa yanxun zan zubamiki na zubawa banxa bbu abinda za'ayi ....kuka tafashe dashi ta duka k'asa tanabashi hkuri...bash ne yazo yajanye yarima dg gefenta ,cikin girmamawa yace y'allab'ai dan ALLAH badan niba karabu da ita tunda da alama tayi nadama intasake yunkurin hakan saikayimata abinda ka gadama,ajiyar zuciya yarima yyi dan dama ba watsamata zaiyiba burgace kawai dan yatsorata "ahankali yace ok nabarta dan ALLAH saidai inaso kisani duk inda Muka hadu Kika nuna kinsanni,saina wulakantaki sakarya wacce ta zubarda da mutuncinta a titi...
Yana fadin hakan fuuuuu yabar gun .
Kallonta bash yyi yace kiyi hkuri kada kiga naci amanarki ah ah na shiryune yanxun ina tsoron ALLAH, kema ALLAH yasa kigane gsky...
" yana kaiwa nan da sauri yabarta anan"
Yana zuwa gun dasukayi parking yasamu yarima acikin motar,nan yabude masa yashigo suka fara tafiya bbu mai mgn acikin su."
Can yarima yace gsky naji dad'in yadda ka shiryu,kuma na gode sosai da kasanar dani abinda salma kesan aikatawa!
Murmushi bash yyi yace ba komai.
Yarima yace aikin me kake yanxun?
Yace karatu nikeyi ina shekarar karshe sai inama wani tsaron shago inasamun nacin abinci..
Cikin tausayawa yarima ce ok b damuwa gobe kasameni a office dina zan samarmaka wani abun yi mai kwari,godiya bash yashiga yi bbu kakk'autawa tun kan yasan me za'abashi."
Adede k'ofar gidansu yarima ya ajesa,shikuma yyi yar tafiya kadan yatsaya yyi sallar la'asar sannan yayo gd...

*********

Yasmeen kuwa tana tashi dh baccin ta duba taga bbu yarima ,cikin jin haushi tace wato wayo yyimunko?"hmm zaidawone ai,tashi tayi ta yo wanka had'e da yin alwarla tayi sallah sannan ta shirya cikin purple din super exclusive Riga da zani tayi daurin daya fito da ita tayi kyau...

Harta zauna taji tanason shan furar ammi,amma me?"tasan wannan masifaffar tsohuwar tana sashen.

"Tashi tayi dan jitake inbatasha furarba ,kamar bazata iya baccin dareba".

Aiko tana zuwa ko tasameta hakimce akan kujera tayiwa tb k'uri kamar tanajin abinake cewa ,ammi na gefe kuyangi 2na matsa mata k'afa,sallama tayi cikin d'ar d'ar ,ammi ta amsa fuska asake nan yasmeen ta gaidasu ,wadda hjy babba ciki ciki ta amsa.ammi tace yayadai yasmeen kinyi shiru?" ahankali tace dama ammi zansha furane...tsaki hjy babba tayi tace oh to a can b'angarenku bbu ne saikin zo nan?"hmm gsky yarinyar nan da alama kingama dasu yodama jikar mlm,koda alhj tsoho yace wannan abar zai aurawa yarima nasan sai mlm yashiga yafito sun gama da.....ammice tace haba hjy dan ALLAH kidena hakan sbd cin fuska ne bbu dadi....

"Baki bude hjy babba tace banga laifinkiba angama dkene."

Ammi ta tsaida kuyanga guda dasuke shirin fita dg parlourn,tace ta dakko gidauniyar fura a frige.,,

"Yasmeen kuwa ko ajikinta da surutun hjy babba dan tasan dg gobe insha ALLAH zata tafi tabar musu gidan".

Karb'ar furar tayi ,ta aje gabanta tafara sha....jin sallamar yarima yasaka ta tafasa shan furar,dan yaje part din su bata can.

,,,,had'e rai yarima yyi had'e da yin kicin kicin da fuska sakamakon ganin hjy babba a parlourn, zama yyi yagaidasu ..tsaki hjy babba tayi tace ka rik'e abunka ,shiru yyi be tankataba,yakalli yasmeen yace my Princess ashe kina nan naduba bakyanan?
Turo baki tayi had'e da harararsa.
Murmushi yyi yace ninefa Prince dinki!tace eh d'in bakaine kayimun wayoba kayi tafiyarkaba ...azuciyarsa yace hmmm bakisan fitata alkhairi bace ba,amma afili sai yace fitarce tazama dole shiyasa my honey kiyi hkuri kinji tawan?"

Itadai ammi tana kallonsu,cike d burgewa da sha'awa dan tasan so ba karya bane ,ta fuskanci soyayya kamar haka gun me martaba Saida hjy babba ta tasota gaba waits mallake mata d'a ,Saida ya auri hjy rahama sannan ta barta tahuta shine yanxun kuma zata koma kan yarima..

Yarima yakalli yasmeen yace my honey zansha furar"make kafada tayi tace um um nidaya ammi tabamawa.dan murmushin gefen baki yyi had'e da matsawa kusada yasmeen yace nikuma nace sainasha b...maganar hjy babba ce tahana yarima kin ida maganarsa jiyyi tace oh ni halima wannan zamani bbu kunya ba tsoron ALLAH agabanmu da gyatumarka kuke wannan abu lallai bakuda kunya kuma yarinyar nan ta cuceni tabata maka tarbiyya tun....magana yarima keshirin yi ,ammi tayi masa alamar ah ah,afusace Yakama hannun yasmeen suna fita,yyinda ammi tasaka abisu da furar part din su.

"" Ahanya yarima yakalli yasmeen yace dg yanxun kada kisake zuwa part din ammi sai wannan masifaffar tsohuwar ta tafi kinji my honey nah?yar dariya yasmeen tayi tace nifa yaya yanxun nadena damuwa tunda kai baka canxamunba dan wani yacanxamun banajin komai..adedenan suka shige parlourn.

Suka tararda fura harta rugasu isowa kan carpet duka zauna yasmeen na tsakkiyar cinyoyinsa suna sha sna firarsu,knocking sukaji,yarima yace yesssss!aka shigo salis ne .

"Bayan sun gaisa,cikin tsokana salis yace to lailah d majnun,inkuna tare na luramanta wa d kowa kkeyi".

Yarima ya hararesa had'e da matse yasmeen gam datake shirin guduwa sbd salis,yace pls mlm yi tafiyarka banason takura lokacin iyalinane wannan.

Dariya salis yyi yace pls yasmeen kitaimakamin wlh kubra tak'i saurarena wlh,yafada fuska kalar tausayi.

" Ahankali yasmeen tace ka kiratane?"

"Yace eh yafi akirga amma bata peaking".

Cikin rada yasmeen tace wa yarima yaya pls bara naxo kaji ,ok yace had'e da saketa ta shige bed room dinta tanajin yarima na tsokanar salis..

Tana zuwa takira kubra ,kogaisawa basuyiba tace haba friend meye? haka wulakanci bbu kyau shine yaya salis yakiraki kikaki dagawa?

Ahankali kubra tace ke jamasa aji nayi ,nimafa yyimun ,tsaki yasmeen tayi tace to bari nasanar dashi hakan..d sauri tace ah ah yi hkuri pls zan daga kiransa ALLAH inmayimasa kwatancen gidanku.

Yar dariya yasmeen tayi tace oh anaso ana kaiwa kasuwa ,nan sukayi sallama, yasmeen ta je tasanar da salis cewa yakirata zata d'aga ,abinda yasa bata d'agaba ,bata daga bak'uwar number..

Cikin jin dadi salis yyi godiya had'e da hararar yarima ,yace to kaji kaimeyimun dariya,adaidai nan kubra ta d'aga kiran dan dama yasmeen na cewa yakira yyi calling d'inta,cikin xakuwa yace hellow baby yafad'a had'e da ficewarsa ,su yarima namasa dariya..

Kallon yasmeen yarima yyi yace baby muje nayi wanka bbu musu ta bisa tahada masa atare suka shige ta cud'asa sunata wassaninsu ,har aka kira magrib ,alwalla sukayi sannan duka fito ,yawuce masjeed,itakuma tayi tata agd...

Bedawoba sai da aka yi isha'i tukum yasamu yasmeen kwance tsakkiyar bed din sa dg ita sa yar have vest iya cibi da Dan mini siket..tana chat d friends d'inta....

Koda yaga hankalinta baya gunsa sai yahaye Samanta yakarbe wayar ,ihu tasaka itasaita karba,aiko yafara yimata cakulkuli sai dariya abinsu suke itama ta mirgina tadawo kansa ta ruk'a yimasa cakulkulin suna dariya dg nan salon yacanxa duka Lula wata duniyar...

Washe gari bayan sun gama kimtsawa,state duka fito dan gaisheda su ammi ya wuce office ita kuma skul dan yanxun itama da guards zata ruka zuwa skul din Wanda yajamusu kunne sosai akan su kula masa da ita..

Koda sukaje bbu kowa apart din ,parlourn Sarki suka wuce ,aiko nan suka sami hjy babba,ammi,mama,da lubna sai alhj tsoho zaune yana Jan casbaha.

Yana ganin su yyi murmushi, yace to Ku k'arasomana.

Sallama sukayi had'e da...


Share pls
AWESOME WRITER'S ASSO..๐Ÿฎ

(palace of excitation and pleasant writer's)

YARIMA ASHMAN
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ


Story & written by mmn fareesa

๐Ÿ…ฟ83&84

"" Sallama sukayi had'e da samun guri suka zauna.
bayan sun gama gaisawa alhj tsoho yyi ajiyar zuciya yace yasmeen!
Ta d'ago kanta had'e da amsawa ,yace kiyi hkuri kinji?" da abinda yafaru kidauka kamar bai faruba ,domin duk Wanda aka bawa hkuri to anxalinceshi."
"Ahankali tace babu komai ya wuce wlh,alh tsoho yace ALHMDLLH to ALLAH yyi muku albarka ,gaba d'aya akace ameen.
Kallon lubna yyi yace ke kuma marar mutunci nadawo gareki, kifita harkar yarinyar nan tun kafin iyayanki suyimiki baki...kibata hkuri yanxun!kinji kobakiji ba?" Yafad'a atsawace ,da sauri lubna tace naji,ta kalli yasmeen tace kiyi hkuri dan ALLAH da abinda yafaru "yasmeen tace ya wuce ,nan lubna ta rok'i Sarki d ammi gafara sukace sun yafe amma duk radda tasake shiga harkar yasmeen hmmm...

" nan alh tsoho yasallami kowa "yyinda hjy babba sai cika take tana batsewa,yakalleta yace halimaaaaaaa!
Halima !Halima!!

,,,har sau3 muddin Kika sake shiga shirgin yarannan wlh saina baki mamaki ,kitashi kishirya mu wuce gd yanxun.,,

Hjy babba baki ya mutu ,bata ce komaiba ta tashi tashige ciki dan hada shirginta su wuce gd...

** ** ** ** ** ** **

Su yarima kuwa suna fita,gun mota suka nufa ,gdn baya suka zauna shida yasmeen motar guards dinsa daban nabinsu abaya dan kai yasmeen skul shikuma yawuce office..

Yasmeen da kanta ke kan kafad'ar yarima" ahankali tace my Prince in antashi zanje gd na gaido ummana pls!

Murmushi yyi yace to my Princess, karfe nawa kke gama lecture's?

"Tace 1:00pm"

Yace ok to zanshigo gurin2:30gidan umma nima nagaida ita saimu dawo tare dan umman bataki bace ke d'aya "yafad'a had'e da Jan hancinta yana murmushi..

Itama ,hancinsa taja ,tace uhmm aidai narama ,kuma ai umman tafi ji dani akanka ai.

Hannunta ya matse yace ba kyau karya ,aixamuje atambayi umman kinyarda?"

"Tace eh"

Adede nan sukayi parking, yasmeen na k'ok'arin fita, Saida ya rungumota yyi mata kiss agoshi d kumatu.

"Ahankali yace kikulamun da kanki kinji Tawan?"

Cikin kissa tace to nawan nima haka,kuma banda kallon y'an mata,girgiza kai yyi yace in inatare da ke duk sauran mata muna matane kece mace kad'ai aguna .jinjina tayi masa had'e da dagamasa hannu har suka fice yyinda guards d'inta ketake mata baya ,nan tace su jirata zata gun lecture's..

Tana juyowa taga kubra namata murmushi, itama murmushi tayi tace Mrs salis ykk?"yar dariya kubra tayi tace uhmm wlh my one d'ina ya iya zuba love wlh gsky inbansami salis ba komai zai iya faruwa dani!

dariya yasmeen tayi ta mata tace oh friend sabon shiga kenan.

"Kubra tace hmm ai dace da masoyi dadi gareshi ...yasmeen ta katseta d cewa bbu abinda yakaishi dadi aduniya ,saiki rik'e salis dinki gam gam....

Suna gama lecture's yasmeen da guards d'inta sukayo gdnsu,saidaime?

Yasmeen ta sha mamaki ganin tun farkon shiga layin titine har kashe..bata auneba taga gidansu da tangamemen get harda bene ,zaro ido tayi cike d mamaki,sunayin parking agaban gdn tace suje ita yarima zaizo sukoma gida tare,nan ta fito ta tura get din gidan,get man zaune kan kujera ya kalli yasmeen yace hjy lfy?

Yasmeen tace banganeba?ina mutanen gdn ummana?

" asannan get man yagane cewa yar gidance,nan yace tana ciki,y'allab'ai ne yace saina tabbatarda kowanene zai shiga ciki umma tasan dashi..

Yasmeen tace hardani yasmeen? wanene y'allab'ai?

"da sauri ya sakko dg bisa kujerar yaduka had'e da cewa tubanake ran ginbiyya yadade,ALLAH shi taimake ki,wannan umarnin mai gidankine..

Wani farin ciki yasmeen ta ji had'e da k'arajin kaunar yarimanta dan yaga ma mata komai aduniya,murmushi tayi tace haba baba katashi kaji bb komai wlh..kudi ta fito yan 1000ajakarta batasan konawa bne tabashi yyita godiya.,,,,

Bayan ta wuce compound din gidan tabi wani dan corridor saigata a filin tsakar gd ,umma na zaune kan resting chair ga mai aikinta tana wanke wanke nan yasmeen tayi sallama d gudu taje tayi hugging din umma,sai murnar ganin juna suke nan suka shige ciki,bayan yasmeen ta gaishe da mai aikin..

Nan suka gaisa da Umma ,takawo mata wannan ta kawo mata wannan sai hidima take da ita..

Bayan ta zauna tace ina d'ana yarima,kai yasmeen wannan yaro ALLAH yyimasa albarka yasa yagama da duniya lfy...cikinjin dadi yasmeen tace ameen umma,amma nayi mamakin baki fadamun ba my Prince ya gyara gidan nan ?"

Murmushi umma ta yi tace hakane wlh ASHMAN ne yace kada a afadamiki shidan ALLAH yyi ,ke nifa yanxun ko aiki banayi yadaukarmin me aiki ga store yacikamun da abinci d cefane kai nidai sai hamdala shigowar yaran nan rayuwarmu alherine ,ALLAH Sarki YARIMA ASHMAN dan albarka kenan fatan shine yasmeen ALLAH yabaku zuriya d'aiyiba....kin k'arasawa tayi sbd wayarta na ringing d'agawa tayi had'e da yin sallama tace Omar faruq hakan take kiransa intaso nishad'i...

Murmushi yasmeen tayi tace Ashe yah Omar ne bani mugaisa!bata wayar tayi Takara akunnanta ,bayan sun gaisa yace my baby nanda 2weeks zanxo hutun shekara ina my girl dina take?

Yar dariya tayi tace hmm tana lfy ,yace pls ta taba yimiki mgn ta ?"

Tace eh

Yace d gaske ?dariya tayi tace inharkadawo namaka promise zanzo da ita agidan nan Ku shirya kanku..

Ahankali yace to ,amma umma najinmu ko?dariya tayi tace eh mana ,saurin kashe kiran yyi,umma tayi dariya tace oh Omar akwai kunya to ALLAH yatabbatar da alkhairi koma wacece..

Yasmeen tace ,ameen nan ta sanar da ita yarima na hanya zaixo sutafi tare yagaisheta,bari tayi sallah..umma tace ai gidan nan ba bakwansa bne asati yazo sau 3ko2yanxun haka furarsa na frige da tuwo akula dan dama yau rabonda da gidan nan kwana3ina tunanin xuwansa..

Cikin jin dadi yasmeen tace Ashe d gaske yake dayace kinfi jidashi akaina?murmushi umma tayi tace tabbas ...

Tashi yasmeen tayi ta na kukan shagwaba ta fita tayo alwarla tazo ta yi sallar azahar..

Zama tayi tace umma mekikadafa?"tace d'an wake ne ,bars akamiki,fita tayi tadawo da plate shake da d'an wake yasha cabbage da kwai dafaffe ga man kuli d yaji..

Yasmeen nasaka hannunta yarima yyi sallama...

Share pls
AWESOME WRITER'S ASSO..๐Ÿฎ


(palace of excitation and pleasant writer's)


YARIMA ASHMAN
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ


Story &written by mmn fareesa


Ina mik'a godiya ta ga masu kirana da turomun text nagode sosae ana mugun tare๐Ÿค๐Ÿค


๐Ÿ…ฟ87&88

Batayi fushiba tabi bayansa har bed room d'in sa, ko juyowa baiyiba yakalleta kayansa yake k'ok'arin ragewa yyi wanka.
"Ahankali taje ta rungumesa tabaya" tana kukan shagwaba cikin kissa ta wani langabe kanta tace Yayana kayi hkuri pls wlh tafiyar tafitarmun arai nafasa bazan jure zama kana fushi dani ba....tureta yyi dg jikin sa cikin tsawa yace kirabu dani kawai tunda Sarki yagama mgn aishikenan inkin tashi kiyi shekara acan ko ki dauwama a can aidama nibaki damu dani ba ,kinason murabu ko?"dama na matsamiki"tunda dakin damu dani bazakiso ko yini daya muyi bama tareba,ninasan bakya sona nine keta haukan sonki ...kuka tafashe dashi tace pls kada kayimun wannan fahimtar kasaurareni aihace nafasa tafiyarko tunda Wanda nike zaune danshi ransa bayaso gara na hakura...gefenta yabi yashige bath room.....
Wani bacin rai yasmeen taji wato bazai hkuraba yakullaceta ko?"
Fita tayi jiki asanyaye,bed room d'in ta tashige tasami wayarta na ringin, kashewa zatayi saitaga yah Omar ne "ahankali tad'aga had'e da yin sallama,bayan sun gaisa yace oh baby bakisan yau nadawo bne?"
Tace ah ah
"Yace ok kinsani kenan?" Kika k'i kirana koxuwa tarbata!murmushin yak'e tayi tace to tuba nake yayanah gobe insha ALLAH zamuzo nida Maryam d'inka..
"Lumshe ido yyi yace harnaji dadi gsky kin kyauta dan nak'agara naganta."
Murmushi tayi sukayi sallama.niyar kwanciya take taji knock tashi tayi tabude,jakkadiya ce tace taje ammi nakiranta..
"To tace tasaka alkyabba tafito,saidai kallo1zakamata kasan tna cikin damuwa."
Yana isa part din ta sami ammi zaune ,k'afafunta kan tuntu,kuyangi na mata tausa ak'afar..
Zama yasmeen tayi suka gaisa saidai tun shigowarta ammi ta fahimci tna cikin damuwa..sallamar kuyangin tayi suka fice dg parlourn.

"Ahankali ammi tace dama akan tafiyarkine ,shine nace dame dame kike bukata dazakiyi tsaraba dashi?"

Kanta aduk'e tace ah ah ammi ai nafasa tafiyar ma gsky.

"da sauri tace meyasa?"

"Tace bbu komai"

Ammi tace wato yasmeen nikike jiwa kunya ko nauyi zance?"bazaki fadamun damuwarki ba?

Tana hawaye tace ammi wlh nahakura da tafiyarnan bazanyiba tunda adalilinta mijina na fushi dani ,gara nabarta tunda Wanda nike zaune karkashinsa ransa bayaso ammi gara nabi abinda yakeso kuma wlh har cikin raina banji haushiba,kuma da nasan hakan zata faru wlh bazanyi maganar tafiyarba amma dan ALLAH ammi kisanar da Sarki cewa nafasa tafiyar sai wani lokaci yanxun inada exams ne na manta nayi mgnar tafiyar..

Shiru ammi tayi tanajin tausayinsa yasmeen wadda cikin maganarta bbu rashin kunya ko bakar mgn gsky yarima ne kyautaba dukda shima sontane yasakashi kinson taje wani guri ta d'ad'e..

"Ahankali tace kiyi shiru kidena kuka kinji yasmeen?" kije kirarrashe sa kushirya zakije insha ALLAH, tashi yasmeen tayi tace to ammi ngd ,tafice had'e da dafe kanta dan yana mugun Sara mata...

** ** **
Yarima kuwa haka yyi wankan xuciyarsa bbu dadi,wani gefen kuma bayason kukanta dan yasan k'ila yanxun tanacan tana kukanta...

Haka yagama shirinsa ,cikin milk din shadda tasha aiki da Orange din zare ga wani fitinan kamshi dke tashi ajikinsa ,yyi kyau saidai fuskar nan bbu annuri ko kad'an..

"Jiyayi bayasan cin komai Co's yasmeen d'in sa bata ciba,part din ammi yawuce."

Yana zuwa yaga ammi ta kallesa ta d'auke kai,afili yace yah salam ammi naga kema fushi kike dani menayi?"

Tsaki tayi tace bansaniba!shine kayi fushi da yasmeen duk ta shiga damuwa tace tafasa tafiyar,ka kyauta kenan?"

Me tace naji mata?"

Nan ammi tasanar dashi yadda ta takurata harta fadamata.

Ajiyar zuciya yarima yyi yanajin kaunar matarsa da wani sonta nasake shigarsa hade da tausayinta dan yana mamakin ita batayi fushi dashiba burinta shi yadena fushi da ita ...muryar ammi ta katsesa gun cewa to yanxun Dan ALLAH kaje ka rarrasheta Ku shirya kaji my son?"

Murmushi yyi yace to amminah yafita.


Part d'insu ya wuce ,kaitseye bed room d'in yasmeen yanufa,yana murd'a k'ofar yajiyo kakarin amanta a toilet,arazane yashige toilet din yasameta ta tallabe kai tanata kwaraya amai tana hawaye,kamar zata amaye abinda ke cikin cikinta baki d'aya...

da sauri ya tallabeta yanajin tausayinta ,sai sannu yaketa mata"

Tana idarwa yaruka dobo ruwa d hannunsa yana wankemata baki d fuska ,ita kuwa zai maida numfashi take..

Yana gama wanke mata ,yasabota kan kafadarsa ,shima duk jikinsa yabaci da ruwa,kan bed yazauna had'e da rungumeta ajikinsa..

"Ahankali tace Yayana pls kadai na fushi dani kada mala'iku su tsinemun wlh na fasa tafiyar."

Rufe mata baki yyi yace, baby nah na hkura ainadena fushin ,munshirya ko ?"aiyawuce kawaidai banji dad'i bne kada kisake kinji matata?"

Cikin dadi tace to mijina na gode insha ALLAH bazan komaba...

Fuskarta yad'ago yace to yimun murmushi! kallonsa tayi idocikin ido tayi masa murmushi hade da cewa my Prince 2milion bucket can not wash your love in my heart...
Cikin jin dad'in kalamanta yace thank you my real one I'm pround of you, you are my special one in my life...

Hade bakinsa tayi da nata, ta zura masa lallausan harshenta bbu gardama yacafke yana sucking...

Wai numfashi suke mayarwa ,yana k'ok'arin tura hannunsa arigarta...jiyyi tayi saurin zare bakinta dg nasa d gudu ta nufi toilet, asukwane yabita cikin damuwa had'e da tausayinta..

Kamata yyi har ta idar ,yataimaka mata ta wanke baki da fuskarta ya dakkota suka fito,kan bed ya ajeta yaciromata gown ta atamfa "ahankali yacire na jikinta yacanxa mata ..

Cikin tausayi ya shafa fuskarta yace my Princess meke damunki?" dama bakda lfy ne?"

Ahankali tace ah ah ,nidai kawai d'zun bayan nadawo dg gun ammi ina kwance naji tashin zuciya dama kuma kaina namun ciwo..


Lumshe ido yyi yace oh ALLAH yabaki lfy my Princess kamar ciwon yadawo kaina ,yafad'a cikin damuwa,wayarsa yafito ykira doctor khadija(itace likitar dke kulada duk Wanda bashida lfy amasarautar) yace gashinan yanxun zai kawo yasmeen batajin dadi.

Yana kashe wayar yaduka had'e da cewa yasmeen ta hau bayansa su tafi,cikin tsantsar mamakinsa da al'ajabinsa dan yau ta k'ara tabbatarwa kanta yarima yana mata SO bana wasaba kuma natane ita d'aya ,amma bazata yarda ba ga barori d bayi suna kallon su Aida kuny...katseta yyi da cewa kihau princess dina mana!


"Ahankali tace innaho amai zanyi kadai kamani muje,bbu musu yatallabeta suka nufi hospital din dke masarautar ...

Babu bata lokaci ,bayan doctor khadija ta mata tambayoyi ta hau treatment d'inta..

Nan tabata wata roba tace taje tayo fitsari " tashi tayi dg kan cinyarsa ta nufi toilet ,shima yamike dan binta ,doctor ta tsaidashi..

Tana sha'awar yadda suke kulada junansu dakuma soyayyarsu.

"Bayan ta fito ,nan ta auna fitsarin atake tagane yasmeen na daukeka d ciki ,shiru tayi tace ta kwanta ayi mata scanning b musu ta kwanta akayi mata.

Murmushi doctor tayi dan cikin duka sati3 ne kacal.

Kallon yarima tayi da yatsareta da ido tace ....


Share pls
AWESOME WRITER'S ASSO..๐Ÿฎ


(palace of excitation and pleasant writer's)

YARIMA ASHMAN
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ


Story & written by mmn fareesa


๐Ÿ…ฟ89&90


Kallon yarima ta yi da yatsareta da ido tace to masha ALLAH Alhmdllh, yasmeen nad'auke da juna biyu na 3weeks....what...yarima yyi exclaiming, doctor tace yes ciki ne da ita...wani uban ihun murna yarima yyi had'e da sungumar yasmeen yad'agata sama yana juyi da ita yana rawar murna,cikin tsantsar farinciki yace ALLAH nagode maka da ka nunamin wannan rana princess yau masucemiki juya zasuji kunya...itama yasmeen farinciki ne kwance fal aranta da fuskarta ALLAH yabasu abinda sukeso sai godiya ,fuskarsa yake k'okarin hadawa da tata sai sabbatun farinciki yake ....doctor tayi saurin yin gyaran murya gudun kada ayi tab'argaza agabanta ,garama tayi masa mgn dan talura fitina ne dashi kada yamatsa mata cikin yazube.
"Kallonta sukayi ,murmushi tayi tace to sauketa kuzauna nayimuku bayanin yadda zaku kula da lafiyar babyn naku..
" babu musu yasauketa yazauna ,tad'ale kan cinyarsa yayinda bakunansu sunki rufuwa".nantabasu shawarwarin kanyadda za'a kula da da lafiyar yasmeen abata duk wani abu datace tanaso namasu ciki,kuma su jinkirta yawan yin sex sai cikin yyi kwari .
"Sun gamsu sosai da bayaninta ,dg bisani ,yarima yace yabata kyautar mota tukwuicinta ne.rissinawa doctor tayi tana zuba godiya bbu iyaka..
" ita kuwa Yasmin dama yaya lafiyar giwa tayi shagwaba da tab'ara bbu dalili Balle yanzun dake da dalili,sai ta wani shagwabe ,shikuwa sai wani nan nan yakeda ita...
Wayarsa yafito had'e da sabar yasmeen akafad'arsa yasaka kira bbu bata lokaci nayi yyi sallama had'e da cewa tsoho mai ran karfe Kaine farkon yiwa wannan albishir dankuma kafi kowa cancanta ,yasmeen nada juna biyu... Wlhy kuwa ,eh to kafadawa wannan matar taka kotabarmu musarara yanxun tasan yasmeen dina ba juya bace....dariya naga yyi had'e da cewa muna godiya dan tsohonmu ALLAH yabar mana kai."
Kashe wayar yyi ,suka ida barin cikin asibitin ,part din ammi suka nufa."ahanya yace my Princess kuma mommy n babynmu me kikeso kici?"pls gayamun kin ji ,turo baki tayi tace nidai sai munje gun ammi nah".yar dariya yyi yace yanxun zankira umma da Omar har da ma bash nagayamusu nakusa zama daddy...cikin mamakinsa tace bash kuma?"yace yes labarin maitsawone saimun zauna zan sanar dke dan yanxun haka bash ne manager na gidan manki dana bud'e miki a shekaran jiya kema kirika Sana'a kitaimaki bayin ALLAH.. wani dad'i da farinciki Yasmin taji wai itace keda gidan mai nata na kanta shin meyarage mata zata nema aduniya?"bbu gashi kuma yau taga ne tanada ciki ita ba juya bace kamar yadda wasu ke cewa ikon ALLAH kenan.
"Ashe ko lokacin da ake mata gorin ma

Please Login or Register in order to submit comment