Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar redio yamik'awa umma ta karba yace duk sadda Kawu bala yaxo gidan nan ki tabbatar kin fito da ita kinsaka a hijan sannan Kuyi mgn yafad'a had'e da nuna mata wani gefe yace nan zata latsa in sun gama ta sake latsawa.

Umma tace to had'e da godiya da saka ma yarima albarka..adedenan Yahaya yashigo.

" nan umma ta sanar dashi gidan Kawu bala zai kai yarima yace to had'e da kai gaosuwarsa gun yarima suka fita sai godiya da saka albarka umma keyi.

Sai bayan sun tafi umma ta lura da radar yan dubu guda2 da yarima ya aje girgiza kai tayi tace basu gajiya da hidima dg shi har iyayansa ,amma da nagani wlh bazan karbaba abun yyi yawa.

Ak'ofar gida kuwa ,yarima yasami sarkin gd da driver sunajiransa nan shida Yahaya suka shige ,Yahaya yadi anguwa r dazsu nufa han suka nufi can.

Sunayin parking agaban gdn Kawu bala ,yarima yace wa Yahaya yaje yyi masa sallama da Kawu bala..

Nan sarkin gd yafito da wata kujera yarima yazauna mutanan anguwar sai kallonsu ake adaidai nan Yahaya da Kawu bala suka fito dg gidan bala.....

Share pls


AWESOME WRITER'S ASSO..🏮

(palace of excitation and pleasant writers)

YARIMA ASHMAN
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

story & written by mmn fareesa

🅿43&44

Wani mummunan fad'uwar gaba Kawu bala yaji sakamakon ganin yarima hakimce akan kujera agaban gdn sa."
Tambayar kansa yake me yaronnann yazo nema agunsa? wata zuciyar tace kasan ko gaidakai yazoyi matsayinka na sirikinsa."
girgiza kansa yyi yace akwai wata a k'asa ,gun yarima ya isa bbu ko sallama kai tsaye yace yaro lfy me kazo nema aguna?"
Yarima yyi murmushnsa na k'asaita yace ,Niko nazo Neman babban abu kuma muhimmi agunka,ak'agare Kwu bala yace inajinka.
"Yarima yakafesa da ido yana nazartarsa dan haryagano wani abu atare dashi" ahankali yace shekara2 dasuka wuce k'aninka yarasu ko?
atake wata zufa ta yankowa Kawu bala yace eh mene natambaya Wanda yamutu ai yarigada yamutu.
Yarima yad'aga kafad'a yace aganinka kenan dan ni yanxun ma aguna mutuwar sabuwace!
Kawu bala yace to mekake nufine da hakan ai d'an uwanane nike da iko akan komai ,kuma tunda iyalinsa sunce sun bari ga ALLAH bashikenanba.
"Murmushi yarima yyi yace hakanma yyi amma amatsayinsa na d'an k'asa yanada hakkin daza ayi masa bincike agane sanadiyar mutuwarsa.
Afusace bala yace to ni me nawa aciki dazakazo har k'ofar gidana kana gayamun mgn oho kaida mariyar kuka had'a baki kuyimun sharri kuce Nina kasheshi ko me?shiru yarima yyi dan yagama fahimtar abinda yazo fahimta ,tashi yyi yace to tunda baza kabari muyi mgn ba inkaje gaban hukuma kayi bayani.
" wani ihu Kawu bala yyi yace ohni nashi ga ukku dan anganni talaka za'amun sharri ,"ALLAH ya isa tsakanina da Mariya...adedenan bash yazo zai shiga gd yanata shan sigari ,kawai kunnuwansa da idanunsa suka ankarar dashi,gunsu yanufa dan yalura da yarima batare da guards dinsa yakeba.
"Cikin ixxa bash yaja babansa gefe hade da cewa wa Nene yasaka kuka haka ?gaban bainar jama 'a dan har mutane sun fara taruwa suna kallon su.
Kawu bala yanuna yarima yace ga Wanda keshirin cimun mutunci da girmana da komai a...yarima yakatsesa da cewa kayi sabo babba dakace wai da girmanka ,ina girman yake anan..afusace bash yawatsa yarima wani mugun kallo yace kai dakata ,nan a anguwarmu kazo ,kuma wadanda kadogara dasu suke taremaka fad'a ai basu biyokaba kaga kamun ba daidaiba saina suburbudaka anan...sarkkin gd da driver ne suka katse bash da cewa kai wawa hattara kasan inda kake mgn yarima mai jiran gado yafi karfin hakan..azuciye yarima yadakatar dasu hade da matsawa gab da bash ,ya kallesa sama da k'asa yatsartar da yawu, yaro yarone,yaro besan wutaba saiyataka zannuna maka kalata,dan ko agaba kabada labarin hakan dukda ni yarima nafi karfin hada jiki da k'azami irinka amma zankoyamaka hankali tukum nasakaka amota naje narufe narufe banxa...
aituni bash jikinsa yafara kirma dan yagane cewa yad'ebo ruwan dafa kansa...be auneba yaji yarima yasaka k'afarsa me takalmi sawu ciki ya tad'osa yafad'i k'asa warwas, yasaka kafarsa yatakasa iya k'arfinsa ,atake bash yasaki k'ara ...
Nanfa mutanan anguwa sukafara taruwa suna kallo sunajin dadi dan dama bash ya ishesu da halin akuyancinsa ..shikuwa Kawu bala kamar yyi kuka dan bakin ciki dan har yafara jin dadi bash zai suburbudi yarima yakunyatasa ,saigashi Ashe rabon shi yariman ya kunyatasu.
Bbu bata lokaci yarima yacigaba da suburbudar bash duk yakumbura masa fuska dg bisani yayima sargin gd nuni asaka bash a boot din mota,nan yazo yaci ka aikin yarima,Kawu bala kuwa kamar yafashe dan bakin ciki,nan yarima sukabar anguwa r afusace...

A police station suka wuce ,yarima yace su ladabtar masa da bash,sannan suka wuce gd...

*********
Yasmeen kuwa duk atsorace take dan batasan wane hukunci yarima zai yanke mataba,koda tadawo dg skul part din ta ta nufa Saida akayi isha'i takira ummanta,nan ta sanar da ita yarima yazo kuma zai fara binkice akan mutuwar abbansu harda kudin da ya ajemata duk tafadawa yasmeen. "wani irin yanayi ta tsintsi kanta duk saitaji dama batayi masa wannan muguntarba. Jiki a sanyaye sukayi sallama .sannan taje part din ammi dan su gaisa ,shima atsaitsaeye suka gaisa ta fito tanata sauri dan kada su hade da yarima .....jitayi an rungumota tabaya, kobata dubaba tasan yarimane sbd k'amshin turaren sa dataji...

" ahankali tace pls yaya kayi hkuri nabari wlh bazan sakeba kajiiiii!"

Shima a hankali yace nibabu abinda zanmiki,muje d'akina kimun tausa,zanyi bacci badan tasoba tace to dan atunaninta wayo yyi mata..

Saketa yyi yace muje,binsa tayi suna tafiya,suna zuwa Dede k'ofar part dinsa ta zura aguje hade da cewa ALLAH yaya mugunta zakamun bazanxoba.

Lumshe ido yyi jiki ba kwari yanufi ciki dan duk wata iron sha'wartace ta motsa masa amma bayason takurata har taruk'a masa kuka,dakyar yasamu yyi bacci.


da misalin karfe 9:30pm Kawu bala ne da alh jamilu ,zaune suna mgn a get House dinsa,bala yace to kaji irin cin mutuncin dayayima na acikin bainar jama'a..

Alh jamilu yyi ajiyar zuciya hade da labartawa Kawu bala ganinsa da yarima yyi d'azun da rana,dg karshe yace meye shawara?

Kawu bala yace duk'o kaji,wata mgn yarad'a masa a kunne wadda nima banjiba...

"" wata dariya suka kece da ita,alh jamilu yace kai gsky ka kawo shawara ,brain dinka naja mutumina,dahar nayi shirin guduwa dg garinnan wlh yau da dare..."

,,,Kawu bala yace ah ah aibbu batun Barin gari muna nan daram,hahahahaha ,sai dariyar bosawa suke..,,,

Washe gari byn yarima yashirya yyi break yakira umma yasanar da ita yadda sukayi da bala ,hade da cewa yanxun xaije yamik'a case d'in kotu,cikin jin dadi umma tace to sukayi sallama.

Part din ammi yaje yagaishe da ita,yafito da kamar yaje gun yasmeen sai yafasa yaje parking space zai dauki mota nan guards dinsa da driver suka nufosa yyi musu alamar ah ah shi d'aya zai fita..

"Motar yashege yaja hade da barin gidan".

Tafiya yakeyi har ya wuce garden din da nanne farkon had'uwarsu da yasmeen ,aisaiyadawo yyi parking yashiga, gun wasu kujeru yazauna yana hangen gun da yahango yasmeen zaune farkon had'uwarsu,lumshe idanuwansa yyi yayi shiru,yafi 30 minit can kuma yatashi yafita...

Dede gun da yayi parking yanufa yana bude murfin k'ofar dg bayansa yayi ance y'allab'ai.. Yana juyowa mutane biyu yagani kafin yyi magana sun maza sun goga masa wani k'yalle bak'i,atake cikin yan d'ak'iku yafita hayyacinsa besan inda kansa yake ba yafad'i,suka jasa suka sakashi moto sukabar gun kasancewar duk gun motocine bbu Wanda yagansu....

Share pl


AWESOME WRITER'S ASSO..🏮

(palace of excitation and pleasant writer's)

YARIMA ASHMAN
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story&written by mmn fareesa

🅿45&46


Wani gidane can karshen gari suka kaisa ,acikin wani d'aki akayasar dashi aka rufe k'ofar dan dama gidan na yan kiddinapping ne duk masu tsaron gidan fuskarsu arufe take ,idanunsu kawai kake gani....
"Acikin gidan Sarki kuwa ", yasmeen ce zaune a waiting parlour na part dinsu,itada Maryam da salim suna fira bbu skul kasan cewar week end ne."
fira suke jefi jefi yasmeen nakallon agogo dan tasan 2:30 pm yarima kedawowa amma har 3:00shiru,koda dg ankira la'asar saita wuce ciki dan yin salla ,shima salim da Maryam suka mik'e hade da cewa yasmeen sun had'e a part din ammi."
Bayan ta idar da sallar ,direct part din ammi ta nufa ,bayan sun gaisa ammi tace oh lfy yasmeen har 4 tagota amma mijinki baidawoba ?ko kinkirasa ne?"
rasa mezatace tayi dan ita batada number yarima,amma saita dake tace eh takira amma bata shiga."
Ammi tace to bara nakirasa ALLAH yasa lfy dai,yasmeen tace ameen, dan itama saitaji wani iri dabaidawoba.
Kiransa ammi tayi amma wayar akashe ,nan dai sukayi shiru dukda dai basu yarda lfy ba dan bai kaiwa har haka baidawo gidaba."
Koda ammi taga 6:00pm tayi ,ai asukwane ta nufi part din me martaba ta sanar da shi hankali tashe."
nan akakira guards dinsa ana tambayarsu ko sunsan gun dayaje yau ?"sukace ah ah ai gsky yace kada Wanda yabiyosa,Sarki yasaka akirasa amma duka layikan akashe,nanfa gaba d'aya gidan Sarki kowa hankalinsa tashe yake ,musammun ammi ,yasmeen kuwa kuka tasakawa ammi ita afitomata da mijinta.
"ita kanta ammin hawayen take dan duk a y'ayanta bbu Wanda yashiga ranta kamar yarima.
" anagama isha'i Sarki yyi report a police station da kafofin sadarwa."
Aiko nan gaba d'aya anguwar Sarki da wasu anguwarni zuwa garin bauci aka dauka wai annemi ,barrister yarima Ashman ba'agansa.
Umma natsakar gida taji aredio,hankali tashe takira yasmeen ,yasmeen na kuka tace eh umma ba'asan inda yakeba tun safe dayafita be dawoba,umma tace harfa waya munyi dashi da safe,anya ba makiyansa bne yasmeen? "
Tace k'ila umma ALLAH ne mafi sani,nan umma tace insha ALLAH ,ALLAH zai karesa kiyita addua da sallar dare kikai kukanki ga ubangiji,nima zantayi insha ALLAH ko wane hannu yake zaisami kariyar ubangiji..
Yasmeen tace to umma zanyi nagode sukayi sallama."

Babu bata lokaci duk wasu masallatai addua akema yarima dan kowa yasan shi mutumin kirkine mai son talakawa,addua kawai da saukar alkur ani ake masa ,wasu har kuka suke ,dan rasa irin yarima acikin wannan zamani hasarace babba ga al,umma,kowa yabansa yake yana addu ar ALLAH yatsaresa aduk inda yake..,,,

*******
Yarima kuwa bai farkaba sai gab da magrib,kafin ya bude idonsa yaji mgn hade da dariya,atake komai yadawo masa ,salati yaketa maimaitawa ,yaki bude idonsa."

,,,muryar Kawu bala da alhj jamilu yaji suna cewa,amma ai antabbatar mana cewa bazaikai mgrib ba zai farka.,,,

Alh jamilu yace eh hakane, inma yamutu me ruwanmu,kawai inyafarko ,mukarbi number Sarki aturamasa text cewa yana gun gummu,sai ankawo milion150. Tukum mubadasa..

Kaga in sun bamu saimu kashesa mugudu......dariya suka sheke da ita..

Yarima kuwa shiru yyi,duk yanajinsu,kaf Saida yagama jin tukum yafara motsa kafarsa dake d'aure da iggiyoyi.

da sauri su Kawu bala da alh jamilu suka saka safar fuska,suna kallonsa.

"Bude idonsa yyi ,kallo d'aya yyi musu yaganesu,amma dayake yafisu brain aisaiyyi pretending da cewa ,subahannallahi ,Ku suwanene Ku?mekukeso aguna ,cikin wata murya alhj jamilu yamik'a masa waya yace kasakamana number mahaifinka.

Yace Kuyi me da ita?

Yace kasaka mana ,ko in yankemaka harshe, nan yakarba yasaka,bala yakallesa da jajayen idanunsa yace bamuson komai dg gareka,kudine kawai za'a bayar mu maidaka gd ,yana fadin hakan suka fita shida alhj jmilu...

Yarima innalillahi wa inna ilaihir raju un kawai yake maimaitawa,dan yasan indai suka kashesa to kwanansa ne yakare kuma bazaiji haushiba sbd adalilin gaskiyarsace hakan tafaru,inkuma yanada rabon shan ruwa ko ta halin k'ak'a saiyafita,kuma yana fita acigaba da case din dan indai akan gsky ne to yanxunma yafara yin gsky a aikin sa...

"" suna fita, alh jamilu yarubuta taxt kamar haka."

Yarima!
Yana gunmu,saikunbada naira million 150 tukum mu badasa
Zamu kiraku anjima inkukayi yunk'urin saka yan sanda zamu kasheshi, kuma zamu fad'i gun da zaku aje kudin.......

Yana gamawa yatura, suka kece da dariya...

Maimartaba da familyn sa harda yasmeen ,duka a fada anata jajanta lamarin gakuma can jami an tsaro suna nasu aikin,kawai taxt yashigo wayar Sarki,da sauri maga takarda yaxube hade da cewa ALLAH shitaimakeka mai martaba sarkin talakawa adali ga sako,inkayi umarni ,aikatawa ne nawa akaranta?

"Sarki yad'aga kai alamar eh".

Maga takarda yyima waya kuri,kowa yamaida attention dinsa agunsa dan jin me xaice....?

Share pls


AWESOME WRITER'S ASSO..🏮

(palace of excitation and pleasant writer's)

YARIMA ASHMAN
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story &written by mmn fareesa


🅿47&48


Ahankali maga takarda yyimusu bayanin komai da aka rubuta..
"salati kawai kowa keyi hade da tsantsar tausayin yarima".
Sarki kuwa yau bbu batun sarauta tashi yyi yana inna lillahi wa inna ilaihir raju un kawai yake maimaitawa yana zagaye fada."
Yasmeen kuwa kuka ta fashe dashi dan sai yanxun tagane cewa tabbas tashak'u da yarima gashi ayini guda dabata ganshiga ko abinci takasaci ,hawaye kawai take amma azuciyarta tana wani zargi.
Ammice itama tana hawaye takama yasmeen tana rarrashinta suka nufi part din ta sbd xata dawo suyi mgn itada Sarki."
Sageer kuwa k'uri yyi wa yasmeen da ido yana kallonta harsuka fice,wani irin tausayinta yaji,dan ganin dayayi musu itada yarima azatonsa suna matuk'ar son junansu.
"nan kowa ya watse dan xuwa yin nafilfili da addu a akan ALLAH yatsare yarima", Sarki kawai da mama aka bari wato hjy rahama dan itakeda girki."
Ammi kuwa rarrashin yasmeen taitayi da ban baki had'e da lallabata taci wani abu dan ammi na lura da ita tun break bata sake cin komaiba ,kasancewar sai 4take lunch kuma a time d'in aka fara jajan yarima."
Yasmeen kuwa catayi bazataciba,ita ba abincine gabantaba,tayidai shiru",jiki a sanyaye ammi a batta a part din ta nufi na Sarki dan suyi mgn.
"tana zuwa tasami Sarki zai tada sallah,nan tace abban yarima yanxun meye mafita?"
Sarki yace insha ALLAH zai fito lfy,inaji ajikina duk inda Ashman yake to tadalilin gskiyarsace hakan yafaru,kuma koya fito zai cigaba da tsaya akanta.
Kije kigayawa ubangiji ,dan duk masallatai ance anata masa addua da saukar alk'ur ani nima yau bazanyi bacciba insha ALLAH zankai kukana gun ubangiji.
"nakira number dasuka turo text message da ita amma akashe,muna nan munata jira ko million 200sukace sai abasu dan ceton ransa...
Ajiyar zuciya ammi tayi ,jiki asan yaye tace to bara natafi, ALLAH yasa kada su cutar mana dashi.
Sarki yace ameen tafita yakabbara sallarsa.";;;;;


"" tana zuwa tasami yasmeen kan prayer mat tana sallah ,ga alk'ur'ani gefenta da casbi.,,,

Wani irin tausayinta had'e da k'aunarta taji,azuciyar ta tace lallai yarima yadace da mace ta gari,yah ALLAH katsaresa aduk inda yake.lallai koda yarima yamutu bazata bari yasmeen tasubuce musuba dole ta auri wani dg cikin y'ayan gidan,wata zuciyar tace bazaima mutuba sai yaga y'ayansa hardama jikoki,da Wannan tunanin ammi ta wuce toilet tayi arwallah taxo ta tada sallarta.,,,

Haka kuwa ammi da yasmeen suka kwana kai kukansu gun ubangiji,Saida sukayi sallar asuba tukum bacci barawo yyi gaba dasu....


************
6angaren yarima kuwa ,har akayi isha 'I yana a d'aure ,sai gurin 8:30pm akazo kamasa wani galbaranren abinci da pure water 2 ,ko kallon abincin beyiba ya juya Kai had'e da cewa kukwanceni nayi sallah..
Wanda yakawo abincin bece komai ba yafita Jim kad'an yadawo da shida wasu katti6 suka kwance yarima had'e da nuna masa toilet din dake cikin d'akin nan yashiga yakama ruwa had'e da alwarla yazo yakalli Gabas yafara rama sallolin dke kansa har xuwa isha'i.
Yyi nafilfili da shafa'i da wutiri sannan yyi adduar samun kubuta dg hannun wad'annan azzaliman..
sannan yatashi,kuma duk kattin nan suna kallon sa ,cikin wata murya sukace ga abinci yaci,ruwa 1kad'ai yafasa yasha shima sbd k'ishirwa amma badan yanasoba,ya ce bazaici abincinba,kamasa sukayi suka d'add'aresa kamar d'azun."
suna fita yyi shiru yana tuna tashin hankalin da family nsa zasu shiga insuka sami lbrin halin dayake ciki,yasandai ammi zatashiga damuwa sosai kuma yasan xata masa adduar dama danginsa baki 'd'aya."
Tunawa yyi da yasmeen ,afili yace koyazataji intasami labari?,koxata damune?wata zuciyar tace bazata damuba sbd ta tsaneka.... Lumshe ido yyi yacigaba da hailala da tahamidi..


,,,washe gari tun da safe sukazo kamar jiya suka kwancesa yyi sallah suka sake dauresa dan yak'icin abin Karin kumallon dasuka kawo masa...,,,

Agidan Sarki kuwa sai gurin 9:00am su ammi da yasmeen suka nufi fada,idanun yasmeen duk sun kumbura sbd kuka da rashin bacci..

"Suna shiga suka sami Anty lubna yayar yarima,da hanan sai sameera sunxo sai kuka suke Sarki na kwantar musu da hankali akan za a maidosa."

Wayar Sarki tayi k'ara ,maga takarda yaduba da sauri yace ALLAH yabaka yawan rai number da aka turo sako ve,da hanxari Sarki yakarbe wayar had'e da d'agawa..

"" alhj jamilu dke zaune gaban yarima shida Kawu bala cikin canxa murya yace kunshirya zaku bayar da abinda Muka buk'ata?"

"da sauri Sarki yace eh."

Yayinda kowa yyi tsit a fada anajin maganar alh jamilu kasancewar Sarki a hands free akasaka wayar.

Alhj jamilu yacigaba da cewa inkuka wuce yau Baku kawoba xamu kasheshi ,da sauri Sarki yace ah ah dan ALLAH kada Ku cutar mana dashi ko yanxun kukeso zamu kawo kuma bazamu saka police ba a case d'in...

"" wata dariya alh jamilu yakece da ita azuciyarsa yace hmm yau nike mgn da Sarki haka bbu ladabi da fadane danasha bulalai.

Wayar yakarawa yarima akunne Wanda yyimusu k'uri da ido yana sauraronsu,amsa yyi yace da sauri yace abbana!

Sarki yace ashimanuna,dan duk sadda Sarki yaso nishad'i da hakan yake kiransa,yace basuyimaka komaiba ko? Yace ah ah Abba ina amminah?

da sauri ammi ta matso ta karb'i wayar had'e da d'agowa tana kallon yasmeen dke hawaye,cikin tausayinsa tana hawaye tace my son gani kaji kana ran ammin ka da sauran yan uwanka baki daya insha ALLAH zakafito lfy ,hawaye yarima yaji na tausayin amminsa ,da wasu banxaye suka d'aga mata hankali hartake xubbada hawayenta,lallai wlh duk sadda yafito su bala da alhj jamilu kashinsu yabushe...

"Ahankali yace amm I ina yasmeen?

Kallon yasmeen dke kuka ammi tayi tace gatanan bataci batasha sai kuka kwana tayi tanamaka addua batayi bacciba wlh da sauri yace ammi bata wayar......

" alhj jamilu dake saurarensu yyi saurin kwace wayar yakashe."yana dariyar mugunta,yarima jiyayi da ace ba ad'aure yakeba da saiyawa alhj jamilu shak'ar da yakasheshi har lahira kuma yakashe banxa...

Ammi da wayar ke hannunta ,d'it taji alamar ankashe wayar...

Kuka yasmeen tasaki maicin rai ...afusace Anty lubna tace dallah malama yimana shiru da wannan kukan munafurcin naki na kar.... Kallon da ammi tayi mata yasakata yin shiru dan dama ammi tagama gane lubna batason yasmeen amma ta yi alk'awarin hankali ya kwanta xata take mata birki..

Sarki kuwa tsawa yyiwa lubna yanacewa da fadanki xataji ko kuwa da rad'ad'in batan mijinta ,ki kiyayeni wlh zan sabamiki..

,,,dukawa tayi tace ALLAH yahuci zuciyar ka,sarkin kirari yace tuba take ALLAH yabaka yawon rai ,nan Sarki yace kowa yatafi yasallamesa,illah sageer.

Bayan duk an watse Sarki yakalli sageer yace kuje kaida security a bank kucuro kudin Ku kawomun nasaka akai musu k'ila da yardar ALLAH su badasa.

Cikin girmamawa sageer yace to ,hade mik'e wa yatafi dan bin umarnin Sarki...

Share pls


AWESOME WRITER'S ASSO..🏮

(palace of excitation and pleasant writer's)

YARIMA ASHMAN
🐾🐾🐾🐾🐾🐾


Story & written by mmn fareesa

Wannan shafin nakine my sweet sister hauwa'u Usman lado (Jidda) kiyi yadda kkso dashi ngd da k'okarinki akan wannan novel ina mugun jidake irin totally din nan.😍😍


🅿49&50

babu bata lokaci sageer befi 40minit ba da fita ,yadawo shida security da kudin ,nan Sarki yasaka waziri da driver sukai kudin inda sukace a aje musu.
"haka kuwa akayi suka kai,amma basuga yarimaba ,suka tafi .
Suna tafiya Kawu bala da alh jamilu dke labe suka fito had'e da d'aukar kud'in."
Basu tsaya ko inaba sai get house din alhj jamilu.
"cikin jin dadi had'e da murna alhj jamilu yace abinda za'ayi shine mu aje kudin nan sai angama komai saimu kasafa abunmu!
bala yace eh hakane amma nidai abani ko dubu Dari 5nayi hidima ,alhj jamilu yace to had'e da xuge jakar yabashi.
dariya suka shek'e da ita."
Bala yace da naso mukashesa ,amma ga shawara,musaka ayimasa allurar dazai manta komai yakoma yaro sai abinda aka koya masa inaga inmukayi hkan baza'a zargemuba.
Alh jamilu yace eh gsky ne ,amma kacika macuci ,bala yyi dariya yace muncika macutadai.
Nan Alh jamilu yace kaga bayan yafito sai kaje kasaka adole yasaki yasmeen ka auramun ita tunda shine gatanta kuma mungama dashi,nikuwa nace lamanta da akwai ubangiji."
bala yace eh ai wlh sai Mariya tagane shayi ruwane aguna zata sani ,amma mubari xuwa jibi zankawo doctor yyi masa allurar sannan saimu kaisa gun da za'a zo adaukesa.
"dariyarsu suoa cigaba da yi abinsu"


***** **** *****
Acikin gidan Sarki kuwa tun sadda akakai kudin suke sauraren xuwan yarima amma shiru.
Duk sun damu har Sarki yakasa hakura yakira number su amma akashe ,nan Sarki yace bakomai ubangiji yana tare da su ,sucigaba da addu a.
"Haka kuwa akayi suka cigaba da yi masa addu'oi."
Amma shiru ba labari har akayi kwana2 dakai kudin hakan Yakama kwanansa3 kenan .
Yasmeen gaba d'aya tayi baki tarame tayi zuru zuru aikinta ,sallah, Karatun kur'ani ,kuka,aikinta kenan ,akuma ranar kwana ukkun da safe ummanta tazo tayimusu jaje ta tafi gd.
duk Wanda ka kalla agidan Sarki to baya cikin kwanciyar hankali....

____________________
da misalin karfe 12:30 pm balane yakutsa kai gidansu yasmeen, bbu ko sallama,kamar yadda yasaba....

Mariya! Mariya!! Mariya!!!

"Yana kwalawa umma kira."

Umma dke kuryar daki ,tajisa Saida gabanta yafadi, hartafito ta tuna abinda yarima yace ,da sauri ta d'auko na urar takunna had'e da dasakawa a hijab dinta ta fito tsakar gd...

"" sama da k'asa bala yakalleta yace to munafuka ,ke har kin isa kija dani ,wai har kituromun wannan yaron kega mai suriki ko?"

Hmmmmm hahahahaha to yanxun yana ina ?

Aibari kiji ni bala nafi karfin ajadani wlh dan duk Wanda yaja dani ,hmmm saidai wani bashiba.

"Kinturamun surikinki ,wato kuna zargina ko?"

To kidaina zargi ma bbu tantama Nina kashe k'anina amadu nakashe banxa, kiyi abinda kka gadama dan Wanda kike tak'ama dashi ma ,yanxun haka ba'an inda yakeba,bbu Wanda zakigaya mawa ya yadda cewa Nina kasheshi...

"" cikin kuka umma tace ALLAH ya isa tsakanunmu da kai kafitarmu dg gida kona taramaka jama'a .""

Murmushi yyi yace yanxun kuwa dama burina, na amaye abinda ke cikina,amma kisani bawai natafi kenanba ah ah zandawo ,yana fadin hakan fuuuuuiuuuu yafita dg gidan....

"Ajiyar zuciya umma ta yi ,afili tace Alhmdllh madallah ai inkasan wata bakasan wataba,amma anya ba akwai saka hannunsaba akan batan yarima....

Bala nafita yakira alhj jamilu yace yazo yasamesa agd suje sutaho da doctor yyi wa yarima allurar,yace to ..

Babu jimawa alhj jamilu yaje yadauki bala da mota sukaje suka dauki doctor, nan suka nufi karshen gari...

Bangaren yarima kuwa bawan ALLAH yyi duhu yarame acikin kwana ukkun nan,dan tunda yazo ruwa yake sha ..

Ayanxun haka zaune yake ,yana tunanin gd da yasmeen wacce ammi tace masa batacin abinci saikuka, kuma wai kwana tayi yimasa addua,azuciyar sa yace wayyo bewar ALLAH nasan tausayina taji,ALLAH Sarki indai nakubuta bazan sake batamata raiba,yafad'a had'e da lumshe ido, dan bbu wani karfi atare dashi sbd yunwa da galabaita,karar bude k'ofa yaji ,juyowa yyi yaga me kamasa abincine,atake ALLAH yasa wata dubara ta fad'o masa..

Kallonsa yyi yawani rufe ido yace kwanceni nashi ga bayi gudawa nake,har xai juya kuma sai yadawo. Yaduk'a ya kwancesa .

" yarima na d'agowa yyi saurin kaimasa wani wawan punch a wuya atake yasulale k'asa sumamme."

Cikin hanxari yacire kayansa ,yacire na mutumin yasaka harda safar fuskar da rufaffun takalmi,sannan yadauresa yafito dg dakin ..

Yana fitowa yahango kattin nan majiya karfi sunkai su 20suna xagaye da gidan ,nan yanufi get,wani yace yah babah sai ina ?

Cikin adduar samun nassara da yarima keyi azuciyarsa yacanxa murya had'e da cewa eh mutumin waya zanyi bbu net work aciki ,ko ina zansamu ,katon yace inkafita kamik'e kadan ,wato hanyar dazata sadaka da cikin gari ,anan zaka sami net work nima scan nake samu ...

To yarima yace ,had'e da bude get yafito,adedenan kuma alhj jamilu ya yi horn dan sushiga yanxun a yiwa yarima allurar.

Alhj jamilu yakalli yarima dake shirin wucesu yace kai babah ina zuwa yanxun ,bacin kasan damun yiwa yaronnan allura Ku xaku kaisa gun da za'a daukesa?gashi kafito da safar fuska bacin kana waje bacikin gidaba....

Share pls


AWESOME WRITER'S ASSO..🏮

(palace of excitation and pleasant writer's)

YARIMA ASHMAN
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

🅿51&52

"" cikin dakiya yarim a yace eh zancire yanxun waya zanyi Ku shiga yana ciki."
batare da sundamuba ,sbd burinsu su aiwatar ta bak'in nufinsu suka cinna hancin motar cikin get din . parking sukayi suka fito suka nufi cikin d'akin

Please Login or Register in order to submit comment