Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasarorin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya cimma a rayuwarsa abu ne da bai da iyaka, dan haka za mu taqaitu da wannan a matsayin misali.


NASARORINSA GA AL’UMMAH :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya cimma ximbin nasarori ta fuskoki da dama na kawo sauyi a al’ummar da yake rayuwa a cikinta, mafi yawan nasarorin Shaikh Zakzaky (H) nasarori ne na baxini, nasarori ne na raya zukata da canza tunane-tunanen al’umma da wasu I’itiqadodinsu iri-iri zuwa sahihan tunanuka ta fuskar addini.


Amma tattare da haka, akwai ximbin nasarori na kawo sauyi a zahirin rayuwar al’umma da ido zai iya shaidawa ta fuskar addini, al’ada da “Social Issues”, wanda Shaikh xin ya samar ga al’ummar da yake rayuwa a cikinta, ga wasu kaxan daga ciki.


SANYA HIJABI : Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ce ta zo da sanya Hijabi ga mata musulmi a Nijeriya, domin kafin Da’awarsa, ba wanda ya san mata da sanya Hijabi a Nijeriya. Tun bayan Jihadin Shehu Xan Fodiye (RA) mata suka watsar da sanya Hijabi. Duk wanda ya wanzu kafin bayyanar Shaikh Zakzaky (H) shaida ne cewa bai ga sanya Hijabi a gidansu ba. Mata sun fara suturtuwa da kammalallen Hijabi ne sakamakon Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).


MATA A ADDINI : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara shigo da mata fagen addini a wannan nahiya. A baya a wannan al’umma tamu ba a san yin hidimar addini da mata ba, abin da kawai aka sani shi ne fitar tsofaffin mata tuguf-tuguf zuwa masallacin juma’a da na Idi. Amma sakamakon Da’awar Shaikh Zakzaky (H) yanzu duk wata hidima ta addini da mata ake yi, kama daga wa’azozi, tarukan qarawa juna ilimi, muzaharori, I’itikafi da duk wata hidima ta addini. Sannan Da’awarsa ce ta fara ba matan aure ‘yancin ci gaba da karatun addini daga gidajen aurensu, shi ya fara samar da makarantar mata kafin Wahabiyanci ya mamaye fagen daga baya.


MUZAHARA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya koyawa al’ummar musulmin wannan nahiya yin Muzahara ta fuskar addini. A baya ba a san yin Muzahara don nuna farin ciki, ko tallata wani abu na addini, ko dan nuna rashin yarda da rashin amincewa kan wani abu da ya shafi cutar da Musulmi ko Musulunci ba. Shaikh Zakzaky (H) ne ya fara yin Muzahara da sunan addini a tarihin Nijeriya, yanzu ta kai ga kusan duk qungiyoyin addini suna yin Muzahara ko gangami dan nuna farin ciki (kamar Muzaharar Maulidi), ko dan nuna rashin amincewa da tozarta addini, ko dan bayyana wata manufa tasu.


I’ITIKAFI : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara yin I’itikafi a Masallaci a watan Ramadan a tarihin Nijeriya. Tun Shaikh yana matashi yake shiga I’itikafi shi kaxai a masallaci. Kafin ya aikata I’itikafi a aikce ba a san I’itikafi a zahiri ba, an dai san bayanin I’itikafi a babuka na littattafan Fiqihu. Dan haka, duk wanda yake I’itikafi a Nijeriya ya kwaikwaya ne daga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da almajiransa. Wannan wani abu ne sallamamme da ba wanda ya jahilce shi sai mai qarancin masaniya da rashin lura da al’amura.


KARE ANNABI (S) : Kafin bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), al’ummar wannan nahiya ba ta san hanyar da ya kamata a bi wajan kare martabar Manzon Allah (S) ba. Ko da wani ya ci zarafin Annabi (S) musulmi sukan ji takaici ne kawai a ransu, amma ba sa iya yin wani katavus na nuna rashin amincewa da hakan. Hatta a farkon lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara kare martabar Annabi (S) ta hanyar nuna rashin amincewa da zagi ko cin zarafinsa, sai da ya fuskanci tsattsauran martani daga waxanda ake kallonsu a matsayin malamai da jagororin addini.


A nahiyar Afirka ta yamma baki xaya, Shaikh Zakzaky (H) ne ya koya wa musulmi yadda ake kare martabar Annabi (S) ta hanyar mayar da martani, rubuce-rubuce, da Muzaharorin Allah wadai na nuna rashin amincewa. Ta haka musulmin wannan nahiya suka koyi kare martabar Annabi (S) da martabar addini idan an tava shi.


HAXIN KAI : Kusan kowa shaida ne cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi ta fafutukar wayar da kan al’ummar Nijeriya wajan ganin sun fahimci juna tare da sanin tushen matsalarsu maimakon gaba da faxace-faxace da juna. Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta fara yaxuwa ne a daidai lokacin da Wahabiyanci ke ganiyar mamaya da yaxa munanan aqidunsa na kafirta musulmi da dasa gaba da qiyayya a junansu. 


Shaikh Zakzaky (H) ya yi ta fafutukar kawar da gaba a tsakanin musulmi da kuma hana faxace-faxacen qabilanci da na addini da ya addabi al’ummarmu. Bayan tsawon shekaru ne Shaikh (H) ya yi nasarar daqile habaqar gaba tsakanin Izala da Xarika, da kuma kashe-kashen qabilanci tsakanin Musulmi da Kirista. Ta kai ga Shaikh (H) ya samar da “Makon Haxin kan Musulmi” wanda ake haxa malaman musulunci na qungiyoyi daban-daban su yi jawabai. Da kuma bikin “Sallah Feast” wanda ake haxa shugabannin Kirista da na musulmi waje xaya su tattauna don samun kusanci da fahimtar juna. Ta haka Shaikh (H) ya yi nasarar kashe kaifin hargitsin Qabilanci da na Addini da Siyasa da ma rage gaba a tsakanin al’umma.


DOGARO DA KAI : Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta koyawa qungiyoyin addini dogaro da kai wajan qoqarin samar da kuxaxen gudanar da ayyukansu da kansu. Domin a baya qungiyoyin addini sun dogara ne kacokam ga tallafin gwamnati da gudunmawar gwamnatoci da qungiyoyi na qasashen waje wajan tafiyar da al’amuransu, sam ba su iya yin abu da kansu ba, komai yi musu ake yi, a gina musu Masallaci, a saya musu motocin zuwa wa’azi, a ba su kuxin gudanar da taruka da sauransu. Malamai sun zama Banbaxawa yaran masu mulki, suna jurewa kowane wulaqanci daga mahukunta don su ci gaba da samun abin da za su rayu da shi.

Sai Shaikh Zakzaky (H) ya zo da Da’awar da ba ruwanta da kwabon wani, ba ta buqatar tallafin gwamnatin qasa balle na qasashen waje, ba ta buqatar gudunmawar masu kuxi balle na qungiyoyin qasa da qasa. Da’awa ce da ta dogara kacokaf da gudunmawar membobinta kaxai, duk abin da za a yi za a haxa taro sisi ne daga membobi a yi shi, ba a neman gudunmawar gwamnati ko ta qasashen waje. Wannan ne kuma sirrin da ya ba Da’awar Shaikh Zakzaky cikakken ‘yanci, ba wani mai ikon juya Harka Islamiyya daga waje ko daga cikin gida, domin bai da tasirin da zai iya sawa a yi wani abin da yake so, ko ya hana yin abin da ba ya so.


RAYA MASALLACI : A bisa al’adar al’ummar wannan nahiya, masallaci wurin yin Sallah ne kawai, ba a komai a cikinsa sai Sallah. Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara raya masallaci ta hanyar yin ayyukan addini a cikinsa, a lokacin da yake xalibta a Jami’ar Ahmadu Bello ya maido da dukkan tarukan qungiyar MSS zuwa masallaci.


A wani jawabinsa yana cewa;- “Ni na tabbatar ba mun gani a aikace a wajan wani bane, mun karanta ne a littafi muka ga cewa a lokacin Annabi (S) masallacin Annabi nan ne cibiyar addini, a nan ne Annabi (S) yake koyarwa, a nan ne yake wa’azi, a nan yake alqalanci, a nan yake sasanta tsakanin mutane, a nan yake karvar baqi daga qasashe daban-daban. Wato masallaci a lokacinsa cikakkiyar cibiya ce ta dukkan ayyukan addini, a nan ake yin taro a yi Mashwara a tattauna shawarwari, haka nan ma tattauna dabarun yaqi da komi da komi duk a masallacin Annabi (S) ake yi a wancan lokacin.


“To, sai muka ce ai a karatu muna karantawa (cewa) komai a zamanin Annabi a masallaci ake yi, amma mu ba mu yin komai a masallaci (sai Sallah). Sai muka ce to harkokin da muke yi na addini mu koma da shi Masallaci. To, sai muka qira lacca irin wanda za a gayyato Malami a ba shi wani Maudhu’i ya yi magana akai, sai muka yi a masallaci, to (ai kuwa) sai muka sha surutu, wai yin lacca a masallaci ba a ‘Assambily Hall’ ba! (Saboda su mutane ba su saba da ganin haka ba a wancan lokacin)”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 71-72).

Hatta wa’azin da yanzu ake yi a kusan dukkan masallatai ranar Juma’a kafin zuwan liman, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara assasa shi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kafinsa ba a san da wannan ba, wanda a yau za mu ga cewa masallatai da dama har da na Wahabiyawa suna yi. Amma yanzu saboda yadda abin ya zamo jiki sai a xauka tun asali ma haka abin yake, alhali a 70s ne Shaikh Zakzaky ya sunnanta hakan.


RAYA SUNAYE : A bisa al’adar al’ummar wannan nahiya (duk da kasancewarsu musulmi), amma ba su cika qiran mutane da cikakkun sunayensu na addini ko na yanka ba, sun fi qiransu da sunaye na al’ada. Za ka ji suna qiran Ibrahim (Iro), Idris (Idi), Usman (Manu), Abdullahi (Audu), Abubakar (Garba), Dawud (Dauda), Adamu (Ado), Salihu (Salele), Mahmud (Mudi), Muhammad (Mamman), Zakariyya (Ya’u), Sulaiman (Sule) da sauransu.


Haka abin yake ga mata, Ruqayya (Rakiya), Bilkisu (Balki), Maimunatu (Munari), A’ishatu (A’i), Khadija (Dije), Zainab (Abu), Maryam (Mairo), Hajara (Hajjo), Fatimah (Fatsuma), Lauratu (Laure) da dai sauransu. Haka nan sunan mutum na al’ada yakan shafe asalin sunansa na yanka daga samuwa, sai ka ji sunan mutum Sallau, Mati, Lado, Tanimu, Gambo, Barau, Gagare, Rabe, Makau, Kwasau, Datti, Xandunawa da sauransu. In kuma mata ne ka ji Kyallu, Kande, ko ka ji mutane xauke da sunayen ranakun da aka haife su irinsu Xan Liti, Xan Jummai, Asabe, Ladi, Talatu, Larai, da sauransu, ko ka ji mutane xauke da sunan lissafi da dai makamantansu.


Amma albarkacin wayewar addini musamman qarqashin tasirin Da’awar Shaikh Zakzaky (H), yanzu duk waxannan abubuwa suna kwaranyewa sannu a hankali, galibi yanzu ana kiran yara ne da sunayensu na addini ba na al’ada ba. Sannan ana sa wa yara sunaye da inkiya masu daxi da ma’ana, musamman yadda Shaikh xin ya koyawa al’umma sa sunayen jikokin Annabi (S) da ‘ya’yayensu, kuma abun ya ratsa gidan kowa har da Wahabiyawa. Yanzu maimakon sunayen su Mati da Lado, za ka riqa jin sunaye ne daxaxa, irinsu Al’ameen, Haneef, Munzir, Ma’aruf, Faisal, Sadiq, Arafat, Zahra, Yaseera, Afrah, Humaira, Sajida, Muslimah, Suhaila, Zeenat da sauransu.


YAXA MANUFA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya fara koyawa musulmin wannan nahiya yadda za su dogara da kansu wajan bayyana ra’ayoyi da manufofi da aqidunsu da kansu ga al’umma ta kafofin yaxa labarai da na sadarwa, ba wai su shantake ta hanyar dogaro da kafafen yaxa labarai na gwamnati da masu zaman kansu su tallata su ba, domin kayan aro ba ya rufe katara, kuma maqiyinka ba zai ma kyakkyawan wakilci ba. Shaikh (H) ya nunawa qungiyoyin musulmi muhimmancin samar da kafar sadarwa ne ta hanyar samar da jaridar ALMIZAN da Mujallar GWAGWARMAYA, waxanda ke bayyana saqon Da’awarsa da manufarta, don al’umma su san manufar Da’awarsa daga bakinsa ba daga bakin wasunsa ba, daga baya an qara samar da jaridar “POINTER EXPRESS” da Mujallar “MUJAHIDAH”.


Sakamakon wannan darasi da Shaikh Zakzaky (H) ya nuna, sai ga qungiyoyin addini su ma sun shiga koyi da shi, Wahabiyawa suka samar da jaridar “AS-SUNNAH” da Mujallar “SAUTUS-SUNNAH”. ‘Yan Tijjaniyya suka samar da Mujallar “AL-QIBLAH”. ‘Yan Qadiriyya suka samar da Mujallar “SAUTUL-WAHDA”. ‘Yan Jama’atut-Tajdeedul-Islam suka samar da Jaridar “ATTAJDEED”. ‘Yan Salafiyya suka samar da jaridar “ATTATBEEQ”. ‘Yan Shi’a Taqleedi suka samar da Mujallar “AL-MAUZOON”. ‘Yan Shi’a ‘Commercial’ suka samar da jaridar “AHLUL-BAITI” da dai sauransu. Wannan yana nuna yadda Shaikh Zakzaky (H) ya cimma nasarar dasa ingantattun tunanuka a cikin al’umma.


RAYA SUNNONI : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi tasiri sosai cikin al’umma a fagage da dama, musamman a fagen raya wasu sunnonin da aka yi watsi da su, misali; Shi ya raya al’amarin sanya Zobe, wanda bayan Istibsari ta kai ga maza suna sanya zobba masu alfarma. Shi ya raya taron addini da ake qira “Goron Sallah”, duk wata qungiyar addini da take taro da sunan ‘Goron Sallah’ ta kwaikwaya ne daga gare shi. Shi ya raya yin Tafsiri ba tare da Alaramma mai jan baqi ba, kafinsa ba a san yin hakan a matsayin Sunnah ba. Shi ya raya ziyarar malamai mabanbanta ra’ayi ga junansu, kafinsa ba a san malamai da ziyarar juna in ba ‘yan qungiya xaya ba. Shi ya raya batun Shariftaka, har ta kai ga yanzu al’amarin Shariftaka ya zama muhimmin al’amari a cikin al’ummarmu.


Shi ya raya Maulidin Annabi (S) ta hanyar qirqiro yin Muzahara a ranar, wanda yanzu ya zama bikin addinin da ya fi kowanne armashi a Nijeriya. Shi ya raya mutunta Rawani, domin a baya kowa ma yana naxa Rawani in ya ga dama, amma yanzu an barwa malamai yin Rawani saboda mutuntawa. Kuma ga shi yanzu yana raya maqarbartu da qaburburan mamata, ta hanyar gyara su da qawata su da yi musu ado da kwalliya da fulawowi, ta yadda maqabartun sun soma zama wurin ziyara mai ban sha’awa, maimako yadda a da suka zamo dazuka na ban tsoron Fatalwa, da ramukan Macizai, Veraye, Buragu da qwari.


Wannan sauyi da Shaikh Zakzaki (H) ke ta samarwa a cikin al’umma, yana qara tabbatar da baiwar da Allah yai masa ta musamman. A taqaice, waxannan abubuwa suna daga cikin fitattun nasarorin da Shaikh Zakzaky (H) ya samar a cikin al’umma, madalla da wannan Jagora!

MATSAYINSA A DUNIYAR SHI’ANCI :


Babu tantama ko ja-in-ja game da matsayin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a duniyar Shi’anci, domin memba ne a Majalisar Ahlul-Bait ta duniya, wato (Ahlul-Bait World Assambly). Memba a Majalisar Taqreeb na Mazhabobin Musulunci, wato (The World Forum for Proximity of Islamic Thoutht). Memba a majalisar haxin kan Shi’a ta duniya, wato (World Federation Shi’a Khoja). Memba a majalisar goyon bayan Palasdinawa ta duniya, wacce Dr. Zahra Khumaini ke wa jagoranci. Memba a qungiyar taimakawa Intifadar Palasdinawa ta duniya, wato … Memba a qungiyar kare haqqin xan adam ta musulunci ta duniya, wato (International Islamic Human Right) mai hedikwata a birnin London, sannan shi wakili ne a wasu majalisu da qungiyoyi da dama na duniya.


Kamar yadda ba buqatar tsawaita bayani game da karvuwarsa da martabawar da duniyar Shi’anci ke masa, domin waxannan wasu abubuwa ne da ke bayyane a fili qarara, musamman ga wanda ke bibiyar kafafen sadarwa na zamani.


Misali; A duk lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fita zuwa wata qasar waje, musamman Iran, Iraqi, Lebanon da qasashen Turai, Asiya, ko Afirka, za ka ga irin tarba ta girmamawa, da liyafofin karramawa, da gayyace-gayyacen jawabi, da neman ganawa a keve, da sauran abubuwa na gayar karamci da ake masa, wannan kawai ya isa ya tabbatar da abin da muke faxa.


Wata babbar shaidar da ta bayyana matsayin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a duniyar Shi’anci shi ne waqi’ar Muzaharar Qudus da ta auku a birnin Zariya a shekarar 2014, inda sojojin gwamnatin Nijeriya suka kashe almajiransa guda 33 a lokacin wannan Muzahara, ciki har da ‘ya’yansa guda uku.


Yadda duniyar Shi’a ta tankawa wannan ta’addanci da aka yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya nuna ko waye Shaikh xin a duniyar ta Shi’anci, domin kusan ba wani babban Marja’i a duniya da bai yi Allah wadai, tare da rubutowa Shaikh Zakzaky (H) wasiqar jaje da ta’aziyya ba. Maraji’ai da manyan malaman Shi’a daga kowane sashe na duniya sun rubuto wasiqun jaje da ta’aziyya ga Shaikh, wasu ma sun tado jakadu ne musamman daga qasashensu, inda suka zo takanas ta Kano don jajantawa Shaikh Zakzaky (H), ciki kuwa har da Marja’il A’ala Ayatullah Sayyid Ali Hussain Khamna’i (DZ), wanda ya tado wakili na musamman Ayatullah Muhammad Hassan Akhtari don jajantawa.


Abu na biyu da ya ja hankali ga matsayin Shaikh Zakzaky (H) a duniyar Shi’anci shi ne, yadda manyan Maraji’ai sanannu a duniya suka riqa kiran Shaikh Zakzaky (H) da sunaye na daraja da girman matsayi ta fuskar ilimi, malanta, jihadi da jagoranci, kamar kiransa da Al-Mujaheed, ko Al-Muslih, ko Ayatullah, ko Allamah da sauransu.


Daga cikin wasiqun da Maraji’ai da manyan malaman Shi’a suka kira Shaikh Zakzaky (H) da “Samahatul ALLAMAH Al-Mujaheed Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)” mafiya jan hankali sune na Hujjah Muhsinul Araky, shugaban majalisar haxin kan Musulmi ta duniya, wato “Majma’ul Aalamy Littaqribi Bainal Mazahibil Islamiyyah”.


Sai wasiqar Sayyid Aliy Qadhiy Askar, Amirul Hajji na qasar Iran, kuma Wakilin Sayyid Qa’id kan al’amuran Hajji. Sai wasiqar Ayatullahil Uzmah Alawy Karkany, fitaccen Marja’i a duniya. Sai wasiqar Jami’ar Al-Mustapha ta duniya, wato “Jami’atul Mustapha Al-Aalamiyyah, Lebanon” da sauransu, (duba kwafin wasiqun a shafin Harka Islamiyya na Intanet, ko ka duba Al-Mizan bugu na 1142 shafi na 7, da bugu na 1144 shafi na 5).


Nasabta Kalmar “Allamah” da fitattun Maraji’an duniya da suka cika sharuxxan Ijtihadi suka yi ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta nuna daraja da girman da yake da shi ne a da’irar Shi’anci na duniya, kuma ya nuna mustawar ilimin Mujaddadin wannan qarnin!


Amma abin da ya fi nuna girman daraja da zurfin matsayin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a duniyar xan adam baki xaya, da duniyar musulmi ta wata fuska, da kuma duniyar Shi’a a fuska ta musamman, shi ne, faruwar waqi’ar ta’addancin sojojin Nijeriya na abkawa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da almajiransa a farkon watan Maulidi na shekarar 1437, wanda ya yi daidai da 12-12-2015.


A wannan waqi’ar, wacce aka kashe xaruruwan almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ciki har da qarin ‘ya’yansa guda uku, aka harbi matarsa Malama Zeenatuddeen a wurare da dama na jikinta, sannan shi kansa Shaikh xin aka yi masa ruwan harsashi da nufin kashe shi, amma Allah ya qi xaukar ransa, daga qarshe suka kama shi suka tsare. Wannan abu da aka yi wa Shaikh Zakzaky (H) ya girgiza duniya, wanda nan da nan duniya ta yi Allah wadai da abin da sojojin Nijeriya suka yi, qasashe da dama sun yi tir da Allah wadai, wasu a gwamnatance kai tsaye, wasu ta hannun jakadun Nijeriya da ke qasashensu.


Ta vangare guda kuma, al’ummomin qasashen duniya daban-daban ne suka fito kan tituna don yin tir da Allah wadai, tare da nuna rashin amincewarsu ga abin da aka yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da kuma kira ga gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta sakin shi. An yi zanga-zanga da muzaharori da gangamin ximbin mutane a qasashe kusan 80 na duniya, ciki har da Iran, Iraqi, Lebanon, Indiya, Amurka, Ingila, Denmark, Norway, Afirka ta kudu, Malesiya, Ghana, Phakistan, Mali, Philipines, Kashmir, Moroko, Dubai, Nijar, Yamen, Kamaru, Bahrain, da sauransu. Wannan martani na bai xaya da duniya ta mayar dangane da kama Shaikh Zakzaky (H), ya qara nunawa duniyar girman matsayin Shaikh xin da gayar tasirinsa a duniyar Shi’anci baki xaya.


A jawabi na musamman da shugaban Shi’a na duniya Ayatullah Sayyid Qa’id Aliyul Khamna’iy (DZ) ya yi wa manyan malaman Shi’a a ganawar musamman da ya yi da su a falonsa cikin watan Janairun 2016, ya nuna cewa wajibi ne duniya ta yi tir da abin da ya faru ga Shaikh Zakzaky (H). Ya ce; “Me ya sa al’ummar musulmi su ka yi shiru akan abin da ya faru ga wannan Shehin Malami, Mumini, mai kawo Gyara, mai son Zaman Lafiya, mai haxa kan (musulmi) Shi’a da Sunnah waje guda! An kashe aqalla kusan mutum dubu da ke tare da shi, sannan ‘ya’yansa sun yi Shahada!” (Sayyid Qa’id ya yi wannan jawabi ne ranar 24 ga watan Janairu na shekarar 2016).


KARRAMAWA (AWARDS) DA AKA BA SHI :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cikin muhimman mutanen da aka yi ta karramawa da muhimman kyaututtuka a duniya, an ba shi kyauttuttukan karramawa masu yawa a qasashe da cibiyoyi daban-daban, kaxan daga cikin muhimman karramawar da aka yi masa sune;


NA XAYA : A watan Janairu na shekarar 1980 Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya amsa gayyatar halartar wani taro akan Musulunci a qasar Iran, bayan kammala taron an karrama Shaikh (H) da ganawa ta musamman da Imam Khumain (QS), wanda ke kwance a gadon asibiti yana jinya a lokacin. A qarshen ganawar, Imam Khumain (QS) ya xauki Alqur’aninsa da yake karatu da shi ya ba Shaikh Zakzaky (H) a matsayin kyautarsa ta karramawa gare shi, inda ya umarce shi da cewa; ya je ya kira mutane zuwa ga aiki da Alqur’ani. 


NA BIYU : Gwamnatin mulkin soja ta jahar Kaduna a Nijeriya cikin shekarar 1996 ta karrama Shaikh Zakzaky (H) da “Award” a matsayin mutum mafi tasiri da ya fi kowa son zaman lafiya a qasa. Gwamnan soja na wancan lokacin Kanar Lawal Ja’afaru Isah ne ya jagoranci karrama Shaikh (H) da wannan kyauta, kuma Shaikh Zakzaky ya kafa shaida da wannan “Award” xin a kotu a lokacin da ake shari’arsa a 1998.


NA UKU : Qungiyar Hizbullah da ke qasar Lebanon qarqashin jagorancin Sayyid Hassan Nasrullah, ta karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da shekararriyar Tutar Haramin Imam Hussain (AS). 


Wannan muhimmiyar karramawa ta baqar Tutar da ke filfilawa akan Qabarin Sayyidish-Shuhada (AS) mai xauke da kalmar “Labbaika Yaa Hussain!” an yi ta ga Shaikh (H) ne a shekarar 2012.


NA HUXU : Haramin Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala a qasar Iraqi, ya Karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da shekararriyar Tutar da ke filfilawa a saman Haramin garkuwan Imam Hussain (AS) wato Abul-Fadal Abbas (AS), wanda ake wa laqabi da “Qamaru Bani Hashim”. An karrama Shaikh (H) da kyautar Tutar Hubbaren Abul-Fadal ne a shekarar 2013.


NA BIYAR : Qungiyar tara gudunmawar jini ta qasa, wato “National Blood Transfussion Services” ta karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da “Award” na musamman don jinjina masa da godiya gare shi bisa umartar miliyoyin almajiransa da ya yi da taimakawa majinyata da gudunmawar jini a duk faxin qasar, kuma wannan gudunmawar jini da ximbin almajiran Shaikh ke bayarwa ta dindindin ce a kowace Munasaba ta bikin haihuwa ko juyayin wafatin wani Ma’asumi (AS). An karrama Shaikh Zakzaky (H) da wannan kyauta ne a shekarar 2013.


NA SHIDA : Qungiyar Kiristoci ta Nijeriya wato “Chirisian Association of Nigeria” (CAN) vangaren matasa, a shekarar 2014 ta Karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da “Award” na gwarzon Malami mai qaunar al’umma da samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin ma’abuta banbancin addini.


NA BAKWAI : Qungiyar kula da iyayen gwarazan Shahidai ta Duniya mai hedikwata a qasar Iran, ta karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da kyauta ta “Uban Gwarazan Shahidai”. An shirya babban taro ne a Iran, inda aka gayyaci iyaye da dangin gwarazan Shahidai daga qasashe daban-daban na duniya aka karrrama su. Kuma Shaikh Zakzaky (H) ne ya zamo gwarzon uba a wannan taron, don shi ne ya rasa haziqan ‘ya’yansa uku a rana guda. An karrama Shaikh (H) da wannan kyauta ne a shekarar 2014.


NA TAKWAS : Haramin Imam Ridha (AS) da ke birnin Mashhad a qasar Iran ya karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da matsayin “Hadimin Imam Ridah (AS)”, inda aka ba shi “Award” haxe da koriyar Tutar da ke filfilawa a saman qabarin Imam Ridha (AS), wanda aka tara manyan Maraji’ai don su shaida bikin wannan karramawa da aka yi ga Shaikh (H) a Hubbaren Imam Ridah (AS) a watan August na shekarar 2015.


NA TARA : Haramin Sayyida Fatimah Ma’asuma (SA) da ke qasar Iran, ya karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da shekararriyar Tutar da aka lulluve Hubbaren na qanwar Imam Ridah (AS), a wani qwarya-qwaryan biki a babban ofishin Haramin da ke birnin Isfahan na qasar Iran cikin watan Zulhajji na shekarar 1436, wanda ya yi daidai da qarshen watan August 2015.


NA GOMA : Haramin Sayyida Zainab (SA), da ke birnin Dimashqa a qasar Siriya, ya karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da kyautar Tutar da ta shekara tana lulluve da qabarin Sayyida Zainab bint Amiril Muminin (SA), wanda aka shirya biki na musamman a xakin taro na Mahdiyyah da ke birnin Mashhad Iran don karrama Shaikh xin da wannan Tuta mai alfarma. An yi wannan karramawa ga Shaikh (H) ne ran 20 ga watan Janairu na shekarar 2016, lokacin yana tsare a hannun gwamnatin Nijeriya, wasu almajiransa ne suka wakilce shi a bikin.


NA 11 : Qungiyar kula da al’adu ta qasar Iran mai suna “Iranian Cultural Caravan” wacce ke qarqashin cibiyar “Under The Shade of The Sun”, wacce kuma kula da Haramin Imam Ridah (AS) ke qarqashinsu, sun karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da kyautar Tutar da ke filfilawa a saman Hubbaren jikan Manzon Allah (S) kuma Khalifa na 8 a jerin Khalifofin Annabi (S) na Shari’a (wato Imam Aliyur-Ridah (AS)). An yi wannan karramawa ne ranar Juma’a 04 ga August 2016, kuma duk da cewa Shaikh Zakzaky (H) yana tsare a kurkuku

1 Comments On SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

sss

Please Login or Register in order to submit comment